Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hanya, har kuma nake jin zan iya rabuwa da ita akansa, bama ita kaɗai ba, kowanene gani nake zan iya rabuwa da shi muddin bai samawa Yaya lafiya ba. Na kauda fuskana gefe guda domin bama zan tankawa maganar da tai ba. tana ƙara riƙe hannuna da nake son ƙwacewa tace, "kinga indai akan Yaya'nki ne kwantar da hankalinki, daga yau ba zaki ƙara jin bakina akansa ba. Wannan alƙawari ne na maki". jin hakan yasa na juyo ina dubanta, idan na kalla shin maganartata da gaske ne, ganin na zuba mata ido ina karantar fuskartata yasa tace, "wallahi da gaske nake miki, ni bazan yarda wani ya lalata mana zumuncinmu ba. Tsakanina da shi Allah ya shirye shi kawai, ko ba hakan kike so ba?". na saki fuskata ina murmushi, kamar yanda muke yi ada yanzu ma haka mukai, domin kuwa tafin hannuna ɗaga na bata muka tafa ina faɗin, "yauwa ko kefa, yanzu naga haskenki". sai tamin harar wasa da cewa, "ji min walaƙanci, duk wannan uban hasken nawa baƙi kike ganinsa dama?". Ina dariya nace, "yo da kike wani kaurara hasken naki, ai na bogi ne tunda na bature ne". Ina faɗa cike da tsokana, ina kaucewa biyo ni da tayi. Har ɗaki ta biyo ni muna dariya, Gwaggo na linke kaya ta bimu da ido. Sai dana ɓuya a bayanta ta sami damar yin magana tana duban Farhana.
"ƙalau kuke kuwa?". Farhana na riƙe da ƙugu take ce mata, "wai Gwaggo saboda kuturun walaƙanci ni yarinyar nan zata cewa fari na bature ne". "ai ba ƙarya nayi ba, uban tulin robobin mayukan ɗakinki na mene?". Ina dariyar ina magana kuma cike da tsokana. Gwaggo ce ta juyo ta dube ni, ta wani yatsine fuska kana tace, "kema ai banda Allah ya rufa maki asiri gyatuminki ya ɗauko hasken Sahibina da ba'a san kalar da zaki kwaso ba, da har kike tsokanar wata, ki bar ganin Samari na aikin sunturi akanki duk tabarakin Sahibina kika ci. Ah tou". tai maganar dan ta ramawa Farahana, amma sai taji ba ki ɗayanmu mun sheƙe da dariya, Na buɗi baki nace, "Wai naci tabarakin Sahibinki, Abunda tarihi ma ya nuna shi Sahibin naki Kawu Baffa Sule ma ya fishi kyau, kinga kuwa in haka ne ai da an gani ajikin sauran Ƴaƴan nasa. Kawai dai shi Babana Allah ya zaɓe shi ne, gashi nan santalele kamar balarabe, Shi yasa ake kishi da shi, don ko Sahibin naki da kike koɗawa albarka". Na faɗa ina ƙunshe dariya ta saboda yanda naga Gwaggo na aika min wani kallo mai kama da harara. Gajeran tsaki ta saki tace, "Ki kiyayi ramata Sabina, shi gyatumin naki har kishin mene zanyi da shi, banda aikin wofi na haife shi kuma na kama kishi da shi". sai kuma ta ɗauko mifici ta shiga dukansa a ƙasa tana faɗin, "Kuma In faɗa miki ƙaryar tarihi ya faɗi abin kushewa akan Sahibina Allah ya jiƙansa da gafara. Ke idan a wannan zamanin naku ne ma ai sai na dinga tofe shi da li'ilafi ƙuraishin, ko da yake a wancan zamanin ma me aka fasa, yanda ƴan mata ke tururuwa akansa kamar ƙuda ya sami zaƙi tsabagen tsantsar kyawunsa da farin jini. Amma haka ya miƙe ya dire yace sai ni, haka ya dinƙa bani tabara ana aika min da yasin a gidanmu, Ɗan baiwa kenan wallahi shima Zaɓin Allah ne domin kuwa Allah ya bashi. Ai naga zallar soyayya a wurinsa, Allah sarki Allah yay maka rahma abin ƙaunata". Kawai sai ganin Gwaggo mukai ta fashe da kuka tana matse ido. Niko mai zanyi banda dariya da tafawa harda ƙwalla. "Allah ya jiƙansa, kice Dai Gwaggo kunsha ƙauna ke da Kakanmu". Farhana ke mata wannan tambayar tana ƙunshe dariyarta. "Hmmm". Gwaggo tace tana juyowa ta fuskanci Farhana."amin ƴar aljannah, ai ke kam mutunci ba daga nan ba, ki godewa Allah da baki ɗauko halin ƙawarki ba na rashin kirki". Farhana na daɗa riƙe dariyarta tace,"Gwaggo yau kuma Sabinan taki guda".
Gwaggo ta harari gefena da cewar,"Wannan ai ƙaunar da take min a baki ne kawai... kina ganin ta haka sam bata ƙaunata. Yo banda rashin ƙauna ana zancen marigayi kina dariya saboda ɗibar albarka, ai yau Sabina ta nuna min matsayina a zuciyarta". Ni dai dariya nake kawai  bance mata komai ba, dan yanzu ina ƙara yin magana zata kuma hawa. dama Gwaggo sarkin zuba zance, sai dai idan baku zauna da ita ba, Nan ta hau bawa Farhana Labarin Kakanmu wato mijinta kenan. "ina faɗa miki Farhana ai naga zallar soyayya daga wurin Sahibina, soyayya ba irin ta ƴan yanzu ba irin ta aljanu. Babu irin kalar walaƙancin da ban masa ba amma bawan Allah'n nan haka ya nace yace idan babu ni sai rijiya. ke abokansa har ce masa suke babu zuciya a ƙirjinsa saboda irin wulaƙancin da nake masa. ni kuwa abunda ma yake ƙara ƙona min rai nake ci masa fuska idan naji yana faɗin wai in bani rijiya zai faɗa ko kuma ya rungumi tiransufo ma. idan ya faɗi hakan raina yana sosuwa, saboda lokacin ina jin tashen ƴan matanci, gani kyakykyawa gashina har gadon baya, idan ba kiyi min farin sani a matsayina na buzuwa ba to zaki rantse kice baƙar balarabiya ce, gidanmu fa Maza dandazo suke a ƙwar gida sai akai asuba ana jiran fitowata, ni kuwa dama ta samu nayi ta juya su kamar waina a tanda, tunms layi yazo kan Sahibina Allah ya jiƙan rai, shi dama ya kwashi buhunhunan rashin mutunci a wurina, amma don tsiya da tusa min takaici duk sanda nayi masa sai yace ai indai ba ƙona shi zanyi ba ya zama toka, to ba zai daina zuwa inda nake ba kuma ba zai fasa furta min soyayya ba. Watarana dana shirya masa mugunta, Ina jin ance yana sallama da ni Na kaɗa karkashi na fita ta bayan gida na sami dakalin ƙofar wani gida na sheƙa a wurin, Sannan na dawo naci gayu na yafa gyale, na fito waje ina tafiyan rangwaɗa sai faman yauƙi nake kyace tarwaɗa kin san mu buzaye bada ganan ba. Shi ko yallaɓai tunda ya ganni yake faman murmushi yana nuna jin daɗi, Ji yake kamar ya sure ni mu shilla sama, ina isa wurinsa na wani kashe masa ido ɗaya sannan nayi masa sigina da hannu ina masa nuni da ƙofar gidan da zamu yi zancen. Hmmm haka ya biyo ni sai wani nishaɗi yake a tunaninsa yau ya taki sa'a ya mallaki zuciyata ne bai san mugunta na shirya masa ba, ɗan Fillo'nka na hawa saman dakali jinsa kike timmjim ya zame ya faɗo cikin kwalbati, salati yake yana neman ɗauki ni kuwa sheƙa masa dariya nake kamar zararriya saboda mugunta, nayita iya kuɗina na kaɗa masa mazaune nace gobe ka ƙara dawowa inda nake". duk yanda naso dariya a wannan lokacin sai ya gagara, saboda yanda Gwaggo ta saito faranti a fuskata, jira take na ƙyalƙyale ta kwaɗo min. Farahana da biye ta dakakke sai ce ma ta tayi, "ohhh Allah sarki Kakanmu, amma dai daga ranar bai kuma zuwa wurinki ba ko Gwaggo?". Gwaggo ta jawo robar goro ta ɓalla ta Kai baki, tana tauna tana cewa, "ai ɗiyar Aljannah ina kai ki bana baroki, daga inda na sallamawa mutumin nan a faɗuwar da yayi sai da yay karaya biyu targaɗe ɗaya amma yana warkewa sai gashi ya dawo yana kuma zayyana min irin soyayyar da yake min, Kuma fa ko da yana kwance kullum sai ya aiko azo duba mishi ni, in taƙaice miki dai ƙarshe ai sara mishi kawai nayi nace Sahibina ai kai bai kamata a kiraka da masoyin zuciya ba, da masheƙin rai da zuciya ya kamata a kiraka". "to fa! garin ya ya cancanci wannan sunan Gwaggo?". Farhana ta faɗa tana waro ido, tana ƙara tunzura Gwaggo. Ina duban Gwaggo ina dariya na miƙo mata hannu ta sammin goron sai ta make hannun nawa, yau harda su murguɗa min baki bayan harar da ake watsa min. Nan taci gaba da bawa Farhana labari, "ai ɗiyar Aljannah ya cancanci wannan sunan shi yasa na raɗa masa. Akaina fa yay faɗa da ƴan daba talatin saboda sun kawon hari, duk wuƙaƙen da suke tare dasu haka yay masu fata-fata, Ya kamo hannuna cikin kulawar so ya dawo dani gida, kamar zai yi kuka yake roƙona don Allah Sahiba karKi sake fitowa waje bare wani banza ya kuma kalle mani Ke, take a wajen naji wani ƙahon sonsa ya huda zuciyata ƙaunarsa ta nemi waje tai malemale, naja da baya na matso kusa da shi na yi masa kirarin so mai jijjiga ruhin masoyi, sannan na koma gida. Ina shiga na cewa mahaifiyata Adi, nifa Fillo zan aura, kowa daya ji haka sai da yayi mamakin abun saboda ada nace akan me zan auri wani matsolon rake, ai ƙwamma na sami ɗan'uwana usulin buzu kakkaura mai ƙwarin ƙashi na aura. Farhana ai banga so da ƙauna ba sai dana je gidan Sahibi na Sahibarsa, Kishiyoyi suka sanyo ni gaba amma sam Sahibina baya bi takansu, ni kuwa haka na dinga tsula tsiyata a gidannan ina gasa su son raina da tawa salon kissar, kuma fa gani ƴar figigiya amma haka na zame musu ciwon idanu. sanda na sami ciki na fara laulayi ai Kamar na zazzagawa kishiyoyina wuta a jiki saboda yanda Sahibina ke Tattalina kyace wata ƙwai". Gwaggo ta numfasa tana kuma fashewa da kuka tace, "Allah ya jiƙan Sahibina, ya mutu yana cikin mayen so na". Wayyo Allah cikina ni Sabina, yau nayi dariya na godewa Allah saboda dramar Gwaggo, na ƙara tsokanota da cewa, "to amma kuma Gwaggo ai tarihi ya nuna Kakanmu kamar yafi son Uwar gidansa Addagana, akace ma yana kan cinyarta ya mutu". Ba shiri naja bakina nai shiru saboda kallon da Gwaggo ta wurgo min haɗe da jefo min murfin bokiti. "to duk wanda ya faɗa miki wannan zancen ƙarya yake munafikin Allah ta'ala. Ke Sabina zanfa iya haɗa ki da D.P.O yau ɗin nan, saboda haka ki fita a idona, ke kiji wata makirar ƙarya, a gidan ubanwa ya mutu akan cinyarta, wanne shegen ne ya faɗa miki haka?". ni dama ba don komai yasa na faɗi hakan ba sai dan kunnata, saboda nasan yanda take tsakaninta da kishiyoyi, gashi dai shekaru da dama amma kamar waɗanda mijin ke aurensu yanzu. Gwaggo dai kamar nai mata me, haushin maganata da dariyata suka tsaya mata a rai. alhalin ita kanta wadda ake bawa labarin dariya ta ke, amma tawa dariyar ita ta zama laifi, na buɗi baki zanyi magana kenan ta dakatar dani cikin kwazazzafa. "ke kin san Allah zan miki adu'a bakinki ya tsaya a haka na tsawon shekara guda, sarai kin san na gada a wurin Kakana na biyu na ɓangaren kishiyar Babata Adi, kasancewar sunyi zaman mutunci sai muka zama kamar ƴan uwa, don haka ahir ɗinki da ni a yau ɗin nan. Ki tambayi kishiyata Hussaina kisha labari, da tayi min ba dai-dai ba sai da ta kwan talatin da bakwai ba tayi kashi ba, shima banda ta bani haƙuri sai dai ta shura a haka". Nai shiru ban kuma magana ba, ina latsa wayar Farhana. Ina jinsu Suna ta shan hirarsu. Ya Abba ne ya shigo ɗakin ɗauke da sallama a bakinsa, muka amsa masa ya shigo ɗakin ya tsaya yana zuba hannayensa a aljihu. Sannan ya shiga buɗe kwanuka da alama abinci yake nema, ya ɗago yana kallon Gwaggo yace, "ina abinci na?". a hasale tace da shi,"Ka kawo ka aje ne, ko kuma aure na kake da zaka shigo min gida har cikin ɗakina kake tambayana abinci". Ya kama ƙugu ya riƙe yana dubanta babu alamar wasa a fuskarsa kamar wani mijin gaske, yay gyaran murya yace, "naji koma mine kice, ni dai ina abinci na, yasin yau na kwaso yunwa baki ga yanda nai wani laushi ba kamar lagwani". Ta harare shi tace, "To ai kai dama lagwanin ne, saboda kullum a yamushe kake Kamar lawashi. Ni wannan yaro don dai Allah yay maka halittar maza ne amma da sai nace mace ne kai". Ya Abba ya ɓata fuska yace,"nifa sai na rubuta miki takarda akan irin wannan cin fuskar da kike mani. Kuma idan kina wasa ki kuma cewa tak ki kalla idan ban sake ki ba...ya zaai a gaban ƙannena kike faɗa min irin wannan maganar". Gwaggo tayi tsaki ta doki cinya tare da tura masa mazaunai tace masa, "karka fasa saki na ɗin, kaine zaka ji haushi. Saboda ina fita zan sami rangaɗeɗen saurayi mai rai da lafiya yayi wuff da ni, kai Abba kana raina wannan Sauran yarintar dake jikina ko, to Rabon kaji na aure shugaban ƙasarku ne". Ya Abba ya kaɗa kai kawai, idan ya biye tata abincin daya dawo ci ba zai sami cinsa ba. Ya dube ni yace, "ke tashi ki ɗauko min abinci na". Kamin na miƙe Gwaggo tace, "ke yi zamanki, yau kam sai dai ya nemi wani gidan yaci abinci. Abba ba dai ni zaka nunawa tsiya ba, zaka ganta iya ganin idonka, dama kowa ai da ranarsa. Idan kaji haushi ka koma can filin ball ɗin su dafa su baka, ko kuma kaje can gidan su budurwar taka daka saci ɗankwalina ka kai mata matsayin toshin sallah saita baka...kana faman ɓoɗara hanci kamar gajeran wando, da wasu idanuwanka ƙifi-ƙifi kamar na ƙaramar touchlight ɗin masu gadi, har na zaka nunawa fushi Abba". Haushi ya tuƙe Ya Abba, don haka ya juya kawai ya fice yana jijjiga kai. Gwaggo tabi bayansa da ido tana murmushi tayi ƙwafa tace, "ɗan ƙwal uba dani kake zancen ai". Muna haka muka jiyo sallaman Baba, da sauri na sakko a saman kafita na fita cikin hanzari ina amsa sallamar tasa, kamin Gwaggo da Farhana su mara min baya. Yana zama kan kujera na ƙaraso da fara'ata ta nuna jin daɗin ganin mahaifina nace, "Baba sannu da zuwa". Ya amsa min da, "yauwa Sabina". Farhana ta ƙaraso itama tana masa sannu da zuwa. Lokacin da Gwaggo ta ƙaraso ta zauna kan kujera, Baba ya sauko ya gaida ita, tana amsa masa tana sanya masa albarka. Baba yace, "Mama mene ya haɗaki da jikin naki, yace kinƙi bashi abinci". "auto kaga masu ɗa, ai ban san kana tuhuma ta ba sai naga ka sanya mini ankwa, sai naji daɗin maka jawabi...amma yanzu ban ganka da kakin ɗan sanda ba ina zan san kana yi Awwalu. Abinci ne na dafa bazan bashi ba, har ni yaron nan zai tsulawa tsiya na roƙe shi nace yazo ya siyo min kayan miya Sabina na makaranta, amma ya buɗi baki yace ai filin ball zaije, koma ba haka ba ai yayi girman a aike shi wurin me kayan miya, ƴan mata ai sai su raina shi. Ranar haka na zauna ban girka na rana ba sai da Ƴar arziƙi irin albarka ta dawo, wadda tayo gadon kirki a wajen mahaifiyarta". Baba yace, "to ayi masa afuwa Gwaggo ba zai ƙara ba. ba'a horo da yunwa ke kika faɗa mana hakan, kuma shi idan baici anan ba aina zaici". ta taɓe baki kamin tace, "ya tafi can wajen matan ubansa yaci, ko kuma tunda Allah ya kawoka ka ciri ashirin ka bashi ya sayo awara, abincina ne dai yau Abba ba zai ci ba". Baba baice komai ba, dan yasan tun da ta kafe kam bata sauya ra'ayinta. ya dai kalla Ya Abba da ido sukai magana, nan ya tashi ya fita bayan Baba ya bashi kuɗi a ɓoye, in ba haka ba Yanzu Gwaggo sai ta kuma sauke masa sababi idan ta gani. Baba ya kira ni yace nazo, na taso na dawo kusa da shi, kasa ɗauke idona nayi akansa duban yanda naga yana ta zabga murmushi da alamu yau ɗin yan cikin farin ciki, don tunda ya shigo na lura da hakan, ni kuma abunda yake min daɗi kenan a rayuwata, naga mahaifina acikin farinciki da kwanciyar hankali. Baƙar jakar hannunsa ta laptop ya buɗe ya zaro wasu takardu ya miƙon yace na karanta. Habawa ai ina karanta layi biyun farko na miƙe tsaye nai wani tsalle nai juyi ina ihun murna, Farhana na fizgo na nuna ma ta itama, tsabar farinciki mun kasa ƙarasa karanta sauran rubutun. baki ɗayanmu tsalle muke muna murna, kamin daga baya na koma na zauna ina hamdala ga Allah, maimaitawa nake, "Alhamdulillah, Alhamdulillah, Allah mun gode maka abisa ni'imar da kayi mana. Ya Allah kaci gaba da bawa mahaifina nasara a rayuwarsa". Gwaggo tace, "wai meke faruwa ne, ni duk kun barni a duhu, ko abin farincikin banda ni ya sama. An baki aba kin wani ƙwaƙwame ke kaɗai, ina ce dai ɗa nawa ne tunda sai dana haifa kika sa me shi a uba". nace, "oh Allah na! nikam yau gwaggo ban san me na maki ba. to gashi nan".Na faɗa ina tasowa na bata takardar. Sai da ta gama mani kallon sama da ƙasa kana ta karɓi takardar, hannu ta miƙa saman abun tv namu ta ɗauko akwatin glass ɗina, ta buɗe shi ta ɗauko glass ɗin ta ƙwaƙwuma a fuska sannan ta wani harɗe ƙafafu ta hau kallon takarda kace gaske karantawar take. Dariya muke so muyi daga ni har Baba amma gudun sababinta yasa muka gimtse kayarmu. ta ɗau kusan mintina biyu sannan ta sauke takardar daga kallonta, ta cire glass ɗin, tana faman juya takardar ta kalla Baba tace, "Kai Auwalu, tunda ta gama nata zagin kai sai ka sami damar min bayanin abinda ke ƙunshe aciki. Sarai ai kasan babu abinda na iya karantawar amma ka barta ta miƙo min saboda cin fuska, dama ranar nan tace min ni ai bana ganewa, kamar Addagana haka nake. Yo Allah na tuba duk lalacewa ai nafi wannan lukutar matar tunda ni nayi makaranar Allo. Ita yarinya ce har yanzu bata san mene kishi ba shi yasa take haɗani da waɗanda suka kusa rabani da mijina". O'o, niko na riƙe baki ina kallonta har tagama magana. Gwaggo ba dai mita ba, wannan zancen anyi wata da yinsa amma duk sanda ta tashi sai tace ai nace bata ganewa Addagana tafi ta jaa, kuma ba komai bane saboda na haɗata da kishiyarta. Baba ya numfasa yace, "Mama wannan takarda ce daga wurin aikinmu...". Ai tun Baba bai ƙarasa ba ta dafe ƙirji cikin tashin hankali tace, "na shiga uku na Auwalu ba dai sun kuma korarka bane, wannan ƙaddara da me tayi kama". tana faɗa tana shirin yin kuka. Ina dubanta ina gwame fuska nace, "kai Gwaggo hakanne zaisa kiga ina murna kuma. Abuja fa zamu koma". Tayi min wani kallon sheƙeƙe na ban gane nufinki ba, "me kuma zai maida mu Baba Ja?". Gwaggo bata taɓa cewa Abuja sai dai tace Babaja, saboda acewarta ai cin mutunci ne yasa aka lanƙwaya sunan ubanta aka maida shi Abuja daga Abubakar. Baba yaci gaba da mata bayani, "ehh Gwaggo zamu koma Abuja ne da zama saboda ƙarin matsayi da ma'aikata ta bani". "kai don manzan Allah??". ta faɗa har tana zamowa daga wurin zamanta. "wallahi kuwa Gwaggo, an bani muƙamin MD na ma'aikatar wutar lantarki. Sun bani gidaje biyu acan Abuja, da motoci uku, da kuma miliyan uku, ta buƙaci na ɗauki iyalaina mu koma can da zama gaba ɗaya nan da sati guda".


_Please Share, Vote and Comment let me know what you think._*AL-HUSSAIN*

_By Oum Ramadhan✍🏼_

*(8)*
Gwaggo ta rangaɗa wata uwar guɗa data amsa a gaba ɗaya cikin gidan, hamdala take ta jerawa ga Allah, har da miƙewa ta taka rawa irin tasu ta tsofaffi. "Allah maji kukan bayinsa...kai gaba ɗaya ma na rasa wacce iriyar murna zanyi". Yaya Abba daya shigo yace da ita,"tsohuwa kina ta ihu fa dare ne, maganarki har soro, dama ke muryar kamar cakwaikwaiwa". tace da shi,"umm Abba ai yau sai dai kayi da wata bada ni ba kam...dan lokacinka dai ban da shi". Murna nake yi sosai kamar babu gobe, amma ɓangare guda na zuciyata yana tunanin halin da zan shiga zai kasance. wannan mutumin, wannan bawan Allah'n da Allah ya haɗani da shi ta ayar da ban san fassararta ba, wannan mutumin da nake jin kamar ina da wata babbar alaƙa da shi, mutumin da babu ƙarya tun a ranar farko nake jin tasirinsa a tare dani a kullu yaumin, mutumin da tunanins akaɗai a sanda bana tare da shi yake sakani zubar hawaye saboda rashin sanin dalilin wanne hali yake ciki.
Gaba ɗaya murnar da nake yi tsayawa tayi cak, saboda tunawa da nai zan tafi na bar Yaya, tunanin daya haifar da wani ɗan ƙaramin tashin hankali a zuciyata, ta fara bugu kamar zata fito waje. dai-dai ta nutsuwata nayi saboda ina gaban wanda bana son ya fahimci yanayin da nake ciki. dan duk wanda ya kallen a yanzu dole sai ya ɓazgo wani abun, Ina kallon Farhana ma yadda ta kafe ni da idanunta, tana son gano sirrin dake zuciyata, amma sam na kafa na tsare saboda yanzu sai ta ruguza min tsari, dan ita bata iya sirri ba. Ganin hakan yasa ni furta, “Yauwa Baba barin zuba maka ruwan alwala, na kalla magriba ta gaba to”. ina gama faɗar haka na miƙe na nufi hanyar fita, idon Farhana na kaina har a lokacin, yayin da Gwaggo take ta faman zuba kamar kanyar da ta samu jeje da iska. Ina fita na samu damar dai-dai ta nutsuwata, amma fa sam hakan ya gagara, don tuni hawaye sun fara zubo min, dama ni Allah ya hore min kamar famfo, hawayena a wajen tausayi da rauni basu da wahalar sauka. ina zuba ruwan na dawo, na samu gefen Gwaggo na zauna ina sauraron hirar ta su, ba wani fuskantar hirar nake ba, tunanina da neman mafita bai wuce yadda za'ayi tafiyar nan tare da Yaya ba. kallon Farhana nai, nayi mata sigina da ido, saboda mu fita mu samu abin faɗa, amma sai naga ta basar kamar bata ganni ba. Ganin haka yasa na miƙe na kama hannunta ina faɗin, “tashi mu shiga ciki”. Hannuna ta kama muka nufi hanyar ɗaki, muna shiga ta dube ni sheƙeƙe tace, “ya dai uwar ɗorawa kai damuwa”. harara na watsa mata ina faɗin. “ke fa ƴar rainin hankali ce Farhana, meye nufinki dama?”. ta ɗan harare ni tace, “Oh oh jimin rainin tunani, ke zan tambaya dai meye ke damunki, naganki sukuku, don tun ɗazu na fuskanci damuwar da kika shiga bayan kin gama murna”. na ɗan ja ƙaramin tsaki kaɗan na miƙe tsaye ina safa da marwa kana na kama ƙugu na tsaya nace, “ba zaki gane ba Farhana, kin san halina sarai, ina da saka damuwa akan abinda nasa a raina but..”. ban ƙarasa faɗin abinda zance ba Gwaggo ta bankaɗo labule tana faɗin, “an kira sallah ko baku ji ne wai, ko kuwa ba zaku yi ba ku duka?”. nace, “kaii Gwaggo mai baiwa, yo waye yace maki bamu ji ne wai, banda abinki Gwaggo kuma anyi ta rashin sallar kenan?”. tace, “oho maki marar kunya, na sani ko ba zaku yi ba, tunda ku ko yaushe a cikin jini kuke. abu da a zamaninmu iwar haka ma yara kamar ku basu fara abin mata ba sai an wuce haka...amma ku yaran yanzu nan da nan sai ku nemi kufi ƙarfin kan mutum”. “gaskiya Gwaggo Allah ya baki baiwa, baiwa ba ta faɗe ba, ina ruwanki ne ke kam, don Allah kije, na san abin da kike nufi gamu nan kije abinki”. na faɗa sanda nake ƙara riƙe ƙugu. Farhana kam dariya kawai take tana faɗin, “ni kam dramar ku tana burge ni, muje muyi alwala kafin ta dawo”. muna idar da Sallah Farhana tace zata tafi, Gwaggo ta zuba mata tuwon shinkafa da miyar kuɓewa tace ta kaima Hajiyarsu. Ta karɓa tana godiya, har mun kai soro naja na tsaya ina faɗin,“muje kice ma Baba zan kwana a gidanku in yaso sai mu tattauna abinda zamu tattauna kinji”. Farhana ta ɗanyi jim kafin tace, “Gwaggo dai nasan zata yarda amma kina ganin Baba fa?”. “ke kam muje zai amince insha'Allah”. na faɗa da ƙosawa, da wani abu dake bin jikina wanda ban san menene shi ba. muka koma ciki, Gwaggo bata

Please Login or Register in order to submit comment