Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mess,naso sosai kiyi aurenki inda zaki huta,momy ta kasa fahimta na,akanki kisane kawai bazan iya ba wlhy bazan juri ana neman tab'ar b'are rayuwar ki ba,ki sani ina sane nake zaginki nacin zarafi sabida kawai ki ce bazaki aure niba dan kisamu freedom me dorewa,ko bayan auren mu danake zaginki dan kawai ki kasa daure wa ne kice bazaki zauna daniba ki huta,ban tab'a zaginki Nayi bacci ba wlhy Hafsat duk sanda naci zarafinki bana iya bacci, sabida bakin ciki ni kanji natsani kaina amma ya zanyi.Tsakanina dan iyayenki biyayya ce me tsafta ki binci kesu kiji,tun ranar da muka taho yau gobe nakejin wasu maganganu daga gida wayanda bazan jura ba,Hafsat zan sauwaqe miki sabida inasan ki dauwa ma a farin ciki badan komai ba,idan ba wannan hukuncin na yanke mana ba wlhy bazasu barki ba Hafsat,sannan kuma bazan tab'a yin bankwana da giya ba idan nace zan rayu dake kina shan wahala,kuma soyayyar kice Zata halla kar dani idan har ban rayu dake amma na sani bakya sona ni kuwa farin cikinki shine nawa,sabida haka zamu rabu Hafsat ki guji yan gidan sarauta,anmiki asara mafi muni a yanzu haka,zuwa next week zan maidaki gida" k'ura masa ido kurin tayi takasa koda k"wak'waran motsi,Mik'ewa yayi yaje ya bud'e wardrobe d'in sa ya d'auko takarda ya miqa mata takardar yace "karanta kigani Hafsat,kuma kar kiga laifina koku zargeni wlhy k'aunace sila,kuma koda kin koma gida dan Allah ki guji faruk wlhy har cikin raina nakejin wannan tab'in dayake wa jikinki" Mik'ewa tayi jikinta se rawa yakeyi ta kasa bud'e takardar illah kallonshi kawai da takeyi cikin rashin fahimtar zancensa, janyota yayi jikinshi ya rungumeta sosai ya saka wani razanannen kuka daya tayar mata da hankali......


Hmmm to wai jama'a meyake damun Abdul,abin zantuttukan hankali yakeyi kuwa? Anya tun farko bamu kasa fahimtar Abdul ba kuwa? Muje zuwa dai kuna tare da alkalamin mom Nu'aiym
[1/8, 10:32 PM] Sha'awa: *🌞HAFSAT ELHAM🌞*

Billy Galadanchi

Haske writer's Asso💡

Vote me on wattpad@68billygaladanchi.
Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).

*Nafi, wannan shafin nakine kyauta,so chill*

15
Zare rungumar daya mata tayi ta tallafi fuskarsa da tafin hannunta tace cikin sassauta murya da sigar rarrashi

"Com down yaa Abdul,ur a man plss try to look as one mana" k'ura mata ido yayi duk da hawayen basu dena tsiyaya daga idon shiba,tace tana me k'ara saisaita fuskarshi da hannunta

"Yaa Abdul plss be like a man kaji,kalle ni plss dena kukan haka" zaunar dashi tayi sannan ta sakashi jikin kafadarta a hankali take Shafa bayanshi tamkar wani jinjiri,dagowa yayi yace "Hafsat yau zan sanar abubuwa da dama wayanda baki san dasuba arayuwa ta" gyad'a masa kanta tayi alamar yaci gaba.....

"Koda na taso naganni a gidan me girman gaske,a labarin danaji Kakanmu wanda ya haifi mahaifina kashe shi akayi ta hanyar yi masa yankan rago, yanada mata Su hudu da kuma yara manya maza Su takwas,se kuma mata Su goma sha uku....Akwai k'aninshi Muhammad shine kadai gareshi dan uwa mahaifinsu Su biyu kad'ai ya haifa,bayan rasuwar sa kasancewar Kakanmu shine Babba se aka bashi sarkin garin,wannan abin ba k'aramin tayarwa mahaifiyar Su Muhammad hankali yayi daga nan ta k'walla fa ranta akan se Muhammad yayi sarauta.....Kakanmu a cikin y'ay'anshi takwas dinnan maza mahaifina shine na shida mahaifin Su faruk shine na biyar, kafin rasuwar kakanmu kuwa ansha fama da Baba Muhammad da mahaifiyarshi daga k'arshe dai sukayi nasarar yi masa yankan rago wanda agaban idon mahaifina hakan ta faru shida kanshi ya sanar dani,bayan rasuwar sa aka gane Sune amma se mutane suka k'aryata hakan,daganan aka bashi sarautar,sauran kishiyoyin kakata kuwa suka d'auki masifar san sarauta suka d'aurawa akan yayan su,daganan me martaba kakana yabar baya da k'ura sabida sune suka kashe Baba Muhammad da Kansu, a wannan lokacin se abin yazama rigima domin kuwa duk wanda yahau sarautar se an kasheshi haka yayyun mahaifina sukayita rasuwa har akazo akan Baban faruk,shine ma ya jima akan sarautar domin kuwa tun muna yara shina taso na gani akan sarautar,zancen da nake miki wayanda fa ake kashewa har matansu da y'ay'ayensu bawai barinsu akeyiba indai kin haifi yaro namiji sedai kiji ance guba yasha idan mace tace Zata motsa ita d'inma a kasheta mututus.....gidan sarauta yazama wani iri domin yayyuna maza guda biyu sace su akayi haryau ba labarin su mahaifiyata duk sanda kikaga tana kunannan dakike damuwa idan tana yinsa yaranta take tunawa,an halakasu duk dan sabida Karsu tasa su gaji sarauta, Ana haka muna aji shida a secondary akayi murdering mahaifin su faruk ta hanyar poisoning d'in sa,wanda haryau ya haddasa rud'ani akan cewa mahaifina shine ya kashe shi,da kunnena naji mamansu faruk na cewa lallai idan nayi aure sedai duk sanda matata tayi ciki su zubar dashi ta hanyar tsafi bazasu tab'a bari na haihuba,sedai ko na gaji sarautar yayan faruk su gada,wannan dalilin ne yasanya na nemi auren Humaira yayar Raihan aka hanani daga baya kuma na nemi auren Raihan ita d'inma ban samu ba,Karfa ki Zata sabida ina sansu ne wlhy kurun sabida nasani bata yanda za'ayi uwa ta cutar da 'yar ta hasalima wlhy banasan tarbiyar yaran,nafara sanki ne tun kina jss 1,Nakuma t'aba sanar da momy ki binci keta kiji amma duk sanda na tuna cewar zasu lahantamun ke su wurgaki cikin halin da ba nakiba senaji bazan iya ba,ahaka na koyawa kaina yi miki kallo iri d'aya da feenah sabida haka na fara jin sassauci,dazaki tariyo farko kece babbr k'awata banida Aboki yar hira seke,tun sanda na fara ganinki da faruk na d'aura aure da giya sosai,nasani rashin ki masifa ne a gareni, Naso Raihan bazan miki k'aryaba amma wannan a rashin kine nasoma sabawa da ita, bayan rashin ki kuma yanzu me martaba ya matsa akan rashin lapiyarshi wai ze sauka ya bani ragamar mulki,Hafsat ko kinsan hallakaki zasuyi bazasu bari kiga k'wanki a duniya ba,bayan nasani Baba Hashim yasha wahala kafin samuwarki Harma ya cire rai da haihuwa kuma bayanki seda suka shekara biyar basu samu wata haihuwar ba,sunci ganin jikokinsu sannan kuma kece zaki basu kulawa,idan kika Shiga damuwa yaushe zaki kula da kanki ma bare su,a yanzu haka an shaida mun tun dawowarmu nan da kwana d'aya an kashe Amir k'anina kuma labari ya riskeni ance saura ni dake!!!!! Hafsat ki yarda da k'addara wannan takardar saki d'aya ne aciki dana miki sabida na tserar da rayuwar ki daga halla ka plss ki fahimceni" shiru tayi ta k'ura masa ido nakusan minti biyar wanda shima d'in ita yake kallo,hannunta ya riqo ta warce da sauri ta mik'e tsaye ta juya masa baya yau kukanma ta kasa yi,cikin d'acin murya tafara magana

"Dukkanin hujjojinka ababen dubawa ne,amma anya ka tausa yamun daka mayar dani k'aramar bazawara? Da kasan kanaso kan kareki daga hannun su aiba seka wulank'anta mun rayuwa ba,akwai wulakncin dayafi ka mayar dani k'aramar bazawara? Baka da labarin idan Kayi imanin da Allah cewar babu wanda ya isa yamaka abinda Allah be makaba kuma kanada adua ba wanda ya isa ya maka wannan mugun abin,wlhy na yarda da dukkanin abinda ka fad'a amma wannan sakin dakamun ya nunamun cewar tsantsar k'iyayyace ba wani so dakake mun se shirin tarwatsa rayuwata,nakuma gode k'warai" tasowa yayi a rud'e ya riqo ta ta kwace kanta da sauri
"Bakada labarin cewar ni ba matarka bace? Kuma banida iddar ka ayau na wanke tsaf daga kanka,idan gobe naso aure na zanyi,sabida haka wlhy kaji na rantse maka wlhy karka kuma tab'ani,kuma yanzunnan zan kira momy na sanar mata" da sauri ya kalleta yace "ki rufamun asiri Elham karki sanar mata,amma ki kirata kimata gaisuwar Ameer,dan Allah dan annabi karki sanar wa kowa" hararar tayi tana me jin tsantsar tsanar sa

"So kakeyi na k'urawa kaina ido a gida koso kakeyi na tabbata ban sanar wa kowaba,kana nufin cewar banaso nayi aure,aure zanyi dama ai acikin d'inbin masoya ka d'aukoni Ba maqiya ba,so namaka alkawarin acikin watanni biyu kacal zanyi aurena kuma kowa sena sanarwa ka sakeni" magiya yashiga mata ita kuwa ta saka wani kuka me ban tausayi,tanajin zafin mutuwar Ameer sun shaqu sosai kwanciya tayi tana ambaton sunan Ameer tana kuka......


Kuyi hakuri da wannan yau ban samu zamaba

Mom Nu'aiym
[1/8, 10:32 PM] Sha'awa: *🌞HAFSAT ELHAM🌞*

Billy Galadanchi

Haske writer's Asso💡

Vote me on wattpad@68billygaladanchi.
Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).

17

Dangin Ibrahim kad'ai ake jira amma basu isoba,me martaba da kanshi yayi kiran sheikh Muhammad Adam,mahaifin Ibrahim amma abin mamaki se cewa yayi dashi

"Ranka ya dade me martaba amin afuwar rashin kira,Allah yayiwa Ibrahim rasuwa yanzunnan,akan hanyar mu ta zuwa,kawai aman jini ya fara juyawar dazamuyi zuwa asibiti mafi kusa akace damu Allah ya karb'i abinsa,hankali nane ya d'auku dan Allah amana afuwa"
Innalillahi wa Innah ilaihirraji'un" itace Kalmar da me martaba ya furta,"Ina rokon Allah ya jikanshi dan rahamarsa,inshaa Allah gobe zamu zo" godiya ya masa sukayi sallama,koda me martaba ya sanarwa mutane se al'ajabi ya kamasu,mahaifin Hafsat ne yace,Dan Allah tunda anrigada an tara mutane kuma dama mijinta na farko ya buk'aci koma warta dan Allah a d'aura dashi,k'anin me martaba ne yayi zumut yace

"Da d'ina dakai Baba magadi haka iya had'iye kwad'a yinka,sarautar nan tunda ba gadar ta kayiba ai ka dena cusa jininka aciki ko?" Rayuwar me martaba ne yayi matukar b'aci dajin wannan zancen,mutane sun d'auki mutuwa ba'a bakin komaiba yanzunnan wani ya mutu amma basu da asara,lallai karshen duniya ne yazo,kallon Mahaifin Elham yayi yace "Ka wakilci ango nine wakilin Mamana" batare da b'ata lokaci ba aka d'aura auren.....kamar saukar aradu haka Elham taji sanda labarin mutuwar Ibrahim ya riske ta, Kuka kam ta shashi,amma tarasa dalilin daya sanya bataji zafi ba da aka mayarda aurenta da Yaa Yarima,da ita akaje gaisuwa har garin abj,yan uwan Ibrahim se kuka sukeyi musamman daya kasance mutuwar huji'a ce kamar daga sama,sosai suka bata tausayi ba kadan ba.

*Bayan sati d'aya*

Har akayi sati d'aya da d'aurin aure baisan inda kanshi yakeba,Elham kuwa duk tabi ta rame duk sanda aka barsu su biyu seta zauna tayita rusa uban kuka gani takeyi tamkar ze mutu ya barta ne,ranar wata alhamis ya fara kwara amai najini tamkar ranshi ze fita,ita kad'ai ce atare dashi tunawa tayi da yanda yan uwan Ibrahim ke bada labarin irin Amman dayazo masa nanjini nonstop kuma be tsayaba har sanda ya dauke sheda,rasa abinyi tayi da sauri taje ta d'auko alqur ani tafara karanta wa da k'arfi lokaci d'aya kuwa ya fara tsagaita aman,bata daka taba taci gaba da karatun sanda taga ya dena aman kwata kwata sannan ta ajiye alquranin tazo kusa dashi ta dafe k'irjinshi tafara tofa masa adu'o i kala kala na tsari,a hankali taga yana bud'e idonshi da sauri ta matsa kusa dashi tace "Sannu yaa Abdul ya jikinka?" Binta da ido yayi yana mata kallon rashin sani,adu'ar taci gaba da tofa masa har taga ya soma bacci cikin nutsuwar da tunda yafara wannan ciwon Bata gani a tare da shiba Mik'ewa tayi taje ta sanar da momy ta k'ara da cewar "momy me za'a hana akira malam uthman na meduguri se nakega abin kamar da iska aciki,dogon nazari momy tayi kan taje ta sanar wa me martaba,hakan kuwa akayi koda malamin yazo aljanai aka turowa Abdul a haka a haka akaso harya mutu,a binciken da malamin yayi wancen ma wanda ya mutu Wato Ibrahim shime same abune ya kashe shi kuma samu ne aka musu,amma Allah be bashi ikon gano wanda yayi wannan aikinba sedai ya bada adu'o I da kuma ruwan adu'a daze riqa sha kullum da du'oin da za'a masa dakuma wanda zena yiwa kanshi,Elham ce ta karb'i wayanda za'a na masa yayinda Abdul aka baiwa wayanda zeyiwa kanshi,gidansu aka maidasu na ainahin wanda tun farkon auren can suka fara zama.....

Zaune yake tana bashi coffee abaki kasancewar har yanzu jikinshi be gama k'wariba yace yana kallon ta " Hafsat na gode sosai,na gode sosai Allah ya miki albarka,wlhy da baki dawo gareni ba nasani mutuwa zanyi" har Wannan lokacin hafsa bata gane komai ba game da son datakewa Abdul, kasancewar har gobe tanason faruk,wanna ya sanya ta sauya akalar zancen

"Zakaci wani abinne?" Coffee dake hannunta ya karb'a ya a jiye sannan ya janyota jikinsa ya d'ago kanta ta fuskanceshi sannan yace "Ellyn yaa moris fushin ne haka har yanzu plss kiyi hakuri mana" k'uramasa ido kurun tayi batayi magana ba, batayi auneba taji bakinshi cikin nata taso sosai ta k'wace kanta amma ta kasa dole ta haqura,yafi minti biyu yana tsotsar bakinta,seda dan kanshi ya gaji ya saketa,da sauri ta sadda kanta k'asa sabida haka kurun taji wata kunya ta lullub'e ta,hannunshi yasa ya d'ago hab'arta yace yana Murmushi "Elham na kalle ni mana" duk'e kanta ta k'ara yi yana Murmushi yace "Kaddai kunya Elham na? Kiyi hakuri na dena miki I just couldn't take my ice off this fine lips of urs" batace komai ba ta tamik'e cikeda kunya ta bar wurin Murmushi yayi yana mamakin yanda yakewa Elham kallon wacce ta saba da maza amma wannan kiss kawai ta wani ji kunya Allah karya sanya zargin shi ya tabbata a kanta" zuwa tayi ta kwanta a bedroom nata,tarasa dalilin daya sanya ta kasa cire wannan moment d'in a ranta,da zaran ta tuna da yanayin da taji lokacin daya kama harshenta setaji wani Yarr har cikin ribs nata takejin wani feelings na shigarta,ba ita tabar cikin d'akin ba se la'asar kai tsaye kitchen ta wuce da sauri ta daura macaronie paper soup da beef souce, tana tsakiya da kwashewa yashigo bata saniba ta bayanta ya rungumeta ya daura hab'arsa sama wuyanta yace cikin wata siririyar murya "Elham na me kike girka mana,kika bar patient da yunwa har yamma Waike kunya ko? soon enough zanyi maganin wannan kunyar taki" kasa bashi ansa tayi ta lumshe ido ta bud'e su a hankali,janye jikinta tayi a hankali ta juyo amma bata bari sun had'a ido ba tace 'Kayi hakuri bacci ne ya sace ni" zagaye hannayenshi yayi a waist nata yace "Gwara daya dawo mun da Elham na,ba wanda ya isa ya sacemun ke" dariya maganar shi ta bata tayi Murmushi har hak'waranta suka bayyana gaba d'aya, d'an gyaran tsayuwa yayi still yana rik'e da waist nata yace "Elham na I'm hungry fa" hannayenta ta d'aura asaman nashi dake zagaye da waist nata ta langwab'e kai tace "To ka bani mintuna goma sha biyar yanzunnan zan kawo maka abincinka" saketa yayi ya juya bece ko maiba, a dining tayi serving nashi kuma tayi serving kanta,amma ga mamakinta yaqiyin koda loma d'aya ne da mamaki ta kalleshi duk yunwar dayake kira ya tasa abinci agaba yaqici

"Yaa Abdul mesa bakacin abincinka ko baka son wannan naje na girka ma wani daban" kamar wani k'ank'anin yaro haka ya shagwabe "Ni bazan iya ci da kaina bafa" wani takaicin shi taji ya kamata amma a zahiri setayi Murmushi tace

"Kona baka da kaina ne?" Murmushi yamata "Dama mana to waye ze bani?" Tasowa tayi ta zauna kujerar dake kusa dashi ta dinga ebar abincin tana bashi a baki cikeda nutsuwa dama mana maza ba kunya yakuwa hankad'e yayi narkar abinshi sanda ya k'oshi sannan ta koma taci nata... Da dare bayan ta shirya cikin rigar bacci mara nauyi tazo ta sameshi yana adu'a Sosa kanta ta d'anyi ta tsaya sanda ya idar,tasowa yayi ha zauna a bakin gadon tace dashi

"Yaa Abdul ina so zanje na kwanta idan baka buqatar komai,na rigada na rufe ko ina na gidan" hannunshi ya saka ya janyota ta fad'a jikinshi kwantar da ita yayi akan gadon yaje daidai saitin kunnenta yace "Bana tunanin ina buqatar komai seke Elham na,yaya zaki tafi Kibarni ni kad'ai kin manta banida lapia?" Wani irin kasala ya saukar mata kasa cewa komai tayi har cikin b'argon ta takejin wani abu dabaza ta iya fassara ko meye ba,hannun shi yakai ya shafi mararta lokaci d'aya numfashin ta ya soma barazanar d'aukewa da sauri ta d'aura hannunta saman nashi se kuma ta soma kuka tace "Yaa Abdul dan Allah Kayi hakuri" hancinshi ya saka a saman nata yana gogawa a hankali batare daya janye hannunshi a saman marar tata ba,ita ma kuma ta kasa d'auke nata,sannan ya kai bakinshi wurin kunnenta yace "Menene yake sakaki kuka Elham na? Bakyaso nake zuwa kusa dakene ko me?" Cikin kukan tace "Nidai Kayi hakuri tsoro nake ji" sakinta yayi yaje kashe fitilar d'akin ya d'are kan gadon,janyota yayi sosai jikinshi ya lalubo bakinta yafara kissing nata passionately, kasa tureshi tayi kurin dai bata dena kukan ba,seda yagaji dan kanshi sannan ya pulling out,yace cikin sigar rarrashi hannunshi na saman kanta "Elham na menene? Bakyaso?" Gyad'a masa kanta tayi alamar e,janyota sosai yayi ya rad'a mata a kunne

"To kiyi baccinki Na dena kinji,ko bakyason ki kwanta ajikin mijinki?" Banza ta masa yace "Ean Elham na bakyaso?" Cura fuskarta tayi acikin k'irjinshi duk da suna cikin duhu,cikeda shagwaba tace "To nidai ban ceba" Murmushi yayi ya k'ara k'ank'ameta a haka bacci me dad'in gaske yayi awon gaba da Dukkansu.

Mom Nu'aiym
[1/8, 10:32 PM] Sha'awa: *🌞HAFSAT ELHAM🌞*

Billy Galadanchi

Haske writer's Asso💡

Vote me on wattpad@68billygaladanchi.
Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).

16
Abdul kamma kuka ya saka ya zauna yana ta bata hakuri,dakinta ta koma ta k'ulle kanta,ta zauna tanata rusan uban kuka,tama rasa me zatayi,kiran momy tayi tayita kuka tamata ta'aziyar Ameer amma ta kasa gaya mata sakin da Abdul ya mata,bayan sun gama ta share hawayenta ta kira Aunty husna,komai sanda ta sanar mata,nisawa Aunty husna tayi tace

"Kinga Elham,bazamu bari aurenki ya lalace haka a banza ba,karki kuskura kowa yaji wannan zancen, koda yace ze dawo dake karki yarda amma ki Barshi wlhy ze kawo kanshi ne,hujjojinshi basuyi karfin da zeyi wasa da saki har Hakaba,duk da yake yanada ban tausayi amma wlhy bazamu aminta ya lalata rayuwar kiba,yanzu ki nutsu Elham saki akwai ciwo ba kad'an ba, kuyita hakuri Koda yace ki dawo Nigeria karki yadda,ki roqa a sama miki makaranta anan" shiru tayi sabida tanaji wannan karon bazata bi zancen Aunty Husna ba kuma sam tama tsani ganin Abdul,se can tace

"Aunty Husna nifa wlhy na tsaneshi bana san a gyara auren,ni sena sanar wa momy" sassauta murya husna tayi cikeda rarrashi

"Haba Elham Karki yiwa momy haka mana,kinsan yanda take k'aunarki d'innan Zata iya yanke jiki ta fad'i ga kuma an mata mutuwar Ameer na damunta,dan Allah na rok'eki ki gyara aurenki da kanki batare da sanin kowa ba" nisawa tayi tace "Idan haka ne Aunty ina da shawara"
"To ina jinki Hafsat" daga nan ta zayyane mata komai yanda take ganin za'ayi dashi,ta k'ara da cewar "Aunty wannan ne kad'ai hanyar danike ganin zamu bi,Abdul be kyauta wa kanshi ba aganina kuma beyi jarumta ba amaimakon yayi jarumta ya nemi mafita seya sakarwa yan uwansa ragamar rayuwar sa gaba d'aya"

"To Elham ina fatan Allah ya sanya wannan tsarin namu yayi working kinji" sallama sukayi ta ajiye wayar cike da bacin rai,har kusan kwana ki biyar bata k'ara ganin Abdul a gidan ba da wannan take tunanin bata yanda za'ayi plan nasu yayi working,a maimakon ta kira Husnah,kurun se fushin zuciya ya d'ebeta ta kira momy ta saka mata kuka,cikeda wauta ta gaya mata komai tsaf daya faru,B'acin rai me tsanani ya ziyarci momy,rayuwarta ta b'aci,bak'in ciki ya lullub'e ta hankalinta ya tashi,kuka kawai ta saka ta kashe wayar,a fusace ta kira Number d'inshi.....

Yana office zaune yana tunanin yanda zeyi da Elham so yakeyi yace ze maida aurenta amma yasani bazata aminta dashiba,yana tunanin yanda zeyi rayuwa batare da Elham ba,yanzu ya haqiqancewa kansa rayuwarshi batada wani amfani idan ba Elham,Mema zesa yayi wannan tunanin har ya biyewa san zuciyarsa ya saketa,yana tsakiya da wannan tunanin wayarsa ya soma ringing, gabanshi ne yayi mummunan fad'uwa ganin sunan momy domin kuwa basufi awanni biyu da gama wayar ba,yakuma sani banza bata kai zomo kasuwa,jiki a mace ya d'aga wayar....

"Baba na na gode da abinda ka sakamun dashi na sakar mun mama na da Kayi, ka mayar mun da ita k'aramar bazawara,ka tozar tar dani,baka dubi halin rashin Ameer danake ciki ba ka sakar mun yarinya,me kake so nace da iyayenta? Wlhy ka wulakanta ni fiye da tunaninka,kuma ka sani sena rama da yardar Allah Mamana Zata auri miji wanda ya fika lallai ka Turo mun ita as soon as possible sabida ta sanar dani ba iddar ka a kanta zamanku tare yanzu had'arine Babba ba k'arami ba" kafin yayi magana ta kashe wayar koda ya kuma kira wayarta a kashe gashi feenah bata gida yanzu bare ya kira ta bata,dafe kanshi yayi yata kuka tamkar k'aramin yaro,seda yayi me isarsa sannan ya tashi zuwa gida,d'akin Elham ya wuce kai tsaye ya tarar ta idar da sallah tana adua zama yayi harta idar,juyowa tayi ta kalleshi ta d'auke kanta

"Hafsat mesa kika mun haka? Mesa zaki zab'i had'ani da mahaifiyata? Menene ban miki ba a rayuwa? Sabida kawai ki dauwama a farin ciki na sadaukar da nawa farin cikin,Ashe ban cancanci ki rufa min asiriba? Bayaga haka na gama yanke hukuncin zan kama aure na,Mesa bazaki fara tambaya na tsarin dana mana ba" wani mugun kallo ta wurga masa tace a fusace

"Wlhy Kayi kad'an na kuma zama matar har abada,da kake zancen kama aurenka sekace wata tinkiya kokuma dabba,bakada labarin cewar Na gama idda,dole ne se an sake daura mana aure,kuma bana buk'atar k'arasa rayuwata da ragon namiji,mutumin daze bar ragamar gidansu ta lalace sabida rashin lissafi,aure na ya kare dakai har abada,banida iddar ka kuma Baba me gadi ya kaini islamiyyah,an sanar dani cewar idan idda ta yanke baza'a k'ara komawa aure ba se an d'aura kuma da waninka zan d'aura bada kaiba,na gama dakai har abada" duk girma irin na Abdul kasa daure wa yayi ya saka kuka

"Elham wlhy bazan iya rayuwa batare dake ba,kuskure ne nayi kuma na gane kuskurene plss give me a second chance" dariya ta kwashe dashi "Off course I can give u one big another chance to destroy my life" matsawa yayi kusa da ita yace

"Ba haka bane Elham,wlhy kece rayuwata gaba d'aya, banajin zan iya rayuwa baki" ka tayi magana wayarta ya soma ringing, dauka tayi taga yaa Ibrahim ne,d'agawa kurin tayi,t wani shagwabe murya

"Yaa Ibrahim dan Allah fa tun yaushe na kiraka shine se yanzu kake kirana?" Daga d'aya bangaren kuma Murmushi yayi najin dad'i yace

"Kiyi hakuri Rose kinji,inata aiki ne yanzunnan na shigo gida go lunch ban ciba" K'ara langwab'e murya tayi tace "Yaa Ibrahim kai kuwa seka riqa wani tunamun da yaa faruk na,shine yake kirana da Rose" Murmushi yayi shi yakasa gane kan Elham yanzu kuma tace dashi wai aurenta ya mutu,kuma batada Idda dama auren dole akayiwa dukkansu

"Ehn love one tintin Kodai yanzu da yaa faruk za'ayi aurenne?" Dukda tasan cewar Abdul bawai yana jiyo me Ibrahim ke cewa bane,amma seta tsinci bakinta da furta Kalmar "Bazan kuma aure a gidan sarauta ba,indai yaa faruk ne na hak'ura gaba d'aya, kawai dai sunanne yake zuwarmun da good memories damuka kasance a tare,he's such a nice person,nasan da ace Shina aura,da Banyi zaman zawarcin k'uruciya ba a yanzu,baze tab'a saki naba sabida yana sona sosai"

"To kiyi hakuri wata rana se labari,idan na kammala abinda nake zanyi kiranki" sallama sukayi ta wuce bathroom kai tsaye tana me jin zafin yanda zuciyarta keso ta bata kunya akan Abdul,mesa takejin tausayin sa ne?" Wannan itace tambayar data kasa samun amsarta tuni.....

Juyin duniya Abdul yayi amma Elham takasa bashi fuska,hasalima zagine ke Shiga tsakaninsu,a haka a rikice ya dakatar da duk abinda yakeyi ya kwaso ta suka dawo Niger.......

Zagi na wulakanci momy ta masa,yashiga magiya amma fir taqi saura rarsa,iyayenta sunyi bak'in cikin wannan wulakncin sedai wannan karon a wurin momy ta dawo da zama gaba d'aya,d'akin feenah shine ya zama nata,hankalin Abdul be kara tashiba seda yaga har me martaba Fushi yake dashi, shirya wa

Please Login or Register in order to submit comment