Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wanda kowa yasan haukanta takeyi sabida tun farko shi Abdul baya san sarautar balantana ma yayi kisa akanta.........

Har cikin Elham yashiga watanshi na haihuwa suna Niger wannan umarnin mahaifin Abdul ne, wata rana da yamma Elham ta tashi da labor ita kad'ai Abdul yaje Kano amma a ranar ze dawo da kanta takira momy ta sanar mata tanajin labor ne yazo mata aikam cikin ikon Allah segashi momy da kanta ta karb'i haihuwar agida sabida koda tazo har kan baby ya soma shirin sulmiyowa ta sunkuco little princess d'inta kyakyawa me matukar kamanni da ita,har sumar kan babyn irin nata tayo,cikeda murna aka sanar a fada take agun me martaba yayi umarni da azo masa da babyn aikam take yabata kyautar wani katafaren kamfanin sa na saqa,kuma ya bata sunan momy,dama a fada suke zama tunda cikinta ya tsufa,se Wuraren 9 Abdul ya qaraso a fusace yazo gidan yana zuwa yaganta zaune a parlor itada wasu hadimai

"Sannu da zuwa yaa Abdul?" Tace dashi tana me kallonshi ko duban inda take beyiba yace "yauwa" atakaice ya wuce ciki abinshi,mamakine ya kamata ta miqe ta baiwa dayar babyn ita kuma tabishi ciki yana daga cikin wardrobe tace "yaa Abdul lapiya dai kashigo cikin gida ranka abace?" Cikeda fusata yace

"Bansaniba tsabar rainin hankali shine tun karfe hudu nake kiranki amma baki daga ba kuma har yanzu baki kirani back ba,ko kinaso...ya zaro kanshi daga wardrobe d'in yana mata magana atake yayi hooking gani ba ciki a jikinta,da sauri yazo ya riqeta da mamakinshi yace " Blossom yadai?" B'ata rai tayi "kaci gaba da masifan da kake mana,banda haka ina fama da labour zaka zo kanamun masifa,Allah ni banmasan inda na wurgar da phone naba,kuma fa nasha wuya,shine kokace ina Baby" wara idonshi cikeda mamaki "Blossom wai da gaske kin haihu? Wlhy babu wanda ya sanar mun hasalima ban lura ba ciki ajikinki ba se yanzu,me kika haifa mun ina babyn?" Murmushi tayi "Baby girl tana hannun hadima adama" wani uban tsalle ya daka yana ihun murna da gudu ya ruga parlor hadimanma sunsha mamakin yanda ya manta da wani girman kan mulki ya sungume y'arsa yana tsallen murna..

*ku taya Nu'aiym da adu'a wlhy bashida lapiya*

Mom Nu'aiym
[1/8, 10:32 PM] Sha'awa: 🌞HAFSAT ELHAM🌞*

Billy Galadanchi

Haske writer's Asso💡

Vote me on wattpad@68billygaladanchi.
Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).

                          29

Zanen Elham ta duqufa tanayi na wani kata faren kamfanin da za'a bud'e a qasar Saudi wanda aka baiwa Abdul kwangila Shikuwa haka kawai yace lallai itace zatayi wannan zanen,yau kusan sati biyu tanayi,tausayinta yaji yabata wahala har kusan k'arfe biyu na dare tana abu d'aya dafa kafadar ta yayi yana daga kwance yace "Blossom mana ki kwanta inyaso da safe kya qarasa kinji?" Batare data dakatar da abinda takeyi ba tace "Hubby sauramun befi 30mnt ba plss kabarni na k'arasa" bece komai ba ya kwanta abinshi..... Lokacin da Abdul yaje gabatar da wannan zanen aka karb'a cikin jin dadi be boye musu ba akan cewar matarshice tayi zanen lokaci d'aya suka buqaci ganinta inda suka jinjina wa k'okarin datayi tare da kyaututtuka masu tsoka ciki kuwa harda gida sukutum kuma suma d'auketa aiki a babban kamfaninsu na Zane Zane, wannan abu ba karamin dad'i yayi Abdul ba alokaci d'aya ya nema mata gurbin karatu a jami'ar dake birnin London tafannin Zane,tana karatun tana aikinta haka suka rayu da juna cikeda Aminci kuma princess har wannan lokacin tana wurin momy susu kad'ai suke zaune  a london d'in suna sha'anin su,wani yammaci suka shirya zuwa yellow London Beach, dogon wandon jeans ta saka blue sa top red,sannan ta daura qatuwar rigar sanyi light brown a sama ta saka hula brown da shade ruwan k'asa shima, ba k'aramun kyau tayi shima kusan irin shigarta yayi suka d'auki hanya a beach elham matashin kai tayi da cinyar shi tana cin strawberries,hannunshi ya d'aura a saman kanta yace "Blossom dama fa inaso muyi wata magana dake" batare data baiwa abun muhimmanci ba tace "To bismillah ina jinka" d'an shiru yayi sanda ta qara cewa "Enhm hubby inajinka menene?"

"So nakeyi ki haqura da karatun nan da kikeyi" sarqewa tayi da Berry d'in da takesha ta miqe da sauri ta juyo ta kalleshi "meya faru hubby? Meya sameka? Meye zesa na dena karatuna ? Wani abin na maka ne? Kokuwa dai haka kawai?" A rud'e ta jero masa wayannan tambayoyin, d'an murtuqe fuska yayi yace "Ba abinda kikamun kawai dai banaso ne ya isheni haka ke har aikin ma ki dena banaso" shiru tayi ta qura masa idonta da a wannan lokacin har sun sauya launi zuwa ja tamkar gaushin wuta,dak'yar ta furta

"Yaa Abdul dan Allah kayi hakuri ka barni na qarasa karatuna kuma inajin dad'in aikina" harara ya wurga mata "Bazan haquraba naga alama kinaso ki maidani qaramun mutum sabida haka daga yau dukka biyun na dakatar dasu bazaki yiba" kasa riqe hawayenta tayi

"Yaa Abdul lapiya lau fa muka fito daga gida kuma bansan menene ze shafi aiki na da karatuna da sauri haka ba mena maka?? Sauramun shekaru biyu kacal fa na kammala" k'ara tamke fuska yayi

"Nasani sarai lapiya lau muka fito kuma ai wannan ba wai shawararki nake nema ba umarni ne nake baki,daga yau na dakatar dake daga zuwa skul d'in aikin ma ki rubuta resignation later ki basu,ke gaba d'aya ma Nigeria zaki koma da zama, shekaru biyun dakike cewa Sune suka rage miki bansan abinda zaki zamar mun ba idan na barki kika karasa sabida haka bazakiyi ba" zaro idonta tayi waje cikeda tashin hankali

"Yaa Abdul to yanzu nikam mena zama arayuwa?? Konayi maka wani laifin ne hala?" Tsawa ya daka mata "Ba abinda kikamun kurin dai bazakiyi bane,kuma kinji na fad'a miki Karki k'aramun maganar skul d'innan kuma kafin hutun dakika d'auka ya qare lallai kiyi resigning" bata qara cewa komai ba haka ta share hawayenta a zuciyarta tana da d'a nanata innalillahi wa Innah ilaihirraji'un ba adadi,har suka bar wurin ba wanda ya kuma qara cewa komai,koda suka je gida kowa part dinsa ya nufa,a can Elham ta zauna ta dirza kukanta ma ishi,ko bayan isha bata fito ba haka Shina bebi ta kanta ba sabida abinda tamasa ba karamin b'ata ranshi tayi ba,yaga alama idan yayi wasa London din Zata haukatar masa da ita......washe gari ma bata fito ba sabida bataji dad'in yanda ya wofintar da itaba bayan kuma ba haka ya saba mata ba kuma ba rashin kunya ta masa ba,a part nata kurun tasha fresh milk ta shirya zuwa skul se time da takeda lecture sannan ta fito,a parlor ta same shi taje ta durkusa kaman yanda ta saba tace "Sabahul khair  hubby" kallonta yayi fuskarsa a daure yace a dakike "kin tashi lapiya?"

"Lapiya lau zan tafi skul ne inada test" da mamaki ya d'ago ya kalleta amma seyayi kokarin Kawar da mamakinshi yace "Allah ya sanya ayi a Sa'a"  "Ameen" tace a taqaice taje ta dauki key a inda suke ajiye key na motocinsu tafice,wannan abin ba qaramun tunzura Abdul yayiba aranshi yace "Wato ma ban isa ba kenan? Lallai kuwa zan shayar dake mamaki" ita kuwa harga Allah bata dauka komai ba batayi tsammanin kawai sabida yace Zata dena zuwa skul ba shikenan Zata dena zuwa ta Zata zeje skul d'inne ya sanar musu Zata dakata tukunna,da wannan tayi hakan, wannan kenan.

*Washe gari*

      Koda Elham tayi wanka tazo ta d'auki key ba key kona mota d'aya a wurin dasuke ajiye Key's na motocinsu d'akinshi ta nufa nanma bayanan,d'aga wayarta tayi tayi kiranshi yana d'agawa suka gaisa tamkar ba komai tace "hubby ba key na mota ko d'aya awurin ajiyewa?"

"Ina dukkanin motocin nine na siya da kudina?" Mamaki maganarshi ta bata a hankali tace "To hubby me kuma ya kawo wannan maganar?" Katse kiran kurin yayi batare dayayi magana ba  ita kuwa tabi kan wayar tata da kallo,sam bata fahimci inda ya dosa ba kuma ta kasa gane kan wannan fushin nashi batasan dalilin suna zaman zaman su lapiya ze tsiri masifa ba,haka tayita fama har sukayi wata fiye da d'aya baya kulata,wannan ya sanya tayi resigning dukda company d'in basuso hakan ba Amma ba yanda zasuyi kasancewar tamusu alqawarin bayan gama karatunta zata dawo wa aikinsu.......A parlor yana zaune yana karatun news paper yana kurbar coffee a hankali ya d'aura k'afa d'aya kan d'aya da madubi Sanye a idonshi tazo ta zameshi,kusa dashi ta zauna a k'asan kafafunshi tace cikin sanyin murya

"Yaa Abdul dan Allah magana nakeso muyi dakai" beko kalli inda takeba bare ta saka ran ze saurareta hawayene ya soma sintiri a akan fuskarta takuma cewa "Yaa Abdul dan Allah Kayi hakuri wlhy nayi dukkanin abinda kakeso, karatun ma Kaine kawai nake jira kaje ka dakatar dani" rausayar da kanshi yayi D'auke da Murmushi akan fuskarshi me nuna irin kanki akeji kenan sannan yace yana me zummar barin wurin "Hafsat dama ke nake jira kiyi Hutu muje gida,so na kammala shirye shiryen da komai ranar Tuesday zamu wuce" kukan tane ya tsananta taje tasha gabanshi tana kuka ta qanqameshi "yaa Abdul wayene yake k'ok'arin shiga tsakanina dakai? Mena maka arayuwa dana cancanci wannan horon,ai kinnan dakaina na dakatar dashi karatunnan kuma qarashen hukuncinka kawai nake jira dan Allah Kayi hakuri" hannunshi ya saka ya b'amb'areta ajikinshi sannan yace bayan ya qura mata ido "A zatonki kin fini wayo,a tunaninki kin fini kwarewa a rayuwar turai a tsammanin ki bazan tab'a gano mugun abinda kike aika tamun ba,Toki sani wlhy nasan komai sabida haka kije can da taurin kanki,ina watannin mu biyu a haka baki damu ba,kinfi damuwa da karatunki,kinfi mayar da hankalinki akan neman ilimi to kije na dena hanaki karatun aikin kuma kije kiyi tayi ba ruwana dake da rayuwar ki gaba d'aya wlhy,ke har yanzu girman kanki kikeji da ganin Kud'in watace,so please kiyi sha'aninki" daga nan ya wuce ya barta gun a tsaye tana famar rusa uban kuka,gashi ta kasa nunawa kowa damuwarta.

*Nigeria*

Tunda suka isa momy ta hadasu da Princess suzo da ita,Abdul idan ba cikin mutane ba ba ruwanshi da Elham,ko abincinta baya ci,kallo daya me hankali ze mata ya gano sam bata cikin kwanciyar hankali,ko mahaifiyarta ta fahimci hakan kuma data tambayeta setace da ita stress din karatu ne ke damunta,dukda bata yarda ba amma haka tayita hakuri ta qyaleta, tafito daga gidan mahaifiyar ta zuwa sashen momy ga had'u da raihan haka kawai taji gabanta na faduwa cikin dakiya ta tsaya Su gaisa,bayan sun gaisa kamar abun arziqi sekuma Raihan ta kalleta tace

"Elham sekuma mukaji zance mara dad'i Ashe yaa Abdul aure ze qara? Ni wlhy se yanzu ma nakeji biki saura sati uku,da har inajin haushi zai auro miki yar talaka wa sekuma na tuna duk k'anwar ja ce,Allah ya sanya alkhairi acikin bikin" haka Elham taji wannan zancen tamkar saukar aradu aranta tace "Aure kuma? Nashiga ukuna,dama akan wannan yaa Abdul ke wulakanta ni ? A fili kuma se tace tana me tattaro nutsuwarsa da kokarin wanzar da yalwar murmushin yaqe a fuskarta " Hakane Wlhy kinji dai abin alkhairi, nima kuma Senayi godiyar Allah sabida Sa'a had'aka kishi da 'ya'yan masu kisan kai wlhy gwara maka yan uwanka talakawa da basu san tashin hankali da hadama akan mulki ba" sumsum Raihan ta wuce batare da ta koma magana ba,anan tabar princess ta wuce gidansu a rikice,tana tuqi tana kuka duk tabi ta rud'e ta gigice, a d'akinshi ta wuce ta sameshi yana waya,zama tayi kusa dashi tana sharar k'wallah harya idar,kallonta yayi yace

"Ke lapiya meye haka?" Tana sheshekar kuka tace " Yaa Abdul waida gaske zaka k'ara aure? Da gaske nanda sati uku aurenka ban saniba" tsaki yaja irin dama akan wannan kike mana kuka,gincirawa yayi yace yana Murmushi "Ea Hakane aure zanyi kuma nan da sati ukun,Meyene aciki to?" Zare ido tayi tace tana me riqe masa kafa "yaa Abdul mena maka zakamun hakan dan Allah Kayi hakuri,wlhy idan kamun haka mutuwa zanyi bana san kishiya tsoron ta nakeyi bazan iya had'a ka da wata ba" miqewa yayi a fusace "ke meye haka? Sabida wannan borin zaki zauna kinamun kukan raini,ubanwa ye yace ki aika tamun abinda kikemun tsabar mugunta, to dolene na auro uwa ta gari wa y'ay'ana wadda Zata kulamun da princess kuma ta haifa mun da yara masu tarbiya kuma na gari kekuma meye nawa na miki yanda kikeso karatu kikeso da gayu da bariki nikuma haqiqanin sunna nakeso na raya ta usuli bawai shirmen kiba" wani razanannen qara ta saka da kuka me ban tausayi......

Mom Nu'aiym
[1/8, 10:32 PM] Sha'awa:      ☀️Hafsat Elham☀️

HASKE WRITER'S  ASSO.

Wattpad@68billygaladanchi.

Sadaukarwa GA qawata Hafsat  Abubuakar qaya.

                                 30
Ethan abun duniya ya isheta,ta Kasa gane inda zancen Abdul ya nufa kome Tamasa ai bata cancanci wannan d'anyen hukuncin  ba, shin Anya Kuwa Abdul Yasan Abinda yake shirin   aikatawa? Da sauri ta miqe  ta zari key na motar ta ta nufi fada tuqin  takeyi Kawai amma Sam hankalinta baya Kan abinda takeyi se uban Kuka takeyi bata tab'a Zata cewar haka azabar kishi yakeyiba ji takeyi tamkar zuciyarta zata faso qirjinta ta fito wani tafarfasa da d'aci zuciyarta ke Mata ikon Allah ne kadai yakaita fada lapiya, Ko lucking  car batayiba ta afka cikin gidan  Kai tsaye part din mommy ta nufa, a parlo  ta Sameta itada Abdul Suna hira Kai tsaye Saman cinyoyin mommy ta d'are ta soma Kuka da sambatu

"mommy Dan Allah Kiwa yaa Abdul magana yamun rai idan wani abun namasa yayi hakuri wlhy banason kishiya banso ya had'ani da kowa, karatun Kuma da bayaso shima na  dena bazan ma koma qasar ba" kukan takeyita baji ba Gani,d'agota mommy tayi " Elham Karki Zamo cikin mataye Marasa yarda da k'haddara ina  tunkafin kuzo me gidanki ya sanarmun Kinsan komai, shine kuma Yanzu zaki biyewa mutane su rikitar dake a karin banza,ina nan ina faman saka Miki albarka akan yarda da khaddarar dakikayi Ashe ba haka bane zaki biyewa mutanen banza su kaiki su Baro,to ki Sani zamu b'ata dake kishiya ba abun gudu bace 'yar uwace kuma abarso,karna kuma ganin kin Tashi hankalinki  Akan zancen kishiya  tunda mijinki Yana qaunarki, Maza  tashi ki koma dakinki yanma nayi" mamakin Jinwai tun Kan Suzo ta Sani  takeyi amma batace da mommy  komai ba Tamata godiya jiki ba k'wari ta Kama Hanyar waje tun a Hanya kafin taje gun mota take ganin Jiri ya soma kwasarta har Abdul yafito tana nan bata qarasa gun Mota ba tana tafiya tana bin bango tana layi ,ta bayanta ya tsaya Yana  nazarinta Harga Allah badasan ranshi zeyi aurennan ba amma yana mamakin sanda Elham tayi wayewar aikata abinda ta aikata ba wannan kadai zeyi ya rage jin zafinta aranshi, da k'yar ta isa mota koda tashiga ma sam batasan me yakeyiba, Allah shiyake halittar mata da mishi amma Elham tana daga cikin mataye Masu azababben kishin tsiya, da k'yar ta iya yin rivers  ta harbawa motar wuta ,mahaifinta ma dayaqi yarda  ya dena aikin gadin  binta yayi da Kallo harta bacewa ganinsa ganin yanda batako tsaya sunyi sallamaba kuma yaga ta sharara da wani uban gudu na Allah ya kiyaye....... Ganin haka ya sanya Abdul juyawa ciki aranshi yana Mata  aduar sauka lapiya.  

   Yana nan zaune wayar mommy ya soma ringing,d'agawa tayi ganin baquwar lamba ya sanya ta ajiye bata d'agaba ta mayarda dubanta Zuwa gareshi tace

"Babana lapiya dai ka tafi kuma ka dawo? " Sosa kanshi yayi yace " Kawai Naji bazan iya zuwa  gidan Yanzu ba" kan tace wani abu wayar yafara ruri a Karo na biyu,ganin Sunan Elham NE,  da Sauri ta d'aga

"Mamana ya akayi? " muryan namiji tajiyo "Haj bame wayar bace tayi accident  Anan kan Hanyar government  house kuma gata a kwance sedai ace Allah ya sauwaqa, Yanzu zamu wuce da ita babbar asibitin kwararru ta jiha shine muka Kira ganin Kamar number dinkine a sama kuma munma Kira wacce Muke tsammanin ta mijintane amma be d'aga ba" miqewa momyn tayi da salati d'auke abakinta

"Malam injin dai Tana da rai? " ta wurgo masa wannan tambayar "Haj bazan iya cewa komai ba, Sabida banida masaniya,kurun dai na kula she's unconscious" a gigice ta ajiye wayar  ta Kalli Abdul

"Babana tashi muje ba lapiya, Elham tayi accident  a Hanyar government  house" haukace mata ne  kurun beyiba amma Kam ya kusan zaucewa, Kasa tuqin yayi kurun yafito ya tsaya yana tunanin wane Hali Illy take cikin, seda driver yazo yajasu,suna zuwa wurin da akayi accident  d'in Abdul ya dakatar dasu Kallo daya Abdul yayiwa motocin guda biyu zufa ta keto masa Sam dazaran kaga Motan Elham Kasan akwai Marsala, fitowa yayi yaje wurin mutanen dake tsatsaye a wurin " Malam Dan Allah meya faru? " ya tambaya bayan ya musu sallama "AI malam wlhy wani mummunan hatsarine ya afku, wata yar matashiyar budurwace tazo dagudu k'addara ta afka mata Kasan wani lokaci idan ajalin mutun yazo bayan Sanin me yakeyi kurun baiwar Allah nan tayi maja da waccen motar ta ibar yashi kaga yanda motar ta ta dawo wlhy malam bakaga yarinyar ba gwanin ban tausayi ni inaga wlhy ko aure batayiba amma mutuwa tazo mata a bazata" wara idonshi yayi ya dafe k'irjinshi dake masa zafi yajuya zuwa mota maganganun da mutumin ya fad'a suna masa yawo aka, ya Kasa gaskata zancen mutumin,koda yashiga motar suna masa maganr kasa amsasu yayi kukan ma ya gagareshi a haka har suka k'arasa asibitin, shine ya fara fitowa daga cikin motar ya nufi cikin asibitin.....

Kallon nutsuwa likitan yayiwa Abdul kan yace " Yarima tun kafin faruwar wannan accident d'in binciken mu ya nuna mana cewar matarka na cikin matsanancin damuwa, Zama mu iya cewa shine yayi sanadin wannan accident data Samu Sabida Tana d'auke da matsanancin ciwon zuciya Wanda akalla zefi shrkaru goma acikinta faruwar wannan abun ya sanya gaba d'aya ya taso mata lokaci d'aya had'uwar sa kuma da wannan accident yasanya kuma lokaci d'aya zuciyarta ta buga!!!" cike da razani Abdul ya d'ago ya kalleshi "Bugawar zuciya fa kace doctor? Mekenan Kake shirin sanarmun? Kuma ni iyakar sanina matana batada ciwon zuciya mema ze haifar mata da ciwon zuciya??" tasowa likitan yayi ya zago ya dafa kafad'arsa yace "Abdulrahman ko bansankaba bazan make k'aryaba balantana muntaso Dakai tun Muna Tara atare, ba dalilin maka haka,abu na gaba kuma ka sani matarka wannan ciwon ya jima ajikinta Danma Tanada qananun shekarune ya shekaru ne ya sanya be bayyana kanshi ba,na tabbatar damuwane ya haddasa mata wannan accident d'in Sannan kuma fad'uwar gaban data Samu yamun faruwar wannan Al'amarin shine ya haifar mata da Bugawar zuciya sabida a zahirin Gaskia bataji wasu raunuka masu yawaba dazasu kaita ga wannan abinba, buguwane kurun Se goguwa kad'an" nisawa Abdul yayi cikeda damuwa

"To Yanzu doctor Meye abinyi?" shima doctor d'in nisawa yayi kan yace " Tsakani da Allah Abdul duk duniyarnan babu Wanda ze iya sanar maka halin da matarka zata kasance daga Yanzu zuwa kowane lokaci Allah ze iya bata lapiya kazalika daga Yanzu zuwa ko wane lokaci zata iya Rasa rayuwarta!" miqewa yayi "Haba Dr marwan ai ba'a Yankewa mutum hukunci irin haka, nasan Allah shike rayawa da kashewa amma Dan Allah ka taimaki rayuwar Hafsat da ikon da Allah ya maka kaji" Sosai likitan Yamasa bayani akan ciwon Nata sannan Yakoma d'akin da take ya qura mata Manya Manyan idonshi yana sauke siraran hawaye a hankali aranshi yanajin zafin abubuwan daya aikata agareta gani yakeyi tamkar ciwon zuciyannan Nata shine sanadi,momy ce tazo ta dafashi Taja hannunshi zuwa cikin d'akin tanemi sanin Meke damun Elham yana kuka ya sanar mata komai da doctor ya fada masa, ya qara da cewa

"Mommy wlhy nasani nine Sila,wata qila zafin qaryar dana mata ne nace dake tasan zanyi aure batasan da zancen ba dawowarnan namune dazu takeji abakin Raihan, kuma Nafi watanni uku Bana kulata akan naga Tanasha qwayoyin Hana d'aukar ciki na sanya ta dakatar da aikinta na kuma tilastata barin zuwa makaranta, sabida taqi dena zuwa makaranta ya Sanya nadena shiga harkarta kuma na dakko zancen aure batare da sanin taba,hasalima yarinyar dazan aura ban Santaba seda Nazo nan Moh ne yanemamun ita dukdan na baqanta Ranta a zatona batasan haihuwa danine sabida taga qaddara na yawan fad'awa zuri'armu, Yanzu abinda doctor kecemun dama Anaso suna d'aga wa haihuwa qafa sabida condition nasu lapiya bata wadacesuba" Sosai mommy ta zazzaga masifa daga baya ta saka kuka sabida batasan yanda zatayi ba inhar Elham ta rasu .......

*Bayan Sati biyu*
Elham taji sauqi Alhamdulillah, sedai har wannan lokacin batawa Abdul magana, idan ze shekara yana mata magana sedai ta tasashi agaba da kuka, bata ce masa ci Kanka amma takan d'an tab'a hira dasu mommy, Suna yawan kwantar mata da hankalin Kamar yanda doctor yace, a haka har taji sauqi ta warke Sarai aka sallameta....... A yanda Elham ta zata yau saura Kwana uku d'aurin auren batada labarin cewar tun Ranar datayi accident mommy ta Hana wannan maganar kuma Koda bata hanaba abun gaba d'aya ya ficewa Abdul akai,tana zaune a parlo ta gama Shan magungunan ta tana kubar fresh milk a hankali,zuwa yayi ya zauna kusa da ita yajanyo hannunta ya cura a nasa "Blossom ya jikinki?" da dan mamaki ta kalleshi kasancewar tasan ya dena kiranta da wannan sunan, a hankali ta kalleshi ta saya d'an murmushi a fuskarta sannan tace "Ango kasha mai Yanzu Kake shigowa" murmushin Shima yayi "Angon hafsatul Elham ba" bata kulashiba Yakuma cewa

"Blossom Dan Allah kiyi hakuri ki gafarceni abin da na miki,wlhy Sam banzata akwai dalilin ki Nashan k'wayoyin Hana d'aukar cikiba kuma zancen auren danamiki Shima na janye har abada" gyaran murya tayi tukunna tace cikeda nutsuwa

" Bance ka fasa auren kaba sabida ni nayi kad'an na haramta maka abinda Allah ya halatta akanka sedai Nasha mamakin sauyawar halayenka akan laifin da bakayi bincike akanshi ba,sabida ina tunanin damuwar dazaka Shiga idan har Kaji cewar ina cikin wannan halin na ciwon zuciya na boye makane sabida Karka shiga damuwa Nabi sha'warar doctor ne nayin tsarin Iyali sabida condition nawa,nakuma kasa sanar maka sabida kurun Karka gano ciwon dake damuna kashiga damuwa, Ashe Kai a wurinka ba haka bane kana iya watanni baka kulani zabida Kawai Dan wannan abin,amaimakon ma kazo ka sanarmun laifin dana maka Seka dauki wannan matakin" D'an dakatawa tayi sannan Taci gaba " Dama kaje ka auri wacce kayi niyyar auren Danni wlhy bazan zauna dakaiba kaficemun arai kuma karkayi tunanin samuna akusa" tana gama fad'ar Hakan tamiqe tabar wurin,da ido kurun ya bita bezata words Nata har zuci bane.......

Wasa Farin girki fa Wuni d'aya cur ba Elham ba kayanta ya zaga gida da dangi kaf be gantaba kuma wayarta akashe hankalinshi ya tashi Matuka bashiba bar mommy......

Mom nuaiym
[1/8, 10:32 PM] Sha'awa: ☀️Hafsat Elham☀️

HASKE WRITER'S ASSO.

Sadaukarwa GA qawata hafsat Abubuakar qaya.

  Vote me on wattpad @68billygaladanchi.

                              31
Zaman dirshan Abdul yayi agaban mommy "Amma babana Kaima da kanka kasani Sam baka kyautawa mamana bako?  Namijin kirki baya tab'a  Yiwa mace yanda kayi,kaine babba agareta kyautuwa yayi kan zauna ka nusar da ita kuskurenta amma ka dauki fushi batare da sanin ainahin meta maka ba, Yanzu Hafsat ta girma ta mallaki hankalin Kanta na tabbatar bazatayi abinda ze cutar da itaba,ba inda zanje nemanta kuma wlhy bazan tab'a  nema maka yafiyartaba sabida kayi Hali irinna qaranta gaba d'aya kayi Hali irinna mutane Marasa dattako musamman dakayi shirin aure bada sanintaba kuma kazo kace ta sani, ni maza bansan jin komai ka bani wuri" yana cikin qunan rai na Rashin hafsatul Elham,yatashi kurun batare da yayi magana ba Yabar  wurin, Kai tsaye part  nasu ya nufa ya tarar mahaifin hafsa na gida,cikeda girma mawa ya gayar  dashi bayan nan ya sunkui Dakai sannan yace

"Baba dama zancen Elham yau kwana biyu kenan bata gidana

Please Login or Register in order to submit comment