Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ke qara harzuqa Abdul,rarrashinta yashigayi har bacci ya d'auketa"

Wuraren k'arfe d'ayan dare me gadin gidan yaji motsi ana k'ok'arin bud'e k'ofar gate d'in a hankali yazo ya wuce jikin k'ofar gidan ya tsaya wayanshi ya janyo yakira Abdul,ya sanar masa,betashi Elham ba amma sarai taji sanda yake wayar kasancewar dukkanin su bawai baccin sukeba sedai dayake bacci b'arawo ne yakan sacesu wani lokacin suna tsaye a lab'e ya samu nasarar bud'e k'aramar k'ofar gate d'in da buhu D'auke a hannun shi ya ajiye ze juya Abdul yace me gadin ya bishi da gudu me gadin ya bi bayanshi kan yakai k'ofar ya rafka masa uwar sandarsa,take ya fad'i wurin a sume,Shikuwa Abdul da sauri wurin buhun yayi wari ne yabugi hancinsa tunkan ya qarasa bud'e Buhun daurewa yayi ya haska fitilar wayarsa ya qarasa bud'e Buhun "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un" itace kalmar dayake ta nanata wa yayinda yayi mutuwar tsaye warin ma ya denaji sabida ganin gawar sultan harta fara zagwanyewa,Elham da tunda yafito take binsa isowa tayi wurin batare da sanin saba,ganin sultan a haka Abdul a tsaye ya sanya ta ture Abdul da hanzari ta wawusheshi,mamakine ya kamata ganin fatarshi ta sab'ule ga uban wari alamomi sun nuna yafi kwana biyu da mutuwa, baka ma gane shine seka kula da kyau,hauka cewa tayi ta soma sambatu kankace meye wannan tafita hayyacinta dak'yar Abdul ya riqeta yana bata baki,kallon shi tayi acikin hasken fitilar wayarshi a daidai lokacinda me gadin ya dawo wurin da gudunshi

"Kaga yaa Abdul kalli sultan na,sun kashe shi fa kalli mutuwar wulakanci,kalli yana warin gawa kalli yanda fatar jikinshi ya zagwanyewa daga jikinshi, anya kasan wahalar da yaronnan yake sha kuwa?? Wlhy baka sani ba cewa akayi damu gawa zafi takeji idan ana mata wanka ma,kalli sultan fatar shi duk a sale kalli idonshi,wlhy zafi yakeji yaa Abdul ka tasheshi mana,sudais na be mutuba wlhy" jijiigata yayi yace "kiyi hakuri Elham dan Allah ki nutsu mana,kiyi hakuri kinji" batace komai ba ta k'ura masa ido,se kuma ta kwashe da dariya cikeda hauka tace

"Mesa ba zaka tasheniba ina bacci, yaya zaka barni ina bacci ina wannan mugun mafarkin, dan Allah yaa Abdul muje ciki mana" ganin tana wannan abin ya tsoratar dashi matuk'a....miqewa yayi shima ya kamo hannunta "Elham na plss mana me haka?? Ki nutsu kiji ni da kyau haquri zakiyi kinji k'addara ta riga fata an rigada an cucemu se hakuri" dukan k'irjinshi tayi "so kake kace dani wai ba bacci nake yiba,da gaske kake wannan sultan nane wannan,kalli fa da kyau wlhy wannan kalarshi tsanwa ne ni kuwa sultan na fari ne qal" kurin seta sake saka kuka,a haka ta sulale a wurin bata koda motsi.....me gadin ya kalla yace "waye wancan"

"Wlhy yallab'ai sale ne?" Da mamaki ya kalleshi yace "wane salen kake magana?"

"Sale dai sale wanda ka sani yallab'ai" d'aga Elham yayi zuwa mota yazo ya kai gawar sultan ma yana matsar kwalla,yace da me gadin ya fara d'aure sale sannan ya watsa masa ruwa,zashi asibiti ya Turo police anan d'in........


Sosai Abdul ya girgiza jin cewar kan Elham ya tab'u saka makon wannan abin daya faru da ita,sosai abinda ta gani ya girgiza ta Baza suce bazata warke ba amma fa sam Baza suce ga tsawon lokacin dazata d'auka ahaka ba,sedai abinda Allah yayi,kuka Abdul ya sakawa momy sosai sam zuciyarsa bazata iya d'aukar wannan abin ba,wanda ya kawo gawar kuwa anyi anyi dashi Amma sam yaqi magana....

A firgice Elham ta farka tana kurma uban ihu tana sambatu "Wai cewa suke dani Sultan ya mutu ni sam sultan d'ina be mukuba yaa Abdul me shine shaida agabanshi nabashi mama yasha,se kuma tasaka kuka tasoma kokarin kunce d'aurin da aka mata, sosai ta baiwa Abdul dake kusa da ita tausayi yasoma sharar k'wallah " Wlhy sun kasheshi kisan wulakanci fa ko binnewa beci albarkacin suka masa ba,gaskia nima sena kashesu,kuma bazan binne suba sesun dawo k'asusuwa sena mayarda su...sekuma ta kwashe da dariya...Abdul barin d'akin kurun yayi cikin tsananin k'unan rai ilahirin mutanen dake d'akin kuka sukeyi na matukar tausayawa Elham.

Mom Nu'aiym.
[1/8, 10:32 PM] Sha'awa: *🌞HAFSAT ELHAM🌞*

Billy Galadanchi

Haske writer's Asso💡

Vote me on wattpad@68billygaladanchi.
Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).

                            25

Zaman nutsuwa sukayi a gaban me martaba suna sauraren abinda zece yayinda yayi mintuna biyar suna saurarensa batare da yayi magana ba se can yayi gyaran murya xanna ya gyara zaman alkyabbar sa yace cikin nutsuwa

"Abubuwa da dama sun faru a wannan masarautar,kuma sanin kanku ne wayannan abubuwan ba masu dad'i bane,dukda yake sace sultan da akayi bawai acikin nan Gidan aka shigo aka sace shiba amma sarai ganin sale da gawar jaririn ya sanya mun tabbatar cewar daga wannan masautar ne,tunda kuwa sale shekararshi kusan talatin da biyar koma fiye da haka anan gidan, koda ya zo nan shekaru nsa basu wuce sha biyar ba har tsufa yazo masa gashi muna tare,yanzu wannan d'anyen aikin ya janyowa mahaifiyar sultan kamuwa da cutar tab'in hankali,tofa ku sani na rantse da Allah mabuwayi duk wanda na kama dasa hannun shi aciki ko waye shi saina hukuntar dashi,sale na nan na saka an kawo mun shi a masarautar nan da kaina zan bincikeshi yana nan a tsohon prison na masu laifi a masarauta gobe da yardar Allah zan bashi azaba mafi muni da Zata saka yayi magana koda beso ba, Mamana kuwa idan visa dinsu ya zama ready zuwa wani watan zan turata India adubamun k'walwarta" jin yayi shiru Haj habiba tace "yallab'ai har yanzu munkasa gane dalilin kirannan da aka mana,bansaniba ko satar da kisan jinjirin ya shafi nida iya laina ne?" Wata mahaukaci yar tsawa ya daka mata wacce a lokaci d'aya ta razanar da ita matuk'a bama itaba d'auka cin mutanen dake wurin

"Wlhy Habeebah zan nuna miki isa da k'arfin mulkin dana keda shi,idan baki saniba na sanar miki cike nake dake FAM kuma wlhy bazanci b'ata lokaciba wurin ganar dake kuskurenki kinji na fad'a miki,maza tashi ku bani wuri dukkanku" jiji a sab'ule dukkansu suka mik'e se adu'o i sukeyi na tonuwar asirin duk wanda ya aikata wannan mummunan aikin..... Wuraren k'arfe biyu na dare me martaba har lokacin be runtsaba yana nan yana zagayen gidan shida fadawanshi guda biyu, B'acin rai sam baya barinshi bacci tun faruwar wannan mummunan abin,muryar dayaji ne ya sanya ga dakatar dasu da hannu tare da nuni da hannu akan cewar su dakata

"Kaga burshi Me martaba fa na sanar maka da gaske yakeyi wannan karon,so yake ya dauko mana rigima,sabida haka wannan babbar damace agaremu dawowar da akayi da sale gida prison na nan gidan,zuwa zakayi ka bashi zab'i Kodai na mallaka masa dukiya me yawa ya koma inda ba wanda ya sanshi kokuma ka kasheshi" kallonta burshi yayi yace " Haj nifa nasan halin saleh,yanda yasha burin adama dashi idan an samu nasarar kashe Yarima faruk yahau baze tab'a barin wannan masarautar ba,ki bani dama kurun na kasheshi" shiru yad'an ratsa wurin kan tace

"Burshi wlhy kaga nifa harka da kisan kai ba santa nake ba,sanin kanka ne ko sultan d'innan bawai da gangan na kashe shiba hasalima dan kanshi ya mutu nida bansan a kashe kowa,ko yayyun Yarima ai gidan marayu na kaisu bana san harka da kisa karka kasheshi adai fitar dashi daga garin kota karfin tuwo ne" Sosa sumar sa yayi "Barin je in sumar da masu gadin in jashi kawai mubar nan" baya da baya me martaba ya koma seda burshi yayi gaba sannan suma sukabi bayanshi acan suna kallonshi ya wurga wata farar Leda yaja da baya had'e da toshe hancinsa,daya daga cikin fadawan dake tare da Sarki ne ya koma ya tashi wasu bardawa shi kuwa me martaba da daya suka lab'e wani wuri,shida sale suka fito sad'ad'a suka wuce Sarki ma suka bi bayanshi suna zuwa gate se gani sukayi fadawa sun zagayesu take aka kama Shegu......

Koda momy taji komai a bakin me martaba gigicewa tayi ta saka kuka dak'yar ya riqeta akan kartaje wurin habeeba har wannan lokacin ita habeeban batasan an damqe su sale ba kuma bata masan me martaba Yaji komai ba police kawai ya sanya akawo su zasu mata tambayoyi dole se ta fad'i inda takai yaran farko Wato yayyun Abdul sannan tayi bayanin zancen sultan menene laifinsa na sace shi kuma menene laifinsa na kasheshin da tayi......."

Hannun Elham acikin na Abdul ya qurawa fuskarta ido data kumbura tayi ja jajir se sheqi takeyi na wahala bacci takeyi sakamakon allurar baccin da aka mata sabida ta samu nutsuwa tamkar matacciya lokaci zuwa lokaci takan kwab'e fuskarta tamkar me shirin yin kuka kota yamutsa fuskar wanda dana hakan d'abi'ar datane,tausayinta sosai yakeji se adu'a yake ta tofa mata haka yakeyi daman dare da rana bashida aikinyi se zaman mata adu'a yana sharar k'walla,yau kusan wata d'aya kenan da faruwar wannan al'amarin kuma har yanzu bata sauya zaniba, Haj Habeeba dai a binciken da akayi dukkanin yayyun Abdul datakai orphanage susu biyu sun rayu acan sedai gabaki d'ayansu sun bar orphanage d'in sunyi aure da yan uwansu na wurin sun fara aiki, ba kad'an ba momy tayi kuka ace kana d'an Sarki ka b'uge da rayuwar gidan marayu tsabar san kai irinna Habeeba da rashin imani,abin bak'in cikimma wai D'ayan me suna jabir Allah ya masa rasuwa yabar matarsa da yaronsu d'aya,se kabir ne aka samu wanda yayiwa Habeeba Allah ya isa cikin buhu buhu........A hankali ta bud'e idonta ta sau kesu akanshi Koda suke a lumshe,a wahalce tace "Yaa Abdul yunwa nakeji sosai ka bani wani abin,se inajin jikina tamkar wata mara lapiya" da sauri ya miqe jin tayi magana irinta masu hankali da sauri yazo ya d'agata yace "me kikeso Kici blossom?" Narkewa tayi ajikinshi sannan tasaka masa kuka "wai yaa Abdul da gaske ba mafarki nake ba sultan naga gawarshi jiya??" Qara qanqameta yayi yace yana kukan shima "Blossom kiyi hakuri ba mafarki kikeba,haka Allah ya tsara abinshi" wani kukan ta kuma fashewa dashi me ban tausayi...

*Dan Allah Kuyi hakuri da wannan yan kwana kinnan bana samun zama*

Mom Nu'aiym
[1/8, 10:32 PM] Sha'awa: *🌞HAFSAT ELHAM🌞*

Billy Galadanchi

Haske writer's Asso💡

Vote me on wattpad@68billygaladanchi.
Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).

                           26
Sosai me martaba yayi murnar samun Lapiyar hafsa,matsala d'aya ne ta kasa kwantar da hankalinta abincinma taqi ci yanzu tunda aka tabbatar mata da mutuwar sultan kuma a hanyar data ganshi take kuka,me martaba da kanshi ya shirya yaje asibitin domin har wannan lokacin asibitin basu sallameta sunce se sunga yanda jikinta ya qarayi,a saman kujerar da masu zuwa duba marasa lapiya ke zama anan me martaba ya zauna ya fuskanci Hafsat sosai ya tattare nutsuwar sa akanta yace bayan yayi gyaran murya

"Mamana yaya Lapiyar jikinki? Ina fatar kin samu sauqi?" Sunkuyar da kanta tayi qasa cikeda kunya sannan tana hawayen data kasa tsaidasu tace

"Naji sauqi ranka ya dade jiki Alhamdulillah" sake yin gyaran murya yayi yace "Na sanar miki karna kumajin kin kirani da wani sunan bayan daddy,Aini mahaifinki ne" murmushin k'arfin hali tayi cikin hawayenta tace murya na rawa "To daddy" shiru ya d'an ratsa d'akin na wani lokaci kan yace "Mamana ko kinsan cewa Allah mahaliccin dukkan komai shine da kanshi yake rayawa kuma shine yake kashewa alokacin dayaso kuma yayi muradi,kamar yanda yake Talauta wa a sanda yazo yakuma azurta a sanda yayi muradi,kana ya fitar da rayayye a cikin matacce kuma ya fitar da matacce a cikin rayayye?? Shin kokinsa ubangiji shiya keda iko akan dukkan kuma shine qadirin ala manyasha'u,kokina labarin cewar agaban idona akayiwa mahaifina yankan rago?? Shin Hafsatu bakida labarin cewar acikin k'addarori na rayuwa taki k'addarar ta fad'o ne acikin mafi sauqin d'auka?? Labari ya riskeni cewar tunda Allah ya baki Lapiyar ki bakyacin abinci bakida aiki se kuka,Anya Mamana kinwa adalci kuwa? Anya Hafsatu kin godewa Allah akan manya manyan ni'imominsa akanki? Ashe ba wani babbar ni'ima bane Allah ya baki na samun lapia ba sanda kika Zata ba? Ashe ba babbar ni'ima bane agareki kin tashi kiga dukkanin Dangin ki suna farin ciki da samun Lapiyar ki?? Shin ko kinsan cewar mutane da dama dasuka samu irin matsalar ki a rayuwa suna nan suna yawo akan titi,bola da juji Nanne makwancinsu, abincin su a bola ruwan shansu a bola sannan kuma suturun su ma daga juji,sabida kasawar Dangin su daga lalurarsu ya sanya ko damar zuwa asibiti basu samu ba,Ashe bakya kulawa masu irin laurarki koda me basu sadaka basa samu sabida kasancewar ana qyamarsu kuma ana tsoron su,lallai Mamana ki farga kuma kiyi istigfari ki godewa Allah da ni'imominsa masu tarin yawa akan ki,ki kuma gaggauta neman gafarar Allah domin kin kasa jure guntuwar kaddarar dabata taka kara ta karya ba,sultan koda a kar kashin kulawar ki yake tsaf Alla ze karb'e abinsa idan lokacinsa yayinda,nasani mutuwar yaro akwai zafi amma shin ko kinsan tanadin Mad'aukakin Sarki akanki??" To akul d'inki karnaji kuma narka ga kin qara saka damuwa aranki inshaa Allah zaki samu wasu 'ya'ya masu alkhairi da tarin albarka arayuwa kuma da yardar Alla sultan ze zamto daga cikin yara masu ceton iyayen su a gobe qiyama". Godiya tashiga yi masa da adu'a gamawa da duniya lapia, sosai yaji dad'i ya mata sallama sannan suka juya shida fadawa nsa........

*Bayan kwana biyar*

Tun bayan da me martaba ya zo ya mata fad'a taji komai ya sure mata,ta mayarda lamuranta ga Allah take aka sallameta a asibiti, komawarsu gida ma ba karamar nutsuwa ya saukarwa Elham ba sabida mijinta yana matukar kulawa da ita,yauma kamar kullum da kanshi ya dafa mata Shawarma da pineapple drink ne sanyi,shine da kanshi yake bata tana ci sanda tayi dam,sannan yace

"Blossom idan Kinyi sallan isha semu kwanta ko?" Kallonshi tayi La langwab'e kai sannan tace "Hubby kafin na kwanta wanka nakeso kamun kaga sanyi ake jikina kuma bayasan sanyi,ruwan zafi sosai zakamun wanka dashi seka shafamun mai den ka sakamun kayan bacci sannan kuma ka rarrasheni nayi bacci" murmushin sa me laushi ya sakar mata sannan yace "blossom duk wanna aikin ni kad'ai?"zaro ido tayi sannan ta shagwab'e fuska ta Turo baki " Ea mana kai kad'ai fa ko bazaka mun ba?" Mikewa yayi "waaa ni na isa?? Wannan ai dolene na miki har brush ma zan miki kannan" miqewa yayi har ya kusa Shiga d'aki ya juyo ya kalleta"blossom to muje mana" maqe kafad'a tayi "Ni bazani dakai naba,sedai ka d'agani zuwa bedroom d'in" dawowa ya d'auketa ya manna mata Sumba a wuya "Blossom wlhy rikicin ki seke amma yau d'innan zanyi maganin rigimar nan taki,sabida kwana biyu kinga ina raga miki ko?" Batace komai kurin dai ta yamutsa fuska ne,da kanshi ya mata wanka ya shirya ta sannan shima yayi wankan ya shirya kwanciya, fitilar d'akin ya kashe musu sannan ya kwanta suna fuskantar juna janyota kurin yayi ya rungumeta ajikinshi sosai amma ba abinda yakeda niyyar mata,ba kad'an ba Ellyn yaa moris tayi missing uncle baby d'inta cikin sanyin murya da shagwab'a tace "Uncle baby" hannunshi yafara d'aurawa akan waist nata shima ahankali yace "Aunty baby ya akayi ne?" Hannu tasaka ta daki bayanshi da wasa cikeda shagwab'a tace "Nice kuma Aunty baby Allah kuwan banaso?" D'an tsikarin ta yayi seda ta zabura sannan yace " to sanar dani Elilin moris me Nene?" K'ara matsawa tayi jikinshi sosai sannan tace "Bakinka da harshenka nakeso kabani aro" Murmushi yayi koda suke a duhu yace "Nabaki aronsu in nayi magana dame?" Sarai yagane inda ta dosa neman magana yakeyi,shura k'afa ta somayi "Dan Allah fa yaa Abdul wlhy matsu" hannunshi ya zura acikin yar rigar baccinta ya kaiwa dukiyar fulaninta cafka, yasoma murzawa a hankali,kasa hanashi tayi sabida wani irin desire takeji a wannan ranar bakinshi ta kama da kanta ta soma tsotsar harshensa tana mayarda numfarfashi kaikace cinye harshen zatayi shima d'in wannan kissing nashi datakeyi passionately ba k'aramin tayar masa da abubuwa sukayi ba,kuma yasha mamakinta domin wannan ne karanta na farko data masa haka,dan kanta tayi pulling out,sannan ta saqala hannunta a wuyanshi,tace cikin wata murya dabe tab'a ji tayi magana da ita "Hubby zaka barni nayi ganda nakeso dakai?" Hannunta dake wuyanshi ya d'aura nashi akai yana murzawa a hankali "sure u can my princess I'm all urs" k'ara matsawa tayi jikinshi ta manna masa wani kiss a k'irjinshi sannan lokaci d'aya ta tuna da hudubar Aunty husna " Elham wlhy karki cuci kanki ki samo tamkar wata hoto a wurin mijinki,komai sedai shi ya miki,kinga d'an breast d'innan na maza ma kamawa kake da baki kana wasa dashi da harshe kuma kana sha,sa annan kuma yan tagwayensa biyu na qasa ma wasa akeyi da su kuma ana ebe kunyar bayan amarci a tsotse masa su tatas,tako ina Abi da harshe ana lasa kuma hura masa kunne ana zura harshe a hankali ana wasa dashi aciki,dan Allah banda cutar kai a zare kunya" tunawa da wannan ya sanya ta saka harshe ta soma wasa da niples nashi tana lasa tana tsotse su,take ogan ya rikice harga Allah be san da wannan salon ba,bata inda bata zura harshenta tana lasar sa gaba d'aya Abdul yagama rikice wa yama rasa ina ze saka Elham sambatu yake mata tamkar wani zautacce ita kuwa tarasa mesa ta nemi kunyar ta tarasa kuma tamkar yana tunzurata wannan ihun dayake yi,dan kanta ta sakeshi kafin yayi wani yunkuri tuni ta d'areshi ta zura abar da kanta wannan ranar dai da kanta tayi aikin sunnah na neman lada....(saura kuma wata ta biyoni pc tace nayi iskanci,daga abun arziqi)

Koda suka sauka dukkansu se wata uwar kunya ta lullub'e ta,bargo ta saka ta rufe jikinta yana kunna fitilar d'akin ta rufe idonta, d'agota yayi ya d'aura ta akan kirjinsa yace "Blossom na bazan tab'a manta alkhairanki agareni ba yau kin shayar dani dad'i wanda yafi dad'i dad'i,sanar dani a wace makarantar aka koyar dake rikitar da k'walwar mutum" hannayenta ta saka ta rufe fuskarta,hannunshi daya ya saka ya janye hannunta dake kan fuskar

"Blossom kunya kuma,ai baki isa ba,wto a duhu shine kika rufe babin kunyar kikasha dad'inki shine yanzu zaki wani maqale wai kunya" Murmushi tayi "Dan Allah yaa Abdul nika qyaleni"

"Naji zan qyaleki amma sekin yimun irin kiss d'in d'azu hot one d'innan" shagwab'a tashigayi da kanshi ya mata wanka ya gyara wuri har bedsheet ya sauya sannan ya rungume abarsa suka fara bacci".....

*Bayan watanni hudu*

A London Abdul se fama fad'a yakeyi da Elham akan zuwa Niger "Allah ni bazan kuma wannan garinba sena haihu,baka ganin wahalar danake sha kuma fa,har yanzu ba abinda akayiwa Fulani Habeeba watakil ma idan ta ganni da ciki tayi asirin dazayi a zubar kaga nifa bazaniba,kuma ai bance dakai wai ni zanyi missing naka ba idan ka tafi abinka" Murmushi yayi yace "Haba blossom, dan Allah kiyi hakuri, to kinga tunda kin dauka haka barin sanar miki dalilin tafiyar momy ne fa batada lapiya kusan kwanan ta biyar a asibiti" zabura tayi kuma seta saka hawaye "Dama momy batada lapiya shine baka sanar dani ba?" Rarrashinta yashigayi harta haqura sannan washe gari suka dauki hanyar Niger.. Tun daga k'ofar gate d'in gidan jikinshi yayi sanyi ganin dandazon mutane kuma ga alama zaman karb'ar gaisuwar mutuwa akeyi kallon driver yayi yace

"Kai me nake gani haka?? Waye ya rasu?" D'an kallonshi driver d'in yayi yace "yallab'ai dama ba'a sanar maka ba?" Cikeda rud'u yace "Meyene ba'a sanar mini ba?".......

Mom Nu'aiym
[1/8, 10:32 PM] Sha'awa: *🌞HAFSAT ELHAM🌞*

Billy Galadanchi

Haske writer's Asso💡

Vote me on wattpad@68billygaladanchi.
Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).

                           27

Kan wani yayi magana Elham ta saki wani razananniyar qara

"Nashiga uku momyyyyyyy......" Dafeta yayi yace "Haba Elham menene abin ihu Bakima ji waya rasu bafa" ganin bata hayyacinta se kukan take taqi ta kulashi ya sanya ya tallafota jikinshi "Jijjigata yayi yace " Blossom ki nutsu mu Shiga cikin gida tukunna kinji" hannu ya sanya akan lips nashi ya girgizawa driver d'in kai alamar karya fad'a waya rasu d'in,sosai yashiga rud'ani kasancewar besan waye ya rasuba idan ko momy ce lallai da babbar matsala,a haka dai ya d'aura ta akan kafad'arsa suka Shiga ciki,a parlor momy mutane sunyi yawa har bazaka iya ratsasu ka shiga cikiba,juyawa sukayi da nufin zuwa sashen su aikam se ganin Fulani Habeeba sukayi da icce qaton gaske "Wlhy bazan yadda ba yanda ya Turo aka kashemun faruk daga dawowar shi haka shima zan kasheshi Mugu kawai azzalumi" hafsa da Abdul da suka kasa gane inda zancenta ya dosa se suka tsaya sororo suna kallonta,da gudunta ta saka wannan uban sandar ta kwad'a wa Abdul a kai,take ya zube wurin a asume,kallonta Hafsat tayi cikeda rud'u sannan ta mayarda dubanta zuwaga Abdul dake kwance jini na masa zuba a kai,durqusawa tayi tama kasa kukan dayazo mata duk wani tunani nata ya tsaya chack baya yi gabaki d'ayan jinin dake zagaye ajikinta yakai saqonni cikin kwanyarta ya dena yawo,a hankali ta saka hannu ta jijjigashi "Yaa Abdul" ta kira sunanshi a hankali ganin be motsa ba ya sanya ta dafe cikinta atake tasoma ganin jiri,isowar momy kenan da sauri tayi kansu,dafata Elham tayi sannan cikin kuka tace "Yaa Abdul momy wlhy zasu kashe mun shi,kalli fa Haj Habeeba ta kwala masa wannan mugun iccen,na rantse da wanda rayuwa ta take hannunsa idan ta kashemun. Yaa Abdul na sena kasheta nima,sekuma ta qara dafe cikin koda ta kalli kafafunta tafara bleeding over,wani sabon kara ta k'walla take itama ta zube wurin asume,mutane sun riqe Haj Habeeba ana mata Nasiha amma ta kafe lallai seta kashe Abdul,kai tsaye momy sawa tayi aka wuce dasu asibiti tana sharar kwallah tabi bayansu........Allah ya tsare Elham bata samu miscarriage ba Abdul kuwa buguwane kawai,shine ya soma farkawa ganin momy akanshi ya sanya a hankali yace " momy dan Allah sanar dani wai meya ke faruwa ne ??" Kallonshi tayi cikeda ban tausayi tace "Babana wlhy qaddarorine,kaga Faruk ne ya dawo jiya da safe ni bama nida lapiya, wlhy da safe koda hadimansa suka je b'angaren sa ganin ya jima be fito ba Sefa gawarsa suka tarar an dab'a masa wuqa a qahon zuci,shine fa Habeeba ke ihun Kaine ka kasheshi karya gaji sarauta" dafe kanshi dake Sara masa yayi

"Wai ita wannan matar yaushe ne zatayi hankali,bazata barni ma Inji da mutuwar wulakancin gudan jinina ba seta zomun da wani salon iskanci wlhy wannan karon ko me martaba be isa ya hanani hukunta Habeeba ba abinta ya isheni,na shiga uku Farouq yanzu ya zanyi...." Rarrashin sa ta soma yayi seda ya hakura sannan yace "Momy ina Elham ?" Dan shiru kan can tace "Elham zazzabi takeyi tana wancan d'akin am bata gado" zabura yayi ya zare qarin ruwan da aka d'aura masa "Momy ta kani na ganta mana dan Allah ina ne d'akin?" Tana yunkurin hanashi amma ina seda yafita dole ta bishi sukayi d'akin, koda sukazo baccinta takeyi amma yaqi komawa d'akin sa sanda ta farka,a gaban momy ya rungume abarsa suka fara hawaye

"Blossom na menene? Meya sameki haka?" Tama manta da wata momy hannun ta ta saka a saman wuyanshi tana shafawa a hankali "Bayan wannan matarne takeso ta kashemun kai,kagafa wannan qaton sandar ta buga maka,Allah ni idan har ta qara tab'aka sena rama maka muguwa ma da ita" rungume abarsa yayi ita dai momy murmushi kurun takeyi Elham ce takuma cewa

"Yaa Abdul gobe zamu tafi London din ko?"

"Noo princess sekin haihu tukunna" shagwab'a ta soma yi wanda ya sanya ba shiri momy tabar musu d'akin ganinfa dukkansu ba wanda yasan da zumanta acikinsu

"Hubby wai ni waye ga rasu ne? Nagane momy ai d'azu tamaji sauqi" k'ara rungumeta yayi sosai "Habeebty se hakuri faruk ne akazo har cikin masarautar nan aka kasheshi jiya" zabura tayi ta dafe k'irji sosai ta sona kuka dakyar ya rarrasheta tayi shiru,sosai taji wannan mutuwar ta faruk musamman dayake ita dashi basuyi rabuwar dadi ba sam.

A haka dai aka kammala zaman jana'iza yayinda Habeeba ta daurawa Abdul alhakin kisan faruk

Please Login or Register in order to submit comment