Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

07
Uban waye kike zance dashi kullum a waje? A ina kika sanshi? Kuma ya akayi yasan kin zonan?" Rikicewa tayi gashi ya mata rikon da bazata iya daurewa ba,take ta fara zubar da k'wallah,

"Yaa Abdul Kayi hakuri dan Allah wlhy anan muka hadu kuma gaisawa kurun mukeyi" wurgar da ita yayi yace "Anan kika sanshi dakika tafi ina kuka had'u? Wato iskancin naki na kula ba akan faruk kadai ya tsaya ba har wasu kartin banzan ko" kukan tane ya tsananta jin furucin shi, janyo ledar yayi yace yana bud'eta "har agogo ma yake baki da turare,shiya sanya kike mu'amala da turarukan dasuka fi karfin talakan ubanki, kin daukar wa kanki rayuwar datafi karfinki ,dole sekinyi abinda wasu masu kudin sukeyi shine kike bin maza ko,wlhy Wannan kaddararren auren da banka d'ad'd'iya irinki asarane,dabadan nayiwa momy alkawarin aurenki ko bayan rantaba ba ba kaddarar dazata sanya na aureki,kuma ki shirya wa kanki zaman kunci a gidana,banza kwad'a yayyiya Wama ya sani ko asircemun iyaye kukayi keda talakawan iyayenki dabasu san halacciba,banza jaka kalli shigar ki menene marabar da yar tasha haihuwar bakin kasuwa,wane me hankalin ne ze ganki ya zaci cewar ked'innan musulma ce? Wlhy an cuceni had'ani dake Hafsat Allah ya isa tsakanina dake, Sekin d'an d'ana kud'arki a hannuna wlhy" fusata tayi yanzu kam tamik'e tsaye tace tana me k'ank'ance idonta cikeda masifa

"I have had enough now yaa Abdul! Nagaji! Nagaji! Kuma wlhy Nagaji! Duk iyakar abinda zakamun zan d'auka amma wlhy karka kuma sako mun iyayena,ba kinnan nawa dakake gani bashida ragowa,ni ba yar iska bace ba,kuma ban gada ba,jikina be taba haduwa dana wani ba dasunan zina kuma duk wanda kemun kallon mazinaciya na Barshi da Allah ciki kuwa harda kai,kasani wlhy badan ina sanka kodan wani abinka zan aureka ba,sabida darajar momy ne kawai dame martaba,naga alama abin naka nasan ya wuce gona da iri kana zagarmun iyaye to my face,ni ka sani iyayenka har abada iyayena ne, kuma duk wanda ya zagesu agabana se inda karfina ya k'are,sabida nasan darajar manya na,zancen zaman k'unci dakake cewa zanyi a gidanka Ai tunba Yauba na shirya wa hakan,bakada wani farin ciki karan kanka dazaka bani da har zanyi mafarkin zaman farin ciki agidanka,zancen yanayin Shiga I will admit it nayi laifi,kuma ina fatan kasan cewar Allah nawa laifin bakaiba so awurinshi nake neman gafara Ba kaiba,so na gode da tunatarwa,dan Allah karka k'ara zuwa inda nake,karka k'ara kirana awaya,kullum kamun d'aya daga ciki da bakin ciki nake kwana,dashi kuma nake tashi,ba abinda yafi mun ciwo irin wai ace mijin dazaka aura shine yake zargin ka....." Kasa karasa wa tayi ta durkushe awurin tana kuka me ban tausayi, Shikuwa jikinsane yayi sanyi,seyake ga koda hakane mazina ciyar ce cin zarafin yayi yawa,beside wane tsautsayinne yakaishi zagin iyayenta,shida kanshi yasani Baba hasan dattijo ne me kirkin gaske,sam bashida hayaniya shekaru kusan talatin yake gagi agidan,tun yana dan shekara 5 aka kawoshi gadi gidan kuma amana ta sanya haryau ba'a sauya wani ba,take yaji ya tsani kanshi kuma se wata zuciyar ke bashi watakil ma ba wani abin Elham keyi itada faruk ko wanin shiba,gwiwa asace ya juya ya bar d'akin gaba daga kansa ya kunce,basu feenah suka dawo ba se shad'a yan dare,zuwa lokacin zazzb'i me zafi yagama rufeta,kanta ba kad'an ba yake Sara mata,zuci yarta zafi takeyi sosai duk sanda ta tuna da maganganun Moris setaji tamkar kasa ta bud'e tashige sabida tsanar kanta da tayi,sosai wutar qiyayyar moris ta k'ara huruwa a birnin zuci yarta, ji take tamkar ta kurma ihu sabida tsananin zafin da kalamnshi ke mata a rai,kwanciyar sukayi batare da sun san meke damun taba,cikin dare Wuraren karfe hudu ta farka da wani razannanen ciwon kai,ga rawar sanyi tanayi jikinta yayi zafi rau tamkar gaushin wuta,dakyar tamatsa kusa da feenah ta d'an bubbuga bayanta,tsaki feenah taja tace dan La Elly rabu dani,bacci nakeji" haka tayita tashinsu basu tashiba,da asubar fari ta mike domin yin Sallah tana matukar ganin jiri,kasawa tayi taje ta kwata,Raihan ce ta tashi ta kunna fitilar d'akin ta dawo ta tashesu itama tashiga ban d'akin tai alwala,tana fitowa taga basu tashiba,ta kara tashin Elham aikam tana mikewa ta sulale wurin ta fad'i,da sauri Raihan ta tareta,jitayi jikinta zafi sosai ,tace "subhanallah Elham dama bakida lapia har haka baki sanar wa kowa ba?" Kasa ansata tayi,dakyar tace "Raihan ku kaini wurin Innah mutuwa zanyi kaina ze rabe gida biyu" feenah ma tasowa tayi tazo ta na tattab'a jikinta rikicewa sukayi ganinta galala,da sauri feenah ta janyo wayarta takira Abdul,yana d'agawa tace " yaa Yarima mun Shiga uku Elham zata mutu wlhy bata da lapia sosai, bata ma iya tashi faa" beyi magana ba ya kashe wayar dama yana d'akin kusa dasu daya kama jiya,aikam da gudun shi ya nufo dakin yayi knocking Raihan ta bud'e masa, yana zuwa ya dauketa ya dora kan gadon,sosai ya rikice jin jikinta tamkar wuta,yace da sauri feenah ta kira masa Ashraf Raihan kuma ta dakko masa ruwa me sanyi da towel,take yafara bata tapinsponge se rirrik'e sa takeyi abinda ya kula ma sambatu takeyi,Ashraf na zuzuwa da kanshi ya kwashe ta zuwa mota suka kaita wata alfijir hospital,likitan yace damuwa ce tamata yawa,jininta ke kokarin hawa amma dai be Hau d'inba,se an bata injection da k'arin ruwa,Abdul ya tsorata dajin Wannan zancen,kaddai maganganun shi na jiya neke daga mata hankali har haka!!! Koda akazo amata allura kasa Tsayawa tayi seda Abdul ya riketa, drip na karewa ta samu karfin jikinta aka sallamesu,Abdul da kanshi yake jinyar ta,Shifa arayuwa yanzu bala'in tausayin Elham yakeji ga masifar kunyar ta dayake ji,ita kuwa duk ta bud'i idonta ta ganshi tsanar sace ke kara ruruwa a cikin zuciyarta.
*Bayan kwana d'aya*

Yana zaune kusa da ita yana bata ayaba dakyar takeci amma ko kallonahi Bata sanyi yakuma kula da hakan,kallonta yayi cikin sanyin jiki yace "Elham dan Allah kiyi hakuri akan abinda na fada miki 2 back wlhy bacin Raine,abinda na fada bawai har raina bane" banza tamishi ta k'ara dauke kanta,yace "Dan Allah Hafsat kice dani kin hakura mana,nasani kalamai na ne suka jefaki a Wannan halin dakike ciki,dan Allah kiyi hakuri kinji" kuka tasaka masa,Shikuwa ayan kwana kinnan tausayin ta yakeji yarasa dalili wlhy gashi kuma bata bashi fuska,cikin rudu yace "kinga Idan zancen ne bakyaso kiyi hakuri na dena wlhy kinji Hafsat" kukan tane ya tsanan ta,harga Allah bata koda sanjin muryar Abdul wlhy ta tsaneshi.....

Tir qashi ga alamafa Abdul ma ya jajibowa kanshi qiyayyar Elham matuqa,gashi shi kuwa yafara yin laushi,muje zuwa dai kuna tare da alk'amin mom Nu'aiym....
[1/8, 10:32 PM] Sha'awa: *🌞HAFSAT ELHAM🌞*

Billy Galadanchi

Haske writer's Asso💡

Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).

     *Mrs j moon mamar love,this page is for u and u alone,start dancing shoki,koda bansan wane team kike ba,nidai team Abdul moris sak*

                          08

Zuwa yayi ya durk'usa daidai inda take zaune ya kamo hannunta ya rike,ta kwace hannun ta ta dauke kanta sannan ta rufe idanuwanta rufe,dafe kanshi yayi yana mejin zafin abinda ya aikata agareta,Shifa bawai yana Santa baneba,kurun dai tausayi take bashi kuma ya sani be kyauta mata ba sam iyaye ba abin wasa bane,matsawa yayi kusa da ita ya zauna yace cikin sigar rarrashi

"Elham mana ki sassauta Wannan fushin dakike dan Allah,Idan muka koma gida kina haka momy zatayi zaton wani abin,ki sassauta wa kanki kinji,kumafa doctor yace damuwa ke damunki" cikin kuka tace

"Yaa Abdul Idan ka fice mun daga rayuwa wlhy zan daina kuka,Idan kadena zuwa wurina,kadena kirana,ka dena damuwa da tawa damuwar,ka manta dani arayuwar ka wlhy zanji sauqi,dan Allah yaa Abdul ka taimakeni kace dasu me martaba bazaka aureni ba,wlhy banasan auren nan dakai,gwaramun na mutu ba aure dana auri wanda besan darajar iyayena ba yake mun kallon fasik'a yake wa iyayena dani kallon matsafa kuma masu kwad'ayi wlhy Yaya Abdul Idan aka daura mun aure dakai mutuwa zanyi,bazan tab'a manta muggan kalaman ka agareniba,Karfa ka manta har cewa Kayi wlhy ka tsaneni,dan Allah yaa Abdul.....kukane ya k'wace mata sosai,Abdul ya rasa ina ze tsoma ransa,tunda yake arayuwar sa be tab'ajin kunyar dayaji ba a yanzu,se yanzu yake gano d'imbin kuskuren daya tafka na kallon Tsakiyar idonta ya gaggasa mata maganganun marasa dad'i, musammamn tafuskar zagin iyayenta dakuma tsanar ta daya furta mata kanshi tsaye,menene ma ya aikeshi cewa ya tsaneta? Ko makiyinka na gaskia bazaka cewa haka agabanshiba,kallonta yayi idonshi har ya kad'a yayi jajir ita d'inma ta tsagaita kukanta shi take kallo, take ya hango tsanarsa k'arara acikin idonta,tashi yayi yabar d'akin  batare dayace kanzil ba,har wani duhu yake gani,yana zuwa d'akinshi ya kwanta se hawaye,gaba d'aya rayuwarsa ta masa k'unci shidai harga Allah bayasan Hafsat amma ya kasa gane tsakanin tausayinta da kuma kunyar ta Wanne yafi sakashi a k'unci a ce da girmansa da komai ya aikata abinda ko d'an shekaru baze aikata ba,wayarshi ya janyo ya dannawa Zayyan kira,suka gaisa sannan be b'oye masa komaiba ya masa bayani ya kara da cewar

"A k'alla ni a ganina be dace na sako iyayen ta ba akoma menene,wlhy zayyan kunya nakeji,kuma na kula Yarinyar ta tsaneni matuka kofa kallona bata iyayi,zayyan koda bana san Yarinyar nan aure fa zamuyi? Kuma fa kaga banida tsarin mata biyu,bayaga haka ba saki tsakanina da Elham haka zamu yita zama?" Nisawa zayyan yayi yace

"Moris Kaine kana da matsala wasu lokutan,nasha fad'a maka cewar yanda kake yi ba'a haka,nafasan Elham ba tun yauba,zan yadda da zancenka na iyayinta da kad'ifirin tsiya amma sam ni bana kawowa raina wai tana wanna abin,yanzu dai ka ajiye zancen Wannan k'iyayyar gefe ka rik'a rarrashinta kana bata hakuri,ninake gaya maka a hankali zaka koyi santa Ba kad'an ba" shimad'in nisawa yayi yace

"Zanyi yanda kace,amma kam zancen soyayya tsakanina da Elham har abada,Bance ma kuma tana zinaba amma dai idona ya ganemin suna wasanni mara kyau da faruk wanda har abada bazan manta Wannan ba,kazalika baze barni na iya had'a makwancina da nata ba,kasancewar ina kyamar ta wlhy" tsaki zayyan yayi yace

"Kanka akeji dai moris mace daice,wlhy tsaf zata rikita maka lissafi,a yanda na lura ma ta fara gigita mun kai" tsakin shima yayi yace "D'an rainin hankali kanka dai akeji wlhy" daga nan sukayi sallama ya koma ya kwata yana nazarin kalaman zayyan.....da yamma su feenah suka fita suda su Ashraf shi kuwa yazo d'akin wurinta,a zaune ya taddata saman sallaya tana adu'a ta idar da sallah,zama akan gadon yana jiranta,tana idarwa ta Kawar da kanta gefe d'aya tace "yaa Abdul ina wuni" da k'yar, d'an Murmushi yamata yace "Lapia lau Elly ya jikinki?"
"Da sauqi" ta ansashi a tak'aice,nuna mata kusa dashi yayi yace "zoki zauna anan Hafsat" bata Musa masa ba taje ta zauna,ya ja hannunta ya riqe yace yana Murmushi
"Nifa banga kina shirin Wannan bikin ba fa,duk gayunnan naki bazaki hada mana wani abinba" bataso ta bada shi ta kula hirar yakeso kuma duk dan ha Kawar mata da damuwa ne,Murmushi tayi tace
"Yaa Abdul nifa banasan wani bidi'an yanzunnan zakaga ance nacika iyayi,walima kurun zanyi" hannunta dake rike da nashi ya matse sanda tayi k'ara kadan yayi dariya yace "kin Cika raki d'an wannan abin kikewa ihu haka,Nakuma sani bakyaso k'awayenki Su ganni fine fine bobo Su mak'alemun shiya sanya bakyason bikin" tafa kula so yakeyi ya mantar da ita abinda ya faru,bashida labarin cewa har abada bazata dena jin zafinsa da kiyayyar sa ba,kallonshi tayi tace " Ea mana Kaima kasan ai koda auren akayi Idan Nayi bak'i a d'aki zaka zauna" yaji dad'in yanda tad'an sake masa,hannu yakai daidai wuyan ta yatab'a yace yana kallonta ita d'inma shi take kallo
"Har yanzu da sauran zafi jikinki Hafsat,dan Allah ki rage damuwa kinji" Murmushi tamasa itafa harga Allah yanacin albarkacin momy ne tace "Naji sauqi fa,kurun dai kwad'ayi nakeji wlhy" murmushin sa ya fad'a d'a yace "me kikeso Kici to?" Langwabe kai tayi tace "popcorn da ice cream" hancinta yaja cikin wasa yace "kwad'ayin kenan oya dress well mu tafi" mikewa tayi ta zare hijabin jikinta ta yane kanta da yalolon mayafi,kallonta yayi dress dake jikinta ya d'ameta da yawa ga heeps sun bala'in fito,wani iri yaji ajikinshi yace murya k'asa k'asa "Hafsat plss mana,yanzu Idan na barki seki fita a haka dan Allah? kowa fa ze gama kalleki" d'an Murmushi tayi tace a shagwabe "Yaa Abdul meye aciki dan Allah nafa saka mayafi" komawa yayi ya zauna yace " ki saka hijab kokuma mu fasa fita gaba d'aya " komawa tayi ta d'auki hijab d'inta ta saka tace "to muje na saka"
"Yauwa ko Kefa? Kinma fi kyau ahaka Allah kuwa" a haka sukaje suka dawo tun a hanya ta shanye roba biyu na ice cream se kallonta yakeyi ko ajikinta,anan fa ta fara fyace hanci lokaci d'aya mura ya taso mata amma bata dena shaba,suna Shiga d'akin suka tarar dukkansu sun dawo har mazan suna kallo, har lokacin ice cream d'inta takesha,wara ido feenah tayi tace " na Shiga uku,yaa Abdul hope dai Elly batasha ice cream d'innan da yawaba momy fa ta hana,ranar damu kazo ma naga kinsha namiki shiru ne sabida d'ayane kurun" kallonta yayi yace

"Bata shan ice cream sabida me to?" Kallon shi taku mayi tace "she's Asthmatic fa,kuma ire iren wayannan qanqarar sam basa bata lapia agida ma ko ruwa me sanyi ba'a bari tanasha" mayar da dubanshi yayi zuwa gareta yace "Hafsat hakane? Wannan fa rofa na ukune kinada hankali kuwa?" Turo baki tayi tana me fyace majina da tissue dake hannunta "kurun ni se'a riqa takurani,koma waye yana jin dadi bandani" nan take ya murtuke fuska dama Abdul akwai saurin Fushi

"Danla can rufawa mutane baki,ke d'innan yar rainin wayau ce wlhy kinsan bakida lapia kike shan abinda ze cutar dake tsabar rashin sanin ciwon kai,maza bani ice cream d'in yanzu" tana shagwaba hadda doka kafa a kasa da k'un k'uni tabar wurin "Allah ni anbi duk an takura ni ice cream dinne bazan shaba kuma bayan kowa ma abinda yake so yake sha" galala ya saki baki yana kallonta harta bacewa ganinsa,kurun seyaji ta bala'in bashi Sha'awa,Binta baya yayi,ya zauna kusa da ita yace "Elham ni kuma kikewa k'un k'uni? Lapiyar ki fa nake dubawa" d'an rausayar da kanta harda kwallah "To Kayi hakuri bazan k'araba,amma plss ka bani na karasa shanye wa" Murmushi yayi yace "Zan dai hakura amma bazan baki ba gaskiya" kan wani cikinsu yayi magana har wayan ta ya soma ringing, Murmushi tayi ganin yaa Ibrahim a rubuce, da sauri ta daga wayar ta kwanta tana duban roof na d'akin a shagwabe tace "Lallai ma yaa Ibrahim,Wato se yau kake tunani,Allah ni Nayi Fushi bazan ma maka magana ba" wani d'aci ne ya tunkaro k'irjin Abdul tun daga kan dan yatsan sa har zuwa zuciyar sa da kwanyar sa,yana tsakiya da tunani yaji tana cewa "Ea mana Nayi bala'in missing hirar ka tun juya fa,Banyi dariya ba" da sauri ya mike yabar d'akin zuciyarsa she zafi take,wanda be san dalilin hakanba.
[1/8, 10:32 PM] Sha'awa: *🌞HAFSAT ELHAM🌞*

Billy Galadanchi

Haske writer's Asso💡

Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).

*kandy  kishiyar Mrs j moon,Wannan nakine Mrs j moon k'awata ta roka abaki,wai kina kuka an bata kyautar page ke ba'a bakiba so chill Wannan nakine ki mata godiya lolxx*
      
                            9
Koda ta kammala wayanta ta juyo ya tafi,kwanciyar ta tayi bata kawo komai aranta ba,harga Allah ita be wani dameta ba,shi kuwa moris kasa koda kwanciyar yayi aranshi yana tunanin wanene Ibrahim? Hankalin shi ya tashi matuka,ya kasa gane mesa ya damu haka,wani barin na zuciyar sa yace dashi,kishi kishi ke damunka Abdul,yayin da d'ayan sashen na zuciyar sa yace dashi,kurun sabida zaka aureta ne bakajin dadin ganin tana huld'a da wasu mazan, "that's all" ya fad'a a sarari "Mema ze saka Nayi kishinta tunda ba santa nakeyi ba nikam" wanka yashiga ya fito ya saka jallabiya ya kwanta amma ya kasa bacci har karfe biyu na daren ranar idon sa biyu....cikin bacci Elham tasoma jin bata iya numfashi da kyau,dama kuma da mura sosai ta kwanta har tari takeyi,feenah ta tayar tace da ita "Feenah I'm sick,I cnt breath well,could u plss help me with my inhaler?" Mik'ewa tayi da sauri ta kunna side lamp d'in d'akin tace "Where d u keep it then,seda nace karki sha Wannan kayan sanyi amma bakyaji" kasa ansata tayi sabida abin ya taso mata sosai,ko ina feenah ta duba bata ga inhaler d'in ba,wayar ta,ta janyo takira Ashraf yana d'agawa tace dashi "Kazo yanzu plss Athsma d'in Hafsat ya tashi kuma gashi na duba ba inhaler d'inta" tashin baba karami yayi yace "Plss ka tashi muje gunsu feenah Waifa er matsalar nan Elham Athma d'inta ya tashi,shine zamuje muga halin datake ciki,zuwa sukayi suka yi cirko cirko akanta,se neman inhaler akeyi ita kuma tana fama da kanta, Ashraf ne yace " kaga K'arami kira yaa Abdul....." Yana zaune yana salati ya idarda da nafila kasance wa ya kasa bacci sabida tunanin Wannan Ibrahim da Elham ke waya dashi,yaji phone nashi na ringing,harta katse be tashi ba,harga Allah be kawo komai aranshi ba haka call d'in ya k'ara shigo yayi banza dashi,a tunaninshi wani balarabe ne dasuke huld'a dashi kasan cewar Su yanzu gari ya dade da wayewa,ganin fa Elham na shirin shrqewa ya sanya Baba karami ya soma danna mata k'irji,feenah ce tace "kunga dan Allah Kuzo mu kaita asibiti, Wannan athsma d'infa Idan ta tashi mata dole se anmata allura,da d'azu ne ma akaga inhaler ze sauka amma yanzu yayi nisa aminipilin injection kurun za'a mata ya sauka" Raihan ce tace "Hakane amma Inaga mu fara sanarwa Yaa Abdul koda ta zuwa d'akin sane tunda yana kusa" Ashraf ne yaje ya masa knocking,da mamakin sa ya bud'e ya k'urawa Ashraf ido,a rud'e Ashraf yace

"Zata mutu wlhy yaya mutuwa zatayi" kallon shi yayi da mamaki dauke a fuskar "kai ka nutsu mana wacece Zata mutu?"
"Yaa Elham ce fa Athma ya tasarwa,munyi kiran wayarka baka..." Ai bankeshi kurun Abdul yayi be tsaya ya karasa jin zancen ba,da gudu ya Shiga d'akin ganin k'arami na dannan mata k'irji ya sanya yaji wani bakin ciki ya taso masa,hawa kan gadon yayi ya dagota saman cinyar sa,gani yayi sam bata numfashi bata ma motsi rikicewa yayi lokaci daya ya kwasheta suka rufa masa baya seda ya sakata a mota sannan ya tuna da key,dagudu yaje d'akin ya had'o da wayanshi da ku d'ad'e,asibitin dasuka kaita ranar ya nufa,da sauri suka karb'eta aka danna mata ox da komai da injections,Abdul se zirga zirga yakeyi dawowa wurin Su Ashraf lokacin sun dawo sallar asuba yace "Waiku kuwa wane iskancinne ya hanaku kirana tun d'azu Idan da wani abin ya samu Yarinyar mutane me zakuce?"

"Yaa munfa kiraka baka d'aga ba,ka duba wayarka" kan wani yayi magana doctor d'in yace "Patient naku ta farfad'o,dama kunsan case na athsma yana sauka da Wannan injection da sauri,sedai ku kiyaye abubuwan dake saurin tayar mata da asthma" da sauri yaje d'akin, yana zuwa yaje wurinta ya riko mata hannu "Sannu Hafsat ya jikin?" Murmushi tamasa tace yaa Abdul zansha ruwa dan Allah" da sauri ya bude robar ruwan dake gefenta ya daga ta,asaman jikinshi ya kara ta ya bata tasha,gani yaye ta lafe ajikinshi ya sanya be d'aga taba yace cikin sanyin murya

"Elly bansan meyasa ba Idan bakida lapiya hankalina gaba d'aya yakan tashi,dan Allah na rokeki ki guje wa duk wani abinda ze kawo miki rashin lapia musamman irin Wannan,nafa Zata mutuwa zakiyi ki barni hankalina ba k'aramin tashi yayiba plss ki dena shan sanyinnan" mamakin kala manshi ne ya sanya ta d'ago ta kalleshi k'wallan datake kokarin tarewa ya sulalo,hannu ya saka ya share mata k'walar ya mayar mata da kanta saman k'irjin sa yana patting bayanta a hankali "Noo plss Elham banasan kina yawan kukannan Alhamdulillah kinji sauqi,koda inda yake miki ciwo ne?" Gyad'a masa kanta tayi alamar e,da sauri yace "sanar mun inane gayamun kinji,ina yake miki ciwo" janye jikinta tayi daga nata,ta kwanta tace "k'irji nane yakemun zafi,kuma se ina jin ribs nawa tamkar iska me sanyi tana Shiga cikin ribs d'in" kurawa dan tsukakken bakin ta ido yayi yanda take magana tana yamutsa fuska dukya gama burgeshi yace "zan sanar wa doctor yanzu I just cnt leave u in pain" Murmushi ta masa tace "Thank you" b'ata fuska yayi da wasa "Sabida na kula da Lapiyar matana kike wani cemun thank you bana so" Murmushi kurun tayi batayi magana ba.

A daddafe suka karasa kwanakin biyu da suka rage musu suka dawo gida da yola,daga kaga Hafsat kasan batada lapia ta d'an rame,ba laipi Abdul yana kula da ita sosai,suna dawowa da kwana biyu ya wuce London......

Abdurrahman Allah yayishi da ilimin Zane tun yana karami,kuma Allah ya daukakashi har girmanshi Zane ba irin wanda bayayi,a London kampanonin dake k'era motoci yake zanawa mota,yayinda har kampanonin builder's yake zanawa gida,a yanzu haka yanada kampanin sa na kansa Abdul builder's dake birnin London,ba k'ananun kud'ad'e yake samu a harkar ba,ya kasance yaro ne d'an k'walisa meji da kansa ga tsananin k'yank'yamin masifa komai nashi CA's dashi.......

Satinsa uku ga dawo,a parlorn sa yake yana kallo tayi sallama ta shigo kasancewar ya sanarwa feenah Idan tazo part din momy ta Turo masa ita phone nata a kashe yake,har qasa ta durk'usa ta gaidashi,da Murmushi d'auke a fuskarsa ya ce "Zonan ki zauna kusa dani Elham" batayi musuba taje a kujerar da yake ta zauna ya kalleta sosai ya janyo hannunta na dama ya rike yace

"Elham mesa kika mun haka?" D'auke kanta tayi zuwa d'ayan side d'in tace cikin wata murya me sanyi
"Yaa Abdul me na maka" karkatowa yayi gefenta ya daura kafafuwan sa gaba d'aya saman gadon yace "Yanzu ke baki masan me kika munba? sati na uku bana k'asar seki kama wayarki ki kashe gaba d'aya,abin takaicin ma nacewa feenah ta baki waya wai kin tafi gidan k'anwar mamanki,dagaske kin kyauta kenan Elham?" Sosai ta juyo ta k'ura masa ido,tana mamakin yanda yake rero kalamai tamkar da gaske,mutumin dayace ya tsaneta ina ruwansa da damuwa da inda taje" iska ya hura mata a ido,ta gyara zaman ta,sannan ta kalleshi ta k'ara ya mutsa fuskarta tace "kaga nifa sauqi namaka,ina dama ko tafiyar damukayi akan momy kake kulawa dani,yanzu baka gari menene ze dameka danna kashe Wayata beside ni a ganina wanda ka tsaneshi ai sauqin kane idan ya janye jikinshi daga naka" Hannunshi d'aya ya saka ya dafe kanshi yace "yaa salaam,Haba Hafsat wayene yace dake na tsaneki?" Murmushin yak'e ta masa tace "Yaa Abdul kenan,kasani matsalar furuci kenan ka furta akan idona kuma idanuwa na suna kallon naka sanda ka furta hakan na hango tsanar tawa k'arara a idonka da zuciyarka gaba d'aya" hannunta dake riqe a nashi ya matse sanda ta kwallah k'ara yace "Haba mana Hafsat,dan Allah ki dena furta irin wayannan kalaman kinji" kallonshi tayi tace "Ka gani ko yanzu fa ka kasa furta cewar ba k'iyayya ta aranka,kurun kace na dena zancen,naji Kayi hakuri bazan k'araba" juna suka k'urawa ido na yan dak'iku yayinda Abdul ya kasa gane ainahin meyakeji game da Wannan baiwar Allah ita kuwa tsanarsa fall a ranta sunan sa ma bata san ana anbata,shine ya Kawar da shirun dacewa

"An sanar dani kince ke kurun a daura aure bakyasan wani bikin mesa ?" Kallonshi tayi dama taci d'amarar gaggasa masa magana tace "Ba bikin bane banaso auren nakane yake batamun rai wlhy banaso yaa Abdul,zargi na fa kake kuma kace ka tsaneni Wannan wane irin zama zamuyi,yaa Abdul bansan wazan sanarwa ba amma wlhy gabana fad'uwa yakeyi,tsoro nakeji" matsawa yayi kusa da ita ganin tana kuka,ya tallafo ta jikinshi,ita kanta mamaki takeyi yanda bata iya tureshi idan yazo jikinta. yace cikin rad'a "ki dena jin tsoro Elham,kuma gaban ki ya dena fad'uwa I promise to always be by ur side,dan Allah karki badani kowa fa jiran ranar aurena yakeyi,ki saki

Please Login or Register in order to submit comment