Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tajiba mamanta zatayi auren Hutu dajin dad'i ,tace "Karka damu umarul faruk zanje da kaina gunta na mata magana da yardar Allah zata a mince,kaga dama na yayanka da Raihan muna jirane nan da watanni shida Su kammala skul inyaso se a hada gaba daya" godiya yayi yatashi yabar wurin cikeda murna,washe gari kuwan momy ta shirya zuwa bangaren Umma,gaisawa sukayi cikeda girmama juna tamkar ba komai a kasan rayukansu game da juna sannan ,gyaran zama Fulani tayi tace

"Fulani Babba dama nazone in roki Alfarma awurinki akan zancen faruk da Mamana,dan Allah ki janye furu cinki ki barsu suyi auren Su,tunda addini da al'ada duk basu hana ba" wani mugun kallo ta wurga mata sannan tace

"Kinga Fulani wlhy ko ubanwa zaki gayawa bazan sauya Wannan maganar ba,ke gani kike kamar bansan tuggun dakike kullawa ba? Kome nawa Kinbi kin kwace mun yatashi daga nawa ya dawo naki,bayan kin hade kai da mijinki kun kashe nawa mijin sabida ya Hau sarauta,yanzu kinzo kinaso ku daura Abdurrahman har dan munafurci wasu na kiranshi Yarima ,shine zaki zo sabida ki kara batawa faruk suna zaki hada shi da wata shegiyar talaka wai ya aura,a zatonki bansan me nake ba kokuma banida hankaline,duk muna funcinku ina kalonshi wlhy, kuma da yardar Allah bazakuci nasaraba faruk shine ze gaji sarautar ubansa,ko Raihan sabida banaso tashiga damuwa ne kasancewar ta mace kurun ya sanya na yarje mata auren Abdul" kura mata ido kurun momy tayi sanda ta kai aya sannan tace

"Kinga Yaya habiba ba zwa nayi Kici mun mutunci ba,zancen kashe margayi me martaba dakike kuma kije mun barki da hukuncin Allah,zancen kuma sarauta dakike keta Shafa ni kina sane yarona bata shafeshi ba,Idan kuma har Allah ya zabeshi keda iyayi nki baku isa ku hana ba,auren Raihan da Abdul dakike magana ita Elham malama ba 'ya bace daki kece Raihan macece ai itama macence bakya duba damuwar dazata Shiga? Tsabar sonkai musulunci da kanshi yamana nuni a sassa daban daban,kuma hadisin ya inganta cewa imanin dayanku baya taba Cika Harse Idan ya sowa dan uwansa abinda yake sowa kansa,kekuwa taki yar kawai kika sani,wlhy kiji tsoron Allah" mikewa tayi a fusace

"Kinga Nana barmun sashen na,borin kunya kikeyi Allah ya Toni asirin ku da wuri Wannan karon,wlhy inhar muddin ina numfashi bazaki taba cin nasaraba,nakara fada ko bayan raina faruk ya auri Elham dashi wayanda suka daure masa gindi Allah ya isa ban yafe ba,Idan gaskiyane ba mugunta kike shirin masaba ki baiwa Abdul Elham d'in ya aura mana" mikewa itama tayi

"Naji Yaya habiba Abu daya nakeso ki rubuta ki ajiye wlhy Nima ko bayan raina ban yarjewa Abdul auren Raihan ba,dukkanin Su suyi asarar ababen kaunar Su,zan kuma tabbatar miki cewar ba mugun nufi araina domin kuwa aure ne Elham da Abdul anyishi an gama,ke kuwa Idan kin isa ki hada auren faruk da Raihan kema din kiyi auren huce haushi" zage juna sukayi tatas wanda da faruk da Raihan duk suna jiyosu, aikam hankalin dukkaninsu ya tashi,bayan Fulani ta wuce suka yita baiwa ummansu hakuri amma bata hakura ba....

"Koda momy takira Abdul dake birnin London tafada masa kasa yi mata musu yayi kasancewar sa me tsananin biyayya....gashi kuma bashida wacce ya tsana arayuwa sama da Elham" kuka sosai ya saka shikadai tamkar wani karamin yaro a ranshi yace "Ina zankai Wannan kazamar? Ina zan iya da yarinyar da faruk ya gama lalatawa gaba daya,kai wlhy gobe dolene nakira momy na bata hakuri,idan ta rabani da Raihan mutuwa zanyi".....


Kasancewar yau weekends yasanya Elham ke kitchen tana girki asaman risho,taba tsakiya da aikin tajuyo sallamr su Raihan itada uwarta,mahaifiyarta inna ma fitowa tayi dauke da mamaki a fuskarta tana musu Barka da zuwa , sheqeqe Umma ta kallesu tace

" ke Asabe gunki nazo,wato sabida kinaso yarki dole setayi kud'i shine kiketa faman qaqa bawa faruk itako,kuma kunga bakuci nasaraba bazan taba bari me jiran gado ya auri yar matsi yataba shine kuka zago kuka koma gun Abdul mijin da kowa yasani Raihan dina ze aura,kuka asirce uwarsa tace yanzu Elham ze aura? To ban hana kuba amma wlhy ku kuka da kanku da abinda zan muku Idan kuka wa y'ata kwacen miji,faruk kuma baze taba auren yar masu Kwana a kofar gida bba".....ba karamin ,baci ran innah yayi ba da Wannan cin kashin bayan sun wuce tayita yowa Elham fada akan shishigin ta da samarin,amma ba ruwanta da zancen aurenta da Abdul domin kuwa uwarshibce ta nemi alfarma, ita kanma bataji Wannan labarin ba se yanzu,ga shi Innah tace ko wayar faruk ta kuma dagawa Allah ya isa,wunin ranar a daki tayishi tana kuka,bazata taba musawa momy ba kodan halaccinta agareta,kazalika bazata taba kaunar Abdul ba kamar yanda bazata taba iya dena san faruk ba.

Mom Nu'aiym
[1/8, 10:32 PM] Sha'awa: *🌞HAFSAT ELHAM🌞*

Billy Galadanchi

Haske writer's Asso💡

Sadaukar wa ga k'awara Hafsat Abubakar qaya (Elham).

                           03

Washe momy na tsakiya da breakfast Abdul ya kirata,k'aidane Awurinta idan tana cin abinci bata magana,Wannan yasanya sam bata d'aga ba,se bayan data kammala sannan tayi kiransa back....gaisawa sukayi cikeda girmama wa,sannan cikin sanyin murya yace

"Momy dama akan zancen Elham ne damukayi jiya,dan Allah momy ki yi hakuri,wlhy narigada na gama tsara rayuwata zanyine tane da Raihan,Idan akaimun haka ba'a mun adalciba" gyrana zaman ta tayi ta daura kafarta daya kan d'aya sannan tace

"Babana Ashe kam kacika me hikima,kuma zuwanka a kasar turawa yayi matukar tasiri akanka,Ashe dai mutum da kanshi shine yake tsarawa kanshi rayuwar dayake so yakuma ga ta dace dashi banida Wannan karatun kuma agidan mu ba'a koyar dani irin shiba,wanda na sani shine Allah wanda ya halicci komai da kowa shine yake karawa bayinsa rayuwar data dace dasu ba wai Su bane suke tsarawa kansu,amma nagode daka sanar dani yanzu....zancen Mamana kuma Idan baka manta ba aiba tilastaka nayi ba,rokarka kurun nayi nace ka fitar dani kunya dacin zarafin da akamun,amma tunda tsarin rayuwar ka a hannunka yake,nagode maka kaje ka ci gaba da tsarin yanda kaso....abu na gaba kuma kaje na janye maka auren Elham sedai fa ko bayan raina ban yarje maka auren Raihan ba,seka shirya tsara wata rayuwar da wata ba itaba me tsari" kit ta kashe wayar gaba d'aya,jikinshi ne ya mace koda yakuma kiranta ta kashe wayarta.....Faruk duk ya gama kad'uwa shida Raihan yayinda Fulani Babba ta dauki k'iyayya me tsanani ta d'aura wa Elham da iyayenta,bata tsammanin zata iya bari faruk ya tab'a auren Elham,kazalika bazata taba iya barin rayuwar Raihan ya tagayyara ba beside koda faruk ze rasa sarauta ai Idan Raihan ta auri Abdul sarauta tamkar a hannunsu take,zasu Shiga malamai su mallakeshi kuma jikokinta su gaji sarautar daga baya,shirya wa tayi taje fadar me martaba....

    Durkusa wa tayi har kasa ta kwashi gaisuwa,me matarba ya bukaci a basu wuri,bayan kowa ya fashe tayi gyaran zaman tamatelarta tace "Ranka ya dade me martaba dama nazone akan wata muhimmiyar magana,dangane da,zancen auren Abdul da Raihan, Haj Nana ce tace wai bazata tab'a bari Yaronta ya auri Raihan sabida wani dalili nata da ban sanshi ba,nikuwa a ganina da Abdul da Raihan duk abu d'aya ne abin beyi zafi har haka ba" jin tayi shiru ya sanya yafara magana
Da daddaya tamkar baya sanyi

"Habiba dukkanin abinda kika zomin dashi yanzu ina sane dashi,ki sani shi Allah ba'a masa wayo,ko kad'an abinda kikayi be kyau tuba,ai kodan darajar mahaifiyata kya duba ki bar faruk ya auri Elham,nine me yanke wa yarana hukunci akan wayanda zasu aura amma fa ki sani wlhy muddin kika hana faruk ya auri Mamana bazan bari Abdul ya auri Raihan ba,sabida Elham tafita bukatar taimako,kisani wanna umarnine na mahaifiyata akan inganta rayuwar Elham ko bayan Ranta,nasani cewar Idan na kuskura na had'a su kishi bazaki tab'a bari Elham ta zauna lapiya ba Wannan dalilin yasanya na ce shi Abdul ko yana so ko baya so ya auri Elham,Raihan kuma Baba karami na zab'a mata,Idan baki manta ba tun farkon dashi suka shirya Kansu kece kika hana kike turawa Abdul,nasani tunaninki Abdul shine ze gaji sarauta Shiyasa kikeso ki Aura wa Raihan shi toki sani ba sankai alamurana kazalika Abdul baya san sarauta sabida haka bazaki b'ata mana zumuncinmu ba sam,ko Nana,na sanar mata tuni bawai dan yanzu zancen faruk ya taso ba,na dade da sanar mata bazan bari akan Raihan zumuncin Baba karami da Abdul ya lalace ba labari yazo min cewar basa koda gaisawa kuma Abdul bashida gaskia tun farko yasani sun daidaita kansu,abin haushin ma har mu iyaye mun Shiga ciki daga zuwan shi ya b'ata komai kekuma habiba kika zuge yarki akan kwadayin mulkin da dukkaninmu a duniya zamu mutu mu barshi,ki sani wlhy Wannan karon bazan saurara miki ba,karna kuma jin zancen Abdul da Raihan,kuma lallai ne ta auri Baba karami,kusan shekaru 4 tana bashi wahala baku isaba" jin yayi shiru ya sanya tayi godiya kurun ta wuce abinta, rayuwarta ta baci,tsakani da Allah bataji dadin Wannan abin ba,dama kuma Raihan ba itace take san Abdul ba kwad'ai ta mata san duniya uwar tayi....jiki a sanyaye tashige part d'inta abin haushi kuma seta taradda Baba karami da Raihan suna zance ga dukkan alamu kiran dame martaba ya musu dukkansu yayi tasiri akan su,dama ga soyayya.

     Abdul na zaune yana mamakin dalilin daya sanya momy ta dauki zafi har haka kusan kwanaki biyar bata daga wayar sa,ga d'ayan bangaren Raihan ma bata daga wayarsa,kullum cikin kiran Feenah yake,akan ta bashi momy amma sam momy bata karbar wayar,jin karar  shigowar message yayi a wayarshi koda ya duba Raihan ce

"Salam yaa Abdul plss Kayi hakuri dani kamar yanda Nima na hakura dakai arayuwa,abubuwa ne iri iri daba kasan dasu ba,banajin dadin rashin daga wayarka amma nasani hakan shine daidai,ban guje ka sabida bana sankaba,wlhy ko kadan ba haka bane na dai gane kuskure na,sam ban kyautawa Baba karami ba,ina fata zaka fahimceni kuma Wannan baze taba mana zumun cin muba.Nagode Raihan." Nisawa yayi bayan ha karasa karanta message din yace a sarari..."Bazan taba dena sanki ba Raihan abu daya na sani tunda kika iya jin zaki rabu dani cikin lokaci kankani haka tofawa Nima zan hakura dake, Elham kuwa bazan taba Santa ba,zande aureta kurun sabida biyayya....

  Yau Kusan kwanaki goma sha d'aya fa momy bata d'aukar wayar Abdul,ya damu matuka,Wannan dalilin yasanya ya kira friend d'inshi zayyan ya sanar masa komai,gyaran murya zayyan yayi yace

"Zancen gaskia moris maganar iyaye ba abin wasa bane,nifa iya gaskiya Na nake gaya maka ka daure wa kanka ka aure yarinyar,kasani Kaima momy tafisan ka fiye da kowa a yaranta mesa d'an wannan abin ze gagareka,macece fa a hankali zaka koyi santa insha Allah" dan nisawa yayi yace "Zandai aureta zayyan amma sam bazan tab'a Santa ba wlhy,kuma yazanyi da san Raihan ? Wlhy ina kaunarta" dan guntun tsaki zayyan yayi yace

"Kaga nifa moris bana sanka da rigima,kaida kanka fa kace dani tajuya wa first love d'inta beside haka zaka bari ran momy yata b'aci mahaifiya uwa fa ? Kasani wlhy ka gyara tunanin ka tawa shawarar kenan" nisawa Abdul yayi yace

"Yanzu ya zanyi zayyan?"

"Zuwa zakayi ka fara  kiran Yarinyar a Waya,kuma ka daure kace ta hadaka da mahaifiyarka ka bata hakuri,ka sani fushin mahaifa wlhy Masifa ne moris"

"Tayaya zan kirata ince tabani momy zayyan?, girmana ze fadi a gunta fa" tsaki zayyan yayi "kaje wurin tariyar girma ka b'atawa mahaifiyar ka rai,bawai nace ne kace ta baka momy kai tsaye ba,kurun kamata dabara,misali bayan kun gaisa ya skul,waye waye Idan kun dan taba hira se kace kana gaida momy kuma ta tabbatar ta sanar mata"

"Zayyan tayaya zanyi hira da Elham dan Allah, ni harga Allah kazantar Yarinyar nakeji Wlhy"

"Kaika sani ni kaga ina kan aiki se an jima" datse wayar yayi kan yace wani abin,shi kuwa yayi sororro yana kallon wayar,ya dade yana nazarin maganga nun zayyan kan daga bisani yakira Safeenah,lokacin ita da Elham ne zauna sunawa momy tausa,domin agunta Abdul ya gado k'yank'yami sam bata huldarta da hadimai,shiya sanya Fulani Babba ke cewa dan bata gada bane. Dagawa tayi cikeda girmamawa ta gaidashi sannan yace "ki sending mun Number din Elham yanzunnan kinji ko?" D'an kallon momy tayi kasance war ita sam bata san meke faruwa ba kuma dama tasu bazuwa tayi d'ai data Raihan ba sannan tace "To Yaya Yarima yanzu zan turo" momy ce ta bude idonta dasuke a lumshe tun sanda suka fara mata tausar tace

"Me zaki tura masa kuma?"
"Number din Elham yake so wai" gaban Elham ne ya fadi yayinda zuciyar momy tamata sanyi ganinta takusa cimma burinta....a d'aya bangaren kuwa Abdul ya baiwa Elham msd col har biyu bata dauka ba kasancewar wayanta nacikin gidansu ita kamma bata gidan tana gun momy,se bayan isha tashigo wanda bata mabi takan phone d'imba,tana gama wanka tabi lafiyar gado,can acikin bacci taji wayarta na ringing janyota kurun tayi ta daga ta kara a kunne,a tunaninta samra Ce tasani ita kadai ke mata Wannan iskancin,cikin muryan bacci tace

"Samrah wai meye haka ne,kina yawan san takura ni wlhy,bacci fa nake" dan gyaran kwanciyar sa yayi sam be fahimceta ba yace

"Hafsat ya gida?" Zabura tayi jin muryar Abdul tace "yaa Abdul ina Kwana ya aiki?" Murmushi rikicewar ta ha sakashi yace batare daya shirya zuwan furucinba "Hafsat ina Kwana fa? Sabida kurun ke kina bacci seki ce dani ina kwana, Toni ban ma kwanta ba balanta na gari ya waye" kasa sakewa tayi da dogon surutunsa tace "kuskure ne Kayi hakuri yaa Abdul" shiru dukkansu sukayi sannan yace "seda safe,gobe Idan kinje wurin yarki kice ina gaidata" Murmushi tayi itama tace "zan fada mata inshaa Allah nagode sosai"

"Kinyi Alkawarin zaki fad'a d'in?" Ita dai binshi tayi da to a ranta tana tunanin yanda za'ayi ta sanar wa momy Wannan zancen, ahaka ta ajiye wayar tana nazarin dalilin kiran,ba wata kwakwarar dalili neman magana ne kurun.

Da safe ya kasance asabar dan haka da wayarta ta tsala ado ta tafi part d'in momy,suna gaisawa tafara gyaran d'akin momy ko ina yayi kalkal sannan ta dawo gyaran parlor tana tsakiya da gyaran wayarta yafara ruri,dagawa tayi takara a kunne da sallamar ta,amsa ta yayi cikeda isa yace "ki ajiye duk abinda kikeyi kije part d'in momy ki kaimata Waya zanyi magana da ita" d'an wai gawa tayi ta kalli momy dake cin breakfast,tace masa tana me shigewa cikin dakin "yaa Abdul inajin nauyi fa mezan ce da ita,dan Allah ka kira yanzu phone nata yana kusa da ita" shiru yamata tayita hello hello,ba amsa can taji ya katse wayar,kiransa tayi back yaki dagawa har kusan so biyu,Sekuma taji ba dadi ganin cewar sam yaqi daga wayar kuma ta fahimceahi yana da saurin Fushi ta sani Fushi yayi,dawowa tayi parlor din taje dakyar tace "Momy dama yaa Abdul ne jiya yace na gaidaki,yanzu kuma yace na baki wayar kanna zo nan ya yanke ko zaki kirashi da wayanki dan Allah" momy gani tayi tamkar Abdul ya sanarwa Elham bata daga kiransa,kuma seta kula tamkar Elham ta damu Wannan ya sanya ta,dauki wayarta tayi kiranshi,jikin shi har rawa yake ganin ta kirashi ya daga,ko gaisawa basui ba yace

"Momy dan manzan Allah kiyi hakuri, wlhy na gane kuskure na,na tuba momy wlhy zan auri Elham din dan Allah kimun gafara" nisawa tayi sannan ta tashi tashige dayan sashen daba kowa tace

"Zan gafarta maka Idan kamun alkawarin zaka rika kiranta so uku a rana,zaka mata yanda kakewa Raihan sanda kake neman aurenta,zaka biya mata bukatunta Idan basufi karfin taba kuma zaka shigo next month" nisawa yayi yace "zan yi momy,wlhy zanyi nanda sati biyu ma Zanso inshaa Allah" sallama tamasa ta sauke qayataccen Murmushi cikeda nishadi ta koma parlor......

Hankalin Fulani Babba sam baya jikinta ganin fa dagaske me martaba yake kuma kowa ya goyo bayan hukuncin ta,ga faruk ya koma paris abinshi baya ma kiran Waya gida, gashi kuma Raihan da Baba karami sun kara d'inkewa Yarinyar taqi bata hadin kai tai bori tace dole se Abdul,duk tashige damuwa sosai.

Wanin ranar Rabin shi Elham a wurin momy ta yishi,se bayan la'asar tabar gidan zuwa gidansu,Innah ta gaida inna ta ansata cikeda kauna tana kallonta ,ta yabawa yar yanda tayi jarumtar cire faruk a ranta gaba d'aya, takuma sani badan bata sansa ba,kurun dai Hafsat ne bata daukar wulakanci tasani wulakancin da Fulani Babba ta musu ne ya sanya ta fitar dashi aranta.....wuraren shidan yamma yakirata,da sauri kuwa ta d'aga wayar

"Yaa Abdul Barka da yamma" seda yadanja fasali sannan yace "Lapia,karki karamun abinda kikamun d'azu bana so" shagwabe wa tayi tamkar zatayi kuka,wanda ita bata dauka komai ba tace "Yaa Abdul dan Allah Kayi hakuri wlhy bazan kara ba" wani yarrrr yaji ajikinshi lokaci daya abubuwan dake kai saqonni na fahimta acikin kwalwarsa suka dena aiki na na 1 mnt,dakyar ya tattaro nutsuwar sa yace "Naji" a takaice,gani tayi tamkar be aminta ba tace cikin wata shagwabar "Yaa Abdul plss mana,trust me bazan kara ba" kasala ce dabesan dalilin taba ta saukar masa ya kasa koda motsi bale yayi magana takuma cewa "yaa Abdul Allah fa nace" cikin muryar kuka,d'if ya kashe wayar yarasa dalilin dakesa kirjinsa ke dokawa dazaran tayi magana,yace aranshi "nifa momy tabani aiki Wannan kazamar jakar zata rainani ko ubanwa take wa shagwaba oho" ita kuwa tsaki taja tana share kwallar data sakko mata tace "Allah yaa Abdul bazan taba sanka ba,na tsaneka Nakuma tsani halayenka na jiji dakai,zan aureka kurun sabida iyaye nka".

Mom Nu'aiym
[1/8, 10:32 PM] Sha'awa: *🌞HAFSAT ELHAM🌞*

Billy Galadanchi

Haske writer's Asso💡

Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).

*A gaskiya kuna sakani farin ciki ba kadan ba,sena tattare dukkan nazari na da tunani,ababen dake sarquwa a kwanyana dan gane da aika saqon fahimta duk se su tsaya cak,ni kanyi mamaki matuka yanda kuke nuna kaunar ku ga rubutuna duk kuwa dayake nidin karamar su ce acikin marubuta.....a wani bangaren mamakine kan kashe ni duk na tuna a shafin farko na book nawa kuke fara comments,dan Allah ku yarda dani ina sanku har raina*

04
Wuraren karfe 9 na daren ranar ya kuma kiranta amma sabida hafsa tafishi zuciya ga kuma rashin daukar raini ya sanya taki dagawa,msd col biyu ya bata,ranshi yaji ya sosu ba bad'an ba, daba dan momy bace wlhy Wannan Yarinyar da tayi kadan yasani sarai tana ganin col nashi tamasa banza,amma zata fahimci baya daukar raini Idan tashigo hannun shi....a bangaren Elham kuwa ta kudiri niyyan bazata kara daukar wayar saba,tunda kullum burin shi ya bata mata rai,ita banda munafurci ma batasan meye na kiran taba,washe gari kuwa bata ma tafi da wayarta sashen momy ba haka taje saddan,ayyukanta tayi tazo ta zauna cin abinci tare da momy da feenah,wayar feenah ya soma ringing, dagawa tayi ganin yaa Abdul ne

"Yaa Abdul ina Kwana" be amsata ba yace kije gidan su Elham ki kai mata Waya Kokuma kice da ita nace lallai ta kirani yanzu" tana kokarin sanar masa Elham na kusa kurun ya datse wayar tabe baki tayi ta kalli Elham tace

"Elly ina wayan kine?"" Kallonta sukayi har momy,sannan tace

"Tana sashen mu,agida na barta" dan yake tayi tace "Gwaramun me martaba ya kirani ban dauka ba nasan ze fahimci bana kusa akan yaa Abdul ya bani ko half msd c ne Idan akwai,ya tsani ya kira mutum yaqi d'agawa ko alama,yanzu kinga masifa yake wai na sanar dake ki kirashi yanzunnan" batayi magana ba shiru kurun tayi momy ce tace "ki tashi kije ki kirashi yanzu" mikewa tayi jiki ba kwari taje gidan msd col hudu ta tarar Nasa ,seta tsinci kanta da kasa kiranshi tsoro me tsanani ya shige ta,ta sani bazata iya gaya mai bakar magana ba amma fa batada juriyar wulakanci,tsaf zata kashe masa Waya Idan yanemi gaya mata ba daidai,daga karshe dai phone nata ta kashe gaba d'aya.... Ba ita ta koma part d'in momy ba se bayan isha sannan ta Shiga, suna wa momy tausa wayar feenah ta fara ringing tana dubawa taga Abdul ne,tana daga wa yace "Idan Elham tana kusa ki bata yanzu" batare da tayi magana ba ta mikawa Elham waya,tana karba tabar wurin seda tashiga d'akin momy sannan tace cikeda faduwar gaba

"Assalamu Alaikum" cikin tsawa yafara masifa

"Ke Elham me kika dauki kanki ne? Tun yaushe kike ganin col dina bakya dagawa kuma bakya kira back,kuma tsabar raini seki kashe wayar gaba daya,me kike tagama dashi kazama dake,ke badan umarnin iyaye ba da kin isa na rab'i hanyar dakika bima,iyayena naso su miki gata amma kina wulakanta musu yaro,ke bakisan halacci ba ko,dama mana tsinatacciyar mage ai bata mage,kisani wlhy talaka irin ki nafi karfin wulakanci daga wurinta,alkawrine nayiwa momy zan kiraki kullum so uku arana,dabadan uwa na uwa ba wlhy bazan kara kiran kiba,jaka kawai dabata san girman na gaba da itaba,kuma Idan kin isa Nakuma kiranki kimun banza,zan miki uzurin bakya kusa amma wlhy bazan miki uzurin rashin kirana back ba,idan katin wayane bakida zan miki VTU yanzunnan" kukane ya kwace mata,jin tana sheshekar kuka yasanya ya kashe wayar dak'yar ta iya saisaita kanta ta koma parlor d'in, momy ta zata wayar arziqi sukayi se washe baki taki,a daddafe ta gama abinda take ta koma gidansu,wanka tayi sannan ta kunna wayarta tayi adu'o in Kwanciya Sekuma ta kasa baccin ta soma kuka me tsuma zuciya,a haka ranar ta Kwana kuka tana mejin zafin zagin wulakncin da yamata,a rayuwar ta ta tsani a Rena mata iyaye da talaucinsu ko sabida kurun suna karkashin inuwarsu bashi ze basu damar wulakan tasu ba,mijin da zaka yana maka zagin na tozarci tunkan ayi auren hmmm...washe gari da ciwon kai ta tashi dama kuma sn fara final exam na kammala secondary skul,ranar ba skul basuda Exam kasa yin komai tayi,Wuraren 9 wayanta yafara ruri janyo wa tayi a wahalce,ta kara da kunne "Assalamu Alaikum" "Alaikissalama" ya fada cike sa isa

"Yaa Abdul ina Kwana?"

"Lapia kin tashi lapia?"

"Alhamdulillah" tabashi amsa a takaice "meyake damunki Elham,muryanki wani iri?" haushi ne ya tarnake ta tace "Ba komai qalau nake" shiru yayi itama hakan kusan minti biyu,daga bisani ya datse call din, tsaki taja tace aranta kadaiji da rainin wayonka d'an masu kud'i.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya sam Elham batajin dad'in rayuwar ta, ta tsani Abdul ta tsani kalar wulakancin shi,ta tsani jin koda muryar sane,ta tsani tunawa da zancen auren sa gaba daya,duk sanda ta tuna cewar sun kammala exams gaba d'aya gashi taji ance me martaba ya saka bikin nanda watanni biyu setaji tamkar ta daura hannunta asaman kai ta zunduma ihu,ba karamin dad'i tajiba sanda akace zezo kuma ya fasa zuwa sabida aiki yamasa yawa sabida bata bukatar ganinsa....

Tafe take cikin doguwar bakar jallabiya me adon yellow stones, ga rigar tasha shape,d'an karamin cikinta daya lafe tamkar ba'a saka masa ko loma d'aya aciki,ga wadaccen kugunta daya ke kad'awa batare da tasaka shiba,tafiya takeyi tamkar tanajin tausayin kasa,fuskarta tayi fayau ba komai a cikinta se powder da lipbalm, kallo d'aya zaka mata ka gano sam bata cikin walwala,dadana wayarta take tana faking murmushin.....shi d'inma wayarsa yake dannawa hankalin shi yana wurin abinda yake se karo sukayi da juna take wayarta ta sub'uce a hannunta tafad'i a kasan interlock dake shinfide a wurin tare sukabi wayar har suna gwara kai,hannun tane yariga nashi kaiwa yayinda nashi ya sauka akan nata,lokaci d'aya wani shock ya sauka musu dukkansu atare suka d'ago suka kalli juna,a haka suka k'urawa juna ido tamkar wasu statues,itane tafara dauke kanta,yayinda shi kuwa da sauri ya dauke hannunshi daga nata,atare suka mik'e batare da kowa ya dauko wayar ba,Kawar da kanta tayi akaro na biyu tace "yaa Abdul Kayi hakuri ban kula kana zuwa ba" dukawa yayi ya dauko wayar ya mata kallon tsafta yace cikin gadara

"Duk lokacin da kuke tafiya kuna maida hankalinku akan hanya kina jina?" Kai kurun ta gyad'a masa tana tunanin what on earth was he doing dabe mayarda hankalinshi akan hanyar ba shima,tana tsakiya da tunanin ta tsinkayi murya sa yana cewa

"Wayar kinnan kai tsaye ta lashe screen Elham,ki shirya karfe 8 daidai ki sameni

Please Login or Register in order to submit comment