Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta shiga shiryawa, kayan tasaka tazauna tana saka kwalli wayanta ya shiga kara da sauri ta dauki wayan dake kan gado ganin Granny ne yasa takai wayan kunnenta da sauri tace "Granny, harkin fara kewana, good morning" "morning diyar kirki, kinada lectures this morning ne"? Ahankali tace "eh, inada shi, but banda second lecture din shi malamin bazaizo ba wai sai gobe kuma zamuyi test dinshi ma" dan jim Granny tayi sanan tace "okay shima this morning lecture ki hakura dashi hope ba matsala"? Dasauri tace "okay dama course din baida wuya nama iya nai covering" Granny tace "good already direba na hanya zaizo yadaukeki in yaso gobeda safe yamaida ke school din sabida test din" ahankali tace "tom, Grann...." batama idasa kiranta ba ta katse wayan hakan yasa tafasa gado ta zauna, Maryam data gama shiryawa ta kalleta tace "menene"? "Granny ta turo adauken waina fasa lecture safen nan" jaka Maryam tadaukaa ta goya tace "to Allah saidai lpy, natafi makesure you read idan kinje gida saimun hadu a test din tomorrow" bye sukama juna Maryam tawuce ta tafi itakuma takoma ta idasa saka kwallin sanan ta feffesa turarukanta sanan takoma gado ta kwanta tadau wayarta tana daddannawa, tashi tayi tunawa dabatasha magungunan safenta ba tadebo ta hahhada tasha tana tabe baki tana kawai dannama Granny alkawarine da tuni nazubar daku kullum ranan duniya sai mutum yasha magunguna daban daban fin kala shidda, idan mutum yaje weekend tawani bashi kaza duk magani instead of abani kaza lafiyayya, ita kadai sai korafi take takoma gado ta kwanta saiga wayanta yahau kuka, tamasan direba ne hakan yasa tadauki jakanta tahada komi ciki littafin da zasuyi test ne kawai gobe akai batasaka ajakan ba sabida zata karantashi amota, sanan tadau gyalenta tayafa kalan sabon yafan da Mum takoya mata acewa yanzu tadawo matan aure ta rufe cikaken kirjinta tass dakenan kaman an hula balan balan ansaka ariga, sanan tadau jakan tagoya tarike wayanta da book din dazata karanta a hannu tafito ta kulle musu kofa da key sanan tawuce tafita, tana zuwa gaida direba tayi ta shiga mota yaja motan suka tafi.



Wuraren 10 sukai parking a compound dinsu, bude kofan baya tayi ahankali tafito tana mamaki yanda yau Amna bata fito tamata oyoyo ba, tana kallon sabuwan bakar mad jeep din datagani tana mamaki Dady yasai sabuwan mota ne, tsayawa tayi tamika hannu tadauko jakanta tagoya sanan tadauki book dinta d waya tataho direct hanyar flat din Mum dan nan take fara shiga ta gaisheta kafin tawuce side din Granny........


Yanda gabanshi ke dukan uku uku tun bayan Granny datake falon cikin harshen turenci tacemai ai gashinan tadawo, kas daurewa yayi ahankali yajuyarda kanshi dan kujeran dayake na saitin window ne dakenan labulen adage ya zuba mayun idanunshi akanta, daidai lokacin mistakenly book da wayan data rike sun kufce daga hannunta suka fadi akan interlock din compound din, da sauri ta tsugunna wayan ta dauka ganin babu abinda yasami wayan yasa tai murmushi tadauki book din ta tashi sanan tacigaba da tafiya.

.da sallama tabude kofan tasawo kanta cikin falon, wani irin sanyin AC dakuma kamshin turaren daya tunamata da wani abune yafara dukan hancinta saikuma da sauri tashigabin yan falon da kallo, Granny na zaune kan one sitter cikin shiga ta alfarma, sa Mum na zaune kusada Dady daduk sukaci gayu, kafin ahankali idanunta suka sauka kan Tobi dake sanye cikin wani farin shadda kal mai shegen tsada tsada, kanshi na sanye da farin hulan yarbawa, hannnshi sanye da agogon hublot mai tsadan gaske yazubamata mayun idanun nan nashi kaman zai hadiyeta.


Chak ta tsaya takasa koda motsi ahankali tasaki waya da littafin hannunta takai hannayenta kan fuskarta tarufe tana kokarin saita kanta dan kaman numfashinta zai fita daga kirjinta takeji...

Tashi yayi dagakan kujeran dayakekai ahankali yafara tafiya haryakai inda take ya tsaya chak yana wani irin murmushi sanan gently yakai hannayenshi kannata dasauri yan dakin suka dauke kansu ganin wanan fa baisan kunya ko kawaici ba bambamcin kabilar kenan fa, ahankali yacire hannunta dagakan fuskanta cikin wata irin murya dashi kanshi baisan yanad itaba yace "Jewel is me, Tobi! Your husband" sanan gently yakai bakinshi kan saman forehead dinta yamata peck mai kara dayasa taji jikinta yadauki kyarma janye bakinshi yayi zaikai mata hug dasauri ta zulle jikinta bai dena rawaba tashigo falon da sauri hargaban Dady daya maida kanshi kan TV ta tsugunna tace "Dady ina kwana,.....Mum good morning, Gran......" dukama takasa magana tsabagen yanda bakinta ke rawa murmushi Dad yamata yace "tun safe mijinki yazo kina school yanata jiranki, ya makaranta"? Ahankali tace "lpy lau" gabaki dayan ta shaking take, tsugunnawa Tobi yayi yadauki wayanta da book dinta sanan yadawo falon yazauna inda take, Granny tace "kin gaida mijinki, wuce ki gaidashi nina tafi part dina na kalli gidan Badamasi" dasauri Dad da Mum suna suka tashi, Granny cikin turenci tace "Son i will be in my flat if u need anything" cikeda fara'a yace "okay SweetMum, thank you Sir, thank you Ma" yay maganan da murmushi sosai yana godema su Dad kaman wani dan gida, Granny tafita tana murmushi aranta tace "yau sun hadu da fetsararren siriki".


Har suka fita tana inda take atsugunne akasa shikuma yana zaune kan kujera yana kallonta, ahankali cikin wata kalan murya yakirata. "Zaaaa.....raaaa" ayanda yakirata yasa she couldn't resist samun kanta tayi da dago kanta ta kallai softly kaman yaune rana na farko data fara ganinshi aduniyan nan, cikin karaman murya yace "is me, Tobi! Are you not happy to see me"? Girgizamai kai tayi ahankali, hakan yasa ya lumshe ido tareda sake budesu sundan kankance kafin ahankali yabude mata hannayenshi ya lauyardakai kaman wani baby yace "come here Jewel" kaman jira take da sauri ta tashi tasaki jakanta awajen sanan tataho batai wata wataba tafada jikinshi sai kuka, maida hannayenshi yayi yahade ya rungumeta tsam ajikinshi, yanajin yanda take kuka ajikinshi jikinta na bari sosai, daura kanshi yayi akanta, yay muryan mai whispering with a very soft voice yace "am so sorry Jewel, I promise to never leave you again, I promise to be yours and yours forever, we will be together henceforth, Am sorry for all the things you went through because of me baby Zara, am here now okay, and I gotcha, I gotcha for life Zaaaraa" yay maganan ahankali idan da xaka shigo dakin bazaka taba sanin magana yakeba dagashi sai ita sukejin junansu. Takai kusan 5min tana kuka ajikinshi kukan data dade tanaso tayi sanan gently yacirota daga jikinshi yana kallon fuskarta, ahankali yakai hannunshi aljihu yaciro handky fari kal sanan yakai kan fuskanta tareda saka dayan hannunshi ya karbe hannunta dake kan fuskan yashiga share mata hawayen murya chan kasa yace "you are now 20 but you still cry, cry cry baby" tabe baki tayi tana kallonshi kaman zata saki wani sabon kukan da sauri yakai bakinshi zai manna mata kiss, kaudakai tayi da sauri jikinta na rawa hakan yasa yamaida kanshi jikin kujera kaman dan karamin baby yace "wlh am hungry banci komiba tun safe" da sauri ta kallai, gyadamata kai yayi ahankali yace "get me something to eat, su Granny sunban abinci nakici nace musu sai wife dina tazo" dan murmushi tayi dake nuna taji kunyan maganan shi saita tashi ahankali zata wuce hannunshi daya rike bakin gyalen data yafane yaja harta fara tafiya taji gyale nafita daga jikinta da sauri ta tsaya jin gyalen yagama fita tajuyo ta kalleshi kaman yanda yabita da kallon tundaga kai har kafa, fatarta yanzu yafi nada haske gawani irin glow da skin dinta keyi kaman madara, ahankali yasauke idanunshi kan kirjinta kodan takara girmane dayasanta tana 19 yanzu tana 20 approaching 21 ne yasa boobs dinta sunfi da girma da cika kaman zasu fasa rigan jikinta hadiye wani mayen miyau yayi tareda cije lips dawani irin sauri tajuya ganin maiyake kallo hakan yabashi daman kallon as dinta ta skirt din datasaka daya matseta tanada hips da bombom masu shape mai kyau bazama kagane hakaba sai ranan da zata saka jean, amman basuda wani girman haukannan daidai jikinta kuma sunyi mugun fitting nata, lashe lips yayi yana kara maimaita she's all mine, ko yanzu naso I can carry her to my house she's ny wife legal weded wife.

Book dinta dake hannunshi ya kalla saikuma yabude ahankali yana kallon yan handwriting dinta mai kyau kanana, sanan yabude wayanta ahankali ganin da password yasa ya ijiye komi akan kujeran yatashi da sauri yay kitchen din abakin kofa ya tsaya yay folding hannu yana kallon yanda take frying egg dasauri da sauri, murmushi yayi yashiga cikin kitchen din, jin karan tafiya yasa dasauri tajuyo ganin Tobi ne yashigo yasa taji hankalinta yatashi da sauri ta kalli kofa tama manta ba hausa yakeji ba tace "dan Allah kakoma falo kaga kar Granny tace bamuda kunya daga zuwanka har kitchen kake biyoni...... " daga kitchen sai Granny yagane amagananta, ganinshi agabanta yasa tasaukarda kanta jikinta na rawa, ahankali yace "am just here to eat the egg ne" jingina yayi da jikinta ya matseta sosai dayasa ta kulle idanunta gam sanan yakai hannunshi kan plate din yadauki kwai da hannunshi sanan yakoma baya yana kallon yanda ta kulle idanunta yace "am done" bude idanunta tayi tadaurasu akanshi ganin egg din yadauka da hannu yasa tajuya da sauri duk haushi yadan cikata yanzu kwai zai dauka saiya matseta a bango yasa gabanta nata faduwa kaman zai fita, tabayanta yazo dawani irin sauri tajuyo kaman zatai kuka gabanta nafaduwa sosai tace "please kabari, uhm stop" jikinta yashige sosai ashagwabe yace "but I want to kiss you" dawani irin sauri ta saukarda kanta tana girgizamai kai da sauri sosai ganin ko kadan shi baimasan menene kunya ba tamakasa magana, ginin yanda takeyi yasa yadan dukarda kanshi yana kanta da fuskarta data ssaukar kasa ahankali yace "plsssas wife" ganin dagaske yake sosai gashi suna kitchen yasa lips dinta har hardewa suke tace "o....k.....la.....later, but now go" tai maganan tana nunamai kofa, murmushi yamata yanaji kaman kawai yahadiyeta takoma cikinshi, yana kallonta still yace "okay I can't wait for later, I will so kiss you Zara" sanan gently yafita daga jikinta yawuce yafita daga kitchen din tabi bayanshi da kallo tana sauke ijiyan zuciya mai karfi sosai sanan tajuya tafara girki tana magana ahankali tace "na shiga uku mesa baida kunya yanzu"? Wata zuciyar tace "sabida kin dawo matarshi" ahankali tace "but ai baitabamin maganan iskanci ba da, amman yanzu daga zuwanshi gidanmu yau har biyoni kitchen yake, idan su Mum suka ganshi fa" agurguje takarasa hadamai coffee da egg da sausage irin yanda taga anamai breakfast a Lagos sanan tadaura komi a tray tadauko tafito, tunda tafito yake kallonta kasama tashi ya karba yayi hartazo taduka tajawo stool yasauke mayun idanunshi akan saman kirjinta dasukai showing sosai sabida yanda taduka yadan lashe lips dinshi, ajiye tray din tayi sanan ta tashi da sauri yadauke kanshi kaman ba kallonta yakeba, dan kallonshi tayi yanda taga hankalinshi nakan tv yamata kyau sosai this is the first time take ganinshi da manyan kaya haka......"am all yours now Jewel no need to stare, you can have me here if you wish" yay maganan yana juyoda kanshi dauke kai tayida sauri tareda turo baki tawuce dinning, bude kulan wajen tayi tadebi pepper soup sanan tajuyo still ita yake kallo yanacin abincin, dan murmushi tayi takoma tazauna ba'a kan kujeran dayake kaiba, hakanan tajima takoshi takasacin abincin wlh har cikin ranta murna take da farincikin ganinshi hakanma yasa taji takoshi, murmushi tasakeyi tadauki spoon tafarasha ahankali duk idan zata dagokai saisun hada ido, tass yacinye abinda tahadamai itama haka hakan yasa ta tashi ahankali tazo gabanshi ta kwashe sanan tawuce kitchen ta ijiye tafito, hanyar kofa tayi batare data kalleshi ba tace "i want to go and change a Granny side" sanan tabude kofa zata fita, muya chan kasa yace "Jewel" juyowa tayi takalleshi yanda ya narkan mata da ido yasada sauri tadauke kanta yace "get ready kifito am taking you out, zamuje sallan jumma'a daganan zamu fita" sakai tayi tafice abinta tai flat din Granny saida takai saikuma taji tana kunyan shiga tunawa datayi tabaro gyalenta achan, "wai waye ya tsayamin agaban kofa" Granny tafadi dayake kifan abude, ahankali tadaga labulen tashiga kanta akasa, daga Granny sai Mum afalo shi Dad yay ficewan shi, ganin wucewa daki zatayi duk akunyace take yasa Granny tace "ina kika baro mijin naki" kasa juyowa tayi tace "yana falon Mum" tabe baki Granny tayi ganin takasa kallonsu tace "je dakina akwai maganin dana hadamiki yanakan drawer ya tsumu yanzu ki dauka kisha" gyadamata kai tayi, zata wuce Mum tace "Zara mijinki nada kyau wlh gashi dan gayu, ki rike abinki da kyau, Allah ne ya sharemiki hawaye, Granny kinga yanda yake kallonta kuwa kaman zai hadiyeta agabanmu" dagudu Fatima tai ciki daga Granny har Mum suka kwashe da dariya, Granny tace "ai indai akace miki mutum ba bahuashe bane, bayerabe fa basuda kunya, gasuda son matansu, agaban kowa zasu nuna sufa sunason matan su, akwai wata kawata lokacin itama bayerebe ta aura zokiga zo" Mum tace "dole Fatima ta dage ta ijiye kunyan nan" Granny tace "tuni ma" daganan suka cigaba da hiransu saida ta shanye maganin sanan tawuce dakinta, tabude ta shiga.


Zama tayi akan gado, gabaki daya tama rasa mezatai tunani saikuma tai murmushi everything looks so strange, Tobi! Sir! Prince! Aremo shine wai yau tagani a gidansu akuma Abuja, shine kumawai mijinta this is so strange, rufe fuskanta tayi saikuma tasaki murmushi sosai, saikawai tafada gado tareda lumshe ido tana wuntsila kafa gabaki dayan kamshin shi taji tanayi, tunawa datayi yace he wants to kiss her yasa ta kulle idanunta gam tana murmushi harda daukan filo ta rungume tana juye juye, is this what love is?? Ta tambayi kanta dan wlh she is damn happy, wani irin farinciki da shauki takeji yau dinan na daban dabazata iya tuna when last a rayuwanta tai kalan wanan farin cikin ba, sake juyi tayi kawai sai jinta tayi akasa Allah yasa akwai carpet data bugu da sauri ta tashi tana turo baki ta kalli gadon tace "kafado dani ko? Saina fadima Tobi, My hus....." saikuma takasa karasa fadi kunya yawani irin kamata tajuya tawuce bayi da sauri kaya tacire tanabin ko'ina na jikinta da kallo, ance idan anyi aure miji na ganin komi na jikinki tayaya zatabari Tobi yaganta haka tsirara lallai nema, tafadi tana hararan mirror sanan tawuce tana kokarin fara wanka ta tuna Granny tacemata duk ranan Friday tadinga shaving, dudda babu wani gashi amman saida ta shaving ko'ina da shaving cream dinta sanan tai lafiyayyen wanka tafito daure da towel, zama tayi ta shafamai sanan ta rambada kwalli a idanunta dake karamata wani mahaukacin kyau, sanan tashafa white man baki daya hasko hadaddun pink lips dinta sanan ta shirya tasaka wani black abaya, kafin takara komawa ta zauna ta tsaga tulin gashin kanta dakenan agyare biyu sanan tai parking dinshi da kyar yawani irin kwanta, tai donut da jelan gashin dayasa tai wani irin kyau tadau gyalen doguwan rigan kenan zata yafa taji Muryan Tobi dasu Granny afalo yana tambaya "Granny where is my wife"?



TALK TO ME M SHAKUR DIRECTLY BY CLICKING ON THIS LINK https://wa.me/+2347012181461
FOR ALL SHIGA GROUP DINA, KO GROUP DIN MATAN AURE.




Baki ta taushe cikeda mugun kunya tana waishe wanan wani irine bazaimace ina Zara ba, turo baki tayi tadau gyalen tayafa akanta ahankali, sanan tadau wani peace lv back, da peach takalmi tasaka combination din yabada kala saman ta feffesa turare tabude kofa tafito kanta akasa ta shigo falon, zaune taganshi kusada Granny yanamata hira kaman yasami kakanshi, yana ganinta yadago kanshi yanabinta da kallo yace "just look at my wife Granny, Mum look at her" hararan shi Granny tayi tace "kaga dauketa kutafi saikun dawo, kudawo dawuri" murmushi yayi yatashi yana kallonta, daure fuska tayi kanta akasa ahankali tace "Granny Mum saimun dawo" "adawo lpy Zara" yana kokarin kama mata hannu taki hakan yasa yabarta suka wuce suka fita sukai wajen motanshi, gani tayi an bude motan anfito wani security agent yana sanye da suit da bakin glasses akan idanunshi hakan yasa tabude idanuwanta, dan dariya Tobi yayi yace "don't mind Dad, yace bansan ko'ina a Abj ba shine yahadani da direba dakuma bodyguard" yay maganan yana nuna mata ta shiga, shiga bayan tayi ahankali ta matsamai shima yashige sanan security yarufe door yazagaya ta dayan bangaren daba nadireba ba direban ya gaidasu cikeda girmamawa suka tafi.


TALK TO ME M SHAKUR DIRECTLY BY CLICKING ON THIS LINK https://wa.me/+2347012181461

Hannunshi yamika yadauki nata yahada su tare sanan ya kalli direban yace "take us to mosque muyi first jumma'at prayerYo dinmu as a couple" yay maganan yana maida idanunshi kanta aiko ta dauke kai tana gimtse murmushin datakeji.




_NAFJAN COLLECTION_
_Nafjan Collection business ne na shahararriyan CEO dinan wato Nafisa, wacce ta kware akan sana'oi kala kala._
_Tana saida kowani kalan kaya dakuka sani, Riga, wando, lace, shadda, atampa, takalma, na maza, na mata, na yara, na manya, sneakers, cambas, sandals, flat shoe duka, handbags, bagpack, akwatuna, dogayen riguna, agoguna, tana shigo da hadaddun kayan daki daga kasan waje, kayanta arahansu zaisa kama rufe baki, dan tuntubarta ko magana da ita directly zaku iya saminta awanan number wayan 08160472711, kowani kalan abu kuke nema kawai ku danna mata kira dan tambayanta kuji kotana dashi kobatada shi_

_Dankuma magana da ita directly a watsapp zaku iya samunta ta hanyar danna wanan link din.👇_

https://wa.me/+2348160472711

_danyin sarin kaya awajenta da sallan nan, just chat her up_ https://wa.me/+2348160472711
7/19/21, 11:57 AM - My Mtn Number: 💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫



✍🏾M SHAKUR



EPISODE 6️⃣6️⃣ & 6️⃣7️⃣
Abuja central mosque yakaisu suka sauko yana rikeda ita kaman za'a kwacemai ita saida yakaita har hanyar dazatabi tashiga side din mata da direban yanuna musu sanan ya kalli fuskanta itama dan kallonshi tayi saikuma tasauke kai ganin yamata wani kalan fuska dakesa heart dinta na racing, ahankali yace "pray for us" dasauri ta kalleshi tadan turo baki, hakan yasa yace "yes, pray Allah yakara miki sona, kisoni kaman yanda nake sonki, cus nasan inda ace zaki soni kwatankwacin yanda nake sonki danafi kowani namiji sa'a" murgudamai baki tayi aranta tace "bakasan yanda nake jinka araina bane Tobi" murya chan kasa yadan kalle gefensu ganin babu kowa yace "pray bayan our first love making, immediately bayan i sex you you should carry my baby" dawani irin sauri ta fizge hannunta tajuya da gudu tai cikin masallaci shikuma yay dariya yajuyo yana murmushi yakoma side din maza yana mamaki maisa takeda kunya haka ko haka yan arewa suke but mata a lagos basuda kunya, they can even ask you for sex but deep down kuma he loves yanda take kunya is freaking turning him nuts, and he promised to be so naughty to her just for reaction dinta which is a killer.



Koda suka fito daga masallacin kasa shiga motan yayi ganin bai ganta ba, ganin anata tafiya bata yasa yay hanyar side din matan, saigata tafito bamata lurada shi ba ta tsugunna tajuyarda takalminta da aka kife sanan tasaka white leg dinta dayabi da kallo, sanan jin kaman ana kallonta yasa tadago kanta hada ido sukayi da sauri ta dauke kai ganin irin wani nayen kallon dayake mata sanan tafara tafiya ahankali harta karaso inda yake, hannu yamika mata ahankali batare dayay magana ba hakan yasa ta kalli hannun saikuma ta kalli fuskanshi kafin ahankali tasaka hannunta ciki sanan sukai wajen motan bodyguard zai budemusu yahanashi yasa hannunshi da kanshi yabude marfin motan ta shiga sanan ya shige.





Hannunta nakan nashi cikin wani kalan lazy voice yace "let's go to Mango" sanan yajuya ya kalleta gabaki dayan kanta na glass tana kallon titi tana murmushi, wayanta dake wurinshine yay ringing hakan yasa daga ita harshi suka kalli wayan anyi saving number da Abdul Classrep, daukan wayan yayi yamika mata karba tayi ahankali tai picking takai kan kunenta, classrep din yace "Hello Zara, yau banganki a aji ba lpy" ahankali tace "naje gidane" "to don't miss tomorrow test fa, 2hrs zaiyi using 1hr test 1hr lecture" gyadamai kai tayi tace "tom" yace "to shikenan sai anjima agaida mutanen gida" ahankali tace "zasuji" sanan takatse wayan tajuyo ta kallai ganin ita yake kallo yasa hakanan taji gabanta yafadi ahankali tace "is our classrep, he called to ask mesa banzo school ba and he told me zamuyi test goben" yanda take maganan kawai da bakinta yake kallo shit he can't wait ya kama this lips wlh saiya chanza musu kala, dan kankance idanunshi yayi yace "don't worry I understand" ya matse hannunta dake cikin nashi har sukakai wajen parking akayi da kanshi yafito yazagayo bangarenta yabude mata kofa tareda mikomata hannu suka shiga ciki shagon phones ya shiga yajuyo ya kalleta yace "kinada system"? Girgizamai kai tayi yace "a ina kike typing project dinki"? Ahankali tace "school Cafe" yana rikeda hannunta har lokacin yasaya mata MacBook, IPhone 12, I watch, dakuma earpods duksai kallonshi take yabiya kudin tass, sanan yabada wayanta da babu wani abun kirki ciki banda notes da kayan school yace a maida abubuwan ciki zuwa new phone din, tass akamaida cikin yan mintoci sanan akabasu bodyguard ne ya karbi ledan yawuce yakai mota jayata suka xhiga wani goldstore, ya kalleta yace "pick anything you want wife" da sauri ta kalleshi, kujera yanema yazauna yace "go" wucewa tayi kamam yanda ya umurceta Madam din shagon na nuna mata latest collection, ita batason sarka yacika mata wuya hakan yasa tanemo simple design na set sarka da dankunne, saikuma zobe mai kyau da warwaro sanan tace "ya isa" biya yayi sanan, suka fito, wani shagon undies da lingerie yahango hannunta yarike suka shiga shagon, shagon babu komi na Nigeria a ciki, hadaddun panties da lingerie irin na celebrities ne ashagon, kujera yasa aka bashi ya zauna sanan ya kalleta yace "shop Jewel" kaman zatai kuka tace "inada su fa" wani irin batarai yayi yace "start" wucewa tayi saikawai tawuce wajen normal bra da pants bana yan iska ba according to her. "Jewel" taji yakirata daidai zata fara dauka, sanan yanuna mata bangaren bra na yan iska wanda kusan duka nono awaje yace "pick from this category" bakaramin kunya tajiba ga shagon da mutane shiko ko ajikinshi inda yanuna mata tazo amman takasa taba komi hakan yasa yatashi yazo ya tsaya kusada ita yace "whats your bra size"? Dauke kai tayi da sauri ta kalli wani waje, hakan yasa yay murmushi yace "you better tell me inbahaka ba I will so kiss u here in front of everyone remember you are my wife" dasauri ta kallai tai fuska kaman zatai kuka tana turomai baki, shima turomata bakin yayi yace "tell me or I do it" murya chan kasa tace "42B" dan zaro ido yayi yana kallonta yace "oh my God they must be so bigggg" kunyan dataji yasa tajuya zata tafi da sauri yakamo hannunta yana dariya, yana picking mad bra of that size yana sawa a cart sanan yace "but I didn't lie now, am a lucky Man, My wife is booby" dasawani irin sauri tashige jikinshi takafa fuskanta akirjinshi kaman zata nitse ciki chak ya tsaya da abinda yake sanan yakai bakinshi kan kunnenta yace "i will so suck them idan nakamasu" dawani irin sauri tasakeshi wanan karan tafita da gudu bodyguard dinshi yakalla yamai alamu dayabita, shikuma yacigaba da kwasan mata mad panties da bra, yaje bangaren lingerie ya jidan mata suma, sanan yabiya kudin komi yafito bodyguard yazo yakarba yasa a mota sanan yashiga baya yana kallonta ganin taki kallonshi, hannunshi yamika zai karbe nata tamake mai kafada tace "let's go home kaga is to 5 yanzu banyi karatu ba" tada motan akayi saida suka tsaya awani masallaci sukai sallan la'asar sanan suka fito wani super market sukaje yama gidan siyayya sosai sanna suka wuce gida lokacin around 6, parking sukayi a tsakar gida, saida su Bodyguard suka tafi sanan tajuyo ta kallai shima ita yake kallo dauke kai tayi tace "please those things just keep them with you banso su Granny sugani" fess yagane maganan Bra take, shidama kobata fadi ba gidanshi zai wuce dasu amman saiya fuske yace "which thing?" Kallon fuskarshi tayi ganin baigane

Please Login or Register in order to submit comment