Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce dan yaran bahaushe ne ai, wani irin cute murmushi tayi cikin baccin daya bayyanar da kananun fararen hakoranta dakuma cute two sided dimples dinta, sanan ahankali tasake dan motsi sanan idanunta suka fara rawa budesu tayi ahankali saikuma tabude su tarrrr ido da ido sukayi da Tobi dake kwance kan gado, laptop nakan pilow akan cikinshi ya janye idanunshi dagakan laptop din yana kallonta gabaki daya, dawani irin sauri ta maida idanunta ta kulle gam tanaganin kaman amafarki taga prince din gidan nan na kallonta sanan ahankali ta shiga bude idanuwanta kaman wacce tai sata har lokacin tana akife tai rubda ciki sanan tabude idanun tatas tasake kallonshi ganin still shidinne dai tana kallonshi yana kallonta kurr yasa tawani fasa uban ihu da kuka duka alokaci daya danyau tai mugun laifi sanan ta shiga tashi da sauri jin abu mai shegen taushi kan jikinta yasa ta kalli abun ganin bargonshi nakan gadonshi dayake rufa dashi yasa tamugun fashe da kuka ta kalleshi still yana kallonta ko kyafta ido baiyi ba ta tashi sosai tana tattare bargon tai kneeling tahade hannayenta biyu duka tana kallon agogon bango ganin sha biyu saura yasa tafashe da mugun kuka tace "sir please please forgive me, please forgive me sir, I don't know how I slept off pls sir dan Allah kayafeni, kayakuri, Sir please don't ask those people to beat me, please I am so afraid of the cane, I promise to never sleep again, pls don't make them beat m.......e....." "go to Mum's flat and get me food I am damn starving" yay maganan ahankali yana mayarda kanshi yana resting akan filo ahankali, tsagaita kukan datakeyi tayi tadan kalleshi ganin yacigaba da abinda yakeyi yasa da sauri ta tashi, kinkiman bargon tayi tai hanyar fita waje dashi dan tabayar awanke harta bude kofa yace "where are you taking my duvet to Boy" da sauri tajuyo ta kalleshi hada ido sukayi ya zubamata mayun idanunshi da sauri ta saukar da idanunta kasa sanan ta taho ahankali ta ijiye agefen gadon tawuce tafita tana share fuskanta hankalinta na kwanciya ganin baimata fadaba towa ya lullubeta da bargo,shine? Ta tambayi kanta, samin kanta tayi da murmushi ahankali tace "yanada kirki, shikadai ne baitamin ihu ba, saidai bai kallon mutane yanada wulakanci kuma" tawuce tafita tajita garau ta watsake ashe tuntuni bacci ne ke neman kassarata.




Flat dinsu zata shiga guard suka tareta ahankali tace "Aremo sent me to collect his food" budemata kofa sukayi ta shiga, falon babu kowa aciki, saidai uban manya manyan hadaddun kulolin abinci akan dining, rasa mezatayi tayi saitahau ihu tana ."Ma Prince sent me" Dami na falon upstairs taja tsaki, tacigaba da chatting datake tana addu'a Allah yasa kar Mum taji balle ma tafito, yabata yakai kusan 10min yana Ma an aikoni, jin shiru yasa wata zuciyan tace takoma tacemai bataga kowaba wata xuciyarta tace mata tobaga abincin nan akan dinning ba ki deba ki kaimai yace yunwa yakeji, tunanin hakan yasa takarasa wajen dinning dudda gabanta nafaduwa zuciyanta na gayamata kul kul karkiyi, ki koma ki gayamishi bakiga kowaba amman takasa dinning din ta tsaya, tray mai kyau datagani awajen ta dauka ta ijiye, sanan tashiga bude kulolin abinci sunfi kala goma, babban plate tadauka ta debanmai jello rice dake kamshin abincin biki, sanan tadau wani bowl tazuba mai salad tadau cream tasa ta ijiye cream din kenan yafadi akasa karan dayayi yasa Dami ta sauke wayar datake tattabawa jin karan abu a downstairs.




Tsugunnawa tayi ta dauki bottle din ta maida inda yake ta ijiye, sanan tadau wani bowl tazubamai farfesun kan ragon datagani dayake tiriri tsabagen zafinshi, ta ijiye akan tray sanan tadau wani plate ta sakamai plantain da namomi soyayyu sanan ta ijiye shima kan tray, ta maida kulolin tarufe tass, sanan tadauki tray tafito daga dinning tafara tafiya hartakai tsakiyan dakin taji an daka mata tsawa. "You this stupid animal Boy!" Da sauri tajuyo jikinta yadan fara rawa ganin wanan yayan prince dince data radama suna mai masifa ce tanamata wani kallo kaman takama barauniya.



_MBM ENTERPRISE company ne mai zaman kanshi that are into anything computer design, graphics design, sunayin ID card, folder, files, meo, baje, sunayin jotter na biki da sauransu, sunayin customize mug da magic mug, sunayin jacket da riguna signout irin idan kun gama school, sunayin invitation card, sunayin p-caps, sunayin throw pillows da sauran su, sunayin calendar na turenci dana larabci, dakomima har kwalaye sunayi, ko'ina kake zasu maka su aikamaka dashi, suna logo creation, suna customized links, flash da souvenirs na biki na birthday na suna daza'a lika suayenku ajiki, sunayin receipt, gift box na birthday koma na menene, jama'a bari kuji indai design ne da ake amfani da kwamputa ayi to MBM Enterprise kaman sunmiki sun gama, har award sunayi, customize umbrella, key holder banda haka all services dinsu are at a very low discount rate, super affordable, idan zaki tuntubesu zaki samesu awanan number takira 07010439656 , sanan zaki samesu a watsapp ta wanan nUmber 08106788714 kuyi saving ku musu magana ko a watsapp kokuma ku kirasu awaya._
7/1/21, 8:50 PM - My Mtn Number: 💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫


_MASIFAFFIYAR KAUNA_




✍🏾M SHAKUR




EPISODE 2️⃣5️⃣
Jin Boy shiru bai dawoba yasa yadanja gajeren tsaki yace "probably Mum ta tare yaron tanamai masifa ba gaira ba dalili akan maisa banzo naci abincin adakinta ba" ijiye laptop din yayi kawai yatashi yawuce yafita dan yajechan yaci abincin kawai kowa yahuta hakan yasa yatashi yazura takalmi yafita..........





Bakinta harwani rawa yake tana rikeda tray abincin gamgam a hannunta tace "uhmm is Aremo that ask me to bring his food for him Anty" wani irin tafiya Dami takeyi harta karasa saukowa dagakan benen sanan takaraso gabanshi tanamai wani irin kallon kyama da tsana da kazanta sanan ta tsaya tana kallon hannayen yaron wanda bayan hannunshi na dama salad cream yadan taba yabata sanan tanuna hannayenshi tace "you use those your filty, bloody, dirty, irritating poor bushy hands of your kaje dinning kataba kwanukan mu da flask din da banana Sarkin lagos gabaki daya ke zama yaci abinci dashi akuma kai, kai dinan mafi kankantaccen bawa, wulakantaccen bawa mara galihu mara darajamn dan aiki agidan nan kadebi abinci" rawa jikinta yafara ganin fuskan matar ba digin rahama akai tace "Arem.......mo.....asked.......me ....... to...to brin......" bata karasa maganan ba Dami ta dauketa dawani mahaukacin tuzurun mari dayasa taji numfashinta yadauke nayan sakanni sanan takai hannunta tadauki bowl din hot pepper soup dinan dake kan tray sai kan fuskarta daidai an budema Tobi kofa yashigo, wani irin razanannen ihu Fatima tasaki tareda sakin tray dama komi na tray akasa jin saukan farfesu mai shegen zafi da mugun yaji akan fuskarta da idanunta tawani irin daura duka hannayenta akan idanunta tana sosawa tana murzawa tanajin haukan zafi da yaji ko'ina, bamatasan ina kwakwalwanta yakeba, tashiga juyi tana ihu, tana tsalle, tana durza da murzan fuskanta da idanunta tana sambatun azaba da hausa."wayyo Baba, Baba na mutu idona, Baba, na mutu na lalace, la'ilahaillallahu" hartakai stairs tana haukan nan bama tasaniba tuntube tayi da stairs na bakin kofan tai baya zata fadi da sauri Tobi yatareta tafada akirjinshi da idanunshi dasukai mugun jajir yana wani irin kallon Dami dake kallon Fatima ranta abace yay bakin kirin tace "you must be very stupid and animal to think kakai matsayin zuwa dinning dinmu kadebi abinci and ina maka magana instead of you to Apologize kana gayamin Prince ya aikoka sabida bakada kunya baka da tarbiya, yaran talakawa marasa galihu wayanda iyayensu ke biyan bashi dasu" ahankali Tobi yasaketa awajen tsabagen yanda ranshi ke tafarfasa yay cikin falon Dami ta tsaya chak tace "ramama errand boy dinka zakay......." baiyi wata wataba yawani irin kwasheta da lafiyayyen mari, rike fuskanta tayi tai ihu tana kallonshi tace "Tobi nika mara? Ina yayanka, am I not your senior kadaga hannu ka wankamin mari" takai hannunta azuciye zata chakumeshi ta wankamai marin, kafanshi yasa yawani irin tadiyeta jikake gundum tazube akasa takume kanta da kujera, dasauri su Taye suka shiga saukowa sabida hayaniyan dasukaji, amugun zuciya yakai hannunshi kan wandon jikinshi ya kwance belt din wandonshi yawani zaro kaman ya zaro sword, baiyi wata wataba ya shiga dukan Dami kaman wanda yasami tabuwan hankali tun tana daurewa tana zaginshi da turenci dakuma yarensu yoruba, saikuma tashiga kuka sosai tana ihu tana kiran Mamanta da Babanta suzo, Mum dasu Taye sukaje kirane suka fito tare ihu Mum tayi tazo dagudu tana rikeshi. "Tobi, Tobi, Tobi don't kill your sister" ganin bayaji kunnenshi ya taushe kaman kara tunzurashi ma Maman tasui take yashiga hadamata harda kafa da belt yasa Mum tai ihu ku kiramin Babanku guard, Taye call your father, aguje akaje kiran mai Martaba ko minti daya basuyiba, saiga Oba yashigo da Fatima yafaracin karo dayaga fukanta yay jajir tana kuka sosai, tana sosa fuskanta sanan ya kalli ciki yanda Mumy kejan Tobi dayake dukan Dami amman bai denaba, dawani irin sauri Baban yashiga cikin dakin akaro na farko Baban yadakamai tsawa. "OluwaTobi" da sauri Mum itama jin muryan Babansu yasa tace "yes Honey come and see your son zai kashemin yarinya" tana maganan ta shiga gaban Tobi ta zauna kusada Dami dake kuka sosai tana ihu tana yayakuri tarike Dami tace "daka dani shikenan kahada dani Tobi saikafijin dadi, harda hardani uwarka dana haifoka nakawoka duniyan nan kaji Tobi bai bakin zuciya kaji dadi" cikin wani mugun zuciya yasakake kai bulalan yana wani irin kallon Mum yace "Mum stand up, wlh yau sainaji mata ciwo, not just her all of them" yanuna su Taye dasukai tsuru tsuru suna bayan Babansu a tsaye, cikin wani irin zuciya yace "Mum I said stand up and get away from here" da sauri Mum tace "nabaka hakuri Son bakaji basaika hada dani kadaka ba kaji dadi da kyau" ta rungume Dami dake kuka sosai, hannu yakai zai fisgo Damin daga jikinta tai wani irin uban ihu tana shigewa jikin Mum tace "Tobi sorry" tsawa Dad yadakamai. "Tobi I am right here standing still kanason kacigaba da dukanta" juyowa Tobi yayi yanunama Dad tray abinci da bowl din pepper soup da namukan dake kasa cikin wani irin azababben zuciya yace "Dad i sent that boy yakawomin abincin because I was damn hungry sabida he didn't see anybody yaje yadebomin abincin shine Dami slapped him ta kwaramai hot pepper soup a face, look at the poor little boy, is that fair"? Yanuna ma Dad Fatima dahar lokacin wani irin kuka take tana dirze idanunta kaman mahaukaciya dasukai jajazir tana ihu Dad ya juya ya kalli yaron, Tobi yace "wayataba mata haka ita tunda take girma har yau? Sabida yan aikine their parents are not here saisa take ganin zata iya wulakantasu? What kind of inhumane attitude ne wanan pepper soup a face if she ruins the small boys eyes fa? And kuna expecting tayi such act na kyaleta sabida she's a princess is this what this palace is all about? Dad i can't stand for injustice, and I swear am not done with you, if anything happens to this boys eyes I swear Dami you will regret having me as your brother" yana maganan ya yarda belt din atsakiyan dakin yazo inda yabarta daukanta yayi chak azuciye yafice, ta mugun tsorata jin an dagata amman idanunta suke gabanta.


Fashewa da kuka Mum tayi ta kalli Oba tace "bazaka dingama danka fadaba akan dan aiki zai kashe sister shi dasuka fito ciki daya" cikin mugun fada Oba yace "kimin shiru anan wajen, kinsan gidan nan, babu bawan ko maaikacin damuke zalinta saisai sunan sarki mai adalci yabini, pepper soup, hot pepper soup a fuskan yaro karami yarki ta watsa and u are still blaming Tobi daya zaneta, wlh yamin daidai kawai nakira sunanshi ne sabida karya kasheta" ya kalli Dami dake kuka sosai jikinta yay rudu rudu yace "bakiga komiba tukunna kiyi addu'a kar wani abu yasami yaron nan dan wlh nima saina miki nawa" ya kalli mamansu yace "kuma ko kwabo na karki dauka kice zaki siyamata magani nagayamiki" yafice daga dakin fuuuu cikin fushi guards dinshi biyedashi, da sauri sauran sisters dinta sukazo kanta, Taye tace "haba Dami you went tooo far, bakida imani ne me dan karamin yaron nan yamiki dazaki watsamai pepper soup a fuska ga yaji ga zafi, idan ya makance fa eh? Mezakice ma Allah? Da Tobi kuke yar jealousy ki this boy knew nothing about it he is just a worker yaushe yazo gidan duka duka, idan danki akamawa haka zakiji dadi"? Cikin kuka sosai Mum tana duba jikinta tace "Dami bataji, bakiji yarnan, narasa yanda zanyi da ita eh, menene matsalanki da Tobi, menene? Me yakai dukga wayannan abubuwan, keda yanzu yakamata kina tunanin aure kishi kike da kanninki keda ba'a gidan nan zaki zauna ba dole kije gidan mijinki, Dami jibi yanda jikinki yay shaidan bulala eh, akanme, zakija Tobi ya kashemin ke a banza a wofi, xaki hada karfin kine da namiji ke mecece? Barinma wanan dakikagan shi kaman basamude jiki dukya daddaure" kallon su Taye tayi cikeda takaici tana share hawayenta tace "ku kaita ciki ku gasamata jiki da ruwan zafi lemme call my Dr tunda ubanku yace bada kudinshi ba ina naga bakin kiran family Dr mu" daukanta sukayi sukai sama da ita Mum tabuga tagumi tana kallon yanda pepper soup da duka abincin ya watse a falon tace "yanzu abinci da Tobi baiciba kenan, kai Allah kadubeni da yaran nan, wanan irin jarabta akan yaran nan biyu, keata keata goshi da keyan Tobi da Dami baya haduwa kai" guards ta jwalama kira suzo su gyara dakin sanan tawuce sama tana kiran Dr a waya.




_MBM ENTERPRISE company ne mai zaman kanshi that are into anything computer design, graphics design, sunayin ID card, folder, files, meo, baje, sunayin jotter na biki da sauransu, sunayin customize mug da magic mug, sunayin jacket da riguna signout irin idan kun gama school, sunayin invitation card, sunayin p-caps, sunayin throw pillows da sauran su, sunayin calendar na turenci dana larabci, dakomima har kwalaye sunayi, ko'ina kake zasu maka su aikamaka dashi, suna logo creation, suna customized links, flash da souvenirs na biki na birthday na suna daza'a lika suayenku ajiki, sunayin receipt, gift box na birthday koma na menene, jama'a bari kuji indai design ne da ake amfani da kwamputa ayi to MBM Enterprise kaman sunmiki sun gama, har award sunayi, customize umbrella, key holder banda haka all services dinsu are at a very low discount rate, super affordable, idan zaki tuntubesu zaki samesu awanan number takira 07010439656 , sanan zaki samesu a watsapp ta wanan nUmber 08106788714 kuyi saving ku musu magana ko a watsapp kokuma ku kirasu awaya._
7/1/21, 8:50 PM - My Mtn Number: 💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫



_MASIFAFFIYAR KAUNA_




✍🏾M SHAKUR



EPISODE 2️⃣7️⃣ & 2️⃣8️⃣
Wanka yayi ya chanza kaya yafito daga ciki, tundaga stairs yake kallonta ganin yanda rigan jikinta yabaci da da pepper soup din tana zaune a inda yabarta tabude idanun da ayanzu sun dena mata zafin saidai kawai yana yana kaman cobweb dasukasa idanun sukai mata wani irin, tunda taji tafiyarshi tadago kanta ta kalli ta saitin datakejin tafiyan shi, kan kujeran datake zaune yasami gu a gefe yazauna ahankali yace "you are hungry right, you haven't eaten" kasa amsashi tayi ta saukar da kanta kasa ahankali hadadden kamshin dayakeyi na ratsa hancinshi, doorbell dayay kara alamun an danna yasa ya kalli kofan yabada izinin ashigo, wasu guards suka shigo da warmers da plate hadaddun gaske aka kawo wajen, ijiye abinci akayi agabansu, yasa suka zubamai sanan yasa suka zubama Boy, ya karbi nata yadaura mata a hannu yace "eat" sanan yabasu izini dasu fita.


Lafiyayyen farin rice ne da stew dayaji namomi zako zako, spoon din tadauka tadebi first spoon of rice din takai bakinta da kyar tahadiye saikuma tahau bude baki tana hura iska tana kokarin danne yajin but ina takasa, yajin is something else da sauri ya kalleta yanda takeyi yas yace "is it pepprish?" Gyadamai kai tayi da sauri idanunta natara ruwa again sabida tsabagen yaji, ruwa yadauka yabude yabata takarba tareda kafawa abaki da sauri tana kwalkwala, sakin baki yayi ya tsaya yana kallonta ganin tana neman shanye ruwan goran sanan ta ijiye, da spoon din yaga rana ture stew din saman abincin gefe sanan tafaracin rice din hakanan tanayi tana shan ruwa hartadanci sosai sanan ta ijye shikuma har lokacin yanacin nashi ahankali yana kallon ball abinci dan in dasabo yasaba cin abinci dayaji tunda aka haifeshi.


Saida yaji ankira la'asar sanan yakawo glass din yabide yakama hannunta yabata yace "saka muga" sakawa tayi ahankali ta kalleshi, ga mamakinta saitaga tana ganinshi amman kadan ba clear ba yafi babu da dazu bata gani ko kadan, da sauri yace "can you see me" gyadamai kai tayi tace "yes but small" ajiyan zuciya yayi da saida taji karanta yazauna kusada ita looking so relieved, ahankali tace "sir I want to go to my room and shower nacire kayan nan" da sauri ya kwalama guard kira, na bakin kofanshi ne suka shigo yace "sukai yaron dakinshi" tafiya dashi sukayi yabisu da kallo sanan yawuce sama yaje yay alwala yay zuhur da asir sanan yakoma ya kwanta sai bacci.


Itama wanka tayi tsaf sanan tadawo dakinta ta kulle tai salla tadade akan dadduma tana addu'an Allah ya tsareta yakareta sanan yabama Baba kudi yazo yacireta tagaji da gidanan nan yautaga azaba iya azaba, tagama tasake tofe kanta da addu'a sanan ta tashi tabude kofa takoma ta kwanta bata koma dakinba kuma bai aiko akirata ba saidai ya aikomata da magungunan ta sanan da biscuits da chocolate din dayasainata.



**************
WASHEGARI!!
Wuraren karfe shidda wani bakin mutumi dake sanye da farin zani kaman yadin likafani yadaurashi yamaidashi kaman wando da riga saidai shoulder shi daya abude da akai wasu irin zane da farin fenti ketahowa cikin fadan yana tafiya yana buga wata sandar hannunshi na karfe, kunenshi na sanye da wasu irin dankunnaye na cowries, hakama hannayenshi yay warwaro da cowries din, kafafunshi ma haka, sanan sandar karfen dayake rikeda shi duk cowries dinne akai dakesa abin yana kara idan yana tafiya yana kara, tundaga nesa duk guard din palace din dazai ganshi zubewa suke suna kwasan gaisuwa yay hanyar fada, da sauri fadawan dake tsare gaban fadan suka budemai kofa ya shiga ciki ya zauna a tsakiyan fadan akasa, fadawan suka shigo suka zube dan gaidashi, cikin harshen yarensu yace "akiramin Oba dakuma Otun yanzun nan" davmsauri fadawan sukace angama, wasu suka fita sukai cikin gida wasu kuma suka fita dan zuwa kiran Waziri agidanshi da baida nisa sosai da nasu.


Waziri yafara isowa wuraren bakwai, saiga Sarki dan saida ya tsaya yay wanka sanan yazo ya shigo falon da Waziri ke zaune kan kujeranshi shikuma mutumin har lokacin yana kasa bai zauna akan daya daga cikin kujerun dake fadanba, Mai Martaba yashigo yakarasa kan kujeranshi ya zauna Otun na gaidashi, sanan Waziri yabada izini guards su fita suka fice aka rufo musu kofa yarage su kadaine afalon.


Anatse cikeda girmamawa Waziri ya kalli mutumin cikin yanayi na tashin hankali yace "Ooluwo (Chief priest) meya kawoka fada da sassafe haka? Kamana aike muzo lpy"? Shiru mutumin daya kirada Ooluwo yayi wato bokan gidan sarautan Chief priest kenan, saikuma yarufe idanuwanshi yana wasu irin surkulle da basaji sunadai ganin bakinshi na motsi sanan yabude idanunshi ya kalli Oba da Otun yace "banson natada ma jama'an wanan fadan hankali ne saisa dakai da Mai Martaba kadai nakira" sanan yasakeyin shiru kafin ya shiga Koro bayani.
"Iya sanina tun zamanin forefathers din wanan gidan sarautan, tun lokacin kakana na uku, wanda ya taka matsayin Chief priest din wanan fadan daya buge duk wani boka maiji dakanshi a Nigeria da kewaye gabaki daya, boka mai amana wanda yay rayuwanshi yagama yana serving kakanninka" yanuna Oba sanan yace "dukanku nan kunsan prophecy da kakana na uku yagani tun a zamanin, annunamai cewa duk randa wanan gidan sarautan zai dauki y'a mace a matsayin yar aiki agidan nan, wanan gidan sarautan, inhar mace zata saka kafarta ta shigo gidanan da sunan aiki to destiny gidan sarautan nan zai chanza gabaki daya, tun awanan zamanin kakana na uku awanan lokacin yasa aka dena dauka masu aiki mata daga ranan dayaga wahayin har zuwa rana irintayau da nasan ko mace daya babu agidan nan da sunan aiki, baku dauka mata amatsayin mai muku aiki kwata kwata" anatse Otun dat was looking confuse yace "kuma tundaga lokacin, har aka nada abokina Sarkina a matsayin sarki har rana irin tayau bamu dauki mace a matsayin yar aiki ba tunda abune damukaga tun iyayemu basuyi ba balle mu, wanan ai rule ne ma nagidan sarautan nan datake ashimfide, tundaga kan fadawa, guards, cooks, masu shara, gardeners, securities, masu wanke wanke dakomima daka sani na wanan gidan maza muke dauka, hatta nani masu mana rainon yaran mu tun suna yara maza ne, certified maza dasukai karatu kan zama nani, Bokanmu hatta gidana babu dan aiki kodaya mace balle ma gidan sarautan nan gabaki daya, meke faruwane? Meke shirin faruwane tsoro yacikamana zukatan mu dagani har Sarkina, ataimaka awarware mana zaren" wasu yan maganganu bokan yafadi dabasu gane meyake nufiba, sanan yay kaman ya sallame salla saikuma yajuyo ya kallesu yace "jiya naga vision da daddare" duk kallonshi suke yay shiru, sanan ya sauke yar ijiyan zuciya yace "naga vision cewa wani gagarumin abu na gabda faruwa awanan gidan, masarautan nan dazai chanza destiny gidan nan gabaki daya, makiyanka da makiyan gidan sarautan nan zasu maka dariya, zasu maka dariya zaka dawo abin magana awanan, gidan sarautan nan zai shiga bakin koya zakubi Nigeria gabaki daya, babu abinda banyi ba anki warwaremin vision din nakasa gane takamaimen menene zai farun"? Kana ganin idanun Oba da Otun kasan suna cikin damuwa sunma kasa magana, hakan yasa yadaga musu hannu yace "ku kwantar da hankalinku" Cowries din wuyanshi ya cire ya yar atsakiyan dakin yay wasu maganganu tareda taba tsakiyan sarkan yace "nunamin komi ke madubin tsafi" gani sukayi tsakiyan cowries din yakoma kaman madubi saidai tsakiyan yay bakin kirin basa iya ganin komi ciki, Chief Priest ya kallesu yace "tun jiya abinda yake nunamini kenan, wanan abun babba ne, babban gaske, babu wanda bazai girgiza ba koma menene abin ba, yan adawan masarautan nan na wasu gari da baku zaman lafiya dasu zasu muku dariya akai, kun tabbatar babu mace agidan nan sabida insan ko sabida macen nan wahayin kakana na uku ke shirin tabbata"? Da sauri Otun yace "har abada babu mace agidan nan, mata bamasa neman aiki agidan nan sabifa sunsan bazamu basu ba sunsan bama abayarwa, duka factories dinmu, companies, gonaki, gidan kaji gidan kifi da duk wasu kafofin kasuwanci damukeda shi a lagos dinan kaf da kewaye maza ne ma'aikatan mu, hatta lawyers dinmu maza ne, likitocin mu mazane, masu mana wanki maza ne, yanayin rayuwan muma babu mata ciki banda yaran da muka haifa mata tota ina mata zasuzo"? Jinjina kai Chief priest yayi cikeda gamsuwa da bayanin Otu yace "yace na yarda dakai, daman nasake tambaya ne dan insake tabbatarwa idan ma akwai sharadin biyune wanda Kakana na uku yafadi a lokacin, aka kama macen koku kasheta ya zamto batada rai gabaki daya hakan zaisa kaddaran yaki faruwa dan wacce kaddaran zata faru ta sanariyarta ta mutu kokuma ku kaita nesa chan nesa da wanan masarautan tayanda bazata taba iya dawowa gidan masarautan nanba har abada! yanzu inaso zaku siyo bakin akuya guda bakwai, ayayyanka atafasa naman aci batare da an soyaba, zanje nacigaba da duba koyaya ake ciki kubani nanda kwana bakwai zanyi communicating the Gods of the night" yatashi yafice batare dayajira cewansu ba.






Kallonshi Oba yayi hakama Otun kallonshi yayi, Otun yace "tayayama zasu dauki mace a matsayin yar aiki wanan ba abu mai faruwa bane bama har abada, so bashi alayi bamashi cikin layine ko kadan, ka hararo wani abin mekake tunani"? Dan jimm sarki yayi saikuma ya kalli Otun shima cikeda shirin damuwa yace "abu daya na hango OluwaTobi"

Please Login or Register in order to submit comment