Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Mum" kujeran dake wajen ta dauko ta ijiye kusadashi ta zauna tareda dafa kafadarshi ahankali tace "OluwaTobi kayakuri kaji, I am still begging you nasan bamu kyauta maka ba but look at this from our perspective okay, we are doing everything to protect you My Love" taidan jim ganin ko kallonta bayayi aikinshi yakeyi abinshi yasa tace "guess what I come to tell you that an kada securities dinan sun tafi, my son is now free, u can go duk inda zaka kaji OluwaTobi" tunda tafara maganan ya tsaida zanen dayakeyi saida tagama tass sanan yajuyo ya kalleta irin juyowan nan na neman assurance, gyadamai kai tayi hakan yasa yadan saki murmushi, rungumoshi jikinta tayi sosai tace "I love you Son sosai, I will do anything in my power to give you wat you want kaji" gyadamata kai yayi ahankali tareda sakin murmushi kadan, tace "nakira Ayoka tazo kufita tare" batarai yayi yace "no" shiru tayi kaman tana kokarin tuno wani abu saikuma ahankali tace "Tobi kaga irin maganganun dana fadama yarinyar nan kuwa ranan kafin tahakura, I told her to calm down tagama service tukunna kafinma tafara maganan wani soyayya dakai" tabe baki yayi yace "Mum I am not interested in Ayoka period, I took her as a sister, and now data kaucema layi I don't even want her close to me ban iya yaudara ba, ban iya raising hope na mace up ba" ajiyan zuciya Mum ta sauke sai kawai ta tashi dukowa tayi ta manna mai kiss a kumatu tace "I love you son" ahankali yace "love you too Mum" wucewa tayi tafita shikuma ahankali yasaki murmushi sai kawai ya cillar da brush din yatashi dagakan kujeran yawuce sama wanka yayi yashiga closet dinshi ya shirya tsaf yana mamakin ya akayi boy baizo aiki ba yau, ko ansashi wani abune, jeans da riga yasaka na gucci masu color brown and white, yadauki p-cap yasa white yasa, slippers din maza ya saka na Prada white shima ya daura agogon hublot a hannunshi sanan yabude wani drawer a closet dinshi dake dauke da keys din motoci kusan 12, key wata hot range rover yadauka da wallet dinshi yafito yana baza uban kamshi, Taye da fitowanta kenan tana sanye da jeans da riga masu kyau tai murmushi tace "we are officially free" hararanta yayi, da sauri tace "Tobi please go with me am bored" hararanta yasake yi, cikeda lallashi tace "please nowwww munfa shirya fa, am sorry for everything kaji little brother" motarshi da kullum sai awanke yayi fara kal, yabude batare daya kalli su guards din dake kokarin budemai ba yatada motar kana ganinshi kaga dan mai kudi asalin definition of yoruba demon ajebota, jan motan yayi da hannu daya dayan hannu kuma yana saka dark shade yaja motan yafice batare daya kalli su Dad dake gaban fada atsaitsaye ba babanshi yabishi da kallo yana addu'a.


Wani babban saloon yaje akamai gyaran fuska aka gyaramai gashin kanshi aka mai wani sabon style bobmarley dayama bakar fuskanshi masifar kyau, sanan yafito yatafi wani beauty spa skin 101 all this are abubuwa da he can order azo amai agida but shi yafiso yaje komi yayi da kanshi.



Facials akamai hadaden gaske, face treatment, akamai lip therapy, lips dinshi suka kara so pinkish dakuma taushi, sanan akamai pedicure da manicure kumbanshi sukai kyau sukai haske, saiyay topping komi with a deep tissue massage dakuma sound deep sleep na two hours!!! That's how the rich roll fa, Allah kamana arziki.


Saida ya farka sanan ya shiga bathroom yay hot bath yanajin dadin jikinshi sosai sanan yasaka kayanshi yafito yatafi sai godiya sukemai, awani masallaci ya tsaya yay alwala yay sallan azahar da la'asar wuraren biyar na yamma saikuma ya shiga mota wani boutique yagani dayaga an rubuta the Teens hakanan yaji Boy yafadomai arai hakan yasa ya gangara yay parking ya shiga, hadaddun kuya masu kyau yasiyama yaron dahar cikin ranshi yakeso, yaron nada hankali even at his young age, and he always takes care of him, yasaimai takalma da sneakers masu tsada yafito aka samai komi a mota sanan yatafi stadium zaije kallon kwallo, saida ya tsaya a hanya awani masallaci yay alwala ya shiga jam'i sukai sallan magrib sanan yafito ya shiga motarshi yahau kan titi, yana tafiya ya hango wani mutum yana sanye da suit da wasu textbooks manya guda biyu a hannunshi, saikuma jaka abayanshi daya rataya yana kokarin tsallaka titi, from no where saiga wasu thugs guda uku lagos boys sunzo sun bangajeshi sun fizge jakan harda textbooks dinma yafadi akasa dan kokadan bai ankara dasu ba, da sauri Tobi ya gangara yay parking a gefe sanan yasauko daga motar yataho da sauri yadagashi ahankali yace "sorry" ahankali yatashi yana gyaran white glasses din idanunshi ya kalli Tobi yasaki murmushi yace "thank you" tareda waigawa yana kallon hanya ganin ko alamunsu baigani ba, ahankali Tobi yace "do you need your things back"? Da sauri ya kalli Tobi yace "yes please all my whole career is in that bag pack, I came to lagos for now exam dazanyi for one week gobe zamu fara niba dan nan bane" yamai magana shima da turenci, Tobi ya kalleshi daga sama har kasa he looks damn neat amman kallo daya yamai yasan badan garin nan bane yace "can you fight" da sauri guy din yace "fight"? Dan ware manyan idanunshi Tobi yayi yace "don't you want your things back"? Da sauri yace "oh I want" ahankali Tobi kaman wanda baison yin magana yace "then gather your strength and techniques dinka na kaucema harin wuka, let's go" Tobi yay hanyar motarshi bin Tobi yayi da kallo danjim yayi baisan mesaba saikuma yaji he trust d guy hakan yasa yabishi ya shiga gaban da Tobi yabude mai ya zauna tareda rufo kofan Tobi kuma ya kunna motan yana murmushi, da sauri mutumin dake kallonshi yace "kasan inda sukene"? Kallo daya Tobi yamai ya dauke kai yace "I was born in lagos anan nan girma, I told you kawai shirya, zamuyi mini wrestling yanzun nan" yaja motar dawani irin gudu dayasa da sauri mutumin yaja seat belt ya daura. Wani anguwa yaga sun shiga da local street ghetto Boys suka cika ko'ina, parking sukayi agaban wani uncompleted building sanan Tobi ya kalleshi yace "ready"? Gyadamai mai kai yayi, hakan yasa Tobi yabude motan ya sauka shima ya sauko suka shiga cikin gidan atare, daidai sun tarar dawasu gang da sunkai su kusan 25 yara haka dabazasu wuce 20 zuwa 25yrs ba, ga jakan shi dakomi a jakan akasa sun zaxzage, ga kudi ga textbooks dinshi da credentials, suna ganin su Tobi duk suka mike tsaye suka cicciro wukake da sauri mutumin ya shige bayan Tobi dan kallonshi Tobi yayi yay murmushi sanan ya kalli wanda yaga shine Ogan su danshi ke rikeda laptop din yace "Hey Bro we came for that bagpack and everything naciki, kindly give it back ba fada mukazo ba ko hayaniya" tashi Ogan yayi cikin harshen yarbanci yace "kaci haukace ko bakason ranka ne dakazo nan inda bazaku fita rayeba" dan murmushi Tobi yayi yana jujjuya wuyanshi irin yana shirin fadan nan da turenci yace "I think you are the one that wants to die dakuka mana sata" da sauri Ogan ya kalli yaran yace "kukai mazan nan lahira" hannun riga Tobi ya tattare yace "get ready my man and now the fun begins" yay maganan daidai yaran sun taho kasu da wukake hakan yasa dayan mutumin ya manne bayanshi dana Tobi sosai jikinshi na rawa baisaba ganin wuka haka ba koyan daba, kwashe su Tobi ya shiga yi da nushi daya yana protecting mutumin dayaga baida karfi a tsorace yake yace "Hy Man be attacking bayan kunnensu ko balls dinsu" jin haka yasa wanda yakawo mai wuka zai chakamai ya kauce da sauri yawani irin tsugunna yakaimai naushi mai kyau a gwailo yaron ya zube agefen Tobi, washe baki Tobi yayi kaman yanda shima mutumin ya washe baki yana kallonshi Tobi yace "that's a beautiful hit my man" daidai nan yaga wani yaro yataho da wuka zai lumama mutumin dawani irin sauri yasa hannu ya fizgo mutumin bayanshi sanan yay wani irin tsalle ya daki habar yaron da takalmin shi yaron ya zube akasa, cikin minti dabasufi goma ba suka barar da yaran dukansu akasa harda Ogan wanda yawanci Tobi ne yay aikin, sanan Tobi ya kashe komi nashi yakawo mai yabashi inda yake tsaye yana kallon yaran dake ihu akasa, daidai lokacin wasu gang din suka shigo ciki wani kallo Tobi yama mutumin sanan da idanu yamai alamu now is time to run sanan suka arce aguje gang din na binsu, saida sukai zagaye dasu awajen sanan suka fice Tobi yabude mota dagudu shima mutumin ya zagaya ya shige daidai gang din sun fito Tobi yaja motar da gudu suka biyosu suna jifa Tobi yahau dariya sosai dariyan dabaitaba yin irinshi ba yanaganin shima haka mutumin sukahau dariya harda tafi suna waigen yanda Gang din har lokacin ke binsu suna gudu har suka musu nisa sosai sanan suka tsaya, su Tobi na kallonsu ta glass din gefen mota suna dariya, mutumin yace "ohh that was fun" gyadakai Tobi yayi yana murmushi yana tuki yace "I told yhaaa" saikuma ya yatsine fuska tareda cije lips sosai da sauri mutumin ya kalleshi ta gefen cikinshi ne yaga jini ta farin rigan jikinshi hakan yasa da sauri yace "stop the car" dan kallonshi Tobi yayi yana tukin. "stop the car" yafada sounding serious hakan yasa Tobi ya gangara gefen hanya yay parking yakeshe motan yace "what you are not expecting me to drop u a middle of road haka azo wanan karan gabaki dayama adaukeka" riganshi yaga mutumin yadaga hakan yasa ya kalleshi saikuma ya kalli abinda yake kallo, ashe zafin dayaji dazu na yanka ne, an yankeshi agefen ciki yana jini sosai, da sauri mutumin ya daura hannunshi akan wajen ajiyan zuciya yayi yace "thank God is not a deep cut" saikuma yasaka hannunshi a aljihu yaciro wani clean handky mai kyau fari yadaura awajen yace "put your hand on it will stop the bleeding give me the key, lemme drive" kallonshi Tobi yayi hakan yasa ahankali yace "please you helped me so lemme help u too" bashi key yayi sanan yasauko ya xaga shima ya zaga suka shima, mutimin yaja motan, yatsine fuska Tobi yayi dan sai yanzu yafarajin zafi saidai ajiyan zuciya kawai yake yana lumshe ido, hakan yasa mutumin yakara gudu, agaban wani pharmacy ya tsaya ya kashe motan yafito da sauri ya shiga ciki abubuwa ya siyo dayawa sanan yafito yazo ta side din da Tobi yake xaune ya kunna wutar motan yace "I am so sorry" sanan yadaga riganshi yadau auduga da spirit yashiga wanke wajen yatsine fuska Tobi yayi kaman xaiyi kuka hakan yasa mutumin yace "sorry" saida yagama gyaramai sanan yasamai bandeji, saikuma Tobi yaga yana zuko allura a syringe da sauri Tobi yakoma baya yace "you are not putting that in me right" murmushi yayi yace "don't tell me ka iya fada but kana tsoron allura" dan murmushi Tobi yayi yana kokarin ya basar amman yama kasa magana hakan yasa ahankali mutumin yace "please kabari namaka a hannu zanma, na tetanus ne, kaga da wuka aka yankaka we need to do this, please friend" friend daya fadi yasada sauri Tobi ya kalleshi gyadamai kai yayi hakan yasa ahankali yamikamai hannun, alluran yamai ahankali saikuma yaciro ya kalli Tobi daya kulle ido yace "done" bude ido Tobi yayi ya kalleshi ganin da gaske sun gama, sanan yabashi magunguna yace "take this idan kakai gida, muje yanzu kamin kwataccen gidanku" yakoma wajen tuki, ahankali Tobi yace "I can drive u don't have to do this" da sauri yace "oh yes I have too, at least that's the least I can do for the man that saved my life" shiru Tobi yayi yaja motar suka shiga hanya sanan ahankali mutumin yace "I am a Dr, I came for wani exam ne, I am hausa from kano, my name is Imam" dan murmushi Tobi yayi ahankali yace "nice name Dr" saikuma ahankali yace "inada two degrees nayi art, sanan kuma na karanci accounting, i am OluwaTobi Tajudeen, yoruba born and brought up here at lag" murmushi Dr Imam yayi yace "you are really a nice guy Tobi thank u".




_MBM ENTERPRISE company ne mai zaman kanshi that are into anything computer design, graphics design, sunayin ID card, folder, files, meo, baje, sunayin jotter na biki da sauransu, sunayin customize mug da magic mug, sunayin jacket da riguna signout irin idan kun gama school, sunayin invitation card, sunayin p-caps, sunayin throw pillows da sauran su, sunayin calendar na turenci dana larabci, dakomima har kwalaye sunayi, ko'ina kake zasu maka su aikamaka dashi, suna logo creation, suna customized links, flash da souvenirs na biki na birthday na suna daza'a lika suayenku ajiki, sunayin receipt, gift box na birthday koma na menene, jama'a bari kuji indai design ne da ake amfani da kwamputa ayi to MBM Enterprise kaman sunmiki sun gama, har award sunayi, customize umbrella, key holder banda haka all services dinsu are at a very low discount rate, super affordable, idan zaki tuntubesu zaki samesu awanan number takira 07010439656 , sanan zaki samesu a watsapp ta wanan number 08106788714 kuyi saving ku musu magana ko a watsapp kokuma ku kirasu awaya._
[25/06, 09:02] My Airtel2: 💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫



_MASIFAFFIYAR KAUNA_



✍🏾M SHAKUR


EPISODE 3️⃣2️⃣


Gyadamai kai kawai yayi batare dayace komi ba, yana tuki amman yana lura dashi zafi yakeji amman baison yanuna hakan yasa idanunshi nakan hanya yace "dazaran kaje gida kasha maganin nan within an hour zaka nemi zafin karasa, nan da 2 zuwa 3days zai warke, next time don't get into fight again I know it was fun" dan lumshe ido yayi yabude saikuma ahankali yace "I've heard" wayanshi ne yashiga ringing dake in between sit din gaban atare suka kalli wayan dan shima yazaci tashice dan ringing tone na iPhone ne ganin Dad dinshi ke kiranshi yasa yadanja tsaki yadaue kanshi daga kallon wayan, harta katse another kiran yashigo Mum, itama ta katse bai daukaba, saikuma Dad yasake kiranshi ganin baida niyyan dauka yasa ahankali yace "please pick up sunga dare yayi basu ganka bane" mika hannu yayi yadauki wayan daidai ta katse saiga wani kirin kuma yana shigowa hakan yasa yakai wayan kunne yace "Dad what" jim yayi yana sauraron Babannashi saikuma adan kubure yace "am on my way back home already" sanan ya katse wayan ya jefar yana maida kanshi jikin kujera yacigaba da nunamai inda zai bi har sukazo ta wajejen anguwansu amman ba'a kai layinsu ba sanan yace "dan gangara gefe kai parking" ahankali yace "but ai nan kan hanya ne" "don't worry am close to gida I can manage" gyadamai kai yayi Tobi yace "lemme call Uber yazo yadaukeka dan ana ganinka ansan you don't belong to the street of Lagos this ghetto Boys will rob u" yana maganan yana shiga app din yakira uber within 5min duk suna zaune acikin motan ya lumshe ido uber direba ya kira bude kofa yayi zai fita da sauri Dr Imam yace "no" dan murmushi yayi yace "i can manage" fitowa yayi yanama uber direba waving hannu hakan yasa yakaraso shima fitowa Dr Imam yayi, uber direban nazuwa Tobi yaciro kudi about 10k yabama uber direban yace "take my man to his hotel, idan y sauka just call me i will end the ride" sanan yadago yajuyo yana cizan baki, hannu Imam yabashi yace "I really appreciate this" gyadamai kai Tobi yayi, ahankali Dr Imam yace "please take care" I will yace sanan yajuya yashiga mota shima Dr Imam yashiga motanshi yanabin Tobi da kallo he's one the the nicest person yahadu dashi a lagos, jan motan Tobi yayi yamike sukuma suka juya suka fita daga layin.


Gidansu yashiga yana addu'a Allah karya hadu da iyayenshi sukaga riganshi da jini ai saisun sunyi panicking halama akara hanashi fita, saida yay parking yaga basa tsakar gida sanan yabude motan yafito, da sauri guards sukazo kafinma su iso yace "nobody should come here dissmiss" bacemai sukayi, sanan yabude boot ya kwaso abinda yasayo ma Boy, da ledojin yay amfani ya kare inda jinin yabata ariganshi yawuce flat dinshi yana bude kofa ya shiga yaga babanshi azaune akan kujera faduwa gabanshi yayi yawani batarai tareda saka leda yasake rufe wajen da kyau, Dad yajuyo yana binshi da kallo yace "iyye I can see anyi aski an chanza style, your face looks very fresh kaje spa ne" dauke kai yayi yace "uhn" sanan Dad yay murmushi yace "dakace kanaso damun kirasu home service suzo sumaka" shiru yayi yana tsaye inda yake baice kalaba Dad dake kallonshi yace "you look very dirty Tobi kaman wanda yaje yay dambe jibi kayanka" yanuna kayanshi da duk yabaci da kasa hakan yasa yace "are you investigating me newai Dad"? Da sauri Baban yace "no Son, just saying it ne sabida naga kai datti" tabe baki yayi yace "i played ball ne" gyadamai kai Baban yayi yace "i see meka sawo a ledojin nan" yanuna ledojin hanunshi, sake rungume ledojin yayi yace "is not mine, I actually got some clothes for Boy, sai gobe zan bashi" sosai Babanshi yay murmushi yace "Tobi u really like that boy, dats the first gift dana taba baka naga kanaso sosai" wucewa yayi yay stairs da sauri yace "i am sleepy when u are done ka kashe tv" binshi da kallo yayi yace "but Son i actually come muyi kallon match tare" "not interested Dad, gud night" night babanshi yace ahankali yana kallonshi, shiga dakinshi yayi yamaida kofan yarufe ya danna key da sauri yana cije lips yanabin dakin da kallo ganin Boy bai gyaraba kaman ma baima zobane kwata kwata ba yau.


Wanka yashiga yayi da hot water sanan yafito ya chanza wasu kayan zuwa pj, yarike magungunan shi yay dinning abincin daya gani wajen yabude yadan tsakuri amalan kadan dan bayawani so kuma yasan da gangan Mum takawomai tanason yay kibane yaci sanan yasha magungunan yatsiyaya juice a glass cup yadawo falo ya zauna yana kallon tashan news din dake aiki wanda ta tabbatar Dad ne yasaka danshi he hardly watch news, yana sipping din juice din yana chanza channel hakanan yake mamakin maiya hana boy zuwa yau aiki, but deep down yasan it will be something daya hanashi zuwa, dan tabe baki yayi sanan yay murmushi tuna irin fadan dayayi dazu, ba yana gayama su Dad yanada karfi basa yardaba just look at the gang he took down shi kadai dan dat Dr babu wani abun arziki daya tabuka. Sai wajajen one sanan ya kashe komi yawuce sama yafada gado sai bacci.


**
Awajen Boy wato Fatima tun jiya ta tashi dawani azababben ciwon mara, ciwon baya cikin kafa da ciwon kirji hakan yasa ta kulle kanta tacire komi ta ijiye dan yanda nononta ke ciwo da kirjinta yasa taji kaman ma zazzabi zazzabi take, nonuwan sunyi jajajir, sunyi wasu kala kaman kumburi kumburi sunyi mata wani irin strange tauri kaman wani maruru maruru tsabagen yanda take dauresu take nanesu, sunmata nauyi sosai idan zata mike tsaye wani zubin saita daura hannu tarikesu sabida ciwon dasuke mata kaman zasu tsage, abinda tsoro yasoma bata karya zaman mata wani babban ciwo danhar zugi suke mata kaman maruru kokuma wani dan kankare, toba doleba sumata ciwo duk uban cikan nononta danko kadan batada kananun nonuwa, boobs dinta are rounded full kaman kwallo, sumcious nd perky, white boobs gareta, ba irin wanan wasu girman haukan nanba, manya ne but daidai masu kan tasa, yanda take matsesu da silki yasa sukai tauri suke mata zugi sukai ja. Allah ne yarufa mata asiri head Guard baizo tashintaba jiya kaman yana wani aiki, dasafe taji muryanshi amman baizo dakinba sabida yaga kofan arufe hakan yasa yay tunani tana wajen aikinta ne, ko fitsari zata fito taje saitaji babu kowa acikin flat din, ko abinci bataci ba ranan daman bata iyacin abinci in tana mp, daga biscuit dasu sweet datakedashi da ruwa kawai takesha, jinin dan ficiline ma yazo as per the first day, haka tawuni tana ciwo har dare, gabaki daya bata runtsa ba daren jiya, jikinta yay mugun zafi, kanta ciwo maranta ciwo boobs dinta ciwo, babu irin kiran sunan Allah dabatayiba akan kar asirinta yatonu yau tana kwance akasa tana burgima dan tama kasa kwanciya agado taji anyi knocking. "Boy wake up and shower is 4 katafi wajen aiki" azabure ta tashi dama zani kawai ta daura, silkin taja jikinta na bari na zazzabi taja zanin kasa ta daura silkin tana runtse idanunta sanan tasa riga da wando da sauri daidai yana jijjiga kofan tabude da sauri tazube kasa, wani mugun kallo yake mata yace "wai how many times zan maka warning akan kadena kulle kofa" bakinshi na rawa tanadan haki tace "sorry head Guard" mugun kallo yasake jifanshi dashi yace "wuce kaje kai wanka fast fast" wucewa tayi bayinsu tai wanka tai brush sanan tasake maida komi tadaura tasaka kaya tafito tana tafiya ahankali da kyar maida kofan tayi tarufe tashiga shiryawa agurguje tasaka pad dinta da duka duka saura uku, daman shi bata wani damuba dan inya kare zata fara amfani da rigunanta tana yagawa dan bazata iya yaga zanin nanba shine hijabin sallanta, adaddafe tasaka takalmi tafito tana nema ta duke dan boobs din zuginsu janta suke sosai idan ta mike tsaye straight, ga maranta kaman ana murza kuli kuli aciki, dayake gari baiyi haskeba ko kadan Head Guard bai gane halin dayake cikiba balle yamaga idanunshi dasuka kumbura sukai suntum.


Ahankali yabude kofar flat dinshi ya shiga bayan head Guard yakawo shi, maida kofan tayi tarufe sanan taduke awajen ta tsugunna tana kokarin hadiye hawayen datakeji tanaso ta daure, kirjinta tasake tabawa dan bamatasan wanne yafi mata ciwoba cikin su biyun, takai sama da minti goma tsugunne awajen sanan ta tashi da kyar tana dafa kofa takai dayan hannunta ta taushe bakinta da sauri tana kokarin hana kanta kuka xafin datakeji yabaci, sai yanzu da aikinta yay nisa tana wata na hudu dan this is her fourth MP shine jikinta ke nema yagaza dan wanan ba ita bane, kirjinta na neman yagaja, ta mike tsaye kaman zata mutu takeji, kasa tsayuwan tayi straight ta duka kawai kaman tai ruku'u tana share hawayen daya zubo mata sanan tai stairs, stairs dinma kaman kara making ciwon worst yakeyi, aduken nan takai tabude kofar dakinshi ahankali ta shiga ta maida kofan tarufe tawuce direct ta shiga bayin shi dayay kacha kacha, kayanshi akasa ako'ina, tsugunnawa tasakeyi tana cijan lips hawaye suka shigabin kuncinta tana wani irin fuzarda iska inda xaka ganta zaka kusan yimata kuka ita karan kanta mugun tausayin kanta takeji but taga rayuwa.





Rarrafe tafara tajawo basket na kwashe kayan dattinshi ta shiga tattarewa tana sakasu a basket din tana kuka sosai mara sauti ko kadan, saida tagama tattare kayan tass sanan takama bathtub dinshi zata mike tsaye dan ihu tayi mai kara takoma ta tsugunna da gudu sabida yanda kirjinta yayi, lallabawa tayi tai kaye kayen bayin a tsugunne batare data iya ta wanke bayin ba, takara jingina da bango tana nishi sama sama, saikuma ta daura duka hannayenta biyu akan fuskanta kaman mai addu'a ta shiga kuka sosai, ita karan kanta she don't know abinda zatama kanta kirjinta ya daure ya rike, maranta ya rike, asalin kirjinta na mata zafi yana mata ciwo kaman wacce keda matsalan ciwon kirji na ulcer, ganin koma menene gwara tabar aikin taje dakinta ta kulle kanta tacire wanan silkin dake neman yasa numfashinta yadauke taita birgima akasa tana jinyan kanta da dandan sarki yagano wani abu game da ita anan, tun yanzu gwara tafice kafin ya farka daga bacci, tunanin haka yasa da rarrafe tazo ta murza hannun kofan sanan ta rarrafo tafito batare data kallo cikin dakinba ta daga hannu zata kama handle din kofan ta maida kofan tarufe kenan taji muryan prince yace "Boyy" awani zabure tajuyo ta kalleshi suka hada ido yana zaune bakin gado, ihun datayi abayi

Please Login or Register in order to submit comment