Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Rahma sun shigo sun jajjatada hira amman shiru, Granny ne kawai kesata tai magan tayi ko Dr Imam batamai magana sai ido, abinci ma taci ba laifi, gabaki dayansu sunawani irin jida ita kaman sun sami kwai.
Da daddare Lawyer Abba yazo yakawomai documents din da Baba yay signing kan ba yarshi bace sanan yakawomao credentials din yarinyar dayasa lawyer ya amsa wajen Baba dan dasu Ibrahima zai nema mata makaranta.

WASHEGARI!!
Tunda sassafe aka fara musu girke girke ana loda kayan Granny a mota dan da motan gida za'a kaisu sudai suna kasa yaran na sama wai acewansu zasu taya new kawarsu Fatima shiryawa.


Dudda yadda take bai hanata tai mugun kyau ba, wata doguwar bakan riga sabuwa Ammi takawo mata datajw Umra tasayo, sanan suka sakamata kwalli a ido dan idanunta sun kore dayawa, saikuma suka samata ban baki akan lips dnta daya bushe sosai sai abin yayi kaman tashafa jan baki, murmushi Rayyana tayi tace "kinga yanda kikai kyau kuwa, banson ina zuwa hutu gidan Baffa sabida yacika fada amman yanzu sabida je zan dinga zuwa I promise" gyadamata kai Fatima tayi, Rahma tace "kunji Granny na kwala mana kira muje" ahankali ta tashi dagakan kujeran tayi kyau sosai Rahma tabude kofa Ya Imam suka gani agaban dakin, yau yana sanye da kananan kaya, farin riga dakuma jean dogo baki idanunshi sanyeda fararen glass ganinshi yasa da sauri kannen nashi suka wuce itakuma takasa tafiya ta tsaya chak kanta akasa tana wasada yatsunta, ahankali yashigo dakin yamaida kofan yarufe tareda jingina da kofan yay folding hands dinshi akirji sanan murya chan kasa yace "Fatima" kasa amsawa tayi hakama takasa dagokai ta kalleshi, fuzarda iska yayi ahankali yace "take care of yourself idan kinje Abuja, be serious with school, I will try na karbi transfer zuwa Abujan idan ban samuba zan dinga zuwa weekend, forget everything about your past and move on kinji" gyadamai kai tayi ahankali batare data kalleshi ba, dan jim yayi sanan yatako ahankali yazo gabanta ya tsaya still kasa dagokanta tayi but you could see yanda gabanta kefaduwa, hannunta yakama ahankali sanan yasaka mata ledan sabuwan wayan da yanzun nan dawowanshi kenan daga zuwa siyomata yace "be using this phone, u will need it idan kika fara school sabida assignment and the rest, Allah kiyaye hanya" yana maganan yajuya yafice daga dakin dasauri.


Tadade tsaye awajen kafin ahankali takalli ledan wayan hannunta, ita kanta batajin dadin kanta she just loose interest in anything and everything, jin Granny ta kwalamata kira yas tabude kofan ahankali tafito ta shiga saukowa kasa Granny na kallonta tace "Ammin su Imamu zokiga yar wajena yanda tai kyau" dariya Ammi tayi tace "ahhh lallai tawajenki kam tahadu wlh" shide Abba dake zaune afalo murmushi take, da sauri Rahma tace "Granny kinga ninefa na shiryata" dasauri Rayyana tace "its a lie, nine wlh Granny" duk dariya akayi saida tazo wajen Granny sanan tace "gani Baaba" murmushi tamata tace "jekima Abba da Ammi sallama" har wajen kujeran da Abba kekai Mama nazubamai ruwan lip tea akai taje, ta tsugunna har kasa tace "Abba zamu tafi, Ammi, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi" kanta Abba yashafa yace "Allah yamiki albarka Fatima Zara" Ammi tace "Allah yakiyaye hanya daughter zamu dinga waya kinji, tashi abinki" tashi tayi ahankali Granny na murmushi tace "to saduwan alheri" rungumeta su Rahma sukayi tabasu kudi sosai sanan duk aka rakosu har mota, shiga motan sukayi, Granny tace "tundashi miskilin vazai iya fitowa yamin addu'a ba acemai natafi" duk dariya akayi Ammi tace "hospital fa yacemiki xai tafi dazun nan daya sakko kasa" dan ware ido tayi tace hakane fa sanan suka shiga musu bye su Rahma na suna hutu zasu taho Abujan, har suka fit daga gidan.

Sundanyi nisa sanan tadauki ledan wayan tabama Granny ahankali tace "Baaba Ya Imam yabani" dasauri takarba tace "masha Allah menene aledan" tai maganan tana cirowa daga kwalin Samsung wayace mai kyau A72 sabuwa gal, murmushi Granny tayi tana bata back tace "iyye Yaya Imamu yasaima y'ata waya, to akashe lafia enjoy your phone, bansan ko kadan ina ganin damuwa kan fuskarki kinji" tai maganan tana kamo kanta tareda daurawa kan cinyanta tace "kwanta" kwanciya tayi ahankali, Granny tashiga shafa kanta tace "zan rikeki amana Fatima, nine mamanki nine babanki, banson komi kina boyemin kome kikeso komeyake damunki kidinga fadamin, I mean komenene kinji, banson ina ganinki so sad, kinga inda zamu gidan Ibrahima ne matarshi nada kirki sosai kuma tanama fita aikin ta, shi datake rikakken dan bokone yara biyu kacal ya haifa, first yaronshi is just 15yrs old yanama boarding house, SS2 yake, sai yarshi tabiyu tanada 7yrs Amna ita kuma tana primary six ta iya surutu, so you will not have any problem with them, idan mukaje ma bakison gidan inada my own personal house dina saimu koma, dama Doctors ne suka hana ina zama nikadai sabida ciwukana, ga diabetes, ga hawan jini, gakuma asma, saisa nake zama da yarana but yanzu ma naji sauki sosai Dr's din UK na sun iya aiki I hardly have attack yanzu, so I want you to be happy, idan kina murna nima I will be fine hankalina ya kwanta nasan cewa ban tauyeki dakomiba, muna kaiwa zankira telana adinko miki kayayyaki kala kala, zamu fita shopping, muje dunes kisai jakunkuna da takalma da gyaluluwa sabida ki shirya fara school kema ki shiga cikin yaran manya ki more yanmatakan ki kaman kowace yarinya of your age kinji" gyadama Granny kai tayi ahankali, fuskanta Granny tashafa tace "to yimin murmushi mana Zara na" batason matan tadamu hakan yasa tamata murmushi bako karamin Dady Granny tajiba haka tadinga mata hira har bacci ya kwasheta Granny na shafa kanta tana kallon fatarta tace "suna isa kaduna zata mata order su scrub glow oil dasauran kayayyakin Glow & Go naturals, sabida hasken fatarnan nata dayadan dishi yafito tadawo da kyanta gashinta zatakaita saloon gobe awanke ayaryada mata kitso, zata gyara yarinyar nan this is just her promise zata zuba kudi ajikin yarinyar nan zasuga yanda yarinyar nan zata dawo, saima tafara makaranta tafara ganin yanda sa'onninta ke gayu sosai zata kara kilewa ne.


Saida suka shiga Abuja sanan Granny ta tadata tace "tashi ki kalli Abuja" tashi tayi tajuya tana kallon waje ta glass harsukakai wani anguwa locust agaban wani dankareren gida dayamafi nasu Imamu girma taga sunyi horn, aduka yaranta Baban su Imam Dr nema wanda baida kudi sosai dudda yanama mallakin private asibitin kanshi, gateman taga yafito yana ganin Granny yakoma ciki dagudu yabude kofa suka shiga cikin katafaren gidan, daidai anbude kofan flat wata cute yarinya fara sol tafito tana sanye da short gown nayara, hannunta rike da sweet mai tsinke tanasha tana hango Granny tabuga uban ihu. "Mummy Granny is here" sanan tataho da gudu tana tsalle. "Oyoyo Granny, oyoyo grandma" daidai lokacin Granny tafito tabude mata hannu aiko yarinyar tadaka tsalle sai jikinta ta kankameta tace "Granny am happy u are back, what did you bring for me" tai maganan tana kallon Zara data fito daga mota, murmushi Granny tayi tace "many things, ya akayi aka miki tsifa rabi akabar rabi"? Kaman zatai kuka tace "Granny tsifan Mummy zafi naki wlh babu" dariya Granny tayi tace "to gobe zan miki saina bada dukanku dakeda Anty Zara akaiku saloon" dasauri yarinyar tace "who is Anty Zara Granny" nunamata Zara dake gefenta tayi tace "ga Anty Zara nan" ware manyan idanunta tayi tana kallon Zara data kakalo murmushi tasakinma yarinyar tace "Granny is she from the Arabs irin na makka damuka je? She looks like them, is she from there"? Dan dariya Granny tayi tace "no she's not from there she's from Maiduguri" baki tabude zata sake magana sukaji murya. "Can you please allow my mother to rest and go to your own mother" yanuna kyakkyawan matar dake kusada shi da akalla zatai 38 ko 39 tana sanye da hadaddiyar atampa tana murmushi, dariya duka akayi banda ita data turo baki tasaki Granny ahankali takama hannun Zara tarike tace "then I will go to my Anty Zara" zuwa mutumin dazaiyi 57 yayi ahankali ya rungume Granny, ahankali yace "welcome home sweet Mum" itama matarshi har kasa taduga tace "barka da zuwa Hajiya, munyi kewanki sosai wlh" dagota Granny tayi tace "how are you Mariya" ahankali tace "fine" kana ganin yanda suke kaga educated couple, har kasa Zara ta tsugunna tace "ina yininku" da sauri Maman Amna tadagota tace "you must be Zara right" gyadamata kai Zara tayi ahankali, fuskarta tashafa tace "welcome, feel at home kinji, take me as your Mum and Dady as your Father" tanuna Baban Amna, sanan tace "let's all go inside and eat, Hajiya namiki fankasau na alkama da miyan taushe" shiga flat din sukayi, yahadu iya haduwa gawani hadadden kamshin turare dake tashi daga dakin, duk sukai dinning while mai gadi na kwasan kayan Granny zuwa side dinta, zama sukayi mijinta tafara zubama abinci sanan tazubama Kaka finkasau din data mata, ta kalli Zara tace "Zara mezakici ke" akunyace kanta akasa tace "anything Mum" murmushi daga Granny har danta Ibrahima sukayi, ita kanta saida Maman Amnan taji wani bala'in dadi yanda takirata tace "alright daughter bari nazuba miki abinda zanci ba boring abincin Granny ba" dariya duk sukayi Granny tace "oho dai" ta kalli Amna daketa kallon Zara da kanta ke kasa tace "kekuma lafiya kiketa kallon diyata" murmushi yarinyar tayi tace "Granny wlh I like her, this Anty Zara" duk dariya akayi Zara tadago kai ta kalli yarinyarnan hakanan taji tanason yarinyar kodan batada kanwa mace data girma hakane oho, da hannu tamata alamu tazo hakan yasa ta taso dagudu tabar kujeran datake kusada Mumy ta tazo wajen Zara tazauna hannunta Zara takama tarike tana kallonta batare datace komiba, Amna tace "Granny maisa bata magana wai" Granny dahar tafaracin abincinta tace "kinga haka take Amna, ni aikinma dazan baki kenan kidinga koya mata surutu dan Allah" daidai nan Mumy tamikoma Zara abinci a plate, hadaddn jollof rice da salad ne agefe sai pepper chicken, karban abincin tayi anatse sanan tace "nagode Mum Allah ampana" hakanan gabaki dayansu saida ransu ya sosu da yanda tai godiyan tabasu tausayi saidai suka daure babu wanda yanuna mata, Mum ta kalli Amna tace "small Madam keme zakici" turobaki tayi ashagwabe tace "nina Anty Zara zamuci tareko" gyadamata kai tayi tadauki spoon dinta tabata sanan ita tadauki wani duk akai shiru aka faracin abincin, dudda batada apatite but surutun Amna da yanda taketa wasa tana raba musu abincin yasa suka cinye tass, Dady ne yafara tashi yatafi falo, Granny ma tawuce yarage Mum ce kawai dasu a dinning din tashi tayi ahankali ta kalli Amna dake kallonta, adan hankali batare dakowa yajiba tace "where's kitchen Amna"? Kofar kitchen dinsu Amna tanuna mata hakan yasa ta shiga tattare plates din dasauri Mum tace "mekikeyi daughter" ahankali tace "zan kai kitchen ne" baki Mum tabude zata hanata Granny tace "Mariya ba'a hana d'a aiki, Zara ba bakuwa bace tazama yar gida" murmushi kawai Mum tayi batasake cewa komiba, Zara ta tattare plates din zata kwasa Amna tamika mata hannu tace "nima Anty Zara" guda daya tabata sanan suka wuce kitchen suka ijiye kafin sukara dawowa lokacin Mum tagama ta sake hade plate din tawuce dasu, Mum kuma tawuce falo, sanan tasake dawowa itada Amna ta gyara dinning din tass kaman ba'aci abinci akaiba sanan tawuce kitchen Amna nabinta kaman bindi tashiga wanke wanke......

Jin karan tana wanke wanke yasa Mum ta kalli Granny tace "Hajiya kinga wanke wanke take akwai mai aiki fa" murmushi Granny tayi tace "ki barta, aikin nan datakeyi zaisa ta watsake" gyara zama Dady yayi yace "ina credentials din nata"? Jakanta dake kan kujeran datake ta dauka tacirosu a file, sanan ta bashi ya karba yana dubawa, yace "yes tanada waec dinta tsaf duk taci science courses din, saidai batai jamb ba" anatse Granny tace "ai akwai schools din dazata iya farawa kafin next year yazo tayi jamb intaci saita fara University, inason nai keeping nata busy ne" gyadamata kai yayi yace "akwai friend dina dake running Private Health School, though anriga anyi admission, zan bashi inyaso saiya bata any course taje tafara, but dole a hostel zata zaune" dasauri Granny tace "a hostel"? Gyadamata kai yayi yace "eh, most health schools lectures dinsu suna farashi very early everyday, sanan suna karatu harda na hauka, kinga kuma wanan dasun fara lectures definitely ana bata admission dole tazauna tai karatu sosai dan an wuceta, kibarta tazauna a hostel din babu abinda zai sameta babban school ne sosai achan karshen Abuja yake, inyaso duk Friday zamu dinga tura direba yana daukota tai weekend agida, ranan Monday da sassafe takoma" kallon Mum Granny tayi tace "ke Mamarta to kin yarda da shawaran mijinki"? Murmushi sosai tayi jin karan da Granny tamata tace "eh na yarda duk weekend zata dingayi agida Hajiya, kinga yanzu idan taje tana xama a hostel cikin student zata waye ta kile, sanan tadage da karatu duk wanan kunya da kas kallon mutane zata dena, idan yaso 1week din dayace mubashi zamuyi amfani dashi mu mata siyayyan school dakuma dinkuna ko Kaka, ni akwai ma wasu atampopina dazan bata" sanan tajuya ta kalli mijin tace "Dady zaka bamu kudi muje muyi shopping ko" gyadamata kai yayi yace "gobe tunda Saturday ne ba work saiku je dukanku" murmushi duk sukayi Granny tace "Allah yamuku albarka, shikuma lukuti na yaushe zasuyi hutu yadawo gida"? Dariya duk sukayi Mum tace "just last week yakoma sunyi resuming first term, shida dawowa gida ba yanzu ba saidai mujemai visit, Granny yasu Dr mara kiran mutane" dariya tayi tace "wanan ai kinga halin mijinki yadauko dan haka karma kiga laifin jikana ehe" dariya duk sukayi daidai Zara tafito rikeda hannun Amna, Mum tace "sannunku to da aikin daban sakaku ba" sauke kanta tayi Granny ta tashi tace "bari muje muyi wanka muyi salla, muje Zara" bin Granny sukayi suka wuce suka fita Mum tabi Zara da kallo, sanan ta kalli mijinta bayan nan tace "Dady wlh na tausayama yarinyar nan sosai at her age dai taga rayuwa" murmushi kawai yayi yace "such is life kowada kaddaran shi, dazaran tafara school tasaki jiki zata manta dakomi and move on" gyadamai kai Tayi tace "hakane" sanan suka cigaba da hiransu.



Bangaren Granny shima hadadde ne agidan, amman shi ba duplex bane sabida rashin lafiyanta bata cikason hawa bene ba, but hadadden flat ne nagaske, ga durmemen TV afalon da speaker, ga kitchen ga dinning, saikuma wani corridor, da dakuna uku keciki, daya daga cikin kofar dakunan tabude, hadadden dakine ga gado da aka gyara royal bed, ga sip din bango, ga bayi ga ac ta kalli Fatima tace "wanan shine dakin ki, kinaso ko kinason achanza miki wani abu"? Dasauri ta girgixa kai tace "inaso, Allah saka da alkhairi Baaba" bayanta Granny ta shafa tace "kidinga kirana da Granny kinji, yanzu shiga ciki kije kiyi wanka akwai komi abayi kihuta, kekuma kibarta tahuta" tai maganan tana kallon Amna dake rikeda hannunta, raurau da ido tayi zatai kuka da sauri Zara cikin sanyin muryanta tace "dan Allah kibarmin ita Granny" murmushi Granny tayi tana kallon Amna dahar lokacin shirin kuka take tace "shikenan to" hakan yasa tafashe da dariya tanajin dadi, Granny tace "toku shiga" shiga sukayi suka maida kofan suka rufe itakuma Granny tasauke ijiyan zuciya tawuce tashiga nata dakin.


Haka ranan tawuni ko kadan Amna bata barta tahuta ba, surutu surutu, bata barta tai tunani ba, ta makala wayanta a chaji tanata kallon wayan har cikin ranta taji dadin wayan dan bata taba wayaba sai wanan, bayan Magrib suka wuce suka tafi flat dinsu sukaci abincin dare as usual tasake gyara dinning tawanke kwanukan dasukaci abinci dashi sanan Amna tajata sama zuwa dakinta tadinga mata surutu, sai wajajen 10 sanan Granny tamike ta kwala ma Zara kira, saukowa sukayi still Amna namakale da ita, ta kalli Mamanta tace "Mum ni i will sleep in grandma's place" tabe baki Mum tayi tace "agais dakansu zasu kadoki parrot" binsu tayi suka wuce side dinsu duk suka shiga Granny ta kulle kofan falo takashe wuta sukai balcony sanan tabisu har dakin Fatima tace "makesure kinyi wanka sanan kiyi nafila saiki kwanta kinji Zara, gobe zamu sayo harda kayan bacci" gyadama Granny kai tayi, sanan Granny ta kalli Amna tace "tsabagen azarbabi bamaki riko pajamas dinki ba" bari nakira Babanki yakawo miki" Kaka tai maganan tana fita zuwa falo itakuma ahankali Fatima tabude bayin ta shiga, dayake yanzu tasan kan irin bayukan yan gayun nan sabida xaman lagos yasa ta kunna heater tafito ta kalli Amna tace "zomuje namiki wanka" dasauri ta tashi riganta tacire mata tana kokarin cire mata pant Granny tashigo rikeda kayan baccinta, sanan dawani kayan baccin a leda tamikama Fatima tace "ungo kema Mum dinki ta aikomiki da sabo" murmushi tayi ahankali sanan takarba tace "thank you" Granny tace "kina gama komi ki kashe wuta ki kwanta" gyadama Granny kai tayi ahankali, Granny tace "saida safen ku" atare suka mata saida safe, sanan tawuce bayi ta tahada ruwa tamata wanka da hadadden shower cream din dake bayin sanan suka fito ta shiryata cikin kayan baccinta ta kwantar da ita akan gado taja bargo tarufa mata ahankali tace "nima bari naje nayi" bayin tawuce tai nata wankan da ruwan zafi sosai tana karajin dadin jikinta sanan tadauro alwala tafito daga bathroom din tana kallon Amna dataga tai bacci, dan murmushi tasaki taje tabude kayan baccin, normal pj ne dogon wando da riga mai kamada t-shirt amman gajeren hannu yanad taushi sosai, hijabin dake kan sallayan tai tahau tai nafila sanan ta tashi ta linke dadduman takarasa takashe wutan saiga hasken wayanta dakuma ringing atare hakan yasa ta kalli screen din wayan dataga an rubuta Imam ajiki.





_Mumies akwai abinda nakeso nagaya muku, shin kunkosan like Did you know........?_
_Scent kamshi shine abu na farko da mutane ke lurada shi idan sun shiga gidan ka ko motan ka bawani abuba?_
_Be memorable.....in a good way Mumies_
_A Fragrant, shi kamshi is like a signature, kaman wani alamune so even after a woman leaves the room, her fragrance should reveal she's been there. Kamshi abune dake nuna kinzo waje idan ma kikabar wajen still zai nuna kinzo_
_Turare heralds a woman's arrival and prolongs her departure_
_The beauty of turare speaks to your heart and hopefully someone else's kunsan da haka Mumies?_
_Kamshi is a word, turare is a literature do you believe this Mumies?_
_Kamshinki amatsayin ki na y'a mace tells more about you sama da handwriting dinki kinsan da hakan?_
_Mata kusaurara kuji, namiji yana iya manta komi naki amman baya iya manta kamshin ki_
_da hakane nake muku introducing turarukan UMMIE COLLECTION dazai baki duka qualities dinan and even MORE tested by M SHAKUR dinku, suna saida turarukan daki, na jiki, na wanka, turarukan tsinke, body oils da sauran su, zaki iya tuntubar su ta wanan number ko awaya ko a watsapp 08186968736, dan samin karin bayani, zaku iyashiga group dinsu dan ganin duka turarukansu, zakuma ku iya following nasu a_ Instagram @UMMIE COLLECTION.

Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/Fov2UbNr4CH0reP9K9zltu


Instagram Handle dinsu https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1c3np4d6vwqbv&utm_content=1g4qyjp

_PRODUCT DINSU_
_SANDAL EXCLUSIVE_
_SANDAL FLAKES_
_SANDAL BANGI_
_KAJIJI_
_DOROT_
_DAMBU_
_DEVINE (PURPLE)_
_REGAL (YELLOW)
_LOVELY (MAROON)_
_DAISY (ORANGES)_
_KHuMRA_
_STAR_
_BELOVED_
_Body oils._
SIGN M SHAKUR
7/6/21, 11:57 AM - My Mtn Number: 💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫




✍? M SHAKUR




EPISODE 5️⃣7️⃣


Saida gabanta yafadi dasauri takarasa gudun kar wayan yatada Amna tazare wayan daga chargy tama rasa mezatayi kawai tadaiga tai picking call din taga alamun yana kirga mata secs, ahankali takai wayan kunnenta tai hannunta nabari jin shiru yasa tacire wayan ta kalla ganin har lokacin call din nanan yasa takara kai wayan kunnenta ahankali tace "h......hello" tai maganan tana tashi ta kwanta akan gado ahankali tanajan bargo tana rufe kafanta, dan lumshe ido yayi yana gyara zama akujeranshi na office dan night yake, ahankali yace "Fatima" murya chan kasa kaman mai tsoron magana tace "uhm" saikuma tai shiru jin yayi shiru yasa ahankali tace "ina yini" ahankali shima yace "ya hanya? Kukai lafiya"? Murya chan kasa tace "lafiya lau" saikuma suka sakeyin shiru for so long hartana ciro wayan daga kunnenta ganin still call din is on yasa murya chan kasa tace "Thank you" ahankali taji yasauke ajiyan zuciya yace "for"? Alamun tambaya dan yanaso yasatai magana, only magana ne zaisa tasaki jikinta ta manta d past life dinta, murya chan ciki kaman tana tsoronshi tace "for bringing me to Baaba" tai shiru saikuma ahankali kaman tana shakkan fadi tace "and for giving me a family" murmushi yayi dahar saida taji sautin murmushin yace "you are welcome Fatima" suka sakeyin shiru saikuma chan yace "kinga Baffa na, da Mum da Amna" murya chan kasa tace "eh" saikuma chan tace "sunada kirki" dan murmushi yayi yace "ina Amna"? Ahankali tace "gatanan" murmushi yasakeyi yace "I guess kinyi sabon kawa kenan, saikin gaji da magana" dan murmushi kadan tayi dayasa yaji dadi dan yaji sound din murmushin, ahankali yace "take care, jeki kwanta" kaman yana ganinta ta gyadamaikai sanan ahankali tace "nagode Ya Imam" lumshe idanu yayi sanan yabude su ahankali tareda katse wayan.


Janye wayan tayi daga kunenta ta ijiyeshi agefenta tajuya takife akatifa sabida hasken, sanan tai shiru tareda lumshe ido. "Ya To....bi" tafadi amugun hankali saikawai hawaye taji ya gangaromata daga idanu, tuna last ganinshi datayi jiyane sama sama yayi butu butu ya lalace kaman bashiba sama sama taga yana kuka yana jijjigata daganan batakara sanin inda kanta yakeba tadai tashi taga kanta a kano. Kife kanta tayi a filo tana kuka dabazama ta iya tantance namiye ba she is happy Allah yafitarda ita daga kangin wahalan nan nagidansu Tobi, yanzu she's back Allah yahadata da masu sonta but wani bangare na zuciyanta na wishing takoma gidan badan komiba saidan kawai taje taga Tobi, ayanda take ayanzu har cikin ranta jitake shikadai kawai zatagani taji she's fully happy. Kasa hakuri tayi tai kuka sosai sanan bacci yay nasaran kwaceta.



Karfe biyar daidai ringing wayar ya tadata harsaida ta firgita dan bata saba da wayaba, bama ta taba wayaba, daukan wayan tayi ganin Dr Imam ne yasa takara a kunnenta ahankali, cikin a very calm and light voice yace "tashi kiyi salla, lokaci yayi" murya chan kasa tace "uhm" sanan yakatse wayan, ijiye wayan tayi ta tashi ahankali tareda kunna wuta ta kalli Amna yanda yarinyar ke diban bacci abinta tai lakur a bargo sanan tawuce tashiga brush tayi da komi tadauro alwala tafito daidai ana bude kofan dakinta Granny ce ganin tana fitowa daga bayi yasa tace "kin tashi Diyar kirki" gyadama Granny kai tayi, Granny dake rikeda da charbi tace "ok" xata juya tafita saikuma tadawo tace "namanta ban fadamiki ba banda tsarki da ruwan sanyi, ga bayi nan akwai ruwan zafi muddin akwai wuta kome kikayi kidinga tsarki da ruwan zafi kinji" ahankali tace "to" sanan takalli Amna dake baccinta sanan tawuce tafita tarufo mata kofa, hawa kan dadduma tayi tai rakatanil fajiri sanan tai sallan asubahi data idar tai azkar tai karatu sanan tashiga addiua Allah yacire mata kunci da damuwan datake ji aranta, wajajen 6:30 tagama komi tacire hijabi tafito tana sanye da kayan baccin dogon wando da riga peace sunmata kyau kanta nacikin hula tafito, kitchen din falon tashiga tadauko tsintsiya da paka tazo tabi falon nan tamai hadadden gyara sanan tabishi da mopping, showglass na turaren daks falon tabude tadauko turare da burner datagani ta kunna turaren sanan takashe komi datai amfani dashi tawuce kitchen saida tafara gyra kitchen din dabaiyi datti ba sanan tashiga store tana kalle kallen abinda zata dafa, wake tafara debowa ta wankesu tass ta jika aruwa sanan tadauko Irish tasami waje ta zauna tashiga ferewa kana ganinta kasan ba yarinya me kiwuya bace saida tagama sanan ta yayyanka, ta tashi tawuce tanika waken da attarugu da albasa a blender tasa ruwa kadan sabida karyay ruwa, tana gamawa tajuye a bowl sanan tasa mai aruwa tazuba Irish din itakuma takoma gefe tashiga bubbuga kosan, tanayin haka tana tashi idan Irish yasoyu ta kwashe tazuba a hadadden kula, bude kofan kitchen din akayi chak Granny ta tsaya tana kallon yanda tazauna kan wata yar karaman turmin dake kitchen din tana bubbuga kosai, salati tayi tace "oh ni yarsu waya saki

Please Login or Register in order to submit comment