Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"zanin ne har‘ yau ba ki iya ba
Jika, kullum ki ta sakin bakin zani yana jan qasa”
Rukayya ta ce, "Ni fa haka .na iya. Kaka“ Tace "
to ai sai ki tayi tunda keba a ba, a baki shawara
ace mace har yanzu bata iya daurin . zaniba
Rukayya'ta ‘warware zanin tana sake daurawa,
Abubakar yai sallama ya shigo yana kallon
Rukayya ya ce
"Ke kuma meye haka? Sai kacc wata aljana?
Kinga yanda kika kwabawa fuska mai sai sheki
take.’ Haka aka fada miki ana shafa man? Yo
ashe ma har gara da ba ki shafawar ma kibar
fuskar a bushenta sai kacc mai qazzuwa. ke
kokarcin jikin ki baki ji?"
Kaka tace"Shin wai kai in tambayc ka jikin ka ko
jikinta? Haba! ka takurawa yarinya da tsinannan
kicilin tsiya".
Abubakar ya ce, "Amma saboda Allah duba fa
Kaka, dama abinka ga baqar fata ’ kuma ta qara
dabbaka uban Basilin, ta qara _ wani uban baqi
Kaka tace "To dai babu rUWan ka da ita kaji k0?
Ai jikinta ne ba naka ba".
Rukayya ta gyara'daurin zanin ta koma ta zauna
gefen Kaka, Abubakar ya ja kujera. 'yar tsugunnc
ya zauna, yace
' "Kaka da wata muhimmiyar magana na
Zo miki. Kaka ts washe baki 'lna jinka nannan
. Sai da ya kara gyara zama kafin ya ce
"Dama maganar aurena ce Kaka ta taso don
wallahi na Janyo fadan da yafi karfina.‘ 'Yar
gidan ubangidana ce muke soyayyah shi ne yau
mahaifinta ya kira ni ya ce naJe na turo iyayena
a cikin satin nan. '
Na fada mashi 'yan matsalolin da ake ciki Shi ne
ya ce ai bai bukatar komi nawa indai
turob‘iyayena da abinda ya sauwaka shi xai Ji ',
da komi Shi ne na nace kije ki masu Malam
magana don su shirya tafiyar kamin -' inje inji
yanda 'za ayi k0 ba haka ba?" ' ' Kaka Wadda a
farkon zancen sa bakinta '.yake a washe har" ta
gagara rufe gibinta, amma 'tana Jin ya ce 'yar
gidan uban gidansa 1mta hade fuska ta gabas da
yamma, har yaje karshen zancen sannan kaka
tace lallai‘ biri ya yi kama‘ da mutum haba! ashe
duk abin'da Uban gidan nan naka" yake maka ba
don Allah yakeyi ba sai don ya hada ku aure da'
yarSa, ti bai isa ba.Wallahi'yar.
Tasa tayi kwantai tayi Jibgaro an rasa mashin
sini ‘ shi ne za a lika maka ga sakarai, to bakaso
Ai muma nan gidan muna da wadda muka baka:
ga‘yar uwarku nan .jika, nima itace wadda na
zaba maka, kuma irmta ce zaka aura. Sai ka
koma ka bashi haquri ka fada mashi a gida an
maka mata kaji na fada maka baki
Sake Abubakar ke kallinta har ta kai aya. sai yace
tunda yake bai taba ganin. Bacin ran Kaka irin na
yau ba. '
Yace Haba Kaka yanxu ki dube ni ki dubi
yarinyarcan Kaka ai kin san bamu ma : dace ba
don Allah ki daina ma wannan
maganar".
Kaka ta mike tsaye da qunshi a qafarta,‘ tace:
"Habu, wallahi lallahi na rantse da Allah
.' in har kaga aure tsakanin ka da jika bai yiwu
ba to saidai in ko bana numfashi".
Abubakar yace "Kiyi hakuri Kaka, abin ba na fada
bane, maganar aure tsakanina da Rukayya
babuma wannan labarin, gaskiya na
Fada ‘maki ma ~ba zan iya auren taba k0 da
kuwa kyauta za, aban ita
babu abinda zanyi da ita" Kaka‘ ta. fashe da kuka
"na shiga uku, yau nagata kaina, qaramin yaro zai
nuna min
iyakata. ‘zaka tozarta habu? Ni zaka wulaqanta a
bainar‘jama'a‘.’ to wallahi baka’isa ba, idan kaga
ka auri waccan to sai ka auri jika; Don ba ni na
haife ko eh ban haifr kaba habu amman riqon da
nai maka kawai ya isa idan nai maka baki ya
bika wallahi". . Tashin hankalin da Abubakar ya
gani qarara a wurin Kaka yaSa ,ya miqe jikinsa a
mace ya bar tsakar gidan‘. ya nufi dandakinsa _
ya kwanta tsananin damuWa tamkar ya‘dora
hannunsa aka ya ce wayyo Allah ' Rukayya kuwa
yana tafiya itama ta miqe ' ta nufi dakin Kaka ta
fada kan gadonta ta fashe da wani irin kuka mai
sauti, Kaka ta cire kunshin kafarta dako kamawa
bai yi ba ta nufi dakin, ta janyo Rukayya a jikinta
tana lallashi tace
"Yi shiru Jika kinji‘. ’ Yi hakuri, ai wallahi
inhar ina raye sai ya aure ki don tada mashida
hankali zanyi dolema sai ya aurc ki".
, Rukayya tace. "Kinji fa-wai bai sona yace
waiban da kyau, kazama ce ‘ni; Kaka saboda
Allah yanzu, ina qazanta take anan'? Ni
wallahi idan har yaqi yarda bazab taba auren
koWa ba, kuma ma mutuwa zanyi ‘Allah kinjima
na rantse .
Kaka tace"kiyi shiru, vaza ki mutu ba jika har sai
naga tattaba kunne na, da kaina gobe zan lafi
gobe da safe mu gama magana, ba zan dawo
gidan‘ nan ba sai an tsaida ranar auren ku". Dadi
ya kama Rukayya ta ce "Ato Kaka, don Allah gari
na wayewa ki tafi
Kaka tace,"Karki damu Jika" “‘
‘ .WaShegari tun da sanyin safiya Kaka-ta'
shirya la lulluBa zani, Rukayya ta rako ta har
bakin hanya ta hau mota ta‘tafl, sai da Rukayya ’
taga Iafiyarsu sannan ta dawo gida.
Kaka na dira garin ta sauka gidan Malam Sale
kanin mijinta ne, qaton gida ne duk ”'yawanci
dangin mijin nata suna zaune a ",wannan gidan' ,
Malam Sale yana makaranta tasa aka kirawo shi
yana shigowa ya ganta ya ce
. .ikon Allah, indo kcce a gidan namu yau‘? Allah
Yasa dai lafiya"
Kaka tacr "To zauna lafiya qalau".
Malam ya 'zauna yana fadar "Ai yanzu Habu
yazo mana da maganar aurensa data taso da
kika aiko kirana, shi yasa nai manaki
Kaka ta ce, "La' ilaha illallahu! Kunga yaran
zamani yanxu har ya riga ni 'zuwa kenan? To kar
ka saurare shi '
Malam yace, "Y0 don mi Hajiya yaron ya samu
yqrinyar da yakeson kuma ai yamin bayanin komi
don haka indo kiyi hakuri ki' janye wannan
maganar tunda dai yaxu ga wacce yaro yakeso to
a barshi ya aura kawai".
Kaka tace"Wallahi bai isa kaji na rantse tunda
itama jika bata da wani mashin shinshini koso
kake inbar yarinya a gabana shekara sha Shidda
babu aure?" . Malam yace, "Eh kuma da wannan
don wannan, amma abinda nake ganin mafita '
anan tundayace yana son waccan yarinyar .kuma
ubanta yace bai buqatar komi, to duk ya hada
da‘ila Rukayya din ya hada da dan abinda Allah
Ya hore masa "aci gaba da biki".
Kaka ta ce, "To sai dai wannan, na yarda da
wannan din‘.‘
Malam yasa aka kira masa Abubakar yazo akai
masa bayani,da farko ya ki aminccwa, amma
daga baya da bakin su ya hadu sun jajirce sai ya
amince don ance sarkin yawa yafi sarkin ,yawa
yafi sarkin qarfi malam ya ba da kudin neman
aure a take Naira dubu biyar aka tsai da rana
daya da _wancan,idan an tsai da iokaci sannan
kaka ta baro kaunyen da yamma likis. ’
Washegari kakannin nasa suka tafi birni' gidan su
Suhailat Abubakar ya ba da kudin neman aura
Naira‘ dubu ishirin" amma mahaifinta yasa aka
dawo da su bai amsa ba, ‘ aka tsai da ranar aure
Wata daya kacal. . Suna dawowa Kaka ta sa aka
sayo mata biskit ta fara rarrabawa makotan nesa
dana kusa bikin . Jika wata guda
Kowa ya yi mamaki, yarinyar da ba zance: take
ba amma har ta sami miji, kazamiyar-“yarinya
babu abin data iya sai masifa kOWa dai da abin
da yake fada.
Kaka kuwa dadi har ina an sawa Jika ranar aure
da Abubakar, daga tsai da ranar Kaka ta garzaya
gidan malam ta amso mata ganyayyaki. '
Kullum cikin yiwa Jika hade haden su na tsaffi
takewa jika jiqa wancan, dafa wancan, daka .
wancaHar Rukayya ta Soma gajiya da hade
haden da Kaka ke mata, dan haka k0 yauda ta.
dafa mata wata budurwar kaza ba maggi ba
gishiri sai baurin itatuwa take.
Rukayya tace, "Ni k0 Kaka na gaji da ciyeciyen
abubuwan nan da kike tura mini, dan Allah ki
kyaleni haka".
-‘ Kaka tace, "Keda Allah gafara, wannan ‘hade
haden ai su ne za su kwato maki mutunci . da
daraja a gidan Abubakar din, baki san gidan
kishiya za ki ba? Ai nan ma ba a fara komi ba, ke
dai kawai ki sa mani ido, ta wannan hanyar ce
kadai za ki iya kwacc Habu ya zamo naki, duk
kyan kishiyar ki duk kuma kWalisar ta, ke dai
zuba ido.
Cikin‘ sanyin jiki RuKayya ta ce "Allah Yasa
Kaka".
Ni kaina dai sai riqe wayata nai gam ina kallon.
’Rukayya, na kare mata kallo a zuciyata dai sai
cewa nai, "Amman da kamar wuya kwacewa'
".Suhailat Abubakar kyakkyawan yarinya wadda
kanta ya faru da boko
" Ammadai..;, Muje zuwa wai mahaukaci ya hau
kura bari
llah
‘RIKON KAKA-2
CHAPTER12
RUkayya na zaune da safe daki aka gefen gado
tana dinkin . zaninta da allura, Kaka ta Shigo ,
dakin hanunta rike da kwanon sha, ta mikawa
Rukayya. ' ’
"Ungo, amshi shanye maza ki miko min kwanon".
' . ‘ Rukayya ta ajiye dinkin, ta amasa tana kallon
.abinda ke cikin kwanon. Kindirmo ne wanda aka
dama da garin magani, Rukayya ta dago ta
dubeta. .. _."Meye ne Kaka?" .Kaka tace "Ke in
zaki sha kisha kinji, ni
‘bana' ,' son yawan ‘ tambaya“. Rukayyah ta
bata fuska, "Ni fa na faragajiya kullum ki ta‘
banka min wasu jiqe-jike ‘sai kace jikar mai
ganye". ‘ ‘ ‘_
.. Kaka ta ce, "Hum! Jika kenan,‘ai wannan jiqe-
jiken shi ne'zai janyo miki mutuncinki a wurin
Habu, ki kwacc shi a hannunki ,yarinyar‘nan": '
Rukayya tai murmushin jin dadi sannan ta kafa
kai tana sha, bata damu da baurin maganin ba.
Sai da ta shanye tsaf sannan ta mikawa Kaka
kwanon, ta amsa ta miqo mata
wani kullin magani. "Ungo, ki dauka ki zuba a
babban baho, akwai ruwan zafl akan wuta ki zuba
a ciki, ki
dauka ki kai kewaye ki tube ki zauna a ciki har
sai ruwan ya huce".
Rukayya ta amsa tana tsalle ta tice, Kaka ta
girgiza kai a zuciyarta tana raya irin tsantsar ‘
son da Jika kewa Habu. ‘ Rukayya na fitowa
tsakar gida ta hadu da .Abubakar yana shigowa,
yana sanye da , (suit) baqa, takalmin kafarsa
sawu ciki ne bar" a fusakarsa. Sumar kan ‘ nan
_tasha gyara, tai bakikkirin, kafadarsa na rataye
da jaka irin ra ma'aikata. ' Kallo daya tayi masa
gabanta ya fadi, irin kyan . da 'ta gani kwance a
jikinsa. Tai ' Saurin jan kafafuwanta ta .wuce shi.
"Ke, Zo nan",
M uryarsa ta daki dodon kunnen
Rukayya, gabanta ya fadi. Ta dawo ta tsuguna
gabansa a tsorace.
‘ Ya kara bata fuska, "Ke baki iya gaida mutane
bane? K0 ko' raina' ni ki kai?"
Tai shiru. _ . . _ gamida girgiza kai
, Abubakar yaja tsaki ya wuce ya barta nan a
tsugune, Rukayya ta daga kai tana satar.
kallonshi. . '
Ya daka yana cire takalmin qafarsa ya” ‘ hangota
tana kallon shi, ya dago a fusace.
' "Kallon uwar me kike min kuma iye?_ “Me kama
da tsohuwar mayya".
. Yanda ya zaburo mata yasa ta zabura ta zura
aguje, yaja kwafa ya nuf dakin kaka . ' ' ,Yana
shiga ,dakin Kaka ya duka har qaga 'yana gaishe
da ita, harara ta watsa mashi:
"Kai ko wannan anyi mai mugun hali, wallahi duk
abinka dai aure kai da Jika kamar anyi an gama".
'
Abubakar ya cire gilas din idnnsa yana fadar.
' Ai kisa a zuciyar ki Kaka, kina son daurawa jikar
ki aure: da wahala, ne kawai kinji ma na fada
miki ban Boye miki ba".
' Kaka ta ce muhammadu dan abdullahi habu to
"Kaje kayi duk abinda kaga dama wallahi ka sake
ka zalinci marainiyar ‘ Allah wallahi Allah ba Zai
barka ba kuma
Allah Ya isa ban yafe maka ba har‘ duniya ta
nade" .
Ya ce, "Ai in Allah Ya ,isanki ba bina zata yi ba
Malama. Na zone ki min addu' a yau zan fara
zuwa (office) din da Alhaji ya samar min’ aiki,
don haka ga kaina ki dafa kimin addu' a"_
Ya duka da kan nasa gabanta, Kaka ta dora
hannunta. ‘ .
“Allah Yasa alkhairi, Yasa wannan aikin
ya zamo abokin arziqinka. Ubangiji Ya dora ,
maka ciwon son Jika kamar ya kashe ka". ‘
Yai saurin janye kansa yana daria yace.
Oh kaka harda wata mummunar
addu, a nara ‘karbuwa kuma?
Kaka tace“Hum! Habu kenan, ai insha Allahu
wannan addu'ar “karbabbiyace don koda raina ko
babu in Allah Ya yarda saika zo ka durqusa
gaban Jika kana kuka da idanuwanka saboda
soyayya'.
Abubakar ya mike, ya aje mata dari biyar
'Yana fadin ni kinga tafiyata karki batamin lokaci
sannan karku tsaya jirana don karfe shiddah ake
tashi kinga kafin na dawo dare yayi'
Kaka tace“Allah Ya kiyaye, Ya bada sa'a".
Yace amin
Sannan ya fice tana mashi addu‘a.
Bayan sati biyu hidima taima Abubakar yawa kai
ya dauki zafi. Sauqinsa guda ma uban Suhailat
ya dauki nauyin hidimar komi.
dai-dai da gidan da zasu zauna Mahaifin Suhailat
ya bashi qaton gida a cikin gari G. R. A mai kyan
gaske, ya bashi kyautar sabuwar mota' yar
karama ta zamani.
‘ Abinda ya qara darsawa Abubakar tsoro
a zuciyarSa kenan har ya kasa sanar da su hadin
da iyayensa ke son yi mashi,kullum idan yazo zai
sanarwa Suhailat sai yaji ya kasa, don‘ haka ya
jaye komi a zuciyarsa ya cigaba da hidimo‘min
gabansa.
K0 kadan bai kula da hidimar bikin shi " 'da
RuKayya, ta Suhailat kawai yake
Kaka tana ta hidimominta, duk wasu yan tarin da
take yi ta fito dasu tanaiwa Jika hidimomi," 'ta
bigewa. kanta_ hadin ; kayan dakin Jika. Tasa
Abubakar a gaba , a dole ya harhada 'yan
kUdadensa _a gidanshi na gado dakevcikin'
qauyen ya biya kudi aka gyara mashi shi sosai
akai fcnti, sannan ya biya kudi akai ‘mata kayan
faki daidai da zaman Rauye. ‘
‘ Ba laifi komai yayi kyau harta kayan aikace
aikace na mata sai da ya sissiya mata nadai
daidai da ita sannan ya dauko kaka ya nuna
mata
Komai yai mata yai sannan ya kama hanyar
katsina
ya Ci gaba da hidimar auren sa
Fatittika kala shida suka shirya fatittikak kuma
irin na gogaggun yan boko masu ji da kudi ‘
Kaka bata qarasa Abubakar a ido ba har
ranar daurin aure, inda jama'a suke ciko
dankam , a gidan , kowa yana ta hidimarsa ,d0n
haka hahkalin Kaka ya dauke batai mitar rashin
ganinsaba
Karfe sha daya na safe dangin su Abubakar suka
gama haduwa Sannan aka daura auren Rukayya,‘
sai suka wuce aka dauro na Suhailat.
“‘hiidima Sosai aka Shirya'wa ’dangin Abubakar
da ab0kansa da sukaxo daurin auren
An shirya maSu Sha tarata arziki Anyi anyi barin
naira abin harya soma bama yan uwan abubakar
tsoro
Abubakar bai samu dawowa kauye ba saboda
(dinner) da uwar amarya ta shirya masu bayan
faurin aure, don haka yaiwa abokansa waya aka
sami mota kwara biyu aka tura gidan Kaka aka
dauki amarya da masu mata rakiya a kai amarya
gidanta, daki biyu n sai dan .qaramin kicin da
kewaya Rukayya dai ita' daya gidan ya isheta, ya
kuma sha gyara sosai. Rukayya bala shiga rudu
ba sai da taga kowa ya watse ya barta ita daya a
wuryar gado tana rarraba idanuwa tun tana
dakewa dare ya 'soma tsalawa tsoro ya kamata,
ta fashe da kuka“ tana .rakube babu mai
lallashinta, dama Kaka ce gashi yanxu bata kusa
da ita tun RuKayya na kukan fili harta koma tana
na zuci batasan lokacin da har barci Barawo ya
dauketa ba Asuba farko Rukayya ta farka a rude
:kamar Wata zararriya, sai waige waige take
daqar ts iya daurewa ta mike ta fita tsakar gida
ta kama ruwa
Sannan ta dauro alwala ta dawo fakinta tai
sallah, duk
abinda take a. Tsorace take . ' , . ' " Tai tSugunne
a kasa ta rafka tagumi,jira kawai take gari ya
kara haske ' tasan.abinyi; a haka, hasken" '
Fasuba ya keto, gari yai haske sosai. '
Rukayya‘ta mike ta janyo hijabinta,ta sa
takalminta ta fice« ta janyo “gidan tai hanyar
gida. .
~ ' Tunda ta sanya kafa cikin gidan ta take Jiyo
hayaniyar: jama, a' da baSu da basu gama
watseWa ba tana sallama tsakar' gidan jama, a
Suka yo kanta ‘ ca
Rukayya ta fashr da kuka,ta fada dakin-Kaka,
mutanen dake gdan Suka rufo mata
baya. Kaka na ganinta ta rude. ' ' "Jika maiya
fito dake daga gidanki K0 wani abin yai miki “‘
ne?" Rukayya tace kaka "Wallahi ni
‘ bazan koma ba, Allah Kaka bazan koma ba
. Kaka ta dauki Sallallami, "Ba zaki koma ba
Jika? Daga . kaiki gidan jiya‘?" Jika tace"Kaka ni
kadai fa na kwana
gidan jiya, har yau bai zoba, Bacin kice mani tare
zamu dinga kwana dashi, Allah. 'ban komawa". ‘ ‘
_ Kaka ta ce "Muhammad-dan' Abdullahi! Yanxu
dan banzan yaron nan bai zo ‘ba can bifi yai
zamansa? Cafdijan! Yanzu, don iyayensa bai san
dake aka fara daura auren ba kuma kece babba
shi ne yaje yai mana haka? Wannan Yaro Allah
Yai maka'yanda kai ' mana“. 'Mutancn dake.
tsaitsaye akansu ganin abin zai yi zafi suka soma
ba da’ hakuri', Yaya rabi diyar qanwar Kaka.ta‘
ce' . '
"Haba ai abin bai yi zafi haka ba, .
. .tunda dai can ya fara sai ku kyale shi, ai kwana
‘bakwaine dole zai dawo kuma k0?" ‘ ' .
Kaka tace "Kada ma ya dawo, nizai, dauka
mutuniyar banza? Wato ga 'yar tsaron gida an
kawo masa, ai wallahi yanzu zan miqe Kafata
qafarki har birin yanzu~yanzun nan, ai ‘ ya kaini
naga gidan, na sani kuma zan iya kai ,kaina, sai
dai suci amarcin.nasu a lare" .
zallah
RIKON KAKA
CHAPTER13
Yaya Rabi tace kar ki haka don Allah Inna, wallahi
abin magana ne zaki janyo mana kawai". "Ta
kashe ku maganar Rabi batun zuwa kam babu
fushi, sai dai in bana numfashi". Ta zabura ta
mike, "Tashi muje Jika,. ai banga ta zama ba wai
an sace dan barawo". Murna ta kama Rukayya
wai za'a kaita birni, Kaka ta mike taja zanin
atamfarta ta yafa, ta dubi jika. "Yi maza harhada
kayanki muje"; Rukayya ta nufi wurin buhun
kayanta ta zazzagesu ta zazzaba ta kulle a zani
guda ta dauka, Kaka ta tasa ta gaba suka tafi,
mutane na bawa Kaka baki amma taki ta saurari
kowa. Suna lafiya kan hanya Kaka na fadar, "Har
ni za,a kawowa iskanci banza Ai wuyar ta kawai
ku hadu amma indai aka hadun. Jika kartyar duk
wani da namiji, don ma kedin ga_ki ga yadda
kike, amma dake wata ce Jika ki zage ki
kwatarwa kanki 'yanci, duk wannan tsoron nasa
da kike ki ajiye shi gefe kija mijinki a jikinki, tunda
banga abinda wata mace ta fiki ba. Kuma ki bude
baki ki rinka magana, in ba haka ba. kishiya zata
raina ki ta maida ke sakarai. Da munje don Allah
Jika ki bude baki ki nuna mata kema fa ba
kanwar lasa bace".
.jika ta duka ta Ciro takalminta guda dan maradi
da ya tsinke, ta dauki leda tana gyarawa, tace
"To Kaka ai da naje da ta sake tai min wata
magana sai dai taji naushi a baki kin san ni qarfi
gareni fa Kaka, kullum ni ke ba 'yan makarantar
mu kashi"._ ‘
Kaka ta ce, "Haka nakeso Jika, ashe dai kina
ganewa".
Rukayya ta tuntsire da dariya wadda tasa har
akuyoyin dake kiwo cikin bola suka kwasa -aguje,
a haka har suka qaraso bakin hanya, suka; tsaya,
suka tari mota suka hau tayo Katsina dasu.
**************
Abubakar anci amarci, an angwance sosai. Kallo
daya za kai masa ka tabbatar yana
cikin farin ciki don tunda gari yai haske‘ya mike
ya nufi kicin ya sanar da kuku abinda zai shirya
masu na (break fast), sannan ya dawo falon ya
gyaggyara, ya nufi (toilet) ya watso ruwa ya fito,
ya zauna gaban madubi ya shirya‘sosai, ya gyara
sumar kansa da mayuka, sai Kyalli take, sannan
ya mike ya nufi kan (wardrop) din dakin ya Ciro
qananan kaya na shan iska irin na Turawa ya
saka, ya mammatsa turare a jikinsa, sannan ya
nufi kan gadon da Suhailal ke kwance tana ta
sharar baccin da bata samu yi ba jiya.
Abubakar ya kwanto jikinta yana hura mata iskar
bakinsa, Suhailat ta Kara gyara kwanciyarta, ta
Kara kanannadewa a jikinsa ta ci gaba da
baccinta, Abubakar yai murmushi ya kira sunanta
a kasan makoshin sa, ta bude idanuwanta da
kyar ta kalle shi, sannan ta maida ta lumshe.
Abubakar ya kai bakinsa yai kamar zai sumbace
ta, ya dan cije ta a lebe kadan. Suhaillat tai
saurin bude idanuwanta tana kallon shi kamar
mai shirin yin kuka.
Yai murmushi, "Ki tashi rana tayi sosai fa, dubi
agogo sha biyu da mintina yanzu ki tashi ki
watsa ruwa za kiji dadin jikinki sosai (my l0ve)
Suhailat ta bata rai kamar mai shirin . kuka, tace
. "Amma don Allah yanzu sai ka tashe nik0 _
tausayina ' baka ji?
Abubakar yace "(Am sorry my lovelyM wife)".
Kafin tai-magana har~ya sureta ya nufi' toilet din
cikin dakin da ita.
**************
Me keke napep ya, faka babur din sa a. Kofar get
din gidan Abubakai', Kaka ta fito' tasa hunnu
cikin dan lalitarta ta ciro kudi ta bawa mai motar,
sannan suka 'nufi (gate) din gidan. :Rukayyah ta
dora kullin tsummokaranta akai suka ,shiga
kwankwasar gidan, mai gadi ya miqe ya bude ya
gansu a tsaitsaye kamar mabarata Kaka tace "Ai
nan ne gidan Habu k0?"
Maigadi ya ce "Nan nc, sannu da zUWa".
Ta amsa da, "Yauwa".
'Sannan ta ja hannun Rukayya suka. yi "cikin
gidan, mai gadin ya bisu da kallo. Bai. ' manta da
tsohuwar ba, ita ce wanda mai gidansa Abubakar
ya kawota taga gidan, ya ‘sanar dashi kakarsa ce
amma in ba haka ba ta yaya zai barsu su shigo
masu gida? Mutane
kamar sundawo daga aikin gona. Ya‘kada kai ya
nufi dan dakinsa da aka . ware masa.
Kaka ta tsaya 'a bakin kofa .suna bubbugar kofar
kamar wadanda zasu Balle kyauren. suna (toilet)
suke jiyo bugun kofar, Abubakar har'ya fara
qulewa, a dolc ya sakar masu shawa suka
dauraye jiki suka nado tawul cikin hanzari suka
fito.
Suhailat k0 dan kwali bata tsaya dauka ' ba
ballantana ‘hijab, tai qofa da saurinta ta bude
don, ganin kowaye? Tana budewa suka shiga
kallon-kallo.
Cikin rashin fahimtar k0 su waye tace
"Lafiya. Baba‘? (my; dear) zo kaga wani ikon
Allah, almajirai har cikin falo".
Abubakar .dake qokarin saka jallabiyya yai saurin
zirawa ya fito yana fadar. ‘
"Almajirai kuma. my love? mai gadin baya nan
ne?" , .
' Turus! Ya tsaya yana kallon Kaka da Rukayya,
gabanshi yai wata mummunar ' faduwa har
kanshi sai da ' ya sara, cikin
makyarkyatar murya ya ce
."A'a kaka, kune? lkon allah
_ Ya dafa kai ya raSa ta cewa, yasan tabbas
asirinsa ne ya tonu Yasan tilas kaka sai ta_ fede
biri har wuziya. .
_ Suhailat dake tsaye ta dan sassauta murya
"(Am sorry)wallahi kaka ban san ku bane kuyi
haquri Muna (bathroom) ne shi yasa ku kai ta
bugun kofa Shiru
‘ Kaka datai mutuwar tsaye saboda_ takaici, tai
karfin halin fadar. . ' ' "Ki zagemu da kyau
yarinya dai wuri kika samu ai
dole kina tunawa da rama, wato kina baza ‘
rama, a' a ba rama ba lafasa ma" ". ‘ Duk yanda
Suhailat ta kai ga dakewa sai da daria ya ta kusa
kufce mata, tace. ‘ "Wayyo! Ba baza rama naCe
ba Kaka,
' (bathroom) na ce, dakin wanka". Kaka ta ce,
"Indai rainin wayo ne kinji
"dashi yarinya in kina nufin kin rainanine iyayenki
ma kauyen ne asalin su, kuma sai shege ke raina
mafarinsa ba dai dan halak ba, sannan kuma. .. .
Abubakar yai saurin tarar zancen, don ya tabbamr
yanzu ~Kaka ta Ballo masa ruwa,‘ ya ce.
”A' a’ yi hakuri don Allah Kaka, mu shiga daga
ciki sannun ku da 'zuwa"
kaka ta watsa masa harara.
" Kai rufemin baki, soko kawai. Ai dama nasan
hakan ce zata faru shi yasa tun farko na , hana
abin nan aka dage. ". TaJa tsaki. , , "Mu
ShigaJika kinji".
‘ Kaka; ta fizgi hannun, Rukayya ta bita kamar
zariya tun shigowar su gidan jikinta yai sanyi ta
rinqa bin gidanda kallo da matar gidan wadda ke
tsaye jawur da ita da tawul a jikinta sai ka rantse
da allah baturi yace, ga fari ga 'kyau, gashin nan
ya sha ruwa duk ya mammanne a kafadunta.
Kan kujera suka dire, Abubakar da‘ ' jikinsa ya
gama yin la'asar ya dubi Suhailat muryarsa a
raunane, ya ce
”Am sorry (my love) kar ki damu da ‘ rigimar
Kaka don Allah, kin san haka nake fama da ita,
rigimammiya ce sosai" ~
Suhailat ta ja wani gajeren murmushi, tace"Ba
komai (my dear) muje kada ranta ya Kara Baci
. ‘ Abubakar ya ce "A‘a, kije kawal daki ki ‘
shirya, kar ki damu zan iya da ita" ' Suhailat tace,
"Ahh. No my dear, muje
na soma rallashinta tukunna, don ba xanso
ta qara fusata dani ba". Abubakar ya ce “A"a kar
ki damu kije
ni zan ji da ita" '
Ta ce. ”A'a, kai gaban ka barni Dear". Cikin
tsananin rudani Abubakar yai ta
maza
ya bata"rai Wai ya zamu zauna muyi ta gardama,
' nace kije kawai k0?" _ Suhailat ta kafa mashi
idanuwa cikin
tuhuma, kafin tace. .
.' ‘ _ "Anya Dear ‘ba akwai abinda kake
‘kakkarcwa da baka son in sani ba? Meye?" 'Au
wai nan zaka girkemu kamar gumaka?”
' Suka ji muryar. Kaka ta daki dodan
kunnuwansu, bai iya bawa Suhailat amsa ba ya,
nufi wurin kakar a hanzarce ya duqa gabanta
cikin rudu yace. “ ”Don girman Allah Kaka kar ki
fada
:mata RuKayya mata tace wallahi mugun kishi ne
da ita", '
Kaka tace "Ina ruwana yau sai dai ya kasheta,
kishin karuwar banza. Ai wannan daga gani kasan
ta zagaya .ina ganin idanuwannaN nasan
tantiriyar' yar... _ Abubakar ya zabura ya dafe
mata baki._ yace don 'Allah ki daina kaka, matata
cefa kuma,
kin san ko a Musulunci babu kyau Irin wannan
Daga shigowar ki kita aibata min mata,ba
kyau irin haka wallahi". Kaka ta ture mashi
hannu. "Kai ni kyaleni kaji, ai dama idonka a
rufe yake, ba zaka gane abinda nake fada ba
tunda an riga an barbada maka kaci ka sha, kai
wanka shi yasa. aka dauro maka aure da
yarinya ka. .. . Abubakar yai saurin amshe zancen
da
‘ fadar. "A'a Kaka, kar muyi haka don Allah don
Annabi, ki rufa min wannan asirin" . Suhailat ta
nufo su da murmushin karfin hali a. fuskarta, ta
ce. ’ . "My Dear .kar ka damu, indai ta nice to
kuwa k0 kadan babu ruwana da duk kalaman da
Kaka zata fada akaina don inka lura ai tsohuwa
ce. _ _ , Kaka ta dauki sallallami, idan ta dauki
wannan kafin ta dire sai ta saki ta dauki wani. ' '
Cikin gigita ta soma fadar, "Yanzu
sana'ar da ka soma kenan Hubu? Dama aikin da
kake kenan a birnin siyar da giya? Me giya? giya
fa Habu? Yau na shiga uku ni Salamatu"; Sai ta
fashe da kuka. ‘ Abubakar ya dafe kai "Yau ni na
shiga uku,

Please Login or Register in order to submit comment