Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a dunjya. ‘
HEHEHEHE SU HABU MANYA DAMAN DADIN
AURE NASA MUTUM yaji hawayen murna na zubo
masane ?
jama,a ku tauani duba
naku har kullum A,I,S KE CEWA BARKA DA
HUTUN QARSHEN MAKO
RIKON KAKA
CHAPTER 29
' Abubakar ya rinqa ririta Rukayya yana
shagwaBa ta hade da -lallashinta har garin Allah
ya Waye, bai Barta tayi komai da kanta-ba, dai _
dai da wanka shi yai mata da kanshi, haka A
abinci da hannunshi ya bata yana qara tattalinta
da lallashinta. Rukayya kuwa jinta take tamkar
zara a cikin taurari, ita da kanta ta tabbatar ita
wata ta dabance a cikin mata mai baiwar da ba .'
kowacce mace bace ke da‘irintaba; don haka
taiwa Allah godiya don ta san ba roqonshi
ba ya bata, :kuma wadanda basu sami irin nataba
suma ba laifi sukai mashi ba ya hana su.ba
Bayan wata guda duk wanda ~ya kalli Abubakar
yasan ya samu canjin rayuwa,' yai wata kiba
kamar bashi 'babya qara sauyawa ya zama wani
na daban a cikin 'yan uwansa maza.
Duk wanda ya kalle shi yasan. yana samun‘
tallali da kular data dace ‘a wurin matarsa,‘ don
Shi kanshi bai san haka rayuwar aure take da
dadi .ba sai yanzu. Ashe da can ‘ haukan banza
yai‘ tayi ga inda dadin auren yake‘yaje yana ta
wahala a wani ‘wuri can.
‘ Shi da kanshi ya_maida 'ta makaranta‘aji
shidda zafa Zana jarrabawar aji shidda Wadda
zata bata_ damar shiga babbar makaranta don
yin karatu mai zurfi.
***************
Bangaren Suhailat kuwa al'amura sun gama
dagule mata duk yanda ta motsa al' amarin
ba haka suka kasane mata ba
don kuwa a ranar da abubakar yaje har gida ya
fadama mahaifin suhailat din abinda ke faruwA a
tsakaninsa da Suhailal din a ranar ya dauki
mataki yaje da kanshi ya ce ta koma gida
zai rufe gidan ya zuba' yan haya . . Abin ya bata
mamaki, Sai dai bata da
damar yin magana don bata ga fuska a wurin
mahaifin nata ba, a'dolenta taja bakinta ta tsuke
ta dawo gida kwana daya, kwana biyu tana zaton
mahaifinta zai kirala yaji ba’asin ‘ abinda ya
hadata da Abubakar din daga bakinta, amma
bai'nemeta ba ta kuma sani duk abinda ya faru
Abubakar ne ya shirya matA makarkashiya.
Sati daya, sati biyu har. zuwa wata daya babu
wanda ya ce Suhuilat ci kanki. 'ta soma 'damuwa
ta shiga matukar tashin hankali kewar'mijinta ta
fara damunta tun tana boyewa har ta soma
gazawa ta fara yiwa momy dinta maganar amma
sai cewa tayi babu. ruwanta, taje taiwa
mahaitinta magana.
Suhailat ta kasa tarar mahaifinta da zancen har
saida takwashe sati guda, ganin
babu sarki mahaifinta tai mashi maganar.
' Amman sai ’da taji da ma bata jeba saboda
yanda ya rufeta da masifa ta. ta inda yake shiga
ba tanan yake fita ba daga karshe ma sai cewa
yai Abubakar yake jira idan ya gaji da qin
kumawarta gidansa ya aiko mata da lakardar
saki. '
Abinda ya dagawa Suhailat hankali kenan, ta sani
babu abinda ta rasa a gidanta sai tattalin miji da
soyayyar da bata faduwa. Lallai dole ta shiga
cikin matukar firgici, to amma yaya za'a ce babu
wanda' zai kira Abubakar balle a sasanta su ta
koma gidanta? ldan ma hakan bata samu ba 'ai
sai a tura manya su rakata, ya za ai aCe ita
kadai zata koma gidan Abubakar‘? Anya idan akai
mata haka an mata adalci kuwa? Anya ba‘a nemi
kwararar mata da aji ba a idanuwansa?
‘ Wannan ne k'esata tai ta kuka ba‘bu mai
lallashinta, shin wai waye ne zai fahimci halin da
take ciki‘.’
Bayan wata biyar Rukayya ta kammala zana
jarrabawarta ta fita sakandire ta zana jamb
Abubakar ya samar mata gurbi a' Jami'ar Umaru
Musa 'Yar Adua zata yi karatu a bangaren
likitanci (MediCine)._ ‘
Rukayya karatu ya kankama don ma laulayi da ya
matsa mata, sauqinta ma daya Abubakar na
taimaka mata da wasu aikace~ aikacen. ' '
Cikin wata goma cikin Rukayyay ya fara fitowa,
Abubakar ya bar mata motarshi shi kuma ya siyi
sabon mashin Motobi yana hawa kafin Allah Ya
qara buda mashi ya sake siyen 'wata motar
shima ' Rukayya ta zama wata zara a cikin
taurari ta canza, ta sauya, ta xama wata daban a
cikin mata duk wanda ya kalleta saiya so ya sake
kallonta saboda yan'da ta zama wata ishasshiyar
mace ‘mai ta‘qama da namijin maza, da kuma
matakin ‘karatun .(dcgrce) ”wanda take akai.
‘ Cikinin rufayya ya shiga watan haihuwa don
haka ta dauki hutu a makaranta, don likita '
ya tabbatar mata nan da kwana biyar zata iya
haihuwa.
. A yanzu hak-a a zaune take saman' carpet tayi
dai-dai .Abubakar yana zaune a gabanta yana
yanka'mata'tufa (apple)_ yana Saka mata ” a
baki aka kwankwaso kofar falon: Abubakar ne ya
bada izinin shigowa, sai dai wa zasu gani? » ~ .
Suhailat ce ta sha lullubi,kafadarta . _ rataye da
qatuwar. jaka, dayan hannun kumana
jaye da qaton akwati K0 dar Rukayya bata ji ba
lokcin da taga shigowar Suhailal din,Abubakar
kuwa zabura . ya yi ya mike, ya daga murya yana
fadar. "Lafiya? Me ya kawo ki gidana?" SUhailat
bata tanka mashi bahar ta Karaso sannan ta
soma fadar ’ ‘ "D0n Allah Abubakar kayi hakuri ka
mantada, abinda ya faru nasan nayi laifi kuma
nayi
nadama ka yafe min
Abubakar ya ce, "To amma neman gafarar ne har
sai kin biyoni cikin gidana?" Suhailat ta dago kai
da sauri tana kallonshi da idanuwanta da suke
zubar da hawaye Ciki" tsananin kaduwa ta soma
girgiza' kai tana fadar.: "Abubakar, kar kai min
haka,'ka yafe min don Allah tunda na gane
kuskurena. Wallahi na gaza jurewa rashinka
Abubakar, ba zan iya rayuwa babu kai b_..."..
Kuka ne yaci. qarfinta, ta ja kafafuwanta wurin
Rukayya ta rungume kafafunta tana kuka da
hannu alamar ta taimaka mata.
Shi kuwa 'Abubakar tsaki yaja don haushi ma '
take bashi. Ruqayya ta dafa Suhailat tana fadar. .
"Ya isahaka Suhailat, ki daina". ,
Suhailat ta ‘ dago' kai tana kallon Rukayyar cikin.
kuka ta soma fadar. .
"taya xan iya daina kuka Rukayya ' bacin son
zuciya ta da hudubar shaidan sun rinjayrni na
rasa mijina'na janyo haushin iyayena akaina?
Rukayya Ya Ya za ai in daina
na 'zalunce ki saboda ' son zuciya kawai?"
Rukayya ta kyara mata kai tana fadar.
"A'a ki daina fadar, na yafe miki kuma Abubakar
ma ya yafe miki, kawai dai .yana cikin Bacin rai
ne nasan zai haqura".
Rukayya ta takarkare ta mike da kyar tana kallon
AbUbaKar wanda_ ya bade mata fuska, ta matsa
daf dashi ta riqo hannunshi ta
‘ . riKe' ta soma magana muryarta a sanyaye.
"Don Allah Yaya na ka zamo mai yafiya da kuma
karBar uzuri ga wanda yai maka ba dai dai ba. Ka
dubi Suhailat ta tuba tayi nadamar abinda ta -
aikata, ni na yafe mata kaima ka yafe mata ka
karBeta‘sai kaima Allah Ya yafe maka
kurakuranta wanda ka sani da ma wanda baka
sani ba
Abubakar ya. danyi shiru yana 'wani nazari,
Rukayyata girgiza hannuwanshi tana fadar.
‘ "Please Yayana, plcasc". Abubakar ya sauke
numfashi yana fadar.
"'Shi kenan,’ na yafe mata saboda ke ‘Rukayya,
ina sonki kinfi qarfinkomi a wurina, babu abinda
bazan iya yi miki, ba a duniyar nan. Rukayya na
yafe mata".
Wani irin farin ciki ne ya lulluBe Suhailat, ta
rungume' Rukayy cikin matukar soyayya 'da
qauna. Rukayya ta cika mace ta gari tunda har.
ta amince da sadata da farin cikinta, wato‘
Abubakar.
ltama Rukayya ta “saki rai da zuciyarta
' suka rungume juna ita da Suhailat suna masu
.yarda da aminci da Juna. '
. Abubakar na tsaye yana kallonsu bakinshi dauke
da murmushi, zuciyarshi na fatan su kasance a
haka har qarshen rayuwarsu '
MASHA ALLAHU.
ALHAMDULILLAHI.
MU HADU A WANI SABON LITTAFIN IN ALLAH YA
YARDA KUDAI KU KASANCE DAMU A KODA
YAUSHE
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment