Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta haka ya rinwa janta har" gida
ya hankada ta tsakar gidan, Ya dauko igiyar guga
ya shiga zabga .mata tana ihu. . Bai ji shigowar
ta ba sai dai yaji kukanta. "Kashe ta zaka yi?
Jama'a ku taimaka, zai kashe marainiyar Allah".
Tana ganin kakar ta kwasa aguje ta rugungumeta
tana ihu, kaka tace
"Cewa naika kirata ka duke ta? Ba 'ccwa nayi ka
nemo min ita ba?" ‘
Cikin takaici Abubakar ya cc, "Duk abinda
yarinyar nan~ke yi duk laifin ki ne, ke ke lalata
ta. Wallahi indai ni zan ci gaba da saka hannuna
a cikin lamarin wannan to wallahi dole ne in
hukunta ta tunda dai ita haka Allah Ya yi ta bata
jin magana k0 miskala . zarratin, kuma harda
hadi da kin shagwaba ta,
kinsa ta raina kowa, bata .ganin kowa da
mutunm, to ni dole na hukunta ta wallahi" "Ina
Naira ta dubu‘?!". ‘ '
Ya daka mata tsawa, tai saurin sakin kaka tana
lalube-lalube a jikinta, har' da su kwance kallaba
tana dubawa.
Abubakar‘ yai murmushin takaici kafin ya ce, "Kin
yar k0? Da kyau, kinwa kanki don wallahi tallahi
sai dai kiyi sallar haka, fada kuma kar ki fasa, ki
tayi, ban ce ki daina ba".
‘ Ya yar da igiyar gugan ya wuce dakinshi
abinshi. Rukayya ta kara fashewa da kuka, "Na
' yar da kudin Kaka wurin kallon' yan kura, bari
inje in dubo". ‘
Kaka ta ce, "Ya za ai ki gansu Jika? Ai ba za ki
gansu ba, kiyi hakuri kawai in lallaBa shi ya Kara
miki". .
Cikin kuka ta ce, "Ai ba zai Kara min ba". .
Kakata ce, "Ya. ma isa? Share hawayen ki, ki na_
zaune sai ya kara su k0 da ya rantse sai dai ya
yi azumin kaffara".
Rukayya ta share 'hawayénta tabi kaka dakinta
tana fadar.
"Dubi, inda ‘duk ya ji min ciwo, wallahi yana
tafiya sai na rama a wurin ragunan sa". ‘
Kaka ta ce, "Shcgun ragunan ma da . kullum ke
ke dawainiya da su amma bai gani, kullum ya
kama ki yai ta duka. Wata rana sai na baSu
shinkafar Beta sun Ci sun mutu inga ta tsiya,
kema ki hula. Allah Ya 'soki ma an kusa kwashe
su ki sami sauki"
Rukayya ta ce"Shinkafar Bera ita ke kashe su
Kaka?"
Ta ce"Sosai ma, ai k0 ke kika ci sai kin . mutu ba
raguna ba". *
Rukayya tai shiru zuciyarta na saqa da
warwara.
Kaka tace, Tashi ki dauro alwala kiyi sallar
magariba".' ' ‘
. “Bata ce Kala ba ta miqe ta nufi wurin da . ake
ajiye butoci ta dauka ta nufi kewaye
Ana gobe daren sallah Abubakar ya karbo
dinkunan sa dana Kaka ya kawo mata yana nuna
mata.
Rukayya na kwance saman gado tana kallon su,
dinkunan shi kala uku, na Kaka kala
biyu. .
Sai data gama ganin nata sannan ta ce.
"Ina na Jika?" ‘ .
Ya ce ”Wacce Jika Kaka? Ai na rantse tunda ta
zubar da kudin wurin fada ba zan qara fitar da
wasu in bata ba, wallahi sai dai tai
sallar haka". _ ' Kaka ta jefa mashi nata, "Ai ko
indai ba _zaka amsowa Jika nata ba to nima ban
so, wallahi sai dai ka hada duka ka rike". ‘
Abubakar ya ninke kayan da ta jefa masa suka
zube qasa, ya ce_
"Ba zan tafi da su ba, sai dai in kinji ' haushi ki
kyasta masu ashana su qone, koki bada sadaka
duk daya wai makafi sunyi dare, kinga tafiya ta".
Ya wuce abinshi ya bar mata kayan
Rukayya ta fashe da kuka tana harbeharbe da ta
tabbatar ya tafi Kaka ta ce, "Ke yi shiru Jika, ai
dama so
yakc ya‘ sa ki_ kuka, idan kika yi ai kinga yai
nasara Ki kyale shi dole ya amso miki dinkin
Inma bai amso ba sai ki saka wadannan nawa
Tana kukan Rukayya ta ce, "Wadanne zan saka?
Wannan dinkin tsaffin su zan saka?
Allah Ya sauwake" . ' Kaka ta ce, ”Ba sai ki ba da
su a rage
miki ba?" Ta ce, "Allah Ya sauwake ni dai ban son
su, nawa nakeso". . Kaka ta ce, "To kiyi shiru
haka nan
muga iya gudun ruwan sa".
Ta samu da kyar tai shiru,“ amma zuciyarta na
mata sake-sake kala-kala. . ' ' ‘ Cikin dare duk
sun‘ kwanta barci amma Rukayya ta kasa barci
saboda tunanin rashin kayam sallah, ta tashi
zaune tana tunanin abinda zata yi itama ta‘
guma masa. Can ta tuno'da
shinkafar bera da Kaka ke ajiya a karkashin gado
saboda Beran dake matsa masu.
Ta lallaBa ta dauko ta tamkar wata munafuka, tai
sadaf-sadaf ta fita waje ta sami kwano ta zuba
shinkafar ta zuba 'ruwa ta lallaba ta nufi wurin
ragunanshi. Duk sun ma yi bacci,‘ ta girgiza
gudayana motsawa .ta miqa mashi. Kamar jira
yake ya kafa kai ya sha sosai.‘
Ta nufo gudan tana girgiza shi, yai kuka
"Beyyy!‘ tai mugun tsorata ta zubar da ruwan. ‘
ta ruga daki aguje ta kudun dine saman gado.
K0 minti biyar batai da kwanciya ba taji ragon ya
soma dire. dire, Abubakar ya fito daga . .dakin shi
hankalin shi tashe, ya kwance ragon yana duba
shi. '
Ragon ya fadi yana harbe-harbe, Abubakar ya
rude yai dakin Kaka aguje ya tayar da ita yana
fada mata rago ba lafiya, ta rude sukai waje. .
A lokacin har jikin ragon ya saki, sai kumfa da ke
fitowa daga bakinsa.
Kaka ta ce, "Maza dauko wuqa ka yanka shi,
gazawa zai yi".
Abubakar ya juya ragon ya kalli gabas, ya ce
"Bismillahi, Allahu Akbar". Sannan ya yanka. ,
Jikin Abubakar ya mutu saboda gazawar ragon
nasa, duk cikin ragunan yafi kowanne girma, Naira
dubu hamsin sukai cinikin sa gobe za a zo a
dauka. Don haka babu wani kuzari a jikinsa ya
tafi daki ya kwanta, sai dai batun barci babu‘
labarinsa, ita kanta Kaka sai data dau lokaci kafin
baccin ya dauke ta.
Rukayya k0 dadi ne dankare a zuciyarta, tana
labe tana kallon su. Yanda ta ga Abubakar ya
rude sai yai nan aguje ya dawo nan aguje dariya
kawai take masa har da rike cike, ta rufe' baki
don kar wani yaji ta.
Tunda sanyin safiya Abubakar ya tashi ya tafi, ya
kira mahauci don 'siyar masa, gashi ranar sallah.
'
Tare suka dawo da mahaucin, ya duba ragon yai
masa kudi dubu ishirin.
Babu yanda ya iya haka ya ce ya bayar, a take
ya kirga kudin ya bayar sannan Abubakar
ya tafi dakin Kaka ya fada mata yanda aka siya
Kaka ta ce ”Anya Habu ragon nan bai mutu ba
aka yanka?" .
Abubakar ya ce, ”Kai Kaka, Allah Ya sauwake, sai
kace dai ba Musulmi ba zan yanka mushc? To ko
da na yanka shi sai da ya harba, yanzu inda
gabansa kika fadi wannan ai kinga ba zai siya
ba".
. Kaka tace, 'A'a, ai nidama ban sone ka aikata
abinda Ubangiji zai yi fushi da kai ne' .
Abubakar ya ce, “To bai mutu ba na
yanka, yanzu ma buhu zaki ara mana zai fede
anan.
Kaka ta ce, "To bari in duba maka” .
Rukayya ta mike simi-simi ta raba Abubakar ta
wuce tamkar wata tsohuwar munafuka, ta nufi
wurin mahaucin tace masa ‘ "Baba ragon nan sai
da ya mutu aka
‘ yanka shi, kar ka siya".
Mutumin ya zaro ido yana mamaki, kamin yai
magana tai saurin rugawa daki abinta ta
haye kan gado“ Kaka ta zakullowa Abubakar buhu
a
Qarqashin gado ta bashi, ya fito. "Yauwa ga
buhun Baba Halliru". Da
yake haka ake kiransa a garin. Ya ce "Riqe shi
nan wurinka Abubakar,
bani kudina". Gaban Abubakar yai wata irin
faduwa,
ya ce
"Saboda me Baba?" ~
Ya ce "Saboda ni ba mutumin banza bane irinka
da zan siyi mushe in saida wa al'ummar
Musulmai. Ba
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Baba wallahi ba
mushe bane, ni na yanka shi da hannu na
wallahi". '
Ya ce”Kai kaga ni dai ba abokin wasanka bane,
ka bani kudina kawai ban siye na fasa Kanwar ka
da bakinta ta fada mini mushe ne ka yanka. wato
ga mutumin banza ko
Idan bakwason wannan littafin kuyi magana mu
canja
zallah shared a profile .
RIKON KAKA
CHAPTER5
zaka siyar mawa, to ban siye, ka bani kudina
kawai". ‘
Sunan qanwarsa da ya ambata shiya bugewa
Abubakar 'dukkanin gaBoBin jiki, jikinsa a sanyaye
ya sa hannu ya Ciro kudin a gaban aljihunsa ya
mika masa.
Ya amsa yana fadar, "Mutanen banza kawai gaku
Musulmai amma kuna aikata aikin kafurai,
marasa tsoron Allah kawai".
Abubakar dai bai tanka, masa ba. har ya fice
banda zafi da:. Kuna babu abinda zUciyarsa keyi,
yaji ya tsani ragon, bai son ma gaminsa
Yajasa ya fita waje ya sa
yaro yai masa sallama da makwabcin su malam
Bala talaka ne . Yana fitowa suka gaisa da
Abubakar sannan ya ce
' "Baba, dama ragona ne zai gaza, nasan kana
jinmu ma wata kila jiya. To shine na yanka, yau
na kira mahauci ya taya min shi yanda nake jin
ba zan iya siyarWa ba, gara ma na ba da shi
sadaka na San ladan tawa tana
wurin Ubangiji tunda mu ma za muyi layya shi
yasa na ce bari inzo in maka magana ka aika a
dauko maka".
Malam bala ya shiga godiya yana zabgawa
Abubakar addu'a, shi dai bai ce komai ba ya
wucc ya koma gida, Malam Lado ya turo yara
suka daukar masa ragon.
Abubakar ya dauki buhun ya maidawa
Kaka, ya ce ”Ga buhun ki". Kaka ta ce ,"Yo ya
fasa fedewar ne?” Abubakar ya ce, "Hmm! Idan
kun bari ba Kaka ta ce, "Kamar yaya kuma in
mun bari?" Ya ce, "Kamar yanda kika kitsa mata
taje ta sanar da mahaucin mushe ne na yanka”.
Kaka ta dauki Salati da sallallami, kafin
Ta hau rantse-rantsen ba ita tasa ta ba". Ta ce
"Ke Jika, wannan kuma wacce dabi'a ce za ki
tsiro mana da ita ne?”
Abubakar ya ce, "Wadda ki ka' koya mata, duk
abinda fitinanniyar yarinyar nan ke
Keyi kaka daurin gindinki ne take samu. Amma ba
komai, ni nasan maganinta, ba zai yiwu yarinyar
nan ta sangarce ta lalace ba, tunda har ta iya
wannan gaba ban san abinda zata yi ba, idan ta
Kara girma a haka to abin kuma sai yafi haka.
Don haka makarantar boko zan saka ta, taje can
ta koyi tarbiyya".
Kaka da dauki Sallallami, "Wa za ka kai
makarantar Abubakar? Jikar? Baka isa ba,
wallahi babu inda za ka kaita a lalata marainiyar
Allah. Ka kai ta makaranlar boko ta koyi tarbiyya
k0 ta koyo iskanci?" Abubakar ya ce,"'Oho dai, ni
dai na fada miki, k0 kina so k0 ba kya so sai na
kaita". .
‘ Ya juya ranshi na suya ya ’bar‘ dakin, . yana jin
Kaka na rantse-rantsen babu me kai mata jika
makaranta.
Anci sallah lafiya, Kaka tayi layya ta
yanka dan marakinta, Abubakar bai yi ba don
gaba daya ya sai da ragunan sa,. ya ce kuma ya
gama kiwon.
Jika kuwa kayan Naira biyar bai siya mata ba,
haka tai sallar da tsofafin kayan ta, shi ya saka
ma ko kofar gida bata leqa ba _ Ana gama hutun
sallah Abubakar ya je yai wa Rukayya takardar;
haihuwa, washegari ranar Monday tun da sanyin
saflya ya sa tai wanka ta sauya kayan jikinta,
sannan ya tisa ta gaba suka tafi.
Kaka tace, "Wai gidan uban wa zaka kaita ne
Habu? Na fada maka kar ka sake ka kaita
makarantar bokon nan, ban son ta”. Abubakar ya
ce, ”Ai ko sai dai kar ki so . ta, amma makaranta
na kaita na gama".
Ta sa kuka, yana jinta ya tisa‘ Rukayya gaba
suka ficce, can tsakiyar garin makarantar take
Sha ruwa Primary School, suka dauke-ta aka
kaita a‘ji uku, saboda ta wuce dauka.
Suna dawowa yaje ya yanko mata (uniform) ya
sai mata jakar makaranla da takalmi, sannan ya
sai mata littattafai.
. washe gari da kanshi ya tayar da ita ta: shirya
ya tisa ta gaba har kofar
makarantar, ya bata Naira ishirin kudin tara;
sannan ya wuce wurin aikinsa.
Rukayya 'yan makaranta, karfe sha biyu aka taso
su daga makarantar, amma idan ka ganta ba
zaka ce ita ce tajc makarantar da sabbin kaya ba,
tai musu budu-budu, farar abayar har ta fita
daga kamannin ta.
‘Tana dawowa gida ta fada jikin kaka tana
murna, Kaka ta ce
"Oh Jika da tsiya dai Habu sai daya kai ki
makarantar nan don yasan ba yanda zan yiko?"
Rukayya ta ce "Kuma Kaka sai da aka buge
ni, dubi baya na".
Ta cire abayar ta nuna mata, wurin yayi
,rudu-rudu da zanen bulala.
‘ Kaka ta ce, ”Wane dan iskan marar imanin ne
yai miki wannan dukan? Shi yasa na ga fuskar ki
‘ da zanen hawaye". Rukayya ta ce "Wani malami
ne, wai daga muna fada ya ka mani yai ta bugu
ni kadai”.
‘ Kaka ta ce, ”Matsiyaci, ya kama ki yai ta duka,
to Allah Ya isa, tsinanne lnsha Allah bai gamawa
lafiya, kawai ka kama 'yar marainiyar
Allah kai ta bugu kumar ka sami mandiri. Bari
Habu din ya dawo Jika, wallahi ba ki komawa
makarantar, sai dai yai duk abinda zaiyi, dauko
furar ki gata can ki sha".
Rukayya ta mike ta dauko kwanon furar tana sha,
ta ce. _
"Kuma Kaka har Turanci aka koya mana da waka,
amma wai (This is a boll, These is our Apple,
That is your watch)".
Kaka ta tintsire da dariya har saida sashinta ya
fito saboda bakin ba haqora, ta ce. '
"Kai amma abun da dadi, duk can aka koya
maku?“ ' Rukayya ta ce, "Eh Kaka".
Ta cc, “Ai don dai azzalumin mutumin nan da kin
Kara zuwa".
. . Rukayya tace. "Ai ban Kara zuwa nima tunda
buguna ake". . Da yamma likis Abubakar ya dawo
gidan .ya iske Rukayya da kayan makarantar duk
ta: musu duwan-duwan, takaici ya cika Shi
Duk inda wata qazamar yarinya ta kai rukayyah
Tafita: Kazanta , daga cikin abubuwan da sukesa
yake qara tsanarta.
Ya watsa mata idanu babu sauqi a fuskarshi,yace
'Wuce kije ki cire kayan ki kawo su wurin maguji'.
Ta mike a tsorace
ta nufi dakin nasu'.
Ya tsai da ita, 'Tsaya ki tattaro dukkanin kayan
daudarki kawomani'.
Rukayya ta daga kai
Ta shige dakin, shi kuma ya wuce Washegari
yana tashi ya nufi dakin Kaka ya tashi rukayyah
tai shirin makaranta
Kaka tace kai babu inda zataje donka jini nan jiya
suka kamata sukaita bugu kamar jaka don haka
bata komawa
Abubakar yace,'ldanta zauna nan me zatai miki?
Nan makarantar allo ce kikai kane kane kika
hanata zuwa wao bugunta ake , sannan kuma
itama makarantar bokon sai ki
hana? To wallahi .ko kasheta za a rinka yi tana
dawowa sai taje har makarantar allon sai ta
koma“.
Kaka ta ce "Tunda dama ba qaunar ta kake ba ai
dole ka kaita inda za a kashe ta saboda
mugunta, haka kawai ka dauki karan tsana ka
dorawa yarinya, ka kaita a kashe ta don Allah,
idan an tashi a aiko mani da kai da qafarta gida".
Abubakar ya finciko Rukayyar dake kan gado ya
jata suka nufi kofa YANA FADAR. ’
”Ba za, a kashe taba amma fa za ta daku kamar
ikon Allah”.
Bai ji abinda take fada ba don har ya kai bakin
kewaye, ya zuba mata ruwa a bokiti ya bata ta
shiga wanka.
Tana fitowa ya mika mata kayan makarantar ta
saka, ya ba ta mai ta murza ya zaro Naira
hamsin ya bata, ya ce.
Maza ki wuce ki tafi, kuma zan biyo bayanki
yanzu, ki tsaya wasa k0 da labe ne kiga ' yanda
zanyi da ke. Kina dawowa daga
makaranta ki ka ci abinci ki ka hula, ana kiran
sallar azahar kiyi sallah ki wucc makarantar allo
idan ba haka ba wallahi kika bari na samu labarin
baki zuwa na lahira sai ya fiki jin dadi wuce ki
tafi. ‘ Simi-simi ta wuce, daga daki Kaka tace.
”Yanzu baka barin tai kalaci haka za~ ta wuce ta
tafi?” , Ya‘ce, "Bata yi, ga Naira hamsin nan na .
bata ta siyi abinci ta ci". ' -Kaka tace, "Indai
mugunta ce irin taka ai ta wucc da haka Habu,
yanzu haka zaka kora , min ita bata ci komai ba
salon tai karo da mayya k0 maye su lashe mini
ita?” » ‘ Abubakar ya e, ”Su hadiye ta idan ta
tafi". ‘ , “ " Kaka ta cc, ”Ba bakin ka ba, me
mugun baki. Insha Allahu aniyar ka sai ta bika". .
Bai tanka mata ba ya wucc dakinsa yai nasa
shirin ya fice ya tafi wurin aikin sa, amma 'yana
can sai da aka kawo mashi kashcdi wai Rukayya
tayi fada da wani yaro har ta cije shi a hannu ya
fasa. Ya basu hawuri sannan yaje
“Tana dawowa daga makarantar tana hutawa
akai sallar azahar ta fito zata tafi makarantar
allo
Kaka tace, 'Yanzu zuwa za: kiyi k0? Mugun yaron
nan ya hanaki zama lafiya, duk indayasan za a
zalunceki saiya turaki Allah Ya saka miki'. .
Jika
Haka ta wuce makaran allon,.a can sukai sallar
la‘asar, Sai biyar na yamma aka tasosu
Tana dawowa tasamu Abubakar na gyaran cefane
cefane ta giftashi zata wuce ya ce‘
.. ’Kezonan'. , ta dawo gabansa ta durkusa ya
dubeta sosai kafin yace ,‘Wato saboda bakeke
wankinba shi ,yasa idan kika dawo makarantar
baki canja kayan sune na zaman gida kuma sune
na
Yawo cikin gari ko?‘
Shiru ba amsa, ya ce "Tashi kije ki ciri kayan ki
kawo mani".
Haka ta mike ta ciro ta dawo da su a hannu, ya
ce
"Dauki bokiti gaya can da ruwa kisa ki wanke".
Gaban‘ta ya fadi don tundatake bata taba wanki
ba, shi ke yi mata da kanshi. Haka ‘ ta mike taje
ta soma wankin kayan, yana kallonta har ta
gama ya amsa ya shanya. . .. ’ Sannan ya ce "ki
wanke hannunki ki , xo ki yanka mani alayyahun
can da albasa". ‘ Rukayya ta dubi hannun nata
babu abinda ya yi amma har sai ta wanke ya ce.
' "K0 baki ji ba?"
, Haka ta wucc ta dauki buta ta wanke hannun
nata sannan ta je ta zauna tana yankan
alayyahun ya dora sanwar taliyar sa,tana gama
yankan alaiyahun ya ce
Jeki ki zuba" Ta tafi zata zuba cikin tukunyar .yai
saurin daka mata tsawa.
‘ "Ke banza, haka za ki zuba shi? Barbada mashi
gishin' ki sa ruwa ki wanke". ’
‘ Ta dauki uban gishiri ta maka yana kallonta ya.
ja tsaki ta zuba ruwa ta wanke ta tsane shi
sannan ya ce '
"Je ki zuba". ' "
Taje ta zuba ta rufe, ta dawo gabansa.
"Na gama".
Ya ce, "Jeki shi kenan".
take ta nufl daki don kar ya qara saka ta wani
aikin
*** ******* ***
Wata ranar Juma'a RuKayya tana . makaranta tai
fada da (monitor) din ajinsu wai ta rubuta
sunanta cikin 'yan surutu, malamin ya buge
su.duka Shine fA yana fita ta ' kama monitar da
kokawa' gata ba iya fada tai ' ba, tai mata, duka
sosai. Akaje aka fadawa ' (headmaster) yazo da
kansa da bulalar sa ya zane Rukayya: radau har
tai fitsari saboda .
.azaba.
Yana fita ta dauki jikkarta ta gudo gida tana
kuka, ta fadawa Kaka. Ta ce, "Ai k0 yau sai ya
san ya debowa
kansa masifa".
Ta dauki mayafinta ta ce "Muje inga matsiyaci". '
Ta ja gida ta rufe suka dauki hanyar
makarantar har office dinsa ta kaita, yana
zaune saman kujerar dake gaban teburinsa sai .
wani mutum dake daga can gefe suna
magana. '
Kaka ta sawo kai cikin office din ba k0 sallama,
ta dubi mutumin dske saman _kujerar gefe tace. '
"Malam wurinka nazo, zuwa nayi inji uban da
yasa ka sa bulala ka rinka laftar mani
jika kamar ka samu jakka, k0 k0 shi Habu din
' nc da ya kawo ta ya ce ka sa bulala kai ta
bugunta harta ‘fita hayyacinta tai fitsari? To kotu
zata rabani da kai, wallahi sai nayi shari'a da kai,
sai ka bani labarin dalilin bugar mani 'ya babu
gaira babu dalili".
Mutumin yace Yi hakuri baiwar Allah, bani ne
(headmaster) din ba, gashi nan, nima zuwa nayi“.
Ta ce, "Karka sake ka zage ni’da turanci wallahi
na gaya maka, nima ina da
jika kamar ka dan makaranta" ~ Saurayin ya ce,
"Ikon Allah, yi hakuri don Allah Hajiya" ‘ '
Ya mike ya bawa (headmaster) hannu sukai
musabiha, ya ce.
"Ni zan wuce Yallabai, zan kira ka a waya k0 mi
kenan". _ Ya wuce abinsa ya bar (headmaster) da
rigima. ‘ . Da yake kwararren dan boko ne sai ya
mike daga kan kujerar da yake ya ce.
"Hajiya zauna, bisimillah sannu da
_ zuwa, bari akawo miki lemu". Kaka ta zauna
tana fadar, "Karka kaWO mani komi, dan iskan da
ya bugi Jika kawai
nake nema, wallahi sai na rama mata ,kaji na
fada maka
Lol ran kakafa ya baci mai zai biyo baya mu tara
later
a zallah shared a profile .
RIKON KAKA
CHAPTER6
, Ya' kwantar da 'murya, "Ayi 'haquri Hajiya,ai duk
abin bai kai na haka ba tunda ni da Jikar taki ai
duka jikokin ki ne,kua zaki' iya‘ hukunta mu idan
munyi laifi, ‘ musamman idan ki ka same mu da
rashin gaskiya. Kiyi hauri kakata, ba a daki
qanwa -ta saboda zalunci ba, ‘sai don laifin da
tayi, ta
; kama shugabar ajinsu tai ta bugu Idan kika, ga
bugun da tai mats sai kin tausaya matA
. shi~yasa. Sanin da nai k0 ke ce kika ga haka
sai» kin daki jikar. nan shi yasa‘ na hukunta ta
saboda gaba amman kiyi haquri kaka Kalaman sa
sun Shiga Kaka don haka ta ~sassauta fadan
tace "Gaskiya kar a sake bugar min jika saboda
wasu yara can, marainiyar Allah ce uwarta da
ubanta duk sun mutu; ni kadai na rage mata. In
bacin yaya'nta ma da ba mai jin magana bané ai
daga yau bata Kara dawowa' ‘ makarantar". '
Ya ce, "A'a ayi hakuri, insha Allahu za a kiyaye"
ta mike, "To sai anjima, Allah Ya _ taimnka". '
Ya ce "Amin Kaka"
Ta tasa Rukayya suka ficc daga (ofiicc) din,
(headmaster) ya koma ya zauna saman kujerar
sa yana murmushi, ya ce. _
"Ho! Allah Ya raba ni da ke lafiya" (Duk wanda ya
girmama tsohon wani shima ’za'a girmama nasa
a gaban idonsa k0 bayan idonsa
Da yamma bayan Abubakar ya dawo
~ daga wurin aikinsa yaji labarin zuwan kaka
makaranta, yai ta fada
' "Haba Kaka, .yanzu in bacin kin hadu da dan
mutunci ai da Allah kadai Yasan
yanda za ayi. Haba! ki ta abu sai kace kanki farai
jika? K0 ina sai kin fito da halin ki
To, "To ubaba, zoka dakan sai in san kaji haushi:
inba dukana kayi ba ai ban ssn kaji haushi ba
Abubakar ya ce, "Ai burinki inji haushi in fitar da
ita daga makarantar, kuma ba zan fitar da ita ba
wallahi ta zo ta dami al'umma, gara ta zauna can
duk wanda taimawa a zane ta".
Kaka ta ce, "A daketa din ni kuma dukwanda ya
bugar min jika idan naji sai naje na rama mata
tabbas".
_ ‘ Abubakar yace, “To shi kenan ki rama mata
din, hukumar makaranta ta sa a kama ki, wallahi
kuma k0 leke ba zan leka ba" Ta ce, "In ka tashi
ka manta dani k0 kasa a rufeni har dan makullin
ya bats" . ' Abubakar yai dariya ya ficce abinsa
don yasan halinta idan ya cika ta yanzu ta sa
masa kuka, ya tafi ya yo cefancn abinci ya_
dawo ya kira Rukayya, ya ce "Maza kisa tsintsiya
ki share gidan nan, idan kin gama ki min magana
ya wuce dakinsa ya barta tsaye".
Ta sumBuro baki ta rasa dalili kwanan ‘ nan da
yake takura mata ba yanda ta .iya, dolenta ta
dauki tsintsiya.ta share gidan
sannan taje ta sanar masa ta gama. --
Ya fito yace, "Hada itatuwa ki hura wuta, ai dai
kinga yanda nake yi?"
. Idanuwanta suka ciko da hawaye haka ta je ta
hada itatuwan yana tsaye yana' kallonta ya ce.‘
~ . ."To sa sabulu ki wanke hannunki ki . dauki
tukunya ki dauraye ki~aza saman ’
wutar". Haka yai ta saka ta aiki daya bayan '
daya har sai da aka gama girka shinkafa' da miya
k0 tsinke bai taBa da hannun‘ saba
Yasa ta dibar masa nasa; sannan ya ce. "Daga
yau aikin ki kenan a gidan nan kullum, don na gaji
komai ni sai kace dan daudu a gida.
_ Shekarar ki sha uku amma babu abinda kika iya
a aikace-aikacen mata, jikin ki ma ba ki damu da
gyaran sa ba balle na gida, , kullum kina, faMa da
qazanta 'da shegen muni kamar don ke aka yi
shi, Mtsw!".
' Ya wuce'dakinsa'ya barta tana ta faman
tukuki
"""""". """""""
. Lamarin Rukayya ya zama sai dai addu'a, don
ma Abubakar yana tsaye akanta
Wajen makarantar boko da ta all, idan kuma ta
dawo ya tisa ta gaba da aikin gida, yana zaune
yana bata umami haka zata yishi kotanaso ko
bataso
Kaka tai mitar tayi amma bai kulata, bai fasa
abinda yai niyya. Wani abin ma da gangan yake
saka ta don ya wahalar‘ da ita saboda ya lura
har yanzu bata yin hankali kullum abinta gaba-
gaba yake
Bakin ciki ya ishi Rukayya, Abubakar ya takuraWa
rayuwarta, bata da sukuni.
Yanda ya tsaneta itama haka take jin ta tsane
shi, musamman yanda yake nuna mata kyama.
‘kara'ra duk abinda za tai masa sai yasa ta
wanke hannu, idan k0 ta'na girki ta fyace ‘majina
sai yasa ta sa sabulu ta wanke hannu. Idan ta
shiga kewaye ta flto k0 tobai bari ta “qara taba
abinda za a zuba cikin abinci sai ta wankc
hannunta da sabulu k0me tai kuwa cikin
kewayen. .
' , Abun nan na ci mata tuwo a kwarya, haka
kuma take daurewa babu yanda zata yl,
duk duniya babu Wanda take jiwa tsoro irinsa; _
Ta ja wani gajeren tsaki yanda ba zai iya'juyo ta
ba, .ta ci gaba da tsane shinkafar cikin kwando
tana gamawa ta zubar da ruwar . tsane shinkafar,
sannan ta dauko mai ta zuba a tukunya, ta‘ zuba
jajjagen ta soya, yana soma soyuwa ta juya ta
dube shi.
' "Kamar yaya za a zuba ruwan?"
Abubakar ya dago kana daga karatun
jaridardayake, ya ce
"Wai ke wacc irin kwakwalwa gare ki ne? Komai
sai kin tamabayi yanda 2
Za a zuba‘? To ban sani ba, ki zuba yanda kike
ganin zai
isa Rukayya ta taBe baki ta wucc ta debi
ruwan ta tafi wurin tukunyar ta zuba, tana tsai da
ruwa .tashshin ya taso mata, sai atishawa wata
na bin wata. Abubakar ya mike da hanzarin sa ya
yo kanta cikc da takaici, ya cc. . . "Wai ke wacce
irin qazamar banza ce? Yanzu kina jin atishawar
ba za ki kauce ba k0ki tara rigar ki amma shi ne
za ki tofewa ; abincin da zamuci? To sai ki cinye
abincin" Ya ja tsaki ya balbalrta da harara ya
wuce abinsa, haushi ya kama Rukayya ta daure
ta ci gaba da. girkinta, ranar bai ci abincin gidan
ba. . Wa Shegari kuwa Rukayya cike take da
shi, sai ai ganin ‘nama me yawa za ayi falfcsu
yasa ta tsaki jiki taci gaba da aikin. ‘
_ Saida aka gama falfesun tas sannan Rukayya

Please Login or Register in order to submit comment