Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

candles din duka ya tashi yaje ya chanza kayan ya maida asalin wanda yasa yamabar akwatin a wurin sanan yacire sakatan kofan yabude kofan yafita daga dakin yarufe kofan da katoton key dinshi sanan yawuce yay tsakar gidan yafice ya shiga mota yaja yabar wajen.



***
Kiran sallan magriba dakuma wani irin zafi dataji sosai ajikinta yasa ahankali ta bude ido, da sauri takara bude idon ganin inda take iskan magrib na kadawa gari yadan soma duhu kadan dudda da haske, dan nauyin dataji dakuma hanun mutum dataji akan cikinta an rike mata ciki gam, gakuma wani irin hadadden kamshin turare datakeji yana shiga hancinta yasa ta mugun zabura tadan dago, arude tace "you" dan wlh ta manta sunanshi amma dai ta tuna fuskar mutumin nan daya kaita asibiti ranan datana Lagos tagani yana bacci kanshi awuyanta jikinshi da kafafunshi akasa close to her own danhar gogan juna suke, jikinshi zafi sosai bana wasaba yana numfashi ahankali ahankali datake jin saukarshi harta cikin wuyanta, long gashin idanunshi duksun tattare waje daya tsabagen kukan dayasha, ihu tayi ganin takasa janye kafadarta. "wayyo Allah na" ta ture kanshi daga jikinta kaman zatai kuka, bude idanunshi yayi ahankali cikin bacci dasukai ja sosai sabida zazzabi ya daurasu akanta kirjinshi nawani irin bugawa da sauri da sauri, zaro idanun tayi danji tayi idanunshi sunmata wani iri ajiki da sauri ta ture kanshi daga kafadarta ta matsa baya da sauri tamakale a jikin bango, saura kadan kanshi dake rawa sosai ya buga kasa yatashi ya zauna zuciyarshi namai wani iri sosai yana kallonta ko kyafta ido bayayi, ahankali kaman dan yaro yace "you are awake" samin kanta tayi da gyadamai kai gabanta na faduwa sosai dan yanda yay maganan saida tajishi har kasan zuciyarta, kallonshi takeyi kaman yanda shima kemata wani irin calm cool look da lumstatsun idanunshi, ganin yanda yake yine kanshi narawa sosai kirjinta na bugawa sosai fiyeda na ranan farko ma data fara ganinshi tace "how did you follow me here?" wani irin kallonta yayi da shanyayyun eyes dinshi dayake budesu sosai, da sauri ta kawad da kanta tana murza hanunta danji tayi she's so nervous, ahankali dawata irin murya chan kasa kaman ba na normal Aadil ba yace "am hungry" da sauri ta kalleshi danjin maganan tayi har zuciyarta, tashi tayi da sauri dan wani irin tsoronshi ne taji ya dirar mata arai da sauri tazo zata wuce shi hakan yasa yasaki kuka sosai yana binta da kallo yarike mata hijabi miyau na zuba daga bakinshi yana cizan lips dinshi dat were looking so pinkish and tender, adan tsorace ta kalleshi ganin yanda yake kuka yana kallon fuskarta kaman zai cinyeta yana taune lips dinshi yana girgiza mata kai alamun karta tafi yasa ta sake kawad dakai cike da mamaki aranta, meya sameshi? Ya akayi ya zama haka? ganin yanda yacigaba da kukan yana goge fuskarshi akafarta yasa tadan juyo ta kalleshi shima ita yake kallo, Ahankali yasa bayan hannu yana goge idanunshi dasukai jajir sundan kumbura ga rigar jikinshi da wandon duksun baci da chabali dahar ya bushe, sake dagowa yayi ya kalleta yana kara rike kafarta hawaye yasake gangarowa daga idanunshi sosai taji zuciyarta yay wani iri dan tsugunnawa tayi agabanshi zatai magana yafada jikinta da sauri ya kankameta yana kuka ahankali babu abinda bayamai ciwo, kanshi ciwo, kafafunshi ciwo, hanunshi ciwo, ga zuciyarshi bayajinta kaman yanda normally yake jinta, yanda yafada jikinta yasa batasan lokacin data zauna dabas a kasan wurin ba ko'ina na jikinta na rawa, fashewa yayi da kuka sosai a wuyanta ya kulle hanunshi abayanta kaman yanda yake rungume Mami, kokarin tura shi take amma takasa ga jikinshi zafi sosai kaman wuta, adan rude tace "to ka sakeni kaga" makemata kafada yayi batare daya gane metake cemai ba, cikin wani irin kuka yace "u want to run and leave me again, that's how you use to do even in my dreams u will come but once I raised d curtain you will run and ask me to find u, I've found you now and I will never let you go" Wani irin tsorone ya shiga jikinta yanda babban namiji yabi ya rungumeta haka ahankali muryanta na rawa sosai tace "please ka sakeni" jin muryanta kaman tana kuka yasa ya saketa ya kalli fuskarta hawayen daya gani yasa ya make mata kafada yakai hanunshi ya share mata hawayen yana turo baki yana wani irin kallon eyes dinta, kallonshi tadanyi kafin murya chan kasa tace "what happen to you why are you like this?" shiru yayi yana wani irin kallonta dayasa taji wani iri da sauri ta dauke kai tace "you are not feeling fine, ur body is hot, stand up and go home" turo baki yayi yanadan lumlumshe ido yace "okay let's go together, you will see Mami, Abie and my Bid, zaki gansu?" yay maganan yana ware mata manyan idanunshi alamun tambaya da sauri ta kalleshi jin yanda yay maganan dan he don't really sound okay to wai meya dawo dashi hakane kodai ba mutumin nan da ya tsinceta a ruwa ya kaita asibiti bane? Kodai idanunta ne, but ha'a bagashi nanba, wanan ai shine but yaushe yasami tabin kwakwalwa haka yadawo zararre ahankali muryanta na breaking sosai tace "please katashi katafi gidanku you are sick" make mata kafada yayi yana neman fadawa jikinta cikin wani irin yanayi yace "pls don't leave me again" matsawa tayi gefe da sauri ta mike tsaye, shima da sauri yamike tsaye ya dafa bango da sauri jin kanshi kaman zai fadi yasaki kuka sosai yana cizan lips dinshi, da sauri tadan matso kusada shi wani irin mugun tausayi taji yabata ahankali tace "are you fine?" turo mata baki yayi yanaso yakara fadawa jikinta da sauri ta matsa baya kirjinta na bugawa, ahankali cikin kuka yace "am sick".


Ji tayi kaman itama zatai kukan sabida yanda yake kukan yana kallonta har yanzu bai dena kallonta ba, da sauri tai hanyar fita tace "stand up and go home kasha magani is magrib" dan juyowa tayi ta kalleshi ganin har lokacin kuka yake yana binta da kallo, sosai taji zuciyarta yay wani iri, lekawa waje tayi amma bataga kowaba hakan yasa kawai tafice abinta da sauri dan taje gida kafin a fara neman ta amma still taji duktabi tadamu da sauri take tafiya dan takusa gida, tafiya tayi nakusan minti goma sanan ta shigo anguwan su, hannu tasa zata bude gate din gidansu taji an rikemata hijabi amugun tsorace ta juyo ganin shine idanunshi sunyi jajir bamaya iya bude idon sosai da kyau yasa ta juya ta kakkali anguwan su ganin ba mutane awaje yasa arude ta kalleshi tace "na bani, you followed me why?" make mata kafada yayi yace "I will never let you go again" da sauri takara kallon ko'ina tace "na shiga uku, wai menene to zakajamin fitina, sakenmin hijabi" ta fizge hijabin ta kaman zatai kuka dukta rude dan tasan ware haka Abba ke shigowa gida, dan sassautar da murya tayi dan wlh mugun tausayi taji yabata ayanda taganshi sha bakwai dinan gashi zazzabi yake sosai kuma koba komi yataimaka mata shima, gashi ya kafe ta da ido idanunshi cike fal da hawaye har wani irin shining suke, sosai taji wani iri hakan yasa ta kwantar da muryanta kasa sosai kaman meson lallashin yaro tace "you are sick, you are very sick, touch your body" ta daura hanunta akan wuyanta tanamai demonstrating yana kallonta kaman yasami wani irin TV, tace "your body is very hot, u are running temperature, go home kaji" takarashe maganan tana kallonshi kaman yanda yake kallonta bayako kyaftawa ahankali ya lumshe ido kafin yabudesu ahankali yadaurasu akanta, da sauri ta janye nata idon danya mugun cika mata ido sosai, batare data kalleshi ba tace "what do you want?" murya chan kasa yana kallonta yace "water" dan juyowa tayi ta kalleshi sanan tace "okay wait here bari naje na daukoma ruwa kaji sai kasha katafi, lemme bring water for you okay" gyadamata kai yayi yana binta da kallo, da sauri tabude gate dinsu ta shiga gidan, babu kowa a tsakar gidan, gidan shiru kaman ba mutane ciki kasancewar babu wuta da taji hayaniyan su Zainab suna kallo a falon Mama, hanyar sassan Kaka tayi da mugun saurinta ta shiga falon, Kaka bata falon hakan yasa tai hanyar dakinta ta hango hasken fitila a dakin Kaka, murmushi tayi aranta tace hala salla take saisa bata kira sunana ba dan data kirani, dakinta ta shiga ta tumbuke takalmin kafarta ta yarda jakan akan gadon takarasa da sauri inda jakan pure water daya da Kaka ta ijiye mata adakin ta dau guda daya ta juyo danta koma waje ta bashi da saurinta, wani irin cin karo taida mutum abayanta tai wani irin ihu tai baya zata fadi da sauri ya rikemata hannu shima afirgice dan yana tsoron ihu sosai, azabure Kaka data sallame salla tadau fitila tace "innalillahi Hamida incedai lafiya daga shigowan ki kin kurma uban ihu haka" arude Hamida ta kalli kofan dake abude na dakin da sauri ta fizge hanunta tai wurin kofan kafin Kaka ta iso tarufe tasaka sakata, mutum taji yafado ta bayanta dan shima ya tsorata sosai ya riketa, zatai magana Kaka ta karaso wajen ta buga wani irin uban salati. "innalillahi Ke Hamida!" a mugun firgice ya juyo da Hamidan data kife da kofa ya ya rungumeta jikinshi na rawa sosai ya kalli Hamidan zaiyi magana, arude Hamida da jikinta ke wani irin masifar rawa ta daura yatsarta akan pink lips dinshi ta girgiza mai kai, ya ware manyan idanunshi yana kallonta, arude Kaka ta buga kofan. "ke Hamida menene? Meya sameki? Budemin kofan nagani? Ko cinnaka ne? Dan dazu na sharo shazumama adakin nan sunfi guda dari uku, ashe kinyi barin sugar kafin kitafi makaranta kinsan kuma duk inda shazumama yake cinnaka na wurin, mugani idan itace ta cijeki nasiyo cacatin a kasuwa dazu na mulka miki a wurin" arude Hamida da jikinta ke wani irin rawa ta runtse ido tana kokarin saita bugun zuciyarta tace "uhn...uhn lafiya lau, bugewa nayi na kofa fa Kaka" tai maganan har lokacin yatsarta nakan soft lips din Aadil dake rungume da ita yana wani irin kallonta da dan ragowan hasken dakin, cikin fushi Kaka ta buga kofan tace "karya kike ja'ira, irin wanan uban ihun dakikayi bude kofan nagani" wasu irin hawayen tsorone suka zubomata, idan Kaka ta shigo dakin nan taga namiji aciki aiyau kasheta za'ayi a gidan nan, Yayyinta biyar duka mata babu wacce ta taba kawo namiji gidan nan bada sanin Baba ba, kumama Maza ne da aka sansu akasan asalin su wayanda zasu aura, ita har cikin dakin kwananta ma kuma kome zatace baza'a yarda ba, wani irin kallonta Aadil yakeyi yanda hawaye ke zuba daga idanunta harwani irin zufa ta shiga yi a goshi tsabagen tsoro da rudewa, numfashin ta na sauka akan fuskarshi dayasa yaji wasu irin abu namai yawo akai, ahankali yasa hanunshi na dama ya janye yatsarta daga bakinshi yarike hanun da sauri ta bude idanunta ta daura akanshi, daga waje Kaka tace "wai bazaki bude kofan nanba Hamida kosai na kira Faruku ya ballata?" matsa hanunta yayi yadan lumshe mata ido yana matso da kanshi saitin fuskarta ahankali kaman wani irin abu na janshi towards her, kokarin matsar da kanta tayi ya make mata kafada cikeda shagwaba yasake matsowa zatai magana takasa sabida kar Kaka dake bakin kofan taji gashi yawani irin cika mata gaba, sakin kuka tayi hakan yasa shima yasaki kuka yana lumlumshe mata ido kafin ahankali yay landing forehead dinshi akan nata yana breathing way too fast, he has never ever experience irin wat he's feeling right now da baimasan ko menene ba, lumshe ido tayi da sauri tana kara shegewa jikin kofan kaman zata fasa ta shige lips dinta nawani irin rawa suna vibrating tana kokarin hanasu fitar da sound din kukan datake yi kar Kaka taji ta taro mata jama' a asirinta ya tonu danyau Abba da Ya Faruk sai sun kasheta, ahankali ya kafe lips din da ido, lumshe ido yayi yakara rike hanunta gam gam kanshi narawa, dawani irin sauri kaman wanda aka bashi naman dawisu for d first time akace yaci yay placing lips dinshi akan nata yana numfashi sosai kirjinshi na bugawa danko ita tanajin yanda heart dinshi ke beating kaman zai fashe yafito, dawani irin sauri ya shiga kissing dinta batare dayamasan meyake yiba yana wani irin nishi da sauri da sauri yajawota yasata ajikinshi sosai.


_Assalamu Alaykum Fanmily, am really sorry bakusamun frequent update, am not that strong, Kano people 😎 you guys have to explain this for me daga zuwa garinku sai zazzabi nake, gaskiya I think air din Kano is foul😜 Just joking. But pray for me okay, I love you all_.
_🌹IN BANI 🌹_



Maman Abd Shakur

19....



_This novel is for sale, karki karanta in baki biyaba, in kika karanta ina binki bashi, pay anan ko pay achan_

_in kinason novel dinan zaki turo just 300 access fee to 3107021073 first bank aisha Muhammad, saiki turo evidence of payment to my watsapp number 07012181461_


_you can also send MTN card zuwa watsapp number na 07012181461, sainai adding dinki a group din danake posting_





Ya wrapping his left hand around her waist yana shesheka kuka sosai yana kissing dinta, da sauri Kaka daharta kai kofar dakinta tasake juyowa tadawo bakin kofarta ta buga kofan cike da masifa tace "wai lafiyan ki Hamida rukuku rukukun menake ji kaman bera na barna?" da sauri ya kabar da hanunta dake kirjinshi tana tureshi cikin hawaye yasake fadawa jikinta yay lamo kirjinshi na bugawa sosai while kissing har lokacin batare daya denaba, runtse ido tayi da kyar ta daddage ta fizge bakinta daga nashi zata tureshi ya riketa sosai yana make mata kafada yana kallonta yana kuka ahankali mara kara, da kyar ta iya saita muryanta gudun kar Kaka ta zargi wani abu tace "Kaka bacci, kidena tashi na" tsaki Kaka tayi tace "kyaji dashi ja'ira kawai, abincin ki na falo dai koda yunwa ta farkar dake cikin dare kije ki dauka" tana maganan tai hanyar dakinta ta shige ta rufo kofa dan itama tagaji yautai aiki da rana, jin karan rufo kofar dakin Kaka yasa ta tureshi daga jikinta da karfi, komawa baya yayi yana turo baki yana share hawayen da yakeyi da bayan hannu, share hawayen daya kasa dena zubo mata tayi ta kalleshi kaman ta zubamai mari dan takaici, yanda yake kallonta ya tsaya a inda ta turashi yana goge idanunshi da bayan hannu kayan jikinshi sunyi daka daka yasa taji yasake bata tausayi dan wanan asibiti yake bukata, ahankali ta saita muryanta ta kalleshi tace "inane gidanku?" dan matsowa yayi kusa da ita da sauri dan kaman jira yake dama tamai magana, da sauri ta matsa takoma kan gado ta zauna, juyowa yasakeyi ya kalleta daga inda yake a tsayen a tsakiyan daki yace "gidan mu?" da sauri ta kallai jin yay mata magana ta gyadamai kai tace "eh gidan ku" kallon yatsunshi yayi yana turo baki yace "gidan mu na chan chan, there's basketball field in our house, Bid and I use to play basket ball" yay maganan yana mata murmushi yana juya mata manyan idanunshi looking super cute, da sauri ta janye idanunta daga kanshi ganin ayanda yake magana ma baisan inda gidansu yakeba yasa ta shiga damuwa sosai. Innalillahi, ita yanzu yazatayi dashi tabani, tayaya ma zatayi ta fitar dashi daga gidan nan yanda ya shigo dinan batare dawani ya gansu tareba?, cikin tsaka da tunani taji mutum ya zauna kusada ita da sauri ta dagokai ta kalleshi kafin ma tai wani yunkuri ya daura kanshi akan kafadarta yana turo baki yace "am hungry" yay maganan yana lumlumshe ido, tsabagen tsorata yasa ta tura kanshi daga kafadarta ta tashi daga kan gadon da sauri tana nishi tace "bari na daukoma abinci" tai hanyar kofa tashi yayi da sauri ya biyota salati tayi a tsorace tace "innalillahi dan Allah ka zauna abinci zan daukoma" make mata kafada yayi hawaye na sake taruwa a idanunshi, sake rudewa tayi dan dazaran yafara kuka zai tona mata asiri jarumta tayi ta daura hanunta akan bakinshi ta rufemai baki da sauri ya ware manyan idanunshi ya kalleta, murmushi tamai tace "yauwa yayama sunanka?" tai maganan tana jan hanunta daga bakinshi da sauri shima yay mata murmushi daya wani irin karama fuskarshi kyau yamata fari da ido a shagwabe yace "Aadil, but Bid use to call me Dil" yanda yay maganan was damn mesmerizing da sauri ta kawad dakai tace "okay muje ka zauna I will bring food and paracetamol for you ok" tai maganan tana nunamai saman gado, zama yay akan gadon yana rike hijabinta ya turo mata baki tareda mikamata kafarshi ya lankwasar dakai a shagwabe yace "remove this shoe from my leg am tired" kallonshi tadanyi kafin ahankali ta tsugunna ta warware igiyan ta ciremai takalmin ta ijiye, ya miko mata dayan kafan ta ciremai shima ta ijiye duk yana kallonta, yace "will you come back?"



Yi tayi kaman batajishi ba ta shareshi ta mike tsaye zata wuce, fizgota yayi da karfi atsorace tajuyo saura kiris tafada kanshi ta cije da kyar ta ta kallai, marmar yay da ido kaman zaiyi kuka yace "will you come back? Don't leave me again pls" gyadamai kai tayi da sauri ta dauke kai ahankali ya saketa ya washe mata baki yay tafi yace "yay am happy" juyawa tayi tai wajen drawer dakin tajawo dan taga Kaka na yawan zuba makulli a drawowin wajen duk yana binta da kallo kaman zai cinye ta da idanu, wani makkulin kwado ta dauka taboye ta hanyar rufe hanunta ta maida drawer tai hanyar kofan dakin ta cire sakata tadan waigo hada ido sukayi har lokacin kallonta yake ya washe mata baki white teeth dinshi suka fito da sauri tafita daga dakin ta tsaya ta ta rufo kofar dakin ahankali gudun karta tashi Kaka tadau key tasaka sanan tai hanyar falon tadau kulan tuwonta da miya sanan tai hanyar doguwan kujeran Kaka tadau kwalin paracetamol din Kaka dake ajiye awajen tabude taciro sachet guda daya tamaida tarufe ya ijiye takwashi kulan tai ciki, agaban dakinta ta tsaya ta ajiye kulolin akasa sanan tasa key tabude kwado ta bude kofan ta kwashi kulan ta shiga ciki tana kallon fuskar Aadil ganin yanda yake kwance kan gadonta ya lumshe ido, ajiye kulan tayi tarufe kofar tasaka sakata sanan ta dau kulan tai wajen gadon ta ijiye akasa tana kallonshi yanda yake numfashi ahankali ahankali yana bacci, yay wani irin kyau kaman ba shine mara lafiya ba, da sauri tadena kallonshi dan sosai fuskarshi yacika mata ido, ahankali takai hanunta dake rawa sosai ta buga katifar muryanta nadan rawa tace "A..Aadil" ko motsi baiyiba bacci yay gaba dashi sosai, kallonshi tayi ta kafeshi da idanu hakanan taji tanajin wani irin tausayinshi, ahankali ta mike tsaye ganin yay bacci yasa tai wajen sip ta bude sip din tana kallon jerin nikakkun kayan ta dake ciki, wani simple free doguwan rigan atampa ta dauka ta maida sip din tarufe tai hanyar bayi, sake juyawa tayi ta kallai ganin har lokacin baccinshi yake yasa tabude bayin ta shiga ta garkama sakata, ahankali tacire hijabinta dayay duku duku ta saka cikin wani empty bucket, tazare kayan jikinta ma duk tasa a botukin sanan tafara wanka, wankan tayi sanan ta tsane jikinta tadau doguwan rigan data shigo dashi ta saka tai alwala sanan tabude kofan ahankali tafito har lokacin bacci yake sip tabude taciro wani hijabin tahau kan dadduma tafara biyan sallolin da ake binta, saida tagama sanan tacire hijabin sabida zafin datake ji sosai ta ijiye hijabin akan dadduma ta juya ta kalli Aadil dahar lokacin ke bacci sosai, ahankali ta matsar da hijabin saman dadduman ta kwanta ta daura kanta kan hijabin datai filo dashi tana kallonshi zuciyarta na tambayarta yazatayi dashi? Ta ina zata fara neman gidansu? Tayaya zata fitar dashi daga gidansu batare da anganshi ba? Idan aka ganshi mezata cema Abba, Mama, Kaka, da Ya Faruk? Yayama zatayi da wanan babban mutun din? Kodai to takaishi asibiti ne adubashi? To ta ina zata sami kudin? Yaya zatayi ta nemo gidansu yanzu? Takai kusan 10min tana kallonshi tana tunane tunane kafin ahankali tajuya mai baya cikin maganin bacci ta kwanta ta hannun damanta wani wahalallen bacci yay gaba da ita.

Kaman amafarki taji ana mata kuka awuya ana bubbuga mata ciki ana shurinta da kafa ahankali, da kyar ta iya bude idanunta cikin bacci tadan juyo Aadil tagani ya kwanta agefen ta yachusa kanshi awuyanta yana mata kuka sosai gabaki daya hawayen shi nabin wuyanta some nabi har cleavage dinta, hanunshi nakan cikinta yana bubbuga matashi yana kuka, sosai tawani irin tsorata tafara ture kanshi daga wuyanta bakinta har rawa yakeyi tace "d...dagani, menene mekake so? Please dagani, katashi daga jikina I can't breath" make mata kafada yayi batare daya tashiba cikin kuka sosai yace "a...am hungry, my stomach hurts"
_🌹IN BANI 🌹_




Maman Abd Shakur


20....

_This novel is for sale, karki karanta in baki biyaba, in kika karanta ina binki bashi, pay anan ko acahn_

_in kinason novel dinan zaki turo 300 access fee to 3107021073 first bank aisha Muhammad, saiki turo evidence of payment to my watsapp number 07012181461_

_you can also send MTN card to watsapp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting_




Tureshi tayi da karfi tace "na shiga uku dan Allah ka dagani, ga abincin ka chan" sake make mata kafada yayi cikinshi na murdawa dan har kukan cikin tanaji, dan kwantar da murya tayi tace "look at your food there, pls dagani" ahankali ya dagata ya kalli fuskarta jin yanda tai maganan muryanta na rawa sosai kaman tana kuka, hawaye yaga tana shareware, ware ido yayi sosai kaman dan yaro saikuma yafashe da kuka maidan kara yace "you are crying whyyy?" da sauri ta tashi daga kwancen gudun kar Kaka tajishi ta share fuskarta da bayan hannu ta kakalo murmushi tamai tace "kagani niba kuka nakeyi ba" hadiye kukan yayi ya kalleta irim kallon da gaske mugani, murmushi ta sakar mai hakan yasa shima yasakin mata murmushi mai kyau sosai yana kara kama cikinshi dayaji ya murdamai da sauri ta tashi ta dauko mai abincin ganin yanda yayi takawo gabanshi ta bude kulan tuwon shinkafa ne da miyan dry kubewa ta kalleshi yanda yake binta da kallo ta nunamai kulan tace "eat" kallon abincin yayi yasake kallo sanan ya yatsine fuska kaman yanda yara keyi yace "wat is this? I want rice with meat balls, i want yam fritata, i want smoked prawns" zaro ido tayi ta kalleshi dan wlh wasu abincin ma daya kira batasan suba hakan yasa tabuga uban tagumi ta lankwashe kafa tana kallonshi inda ace za'a gwada jinin ta yanzu sai anga yahau dan wlh fargaban gobe take, kukan shi ne yasa ta dago kai da sauri ta kalleshi sosai yabata tausayi dan ayanda yayi gaskiya baisan abincin bane, da sauri tace "zakaci biscuit to?" gyadamata kai yayi yana neman fadowa jikinta da sauri ta tashi tabude sip dinta, chan saman kayan ta taboye biscuit din sabida kar Ihsan tagani ko Zainab ta dauko guda biyu ne short bread biscuit tadawo ta zauna agabanshi ta mikamai, karba yayi da sauri yana murmushi yana kallonta sanan yabude daya ya ijiye daya agefe yasa hannu yaciro biscuit daya ya dago kai da sauri ya kalleta kaimata dayan bakinta yayi da sauri ta kalleshi, murmushi yamata yana wani irin kallonta kaman wani mai lafiya ya ware manta manyan idanunshi dake cike da bacci gashin idon duk sun tattare sabida lema leman ruwan hawaye yace "eat my wife yay" zaro ido tayi ta kallai, fari yamata da ido yana goga mata biscuit din a lips kaman yana shafa mata jan baki yace "eat, haaa, haaa, hamm" yay maganan yana bude mata baki kaman yanda akema small baby yaci abinci, dan murmushi tayi ganin yanda yake bude mata baki bama tasan lokacin data saki murmushin ba sabida yanda yay maganan dan har yasa ta manta da fargaban datake ciki na gobe, ahankali tasa hanunta ta karbi biscuit din daga hanunshi takai bakinshi tai murmushi tace "kaika ci kaine kejin yunwa, eat" bude bakin yayi da sauri kaman jira

Please Login or Register in order to submit comment