Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

to watsapp number na 07012181461_


_masu fitarmin da book kuda Allah_

Hanyar bedroom Abie yayi ganin babu kowa afalon straight cikin fushi yana daga murya yace "ina take zoki barmin gidana, mai bakin jini, mai kashin tsiya daga auroki kindawo mana bala'i" Hamida dake baki bakin kofar bedroom dinne tafara juyowa jin hayaniya da sahun tafiyan mutane, tana ganin Abie tareda Aadil daya fara tsalle zaiyo kanta gabanta yawani irin mummunan fadi sabida wani mugun kallo da Abie yake mata kaman zai chaka mata wuka, batasan lokacin data rike hanun mutum din dataji kusada itaba, hanun big Mum takama tarike gam da
sauri big Mum ta juyo jin anrike mata hannu ganin Abie da Aadil da yarike gama yasa tace "Baban yan biyu yauwa zokaga ikon Allah" daidai lokacin Baffa daya gama kiran liman din masallaci dan d whole scene looks spiritual da jinnish ya kalli Suleman da Muhammadu dasuke kafe a tsaye suna ganin abinda basu tabaganiba aduniya yace "kuje ku shigo da liman koma menene wanan abin ayar Allah yau zata kona manashi" da sauri suka jujjuya suka fita daga dakin ganin Abie a corridor rike da Aadil dayake kokarin fizge kanshi yana kuka yasa sukace "jeka gani kaima Abdullahi, abin mamaki" matsawa Mami databi Abie da kallo asanyaye tayi ganin yafara tafiya big Mum ma ta matsamai suka bashi wuri abakin kofan, sakin hanun Aadil yayi ganin yakaraso kuda da Mami da wani irin gudu Aadil yay wani irin tsalle ya rungume Hamida data makale ajikin big mum yace "oyoyo My Hamida" fashewa da kuka tayi sosai ajikinshi ta kankameshi tama kasa magana but she just miss him, jin muryan Aadil yasa Aabid yajuyo da sauri hada ido sukayi da Aadil daya rungume Hamida yana mata kuka ahankali itama tana kuka, ganin Aabid acikin daki yasa yasaki Hamida da sauri yawani irin ware manyan idanunshi yace "Bid" wani irin tsalle yayi ya shigo dakin batare daya lura da komiba yay wani irin jumping ya rungume Aabid kaman zai kadashi yace "oyoyo Bid" kyam idanunshi suka sauka akan ring din dake aman kudin har lokacin daidai lokacin Abie shima ya shigo cikin dakin, yanda gabanshi yafadi saida dan gajeren fitsari yazubomai daga wando yana tuna warning din OZo aranan da akabashi zoben kudin nan. "koda wasa karka bari zoben nan yay aman kudi agaban idanun wayanda basu taba shan jini ba, danka na zoben nan, karka bari zoben nan yay amai agaban mutanen daba yan gidaba, ka kiyaye, ka kiyaye idanu mashan jini ne kadai aka yarda su kalli zoben nan alokacin dayake baka kudi, idanun masu tsarki wanda suke gauraye da jini kadai sukeda ikon ganin lokacin aman kudin zoben nan, kariga kasan ranan dayake aman kudi sanan kariga kasan lokacin dazaima aman kudi ka kiyaye Tursoso, kakiyayeee".


Wani irin race da zuciyarshi Abie yafara yasa yaji saliva bakinshi ya bushe gabaki daya zaiyi magana, yana kokarin magana amma maganan taki fitowa sai iska yake fita. "ahhh, huuuu"....


Ahankali Aadil yasaki Aabid yamike tsaye kanshi narawa sosai miyau nazuba daga bakinshi, kafe zoben Aadil yayi da ido yana kallon kullutun jikin zoben yaga yakawo wuta a jan wuta a idanunshi, kanshi yagani ajikin kullutun amma dan karamin shi, yana cikin keji an rufe, ganin Aadil karami yayi yarike karfen kejin yana girgizawa yana mai magana directly. "free me, free me kafin yagama aman nan, ninekai dasuka shanye, nine brain dinka dasuka shanye, free meee nowww, yakusa gamawa" wani irin juyawa idanun Aadil sukayi sama gabaki daya kafafunshi su lankwashe, duk dakin babu wanda ya lura dashi asandare yay baya ya zube akasa gabaki daya asume akan kudaden, ihu Hamida tayi ta shigo dakin da gudu kafin ta iso Aabid ya dagashi afirgice ya rungume kanshi a kirjinshi Mami ma ta shigo daidai nan su Muhammad suka shigo da limam dawasu malamai guda biyu alarammomi, dago kai Aabid yayi ya kalli Hamida data tsaya gefe takasa zuwa kusada shi tafashe da kuka sosai tana kallon Aadil datake so ta taba amma takasa sabida yanda Aabid yarikeshi, kallan Mami Aabid yayi yace "Mami take her to your room ta nemi hijabi tasaka please" tashi Mami tayi takama hanunta suka fita daga dakin Mami ta karbo mata hijabi
.




_karki karanta in baki biyaba, in kika karanta ina binki bashi, pay anan or pay achan_


_this book is for sale, just 300 naira zaki turo ta 3107021073 first bank aisha Muhammad, idan baki da account u can send MTN card, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461_




Shiga malaman sukayi suna kallon abinda ke faruwa da karfi liman din ganin yanda baban zobe ke fitar da kudi yafara karanto addu'a. "Bismillahil lazi la yadurru ma' ismihi shai'un fil-ardi wa-laa fil-samaa'i wa huwas Samee'ul Aleem" yakaranto addu'an yana tsugunnawa yakai hanunshi kan saman idanun Aadil dake hanun Aabid yabude idanun yana ganin yanda idanunshi suka juya sama baka ganin bakin ko kadan, jinin jikinshi yasha batare dayay magana ba ya kalli sauran malaman dake tareda shi, hakan yasa daya daga cikinsu yakalli baffa yace "muna bukatan ruwa a gora Alhaji danka kodai aljanu sun shafeshi kokuma da sihiri ajikinshi" gyara zama limam yayi yana kallon zoben dayake fitar da kudi har lokacin yafara karatun al Qur'ani, sauran malaman suka zauna kusa dashi suka jonashi suna karantowa atare da karfi sosai kaman zasu fasa dakin da zakin murya, wani irin girma zoben yakarayi kaman an huramai iska, Suleman Big Mum tarike gam dan wani irin tsoro taji tanaji kowani mutum na dakin tambayoyine fal aransu daga ina zoben nan yake? Daga ina tayaya yazo dakin nan?


Abie ko kyafta ido bayayi yay kokarin dazaiyi yay magana yakasa kaman wanda aka dinkemai baki yana kallon yanda zoben ke kumbura yana kumbura yana kumbura.
Ayoyi daban daban suke karantawa suna fuskantar zoben wani irin girgiza zoben yafara yana rawa rawa kaman abinda ke shirin fashewa kafin tuss yawani irin fashe ya tarwatse, kumfane yafara fita daga bakin Aadil jikinshi na girgiza kaman mai ciwon farfadiya yana mikewa yana bankarewa da sauri Aabid dake rike yana neman fizgemai yace "innalillah, Malam my brother meke faruwa dashi" cigaba da karatu malam yayi batare daya amsa Aadil ba, wani irin girgiza dakin yafara kaman saukan aradu hakan yasa malaman suka kara karfin karatu suna kiran Allah, rike Baffa Muhammad yayi gam yayi dakin na kara yana making sound kaman sound din guguwa, wutan dakinne sukai kara suka fashe tareda tarwatse wa dakin yay duhu dumdun abunku dadama darene kara karfi karatu malaman sukayi Aabid ya rungume Aadil da jikinshi ke rawa sosai har lokacin miyau nafita daga bakinshi yana zuba awuyanshi.



Wani irin bulluwo Ozo yayi da kwarangwal dinshi jikinsu na hayaki sosai ta bango, magana sukaji kaman daga sama maikama da murya irin ta abumai tsoratarwa. "Tursoso kanagani ana konamu kai shiru bakace komiba, Tursosooo!" yakira sunan Abie cikin wani irin fushi tone, tundaga silin gashin Abie nakai har zuwa karkashin tafin kafarshi rawa yake jin muryan Ozo, cikin wani irin yanayi na daburcewa da rashin sanin mai yake fadi yace "O...Ozo the g..great bansan cewa anan nabar zobena ba hala danazo inajan Aadil ne yana fada dani shine zoben yafita daga hannuna, Ozo dan Allah karafumin asiri kayakuri" Abie yakarashe maganan cikin tone din kuka, waya Baffa yaciro tsabagen son ya gasgasata me kunnuwanshi suka gama jiyemai ya kunna flash kaman dukansu sun hada bakine gabaki dayansu harda Aabid wayoyinsu atare suka ciro suka kunna flash light dakin yay haske bauu duk suna kallon Abie da idanunshi yay kuri alamun mara gaskiya sunyi jajir kirjinshi nawani irin bugawa gabaki daya yay wani iri yana kallon Ozo da kwarangwal dinshi dake jikin bangon dakin jikinsu na hayaki while malaman na karatun su har lokacin batare dasun yankeba, wani irin kara Ozo yayi ya buga karfen hanunshi sabida konewan dayakeyi yace "bazaka hanasu konamu ba Tursoso" da sauri Abie kaman mahaukaci ya tsugunna yanajan gwuiwa ya zagayo tagaban malaman yace "kuwa Allah, kuwa Allah nace baniba kudena karatun nan zan fadi muku komi, kunga ran Ozo the great yariga yabaci, inhar kuka konashi kashe Aadil zaiyi, wlh, wlh, billahillazi la'ilaha illahuwa kuruwan Aadil na tareda shi, kai rayuwan Aadil gabaki dayanta ma yana wurinshi, shine ya shanye rayuwan Aadil ya shafemai kwakwalwa, shine ya zamad da Aadil abinan dakuke gani, inhar baku denaba mutuwa zaiyi, zuge jinin Aadil zaiyi tass" babu wanda bai girgiza ba dajin kalaman Abie ba, shiko Abie ko kadan bai damuda wanan ba yasan dukansu babu abinda suka isa sumai, yanada kudin da zai iya kullesu dukansu, yanada kudin dazai iya batar dasu aduniyan nan gabaki daya anemesu arasa, sanan yanada kudin da zaije daganan harbangon duniya inyanaso yaje just to free his self daga shame and talk of the town. Wani jarababben tsawa Ozo yadakamai karfen hanunshi yay haske yace "bazaka hanasu ba Tursoso" da sauri Abie yasa hannayenshi ya rufe bakin limam kaman zaiyi kuka yace "kudena konamin Ozo, Ozo ne rayuwata, shine gatana, yabani abinda wanan mutumin marikina bai baniba dudda uwarshi tacemai yasoni sama da yaran daya haifa amma tana mutuwa ya manta da batun, Ozo ya soni ya fifitani akan duka members yan cult, shiko wanan tsohon yaranshi yafiso, suya sani baniba, dudda nafi yaranshi ilimi nafisu iya aiki, nafisu kaifin basira kullum ninake samamai customers da ciniki a kampani amma daya tashi raba motoci bai baniba yabama yaranshi, Ozo shiya bani kudi saisama har yarshi ta yarda zata aureni da bata aureniba ai, sanan Ozo ya zamaddani popular yabani fame akasanni globally aduka kasashen duniya, nazama babban mutum, kuduba fa duka abubuwan nan dayamin abu daya kawai ya nema awurina shine jinin dan farina, amma dana haifi Aadil nakasa badawa, nama Ozo daya sharemin hawaye butulci sabida yanda nake son Aadil, gadai yaron imbecile amma shine rayuwata duka, Allah ya jarabeni da masifaffen son Aadil, na roki alfarma Ozo yamin da sharadin duk cikin da Maryama zata kara samu tun kafin ahaifa zasu shanye duka, barin Maryama sau uku ba bari bane Ozo nabama yaran nawa tun suna cikin cikin uwarsu, dan Ozo ya chanchanci abinda yafi haka agareni ma, yamin komi a duniya, yaban duk abinda nabukata, inhar kundena konamin Ozo na zan baku ganamasgo manya manya na dollars guda dari uku na rantse da zatin Allah" yafada ahaukace, kabar da hanunshi limam yayi yacigaba da karatun da karfi dan maganganun Abie kara musu karfin guwiwa yin karatun more and more yayi, dole yau su babbaka matsafan nan da ayoyin Allah, su kawo karshen su sanan su kubutar da Aadil, wani irin haske karfen Ozo yafara ran Ozo amasifar bace, kwarangwal dinshi tafara rawa tana narkewa kafafunta sun narke suna diddiga kaman roba da akai melting da wuta, wani irin girgiza karfen Ozo yayi yana nishi yana kallon Aadil da Aabid da gudu Abie kaman zarare ya tube riga yay wani irin tsalle ya tare Aadil da Aabid ya karesu yace "dont kill my children Ozo, na rokeka idan akwai any atom of son dakake min aranka karka kashemin yaran nan, amma nabaka izini ka kashe kowane ne agidanan, kama kashesu gabaki daya banda asara, they're all bloodline but don't touch my children please Ozo, Ozo karka kashemin boys dina, Aadil baisan dadin asalin duniya ba, na tauyemai 30yrs of fresh life, kabarmin shi har lokacin da Allah ya kindayamai aduniya su cika karka kashemin Aadil Ozo na rokeka" wani irin hayaki ne ke fitowa daga bakin Ozo idanunshi na fitar da bakin ruwa, karfenshi na wuta sosai yana hayaki, ganin haka yasa Abie ya warware mazariyan wandonshi yace "Ozo kawa Allah karka kashemin yara, kai nace karka tabamin yarana fa, bakajina ne? Karka tabamin yara, Aadil zuciyata ne, karka tabamin yan biyuna, zanyi tsirara agaban duka duniya inhar bazaka kashemin yarana ba, karka tabamin yan biyuna Ozo" kana ganin Abie kasan ya haukace bil hakki dan maganganun dayakeyi basuda kan gado, daidai lokacin Hamida ta shigo dakin da gudu sanye da dogon hijabin Mami hankalinta atashe tana kallon fuskar Aadil dahar lokacin ke kulle bakinshi na fitar da yellowish kumfa tareda hancishi, mugun rudewa tayi batare data lura dasu Ozo ba tai wajen Aabid dake rungume da Aadil da mugun gudu tana kallon fuskar Aadil din ganin kaman yamutu daidai lokacin Ozo yasaki wutan tsafin karfenshi direct sai wutan tsafi yay saitin cikin Hamida ya shige, tsayawa Hamida tayi chak daidai ta karaso kusada Aabid ta mika hannu tana shirin taba kan Aadil dake kan kafadar Aabid ta zaro idanunta gabaki daya tareda daura hanunta akan cikinta tawani irin ja numfashi. "uhhh ahhhhh" sakin Aadil Aabid yayi yawani irin tashi da mugun sauri yatarota yakira sunanta cikin zafin rai. "Hamida!" lumshe ido tayi tabudesu ahankali ta kallai wasu irin hawaye masu dumi na fitowa ta gefen idanunta kafin ahankali wani irin jini with force yagangaro yana bulbulowa ta hancinta da gefen bakinta tai luuuuu hanunta na lilo akasa, riketa gam Aabid yayi zuciyarshi nawani irin bugawa dabai taba yiba in his life yace "ke Amatullah where do you think you are going? Stay with me, i said stay with me okay me and my brother, Aadil needs you, and...and...I..I need you too Amatullah" yay maganan yana jijiga fuskarta hakan yasa kanta yay luu ya kife akan kirjinshi ba alamun numfashi ko kadan atattare da ita wani irin ihu Aabid yayi da mugun karfi. "Nooooooooo! Jewel Noooo!" wani irin tsalle Abie yayi yana sosa kunne yatube boxer din jikinshi yace "yesssss, Ozona you spare my children once again Ozo" kara karfin karatu malaman sukayi trying to handle one situation at a time shine Ozo, hakan yasa jikin Ozo yakama da wuta sosai yana narkewa, ihu Abie yayi yace "noooo Ozo, na shiga uku" yarike kashiyarshi yasaki fitsari yana dariya yace "bari nakashe wutan da fitsari na Ozo na, yauwa kagani, kagani, kagani fitsarina dayawa karka damu saina rama maka zan dauresu, zanyi amfani da kudina na batar dasu a duniya, saimun sha jinin yaransu harda na jikokin su" kara karfin karatun sukayi hakan yasa sosai Ozo keci da wuta yana narkewa kaman dalma yana diddiga hakan yasa kudaden wurin ma suka shiga ci da wuta, alamu Malam yamusu dasu fice daga dakin, Suleman da Muhammad sukadau Aadil dake kwance flat akasa, Aabid narike da Hamida suka fice malaman kuma suka tsaya abakin kofa suna karatun sosai, Abie na ihu batare daya bar wurin wutanba yace "kubar konamin Ozo na, Ozo zan mutu taredakai yau zan mutu taredakai yau" dakin yakama da wuta sosai sukaji Abie yafara ihu kafin yafito daga dakin da sauri yana sossosa jiki yana zaro ido yana dariya, tashin hankali shine abinda idanuwansu yagane musu dis night, wanan abin shine definition of tashin hankali.



Jin yanda jikin Hamida yay sanyi ahanun Aabid yasa hawaye ya gangaro daga idanunshi da sauri yay hanyar fita da ita su Suleman da Muhammad dake rike da Aadil biye dasu, Baffa da Big Mum suka rike Big Mum dake wani irin kuka kaman zata shide dan gabaki daya taji bayanin Abie, har sunkai falo tasake fizge hanunta cikin kuka sosai daga na Big Mum takoma Corridor inda Abie ke tsaye yana kallon malaman dake karatu har lokacin yana sosa jikinshi, wani irin mari Mami ta daukeshi dashi cikin kuka tace "ka cuceni, ka cuceni, ka cuceni Abdullahi, ka cuci danmu, ka kashemin yara har uku, yaran da Allah yabani akan son duniya, Allah ya isa tsakanina dakai, all dis while dakai muke wahalan Aadil kaishi asibitici gari gari, daban daban, ashe harda sa hanunka, kawai kallona kake kasan bazai taba warkewaba, Abdullahi, Abdullahi i will never forgive you, all pains din wankin ciki da azaban daduk nasha a wuraren barin yara ukun nan are still fresh a heart dina ashe u were behind it banyafema ba wlh, banyafema ba" tarufe Abie da duka sosai yana mata dariya. "hahahhahah, kekekekee, kyalkyalkyal kyal" fizgota Big Mum tayi tace "let it goo is too late gashinan Allah yafara nunamai ai tajata suka fita daga dakin, sukai tsakar gida, sosai wuta ya shiga ci adakin yana fitowa falo hakan yasa malaman suka fito shashin da sauri daidai Abie yafito yana tsalle ginin part din yawani irin rushe sukayi ginin ya zubo kanshi agabansu kan Abie ya tarwatse Aabid ya runtse ido da karfi hawaye masu mugun zafi suna fitowa daga idanunshi.
...






Ahankali take bude idanunta dasuka mata nauyi sosai jikinta ko kadan ba karfi gabobin jikinta sun mata tsami sosai, bude idanun tayi gabaki daya ta daura shanyayyun idanunta akan makeken agogon bangon, tana fitar da numfashi ahankali ahankali da baki bata feeling jikinta ko kadan, motsin da kunnuwanta sukaji yasa tajuyo da kanta ahankali, sauka idanunta sukayi akan fuskar Aadil dake kwance agadon dake dayan bangaren dakin akwai dan gab a tsakanin su, motsi yake sosai batare daya bude idoba sai motsi dayakeyi idanunshi na rawa suna shirin su bude, lumshe idanunta tayi asanyaye takara budesu ahankali tasauke su akan fuskarshi, wani irin sanyi taji ajikinta bana wasaba, ahankali ta matsar da hanunta da kyar zuwa baki bakin gadon datake kai tai pointing Aadil din da hanunta tana lumshe ido batare datai koda kwakkwaran motsi ba, bude ido Aadil yayi gabaki daya yana kallon dakin yanabin ko ina da kallo, yakai kusan minti biyar ahaka kaman mai nazarin wani abu kafin ahankali yatashi ya zauna yana kallon drip din da ake karamai yadan yatsine fuska sabida ciwo da jikinshi kemai sosai yana shafa hanun nashi dan wurin karin ruwan namai zafi sosai, lumshe ido tasakeyi ahankali tanajin wani irin murna har cikin ranta ganinshi atare da ita dat means he's fine bai mutu ya barta ba, bude bakinta dayamata nauyi sosai tayi zatai magana wani atishawa mai karfi yazo mata tayi, da sauri ya waigo ya kalli bayanshi jin karan atishawa tsayawa yayi chak batare dayace komiba yakafeta da ido, wata yarinya yagani fara sosai kan gadon, tana sanye da wani pink rigan asibitin akwai bandeji biyu a jaws dinta tana kwance gashin kanta ya barbarzu kaman na yar buzuwa ta kafeshi da ido kaman mayyar dataga yaron dazata lashe, murmushi tasankin mai daya bayyanar da cute dimples dinta ganin ya ganta yajuyo yana kallonta, yatsine fuska yayi akasalance ya dauke kai ganin yarinyar tanamai murmushi tana wani irin kallonshi kaman zata hadiyeshi daidai lokacin aka bude kofar dakin za'a shigo, atare dukansu sukabi kofar da kallo, Big Mum ce ta shigo dakin tareda Baba Suleman suna hira batare da sunma lura dasuba. "eh saida na tabbatar tasha maganin Yaya sanan nafito, saida nahada da yimata alkawari zan kirata a video call taga fuskokin su sanan ta yard...." shiru tayi batare data karasa maganan ba ganin Aadil zaune abakin gado ya kafesu da ido yana kallonsu, dukansu kamewa sukayi tsaye suna kallon Aadil din daya kafesu da ido bayako kyaftawa, da wani irin sauri Big Mum tai wurin gadon ta zauna kusa dashi cikin murna tadaura hanunta akan fuskarshi tana shafawa tace "Aadil, Boy katashi, yaushe katashi ya jikin?" hanunshi ya daura akan nata dake kan fuskarshi yadan lumshe ido ya bude ahankali kafin cikin wani cool calm voice yace "Big Mum ina Mami na? Ina Bid?" chak daga Big Mum har Baba Suleman suka tsaya suna kallonshi ganin for the first time in life sunga Aadil yay magana batareda kanshi yay rawa ba batare da miyau ya zuba daga bakinshi ba and magana ba childish magana daya sabayi ba yana turo baki a shagwabe yana fari da ido yana lankwasa kai yana make kafada, tashi Big Mum tayi tafada kasa cikin so much happiness tai sujjada kafin ta tashi tafashe da kuka sosai tana kallon Aadil din dake binta da kallo, kawai takasa holding tears nata back ne, sake zama tayi ta matso kusada Aadil din sosai taima fuskarshi kyakkyawar cupping tace "Aadil, Aadil am I dreaming kaine Aadil, Aadil u are fine kaji sauki wayyo Allah na Yaya am so happy today, kalli Aadil dinmu fa, Alhamdulillah, ya rabb i can't wait to tell kanwata this good news dasu Baffa" tai maganan tana wani irin rungume Aadil dayay shiru yana kallonta kaman mai tunani yanason gano wani abu, karasowa cikin dakin Baba Suleman yayi ya zauna adayan gefen side din Aadil din yana kallon Aadil din today is such a good day hanun Aadil din yakama yarike, hakan yasa Big Mum tace "kagane shi Aadil?" juyodakai yayi ya saukar da manyan eyes dinshi akan fuskar Baba Suleman din ya kafeshi da manyan milky eyes dinshi yana kallo ahankali yace "Uncle" wani irin ihun dadi Big Mum tasakeyi tana goge hawayen datakeyi nonstop tana kokarin ciro wayarta daga jaka da sauri Baba Suleman ya fizge wayan yace "babu wanda zaki fadamawa saidai su ganmu mun da Aadil din kawai, lemme go an call Dr yazo yaduba shi" tashi yayi daga kan gadon daidai zai juya yay wurin kofa idanunshi suka sauka akan Hamida dayagani idanunta biyu tana kallonsu hawaye nafita daga gefen idanunta tana kallonsu da sauri Baba Suleman yace "H...Hamida" yay maganan yana karasawa wurin gadon cikin tsananin farin ciki da sauri Big Mum ta mike tsaye jin sunan da Baba Suleman yakira, karawasa gaban gadon Baba Suleman yayi ya tsaya yana kallon Hamidan ahankali yace "Hamida kin farka?" kafin ma tabada amsa big mum takaraso wajen tana Share kwalla tace "daughter na, Hamida na kintashi" da kyar Hamida ta iya ta gyadamata kai sabida bones dinta dake mata ciwo sosai daidai lokacin Aadil yamike tsaye ahankali yana yatsine fuska ya cizge karin ruwan dake hanunshi ya yar, singlet da 3quater dayagani kan gadon ya dauka yadaga kafa ahankali yay hanyar kofar dakin dayagani wanda ya kyautata zaton na bathroom ne, yanda Hamida tabishi da kallo batare databa Big Mum amsar tambayanta ba yasa Big Mum da Baba Suleman suka juya atare dan suga metake kallo haka, ganin Aadil ne yatashi yana tafiya yabude bathroom ya shiga yasa big Mum tace "Yaya akira mana Dr yakamata yasan sun farka beside Hamida doesn't look good, meke miki ciwo daughter?" fita Baba Suleman yayi dan zuwa kiran Dr, ahankali batare datai magana ba Hamida ta nuna mata fuskarta da jaws dinta alamun su kemata ciwo, a forehead big Mum tamata peck cikin tsananin son yarinyar tace "don't worry zakiji sauki kinji, Maman ki kullum saita kira taji yaya jikin ki, i know she will be very happy idan taji kin farka" shigowa Baba Suleman yayi tareda Dr da nurses guda biyu, kana ganin su kaga larabawa, da farin ciki gabaki dayansu suka shigo suna tambayan ina Aadil Baba Suleman yace "ya shiga bathroom wanka" Dr ya shiga duba Hamida daidai lokacin Aadil yafito daga bathroom din sanye da white single da 3quater ajikinshi yana tafiya ahankali, tafi duka Dr da nurses din suka fara suna kallonshi suna murna ganin patient dinsu yatashi strong and healthy, dan kallonsu yayi kafin ya dauke kai yakarasa yazauna akan wani plastic chair dan yagaji da kwanciya Hamida tabishi da kallo, so kawai take yamata magana koma ya kalleta amma yaki, saida aka gama dubata sanan Dr yaduba shi, babu wata matsala tattare da shi sai rashin kuzari wanda dazaran yaci abinci zai dawo normal, har Dr zai fita Baba Suleman yace "yaushe za'a sallame mu Dr? Munkosa mutafi gida dasu" dariya Dr yayi yace "i just want to run two scans for Amatullah once d result is clear and fine zanyi discharging naku yau, but before then amata wanka zan turo dietitian yazo yaduba su yafadi abinda zasu iyaci" murmushi Baba Suleman yayi looking satisfy da service dinsu yace "angode Dr" fita Dr yayi nurses biyedashi hakan yasa Big Mum yaye lullubin jikinta ta ijiye akan gadon da jakar hanunta tace "bari naje nahada miki ruwa mai zafi sosai ko kyaji dadin jikinki nazo muje muyi wankan, dan bude ido Aadil yayi kadan ya kallesu kafin yasake lumshe ido abinshi ya kishingida, shiga bathroom Big Mum tayi tahada ruwa sanan ta dawo dakin takama hanun Hamidan tace "yauwa tashi muje daughter na" ahankali Hamidan ta tashi tana yatsine fuska gashin kanta yakara barbajewa ta sauko da fararen kafafunta kasa ta zauna tana runtse ido sabida yanda jikinta ke ciwo bana wasaba kaman Big mum zatai kuka tace

Please Login or Register in order to submit comment