Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su, motsi yake sosai batare daya bude idoba sai motsi dayakeyi idanunshi na rawa suna shirin su bude, lumshe idanunta tayi asanyaye takara budesu ahankali tasauke su akan fuskarshi, wani irin sanyi taji ajikinta bana wasaba, ahankali ta matsar da hanunta da kyar zuwa baki bakin gadon datake kai tai pointing Aadil din da hanunta tana lumshe ido batare datai koda kwakkwaran motsi ba, bude ido Aadil yayi gabaki daya yana kallon dakin yanabin ko ina da kallo, yakai kusan minti biyar ahaka kaman mai nazarin wani abu kafin ahankali yatashi ya zauna yana kallon drip din da ake karamai yadan yatsine fuska sabida ciwo da jikinshi kemai sosai yana shafa hanun nashi dan wurin karin ruwan namai zafi sosai, lumshe ido tasakeyi ahankali tanajin wani irin murna har cikin ranta ganinshi atare da ita dat means he's fine bai mutu ya barta ba, bude bakinta dayamata nauyi sosai tayi zatai magana wani atishawa mai karfi yazo mata tayi, da sauri ya waigo ya kalli bayanshi jin karan atishawa tsayawa yayi chak batare dayace komiba yakafeta da ido, wata yarinya yagani fara sosai kan gadon, tana sanye da wani pink rigan asibitin akwai bandeji biyu a jaws dinta tana kwance gashin kanta ya barbarzu kaman na yar buzuwa ta kafeshi da ido kaman mayyar dataga yaron dazata lashe, murmushi tasankin mai daya bayyanar da cute dimples dinta ganin ya ganta yajuyo yana kallonta, yatsine fuska yayi akasalance ya dauke kai ganin yarinyar tanamai murmushi tana wani irin kallonshi kaman zata hadiyeshi daidai lokacin aka bude kofar dakin za'a shigo, atare dukansu sukabi kofar da kallo, Big Mum ce ta shigo dakin tareda Baba Suleman suna hira batare da sunma lura dasuba. "eh saida na tabbatar tasha maganin Yaya sanan nafito, saida nahada da yimata alkawari zan kirata a video call taga fuskokin su sanan ta yard...." shiru tayi batare data karasa maganan ba ganin Aadil zaune abakin gado ya kafesu da ido yana kallonsu, dukansu kamewa sukayi tsaye suna kallon Aadil din daya kafesu da ido bayako kyaftawa, da wani irin sauri Big Mum tai wurin gadon ta zauna kusa dashi cikin murna tadaura hanunta akan fuskarshi tana shafawa tace "Aadil, Boy katashi, yaushe katashi ya jikin?" hanunshi ya daura akan nata dake kan fuskarshi yadan lumshe ido ya bude ahankali kafin cikin wani cool calm voice yace "Big Mum ina Mami na? Ina Bid?" chak daga Big Mum har Baba Suleman suka tsaya suna kallonshi ganin for the first time in life sunga Aadil yay magana batareda kanshi yay rawa ba batare da miyau ya zuba daga bakinshi ba and magana ba childish magana daya sabayi ba yana turo baki a shagwabe yana fari da ido yana lankwasa kai yana make kafada, tashi Big Mum tayi tafada kasa cikin so much happiness tai sujjada kafin ta tashi tafashe da kuka sosai tana kallon Aadil din dake binta da kallo, kawai takasa holding tears nata back ne, sake zama tayi ta matso kusada Aadil din sosai taima fuskarshi kyakkyawar cupping tace "Aadil, Aadil am I dreaming kaine Aadil, Aadil u are fine kaji sauki wayyo Allah na Yaya am so happy today, kalli Aadil dinmu fa, Alhamdulillah, ya rabb i can't wait to tell kanwata this good news dasu Baffa" tai maganan tana wani irin rungume Aadil dayay shiru yana kallonta kaman mai tunani yanason gano wani abu, karasowa cikin dakin Baba Suleman yayi ya zauna adayan gefen side din Aadil din yana kallon Aadil din today is such a good day hanun Aadil din yakama yarike, hakan yasa Big Mum tace "kagane shi Aadil?" juyodakai yayi ya saukar da manyan eyes dinshi akan fuskar Baba Suleman din ya kafeshi da manyan milky eyes dinshi yana kallo ahankali yace "Uncle" wani irin ihun dadi Big Mum tasakeyi tana goge hawayen datakeyi nonstop tana kokarin ciro wayarta daga jaka da sauri Baba Suleman ya fizge wayan yace "babu wanda zaki fadamawa saidai su ganmu mun da Aadil din kawai, lemme go an call Dr yazo yaduba shi" tashi yayi daga kan gadon daidai zai juya yay wurin kofa idanunshi suka sauka akan Hamida dayagani idanunta biyu tana kallonsu hawaye nafita daga gefen idanunta tana kallonsu da sauri Baba Suleman yace "H...Hamida" yay maganan yana karasawa wurin gadon cikin tsananin farin ciki da sauri Big Mum ta mike tsaye jin sunan da Baba Suleman yakira, karawasa gaban gadon Baba Suleman yayi ya tsaya yana kallon Hamidan ahankali yace "Hamida kin farka?" kafin ma tabada amsa big mum takaraso wajen tana Share kwalla tace "daughter na, Hamida na kintashi" da kyar Hamida ta iya ta gyadamata kai sabida bones dinta dake mata ciwo sosai daidai lokacin Aadil yamike tsaye ahankali yana yatsine fuska ya cizge karin ruwan dake hanunshi ya yar, singlet da 3quater dayagani kan gadon ya dauka yadaga kafa ahankali yay hanyar kofar dakin dayagani wanda ya kyautata zaton na bathroom ne, yanda Hamida tabishi da kallo batare databa Big Mum amsar tambayanta ba yasa Big Mum da Baba Suleman suka juya atare dan suga metake kallo haka, ganin Aadil ne yatashi yana tafiya yabude bathroom ya shiga yasa big Mum tace "Yaya akira mana Dr yakamata yasan sun farka beside Hamida doesn't look good, meke miki ciwo daughter?" fita Baba Suleman yayi dan zuwa kiran Dr, ahankali batare datai magana ba Hamida ta nuna mata fuskarta da jaws dinta alamun su kemata ciwo, a forehead big Mum tamata peck cikin tsananin son yarinyar tace "don't worry zakiji sauki kinji, Maman ki kullum saita kira taji yaya jikin ki, i know she will be very happy idan taji kin farka" shigowa Baba Suleman yayi tareda Dr da nurses guda biyu, kana ganin su kaga larabawa, da farin ciki gabaki dayansu suka shigo suna tambayan ina Aadil Baba Suleman yace "ya shiga bathroom wanka" Dr ya shiga duba Hamida daidai lokacin Aadil yafito daga bathroom din sanye da white single da 3quater ajikinshi yana tafiya ahankali, tafi duka Dr da nurses din suka fara suna kallonshi suna murna ganin patient dinsu yatashi strong and healthy, dan kallonsu yayi kafin ya dauke kai yakarasa yazauna akan wani plastic chair dan yagaji da kwanciya Hamida tabishi da kallo, so kawai take yamata magana koma ya kalleta amma yaki, saida aka gama dubata sanan Dr yaduba shi, babu wata matsala tattare da shi sai rashin kuzari wanda dazaran yaci abinci zai dawo normal, har Dr zai fita Baba Suleman yace "yaushe za'a sallame mu Dr? Munkosa mutafi gida dasu" dariya Dr yayi yace "i just want to run two scans for Amatullah once d result is clear and fine zanyi discharging naku yau, but before then amata wanka zan turo dietitian yazo yaduba su yafadi abinda zasu iyaci" murmushi Baba Suleman yayi looking satisfy da service dinsu yace "angode Dr" fita Dr yayi nurses biyedashi hakan yasa Big Mum yaye lullubin jikinta ta ijiye akan gadon da jakar hanunta tace "bari naje nahada miki ruwa mai zafi sosai ko kyaji dadin jikinki nazo muje muyi wankan, dan bude ido Aadil yayi kadan ya kallesu kafin yasake lumshe ido abinshi ya kishingida, shiga bathroom Big Mum tayi tahada ruwa sanan ta dawo dakin takama hanun Hamidan tace "yauwa tashi muje daughter na" ahankali Hamidan ta tashi tana yatsine fuska gashin kanta yakara barbajewa ta sauko da fararen kafafunta kasa ta zauna tana runtse ido sabida yanda jikinta ke ciwo bana wasaba kaman Big mum zatai kuka tace "sorry kinji" huta saimu tashi, kai ta gyadama Big Mum tadan saci kallon Aadil dahar lokacin idanushi ke lumshe kaman wanda yay bacci, hanunta da kafadarta bigmum takama tace "yauwa muje" saukowa tayi daga kan gadon ta mike tsaye da kyar jikinta na rawa kaman zata fadi hawaye ya gangaro daga idanunta sai sannu Big Mum take mata takaita gaban bathroom din tabude bathroom din suka shiga, yatsine fuska Aadil yayi dan surutun Mami na damun brain dinshi yabude ido kadan yana kallon kan gadon data tashi daga kai kafin yasake lumshe idon, basu jima da shiga bayin ba Big Mum tafito tabude wardrobe din dakin taciro free plain gown na cotton black mai kama da rigan da sauran abubuwan dasuke bukata da ribbon takoma bayin, sunbata almost 20min sanan suka fito yanzu tafiyarta yadanfi nada dan tanayi ahankali rigan jikinta yamata kyau yakara haskata, big Mum ta zaunar da ita akan gado zama tayi ahankali, daidai lokacin dietitian din ya shigo da abubuwan da zasuci bigmum ta karbi na Hamida Baba Suleman yakarbi na Aadil, sanan Dr yace "Hamida tagama da wuri za'a mata scanning" to Big Mum tace "ta shiga bama Hamida abincin" da kyar ta iya ta karbi abincin tanaci ko kadan batajin dadin komi ganin yanda ko kallonta Aadil bayayi bama ya magana ya lumshe ido kaman mai bacci, tana gamawa nurses suka shigo suka fita da ita dan zuwa scanning big Mum tabisu.




Sai wajen la'asar aka dawo d ita komi is fine babu wani complication, bakaramin dadi su big Mum sukaji ba nan aka basu sallama bayan Baba Suleman yagama clearing komi na bill, big Mum kuma ta shiga hada kayayyakin su she can't wait to see Mami's face dana Aabid idan sukaga new Aadil not baby Aadil.



Wuraren biyar da rabi suka gama komi tsaf suka fiffito har haraban asibitin Aadil da Baba Suleman suka shiga gaban mota itakuma da big Mum suna baya, Baba Suleman ya kunna motar yaja suka shiga hanya yace "i can't wait to see yanda su Mami da Aabid zasuyi idan suka ganmu" dan dagokai Hamida tayi ta side glass ta kalli fuskar Aadil taga idanunshi a lumshe suke kaman mai bacci, kuka ne sosai taji yazo mata, she's so longing for his talk, so kawai take yamata magana amma ya share ta, da kyar ta daure ta hana kanta kukan dan bamata da karfin yin kukan tanata kallon garin dasuke dan daga gani tasan ba Nigeria bane dan larabawa take ta gani tako ina, tafiyan kusan 20min sukayi taga Baba Suleman yay parking agaban wani babban gida yace "muna shiga da mota zasu gane kuzo muje" fitowa yayi hakan yasa Aadil yabude kofa shima yafito yakosa yaga Mami da dan uwanshi, big Mum ma tafito ta taimakama Hamida itama tafito, Baba Suleman yabude gate suka shiga har gaban babban flat dinsu Baba, Suleman ne yajuyo yana zare ido hadaura yatsarahi akan lips dinshi ya kallesu, hanun Aadil yakama ya daura akan na Hamida da sauri Aadil ya yatsine fuska tareda janye hanunshi da sauri yana kallon Baba Suleman irin me haka, ahankali Hamida ta kallai yanda yake yatsine fuska, cikin rage murya batare da yalura damai yafaru ba Baba Suleman yace "kariketa karta fadi kaga batada karfi nida Aisha ne zamu fara shiga ciki kafin ku kubiyomu abaya" yay maganan yana kara daura hanun Aadil akan na Hamida ahankali Hamida ta saukar da kanta kasa dan tana gabda sakin kuka, Baba Suleman da Big Mum suka juya suka bude kofa suka shiga ciki atare, wani irin gajeren wahalallen tsaki Aadil yaja ya saki hanunta da sauri hakan yasa tai baya zata fadi atsorace taidan kara tadafe bango ahankali tana maida ajiyan zuciya, ko kallonta baiyiba yasa hannu yabude kofa ya shiga dakin idanunshi suka hadu dana Mami da Aabid yadebo rice a spoon yana kokarin kaimata baki danko kadan bata iyacin abinci sai an tursasata tarame sosai bana wasaba, Baba Suleman da Big
Mum tsaye agefe suna murmushi sosai suna kallonsu sunyi folding hand akirji, atare Mami da Aabid suka mike tsaye suna kallon Aadil din, wani irin cute adorable smile Aadil yayi yace "Mami na" ya kalli Aabid yace "rascal" sakin plate din abincin Aabid yayi akasa jikinshi yadau wani irin rawa bakinshi har rawa yake yana kallon Aadil din yace "d...Dil"
[2/17, 2:37 PM] +2347066933957: ..







Durkushewa Mami tayi tana kuka kuka kaman zata mutu ganin yanda gini ya ruguzo kan Abie, Baffa duk shine mai dan kwari a cikinsu ya kalli su Suleman da muryanshi data dishashe yace "ku wuce kukai yaran nan asibiti we will take care of the rest anan" juyawa duk sukayi Aabid da kyar ya iya daga kafarshi yay hanyar gate dan motarshi na waje har wani jiri jiri yake gani, bude motar yayi ya kwantar da ita abaya yamaida kofar yarufe ya shiga gaba ya tada motar, su suleman ma suka shiga tasu motar bayan sun kwantar da Aadil abaya sukaja motar sukabar anguwan sukai wani babban private hospital dasu inda da gudu Nurses and Dr suka karbesu sukai placing dinsu on admission, Baba Suleman ne yace "VIP room mukeso asasu" nan aka kwantar dasu awani hadadden daki mai gado biyu Dr suka taru akansu ana kokarin saving their lives, ahankali Aabid yatashi daga jikin kofan inda yake leka yanda Dr's ke battling suna kokarin cetosu ya zauna akan one of the kujera dake corridor da dakinsu yake ya saukar da kanshi kasa yadafe kanshi zuciyarshi na bugawa yanamai zafi, yanamai daci sanan yanamai yaji, for the first time a history din life dinshi yaji ya tsani life dinshi, ya tsani his life he hates who he is, yanzu dama cikin kudin jini Abie ya rainesu? Yasasu makaranta har ya karanci business administration, da blood money ya rayu daman? Thank God yanada aikin kanshi, yanada kampanin kanshi dayay establishing bayan yagama masters dinshi but dudda hakan d thought of yarasu yaci yasha yay karatu da blood money yakasa fita daga ranshi. "Astagafurullah" yafada sounding weak, he promised kanshi daidai da riga daya tak wanda Abie yasaimai shida Brother shi saiya cire ya kona ya zubar, komi na Abie daya saima shida Aadil saiya kona tass.



Dafashi da akayi yasa ya dago kanshi da kyar idanunshi sunyi jajir, Baba Suleman ne ya zauna kusa dashi yana kallonshi cikeda tausayawa yasan this is hard dole abin ya daki zuciyar Aabid da karfi. Murya chan kasa mai cike da calmness nason kwantar ma da yaro hankali yace "let it out Boy, let it out Hussain, Men cry too, am here for you, am here for you kaji" fadawa jikin Baba Suleman Aadil yayi yace "Uncle m...my....my father is is a ri...ritualist, he did all this thing to my brother, Uncle Abie, he feed us da bloodmoney, he cloth us da blood money, he did everything mana da kudin jini, Abie killed and ruin my brother's 30yrs of life, Abie yakashe mini kannai n...." zaiyi magana Baba Suleman ya taushemai baki yana sharemai hawayen daya dake zuba nonstop yace "is okay, is okay Aabid, kaddara ce haka Allah yariga ya tsara rayuwan dan uwanka Aadil, ahaka Allah yariga yarubuta zaiyi shekaru talatin a duniya batare da yasan waye shiba, koda Abie baiyi komiba one way or the other saikaga something happen dazaisa yay rayuwanshi ahaka, now lets all hope for the best, muyi creating new beginning and new memories and let's all forget d past okay, think of your Mum and think abinda take going through yanzu haka, wahala da dawainiyan Aadil tun yana jariri datasha kullum suna hanyan asibiti, sanan ga barin ciki har sau uku yaya kake tunanin takeji yanzu datasan dalilin? Ga kuma dan uwanka a asibiti shida matarshi yaya kake tunani takeji? Let's pray murokan ma Abie gafara daga Allah kaddara ce, dama annabi yafada aciki hadisi cewa kowace alumma nada fitinarta yace fitinar alumma ta itace dokiya, kaga arayuwan nan wasu mutane can do anything for money, inhar dai zasu sami kudi they can do anything, arayuwar nan tamu tayau mutum ya kasance mai godiyan Allah, d little da Allah yabaka ka godemai and be contented saikaga Allah will give you more masu albarka, one shouldn't be greedy da mugun son kudi, greediness dason banza can lead you to astray daga hakane zaka fara karban cin hanci which annabi yay hani akai yafadi ahadisi akan Allah ya tsinema mai bayar da cin hanci damai karba, yawan son kudi ma da mutane keso fitina ne, kudi kayane aka dan ranan gobe kiyama saikama Allah bayani akan each and every single kobo daka kashe, how? Tayaya ka kashe su ta hanya mai kyau ce kota hanyar sabon Allah ne sanan tayaya ka samesu ta hanyar halal ce, ta guminka ne kota hanyar haram, duksai kafadi ma Allah, saisa yakamata kowa kowani musulmi ya yawaita yin addu'a Ya Allah kabani dukiya ta halas, Ya Allah ka sanyama dukiyar Albarka sanan Ya Allah kasa na kashe su ta hanya mai kyau bata hanyar saboba, Allah yasa mudace kawai Aabid, Allah kuma yasa karshen mu tai kyau, Allah kuma ya kashemu muna musulmai sanan Allah ya ganar da dukkan musulmai dakeson kawai suyi kudi kota yayane kotahalin k'ak'a ne, sanan Ya Allah ya shiryi musulmai masu hali irin na Abie wayanda are willing to sacrifice koda mahaifiyar suce dandai kawai suyi kudi su sami abin duniya, wayanda zasu iya zuwa su sadu da gawa dan samin abin duniya, su sami kudi su sami na nunama jama'a ace wai wanan fa babba ne Alhaji ne motoci guda dari gareshi baya sati a nigeria yau yana dubai gobe yana china, Allah yarabamu da dukiyar dazata halaka mu, mu koma ga Allah kawai Aadil, is high time malamai sun tashi a tunatar sukuma tsawatar, kaga shi tunatarwa yana karkato da zuciyan mumini sanan yana kara samai tsoron Allah dakuma gujema kaba'ir, Allah yasa mudace, tashi muje masallaci muyi sallan asuba daganan saimu tafi gida dan akai Abdullahi gidan gaskiya, Allah ya jikanshi ya gafartamai yasa yahuta Allah kuma ya gafartamai kurakuran shi, May Allah forgive all his short comings" ahankali Aabid yace "Ameen" ya share hot hawayen daya zubomai deep down ko Allah yasani yanason mahaifinshi danshi shaida ne akan yanda mahaifinsu ke sonsu, sune komi na Abie amma wat can he do abu daya kawai zaimai shine ya rokamai gafara, yamai addu'a sanan yabude abubuwan sadakatun jariya wanda lada zai dinga kaimai kabari, saida Baba Suleman ya dagashi sanan ya iya tashi ko kadan baida karfi fita sukayi Baba Suleman da Muhammad suka rikeshi alwala sukayi sukai salla sanan suka fito suka shiga mota koda sukakai anguwan su mutane an cika fal tako ina, cikinsu harda baban Hamida da Abban su Ra'is dudda liman da Baffa sunriga sunce babu kyau fadin mummunan halin mamaci boyewa ake, addu'a kawai za'ama Abie saisa kosu baban Hamida ba'a fada musu gaskiyan abinda yafaru ba, banda limaman nan guda uku dasu babu wanda yasan zancen, ancedai wuta ce takama shine ginin ya zubo yafado kan Abie, sanan sukace musu antafi da Hamida da Aadil asibiti sosai su Aban Hamida sukai addu'a sanan sukai musu jaje aka dauko motar daga gidi aka daga ginin aka tattaro pieces din jikin Abie aka atattare awuri daya, rayuwan fa kenan! Saisa in this world d best thing to do shine kabi Allah koka samu kyakkyawan karshe, yau ina Abie dakeda kudi ghana masgo manya manya sama da dari na yan dollars? Ina Abie mai kampanin mota? Ina Abie maisa hadadden shadda dake kyalli yahau jeep yafita ina yake? Uban dukiyan daya tara yanzu sun hanashi mutuwa? Dukiyarshi ta taimakeshi? Ta amfane shi? Jama'ar musulmi mubi Allah mukoma ga Allah kar son kudi yarufe muku ido yasa kuyi sata, chacha, gambling, riba ta hanyar karban loan kabiya with interest and other ways, kisan kai, cuta, and many more, all kudin at d end of the day bazasu miki komiba bazasu tsinana miki komiba afarin kyalle za'a kaiki/ka, Allah ya gafarta mana kura kuran mu ameen yabamu ikon cin jarabawa dan no body is perfect, Allah saidai yasamu a aljanna dan rahaman sa badan aikin muba dan we are not doing enough.



Haka aka tattara Abie bayan an sallace shi aka kaishi makwancin shi duk dauriya da taurin zuciyan Aabid saida ya dinga kuka wata irin nadama ta shigeshi shima ya shiga tubanma Allah akan kurakuran shi, shan giya bin mata yay taubatan nasuha yama Allah alkawari bazai karaba, dawowa gida akayi ana amsan gaisuwa, Mama da Anty Lami da Kaka harda Zainab da Ihsan suma suka shiryo sukazo gidan gaisuwa ananta lallashin Mami da idanunta suka kumbura sosai babu wanda zai ganta dabazai tausaya mataba bayan sun gama aka kaisu hospital sukaje duba Hamida da Aadil danhar lokacin bacci suke bama asan ranan farfadowan suba.






***
_Bayan Wata Daya_

Yauwa yanzu labari zai fara dadi na zare Abie 😜😜😜



Ya Allah ya gafarta ma wayanda suka rig[2/17, 2:37 PM] +2347066933957: ....





Yace "D...Dil" murmushi Aadil yamai asanyaye yace "Bid" Aabid couldn't believe wat he is seeing, ahankali yabude hanunshi alamun big hug dan d way he's feeling right now happiness din ganin twin brother shi, Aadil as normal person jiyake kaman zuciyarshi zata fashe, da sauri Aadil ya shigo dakin yabude hannayenshi shima da sauri Aabid yataho sukai hugging juna so tight, Aabid sai hawaye yawani irin kankameshi yace "I love you Twin, I love you so much Hassan, I love y..." yakasa magana sai hawaye amma mara kara ta yanda Aadil dinne kadai zai iya jinshi, rungume dan uwan nashi yayi tsam ajikinshi yace "I love you more Twin, I love you so so much, I love you Hussain, am feeling somehow i don't know wats wrong with my head inajin wani iri, did anything happen to me? ina Abie?" jin kukan Mami yasa da sauri yasaki Aabid ya kalli Mami data zauna akan kujera tana wani irin kuka mai tsuma rai she can't believe Aadil yawarke bata taba sanin cewa zataga wanan rana aduniya ba dan tariga ta yanke tsammani, ahankali yakaraso yay kneeling agaban Mami yakamo hanunta yarike gam yana kallon fuskarta kaman zaiyi kuka yace "why are you crying Mami?" girgiza mai kai Mami tayi tadaura hannayenta akan fuskarshi tana tattabashi cikin kuka tace "Aa...dil" sashi tayi ajikinta ta rungumeshi a kirjinta tsam tsam tana kuka tadago kai ta mikama Aabid dake share hawaye shima hannu yana kallon su, da sauri yazo tahada su biyun ta rungume su ajikinta tana hawaye, big Mum ma kuka take takasa dena hawaye tana kallonsu, Baba Suleman ne kawai yayta maza bai zubda hawaye ba amma sun bashi tausayi da sauri big Mum ta share hawayen fuskarta tace "laaa Hamida, kai Aadil barinta kai awaje" sakin su Aadil Mami tayi jin an ambato Hamida da sauri ta tashi tsaye tace "dama tare kuke?" "eh harda ita aka sallama" da sauri Mami tai hanyar waje tabude kofa tafita, atsugunne taga Hamidan ta rabe abango ta tsugunna kaman wata marainiya dan tagaji da tsayuwa, da sauri Mami tace "Amatullah" dago fuskarta tayi ta kalli Mami asanyaye, da sauri Mami ta dagata ta rungumeta da sauri ajikinta, jin Hamida take har ranta bubbuga bayanta tayi tama kasa magana sabida yanda taji gabaki daya damuwarta sun kau matar danta da danta duksun warke, sakin Hamidan tayi tai cupping face dinta tace "muje ciki kihuta" shigowa sukayi tareda Hamidan Aabid yakafeta da ido dudda kanta nakasa bai samu yaga fuskarta ba but he's still very happy ganin ta tashi takuma ji sauki, tashi Aadil yayi daga kan kujeran ya kalli Aabid yace "am sleepy Bid, zanyi wanka, let's go to our room" hararanshi Aabid yayi cikin tsananin sonshi dawani irin kewanshi yace "dakina dai, kai dakin ka dana matarka daban danawa" kallonshi yayi kaman maison gane meyace hakan yasa ya maimaita maganan shi din yace "dakina dana matata?" sosai Aabid ya danne zuciyarshi dan yariga yay alkawari he's now a changed man, ya kalli Hamida dake zaune kusada Mami tana wasa da yatsunta Mami na duba jaws dinta da aka cirema bandeji yace "Mami bashi matarshi suje suyi wanka su kwanta duk sun gaji" wani irin juyawa Aadil yayi da kyau ya kalli Mami dakuma yarinyar da Aabid yake cema ace tazo tabi mijinta suje su kwanta sanan ya sake kallon Aadil yanuna kanshi da yatsa yace "matata?" kafin Aadil yay magana Mami ta janye hanunta daga jaws din Hamidan tace "eh matar ka, Hamidar ka baka ganeta bane Aadil?" nuna Hamida yayi da yatsa daga sama har kasa yace "wanan yarinyar ce Matata Mami?" tambayar shi bakaramin dukan zukatan yan dakin yayiba hakan yasa kowa ya kallai, ahankali Hamida ta dago idanunta dasuka cika da kwalla sosai ta

Please Login or Register in order to submit comment