Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanzu haka, bansan wani hali Aadil dina yakeba, tayaya zan iyacin abinci bansan wani hali my poor innocent boy yake cikiba" hanunta Aabid yakamo yarike zaiyi magana Baffa da shigowan shi dakin kenan kusan shi yamafi kowa damuwa ya nunata da Sanda cike da masifa yace "tashi ki karbi shayin nan kisha, kashe kanki zakiyi tunda yaro yabata babu abinda kika sama bakin salati, tashi ki karbi shayin nan kisha Maryama kona mugun saba miki wlh" cikin kwantar da murya Suleman yace "ya isa Baba muje kahuta kaima bakajin dadin, yanzu nida Abdullahi zamu koma police station din da Hussain" wayar Aabid ne yay ringing da sauri yaciro wayar daga aljihu ya kalli screen din, da sauri yadaga kai ya kalli Abie dake kusa dasu Baffa yace "Inspecta ne" da sauri Mami ta yunkura ta tashi zaune tanajin wani irin masifaffen ciwon kai tace "dauka hala anga Aadil dina ne" da sauri yay picking call din yakai wayar kunenshi daga tachan bangaren inspecta yace "yallabai..." da sauri Mami da jikinta har bari yake tace "sa, saka a speaker Son" zare wayan yayi daga kunenshi yasa a speaker yace "i can hear you inspecta kace mene?" "yallabai jami'an tsaro damuka baza a kowani anguwa ne muka sami wani information da safen nan dayasa muke bukatar kuzo kuyi comfarming ko shine" da sauri Mami ta fizge wayar daga hannun Aabid tsabagen yanda jikinta ke bari tace "inspecta anga d'ana?" anatse inspecta yace "abinda yasa nake neman ku kenan anga wani amma shi gaskiya ga dukkan alamu ba kidnapping dinshi akayiba kaman yanda muke zargi ba, dawata mace muka ganshi yanzu haka suna under our watch suna wani uncompleted building da ba'a gamaba awata sabuwar unguwa, na zuba jami'an tsaro da yawa a anguwan tayanda bazasu fitaba harsai kunzo kun tattance idan shine na hoton dakuka bamu, dan gaskiya wanan yay datti sosai yay budu budu kaman mahaukaci ko takalmi babu akafarshi kawai nadai ga dan kamaninsa da wanan saurayin daya kawo case din offis ne saisa mukace bari mukira" da sauri Mami ta share hawayen dake zubo mata tace "i...ina...inane wurin?" "zan tura muku address din yanzu" ya katse wayar saukowa Mami tai daga gadon tai baya luuu zata fadi sabida rashin karfi babu abinci acikinta tun jiya da sauri Aabid ya riketa, Baffa ne yace "ki zauna agida bari mu muje" fashewa tayi da kuka tace "Baba dan Allah zanje" share mata hawayen Aabid yayi yadau mayafinta ya yafa mata yace "muje grandfather muje da ita" fita dukan su sukayi harda big mum, Kafin ma su shiga mota har inspecta ya tura musu address din location din suka shiga manya manyan jeep dinsu kusan guda uku sukaja suka sukabar gidan.

Tafiyan wurin 25min yakaisu anguwan, parking sukayi agaban junction din anguwan nan inspecta da sauran yaranshi suka fito daga inda suka boye, fiffitowa daga mota sukayi inspecta yakarso wajen yace "muje".....




Yanda yake wani irin shishigewa jikinta yana numfashi da sauri da sauri yasa ta tureshi tace "stop" make mata kafada yayi da idanunshi dasukai ja sundan kankance kaman zaiyi kuka yace "am sleepy" matsawa gefenshi tayi da sauri tace "to sleep ga fili nan" make mata kafada yasakeyi hawaye ya cicciko a idanunshi yace "i want to sleep on your body" yay maganan yana matsowa kusada ita gabaki daya idanunshi sun chanza kala, da sauri ta mike tsaye adan tsorace ganin yanda ya chanza, kadangare tagani abango da sauri ta matsa baya tace "wayyo lizard" kallon bangon yayi kafin ya fizgo riganta tabaya juyowa tayi da sauri ta kallai tamai pointing lizard din tace "come let's play with lizard, kadangaren babba ne sosai ko" tashi tsaye yayi shima batare daya saki riganta ba ya kalli lizard din sanan ya kalleta yanda yaga tana kallon kadangaren tana komawa baya alamun tsoron kadangaren take yasa yaturata da karfi yace "lizard catch her" ihu tayi sosai takoma bayanshi da gudu ya kyalkyace dawani irin dariya yana clapping hands dinshi yace "Hamida my wife is afraid of lizard" kaman daga sama idanunshi suka sarke dana Mami data fara kunno kai dakin.
_🌹 IN BANI 🌹_



Maman Abd Shakur


23 & 24

_This novel is for sale karki karanta in baki biyaba_

_in kinason this novel, xaki turo 300 access fee to 3107021073 first bank aisha Muhammad, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461_


_you can also send MTN card ta watsapp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting_





Ware manyan fararen eyes dinshi yayi yana wani irin cute smile yace "Mami" daidai lokacin sauran mutanen duk suka iso sukai turus ganinshi tsaye yana kallon Mami dasu dasuka karaso wajen, dan duhun data gani dan sunyi blocking ray din rana dayake shigowa ta kofan yasa ahankali tadan leko da kanta daga bayanshi, mutanen data gani yasa da sauri ta komar da kanta bayanshi ta labe.

Sake zaro ido Aadil yayi sosai ya kalli Aabid dayay shiru yana kallonshi kaman yanda kowa na dakin ke kallonshi yanda yay mugun butu butu, wandon jikinshi kaman an kwaba kasa akai, kafarnan da babu ko takalmi ajiki tai busu busu, shimin jikinshi ma tai datti idanunshi sunyi suntum sunyi wani iri alamun yaci kuka, fashewa dawani irin Kuka Mami tayi ta shigo dakin da sauri tayo kanshi tace "Aadil, my baby" budema Mami hannu yayi yana wani irin jumping yana murna kaman dan yaro. "oyoyo Mami, oyoyo Mami, oyoyo Mami na" tana karasowa gabanshi yawani irin fadajikinta ya kankameta yana tsalle da kafa hakan ya bayyanar da Hamida dake labe abayanshi ta sunnar dakai kasa tama rasa ma me zatayi har wani soshe soshe take, kallon ta Mami da duka kowa na dakin suke yi barin ma Aabid dayaji gabaki daya numfashin shi ya tsaya chak, Cikin wata irin murya yace "Amatullah" da sauri ta dago kanta ta kalli direction din da aka kira sunanta daidai lokacin Aadil yasaki Mami shima yajuyo cike da murna yace "Mami look at Hamida, my wife" kallon Aabid Hamida tayi saikuma ta kalli Aadil dayay magana yanzun nan wani irin faduwa gabanta yayi bana wasa ba dan bambamcin da ayanzu tagani ajikinsu shine daya tsaf tsaf yake yaci shadda gizna kanshi sanye da hula tangaran, shaddar jikinshi har wani irin kyalli yake yana walkiya sai dayan kuma wanda yake daka daka yana sanye da singlet da dogon wando amma kamaninsu daya tsaf, kasa kallon sauran manyan mazan dakin tayi da tsohon dake sanye da glsass yana rike dayar Sanda tasake sunnar dakai tahade hannayenta dake wani irin bari tana murzawa da sauri da sauri tana numfashi sama sama. Sakin Mami Aadil yayi yaje dawani irin gudu yafada jikin Aabid batare daya lura da yanayin dayake ciki ba yaja hanunshi yace "come, come and talk to My Hamida Bid" yaja hanunshi yakawo shi gaban Hamida da kanta ke kasa har lokacin tana murza hannuwanta yace "Bid see my Hamida" yasaki Bid yajuya da sauri ya kalli Mami daketa binshi da kallo kaman zata hadiyeshi da so yace "Mami see Hamida my wife" da gudu yay wurin Baffa yafada jikinshi wani irin murmushi tsohon yayi ya shafa kanshi yace "Hassan" da sauri ya dago kanshi yana turamai baki a shagwabe yace "Am Aadil grandfather not Hassan" sake bubbude manyan idanunshi yayi yakama hanun Baffan yace "zokaga My Hamida Baffa" da sauri yakawo grandfather wajen, sanan yakoma yana wani irin tsalle yana kallon Abie da idanunshi sukai jajir yanamai wani irin murmushi kaman ya cinyeshi da so yace "Abie come and see my Hamidaaa" yaja hanun Abie yakaishi wurin kafin yakoma ya kwaso duka Uncles dinshi yakaisu gaban Hamida sanan ya tsaya shima kusa da Aabid yana kallon Hamidan da duk suka tsaya suna kallonta babu wanda yay magana cikinsu yana murmushi yace "Bid u see my Hamida, she's my Hamida" wani irin murza hanunwanta Hamida take jikinta nawani rawa, murmushi Mami tayi tace "baiwar Allah a ina kikaga Aadil?" ahankali tadago kanta ta kallesu, wani irin jiri tafara gani yanda duk suke kallonta bakinta har rawa yake tana nishi sama sama tace "i...ina...na...w...wun..." batakarasa gaisuwan ba tai wani irin baya a sume dan kwalin ta data lulluba dashi tai daurin ta wuya ya xame yay kasa arude Aabid ya mika hannu zai tarota yace "Amatullah! " arude Aadil yamika hanunshi zai tarota shima yace "my Hamida" da sauri Aabid yatarota Aadil ya tsugunna ya dafa kafadar Aabid yana kallonta yasaki kuka yana kallon fuskarta yace "wat happen to her Bid?" dagokai Aabid yayi yace "mutafi da ita gida Mami" da sauri Abie yace "munsan tane da zamu kwasheta mutafi da ita gida?" makemai kafada Aadil yayi yana goge kwallan dayake hakan yasa Baffa yace "muje akira likita yadubata koba komi ga Aadil nan yasaba da ita, daga gani ita ta taimake shi, kumuje, yaka Aadil" zuwa wurinshi Aadil yayi yana waigen Hamida da Aabid yadaga, Baffa yarike mai hannu duk suka dunguma suka fita daga wajen, saida suka salami su inspecta sanan suka shiga mota sai gida.



Wani hadadden daki Aabid ya shimfidar da ita kan makeken gadon dake dakin yana kallon fuskarta, tsugunnawa Aadil yayi gefen gadon yana kallonta shima idanunshi yay jajir, ahankali Aabid yajuyo da kanshi yana kallon yanda Aadil ke kallonta yana leka fuskarta, runtse idanunshi yayi da karfi yanajin ciwo aranshi sosai, daidai lokacin Mami ta shigo dakin karasawa tayi gaban gadon ta zauna ata saitin kafafun Hamidan tana kallon fuskarta tace "ga Dr nan zuwa ya dubata Baba yakira shi, Aabid stay with her karta tashi bakowa" ta kalli Aadil dake wani irin kallonta tamikamai hannu tana murmushi tace "come Aadil, muje kai wanka and change this cloth, kaima Dr zai dubaka inyazo duba friend dinka" make mata kafada yayi yana hararanta a shagwabe yace "she's my wife" shiru Mami tayi tana kallonshi saikuma tai murmushi tace "naji, muje kayi wankan to kafin kafito nahada maka abinci" tashi yayi ahankali kanshi narawa yana kallon Hamidan tashi itama Mami tayi taja bargo ta lullubeta dashi tarike hanun Aadil suka fice suka rufo kofan, wani irin runtse ido Aabid yayi yafuzar da iska kafin yadaura hanunshi kan zuciyarshi yana dukan zuciyarshi yay hakan kusan na 2min sanan yadawo daidai, zama yayi agefen gadon yay shiru yana wani irin kallon fuskarta, dawani irin murya mai rauni sosai yace "tayaya kika hadu da brother na Jewel? I'm the one for you Amatullah" yay shiru yana kallon fuskarta, knocking da akayi yasa yatashi yay wurin kofan bude kofan yayi Dr ne da Baffa suka shigo dakin, Baffa yace "yauwa gatachan likita adubata" karasawa Dr yayi bakin gado yaduba ta sanan yaciro drip daga katon jakan hanunshi yamata fixing yay allura aciki wurin 15 minutes yabata akanta sanan yajuyo ya kalli Baffa yace "fever ne kawai, i guess tsoron kune yasta ta suma, yanzu dai komi lpy dazaran drip dinan ya kare aciremata and yanzu dai bacci take zuwa anjima chan haka zata farka" murmushi Baffa yayi yace "masha Allah itace taga jikana ta taimaka mai, muje kadubamin jika" wucewa sukayi suka fita daga dakin Aabid yadawo ya zauna.

Duba Aadil Dr yayi yarubuta magungunan daza asayomai sanan yamai allura da kyar ya yarda akamai, yaci abinci nan wani baccin gajiya da wahala yay gaba dashi shima.



Saida yay bacci sanan Mami tarufa mai bargo takashe wutan dakin nasu tarage karfin Ac tafito, dakin da Hamida take tawuce ahankali tabude kofan har lokacin Aabid na zaune agefen gadon yazuba mata ido, budewan kofan dayaji yasa yadago kai, murmushi Mami ta sakinmai takaraso ta zauna kusada shi, ahankali yadaura kanshi kan kafadarta ya sauke ajiyar zuciya, shafa kanshi Mami tayi tace "menene Son?" dan murmushin yake ya kakalo mata yace "babu komi Mami na" dagashi tai daga kafadarta ta kalli fuskarshi jin yanda yay maganan danta tabbatar da abinda ke damun shi, lumshe ido yayi da sauri dan yasan tsaf Mami zata gano da damuwa a idanunshi, ahankali kira sunanshi. "Aabid" bude idanunshi yayi ya kalleta, nunamai Hamida tayi da ido tace "you called her Amatullah dazu kasanta ne daman?" shiru yayi yana kallon fuskar Mami kaman bazaice komiba saikuma yace "eh nasanta a Lagos nataba ganinta tafada ruwa nacirota nakaita asibiti daganan bankara ganinta ba saiyau" murmushi Mami tayi tace "Allah sarki, hala saisa itama ta taimaki Aadil maybe tazaci kaine" murmushi tasakeyi tasake jan kumatun shi tace "tashi muje kaci abinci idan ta farka sai a gaggaisa da kyau amata godiya saimu maidata gidansu ko" gyadama Mami kai yayi yatashi suka fita daga dakin, dining ta kaishi tazubamai abincin kadan ya iyaci sanan yakoma ya zauna a falon yana kallon CNN amma gabaki daya hankalinshi nakan dakin da Hamida keciki.



Kiran sallan azahar dayaji yasa yatashi yafita masallaci hakanan yakejinshi wani iri yarasa mesa kalman da Aadil yafada saimai yawo yake a kunne. "Hamida my wife" runtse ido yayi da karfi da kyar ya lallaba ya shiga masallaci yaje yay salla sanan yadawo ya bude kofar dakin datake har lokacin bacci take, maida kofar yayi yarufe yakoma kan kujera ya zauna har akai la'asar yasake dawowa ya lekata har lokacin bacci take yakoma kan dogon kujera yasake zama yana chanza tasha zuwa tashan kwallo.

Bude kofan da akayi yasa yadago kai Aadil ne ke saukowa yana sanye da plain white t-shirt dakuma wani black 3quater sai uban kamshi yake yay wani irin kyau da inka kallai saika kara, hanunshi rike da manya manyan chocolate guda biyu acikin ledan su, Aabid daya gani azaune yasa ya washe baki yataho da sauri yana tsalle tsalle, shiru Aabid yayi yana kallonshi shi kanshi baisan meka damun shi ba hakanan yaji yanajin haushin shi bana wasaba yakasa manta kalman Hamida my wife dayafada aranshi, inda dane all this tsalle tsallen dayake yi idan yaganshi yanajin dadi amma yau sosai yakejin haushin shi, fadowa jikinshi da Aadil din yayi yasa yadan fuzar da iska yatureshi kadan, dago kai Aadil yayi yaleka fuskarshi yana murmushi, dan murmushin yake Aabid ya sakan mishi ya lumshe ido batare dayacemai komiba, hakan yasa da sauri Aadil ya kalli chocolate din hanunshi dudda ya daukoma kanshi ne da Hamida amma saiya mikamai daya da sauri yace "Bid" dan bude ido Aabid yayi ya kalleshi ya kalli chocolate din dayake mikamai, girgizamai kai yayi yatureshi murya chan kasan makoshi yace "stand up from my body" kin tashi yayi yay shiru yana kara leka fuskanshi kaman maiso gano abinda ke damun shi wani irin tsawa Aabid ya dakamai tareda tureshi da karfi daga jikinshi yace "nace katashi daga kan jikina ko" yay maganan yana tureshi dawani irin fushi yafadi akasa, atsorace Aadil ya kallai dan idan da abinda ya tsana a duniya yakuma kejin tsoro bai wuce tsawa ba, tsaki Aabid yayi cikin fushi yatashi yana kakkabe shaddar jikinshi da Aadil ya yatsine yawuce yafita daga dakin, binshi da kallo Aadil yayi idanunshi nataruwa da kwalla sosai, ahankali ya lankwashe kafa anan kasan falon ya shiga kuka yana share ido yana kallon kofan, kukan shi da Abie yaji yasa ya shigo dakin da sauri dan shigowan shi kenan gidan, karasowa yayi inda yake zaune akasa arude dan kowa nagidan nan ya tsani yaga abu nadamun Aadil yace "menene? Why are you crying" kasa bama Abie amsa yayi sabida yanda Aabid yaturashi kemai ciwo baitaba mai hakaba, da sauri Abie yaciro handkerchief daga aljihun shi ya sharemai bakinshi da fuskarshi yace "wai menene? Why are you crying haka?" kasa magana yayi sai kukan dayake yi sosai, sallama Baffa yayi ya shigo shashin da sauri daidai lokacin itama Mami tafito dan dama wanka take, da sauri Baffa yakaraso yana dogara sanda ya kalli Abie yace "me kuka mishi wai? Yaufa yadawo harkun fara sakashi kuka, dan Allah kome yakeso kudinga mai gobe za'a faramai maganin, daga sokoto mai maganinshi dana kira zaizo" ya zauna akan kujeran dake saitin Aadil din dake kuka sosai yake yadafa kanshi yace "menene? Waya tabamin Hassan iyye?" makemai kafada Aadil yayi cikin kuka yana turomai baki yace "my name is Aadil right Mami" dariya dukansu sukayi harda Baffan yace "dan tselen uwa gadai ubanka nan katambaye shi da aka haifeka Hassan aka yanka rago aka sakama, yanzu dai dena kuka kaji, zomuje mu baga basket ball" yay maganan yana zazzago glass din idanunshi cike da tsokana, Mami murmushi tayi ta tashi ta wuce kitchen dan kawomai fruits din data yankamai ta sakamai a fridge. Makema Baffan kafada yayi yana turo baki yana goge hawaye da bayan hanunshi dayake rike da chocolate da sauri Abie ya karbi chocolate din yace "kawo nan karka tsole idanunka dasu" turoma Abie baki yayi sanan ya kalli Baffan dake kallonshi yana murmushi ya makemai kafada yace "you don't know how to play basket ball bazan buga dakai ba, i will only play with Bid ko Abie" ya kalli Abie dayay shiru yana kallon d'an nashi feeling wani irin guilt, murmushi Abie yayi ya mikamai chocolate din yace "hakane, nabude ma chocolate din?" gyadamai kai yayi ahankali hakan yasa Abie yabude mai daya ya mikamai, karba yayi yakai bakinshi ya gutsura yanaci kallonshi Abie yayi kafin yatashi ya shafa kanshi yawuce yafita dan yanda yakeji yasa bazaima iya shiga gidan ba yawuce ya shiga motarshi yafita daga gidan, binshi Baffa yay da kallo ganin damuwa akan fuskarshi amma bai kawo komiba dan yasan damuwan bazai wuce ta Aadil bace, taba keyan Aadil yayi hakan yasa Aadil yajuyo ya kalleshi, gefenshi Baffa ya nunamai hakan yasa ya murgudamai baki sanan yatashi ahankali ya zauna a kusa dashi, hannu Baffa yamika mai yace "bazaka sammin ba" wanda yakeci ya mikamai hakan yasa Baffa ya makemai kafada kaman yanda yakema mutane yace "ni kabani wanchan sabon shi nakeso" makemai kafada Aadil yayi sosai yace "this one is for Hamida my wife" zaro ido Baffa yayi cikeda wasa yace "wife kuma Hassan" gyadamai kai yayi da sauri yana washe baki yace "yes i will marry her, she will be my wifeee, just like Abie and Mami" yakarashe maganan awani irin sangarce yana murmushi yana fari da ido sosai, shiru Baffa yayi yana kallonshi yama kasa magana tashi Aadil yayi daga kan kujeran yasa chocolate din a bakinshi ya ballomai yakamo hanunshi yasaka mai aciki yace "bye bye Oldman, lemme go and see My Hamida, Mami" ya kwalama Mami kira kaman zaiyi kuka yace "my fruits" fitowa Mami tayi daga kitchen tamikamai bowl dake cike da sliced fruits dasukai sanyi sosai da fork ya karba da gudu yana tsalle tsalle yay hanyar dakin Hamida Baffa yabishi da kallo har lokacin maganan da Aadil din yayi na ringing akanshi saikuma yay murmushi yaciro wayarshi daga aljihu yatashi yana dogara sandarshi yafice daga dakin yaje rumfan da akamai musamman ta zama ya zauna yay dailing wata number.


Tura kofan yayi ya shiga dakin yana rike da chocolate din gam da bowl din fruits din, hada ido yayi da Hamida da bude idanunta kenan, da sauri yatura kofan yarufe yazo wajen gadon yana tsalle ya ijiye fruits din agefe, wani irin farin ciki yakeji idan yaga fuskarta bana wasaba, ahankali ta dafe kanta ta tashi ta zauna da kyar tana kallon karin ruwan dake hanunta wanda kadan kadan yake shiga jikinta, wani irin tsalle yayi yafado kan gadon yana leka fuskarta yanda ta runtse ido, dawani irin murya chan kasa yace "My Hamida" ahankali tabude idanunta ta daura akanshi tai shiru tana kallonshi yanda yay wani irin kyau sai kamshi yakeyi farin t-shirt din jikinshi yakamashi daidaishi, murmushi yamata yamika mata sabon chocolate din hanunshi da sauri yace "take" sake lumshe ido tayi tana kara tuna irinshi biyu tagani fa dazu, ganin tai shiru taki karba ta shareshi kuma taki bude ido yasa yafada jikinta kaman zaiyi kuka yace "Hamida my wife wat is it? Are you sick?" da sauri ta bude idanunta ta shiga tureshi da hanunta daya mai lafiya cikin yar siririyan muryanta tace "kadagani" daidai lokacin aka bude kofa aka shigo, da sauri ta dago kanta tana tureshi sukai ido biyu da Aabid da shima ya chanza kaya zuwa black 3quater da white long-sleeve t-shirt dan hakanan yaji yanadan jin sanyi sanyi kaman zaiyi zazzabi wani irin kallo ya watsa musu yana tsaye a wurin yay folding hand dinshi akirji hakan yasa gabanta yawani irin fadi da hannu tasake tureshi tace "ka dagani Aadil" make mata kafada yayi ahankali yana turo baki yace "u are angry with me Hamida my wife" da sauri bakinta har rawa yake tace "a'a am not nika dagani" da sauri yadago kanshi ya kalli fuskarta yana wani irin murmushi yana kallonta yace "yay am happy my wife, take my chocolate" yay maganan yana ciro chocolate din dake bakinshi yakai saitin bakinta yana ware manyan eyes dinshi dawani irin excitement yace "d chocolate is very sweet Hamida my wife" yakai bakinta, kin bude bakin tayi ta kawad da hanunshi, kaman zaiyi kuka ya make mata kafada. "oh'oh" yasake kaiwa bakinta da sauri, kin karba tayi hakan yasa yasaki kuka yafada jikinta zai kankameta, wani irin fizgoshi akayi a zuciye da sauri ya juyo da kanshi hada ido yayi da Aabid da idanunshi sukai ja, kafin ma yace wani abu Aabid yawani irin fizgoshi kaman zai karyashi ita kanta Hamidan saida ta tsorota yawani irin jashi yafitar dashi daga dakin yabugo mata kofa yay dakinsu dashi, bude kofar dakinsu yay azuciye yawani irin turashi da duka karfinshi saura kadan ya buge kanshi a gado yadafa bangon yana haki, da sauri yadago kai ya kalli Aabid din daya mayar da kofa ya rufe yanamai wani irin mugun kallo, yayo kanshi a zuciye yana tattare hanun riganshi sama hakan yasa Aadil yakoma jikin bango a tsorace idanunshi yataru da hawaye sosai yana kallon Aabid din da mugun mamaki dudda baida Ishashen hankali hakanan saiyake ganin Aabid kaman bashiba yau, dan koda wasa ko amafarki Aabid baitaba koda dauremai fuska ba balle ya hankadashi haka cikeda tsana.



Wani irin tsayawa Aabid yayi agabanshi yay folding hanunshi akirji yana wani irin kallonshi, ahankali Aadil ya saukar da kanshi dake rawa sosai kasa hakanan yaji yana wani irin shakkan Aabid din for the first time in his life, ahankali kanshi na rawa sosai ya matsa ta gefenshi batare dayace komiba yazo zai wuce shi da sauri, wani irin fizgo hanunshi Aabid yayi azuciye yadawo dashi inda yake har saida yabuge bayanshi da bango cikin tsawa yace "where do you think you are going?" sosai idanunshi suka cicciko da hawaye kaman maison kara tantance anya Aabid ne wanan yadan dago kai ya kalleshi ganin shine dai yanamai wani irin mugun kallo yasa ya saukar da kanshi dake rawa sosai kasa cike da tsoro dawata irin murya chan kasa yace "i want to go to Hamida My wife's place" wani irin fizgoshi Aabid yayi yarikemai wuyan riga yace "karka kara cemata your wife" makemai kafada yayi ahankali atsorace hawaye na gangarowa daga idanunshi yace "i don't want to stay here, i want to go to Hamida my wife's place" cikin wani irin bakin zuciya Aabid ya sakeshi yadaura hanunshi kan belt din jikinshi yana kwancewa yana zarowa yana kallonshi yace "karka kara cemata your wife" makemai kafada Aadil yayi hawaye na fita daga idanunshi sosai yace "she's my wife i will marry her just like Abie and Mam..." wani irin zaulamai belt din Aabid yayi da duka karfinshi cikin fushi sosai yace "karka sake cemata your wife" makemai kafada Aadil yayi yafashe da kuka sosai yana sosa kirjinshi da cinyarshi da belt din yasama sabida azaba da zafi dayaji yace "Hamida is my wife" zaulamai belt din yayi da shegen zafi hakan yasa yay ihu cikin kuka sosai yana sosa wajen yace "stop beating me Bid" shima Aabid cikin ihu yace "kaima stop calling her your wife and karka kara rungumeta, she's my Jewel" Make mai kafada Aadil yayi cikin kuka sosai yace "Hamida is my wife" wani irin mari Aabid ya daukeshi dashi da saida yaga wuta da jiri cikin wani irin layi idanunshi najuyawa sosai yace "she's my wife" bugashi da bango Aabid yayi ya shiga dukanshi sosai yace "kai mahaukaci ne, Aadil kai mahaukaci ne bazaka taba aure ba danba abinda kasani kanajina, u are mentally unstable, kai pagal ne stay away from my Jewel kanajina mahaukaci" makemai

Please Login or Register in order to submit comment