Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kaka batai laifi ba dan ko kadan Ammi batada kirki yana ganin yanda takema yan aiki wani zubin ma shiyake hanata, yasan mahaifiyarshi sosaisosai. Yakai kusan 5min a wurin yana tunane tunane sanan yaja mota yabar wajen yadau hanyar gidansu.

Faruk yaron kanin mahaifin su Hamida ne, shika dai suka Haifa shikadai ne kuma jikan Kaka namiji, inda Baban su Hamida yahaifi yara bakwai dukansu mata, baban Faruk ya rasu a plane crash ne, his Mum is from a rich wealthy family, bayan rasuwan baban Faruk Faruk yadawo hanun Abba da Kaka, rashin mutunci Ammi tazo tai dasu Kaka akan abata danta, in other to maintain peace yasa Abba yacema Faruk yakoma wurinta but dudda haka kullum yana gidansu, weekend yana yawan zuwa gidan kajin Abba yana tayashi aiki dan sana'ar baban su Hamida kenan saida kaji da Kwai and he's making it Alhamdulillah Allah ya sanya mai albarka a sana'ar.

**
Dan lekowa tayi daga inda ta labe ganin yatafi babu yasa tafito ahankali tana tafiya da sauri da sauri wani kantin taje dayake safiya ne ba mutane sosai, take away abinci merai da lafiya tayi guda biyu tabiya kudi ta karba tafito tafita daga school din gabanta na faduwa sosai, kasa samin Keke tayi hakan yasa tafara tafiya akasa tana kakkare fuskarta, saida tai nisa sosai tamugun gaji da tafiya takai junction din wani layi keke napep ta tare ta shiga tace "old railway" "hajiya dari uku" ahankali kanta akasa tace "muje" tada keke napep yayi suka shiga hanya, sukayi tafiyan kusan 15 minute yakaisu wurin, ahankali ta sauko taciro dari uku tabashi batare data kalli fuskarshi shi tajuya ta shiga wajen tana kallon kan kujeran da Baba yake zama yanajin yar radio shi ganin bashi yasa ta karasa wajen, takeaways din ta ijiyemai ta ta wuce ciki hango wasu samari tayi kusan biyar ko shida zaune a inda ta saba zama suna kokarin kunna wiwi da sauri ta juya kafinma su lura da ita, cin karo tai dawani abayanta idanunshi jajir da alamun yasha yai tatil yace "ke waya kiraki nan?" kwalama sauran dabama su lura da ita kira yayi yace "babaa jimana, tawaye ne tazo? Ba munce babu wacce zai kira tashi nanba yau" da sauri amugun rude tai gefenshi zata wuce yatareta yace "ki tsaya mana baby nakira miki su, hala wajen Sani kikazo dan nasan mayen da shegen iya zabo zafafan mata" arude tana dan waigen bayanta jin sahun mutane suna zuwa ta kwalama tsohon dake gadin wajen kira. "Baba, Baba" daidai lokacin sauran sun iso wajen fashewa sukai da dariya dayan yace "Baba wai me gadi kike kira? Ke yarshi ce?" daya daga cikin su yace "kaima jibeka dawata magana ina Baba mai gadi yakeda kyan haifan irin wanan lu'u lu'un?" daya daga cikinsu yace "kodai me zuwa bashi kayane?" kulle bakinsu sukayi suna zaro ido irin na isgilanci atare sukace "tsoho yaji chakwai" fashewa tai da kuka ta duka a tsakiyan su tana kwalama Baba kira. "Babaa" daya daga cikinsu yace "ankai Baba kauyen su Baba ba lafiya muma fanshi Baba yau, kingan mu mushida kici har ki koshi ko yan mata" yay maganan zai kama mata hannu boye hanunta tayi ajikinta tafashe da kuka, hijabinta ya fizgo ya mikar da ita tsaye fasa wani irin ihu tayi a mugun tsorace ta bugamai kafarta hakan yasa yay baya yasaketa yana tsaki dan yaji zafi da sauri sauran sukayo kanta tawani irin kwasa da gudu tana kuka wanda ta hambaran yawani irin tadiyota tafadi akasa hancinta ya shiga cikin dan kasan yashin dake wurin.
_🌹IN BANI 🌹_




Maman Abd Shakur


16....



_This novel is for sale, karki karanta in baki biyaba_

_in kinason novel dinan zaki turo 300 access fee to 3107021073 first bank aisha Muhammad saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461_

_you can also send MTN card 300 ta watsapp number na 07012181461_





Kafafunta yajawo tafasa ihu sosai tana kuka ta dibi kasan wajen da hannuwanta biyu ta juyo da kanta cikin kuka, watsa musu kasan tayi a idanu hakan yasa ya saketa da sauri yay ihu shida sauran suna sosa ido suna kokarin budewa sun kasa, dawani irin sauri ta tashi tadau jakanta taruga aguje suka biyota, fitowa tayi tana gudu sosai tana kuka, black hijabin ta gabaki daya ya baci da kasa tana gudu suna binta....


Anatse Mami ke tuki taci gayu sosai tasa wani hadadden exclusive atampa brown da yellow dayay mata kyau tayafa wani babban mayafi brown tana tuki, gefenta kuma Aadil ne yana zaune agaba yana wasa da fingers dinshi yana counting dinsu one, two, three, yana sanye cikin wani Fendi white t-shirt daya kama jikinshi sosai, hanun rigan are dark brown, yana sanye da dogon brown pant yasanya white sneaker na Fendi, wrist dinshi daure da agogo na rolex gashin kanshi a kwance yana kara bubbude manyan idanunshi yana magana kasa kasa yana counting yatsunshi sai wani hadadden kamshi dake tashi ajikinshi, murmushi Mami tayi tadan kalleshi ta maida hankalinta kan tukin datake yi tana tunani Aadil kenan, Ball fa suke bugawa a compound shida Aabid Baffa kuma na zaune acikin bukkan dake compound din yana kallonsu yana murmushi, yana ganin Mami tafito rike da car key gidan BigMum zata yafashe da kuka ya yarda kallon zai bita shine ta taho dashi.
Ahankali takira sunanshi. "Son" dan juyowa yayi ya kalleta da manya manyan idanunshi yadan daga cikakken gyararren giranshi sama kaman na tamace yana kallonta, itama dan kallonshi tayi ta maida hankalinta kan tuki tace "wat are you counting Son" turo mata baki yayi kafin ya maida kanshi kan hanya yana lankwasa kan yana cizan wet lips dinshi batare dayace mata komiba yafara counting motocin gabansu. Dawani irin mugun gudu Hamida tafado kan titin tana waigen baya saura kiris Mami ta bigeta ta gitta, dan batakai ga taka birki ba ta buga salati. "subhannallahi wanan lafiyanta kuwa" wani irin ganin gittawan ta yayi kaman flash of light, dasauri yakara ware ido yabi bayanta da kallo harta karasa tsallake titin da gudu tana waigen baya tana kuka tana share fuskarta da hijabi dan gani tayi kaman suna binta, da sauri cikin wani irin rudewa kirjinshi nawani irin bugawa kaman zai tsage yasaki lips dinshi daya rike da hakori tun dazu dayake wasa yana waigenta ta baya dan sunriga sun mata dan nisa, arude yay pointing saitin Hamida yana kyafkyfata ido kaman mai stammering yace "s...s...she Mami" wani irin juyawa yayi batare daya damu tafiya suke akan titi ba ya tuge sitbelt din jikinshi yawani irin bude kofan motan iska yaja kofan, kofan ya bude gaba daya ya daki wani mai machine dake tafiya, salati Mami tayi arude dan bama ta lura dazai bude motar ba saida taji wani irin iska, kafin kyaftawan ido yafita daga motan kanshi na rawa sosai yawani irin fadi akasa sosai dan da wuya in baiji ciwo ba, ihu Mami tayi tawani irin taka brake din motarta duka tana kallonshi kar wani abin hawa ko babban mota yatakeshi before you know it motar dake bayan Mami dat was on speed tazo da gudu ta bugi boot din motan Mami danta taka burki ne unexpectedly ta tsaya, motar Mami tai gaba kan Mami dayake ta lekone tana kallon Aadil arude kanta yawani irin bugu da starring, cikin ikon Allah mota bata bugeshi ba, da sauri batare daya lura da Mami bama yatashi yana waige waige kanshi na rawa sosai yana yarfe hannu danya bugu sosai akafa baima damu da mutanen dake salati ba ana kallonshi ana kallon mai machine dayay hatsari da two cars ya shiga gudu yana hango Hamida datamai nisa sosai yana yarfa hannu yafashe da kuka yace "she noo, don't go" yacigaba da gudu, gajiya yayi sosai kaman zai suma yafashe da kuka yana kallon titin dan baitaba gudu hakaba a rayuwan shiba, wani mai machine ne dayazo wucewa ya tsaya yana kallonshi cikeda mamaki yace "malam amma mutuwa ne kake kuka haka miyau na zuba" cikin kuka sosai yamai pointing Hamida dake shirin yin kwana tai nisa sosai yace "she" kallon inda yake nunamai yayi sanan ya kalleshi ganin yanda yake kaman mara lafiya sanan wanda yake nunamai itama gudu take yasa yakawo aranshi halama mai gudun shi take nema itama, tausayi yabashi hakan yasa yace "hauna kaikah wurinta to" tsayawa yayi yana kallon machine din yana kuka hannu mai machine din yamika mai da sauri yarike shi ya dafa shi sanan ya iya hawa kan machine din, mai machine din ya kunna yaja machine din, rikeshi yayi a tsorace yana kuka, adaidai bakin layin lokacin harta shiga layin mai machine din ya tsaya yace "sauko ka bita bazan shiga layin nanba, machine dinan daga wajen wanki na karbota yanzu haka, layin nan duk chabalbali" lekoshi yayi da kai yana kallon fuskanshi dan baicika gane manyan hausaba, ahankali mai machine din yace "come down" saukowa yayi yana kallonta yana kuka da karfi ya kwala mata kira. "sheeee" arude Hamida dake gudu har lokacin tana kuka sosai tafada wani uncompleted building ta tsugunna tana kuka sosai tana addu'a Allah yasa basu ganta ba, tabude jakanta arude ta shiga neman wayanta tanaso takira Ya Faruk amma bataga wayanba hala tafadi awurin, tafashe da wani sabon kuka tana kare fuskarta ta hijabi ta.

Da gudu yay cikin layin clean white sneaker dinshi na shiga cikin chabali, bai damuba burunshi yakai gidan data shiga yaganta, wani irin mugun faduwa yayi cikin ruwan chabalin white rigan shi da wandonshi suka baci sosai, tashi yayi ahankali yana kuka sosai yana kallon hanunshi da jikinshi danko kadan ya tsani datti yacigaba da gudu yakai gaban gidan, da gudu shima ya shiga haryana neman faduwa sabida block dake wajen ya buge kafanshi ya kwala mata kira yana kalle kalle. "shee" amugun tsorace Hamida ta dagokai ta mike tsaye da mugun sauri tana kuka tana komawa baya, tsabagen yanda tai gudu tana haki, ga heart dinta dake beating way to fast yasa har dishi dishi take gani, zaro idanun dabata gani sosai tayi ta kalleshi kaman yanda yake kuka sosai yake wani irin kallonta cikin wani irin low and calm voice yace "uhmm is me" yay maganan yana takowa gabanta kanshi na rawa yanadan dingishi danya buge kafanshi sosai, zaro ido Hamida tayi tana komawa da baya tana ganin dishi dishi tana ganin mutum na tahowa amma bata ganin fuskarshi da kyau tsabagen dishi dishin dayake gani, ahankali take komawa baya yana tafiya ahankali shima yana goge kukan dayake yi yakeyi yana tafiya ahankali yana kallonta yana biyota hartakai jikin bango ta tsaya, karasawa yayi shima har inda take yana breathing fast sosai yana wani irin kallonta numfashin duka na sauka akan fuskarta, wani irin kallonshi take da idanunta that went completely blind tsabagen yanda zuciyata ke bugu shima kallonta yake zuciyarshi nawani irin bugawan da tunda yake baitaba jin yamai irin bugun ba, wani irin nishi yayi yana kara matso ta har kafafunshi na gogan nata, dawata irin murya chan kasa yar karama chan ciki yasakin mata wani irin kuka dako su Aabid baitaba sakin musu irinshi ba yabude hannayenshi ahankali yafada jikinta yana kuka yay cuddling nata so tight not knowing what exactly yakeyi and yake feeling but he just wanna cuddle and cuddle and cuddle her, dip wuta ya daukemata tai wani irin passing out instantly kafafunta suka lankwashe zatai kasa, ahankali yadaga kanshi daga wuyanta yana kuka sosai yana kallonta dukya jika mata wuyan hijabi da hawaye da miyau, binta yay da kallo ta yanda arms dinshi ne are d only things dake rike da ita danda tuni tazube akasa asume, jijjigata yayi ahankali ya fashe da kuka kaman karamin yaro yace "wake up, are you sleeping?".
_🌹IN BANI 🌹_



_This novel is for sale, karki karanta in baki biyaba, in kika karanta ina binki bashi, pay anan or pay achan_


_in kinason novel dinan zaki turo 300 access fee to 3107021073 first bank aisha Muhammad, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461_

_you can also send MTN card 300 ta watsapp number na sainai adding a group din danake posting_



Maman Abd Shakur


17....

Goga fuskarshi yayi anata yana kuka sosai yace "wake up pls" yay maganan yana turo baki cikin kuka yana kallonta ganin shiru yasa ahankali ya kwantar da ita a kasan wajen, kwanciya yayi shima gefenta yana kallonta shi kanshi baisan meke damubshi ba, fashewa yasakeyi da kuka yarike hanunta dan wani iri heart dinshi kemai, he's feeling something all over his body, stomach dinshi kaman an watsa ice a ciki sabida wani irin sanyin dayake mai dayake kaiwa kowani nerve najikinshi, ahankali ya daura kanshi a wuyanta yana kuka sosai bana wasaba ahaka shima baccin wahala da ciwo sukai gaba dashi jikinshi yadau wani irin zafi sabida ciwukan dayaji a kafa gakuma zazzabi.


Ahankali Mami ke bude ido, dishi dishi take gani sosai maganar bigmum taji dakuma matse hanunta da akayi. "Maryam kin tashi" dan juyo dakai tayi da kyar ta kalli gefenta Big Mum tagani zaune akan kujera idanunta sunyi ja sosai ta rike hanunta gam, baki Mami tabude zatai magana takasa sabida yanda bakinta yamata wani irin nauyi sai kallon ko ina datake yi dakuma kanta daya mata wani irin nauyi da zafi, shiru tayi tana lumshe ido tana kokarin tunano abinda yafaru. "Maryam" Bigmum tasake kiranta hakan yasa tabude idanunta da kyau tanadan lumlumshe ido sabida yanda kanta ke mata ciwo zatai magana aka bude dakin aka shigo yayyinta Mazane su uku da Abie dakuma Aabid da taga idanunshi sunyi jajir, da sauri Aabid yama rigasu zuwa wajen Mamin, cupping fuskarta yayi kaman zaiyi kuka yace "Mami na ina..ina Aadil?" sunan Aadil daya kira yasa ta lumshe ido da sauri, ahankali komi yafara dawo mata har lokacin daya bude kofar motan yafadi akasan tsakiyan titi, dawani irin sauri tabude ido tai wani irin ihu tana mika hannu kaman zata kamoshi. "Aadilll" arude ta shiga kalle kallen dakin ganin dakin asibiti take babu Aadil a wurin saima ruwa da ake samata fashewa da wani irin kuka tayi numfashin ta na sama sama arude tarike Aabid tace "where's Aadil Aabid? Tell me what happen to Aadil?" da sauri tasaki Aabid tana kallon sauran yan dakin tana nunasa da yatsa tana magana kaman wacce ta zare. "kufadamin gaskiya ina yarona yake? Ina d'ana? Abie where is Aadil eh" da sauri Abie yakaraso wajen Big Mum ma tariketa ahankali yace "calm down wife, calm down, muma bamusan meya sami Aadil ba, wani bawan Allah dai yakira ta wayarki Big Mum ma aka kira dan anga itace last contact din dakikai waya da ita a phone dinki ance you had an accident u were unconcious" "noooo" ta fizge kanta daga jikin big mum tace "karya kuke yimin kufadamin gaskiya mota ya takeshi ko? Aadil dina yamutu?" kaman wacce tasami tabin brain ta kalli yatsunta kaman yanda Aadil keyi tafara kirgawa cikin sambatu tace "Aadil was counting his fingers playing while I was driving, all of a sudden ya cire sitbelt yabude kofan mota yafice, yabuge yafadi sosai a kasa, matching brake nayi arude na kalleshi daganan bansan meya faruba, tell me!" tai wani irin ihu tana kama rigan Abie dake kanta tace "Abie meya sami d'ana wlh inkamin karya zanyi fushi da dukanku kafadamin" alamu yama Aabid dake zaune yana kallon Mami yamatsa, zama yayi ya bata one side hug yadan jijjigata yace "in sha Allah nothing will happen to Aadil, zamu nemeshi zamu bada cigiyarshi, and we will get d police involve inma d accident was a well careful plan accident dan ayi kidnapping nashi we will know, calm down okay karwani ciwon yakama ki, I swear, I swear to you zan nemo mana danmu" cikin wani irin kuka mara kara tace "promise me Abie u will find my Aadil for me" shima idanunshi sunyi jajir jijiyoyin kanshi duksun fito yace "I promise you Mum Aadil" tashi yayi da sauri yay hanyar kofa su Suleman zasu bishi yay murmushi irin na tashin hankali yace "karku damu am coming, in baku ganni dawuri ba get d police involve" da sauri Suleman yace "ina zaka Abdullahi?" Juyawa kawai yayi yana kokarin hana kanshi hawayen dazasu zobomai yace "ina zuwa kawai Yaya" ficewa yayi da sauri Mami ta fashe da kuka tai hugging Aabid tace "Son where is your brother? Idan ban ganshi ba mutuwa zanyi wlh, you and Aadil are my entire life, please So.." tafashe da kuka sosai, ahankali yadago kanta daga jikinshi yasa hannu ya share mata hawayen, da muryanshi data dishe sosai yace "stop crying Mami, I will find my Bro okay" gyadamai kai tayi tana kuka, Big Mum ta kwantar da ita tace "kwanta ki huta ruwan ya shiga jikin ki da kyau" tashi Aabid yayi yafita shida Yayin mamanshi.



Sosai Abie ke zuba wani irin uban gudu akan hanya, bini bini yake share yan hawayen dake zubomai, sosai yay tafiya kaman zaibar garin kano sanan ya yanki cikin wata yar karamin kauye yadinga kutsawa cikin kauyen nan da jeep dinshi haryakai wani babban farm house, a kofar gidan yay parking yafito rike dawata yar jaka yarufe motar, yaciro wasu key yabude gate din ya shiga, gidan ciyayi sunma soma girma kota ina, ya karasa har gaban wani flat dake compound din ya shiga yar barandan dazai sadashi da daki rike da makullin da wayarshi, ciro key yayi yabude kofan ya shiga ciki, babban falone dayay dan kura da alamu an dade ba'a shiga gidan ba, wani dan corridor yayi hanunshi har rawa yake yabude wani katoton makulli dake makale jikin kofan ya bude sanan ya zare ya ijiye key yabude kofan amugun hankali ya shiga dakin, dakine da komi nacikinshi ja, kaman dajan kyalle aka zagaye bangon dakin, kasanma wani irin jan carpet ne ja sosai a shimfide kota ina, ahankali ya shiga dakin da yay dan kura ya maida kofar ya rufe yasaka sakatan sama data kasa sanan ya shigo ciki ya ijiye jakan daya dauko akasa duk da sauri sauri yake komi ya zage jakan ya bude wasu jajayen kayane suka bayyana da sauri ya kwabe manyan kayan jikinshi ya ijiye kasa sanan yadau jajayen kayan yasaka babban bubun rigane dake jamai har kasa da sauri ya tsugunna ya kwashi kayan daya cire ya maida cikin jakan yaciro ashana daga jakan ya daga jakan ya jinginata da bango yatashi yaje gaban dakin inda wani manyan gumaka suke da aka musu zane a fuska kaman da chalk, kafafunsu daure dawasu irin bangles sai kuma jajayen candles guda shidda suma, kneeling yayi ahankali agaban gumakan sanan ya kyasta ashana ya kunna duka candles din sanan ya hura tsinken ashanar ta mutu ya yar a gefe, shiru yayi yana tunani yana kallon gumakan kafin ahankali ya dukar da kanshi yahade hannayenshi biyu agaban gumakan yace "Ozo the tittle holder, Ozo the tittle holder, Ozo the tittle holder, macukubelebele kaino kaino, macukubelebele kaino kanooo" shiru yadanyi zuciyarshi namai wani irin azababben zafi, ahankali cikin wani irin dishashiyar murya yace "Ozo ka bayyana agareni inada bukatar ka, I summon you Ozooo" bai karasa kiran sunan ba wasu mutane guda uku suka bayyana a dakin a tsaye da ba'a ganin fuskokin su suna sanye da jajayen dogayen riguna daya rufe har kafarsu sai babban su dake sanye cikin black doguwan riga shima kanshi akasa yana rike dawani karfe dakeda Kwai kaman kwan jimina asaman karfen, cikin wani irin magana mai echo sukace. "mesa kake neman Ozo" kaman jira yake ya rarrafa da gudu yaje gaban me bakaken kayan yay kneeling yana hada hannayenshi yace "great one Ozo, Ozo nakiyaye kowace irin dokan ka, wanan zoben" yanuna babban zoben yatsarshi arude yace "kaman yanda kace bantaba cireta daga yatsata ba, Ozo nasan ni mai laifine tun kafin na shigo kungiya aka fadamin sharuddan kungiya wacce shine d'a namiji dazan fara haihuwa a duniya nakune shine sacrifice dazan...." yay shiru hawaye na zuba daga idanunshi sosai da kyar cikin wani irin asalin tashin hankali yace "great Ozo bantaba sanin haka abin yakeda mugun wuya and tough ba saida na haifo yan biyuna mazaje kyawawa" yadanyi shiru yana goge hawaye sanan yace "great one Ozo da gudu nabarosu a asibiti nadawo gida na shiga boyayyen daki namaka kira ka amsani, ka bayyanan min, naroki afuwa da alfarma akan karku daukemini Hassan wanda yake na farkon, karku kashemin shi, great one Ozo nasan kamin adalcin da baka taba yima wani a kungiyan nan ba, kabani zabi biyu masu sharudda sabida yanda ka tausayamin kakuma Soni, zabin shine ko kukashe shi kusha jini, koku shanye min shi, da ranshi amma shida yaro basuda bambamci, da gudu na yarda tsabagen yanda nakeson Yan biyuna, gakuma wani irin special son Hassan din da Allah ya dauramin danshi nafara dauka a hannuna a tsumma kafin na dauki dan uwanshi Hussain, na yarda da Hassan mutu gwara kunsaka ranshi a kwalban kunyi duk yanda kukaga dama dashi daku kashemin shi na yarda dari bisa dari ku maidashi yaron kusa ranshi a kwalban bakomi, sai kuka fara koromin sharuddan zabin danayi na karya mutu, kace duk wani ciki da Maryama zatayi tun cikin na wata biyar zaku shanye cikin, haka na yarda cikin da Maryam ke dauka dai, dai, dai, har sau uku Maryama nayi duk kuna shanye wa tana bari duk sabida karku kashemin abin kaunata Hassan ban damuba har mahaifanta ya sami matsala tsabagen wankin ciki da ake mata tadena samin cikin, bayan haka kuka bani sharadin cewa ko bayan shanyayyen dan nawa yay girma bazai sake yay aureba shima na yarda to tayaya ma mara lafiya yaro mai kwakwalwan yara zaiga mace yace yanaso duk na yarda, kun hanani cin naman rago duk banaci, kun hanani cin dabino shan zuma duka banyiba dukdan karku kashemini Hassan, mesa yanzu zaku chanza komi ki daukemin farin cikina eh bayan na kiyaye kowace doka da sharuddan ku eh Ozo the great one?".
_🌹IN BANI🌹_



Maman Abd Shakur


18....

_This novel is for sale, karki karanta in baki biyaba, in kika karanta ina binki bashi, pay anan or pay achan_

_in kinason novel dinan zaki turo 300 access fee to 3107021073 first bank aisha Muhammad, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461_

_you can also send MTN card 300 ta watsapp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting_

_masu fitarmin da novel waje, please kindly stop_




Sosai Abie yafashe dawani irin kuka ya kife kanshi akasa yana kuka sosai yana hawaye, shi karan kanshi baisan wani irin so yakema Aadil ba, Allah yaga abinda yagani ne ya jarabce shi da mugun son yaron, Aadil nada wani irin shiga rai fiye da tunanin kowa saika zauna dashi zaka gane hakan, son Aadil yake bana wasaba, idan har Ozo ne ya daukeshi hala mutuwa zaiyi dan baijin zai iya rayuwa babu yaronba. "Tursoso!" yaji an kiranshi dan bayan ya jona kungiya sunan da Ozo the great one yasamai kenan, da sauri ya dago kanshi yana goge hawayen daya gama wanke mai fuska idanunshi sunyi ja sosai, cikin wani irin murya dake echo adakin mai bakaken yace "bayan kasan ka kiyaye sharudda, me a tunanin ka zaisa mu daukema d'a? Bama dauka saidai mu tsotsa agabanka, bama dauka saidai mu tsotsa kaman yanda muka tsotse cikin matarka agabanka haka zamu tsotsemai jini agaban ka ya mutu babu jini ko digo a jikinshi" yaydan shiru sai chan cikin wani irin murya mai firgita zuciya yace "babu hanun mu abatan danka saidai zamu gargadeka akan abu daya" yasakeyi yin shiru yace "ba danka ba aure Tursoso, ba danka ba aure Tursoso, ba danka ba aure Tursoso" gyadamai kai yayi hankalinshi yawani irin kwanta kaman an yayemai wata irin bakin tsoka daga kirjinshi yay murmushi yace "nagode, nagode Ozo the great one" wani irin nishi Ozo yayi irin na matsafa yace "shikenan matsalan ka ko akwai wata?" murmushi yayi cikin jin dadi yanda Ozo keji dashi yace "dama Ozo naga jiya yakamata zobena yamin aman kudi, jiya lahadi amma baiyiba, shine nace maisa baimin ba? Ko wata laifin nayi?" dariya Ozo yayi irin dariyan matsafan nan. "ha ha ha hmmm, Tursoso anchanza ranan aman kudin ne, gobe ne zaimaka aman kudin" da sauri yay murmushi yace "to Ozo nagode" batcewa sukayi bat da sauri ya hure

Please Login or Register in order to submit comment