Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah kamin magana kaji" shiru yayi yana kallonta batare dayace komiba hakan yasa Abie ya karbe shi daga hanunta, ahankali ya kalli Abie hawaye na gangarowa daga idanunshi yay wani irin shiru kaman bashiba, murya chan Abie yace "menene Aadil mekema ciwo? Mutafi asibiti? Me kakeso" shiru yayi yana kallon Abie hawaye yasake gangarowa daga gefen idanunshi yakasa magana, dan ajiyan zuciya Suleman ya sauke yace "kodai natado Baba ne?" da sauri Abie yace "a'a kasan Baba nada hawan jini in gari yawaye yasani, mubarshi yay bacci yana bukatar bacci" kallon Aadil yayi ahankali ya sharemai hawaye yace "ga Hamida nan zuwa kaji, be fine kaga Mamin ka dukta damu" gyadamai kai yayi yafashe da kuka ahankali mara kara dake fita da kyar, zuciyarshi namai wani irin zafi sosai jiyake kaman zai mutu, kirjin Abie wani irin bugawa yake sabida abinda ke shirin faruwa, da kyar ya tattaro duka kuzarinshi ya kalli Sulemanu yace "mutafi dashi asibitin" tashi sukayi ahankali suka dago Aadil din dake kuka sosai mara kara Mami na sharemai hawayen sukai hanyar fita daga dakin, Suleman ne ya kalli Aabid dayay wani irin zama akasa kanshi akasa kaman wanda akama mutuwa hakan yasa yace "lafiyan ka Aabid kokaima ba lafiyar ne" ahankali ya dago kai ya kalli Mami da sauri Mami cikin fushi ta wuce tafita daga dakin Abie yace "muje Suleman" sukawuce suka fita daga dakin suka saka Aadil din a mota Suleman yaja motar sai asibiti, wani irin tari Aadik din yafarayi yana kuka agalabaice yana dukan kirjinshi dakemai zafi sosai, bottle water Mami ta bude ta mikamai da sauri tace "ungo kasha" ture ruwan yayi da hannu yana tari sosai jinin da Mami tagani jikin goran ruwan datake mikamai ta sanadin tarin dayayi mai karfi yafito yasa tasaki salati tasaki ruwan akasa. "innalillahi wa innailaihi raji'un, Abie Aadil, Ab..." baya Aadil yay luuu kaman ya sume jini duk a lips dinshi da gefen bakinshi, da sauri Mami ta kamoshi ta rungume shi sosai tama rasa mezakayi, chan kasan makoshi idanunshi a kulle yana wani irin nishi yace "Mami Hamida my wife, call her for me" yafara wani tarin jini na fitowa sosai, fashewa da kuka Mami tayi tace "Abie, Abie d'ana, Yaya Suleman ka kara gudu, Abie Aad...." denajin numfashin shi da tayi a wuyanta yasa gabanta yay wani irin mummunar fadi tawani irin sakeshi yay baya luuu daidai lokacin suka iso asibitin.....


Aabid yakai kusan minti arba'in a zaune kanshi yadau wani irin zafin daya dade baimai ba, da kyar ya iya tashi ya ja kafa yay hanyar dakinsu, ahankali ya bude kofar dakin yay shiru yana kallon dakin ya sauke idanunshi akan belt dinshi da Mami ta jefomai dazu akwance akasa wanda ya daki Aadil dashi, shiru yayi yana kallon ko ina yanda ya bugi Aadil na dawo mishi sabo a ido yana kallon fuskar Aadil yana kuka yana sosa inda ya dakai yana cemai. "stop beating me Bid" shigowa dakin yay ahankali yana jan kafa, idanunshi ya sauka akan aman da yasan Aadil dinne yayi sosai zuciyarshi tamai daci, miyan bakinshi ma yamai daci yakasa hadiyewa, fita yayi yakoma yadauko mop da bucket ya gyara kasan dakin tass ko ina ya dauki kamshi sanan ya shiga bathroom yayo wanka yafito sanye da bathrobe yarasa meyake mai dadi, zama yayi abakin gadon su ya kurama hotonshi dayay tareda Aadil din ranan salla ido yana kallon Aadil din, yay mugun nadaman dukanshi dayayi bana wasaba, har tsoron kulle ido yake dan ganin fuskar Aadil yake yana kuka yana cemai "stop beating me Bid" wani irin fadawa gado yayi ya daura hanunshi akan heart dinshi dake beating fast, kafin yatashi da kyar yabude wardrobe dinsu ya zaro white jallabiya yasaka, ya shimfida dadduma yay sallolin da ake binshi sanan yadau car key yafita yabisu asibitin.







**
Da asuban fari ta tashi daga baccin daya dauketa kan daddumar, jinginar da bayanta tai jikin gado tana karanto addu'an tashi daga bacci, ko kadan batajin dadi jikinta saima wani irin kanta dataji yana mata ciwo, bude kofar dakin da akayi yasa ta dago kai ahankali, Anty Lami ne ta shigo sanye da dogon hijabi tace "au harkin tashi" gyadamata kai tayi tana sosa ido hakan yasa yace "to tashi kije ki dauro alwala" gyadamata kai tayi ahankali ta mike tsaye Anty Lami tabita da kallo harta shiga bayi, yarinya kyau har kyau ga diri amma haryau bata da saurayi ko daya, shiru tayi tadan tabe baki dam bataso tasaka lamarin Hamida arranta da sassafen nan dan zata tashi da ciwon kaine abanza ta maida kofar ta rufe tai dakin yaranta maza danta tasosu subi Abban su masallaci.

Baki kawai ta wanke tafito daga bayin ahankali danji tayi cikinta namata ciwo sosai, drawer Anty Lami taja nanko taci karo da pad, guda daya ta dauka takoma bayi wanka tayo ta shirya tsaf sanan ta dauro alwala tafito daga bayin, adaddafe ta shafa mai tasa riga tahau gado ta kwanta dan sosai taji zazzabi na neman kadata, wajejen 7 Anty Lami takara shigowa dakin ganinta dukunkune kan gado yasa ta maida kofar ta rufe takaraso ciki da sauri dantasan Hamida bata komawa baccin asuba saitai karatun Al Qur'ani, ahankali ta yaye bargo data rufa dashi hakan yasa Hamida tabude jajayen idanunta ta kalli Anty Lami dake wani irin kallonta, ahankali tace "ina kwana Anty" dasauri Anty Lami takai hanunta kan wuyanta ganin yanda take maganan arude ta janye hanunta daga kan wuyanta tace "bakida lafiya Hamida, meke miki ciwo?" dan yamutse fuska tayi tace "cikina ke ciwo" da sauri Anty tace "kin fara kenan kinga pad a drawer na?" gyada mata kai tayi tana goge hawayen dasuka zubomata na wahala, maida bargon tayi ta lullubeta tace "sannu kinji bari nakarasa breakfast nakawo miki kici kisha magani anjima idan ya lafa saimu je gida" gyada mata kai tayi hakan yasa Anty lami ta shafa fuskarta tawuce tafita daga dakin. Fashewa tayi da kuka sosai tarasa meke damunta deep down jitaje kawai so take taga Aadil, she miss his innocence dakomi ma nashi, ko hanunta ta daga saita dingajin kamshin shi, hakanan ma saita dingajin kamshin shi kaman yana wurin, gashi batada waya balle yadan rage mata kewa kokuma wani abun, kasa dena kukan tayi har Anty Lami tadawo dakin da sauri ta share hawayen fuskarta gudun karta gani tafara mata masifa, karasowa ciki tayi rike da tray tana kallon fuskarta tace "kuka kike ko? Kodai muje asibiti ne" girgiza mata kai tayi ahankali, ajiyen abincin tayi akan rug tayaye bargon jikinta ta miko hannu ta dagata ta sauko da ita tace "ga kunun nan kisha da chips kisha magani saiki kwanta wuraren shadaya zamu je gidan, yanzun nan ma muka gama waya da maman ki" kallonta tayi ahankali tace "Mama" "eh maman ki tace nagaishe ki" murmushi tayi tadau kopin kunun takai baki hakan yasa Anty Lami tai murmushi tawuce tafita ta shiga kitchen ta kwaso lunch box din yaranta ta mimmika musu tace "kuje ku gaishe da Antyn ku saiku tafi driver na jiranku" da sauri sukai dakin Hamidan fadawa jikinta sukayi ta washe baki sosai dan tanason yara ta shafa kansu tace "byee ayi karatu da kyau" da gudu suka fita ta cigaba da shan kokon taci chips din kadan sanan ta tatatara ta kwashe tafita daga dakin ta shiga kitchen ta wanke duka kwanukan data gani a wurin ta share kitchen din tsaf konina na kyalli. kwala mata kira akayi. "Hamida jeki shirya Abban ku zai tafi aiki yanzu" ahankali tace "to" ta dauraye hanunta a sink tawuce tafita daga dakin ta shiga dakin Anty Lami kayan data gani anty Lami ta ijiye mata akan gado ta shirya acikin su bakin gown ne mai kyau tadau hijabin tasaka daidai nan Anty Lami tashigo dakin tace "iyye mai kama da mamanta kinyi kyau, mutafi to" murmushi tayi ta sunnar dakai tana wasa da yatsunta ta, tabi bayan Anty Lami suka fita tsakar gida motan Abban ta shiga bayan sun gaisa yatada motar suka shiga hanya dashi da Anty Lami sai hira suke gwanin ban sha'awa har jan bulo, ganin kofar gidansu yasa gabanta yawani irin fadi, akofar gidansu Abba yay parking suka fiffito daga motar, Anty Lami takama hanunta ganin takasa shiga jikinta sai wani rawa yake suka shiga cikin gidan, Abban su Ra'is biye dasu, agaban falon su Anty Lami ta kwada sallama ta shiga Abba da Mama dake zaune kan kujera ne suka amsa su Zainab da Ihsan kuma nakan dining suna gyaran wake a tray, Tashi Mama tayi tai murmushi jin muryan Anty Lami tace "shigo Yaya" shigowa Anty Lami tayi Hamida biye da ita abaya kanta akasa, ta kalli Abba dayawani irin kafe Hamidan da manyan idanu tace "ina kwana Abban su Ayush" dan murmushi yayi yace "barka da zuwa ga wuri" kokarin zama tayi tana mikama Mama jakarta tace "tareda Abban su Ra'is muke yana tsakar gida" da sauri Abba yamike tsaye yace "la shine kika barshi waje" yafita dan shigo dashi, wani irin kallonta Mama tayi yanda kanta ke kasa takasa dago kai sai wasa take da yatsunta yasa Mama buga uban tagumi, da gudu Ihsan ta sauko daga dining tazo tafada jikinta tace "oyoyo Anty Hamida naaa" Zainab kuma ta balla mata harara tacigaba da gyaran wakenta dan lamarin Hamida yanzu haushi yake bata, Sallaman su Abba yasa Ihsan tasaketa tai dining Anty Lami ta nuna mata gefen ta hakan yasa taje ahankali ta zauna akasa kusada kafarta, Abba kuma ya shigo tareda Abban Ra'is Mama kuma tadawo gefen yar uwan ta ta zauna, su Ihsan suka taso suka gaishesu ya amsa cikin fara'a Zainab tawuce kitchen tafito da tray da drinks ke ciki da snacks takawo ta ijiye sanan tadau tray din tawuce itada Ihsan suka wuce dakinsu.

Ruwa kawai Abban su Ra'is ya dauka yasha sanan ya ijiye ya fuskanci Abba da kyau zaiyi magana saikuma yajuyo ya kalli Hamida dake zaune akasa kusada matarshi kanta akasa gabanta sai wani irin faduwa yake yace "tashi kiwuce ciki Hamida, tafi dakinku" ahankali ta gyada kai tana goge kwalla tawuce ciki Abba yabita dawani irin kallo harta shige corridor, sake kallon Abba yayi sanan ya kalli Mama dake dan murmushi cikin tattausan murya yace "haba, haba, haba dan Allah, a gaskiya raina yay matukar baci saisa nazo har gida namuku fada sanan nadawo da Hamida, ko kadan bakuma yarku adalci ba wlh, kuma nan gaba karku kara yankema yara mata irin hukuncin nan dan irinshi ne ke jafa yaro ga halaka, karuwai da sauran su dakuke gani duddaga haka aka fara daga koransu daga gida ne, to ina amfanin wanan? kome yaro yayi afara bashi damar bayani tukunna kafin a yanke hukunci, sanan adena yankema yaro hukunci cikin fushi, hanunka ai baya rubewa ka yanke ka yar, kai yanzu idan ka kalli Hamida fisabillahi bata baka tausayi?" yay maganan yana karkada kafa yana kallon Abba dake kallonshi asanyaye sanan ya cigaba."yarinyar nan ta shiga duk bala'in data shigane daga taimako, taimako fa jama'a, taimakon da annabin mu shiyace muyita, jiya har gida iyayen yaron nan sukazo suka mana godiya wlh idan kaji labarin yaron ma saika zubda mai da hawaye abin tausayi......" nan yafara bama Abba labarin da Hamida ta bayar na yanda ta taimakai dana Mami data bayar na Aadil din, dakuma labarin rashin lafiyan shi, sanan yace "yanxu abinda kukayi kun mata adalci?" dan ajiyan zuciya Abba ya sauke yace "nima nasan bamu kyauta ba kuma tun jiyan hankalina yaki kwanciya, naba Kaka hakuri, nabata hakuri harna gaji da bata hakurin amma taki fahimta ta tsaya akan bakanta, abinda yakara batamin rai shine yanda bata attending lectures ko kadan inda tasan bazatai makarantan ba dabatasa nai asaran kudina ba jiya result dinsu na first semester yafito Zainab ta dauko hoton takawomin wlh carry over bakwai gareta acikin courses tara dasukeyi last semester ina amfanin haka fisabillahi? Hamida bayar gidan nan bane? Hamida yarinya ce? Ba nannan ta taso taga yan uwa ta ba? Narasa yanda zanyi da ita, isilamiyan ma inda ba har gida na dauko musu malamin ba shima na tabbatar maka da bazata jeba, yaya zan mata? Saisa na yanke shawara da zaran miji yafito wlh aure kawai zan mata hala ta chanza muma ma huta dan lamarinta sai godiya...." sallaman da Kaka ta rafka yasa duk sukai shiru sai Anty Lami data amsa Kaka ta shigo tana kallonsu daidai, Anty Lami ce tadan zamo daga kujera tana murmushi tace "ina kwana Kaka" wani irin mugun kallo Kaka tamata kafin ta kalli Abba dayay shiru yana kallonta asanyaye tace "Sama'ila me wayan nan sukazo yi gidan nan da sassafen nan? Ince ba yarinyar nan suka kawoba" ahankali Abba yace "itace Umma tanama ciki amma duk ba abinda muke tunani bane, ashe taimakon yaron tayi, yaron kuma baima da lafiyan kwakwalwa, kinsan komu munga haka mun zaci pretending yake ashe da gaske ne baida lafiyan kai ne, jiyama saida iyayen yaron sukazo suka yima su Alhaji Ibrahim godiya, yanzu komi yawuce Umma" wani matsiyacin kallo Kaka tamai tace "idan kai yaro ne sunzo sun wanke ma kwakwalwa bayan Hamida taje ta shirga musu karya ka yarda niba yarinya bace, sanan abinda babba ya hango yaro ko yahau bishiyar kwakwa bazai hango ba, na kori Hamida daga gidan nan kuma ta koru ne, billahillazi la'ilaha illahuwa duk wanda yace zai nunamin ban isaba sainaje naci abincin gidan kajinka na mutun maka a wuya Sama'ila kana jina" tai maganan tana gyara kullin zaninta ta kwalama Hamida kira daga nan inda take tsaye. "Hamida! Hamida, dan uwaki kifito daga dakin nan kafin nazo dan wlh idan kika bari na shigo dakin nan sainai miki ruwan zabori aka, kifito nace" tagumi Mama tayi kawai tana kallon Kakan cikeda mugun takaici, Anty Lami ne ta tashi tace "Haba Kaka ki mata afuwa ki yafe mata mana idan kika korata daga gidan uban ta to ina kikeso taje? Tanada wani ubanne?" nunata Kaka tai da yatsa tace "kinga Lami lamiso kinga ina ganin mutuncun kiko karki kara kiran Hamida diyar Sama'ila, nariga nacireta daga yaranshi karki kara, Hamida!" ta kwalama Hamida kira da mugun karfi daidai lokacin wasu yara suka shigo guda biyu. "salama alaykum wai ana neman megidan awaje, ance ana sallama damai gidan" tashi Abba yayi ya kalli baban Ra'is yace "ina zuwa dan Allah" yawuce yafita, hakan yasa Abban Ra'is yace "Kaka kima Allah ki yakuri ki zauna ki saurareni haba Kaka ta" shiru tayi ganin yadan cika mata ido ta zauna akan kujera ta daure fuska tace "ina jinka yimaganan tun ina ganinka da gashi" sake kwantar dakai yayi yace "yauwa Kakana, wlh yarinyar nan ba iskanci tayiba taimakon mutumin nan tayi na rantse miki bari nabaki labarin yaron kiji...." nan yafara koro mata labarin har karshe zai cigaba da magana Abba yay sallama ya shigo ya kallesu dukansu yace "tareda baki nake ku gyara, iyayen yaron nanne sukazo" tashi Baban Ra'is yayi yace "masha Allah gasunan Kaka kyaji gaskiyan zancen daga bakinsu ai" fita Abba yayi tareda Baban Ra'is ko minti biyu basu dauka ba suka shigo da manya manyan baki sunci manyan kaya, Baffa, Suleman da Abie da idanunshi yay mugun jajir yau yana cikin tashin hankalin da rabonshi daya shiga irinshi tun ranan da aka haifi Aadil, gefe daya Aadil ne rai ahannun Allah yana sambatu yana kiran Hamida yana asibiti ansaka mai oxygen, gefe daya kuma Ozo ne dayace mai karya sake yabari Aadil yay aure, kanshi yadau zafi bana wasaba binsu Baffa kawai yake amma hankalin shi baya jikinshi baimasan me akeyiba, sai Mami da itama idanunta har kumbura sunyi tsabagen kuka saikuma big Mum dake biye da Mami, dawani babban Abokin Baffa wanda yake limamin jumma'a na masallacin dan ja, malam Kabir duk suka shigo dakin aka zazzauna, Mami daurewa kawai take tama kasa zama akan kujeran da kyau Kaka dai saibin manyan mutanen take da kallo danji tayi falon yadau wani irin sabon kamshi, Anty Lami ne ta tashi taje kitchen da kanta ta kwaso lemukan kwali tafito dasu a ijiye a tsakar falon sanan tadawo gefen Mama ta zauna tana kallon yanda su Abba ke gaisawa da mazan ana gaishe gaishe.


Gyaran murya Baffa yayi zai fara magana, Mami takasa daurewa ahankali ta zamo daga kan kujera ta saukar da gwuiwanta kasa ta hade hannayenta biyu alamun roko tana kallon matar da kamanin ta da Hamida yasa tagane itace mahaifiyar Hamidan tace "dan Allah, dan Allah ba danniba, ku dauki Aadil a matsayin danku kunsan duk abinda zaisa yaron nan farin ciki ya taimaki rayuwan shi, kome yakeso zaku iyayimai koma menene abin dan samun lafiyan shi" da sauri ta share hawayen daya zubo mata, zatai magana saikuma wani irin kuka yazo mata tafashe da kuka sosai tsabagen yanda zuciyarta kemata wani irin rawa, da sauri Mama da Anty Lami sukace "subhanallahi, hajiya dan Allah kidena kuka" cikin wani irin kuka Mami ta girgiza musu kai ta kalli Abban Ra'is da Abba ta kalli Kaka data kafeta da ido sanan tasake kallon Mama har lokacin hannayenta ahade tace "dan girman Allah badanni ba bakuma dan halina ba, alfarma nake nema dudda nasan mai girma ne, mai kuma wuya babu wanda zai dauki yarshi yabama mai kwakwalwan yara, amma dudda haka da Allah nake hadaku Maman Hamida da baban Hamida, ku dubi girman Allah, ku taimakama d'ana kubama d'ana Aadil auren Hamida karya rasa ranshi dan darajan All...Allah" tafashe da kuka sosai kowa na dakin saida kukanta yataba ranshi har Kaka, da sauri Mama ta dagata tama kasa magana Baffa yace "ku shiga ciki mu maza zamuyi maganan mu anan" tashi Big Mum tayi da Anty Lami da Mama suka wuce da Mami dake wani irin kuka sosai ciki tana sambatu bama tasan metake cewaba.
_🌹 IN BANI 🌹_



Maman Abd Shakur


33...


_This novel is for sale, karki karanta in baki biyaba, in kika karanta ina binki bashi pay anan or pay achan_


_in kinason novel dinan, zaki turo 300 access fee to 3107021073 first bank aisha Muhammad saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461_


_you can also send MTN card 300 for those da basu da account ta watsapp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting_




Tsaki tayi tana kokarin warware daurin zaninta tace "wa kuwa, Hamida mana" wani irin taka birkin dayayi saida ta tsorata tasaki namijin goron hanunta tadafa kirji tana kallon ko ina tana zare ido tace "innahu min sulaymana, wa innahu Bismillah rahmani rahim, kai meya faru haka? Kasheni zakayi?" da kyar ya iya gangarawa gefen hanya yay parking yajuyo ya kalleta yace "wace Hamidan?" hararanshi tayi har lokacin kirjinta nawani irin masifaffen bugawa batadawo daidai ba tace "dan ubanka kana neman kasheni a hanya sanan kuma kana tambayata wace Hamida, tunda munada wata Hamida ne bayan wanda kasani ai shikenan nidai tada mutafi ka kaini gida akwai shirye shirye agabana" Kasa koda kunna motar yayi yajuyo yana kallon Kakan, hararanshi tayi tace "nidai yanda nake cikin farin cikin nan bazan bari bakin cikin ka yabata mini raiba, kaga tafiyata ka jika motarka da ruwan bunu ka tsoma tayoyin motar aciki kasha ka cinye shege mai kama da ifiritu tsabagen bakar mugunta" tabude motan tafita tana surutu ta tare keke napep ta shige tana ballama motar Faruk harara kaman idanunta zasu zazzago kasa.



Akofar gidansu aka sauketa tafito tana soka hannu a lalita tace "nawane kudin ka Malam?" "dari biyu ne Hajiya" hararanshi tayi tazaro dari dakuma naira hamsin tace "dari da hamsin zan baka yaro tsadarka tai waya nagadai ba wuyan fetur akeyiba" ta mikomai kudin karba yayi ganin tsohuwa ce yace "to shikenan Allah sa musu albarka" Ameen tace tajuya tabude gate ta shiga cikin gidan, Mama tagani a tsakar gidan da Baba dabasu dade da dawowa daga rakiyan Anty Lami da mijinta ba, dauke kai tayi tai kaman bata gansu ba tai hanyar sasanta, da sauri Abba yabita yace "daga ina kike Umma?" "inda ka aikeni" tafada atakaice tana kokarin bude kofar sasanta, zai biyota ta juyo fuska adaure tace "karka sake ka shigomin sasa ka wuce kacema Haleema a shirya gobe zanyi baki, manya manyan baki kuwa, sanan kabata kudi tai cefane, sanan katuromin Hamida yanzun nan ina jiranta" tana maganan ta rufo kofarta ta wuce ciki abinta, shiru Abba yayi yanabin kofar da kallo kafin ahankali ya saukar da ijiyan zuciya ya juya ya shiga dakinsu dan Mama tabar tsakar gidan, labulen falon ya yaye yaga Mama na kokarin shiga corridor yace "kirama Kaka Hamida zan tafi gidan kaji ni" ahankali takaraso inda yake tsaye tana kallonshi ganin damuwa karara sosai akan fuskarshi, hanunshi takama ahankali takai kan bakinta ta sumbaci hanun kadan tace "karka damu Umma zata sauko okay" gyadamata kai yayi yakai hanun nata kirjinshi ya rungume yana kallonta nayan sakanni kaman yanda itama take kallonshi asanyaye cikeda tausayin shi, saida yadanji dama dama sanan yasaki hanunta ahankali yace "thank you best wife, natafi" murmushi tayi tace "Allah kaika lafiya yakawo kasuwa best husband" kiss yama forehead dinta sanan yawuce yatafi itakuma takoma ciki, dakinsu tabude ahankali suka hada ido da Hamidan da har lokacin bata cire hijabi ba tana zaune kan gado kirjinta bai dena dukan uku uku ba, sai harba ido take kaman wacce tai kisan kai, Ihsan na gefen ta tana homework sai Zainab data gama gyara waken ta turesu gefe ta bude wani littafi tana dubawa, duk dagokai sukayi suna kallon Maman banda ita data saukar da kanta da sauri kasa tana wasa da yatsunta ahankali, da sauri Ihsan ta ajiye byron ta sauko daga kan gadon tace "Mama biscuit din dakikace zaki bani" hanun Ihsan tarike tace "muje yana dakina" sanan ta kalli Hamidan dataki dago kai tace "inkinga dama kije Kaka na kiranki" tana fadin haka tai gaba abinta, Zainab ta gimtse dariyan dake cinta saida taga Mama ta wuce sanan tasaki dariyan da sauri Hamidan ta kalleta da idanunta dasuka cicciko da kwalla, hararanta Zainab tayi tace "Allah ya tsagamin baki sainaki dariya ni" sauka tai daga gadon da sauri Zainab ta tashi itama daga kasa tana kallonta tace "wai ba cewa Mama tayi Kaka na kiranki ba eh hajjaju" harara ta watsama zainab din da manya idanunta tawuce tafita daga dakin ahankali tai sasan Kaka.


Ahankali ta shiga falon da sallama tana kallon ko'ina komi nadawo mata kaman wata matsoraciya, daidai Kaka tafito daga uwar dakan ta rike da wani turmi da tabarya na karfe, shigowa falon tayi ta ijiye turmin a tsakar dakin ta kalli Hamidan tace "kin wani tsaya hala nadawo aljana ce ko kike kallona da katun katun idanun ki kaman kwan lantarki, bazaki shigoba" shigowa tayi dakin Kaka kuma tadau ledojin data fito dasu tana budewa tana dubawa tace "yauwa saiwar ce" ta dago kai ta kalli Hamidan data zauna achan gefe tace "tashi ki cire hijabin nan kije fridge ki daukomin nono da kofi da chokali kizo nan" tashi tayi ta cire hijabin ta ijiye akan kujera taje fridge ta dauko nonon dakeda sanyi ta maida fridge din ta rufe ta kawo ta ijiye kusada ita sanan taje ta dauko kofi ta chokali takawo da sauri Kaka ta ijiye dakan ta karba ta zuba nonon a kofi ta zuba wasu magunguna aciki ta juya sosai sanan ta mika mata tace "yauwa shanye wanan kafin gobe suzo su kawomin kudaden saina dauko miki yar buzu tazo ta fara miki gyaran jiki dan wanan fatar taki fatar manya ce dole kiji gyara, ungo" ahankali ta karba tana kallonta dan ko kadan bamata gane metake cewaba ganin bata mata fadaba yasa taji zuciyata tai sanyi tai maza ta shanye batare data damu da dacin maganin ba.

Haka Kaka tarike ta a Sasan batare data bari tafita ba, tabata wanan tabata wanchan har bayan magrib sanan tasata taje tayo wanka, wanka tayi ta shirya cikin doguwan riganta na atampa sanan tasaka hijab tafito tai sasan su.

Falonsu ta shiga, babu kowa sai kamshin turaren wuta dayake yi, ahankali tawuce ciki ta tsaya agaban dakin Mama, sallama tayi chan kasa tanajin wani irin tsoro aranta, daga taciki Mama tace "waye, shigo" bude kofan tayi kaman wata matsoraciya ta shiga tana zare ido hada ido sukayi

Please Login or Register in order to submit comment