Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

ο»Ώ[20/06, 18:08] Maman noorul huda marubuciya: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
NiDA YAYA
SUDAIS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

wanan labarin kagagen labari ne banyi shi dan cin zarafin kowa ba

ban yarda wani ko wata ta canjamin labari ta kowani siga ba

DEDICATED TO MY HUSBAND HAPPY 5years Anniversary.tanks 4 loving me


Please masu daga farko Ku dinga tambaya a group bani da ishashe lokaci
πŸ…Ώ1⃣&2⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Abuja national stadium,mutane ne cike sun zauna suna jira a fara bike race domin yau ta kasance laraba kuma ko wani laraba ake tsaren mashin din watoh (bike race)

Wani saurayi ne Wanda a kalla ya kai 37yrs tsaye da tsanye da 3qtr sai armless da karamin towel a wuyar shi da alamun yana jira Wanda zasu yi race din tare ne amma shiru har an shafe minti 40

Kallon ref din yayi yace"wanan wani irin wulakancine a ce ana jiranshi har minti arbain be zo ba"

Ref yace"bana miji bane macece"

Yace"what mace ai da ka fada min tun dazun da na tafi domin maza ma basu taba wining dina ba balle mata,nasan ma kila ta tsorata n...."bai gama magana ba ref ya katseshi tare da cewa"ai gata ta zo "yayi maganan ne tare da Nuna me hanyar da ta bullo

Hango su yayi su biyu a saman power bike da helmet a kai na bayan ta rungume mai Jan mashin din

A gaban su ta paka tare da saukowa sanye take da short niker iya guiwa sai wani d'an rigar da be gama rufe jibin ta ba da dogon high heel a kafanta

Cire helmet suka yi na gaban ta mikawa ta bayan

Ref ta kalla tace"iam so sorry 4 coming late" tayi maganar ne ba tare da ta kalleshi ba

Ref yace"babu komai"

Tace"good what are we waiting 4 muje mu fara wasan"

Ref yace"je ciki ki shirya"

Tace"ai a shirye nike"zaro ido yayi yace"da wanan takalmin?"

Tace"don't worry"

Saurayin kallonta yayi sai kawai ya fara dariyar rainin hankali

Yace"ke a ganin ki zaki iya race dani ne?ki yi gaggawan barin wurin nan in ba haka ba zaki sha kunya because kina zance ne da unbeatable SUDAIS the bike man"

Kafin tayi magana kawarta tace"ka damu da kanka"shiko dariya yake har da rike ciki

Karasawa tayi gabanshi tace"are you challenging me?"

Yace"ba ki kai inyi challenging dinki ba"

Lashe baki tayi kafin tayi murmushi tace"in nayi wining dinka ka min alkawarin zaka daina jan mashin,in kuma kai kayi wining daga yau nayi maka alkawarin na daina jan mashin"tana magana ne cikin wani irin hausa mai dadi wanda da jin shi kasan bata da isheshen hausa sosai domin sai kayi mamakin ma tana jin Hausa kasancewarta india

Ba tare da tunanin komai ba yace"ya amince"

Kawar tace"think twice before accepting the challenge"

Yace"no need"

Yariyar tace" BEELAH sit there and video everything ina son in ya koma gida yayi ta kallon defeat dinshi wanan zai zama me darasi akan challenging NEESA"tayi mata nuni da kujera

Shima kiran abokinshi yayi yace"hafiz kayi video komai"kallon Hafiz BEELA tayi kamar tasan shi a wani wuri sai kuma ta basar tare da sakin murmushi

Ref yace"kudin gasa"

Ba tare da ta kalleshi ba tace"nawa?"

Yace"50,000"

Dubu Hamsin hafiz ya mikawa ref

Beelah dubu Dari tace"nayi doubling dan su samu na jinyar zuciyar shi in ya fadi a race"

Helmet suka sa NEESA ta mika me hanun alamun handshake tace"best of luck"

Shima mika mata yayi yana murmushi,sai dai hannayen su na haduwa kowa ya janye nashi sakamakon wani shock da kowane su yaji

Halmet suka sa kowa ya haye bike dinshi

Beelah tace"best of luck besty"

NEESA tace"wani style zan bashi"

Beela tace"hrithk roshan da Katrina kaif a film din bang-bang"

Tace"ok"

Ana hurawa suka tada mashin gudu suke yi sai dai SUDAIS ne a baya kasancewar NEESA ta nuna korewa harda Salle take had'awa kamar a film

Sai dariya beelah keyi tana tafi yayin da Hafiz ya zauna shiru kamar maraya yana tunanin in akayi wining dinsu ba karamin kunya zasu ji ba kuma SUDAIS zai iya samun matsala kasancewar ya fi son bike fiye da mota gashi yayi alkawarin daina hawa in ta yi wining,kai dole yayi wani abu"

Wasu beat ya ciro a aljihu mai santsin gaske ya wasa a dai-dai layin NEESA duk abinda yake yi Beela na kallonshi amma ta share

Bayan wasu mintina sai ga NEESA ta juyo da flag a hanun babu ma alaman SUDAIS

kafin NEESA ta karaso inda Hafiz ya zuba beat beelah tayi ihu

Tace"oil oil"da alamun NEESA ta gane me take nufi ai sai ta kalli kasa ta gan beat a zube sai kawai ta sallake gun

Bella ta fara yiwa Hafiz dariya a gaban shugabanin race din ta parka ta cire halmet ta amshi ruwa goran hanun Beella tasha sanan ta fara goge zufa

Bayan minti 30 sai ga SUDAIS ya karaso tun kan yayi parking aka declaring NEESA winner

mutane ko sai hailing NEESA ake anawa SUDAIS dariya

Karasawa suka yi gabanshi beelah tace"hope u remembere the deal daga yau babu kai ba power bike"

Shiru yayi cike da kunya zuciyar shi na kona

Har sun juya zasu wuce suka ji Hafiz yace"gaskiya yariyar nan ta iya mashin kamar a movies"

SUDAIS yace"ai ba abin mamaki bane domin kasan yan duniya ne Allah ka dai yasan adadin kasar da suka je karuwanci kasan karuwai ne"

Cikin zafin nama beelah zata je wurinsu NEESA ta rike ta

Hafiz yace"


Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
[21/06, 02:59] Maman noorul huda marubuciya: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
NIDA YAYA
SUDAIS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.


DEDICATED TO ANTY SHAMSIYA

πŸ…Ώ3⃣&4⃣

Bismillahi Rahmanir Rahim

Hafiz yace"ai gomma d'ayan ansa indiya ce amma wancan da tasa guntu kaya kamar fa bahaushiya ce kuma musulma take irin wanan shigan"

SUDAIS yace "hm mm ai sunyi nisa"

Kwafa beelah tayi NEESA ko ta ja mashin kamar wanda zai tashi sama

A wani restaurant suka zauna suka yi ordering abinci
Suna ci suna hira

Beela tace"wanan d'ayan gayen kamar cousin dina"

NEESA tace"ta ya kika gane shi?"

Tace "besty bazan taba manta da shi ba domin sanadiyar shi abbana yayi ta wulakanta ni har ummana tasa na bar gidan zuwa gidan yayanta"tana magana ne tana hawaye

NEESA tace"please beela don't start ai zamu koya musu hankali,kuma ban ga abin kuka ba tunda we are successful in life"

Tace"you are right dear"amma yaushe zamu koma gida cause I miss my mum"

NEESA tace"I miss my parent I want to live with them but I will never forgive them 4 abandoning me the way they did"

Beela tace"ba za mu taba bari su San mun zama wani abu ba,zamu dinga nuna musu bamu da tarbiya hakan zai sa su yi nadama abinda suka mana,ko da dai nasan baba na ba zai taba sona ba kuma ba zai canja halin shi na kin ya'mace ba"

NEESA tace"karki damu ranan da ya gane ko ke waye zai ji kunya a ranan zai San ya'mace rahama ne"
Suna gama cin abinci suka mike sanan NEESA tace"muje mu yi wanka kafin mu leka site din ko aiki na tafiya"

Suna barin wurin a titi Beela ta hango wani dattijo mutum na kokarin sallakowa

Tace"NEESA ga babanki"kallon lane din NEESA tayi ta gan yana kokarin sallakowa da ledar kayar da ya siyo a super market amma ya kasa saboda titi yayi busy

Parking tayi a gefen hanya ta sauka suka sallake dai-dai lokacin da wani b'arawo da aka biyo ya ture shi yana so ya fadi NEESA ta taro shi

Yace"thank you dear"yana magana yana daidaita tsayuwar shi ba tare da ya kalleta ba

Itako wani felling ta ji da bata taba ji ba ji take kamar ta rungumeshi

Yace"once again tanks dear"

Tace"urmmmm"kallonta yayi ai sai ya ji wani mumunan fadiwar gaba sai ya gan tayi me kama da matarshi sak,a ranshi yace"this is my princess"

Itama kallonshi take,tana son tasan ko zai gane ta

Shiko wayar shi ya Ciro ya kalli hoton screen din tabbas yar'shi ne wanan

Beela ma kallonsu take

Ai bata yi aune ba taji ya rungumeta yana kuka kamar yaro


Yace"ANEESA where have you been"itama hawayen take yi

Beela ta kalleta ta girgiza mata kai sai tayi sauri gogewa ta raba jikinta da nashi

Tace"your ANEESA is long dead"

Yace"no dear you are my princess right?ANEESA UZAIFA YUSUF my daughter "shiru tayi

Yace" nasan nayi miki laifi amma ki saurare ni please"jiki na rawa ya ciro waya ya fara dialling number matar shi

Tana d'agawa yace"guest what?"be ma jira me zata ce ba yace"iam together with our princess ANEESA"

Priya na zaune ne amma sanda ta mike tace"alhaji me ka ce?"

Yace"abinda kika ji she is with me"
Kuka mai hade dariya ta fara yi tace"please alhaji duk inda zaka yi kayi amma ka dawo min da dota na don't let her escape this time around "

Yace"OK gata kuyi magana"mika mata waya yayi yace"ta amsa amma taki, bai damu ba kawai sai ya sa mata a kunni

Sai hello!hello!mominta keyi amma tayi shiru

Priya tace"nasan kina jina amma dan Allah ki dawo zan miki bayani komai"

Ganin bata yi magana ba yasa shi cewa"dear muje ko kin gan an fara kallon mu"

Beela ta kalleta ta girgiza kai ganin tana son tayi kuka

Shiko har ya bude mota yana jira su Shiga amma basu ko motsa ba

Yace"let go"

Beela tace"ai da mashin muke"

Yace"don't worry muje kawai"

NEESA tace"ba inda zani
Yace"meyasa? baki son ki gan yan uwanki ne?"
Tace"
Ni bani da kowa ni kadai na taso"

Yace"ki yi hakuri ai nace zan miki bayani ko?"

Amma taki jin magana shi

Yace"ANEESA if you are stobborn ni ma baba kin iam more stubborn than you babu inda zanje sai kin Bini"

Ganin zai rikece mata yasa tace"gobe ka same ni a hill guest inn by 2:pm"

Yace"zaki gudu ko?"

Tace"no"

Yace"kin yi alkawarin?"

Tace"yes"

Yace"please karki karya alkawarin ki"

A fusace tace"ni ba kamar kai bane mai alkawari baya cikawa"tana gama magana suka bar wurin

Sanda ya gan sun ja mashin ya shige mota ya koma gida su na abuja

A falo ya tarar da alhaji jabir yana aiki a laptop ya karasa da sauri yace"yaya na gan ANEESA a cikin gari"

Yace"wata ANEESA?"

Yace"ya'ta"

Cikin farin ciki alhaji jabir yace"ina take?"

Yace"taki biyo ni amma tace gobe in same ta a hill guest inn dan Allah yaya ka mata magana ko zata bi mu gida gobe"

Yace"inshaallah wanan karon baza mu bari ta gudu ba"

Bangaren NEESA ko suna barin wurin

Beela tace"


Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Please share
[21/06, 13:40] Maman noorul huda marubuciya: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
NIDA YAYA
SUDAIS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

This page is dedicated to my friend MAMAN FAREESA MARUBUCIYAR INA TARE DA ITA

πŸ…Ώ5⃣&6⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Beela tace"amma meyasa kika bashi adress din guest in bayan muna da gida"

NEESA tace"saboda bana son yasan ni mai kudi ne, ko kin matan baza mu bari susan ko mu waye ba?"

Beela tace"eh na fahimta"

NEESA tace"gobe zamu bisu ko?"

Tace"inshaallah"

Abba ko sai murna yake ya gan yar'shi a haka SUDAIS ya dawo ya same shi

SUDAIS yace"Abba lafiya kake cikin farin ciki?"

Abba yace"ai dole in yi farin ciki Allah ya hada ni da ya"ta ANEESA "

Duk da SUDAIS na cikin b'acin rai baisan sanda ya saki murmushi ba yace"wow Abba na taya ka murna yanzu ina take?"

Yace"gobe zamu je mu d'auko ta by 2pm a hill guest inn"

SUDAIS yace"what a pity a cheap guest inn take zama?gashi gobe da asuba zan koma minna saboda ina da emergency amma zamu hadu a gida inshaallah"

Abba yace babu damuwa

Washe gari da asuba Hafiz da SUDAIS suka bar garin abuja saboda suna da aiki


Misalin 2pm Abbu da Abba suka tafi hill guest inn direct room noban da NEESA ta basu suka je suka kwankwasa

NEESA ne ta bude musu sanye da 3qtr da riga Mara hanun

Tace Ku shigo mana ba tare da ta kallesu ba ta koma ciki

Abba yace"dear ya kike"

Tace"lafiya lau"shiru ne ya d'an rasa kafin

Abbu yace"dear ina son ki shirya mu koma gida zaman hotel bai kamace ki ba,a ce kina mace kina zama a wanan kazamin hotel"

NEESA tace"ya zanyi tunda bani da kowa iyayena sun manta dani"

Abba zaiyi magana Abbu ya dakatar dashi

Yace"dear your anger is justified but please give us a chance"

Yanayin inda yake mata magana yasa jikinta yin sanyi sai ta ji son shi har ranta

Zata yi magana sai ga beela ta shigo da ledar take away

Tana cewa"besty ga abinci"

Abbu ne ya kalleta yace"kamar NABEELA ko?"

Dukawa tayi ta gaishe shi ya amsa cikin sakin fuska

Abba yace"wata nabeelan?"

Abbu yace"yar malam Abbas abokin ka"

Abba yace"wallahi ban ganeta ba"

Abbu yace"Ku shirya muje gida"

Beela zata yi magana abbu ya d'aga mata hanun yace"in na isa dake ki shirya muje"

Tace"toh Abba amma kasan mahaifina baya son ya'mace"

Abbu yace"muje kawai"


Dama sun hada kayan su dan haka suka ce a shirye muke

Abbu yace"toh Ku saka kaya mana"

Kallon jikinsu suka yi suka ce ai mun gama

Yace"ko hijabine Ku saka"

Suka ce mu bamu da shi

Yace"toh muje kawai"Dan ya lura sun fara gunguni

Bangaren priya ko bayan ta gama waya da Abba da gudu ta je part din umma tana cewa"hajiya"

umma tace"na'am lafiya kike gudu"

ajiyar zuciya ta sauke tace"su alhaji sun gan ANEESA yau za a dawo da ita"

umma tace"kai amma na ji da muje mu had'a mata abinci"

cikin murna suka shige kicin yayin da mummy dake zauna ta gan sun wuce ta ta tabe baki tace"munafukan bazan"

abinci suka girka umma ta dafa mata abinci Nigeria ita kuma ummi(priya ta dafa India dishes)sai hira suke

da misalin karfe 3:pm SUDAIS ya dawo daga asibiti a gajiye dashi da Hafiz a babban falon gidan suka zauna suna jiran su Abbu

da misalin karfe hudu su Abba suka shigo gidan da sallama su NEESA na binsu a baya rike da akwati

umma ta karaso ta rungume ANEESA tace"welcome home dear"

babu fara'a a fuskar NEESA tace"thank you"kama hanunta umma tayi ta shigar dasu babban falon inda jama'a gidan suka taru

Hafiz ne ya kalli su NEESA bayan su kawai ya gani ba tare da ya gan fuskan su ba domin sun basu baya shiri su kawai ya gani sai ya kalli SUDAIS dake aiki a laptop yace"kar dai wanan yar iska ce yariyar Abba?"

SUDAIS ya kallesu yace" kasan yaran yanzu sun lalace sai karuwanci na tsani ganin mace da bazan shiga"

duk maganan su a konin nisa hakan yasa ta juya ta kalleshi ai sai ta ga looser da suka yi game ne

shima SUDAIS za ido yayi yace"you"tare da nuna mata hannu

kashe me ido tayi tana murmushi a ranta tana tunanin rashin mutuncin da zata me

Hafiz yace.....



maman
noorul
hudah
luv u my fans
please share
[22/06, 02:18] Maman noorul huda marubuciya: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
NIDA YAYA
SUDAIS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

Dedicated to my HUSBAND

πŸ…Ώ7⃣&8⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Hafiz yace"hmm Ashe yar Abba ce no wonder tayi min kama da ummi"

Abbu ne yace ANEESA muje dining ku ci abinci daga nan sai ki je ciki ki huta"

Tace"toh"

Beela dai shiru tayi bata yi magana ba

Wani saurayi ne da ba zai wuce 30yrs ba ya shigo tare da wani tsoho sai fara'a suke


Saurayi yace"ina sis dina"

Kafin a bashi amsa ya je gaban NEESA ya rungume yace"nasan kene sister na domin kamar ki d'aya da ummi"

Murmushi tayi tsohon yace"itace amaryar tawa"

Akace eh

Dukawa su Abba suka yi da alamun mahaifinsu ne watoh kakan su SUDAIS

Kafin kace me yaran gidan sun cika sun zagaye NEESA suna kallonta sai zuba suke

Abba yace"son zo mana ku gaisa da yar uwar ka"

Yana zuwa ya mika mata hanun amma sai ta basar ta hade hannayen kamar inda indiya ke yi

Hakan da tayi ba karamin haushi ya bashi ba a ranshi yace"in ba saboda su Abba ba ai da bazan ma so had'a hanun da ke ba Mara kamun kai,ni da nike da malama Batul"

Ita dai NEESA share shi tayi ta cigaba da harkokin gabanta

Sai dai taki magana da umminta ko Abba yayi da ita bata amsawa sai dai umma da Abbu da sauran yaran gidan da sauranyin nan da ya shigo Hamza me kama da SUDAIS sak

Alhaji ne yayi magana yace"a kira sauran mutanan gidan a ci abinci"

Farida ne ta mike ta tafi part din mummy ta kirata da ya'yan ta sai wani cika take tana basewa

Babu Wanda ya kula ta da ya'yan ta domin sun San halinta

A haka daddy ya shigo ya same su yace"wai ina Batul?"

Mummy tace"bata dawo ba tana makaranta"be kara wani magana ba suka fara cin abin

Abinci umma NEESA ta ci

Ummi tace"ga indiya dishes amma ko kallonta bata yi ba,umma ne ta mata alama da ido akan karta damu

Bayan sun gama cin abinci SUDAIS ya mike NEESA ta bishi da kallo

Har ya shige part dinshi

Abbu yace"dear kuje farida ta nuna miki dakuna ki zaba"

Tace"Abbu ni fa wancan nike so"ta me nuni da d'akin SUDAIS

Abba yace"d'akin yaya kine SUDAIS ki je ki zabi wani please"

Ganin ta hade rai yasa Alhaji cewa"dole fa a yiwa amaryata abinda take so"

Abbu yace"hamza kira SUDAIS"

Yace "toh" a tare suka dawo

Abbu yace"ka kwashi duk wani abinda kasan yana da muhimmancin a gunka ka koma boys quarters domin anan ANEESA zata zauna"

Yace"what?"

Abbu yace"yes ko ban isa bane?"

Abba yace"gaskiya in aka me haka ba a me adalci ba"

Umma tace"ai dole ya bar mata tunda shine babba"

Ummi tace"amma be dace a kore shi ba kowa yasan inda SUDAIS ke mutuwan son d'akin shi"

Umma tace"mutum ya rasa ranshi balle d'akin"

Ganin suna b'ata mata lokaci yasa ta sakin kukan karya

Da sauri umma ta karasa inda take tace" subhannallah baby meya same ki?"

NEESA tace"ni dama nasan ba sona ake ba tunda common d'aki an gagara bani ni zan koma inda na fito"ta kareshe maganan da jan akwati

Tsawa Abba ya dakawa SUDAIS yace"zaka bi umurni na ko sai rain ka ya b'aci?"

Rai b'ace ya kalli NEESA da ke kukan karya umma na lallashinta

Ai sai ta fakin idan jama'a tayi me gwalo tana murmushi har da kashe me ido tana lashe baki

Wani haushi ne ya dibe shi da gudu ya haura sama ranshi na kuna

Wani kukan ta saki Abba yace"miye kuma?"

Tace"kayan shi kadai zai kwashe ya barmin gadon"

Umma tace"angama"

Yana saukowa da akwati ta karasa gabanshi tace"bari in taimaka ma"tana magana tana murmushi kasa-kasa

Hararanta yayi sanan ya janye akwati har yana turata

Umma tace"bashi hanya kar yayi miki illa kin San ba hankaline dashi ba"

NEESA tace"oh ummi kina nufin yana da tabin hankali toh ai ba boys quters ya kamata a kai shi ba asibiti ne"

Yana jin abinda ta fadi ya juya ya kalleta

Idon su na haduwa tace"sannu ashe baka da lafiya"

Wani haushi da tsananta ne ya fara bin jinin jikin shi

Suna hada ido da beela ta d'aga mata gira tace"oil oil"

Beela ta jinjina mata ta hanya yi mata alama da babban yasa

Shiko Hafiz bin abokin shi yayi a baya

Abbu yace"kuje Ku huta NABEELA bayan sallah isha'i zanwa abban ki magana

Tace"toh tare da jan akwati zuwa ciki"

Suna shiga d'akin NEESA ta lumshe ido tana lashe baki a falo suka zauna

beelah tace "ai ban tunanin yau zaki fara yi me rashin mutunci ba"

ajiyar zuciya NEESA ta tace"ke a tunanin ki zan barshi ne bayan ya kira mu karuwai?beelah na sani mazinaci bana kuma so amin zargin zina domin nima bana yiwa wani ko da kuwa na gan mutum ya kebe da wata ko wani nikan yi musu uzuri domin zina ba karamin laifi bane kamata in zaka zarge mutum ka tabbatar kana da hujja,amma a abuja sai ya kira mu da karuwai a nan ma sanda yayi gulma mu wallahi ina jin tsanan shi har cikin jini na kuma zan koya me hankali"

beelah tace"kamar inda na tsani Hafiz ba"

NEESA tace"bari inje kasa na manta da wayana a dining"

tana saukowa ta fara jin magana a falon umma tace"yanzu haka ma kila gulma na suke"karasawa tayi sai ta ji abbu na cewa" dole fa muyi abinda take so in muna son zamanta a gidan nan"

Abba yace"amma gaskiya ba a kyautawa SUDAIS ba"

abbu yace"dole ne ya ci girma"

ummi tace"ni ko magana bata son min"

daddy yace"Ku bata lokaci"

budan bakin mummy sai tace"mu dai an kawo mana mara tarbiya"tsawa daddy ya daka mata tare dacewa bar nan wurin mara mutunci kawai

jin motsin fitowar mutum yasa NEESA barin wurin da ta makale ta je ta d'auki wayarta ta haura sama cike da nishadi

tana zuwa tace"beela guest what?"

beelah tace"what?"

tace"an bani lasisi koyawa wanan mara mutuncin hankali"

tace"bangane ba"

tace"yanzu na ji suna cewa kome nike so shi za a min kin gan da wanan dama zan koya me hankali"

beela tayi dariya tace"oil oil "

NEESA tace"muje bedroom in gyra d'akin"

wacece NEESA da Beela




gaskiaya comment Ι—in ki yayi min Ζ™kadai Ζ™ko a bar labarin ne Ι“e muku ba cause baku bani karfin guiwa as usual

maman
noorul
hudah
luv u my fans
please share
[22/06, 14:13] Maman noorul huda marubuciya: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
NIDA YAYA
SUDAIS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

DEDICATED TO MY FANS

πŸ…Ώ9⃣&1⃣0⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

UZAIFA YUSUF shine cikeken sunan mahaifinta haifafen garin taraba ne watoh fulanin jalingo

Sunan maihaifinshi alhaji yusuf da mahaifiyar shi fatima su uku ne a gurin mahaifansu duk maza Jabir ne babba sai shi uzaifa sai autan su Jibrin sun taso ne cikin so da kaunar juna inda suke girmama juna

Sai dai mahaifinsu gadi yake yi mahaifiyarsu kuma sana'ar sayar da kayan miya a kofar gida alhaji Yusuf duk kokarin shi kan yaran shi ne dan su samu ingantace ilimi da tarbiya

A haka ya reine su har suka girma inda jabir watoh(abbu)da uzaifa watoh Abba)suka gama sekandari suka samu scholarship zuwa jami'a da taimakon wanda alhaji keyi wa gadi

Abbu na gama sekandari me gidan alhaji ya aura me yar'shi khadija da yike a lokacin yana da shekara 23 da uku bai gama bane da wuri domin ana yawan yi me repeat baya son makaranta sai kasuwanci alhaji isah ya yaba da hankalinshi da kuma natsuwa da rikon amana domin yana zuwa kasuwa taya shi kasuwanci

samun scholarship dinsu
Hakan ba karamin sauki alhaji ya samu ba sai kawai ya fuskaci autan watoh jibrin

bayan shekara biyar da auren jabir khadijat ta haihu d'anta namiji ya suna ABDULSUDAIS

Bayan shekara biyar suka kammala karatun su inda jabir ya karanta accounting shi kuma Abba business admin sai dai babu aiki gomma abbu yana bin alhaji isah kasuwa taimakawa shiko Abba sai dai zaman gida wasa-wasa har ya shafe shara biyar a gida

Hakan yasa uzaifa barin jalingo da niyar niman aiki

Direct minna ya je amma ba karamin wahala ya sha ba kasancewar shi bakone wanda basan kowa ba

Har kwana yake a tasha cikin ikon Allah ya hadu da wani mai kwana a shago mai suna Abbas

Ashe Abbas ya kula domin in ya dawo aiki da asuba sai ya ganshi kwance yana barci

Wata rana sai yayi me magana nan Abba yayi me bayanin ko shi waye ne

Yace"toh shigo ciki mana,abinci ya bashi suna ci suna hira

Abba yace"ni wallahi ko wani irin aiki na samu zanyi"

Abbas yace"nidai da rana ina zuwa aiki gidan block da dare kuma aikin company DANA company ne da ake magunguna da robobi nan maitumbi yake

India ke dashi in kana so sai ka ka zo muje gobe ka biya 2500 kudin unifoam da safan hanun

Abba yace Allah ya kaimu hira suke kamar sun taba sanin juna domin abba akwai barkwanci ga sabo da mutane wanda yawanci maganan Abbas a kan kiyayya shi ne ga yara mata

Abba yace"ai da namiji da mace duk d'aya ne in ka lura yara mata rahama ne kuma suna da tausayi da jinkai amma in baka yi sa'a haihuwar namiji

Please Login or Register in order to submit comment