Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta tabbatar ta tusa me bakin ciki sanan ta bar gidan

Direct dakin su taje ta bawa NEESA labari suna dariya

Haka fa NEESABEELA suka cigaba da wahalal da YAYA SUDAI ta hanya daban daban da taimakon A'i har yaji suka zuba me a ruwan wanka SUDAIS sanda yayi kamar zaiyi hauka ranan sanda yayi kwana uku bai fita ba

A yau NEESA ta fara takawa kuma suna shirin zuwa abuja ranan lahadi kasancewar yau juma'a washe gari zasu yi celebrating holy

Hafiz ko fama yake da hanun shi ko aiki be zuwa

SUDAIS ne a office yana aiki sai ga Hafiz ya shigo da hanun makale a wuya

Zama yayi ba tare da yayi magana ba

SUDAIS yace"sannu ai wallahi sai na rama abinda suka yi mana"

Katseshi Hafiz yayi da cewa"look SUDAIS ya kamata muyiwa kanmu fad'a haka be kamata muna biye ma yaran nan for goodness sake mun girme su,kuma mu muka fara tsokanan su which is very wrong of us be kamata a matsayin su na kanne mu muna kiransu da munana suna ba,abinda bamu da tabbaci akanshi zargi kuma ai zato zunubi in ma suna yi jan su jiki zamu yi muna nuna musu so bawai muta aibanta jinin mu ba,dan na lura yaran nan basu da matsala kiransu da muke da karuwai shike b'ata musu rai

SUDAIS yace"wallahi basu isa nayi give up akan su ba in nayi haka yana nufin sunyi wining kenan fa,kuma ai ba karya na musu ba yan iskan ne in basa su a kira su da sunan su canja shiga kuma su daina zuwa kwanan gida"

Hafiz yace"miye a ciki?ina jiye maka ranan na dama wallahi"

Yace"na ratse sai na rama"

Hafiz yace"babu ruwana na fita a wanan harka"

SUDAIS zaiyi magana sai wayarshi tayi kara kallon Hafiz yayi yace"Afan ne"

Hafiz yace"d'auka mana"

Yana d'aukawa yace"OK gani nan zuwa"

Makulli mota ya d'auka suka fita a office

A wani babban joint suka pska joint ne da maza ke chamber ko wani juma'a

Suna shiga suka sami wuri suka zauna

Nan fa na gan star din maman noorul hudah tun daga kan farhan na(EESHA)sai RAYHAN na(IKLAS)sai IMRAN na(IMRANFAD)sai AMEER na (matan Gida)da sauran mazan su aminu Amar Deen da mustapha

Sai Afan da Sameer na (rayuwar nur)

Nan hira ya b'arke tsakanin su inda suke tambayar abinda ya same Hafiz a hanun

Be boye musu ba ya basu labarin komai tun farkon haduwar su da su NEESA

Kallon SUDAIS Afan

Yayi yace"kar kayi kuskuren da nayi a baya hanyar kiran NUR da sunayen bazan"

Farhan ko tashi yayi yace"shi zai wuce gida EESHA na jiran shi"sai suka fara me sharri wai ya iya naci

Sameer yace"ni har na fara tausaya ma"

Ameer yace"har na hango haukan da zaka yi nan gaba domin ni Allah ya had'a ni da mai riko sanda na haukace ta yafe min"

IMRAN yace"please ka daina babu kyau zargi"

Babu inda basuyi dashi ba amma yaki ji yace"ai shi ba auran NEESA zaiyi ba kuma ai yana da hujja"nan fa suka mike

Aminu yace"karma ka nime mu in tayi wari"

Musty yace"muje kawai"

Nan fa kowa ya waste

Da misalin karfe 11:pm



Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
NIDA YAYA
SUDAIS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

Dedicated to MAMA NOORUL HUDAH FANS CHAMBERS

πŸ…Ώ5⃣1⃣&5⃣2⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

29/06/2019
Misalin karfe 11:pm SUDAIS ne kwance har ya fara barci wayarshi yayi kara

Yana d'agawa yace"gashi nan zuwa"a gurguje yasa kaya domin a asibiti ne yana da emergency

Yana kaiwa ya shirya ya Shiga labour room

Wata ce mai suna Esther take labour

Yana zuwa ya fara kokarin taimaka mata sai fad'a yake domin mahaifanta babu karfi saboda abortion

Da k'yar yayi kokari aka samu ta haihu domin har ya kusa kaita tiyata

Amma dayake yasan aikin shi da kuma taimakon Allah ta haihu mace

Aka maiyarda ita dakin hutu

Su biyu suka zo daka gansu ka gan yan duniya

SUDAIS na gamawa ya ba nurse jummai umurnin basu kulawa

Sanan ya bar wurin

Bangaren NEESA ko ta kasa barci sai juyi take a gado beela tace"wai lafiyar ki ai dai kin ji sauki balle a ce zafin kafan ne"

Tashi tayi ta zauna tace"dear iam feeling restless ina jin kamar wani na kusa dani zai Shiga matsala ko kuma ya shiga,in fact kamar rabin jikina na cikin hasari"

Tsaki beela tayi tace"ke dai da jin restless ni dai barci nike ji"ta kwanta abinta

NEESA ko tashi tayi taje wurin window ta tsaya abinta tana kallon

Har shigowar SUDAIS duk a idonta

Yana shiga d'aki ta shige toilet tayi alwala ta tada sallah

Washe gari da asuba aka kira NEESA an sinci jaririya a gaban ophanage dinsu
A gurguje ta shirya ta fita

Bangaren SUDAIS ma haka ne da asuba aka kira shi wai an sace jaririyar da aka haifa jiya

Ai jiki na rawa ya shirya suka tafi asibiti da Hafiz

Nan ya tarar da Esther da blessing suna shirin barin asibiti kamar ba yar'su aka sace ba

Yace"ki bari muyi report a station

Tace"ni bani da wanan lokacin"

Mamaki ne ya kamashi ya bi ta da kallo binta yayi har haraban asibiti yace"gaskiya ki bari police su zo kafin ki tafi"

Tsawa blessing ta daka me tace"kai dole munce bamu so ayi involving police"tana fadin haka suka wuce suka barshi tsaye

Hafiz yace"dole mu kira yan sanda nan fa su d'auki statement "

SUDAIS yace"is of no use su da yar'su ta b'ata basu damu ba sai mu"

Hafiz yace "is important"

Yace"no"

Su Esther na barin wurin blessing tace"kin gan gomma da muka yi haka babu wanda zaiyi zargin mu muka b'atar da ita da kanmu yanzu da kin gama jego sai ki cigaba da rayuwar ki nasan Don zai mayar dake gidanshi"

Tace"thanks dear"

NEESA ko bayan tana zuwa ta iske jariri agun mama almajirar da ta taimakawa

Nan bash ya kaita station tayi filling duk wasu formalities aka bar mata yariyar tare da bata copy suma suka ajiye copy

Ta dawo ta damkawa mama tare da bata madara

Babu laifi orphanage din ya fara jama'a

Daga nan ta biya asibiti ta d'auki beela suka koma gida

A mashin beela ke sanan da ita abinda ta gani wuyar abbanta

NEESA tace"kila maruru ne"

Beela tace"no cancer ne a wuya yake fitowa a hankali zai ta girma har ya zo ya toshe ma magogoro is very dangerous ya kamata ayi maganin shi yanzu"ta karashe magana cikin damuwa

NEESA tace "toh kiyi me magana mana"

Tace"I try to amma bai saurare ni ba"

NEESA tace"ki yi ta addu'a"

4:pm suka kai gida nan fa suka fito da babban radio da speakers suka sa kidi a garden domin already sun shirya cikin fararen kaya

Nan suka fara wasan holi da colours da suka yi order

Mutane gidan kowa ya fito yana kallon su

Da gudu NEESA ta karasa gaban ummi ta tafa kafanta sanan ta shafa mata colour tace"happy holi mom"wani dadi ummi taji ta rungume ta suna dariya itama tasa mata colour

Beela dake gefe tana kallon su ummi tace"common zo ki yi hugging ummi"da gudu taje tayi huggin dinta

Haka suka ma umma itama tasa musu albarka

Hamza yace"hmm mun zama indiyawa"

Wasa su suke yi a haka SUDAIS ya dawo ya same su

Dan tuni su ummi suka shige ciki

A falo mummy keyi wa ummi magana tace"hmm mu dai an had'o mu da karuwai yara duk sun dame mu da kida a gari"

Ko kulata su umma basu yi ba suka shige

SUDAIS ko shigewa yayi d'aki ya tsaya yana leken su ta window

Sai ya sinci kanshi da jin nishadi

Hadari ne ya d'auro beela tace nidai na shige domin nasan ke ruwan nan a jikin ki zai Kate

Ai ko haka akayi wasa NEESA keyi a ruwa tana rawa duk a idon SUDAIS

Sanda aka gama ruwa ta shige shima ya bar wurin

Washe gari da sassafe suka bar gida

SUDAIS na zuwa office zai murd'a kofa yaji ta a bude yana shiga ya gan mutum zaune ta juya me baya yace"waye"

Juyowa NEESA ta yi tace"nine na zo in maka ya jiki ne"

Yace"ina kika samu makulli"

Tace"is not important ,na zo ne in gargade ka akan ka fita harka na domin next time ba kunnama zan sa ya halbe ka ba maciji ne"

Yace"oh dama kene kika sa kunnama ya halbe ni"

Tace"yes ai alkawari na d'auka kaima zaka shiga halin da nashiga"

Yace "zaki yi nadama"

Tashi ta yi tace"banda lokacin ka"

Tana barin asibiti suka tafi abuja ba tare da sun sallami kowa ba

A gida ko niman su ake umma ko ta kira NEESA bats d'agawa Abu kamar wasa har sukayi sari biyu

Ran abbu yayi mugun b'aci ya d'au alkawarin nuna musu kuskurensu
SUDAIS ko sai kara zugawa yake yi

Bangaren su NEESA ko aikine ya musu yawa dan sati d'aya suka yi a abuja sanan suka tafi Lagos

A'i na sanar dasu ko mai dake faruwa a gida

A yau suka shirya zasu dawo

NEESA tace


Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
NIDA YAYA
SUDAIS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers we are the best among the rest.

Dedicated to MAMAN NOORUL HUDAH FANS CLUB comment dinku na sani nishadi


πŸ…Ώ5⃣3⃣&5⃣4⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

NEESA tace"tunanin abinda zamu fad'awa abbu nikeyi domin A'i tace ranshi ya b'ace"

Beela tace"gaskiya ne munyi laifi but we are helpless"

NEESA tace"no we are not,we are wrong this time around kuma zamu amshi kuskuren mu at least ko zamu wa mutane rashin kunya be kamata muyi wa abbu ba"

Beela tace"hakane"

Da misalin karfe 4:32pm suka isa gida a babban falo suka tarar da kowa da alamun ma maganar su ake

Kallon su abbu yayi sama da kasa sun sa riga bodyhug long sleev da pencil long jeans kan su ko d'an kwali babu

Cikin b'acin rai abbu yace"daga ina kuke"

Kafin NEESA tayi magana SUDAIS ya karbe maganan da cewa ai yawo suka je ina kuwa"

Ran abbu ne ya kara b'aci yace"da Ku nike magana"

Mummy tace"yo ina kuwa in banda karuwanci kai baka gan shigarsu ba"

Daddy ne ya daka mata sawa nan fa tayi shiru

Alhaji yace"amaryata fad'a mana inda kuka je"

Jiki a matsayin sanyaye ta karasa gaban abbu ta sunguna da guiwawi ta tace"Abbu dan Allah ka yi hakuri baza mu kara ba mun tuba please"karasawa tayi gaban umma ai sai umma ta shige ciki

Ummi ta kalle sai ta gan sunyi fushi

Ba tare da abbu yayi magana ba ya shige ciki

SUDAIS yace"yara kanana sai shegen iskancin tsiya

A fusace NEESA tace"allah ya tsare mu da zama yan iska wallahi"

Yace"ni kikewa rashin kunya?"

Basu ko kalle shi ba suka shige daki

Wanka sukayi beela tace"ya zamu yi kowa na fushi damu"

NEESA tace"karki damu zamu yi fixing komai,kuma zamu gyra kuskuren mu inshaallahu zamu bar tafiya sai komai ya dai-daita"

Tace"inshaallah "

Armless gown suka sa suka kama hanyar part din umma a falo suka tarar da abbu

Karasawa suka suka sunguna NEESA tace"abbu dan Allah kayi hakuri"jikin shine yayi sanyi

Yace"na hakura amma ina kuka je?"

Kallon juna sukayi kafin NEESA tace"abbu wallahi a gidan marayun da muka girma ne ake wani program shine muka je"

Yace"amma meyasa baku sallame kowa ba?"

Shiru sukayi yace"ANEESA meyasa kuke irin shigan nan?"

Tace"abbu na fison irin kayan ne"

Yace"ko kin san da irin wanan shigar ana muku kallon yan iska karuwai ne?"

Kallon juna suka yi yace"yes duk mace dake barin jikinta a waje bata da kima a idon jama'a domin ana mata kallon gagarariya"

Suka ce da gaske?

Yace"eh Ku jira ni ina zuwa"

D'aki ya shiga sai gashi ya fito da sweet guda biyu d'aya an bude d'aya a rufe

Yace"d'auki d'aya"

NEESA ta d'auki wanda ba a bude ba yace"meyasa kika zab'i wanda ba a bude ba?
Tace"saboda ya fi safta kuma babu datti"

Yace"good,kefa NABEELA?"

Beela tace"saboda yafi mutunci babu datti da ya shiga"

Yace"toh haka ake kallon duk wata mace mai kulle jikinta ko da kuwa tana da halin banza,wallahi ko namiji ne yafi son wanda ke mutunta jikinta"

Beela tace"amma abbu akwai yan mata dayawa masu amfani da hijab suke abinda suka gan dama su fa ba a ganin laifin su?"

Abbu yace"karki damu duk zasu karbi sakamanko su tun a duniya domin hijabin ma sai ya ci mutuncin su"

NEESA tace"Abbu mun gode kuma inshaalah zamu gyra domin mun gane kuskuren mu"


Bunch din dubu ya Ciro ya mikawa NEESA yace"gashi Ku je Ku siyi hijabi ni ban hanaku shigar da kuke so ba amma kusa hijabi a sama"

Suka ce mungode abbu Allah ya kara girma

Yace"amin,Ku je ku bawa iyayen Ku hakuri harda abdulaziz dan na ji d'azun kuna me ihu"

NEESA tace"toh"

Wurin umma suka shiga suka bata hakuri da k'yar ta hakuri amma ta musu fad'a sosai tace"karku ba da dama ayiwa ummi Ku dariya"

Bayan sun bar wurin suka tafi part din mummy hakuri auka bashi ya musu nasiha

Mummy ko sai zaginsu take amma basu kulata ba

Bayan nan suka tafi gun ummi

Rungumeta NEESA ta yi tace"iam sorry"

Ummi ma fad'a ta musu tace"please Ku rike budurcinku please"nan ma suka mata alkawari


Boys quarters suka je a falo suka tarar da SUDAIS Hafiz na kwance a 3 seater kamar yayi barci amma idon shi biyu

Karasawa NEESA tayi tace.......



Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Please share
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
NIDA YAYA
SUDAIA
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest

Dedicated to NIDA YAYA SUDAIS FANS GROUPS

πŸ…Ώ5⃣5⃣&5⃣6⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

NEESA tace"YAYA SUDAIS ina wuni"

Yi yayi kamar be ji ba tace"YAYA SUDAIS da kai nike yi"

Yace"wai meyasa kike damuna?"

Tace"yi hakuri na zo ne in baka hakuri akan abubuwar da suka faru a baya dan Allah ka yi hakuri na tuba"

Yace"oh ta nan kika bullo kuma salon ki kara cutata toh wallahi bazan taba yarda dake ba kuma bazan daina jin tsanan ki a zuciyata ba na tsane ki domin ni a rayuwata na tsani mazinaci"

Tace"toh babu komai ni dai na sauke hakkin da ya rataya a wuyana,kai kuma ka cigaba da zargina bazan hana ka ba"

Yace"aini bazan taba yarda dake ba domin ina da hujja ta dan iskanci sanda kuka gama karuwanci ku har na sati biyu zaki wani dawo kina ragewa mutane murya"

Murmushin yake tayi tace"Allah yasa mu gane.muje beela"

Fita suka yi suka barshi yana ta fad'a

Suna kaiwa d'aki NEESA ta kwanta tana tunanin maganganun SUDAIS

Beela tace"meyasa baki bashi amsa ba"

Zama NEESA tayi tace"saboda muke da laifi "

Beela tace"me mukayi?"

NEESA tace"mu muka hardasa zargi a zuciyarshi domin maganan abbu gaskiya ne your appearance tells who you are,shiyasa we can stop or blame any body that don't our character,sai dai abinda ke bani haushi inda yake magana with full confident,amma inshaallah zamu gyra sai dai zaiyi wuya na manta magaganun SUDAIS"

Beela tace"Allah ya shiryamu ya sarkake zuciyar mu"

NEESA tace"amin ki shirya gobe zamu shopping kayar sawa"

Bayan mazan gidan sun dawo daga masalaci a dining aka zauna danyi dinner

Suna cikin cin abinci sai ga mai gdin gidan ya shigo wai ana sallama da ANEESA"

Da mamaki NEESA ta kalleshi tace"ni waye?"

Yace"wani ne"

NEESA tace"je kace kuskure ne bani NEESA bane"

Abbu yace"je ki gan ko waye ne"

Komawa tayi daki tasa hijab har kasa domin tun nasiha abbu jikinta yayi sanyi

Tana fita ta gan mota a kofar gidan karasawa tayi ta buga motan

Don ne ya fito ya yana murmushi hade rai tayi tace"meya kawo ka nan kuma waya nuna maka inda nike?"

Yace"haba ANEESA ai ke bari mu gaisa ko?ni bansan abinda na miki ba kika guje ni"

Tace"saboda ni bana harka da d'an iska kuma daga yau bana so ka kara zuwa Inda nike"

Yace"wallahi zan zo domin kece matar da nike so in aura"

Tace"Allah ya kare ni daga auren irinka"

SUDAIS da tun fitar NEESA ya ji gabanshi na fad'awa kuma haka kawai yaji haushi fitar ta

Tashi yayi ummi tace"ina zuwa?"

Yace"ina zuwa zan duba abu ne"

Yana fitowa ya gan NEESA tsaye da Don ai ji yayi kamar wani abu ya caki zuciyar shi

A zafafe ya karaso ba tare da yayi magana ba ya kama hanun NEESA ya fara ja

Kwacewa take sonyi amma ya riketa gam sanda ya tabbatar sun shiga gida sanan ya sake ta yace"ke nan ba gidan karuwai bane da zaki ta kawo mana yan iska"

Tace"toh ina ruwan ka?"

Yace"da ruwa na dan yarda da iskanci a nan gidan ba"

Wucewa tayi ciki domin ta lura rigima take nima

Washe gari suka tafi shoping a store

Kaya sosai suka siye wanda yawanci jallabiya ne da kimono dress sai irin su turkey gowns da already made hijab da Arabian gowns

Suna fitowa suka hango batul a d'ayan lane da Don tsaye

Beela tace"besty kalli can bana gaya miki ban yarda da yariyar nan ba"

NEESA tace"ki mata uzuri domin zargi kike karki kwashi alhakinta"

Beela ta yi shiru amma ba dan ta yarda ba

Suna dawowa gida da minti talatin sai ga batul ta shigo

NEESA tace"batul dan Allah ina son magana dake"

Batul tace"fadi ina jin ki"

NEESA tace"d'azu ne na ganki da Abubakar Don shine nace bari in fad'a miki halinshi dan kar ya yaudare ki domin ba mutumin kirki bane"

Tsaki batul ta yi tace"toh munafuka ina ruwanki mutum sai shagen sa idon siya"tsaki tayi ta bar wurin

Beela tace"bana gaya miki ba yariyar bata da mutunci ba"

NEESA tace"babu komai na fita hakkinta"

Haka rayuwa ya cigaba da tafiya inda yanzu dawowar su NEESA sati biyu kenan sun nasu sun daina kula SUDAIS kuma sun daina shigan bazan kullum suna cikin jallabiya

Kuma aikin su na tafiya inda ya kamata

Yanzu kuma abbu ya saka binkin SUDAIS da batula nan da sati biyu har anje kauyen su niman aure kuma an yarda ayi komai a nan

Shakuwa ce mai karfi tsakanin umma da NEESA domin NEESA tafi sakewa da umma kuma ba laifi tana kula ummita wanda kullum nasiharta baya wuce su rike mutuncin su

Beela ko tana zuwa ganin mami time to time kuma babu inda bata yi ba danyiwa abbanta maganan lalurar shi amma yaki saurarenta babu inda ta iya haka ta hakura

Bangaren SUDAIS ko allah-allah yake ayi aurenshi da batul

Daddy ma sanda ya gargade shi cewa"batul bata da mutunci"amma ya nuna sai it a

Umma ma ta yi me magana akan ya nimi wata amma yaki

Abbu ko baka ganewa ko yana so ko baya so shidai yace"tun da yana so za a mai"

Don ko yana zuwa amma NEESA bata kulashi kuma ya d'au alwashin koyawa SUDAIS hankalin janta da yayi suna hira
Kuma ya samu labarin yana niman batul domin yana ganin text dinshi a wayar batul sai dai tana boye me hakan yasa yayi alkawarin dealing da SUDAIS domin be isa ya shiga inda yake Shiga ba

Shiko SUDAIS ya d'au alwashin koyawa NEESA hankali na abubuwan da suka me

A kwanta a tashi ba wuya yau bikin SUDAIS da batul saura kwana uku gida ya cika ana shirye-shirye

Batul ko karya tawa Don zata yi tafiya kuma har dinki taje yayi

Yau za ayi kamu a harabar gidan

A yau kuma NEESA ta tashi da amai da ciwon ciki
Komai taci sai tayi aman shi

SUDAIS da yaje d'akin dan ganin ko ta kwana a gida domin kowani safe sai yaje d'akin tun randa ya ganta da Don kuma ga batul na kara
zugashi domin ceme tayi ta taba ganin Don ya sauke NEESA da asuba lokacin tana diba ruwa a masalaci

Yana zuwa ya ji kakarin amai

Tana fitowa ya kalleta sai ya gan ta karame haske kuma tayi fayau kallon tuhuma yayi mata

Yace"



Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Please share
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
NIDA YAYA
SUDAIS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

Dedicated to Rayuwar nur fans group

πŸ…Ώ5⃣7⃣&5⃣8⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Kallon tuhuma yayi mata yace"ke meke damun ki?"

Zata yi magana sai kuma ta koma toilet ta fara kwarara amai

Sanda ta jigata sanan ta fito ta kwanta ta rufe kanta da bargo

Kallonta yayi tana nishi a ranshi yace"lokaci yayi da zan tona miki asiri

Fita yayi cike da zargin NEESA

Yana Fita sai ga beela ta shigo da ledar magunguna tace "besty tashi in miki allura sanan ki sha magani"

Da k'yar ta mike beela ta mata allura

Beela tace"aure kike bukata na gaji da ganin ki haka a ce kowani wata sai kin yi wahala"haka NEESA ke fama in zata yi mensturation

NEESA tace"karki damu zai bari"

Can anjima sai ga jinin ya fara zuwa toilet ta koma tayi wanka tasa pad sanan ta fito

Tana murmushi tace"beela muyi shiri muje kasa su anty amina sun zo"

Beela tace"toh"

Suna gamawa suka sauko aka fara hira dasu karfe 4:pm akayi kamu bakin SUDAIS ya ki rufuwa dan murna zai mallaki batul

Washe gari da safe NEESA ne zaune a d'aki da laptop a gabanta tana aiki sai wayarta yayi kara tana d'agawa tace"bash ya dai"

Yace"lafiya yanzu zan kai saratu test"

Tace"ok ana biki a gidan mu da na biku amma kome ya faru kamin test din result din"

Yace"ok"

Saratu yariya ce yar 16yrs da wani d'an 40yers yawa fade kuma marainiyace mutumin ya nunawa hukuma kudi shine akayi wasi da maganar
Wata ce taba mahaifiyar saratu shawaran zuwa ANEESA U Y Chambers dan niman taimako inda tana zuwa aka taimaka ba tare da ta biya ko sisi ba kuma bash ke Jan case din

Sati uku kenan ana shari'a kuma kamar alamun ciki ya fara bayyana a jikin saratu shine suka roki alfarma kotu da a bari su kaita test

Bayan awa d'aya NEESA ta fita waje niman A'i zata aiketa

Tana fita SUDAIS ya shiga ya fara bincike be gan komi ba

Can ya hango wayarta da yayi karan shigowar text budewa yayi dan NEESA bats sa lock

Sai kawai ya gan text kamar haka:the prenancy test result is positive "

Yace"zargi na ya tabbata gaskiya wallahi sai na tozarta ki,sai na tona miki asiri inda kika tozarta ni aka min wakar looser"

Fita yayi yana tunanin hanyar da zaibi dan ganin ya tozarta ta

Da yamma ya zo part din ammi kafin ya shiga yaji beela na cewa"kiyi kokari kisha maganin nan zai yi flushing dinshi dan ciwon ciki ya ragu"

A ranshi yace "oh zubarwa zasu yi hmm dai-dai kenan"

Da misalin karfe 9:pm duk suna zaune a garden da farida da NEESA da beela sai A'I

NEESA ne taji ta fara stain har ya fara b'ata inda ta zauna tace"beela zan shiga ciki"

Beela tace "muje kawai nima zan kwanta da wuri saboda gobe nasan akwai aikin biki tunda jibi ne d'aurin auren"

Gaba d'ayan su suka mike suka bar wurin

Suna shigewa SUDAIS ya zo zai zauna a inda beela ta zauna sai kawai ya gan jini

Yace"har sun zubar kenan?Allah ya kaimu gobe"

Washe gari an cika a gidan NEESA suna zaune a balcony sai ga SUDAIS ya zo a zafafe ya rufe ta da duka

Ihu take tana niman taimako inda kowa na gidan ya fito

Abbu yace"kai lafiya?"

SUDAIS yace"abbu ka bari in koya mata hankali yariya karama har tasan ta zubar da ciki"

Kowa zaro ido yayi yace"ciki?"

Yace "eh ciki"

Ummi ko kuka ta saki ganin inda jama'a suka zagaye su

Mummy ko tayi guda tace"asirin masafa ya tonu "

Kuka NEESA ta saki tace"wallahi karya yake yi"

Beela ma kuka takeyi tace"Karya kake mata"

Wanka mata mari yayi yace"munfuka bake kika kawo mata maganin ba ai ina jinku"
Kwace wayar NEESA yayi ya fara nunawa kowa text din

Umma ko ba karamin b'acin rainta yayi ba ganin SUDAIS ya dage yana tozarta NEESA ai ko ba komai ya dubi soyyayar da ummi keme ya bari a gama biki ayi maganar a sirrince amma ya zabi tozarta masu zuri'a wallahi sai ta sab'a me

NEESA ko ganin ummi na kuka ya kara d'aga mata hankali tunawa tayi da nasihar ummi karasawa tayi zata riketa sai ta turata

Kuka takeyi kamar ranta zai fita bana dukan da yayi mata ba a'a na tozarta ta da yayi

Haka tayi ta zuwa wurin kowa Rana bayani amma babu wanda ya kalleta

Beela ko kuka takeyi tace"wallahi kaji tsoron Allah "

Ummi tace"NEESA daga yau na fita Harka ki tunda ban is a dake ba"kuka takeyi tana cewa wallahi ummi ki yarda dani ban karya alkawarin dana miki ba"

Amma ina ummi ta shige ciki tana kuka

Wajen Abba taje ta rike me kafa tace"Abba ka yarda dani"shima tureta yayi ya shige

Gun abbu taje tana kuka tama rasa me zata ce

Umma ne taje ta d'agata ta kaita ciki

Abbu ya kalli SUDAIS ciki b'acin rai yace"bamu ka tozarta ba kanka ka tozarta muje masalaci "nan duka suka wuce masalaci dama 3:49 ne"

Mummy ko maganganu tayi ta yab'awa ummi

Yan biki kowa da abinda yake fadi

Bayan an idar da sallah abbu yana da magana

Sai yace".........




Yau akeyinta gobe auren batul kome abbu zai yi oho

Team SUDAIS anty shamsiya ta gudu tace in fada muku SUDAIS ya bata haushi


Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„


Please Login or Register in order to submit comment