Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba sai yayi ta jawo,maka magana"

Abbas yace"shidai a nashi ra'ayin baya kaunar mata ai maza suna magada "

Abba dai shiru yayi dan ya lura iya gaskiyar shi yake fadi

Washe gari da safe suka je akayi komai tare da umurtan Abba da ya bude account aka bashi katin shi domin aikin daily pay ne ranan da baka zo ba za a cire kudin ka in kuma kazo late half day za a baka

Nan Abba yace"double shift zaiyi"a inda ake hada drip aka kai shi

Yana zuwa da dare da karfe tara na safe da rana kuma karfe biyu sai kuma safe

Ya dawo ya huta

Cikin kwana biyu ya saba da aikin har indiya na yaba shi domin be da San jiki ko kadan

Hakan yasa jinin shi ya hado da Mr manish

Har ya kai ga Mr manish na aike shi gidan shi dake farm centre ya kaiwa yar shi priya sako

Priya macece mai saukin kai kullum in Abba ya je sai tasa sun tsaya sunyi hira,tun baya sakewa da ita har ya fara

A hankali soyyaya ya fara shiga tsakanin su amma basu sani ba

Mr manish bai da wanan labari domin ya tsani Africans

Kwana biyu sai ya daina aiken Abba gida

Priya ko ta Shiga damuwa sosai har ta kasa hakuri ta fara biyo Abba Dana

Mr manish sai ya fara tunanin dalilin zuwan ta companing sai tace"wajen shi take zuwa domin ta gaji da zama ita kadai a gida"

Babu inda ya iya ya yarda da maganarta domin baya son b'acin ranta kasancewar ita kadai ya haifa kuma wajen haihuwarta mahaifiyarta Gauri ta bar duniya hakan yasa ma ya taho da ita Nigeria

Haka fa rayuwa ta cigaba da tafiya inda yanzu Abba ya shekara da aikin Dana gashi sun shaku da priya zuwa yanzu ya gane sonta yake kuma ba zai iya rayuwa babu ita ba

Bangaren Mr manish ko har ya sa ranan aurenta nan da wata d'aya tare da Arjun a indiya

Ranan da ya fad'a mata kwana tayi tana kuka amma gari na waye ta bi kofar baya ta bar gida

Direct inda Abba ke kwana taje domin ya kama hayar d'aki d'aya shida Abbas

Tana zuwa ta fara yi me kuka hankalinshi ya mugun tashi cikin kuka

Yace"priya what happen?"

Domin bata jin Hausa

Nan ta kwashe inda suka yi da Mr manish ta fad'a me

Shima ya shiga tashin hankali tace"me zata bashi as dowry ya aureta"

Murmushi yayi yace"in African mata basa biyan sadaki sai maza"

Tace"then marry me"

Yace"are you ready to accept Islam?"

Tace"anything for you"

Yace"let go"

Tace"where?"

Yace"mosque inda za a d'aura mana aure Dan nima bana son nayi loosing dinki"

Da sauri ta mike ta bi bayan shi yana zuwa yayi wa limamin masalaci bayani

Bayan an idar da sallah zuhr aka daura auren su a kan sadaki dubu 10 wani ne ma ya biya dama kafin aure priya ta musulunta an bata sunan mahaifiyar shi Fatima

Sai bayan auren ne ya tuna yan uwanshi me zaicewa iyayen shi

Kawai sai yace"kome miye zai faru tunda na samu priya me sauki ne"a masallacin wani alhaji ya bashi business card yace"ya zo zai bashi aiki"

godiya sanan suka bar masalanci zuwa gidan su priya a falo suka tarar da Mr manish yana kallo

priya ne ta sanar dashi an d'aura mata aure da abba,ai mikewa yayi yace"what?"

tace"yes father"

ranshi ba karamin b'aci yayi ba ya shake abba amma priya ra d'auko wuka akan in be sake ba zata kashe kanta

da sauri ya sake shi,sanan ta rusuna ta taba kafan shi inda indiya keyi tace"bless me father"

ko kallon ta beyi ba balle tasa ran zai dafa kanta yace"bless you"gajiya tayi ta mike ta ja hanun abba suka bar gidan tana kuka ita kanta tasan bata kyautawa mahaifinta ba amma zata yi ba laifin ta bane sone

bayan sun bar gidan Mr manish yayi zaman dirsha yana kuka kamar d'an yaro

yace"sai ya d'au fansa (revenge) abinda abba yayi me inda ya raba shi da yar'shi shima zai raba shi da abu mafi muhimmanci"


bayan kwana biyu ya nimi mai bincike yasa a binciko labarin abba sai dai ance me abba ba d'an nan bane babu Wanda yasa kowa nashi

su priya ko suna barin gidan agent abba ya nima aka nimo musu gida safe contain lallashin ta yayi da k'yar tayi shiru

suka ci amarcin su inda abba ya kara sonta saboda ya same ta a cikkaken budurwa

aiki abba ya samu mai kyau ana biyan shi 70k a wata nan ya fara nunawa priya so da kulawa da kuma yana aika waji Abu gida

a haka har priya ta samu ciki bayan wata tara ta haihu yar'ta mace me kama da ita sak akayi suna yariya ta ci sunan ANEESA

abba na zuwa jalingo lokaci lokaci amma bai sanan dasu yana da mata ba

a fara samun matsala ne a lokacin da alhaji ya yanke shawaran abba zai auri yar abokin shi zainab a cewar shi ai yanzu yana da aiki

abba na minna alhaji ya kira shi yace"


maman
noorul
hudah
luv u my fans
please share
[22/06, 23:44] Maman noorul huda marubuciya: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
NIDA YAYA
SUDAIS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.


DEDICATED TO BALKISU

please zaku gan nasa Abdulsudais
mistake nayi wallahi Ku min uzuri please zaku fahimta in mu kai inda zan yi bayanin wanene sudai

πŸ…Ώ1⃣1⃣&1⃣2⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Alhaji yace"duk abinda kake yi ka zo karshen wanan makon ina niman ka"

Abba yace "inshaallah"

Yana dawowa gida ya sanar da matar shi fatima

Nan tada rigiman sai ta bishi ta gan yan uwanshi

Yace"iam soory priya u can't follow me saboda har yanzu ban fad'a musu nayi aure ba,ai kin gan it will be some how a ce naje dake da yariyar shekara uku,kuma ina zuwa gida ko hiran ban taba yi da su ba"kuka take yi sosai har hankalinshi ya tashi

Lallashinta yayi har tayi shiru tare da yi mata alkawarin wanan karon zai sanan dasu sanan ya dawo ya kaita"

Tace "yayi mata alkawari "

Yace "yayi alkawari"sai dai tunanin yake yi ta ya zai sanan dasu cewa yayi aure shekara hudu da ta wuce kuma ma India tunawa da yayi da zuwa gidan shi na karshe ya d'an fara yiwa mahaifiyar shi magana a cikin wasa

Yace" umma nifa yar India zan aura"

Tace"Allah ya kiyaye India dake safi"

Yace"ai wana musulma ce"

Yace"ai komi musulcin ba indiye sai ya had'a da safi ni dai ban amince ba"sai jikin shi yayi sanyi

Shiyasa ma yayi loosing courage na fad'a musu

Ranan da zai tafi kuka tasha kamar ba zai dawo ba

A hanya shi ta zuwa har ya shiga garin taraba yayi wani mugun hasari Wanda babu wanda yayi tunani zai rayu domin motar shi a cliff ya fada da k'yar aka fito dashi inda ana fitowa dashi ko minti 5 ba a yi ba motan ya kama da wuta

Ya bugu sosai a kai ko motsi baya yi dashi da mutace ba babbanci wani ne a wajen yace"ya sanshi kanin jabir ne kiran jabir yayi ya sanar dashi halin da ake ciki

Cikin tashin hankali suka zo da jibrin

Asibiti aka kaishi sai dai fa likitoci sunyi iya kokarin su amma babu alaman zai motsa domin ya shiga coma

In takaice muku sanda abba yayi shekara d'aya cif a koma sanan ya farfado amma ya manta tunanin shi

Bangaren priya ko tasha kuka ta gaji domin noban shi bai shiga wayar ta kona mota

Har companin g da yake aiki taje ko ya kira amma suka ce mata basu da labarin shi gashi Abbas ya bar gari zuwa Lagos

A daddafe tayi shekara biyu amma babu labarin shi

Sai dai in ta gaji da kuka sai taje gidan alhajin da ya taimaka musu dan Suna shiri da matan ita ke koya mata abubuwan addini

Babu abinda hajiya keyi sai dai tayi ta bata hakuri

Mr manish na samun labarin b'atan abba ya yanke shawarar amfanin da damanshi

Nan fa ya zo har gidansu tana ganin shi ta saki kuka ta fad'a jikin shi shafa mata kai yayi tayi yana bata baki har tayi shiru

Nan fa ya fara cewa"ai ya fad'a mata ba sonta yake ba he is just trying to take advantage of her gashi da ya samu abinda yake so ya gudu ya barta"

Cikin kuka tace"ba haka kawai bane dole akwai abinda ya faru Dan tasan uzaifa ba zaiyi mata haka ba"

Shiko abba har an sallamo shi ya ji sauki amma baya tuna komai sai dai yayi ta kallon mutane

A haka rayuwa ta cigaba tun priya bata yarda da maganan babbanta har yayi nasara ta fara yarda domin shekara uku kenan babu labarin ga alhaji nan da ya basu aiki yana niman yayi lalata da ita

Hakan yasa ta yanke shawaran bin mahaifinta indiya da yar'ta yar shekara shida

A cikin kankani lokaci ta hada kayarta suka tafi

Mr manish ko dadi ya ji domin yasan ya raba yar'shi da uzaifa sauran ya raba shi da yar'ta

Ai tunda abba ya raba shi da yar shima sai ya rama

Abba ne kwance yana barci sai ya fara mafalki fatiman shi (priya)ai sai ya farka da ihu yana priya

da gudu alhaji da umma da abbu suka Shiga dakin nan suka zagaye shi ana tambayar shi wacece priya?"

shiru yayi abbu yace"ina tunanin ya dawo tunanin shi dama malamin me rubuta rubutu yace inshaallahu yau ko gobe zai tuna komai"

Abba yayi shiru yana juya maganan tuna komai sai yace"yaya me ya same ni?"

abbu yace"ai shekaran ka uku kana jinya sakamakon hasarin mota da kayi ka manta tunanin ka"

yace"what?"shekara uku?"besan sanda yace"toh ina Fatima da ANEESA?'

alhaji yace"waye su?"

yace"alhaji ka min gafara matata ce"labari komai ya basu

a zaton shi alhajin fushi zaiyi sai ya gan yayi murmushi yace"toh ina take yanzu"

cike da mamaki yace"minna"

alhaji yace"toh gobe zaku a dauko ta"

abbu yace"toh ya maganan auren shi da zainab ranan juma'a ne fa ai wanan dalilin yasa ka kira shi har ya samu hasari"

alhaji yace"babu komai za a yi da jibrin"

a waya alahaji yayi wa jibrin magana kasancewar yana B U K kano(daddy)amma da shike suna da biyayya ya amince albarka

yaje har gida ya same mahaifin zainab (mummy)yayi me bayani shima yace"ba matsala

washe gari suka zo minna amma suka samu labarin gun hajiya priya ta koma indiya wata ukun da suka wuce domin ta jira ta gaji

jikin sanyaye suka koma taraba

ranan juma'a aka daura aure zainab da jibrin Wanda ita zainab bata so ba domin Abba take so hakan yasa ta tsani Fatima

banganren Fatima kuwa bayan sun koma indiya damuwa ne fal a ranta na rashin abba yau lafiya gobe lafiya

Mr manish ko babu aikin da yake yi sai tusawa ANEESA sanan babbanta amma yariyar ta taso da kaunar abbanta

a kwana s tashi zuwa abba indiya biyu amma be gane kan garin ba ya ma rasa daga inda zai fara nimanta in ya gaji sai ya dawo

shima damuwa ce a ranshi daurewa kawai yake yi
bayan wasu shekaru a lokacin ANEESA na da shekara sha biyar har ta gama college burinta ta gan abbanta ta tambaye shi meyasa yayi abdoning dinta da ummi ta

ta taso ne cikin so da kaunar Fatima kuma tana sallah domin Fatima na kokarin koya mata abinda ta sani a musulcin sai dai al-adun India na jinin ANEESA irin su celebrating holi da tafa feet din na gaba da ita dan niman albarka

sai dai fa jinya sosai Fatima keyi na rashin abba

Mr manish da ya gan fa soyayya abba na niman kashe me ya sai kawai ya yanke shawaran yin plan sinshi na d'auka fansa ta hanya raba Fatima da ANEESA inda abba ya raba shi da yarshi

sai yace"priya zai je Nigeria niman abban amma da ANEESA zashi"

tayi farin ciki sosai harda ANEESA ma farin ciki tayi ba tare da sun San abinda ke zuciyar shi ba domin haushin Fatima yake ji dan babu inda beyi da ita ba akan ta dawo addinin Hindu taki

ANEESA dai bata jin Hausa sai English da Hindu

babu b'ata lokaci ya shigo Nigeria amma a Lagos ya tsaya wani gidan marayu ya ajiye ANEESA tana kuka amma ya tafi yana farin ciki ya d'auki fansa

wani letter ya rubuta ya kaiwa priya wai Abba ne ya bashi kuma yace baya sonta ya kara aure mai zaiyi da indiya dama dan ya samu abinda yake so ne

cikin kuka tace"toh ina ANEESA"

Mr manish yace"ai ya kwace ta wai ba zai iya barin ta gun indiya ba"

kuka sosai Fatima ta sha daga karshe rashin lafiya ya kamata

bangaren ANEESA ko


maman
noorul
hudah
luv u my fans
please share
[23/06, 00:07] Maman noorul huda marubuciya: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
NIDA YAYA
SUDAIS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.


Wanan page din naki ne MAMAN IHSAN na GORGEOUS WRITERS FORUM ke ta daban ne a zuciyata Allah ya barmu tare

πŸ…Ώ1⃣3⃣&1⃣4⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Bangaren NEESA ko yana barinta a wajen ta dinga kuka tana niman taimako amma babu wanda ya kulata sai dadi da madam bose ta ji an kawo mata kala domin wanan gidan marayu babu abinda ake a ciki in banda sanfara mata da miyagun kwayoyi an dai fake ne da sunan gidan marayu
(Allah ka kare mana marayu mu da marasa galihu domin yanzu dasu ake neman kudi)

Yawanci jama'a Lagos sun San abinda akeyi a Bose ophanaga an sha kai karanta amma gwamnatin basa d'aukan mataki saboda costomers dinta ne kuma da hanun manya a ciki

Haka ANEESA taci gaba da rayuwa bakin ciki kullum kuka bata da walwalla dan ko magana bata yi da kowa ko tayi ba a,ganewa domin turancin ta wani Irine,sai dai in lokacin sallah yayi tayi

Abinci ma sai ta gan dama take ci saboda bata iya cin abinci mu na Nigeria ba

Sai dai akwai wata yariya da baza ta wuce shekara goma sha biyu bs dake saman gadonta mai suna NABEELA ta takura ta domin NABEELA bata jin magana ko kadan kai tsokanan tsiya

Kullum in tana barci sai ta samu abu tayi ta sa mata a kunni amma NEESA bata kulata ko kadan

Wata rana tayi ta mata dariya domin sallah NEESA akwai gyra

Ita dai NABEELA tana zuwa secondary na cikin orphanage din

Wata rana NEESA na zaune tana kuka domin tunanin gida ya addabe ta sai NABEELA ta shigo da ruwa daure a farin leda ta bude bakin shi ta fara wasawa NEESA a jiki cikin b'acin rai ta fara mata masifa da halshen Hindu

Beela dai ba yaren ta ji ba sai kawai ta fara mata dariya tana cewa"kai oil oil"

Haka NEESA tayi ta fada har ta gaji ta bari dan kanta

Bayan shekara d'aya har wanan lokacin beela da NEESA basa jituwa

A yau ake shirin sayar da su NEESA zuwa wani Italy danyi karuwanci mata dai-dai shekarunta ake so a diba

Da dare aka yi layi dasu ana saka su a mota

Wanan abin na d'aurewa beela kai domin ita shekaranta biyu a orphanage din kuma kullum da dare ta gan manya sun zo sun dibe yara wasu na dawowa wasu kuma shikenan in kuma sun dawo sai sunyi jinya

A take ta gane koma menene ba abune mai kyau ba domin NABEELA akwai shagen wayau

A na kokarin saka NEESA a mota beela ta fito bayan taje tayiwa mai gadi wayau ya bar gate

Ta bude kofa sanan ta dawo ta koma d'akinsu tayi dinga ihu wai ga maciji ai da gudu kattin suka shigo ana tambayarta ina yake


Nan fa ta fara wasa da hankalin su tace"gashi yabi can sai tace gashi can

Gani tayi hankalin su ya karkata da niman maciji domin har sauran yaran aka tambaya suka ce eh sun gan maciji kato dan tuni beela ta hada baki dasu

Zamewa tayi ta fito ta nimi katon dutse ta halbe driver tuni jini ya b'alle me

Bayan mota ta bude tace kowa ya gudu amma hankalinta yafi karkata gun NEESA tana fitowa ta kama hanunta suka gudu sai cewa take oil oil

Ba karamin gudu suka yi ba ana binsu da beelah ta gan haka sai ta boye a daji gari na wayewa suka fito gari


A kofan wani babban gida suka zauna suna kuka

Har mata gidan ta fito ta d'auke su ta shigar cikin gida tare da yi musu tambayoyi

Beela ne ta bata ansa tace"mata ni sunana NABEELA Abbas ni kadai mahaifiyata ta haifa amma maihafina ya tsane ni saboda ni ya'macece yan shekara na sha uku dan ya samu d'an namiji yasa yana ta aure aure a cikin shekara uku sanda ya auri mata uku yana sakin su domin ko ciki basa yi balle su haifa me namiji

Hakan yasa ya dauko d'an yaya shi Hafiz domin tun bayan haihuwata mahaifiyata bata kara samun ciki ba

Hafiz dai maraya ne haka mami na ta amshe shi hanun biyu biyu ta bashi kulawa amma ko ganina abbana baya son yi

Komai nashi hafiz ne,wata rana naje makaranta ban dawo da wuri ba domin na tsaya wasa a hanya kasancewar a waje nike sakewa ina dawowa abbana ya rufe daki yayi ta dukana kamar wata babba dudu a lokacin shekaruna basu fi goma ba duka yayi min kamar zai hallaka ina kuka mahaifiyata na kuka
A Cewar shi karuwanci naje kamar wata babba

Yana gamawa yace"in barme gida shi baya kaunar ya'mace a gidanshi

Nima fushi nayi nace mahaifiyata mu tafi amma sai taki ta kira yar wata kawarta hajiya turai tace in babu damuwa ta kula dani tare da bata duk wani kudi nata da gulagulanta wai hajiyar ta sani a makaranta toh Ashe hajiyar mata take sayarwa shine ta kaini bose orphanage ta sayar dani a gabana a ka bata kudi mai yawa bayan ta ma mahaifiyata alkawarin a Lagos zamu zauna

Bayan na bar gidan abbana ya kara auro wata mai sun lami cikin ikon Allah lami ta haifa me ya'ya maza uku

Toh nan aka fara wulakanta mami domin da ita da bola duk d'aya

Bangaren Fatima ko jin shiru har bayan shekara d'aya tana sa zuwan Abba amma shiru yasa ta taho Nigeria ba tare da sanin mahaifinta ba

A gidan alhaji ta na minna ta sauka ta fara tambayan su sai tayi sa'a bai gari matarshi ce kawai

Kwasam washe garin zuwanta aka nuna company abbu a tv domin abbu nada companies a abuja minna da kuma kano surikin shi ya taimakame da hanun jari da Abba da sauri ta kwashe address din

Na minna taje abba a cikin office tayiwa secretary bayani wai yace"priya"ai na jin priya ya fito har yana tuntube yana zuwa ya tsaya yana kallonta yana hawaye shima hawayen yake a tare suka rungume juna ya shigar da ita office

Baki suka hada wajen cewa in ANEESA?

Yace"me kike nufi"

Tace"ba banana ya kawo maka ANEESA ba"
Yace"ban fahimta ba"labarin inda suka yi da abbanta ta bashi tare da nuna me wasikan da ya bata

Abba yace"ni be kawota ba kuma karya yake da yace nayi aure domin babu inda ba ayi dani ba inyi aure naki ina jiran ki so biyu ina zuwa India amma basan daga inda zan fara ba"labarin hasarin da ya faru dashi ya bata

Kuka ta fashe dashi yace"karki damu gobe zamul indiya ya fada mana inda ya kai min ya"

Yana barin office ya kaita gidan su domin sun dawo minna da zama sanadiyar kisan gilla da akayiwa ummasu yan ta'ada shiyasa suka bar taraba

Kowa yayi maraba da zuwan Fatima banda zainab domin ta tsani priya tans ganin saboda dalilinta ne Abba bai aureta ba yanzu yaranta uku duk mata amma tana rukon yar yayanta BATULA

khadija (umma) kamar ta goya fatima sai nan nan da ita takeyi

Abbu yace"gaskiya ya kamata su je indiya su tambaye Mr manish inda ya kai NEESA

A wanan lokaci SUDAIS Nada shekara 26
Hafiz ko shekara 23 kuma abokai ne

Indiya

Suna zuwa suka sa Mr manish gaba sai ya fada musu inda ya kai ANEESA

Dariya yayi yace"fansa ya d'auka ta hanya kaita gidan marayu a Nigeria"

Abba baisan sanda ya shake shi ba ai sai Fatima ta fara kuka tana dukan Abba tana cewa don't forget he is my father "

Sake shi Abba yayi yace"sorry I lost my cool"

Haka dai suka Bari indiya cike da farin ciki bayan Fatima tayiwa mahaifinta alkawarin bazai sake ganin ta ba
A Nigeria babu inda basu nime ANEESA ba amma babu labari sai kawai suka cigaba da rokon Allah ya bayyana musu it's

Suka cigaba da rayuwar aurensu India abbu yayi wa fatima komai umma kuma na koya mata abubuwa addinin da al'adar

Mummy ko gaba take da kowa dan taso ne su hada kai su kori Fatima
Amma umma bata aminta ba

Su NEESA ko hajiyar nan ta amshe su hannu biyu biyu domin bata taba haihuwa ba tana basu kulawa a ss1 akayiwa beela registration na waec ta rubu ta taci

nan fa ta tambaye su mai suke son karantawa

NEESA tace"law"
beela tace"Dr "

hajiya Rabi tana da kudi sai dai bata da kowa domin familyn ta sunyi hasarin jirgin sama babu wanda ya rayu kuma yanzu tana da breast cancer
shiyasa ta taimaki su NEESA dan tasan bazata rayu ba
amma su basu San tana da cutar ba

a kwana a tashi NEESA nada shekara 24 ta zama barrister ammi na matukan ji dasu ga ciwonta na sanani ba Inda bata yi dasu ba akan su bari a nimi iyayen su amma suka ki wai sai sun zama abin alfari babu ma kamar beela da take son nunawa abbanta cewa mata ma ya'ya ne wanda a yanzu duk yayan shi maza babu mai hankali ko d'aya daga mai shaye shaye sai mai sata

a shekara ashirin da biyu beelah ta gama makaranta ta zama cikeken Dr da yike an mata sallake duk a Lagos suka yi karatu

beela ko ta koyawa NEESA abubuwa sosai da Hausa da kuma addinin domin ita tun tan shekara 10ta sauke yariyar akwai ilimi kuma ammi su na kokarin koya musu abubuwa

NEESA ko bata da aiki sai kallon hoton iyaye ta

rana d'aya beela ta tashi da zancen zuwa gida dan ganin maminta minna taje babu wahala ta gane gidan su domin tasa an mata bincike

tana zuwa ta tarar da maminta ta lalace tayi baki saboda wahala

ranta ya mugun b'aci tana ce sai dai mami ta rabu da abbanta Hafiz ne kadai mai kwantarwa mami hankali bayan b'ata beela

shima tunda Abba ya samu yara maza ya daina kulashi abbu ke d'aukan nauyin shi

beela tace"mami kotu zani in raba auren ki da Abba

mami tace".....




[23/06, 13:46] Maman noorul huda marubuciya: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
NIDA YAYA
SUDAIS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟


🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers we are the best among the rest.


πŸ…Ώ1⃣5⃣&1⃣6⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Mami tace"ke ko wacce irin ya'ce mai son raba auren iyayen ta ai ko saboda ke zan zauna ko,nagode tunda kina lafiya"

Beela tace"nifa mami dake zan tafi"suna cikin hira sai ga Abba ya shigo yana ganin nabbela ya karaso ya tada siya sai ta bar me gida,sanda ta gama karuwancinta shekara da shekaru zata dawo me gida

Beela tace"ni wajen mahaifiyata na zo ba kai ba kuma da kake kira na karuwa ai kaine babana kuma dole a kira ka da baban karuwa"

Magana yake NABEELA na bashi amsa har mami ta wanka mata mari

Tace"da baban ki kike sainsa NABEELA?"

Abba yace"kyaleta ta gaya mun ai ke kika d'aure mata gindi sha-shasha Wanda bata da gindi haihuwar yara maza sai cin abinci"

NABEELA tace"ai abinda ka bata shi zata Haifa maka"

Ganin ba zata yi shiru ba yasa mami janta zuwa gun umma domin makota ne

(Karku manta Abbas da Abba abokai ne)

A falo suka tarar da abbu cikin kuka mami ta me bayani

Nasiha yayi wa NABEELA umma ma ta tofa albarkacin bakinta

Ummi da shigowarta kenan ta tsaya tambayar abinda ya faru

Shiru NABEELA tayi tana kallonta nan take ta gane ummi NEESA ne domin suna kama kuma tasha ganin hoton su a hanun NEESA

Shigowar Abba ya kara tabbatar da zarginta

Amma sai bata ce komai ba

Abbu yace"je ciki ki huta a baki abinci"

Beela na barin wurin kofar bata tabi ta bar gidan a hotel ta kwana washe gari ta tafi Lagos cike da haushi mamin ta

Domin gani take mami ta fison Abba akanta

Hamza ne zauna yana Facebook kawai zai ya gan hoton NEESA a people u may know

Yace"yariyar nan tayi kama da ummi"sunan

Please Login or Register in order to submit comment