Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da abbaku,ki rike mutuncin kanki domin hausawa babu abinda yafi daraja a gun ya'mace kamar ta kai budurcinta gidan miji ni nagan ribanshi shiyasa abbanku ki sona,in kika min haka kin gama min komai a rayuwata,karki bari a min dariya ya'ta domin ranan da zan samu labarin kiyi wasa da Martaban ki zan iya samun ciwon zuciya domin ina tabbatar miki zaman gidan nan sai ya gagareni"mikewa tayi tace"na tafi kome kike so kimin magana

Tana fita NEESA tace"I love u mom nayi miki alkawari domin da zaki San koni wanene da kin rungume ni dan farin ciki amma lokaci ya kusa"

Beela ne ta shigo ta gan kafar har ya kumbura tace"ya haka ta faru?"

NEESA tace"......


Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
NIDA YAYA
SUDAIS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

πŸ…Ώ3⃣9⃣&4⃣0⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

NEESA tace"ki bari kawai YAYA SUDAIS da hafiz suka samin mai na zame"

Beela tace"what?" a fusace ta kama hanyar kofa tace"yanzu zanje in ci me mutunci wanan wani irin mugunta ne da ganganci inda kin karye fa me zaice"

NEESA tace"calm down zo ki zauna"

Dawowa tayi ta zauna bakin gado NEESA tace"ai in kika je yanzu kin b'ata plan din ba komai yasa yayi haka ba sai dan kar inje race,amma besan ni a rayuwata bana loosing challenge ba"

Beela tace"toh yanzu ya kike so ayi ne?"

Tace"ke zaki je race din"

Beela tace"ni kuma gaskiya bazan je ba"

NEESA tace"please dear ko so kike in fadi gasan"

Beela tace"ni kin San bason tuka mashin nike ba dama motane"

NEESA da beela suna da babancin ra'ayi domin NEESA ta fi son mashin fiye da mota komai sadan shi,itakuma beelah tafi son mota ko mashin bata son tukawa

(Shiyasa tun farko nace muku akwai connection sakanin NEESA da beela amma muje zuwa)

NEESA tace" yi hakuri ke kadai zaki iya tureshi domin na lura ya iya mashin sai dai yana da tsoro ne shiyasa na yi wining dinshi,kuma ai kin fini iya mashin tun a indiya ke ce kike wining please beela"

Beela tace"toh,shi ya dauka zai iya wining din mu ne a bike race mu da muka koyi mashin a India tun kan mu dawo nigeria sanda fa muka yi wata shida dan mu koya kin tuna har race muke hadawa da su arjun kuma muke wining"

NEESA tace"har nayi missing Arjun,da abbu zai yarda da na aureshi wallahi"

Hararanta beela tayi tace"karki wahalal da kanki domin inshaallahu Nigerian zaki aura"

Tace"me zanyi da Nigerian guys su da basu iya soyyaya ba,ko kin manta abubakar da muka hadu a Lagos ya nuna yana sona da aure ashe dan iska ne har clubs yake dashi a different state yana b'ata yaran mutane "

Beela tace"hmmm na tuna amma ai ba dukan mazan Nigeria ke haka ba kuma ai wancan tantiri ne kin San fa har DON ake kiran shi"

(Maimaita sunan nayi kamar na taba jin shi DON eh na tuna saurayin batula ne)

NEESA tace"beela na bar SUDAIS a hanun ki so nike ki cime mutunci ya ji abinda nike ji na sati d'aya"

Beela tace"hmmm kisan bani da hakuri kuma mugunta ne dani kuma kike son in rama miki?"

NEESA tace"ai shiyasa nace ki rama min karki raga me ko kadan"

Dariya beela tayi tace"zaki ji kukan shi kwana nan kamar jariri"


4:pm na bugawa SUDAIS ya shirya cikin 3quater sport wando da rigar shi armless a gaban madubi ya tsaya yana gyra sumar kanshi


SUDAIS handsome ne sosai fari ne tass shiyasa mutane ke d'auka yaron ummi ne yana da tsayi yana da jiki amma ba sosai ba

Ga sajen shi abin ban sha'awa in ka ganshi sai ka d'au balarabe ne domin be mayi kama da Africans ba kyau fulanin asali yake dashi

Yana gamawa ya d'auki key din mota ya fita

Yana fitowa ya kira Hafiz ya a waya

Yace"ka samu mashin din"

Hafiz yace"eh ina ma stadium ina jiranka antaru,harda DON daka taba wining a gasan da musa shima ka taba wining din shi sai wani emeka da chris,na shida basan ko waye bane"

Yace"koma waye nine winner "

Hafiz amma sunce duk wanda yayi fadi za a me wanan looser!looser!!looser!!!"

SUDAIS yace"lallai wanda ya fadi zai kwashi kunya,gani nan zuwa"


Bangaren beela ma shiryawa tayi cikin 3quarter jeans da riga armless ta parker sumarta a keya

Ta kalli NEESA dake kwance tace"na shirya"

NEESA tace"sai kin dawo kiyi make sure kin wining din shi"

Tace"trust me"

Flat black shoe ta jawo ta d'auki key din mashin ta wuce

Minna central stadium


Mutane ne cike da samari da yan mata zaune suna jira a fara race din


Su ko Wanda zasu yi race sun shirya a jiran mutum d'aya

4:20 beela ta shigo cikin stadium din a hankali take tuki har ta karaso

Hafiz na ganinta ya kalli SUDAIS

Yace"muyi back out a wasan nan tun da wuri"

SUDAIS yace"babu abinda ta iya kai baka gan inda take tuki bane?"

Yace"ni ina gudun abin kunya"

Beela na sauka ta karasa gabansu tayi kamar bata San su ba


D'aya daga cikin commentator yace"toh a fara wasan"

Beela tace"ita bazata mass race ba sai dai suyi duk wanda ya ci dashi zata yi"

Mai organizing race din yace"zata biya dubu Dari"

Tace"ta amince zata ninkan kudin a take ta basu bandir din dubu guda biyu"

SUDAIS sai kallonta yake yana tunanin ina suke samun kudi

Don ne ya karaso inda take ya mika mata hannu hada rai tayi

Yace"ina ANEESA?"

Tace"tana nan lafiya"

Yace"please ki fada min inda take"

Tace"stay away from us"

Yace"never duk inda take sai na nimo ta na aure ta"

Tace"kayi karya domin NEESA ta fi karfin ka"

Yace"kema kinsan mace bata fin karfin namiji"

Dariya beela tayi tace"we shall see"

Shiko SUDAIS kallonsu yake daga Nisa a ranshi yace"lallai yaran nan sunyi nisa tunda har suke harka da DON"

Ba tare da b'ata lokaci ba aka fara su hudu domin don yace"da winner zaiyi"

SUDAIS ne yayi winning dan haka don yace"dashi zaiyi "

Aiko suna yi SUDAIS yayi wining akayiwa DON waka looser

Ba karamin haushi DON ya ji ba domin so biyu kenan SUDAIS na wining din shi

Kuma yayi alkawarin wanan shine last time da SUDAIS zai kara wining din shi akan wani abu dama yana jin haushin shi na kiran batul da yake yi in suna hutawa ya fuskanci son batul yake domin yana ganin text dinshi a wayarta amma taki ta fada me gaskiya

Bayan sun gama aka kira beela

Nan fa aka fara race beela tuki take cikin kwarewa hartafi NEESA ma Hafiz ko na zaune sai hadiye miyau bakin ciki yakeyi domin yasan SUDAIS ba zaiyi wining beela ba

Aiko haka ta faru domin beela sanda ta iso da minti 30 kafin SUDAIS ya iso mutane sai ihun kiran sunanta ake

Shiko wanka looser ake me

Rai b'ace ya bar wurin itama beela barin wurin tayi sai dai abinda bata sani ba DON na binta a bays


Wanene Abubakar DON?"


Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
NIDA YAYA
SUDAIS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous, interllingent,and expert writers,we are the best among the rest

Dedicated to my FANS

πŸ…Ώ4⃣1⃣&4⃣2⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Abubakar Ibrahim a k a DON shine cikeken sunan d'an ne ga wata tantiriya karuwa Binta amma anfi saninta da LADY B Wanda tayi kaurin suna a karuwanci tana zuwa kasashe daban-daban shiyasa ma ba a San mahaifin shi ma'ana shage me

Don ya girma ne a porthort tare da mahaifiyarshi kuma a gaban idon shi take komai shiyasa shima ya taso babu tarbiya bayan ya gama secondary ya tafi university of port-hacort nan fa ya kafa kungiya the kapons kuma shine oga cultist din shi babu ruwan shi da karatu nan ya dinga tafka b'arna har ya gai ka suna zuwa fashi

Shakara biyu da ya wuce mahaifiyar shi ta rasu sakamanko cutar kanjamau AIDS nan ya tattara dukiyarta ya dawo arewa ya bude hotels inda yake shashanshi da kuma harkan sayar da miyagun kwayoyi yanzu baya zuwa fashi sai dai ya tura yaran shi

Shekaru biyu da ya wuce yaje Lagos dan kaiwa abokin kasuwancin shi hudar iblis sai ya hadu da NEESA da beela a restaurant babu b'ata lokaci yaje ya nuna mata yana sonta

Har suka yi exchanging number domin yaje mata ne a matsayi mutumin kirki

A lokacin da bash yaron NEESA ya zo Niger siyar fili kuma lokacin NEESA na shari'a da bose orphanage

Bash yaje hottest hotel yayi hayar d'aki sai kawai sai ya gan DON yana shakatawa dama ya taba ganin shi da NEESA

Ai a take ya fara bincike ta hanyar bawa wata karuwa kudi ai ta zaiyana mashi komai yana recording

Yana komawa Lagos ya zaiyanawa NEESA komai yace"in baki yarda ba bari inyi miki playing record din"

Tace"bash na yards da kai baza kamun karya ba"domin NEESA ta yarda da bash da jamila sun hadu ne a jami'a lokacin da take karanta law kafin su tafi kasan waje bash bashi da kowa domin ya rasa yan uwanshi a Maiduguri lokacin boko haram

Sai yayi aiki sosai yake samun kudin school fees da abinci hakan yasa ta d'auki nauyin shi da jamila

Jamila marainiya ce da iyayen ta suka rasu a hasarin mota amma kawunta sai ya gugu da dukiyar ta

Bash zai iya bawa NEESA rayuwar shi

Don ya hadu da batul ne ta sanadiyar karuwan hotel blessing din shi da take zuwa C O E

Blessing kawar batul ce sosai blessing babbar yariya ce dan da mota take zuwa makaranta lectures ma na tsoronta hakan yasa batul ke makale mata domin batul akwai kwadayi da son girma ta manta ita ba kowa bane a kauye taraba aka kawo dan tayi karatu kauyen ma ruga

A hankali blessing ta fara Jan ra'ayin batul har ta fara kaita hottest hotel inda ya zama joint din karuwan gari

Nan Don ya ganta ya nuna sha'awarshi akanta da farko taki yarda amma blessing tace"ashe ke ba ajina bane baki waye ba"

Haka tayi ta Jan ra'ayin batul har tayi nasara

Nan fa DON ke abinda ya gan dama da ita idan yanzu ta fishi kwarewa domin in zaka bude wayar batul toh blue film ne cike nan take gani style din kwanciya daban-daban tana yiwa DON shiyasa ya fi sonta cikin yan matan dayake harka dasu

Domin tana bari yayi inda yake so da ita

Sai dai baya bari kowa ya rabe ta domin zai ita kisa saboda ita gefe d'aya kuma ga soyyayar NEESA da ya me mugun kamu

Don zai iya yin komai akan abinda yake so

sai dai fa duk abinda batul keyi babu wanda ya sani a gida harda mummy

Domin burin mummy batul ta auri SUDAI su kwace gida su kuma kore ummi
So take batul ta mallake SUDAIS

Umma kuma haka kawai taji bata kaunar batul amma SUDAIS yaki ji ya nace sai batul

Abbu yace a barshi kawai

Wanan kenan

Cigaban labari

Toh fans ga DON ga SUDAIS

Ga kuma NEESA ga batul ko mai zai faru?"


Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
NIDA YAYA
SUDAIS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers we are the best among the rest.

DEDICATED TO ANTY SHAMSIYA

πŸ…Ώ4⃣3⃣&4⃣4⃣

Bismillahi Rahmanir Rahim

Suna kaiwa gida a garage Hafiz ya paka mota

Sai suka zauna a garden Hafiz yace"da kabi shawara na tun farko da haka bata faru ba yanzu tayaya zamu shiga cikin gari?ga yaran nan sun samu gaba ni nasan yanzu bamu da sauran kima a idonsu domin raini ya riga ya shiga tsakanin mu dasu tunda so biyu suna wining dinmu"

SUDAIS yace"rabu da yan duniya sun gama yawon duniya ba dole su iya race ba,ji fa har da DON suke harka da aika San sunyi nisa domin kowa yasan DON dan iska ne"

Hafiz yace"wanan ba damuwan ka bane wai ma meyasa ka damu dasu ne,ni tunani nike kome zai biyo bayan tarkaden da kayi NEESA domin nasan Sai sun rama,muyi give kawai"

SUDAIS yace"ai wallahi basu isa in yi give up ba ina dai-dai dasu wallahi Sai na rama kome suka min"

Kafin Hafiz yayi magana beela ta shigo a garden ta hango su ai nan taje ta paka mashin a gefen su ta sauko tace"ya dai looser of the years"zuwa tayi karma zata zauna a kafan su ai Sai suka masa ta zauna a tsakiyar su

Tace"yauwa ashe kun gane"kallon SUDAIS tayi tace"ya kake ji yanzu da ka zama looser, me kake tunani wai dan ka sa NEESA tayi tarkade zai sa tayi loosing challenge,never domin NEESA bata taba loosing ba kuma baza ta fara yanzu ba kasan saboda me?"addu'ar dinbin jama'a na tasiri akanta"waya ta ciro tayi dialling noban NEESA

Da sauri ta d'aga dan dama jira take beela ta kirata

Tana d'agawa beela tace"kin yi wining "

NEESA tace"I know domin nasan baza ki bari inyi loosing ba"

Beela tace"looser na jinki"dariyar shakeyanci tayi tace"waya na speaker kenan?"

Beela tace"eh"

NEESA tace"good looser kana jina?karka d'au dan kasa nayi targade kayi zata ko kayi wining a kwancen nan da nake Sai na kusan saka hauka domin Sai ka ji zafi fiye da inda naji"

Beela tace"besty ai bashi kadai ba har da d'ayan"zaro ido Hafiz yayi a ranshi yace"na shiga uku"

NEESA tace"ka zauna da shiri domin yanzu zaka San wanene NEESA "

SUDAIS yace"ni kuma ina jiran ki"

NEESA tace"good I like your courage beela shafa min kanshi bye"

Tana kashe wayar ta mike tace"zan barka ka huta yau dan kar abin ya maka yawa amma daga gobe babu hutu"tana barin wurin Hafiz yace"ka gan abinda ka jawo mana ko?ni dai na wuce gobe zamu hadu

Yana shiga gida ya tarar da mami tayi tagumi

Yace"mami lafiya?"

Tace"kalau zazzabi ne ke niman kamani jiki na rawa yaje daki ya kawo mata magani da ruwa yace"mami na fad'a miki ki daina wasa da lafiyar ki wallahi bazan yafewa kaina ba in wani abu ya same ki ba domin saboda ke na zama abinda na zama yau"

Murmushi tayi ta shafa kumatun shi tace"karka damu da sauki ai ,ya NABEELA take?"

Yace"kalau take mami mai zai hana ki bi shawarar beela a raba auren nan da bashi da amfani"

Mami tace"d'an nan ko saboda kai da beela na hakura in zauna ko"

Kafin Hafiz ya bata amsa yaron lami ya shigo kamar wanda zai fad'a Kansu domin ya sha Wiwi ya shige daki

Mami tace"Allah ya shirya"ai Sai lami ta fito ta fara bala'i wai dan bakin ciki ana matsawa yaranta dan kawai mutum bai da gidin haihuwa maza

Hafiz ko taimakawa mami yayi suka shige ciki suka barta tana masifar bazanta

Bangaren NEESA ko dai-dai zata shiga falo suka yi karo da farida kanwar SUDAIS ta fito a guje tana dariya Aisha yar aiki na binta da kunnama a sinks

Beela tace "miye haka ne wai?"

Farida tace"anty walla A'i ne ke bina da kunnama zata saka min a Riga"

Beela tace"kunnama bata tsoro ne?"

A'i tace"ai na danne bindin shi da sinsiya ba zai yi min komai ba"

Beela tace"ke haka Allah ya yi ki baki tsoron kunnama kenan toh kuyi ta guje gujen Ku"

Har ta wuce ko me ta tuna sai kuma ta juyo tace"A'i boyo ni da kunnaman nan"

Tace"toh"

Farida tace"me zaki yi dashi?"

Tace"ni sa'ar ki ce da zaki tambaye ni"

Farida ta tabe baki tace"yi hakuri anty na"

A'i bin beela ta yi a zaune suka tarar da beela ta idar da sallah ta Mike kafa d'aya inda ba zaiyi mata zafi ba"

NEESA tace"har kin idar ina ta sauri in zo in taimaka miki"

NEESA tace"karki damu umma da farida suka taimaka min nayi zaune

Tace"OK"hanun A'i NEESA ta gani tace"meya haka kuma da kunnama"

Beela ta kashe mata ido,ai sai suka hade baki waken cewa oil-oil"

Beela tace"A'i aiki nike son ki min"

A'i tace"wani iri"

Beela tace"so nike ki sawa YAYA SUDAIS kunnama a gado da dare"

A'i tace"miye ribata"

Beela tace"fadi abinda kike so"

Tace"so nike ki yi wa abbu magana yana sani makaranta"

NEESA tace"karki damu wani aji kika tsaya"

Tace"nayi wa'ec jami'a nike son zuwa,kuma ina jin kunya inda zanyi wa abbu magana domin ya gama min komai na rayuwa"

NEESA tace"karki damu zaki je makaranta nidai buri na ki yi aiki da kyau"

A'i tace"karki damu je kyauye mu ki tambaya za a baki labarina"

Beela tace"dan bamu toh labarin"

A'i tayi dariya tace"ni sunana Aisha abdullahi mahaifiyata ta rasu tun ina da shekara biyar sai mahaifi na ya auro wata kande bazawara ce da yara uku wai dan in samu kulawa bayan shekara biyu kande ta mallake shi nan na fara fuskanta kunci rayuwa domin sai abinda take so Abba na keyi

Tun ina hakuri harya kai ga na fara mayar da martani domin duk kauyen mu bana tsoron kowa a dadafe nayi secondary school na gama

Shine inna kande ta hada aurena da wani azalumi wanda yayi shekarun babana da mata uku

Shiyasa na gudo birni har na hadu da wata mata na ta had'a ni da umma

Beela tace"karki damu sai NEESABEELA sun canja rayuwarki"

Tace"nagode yanzu miye abinyi domin ina ganin su lokacin da suka zuba mai a kofar d'akin ki"

Beela tace"Abu na farko shine ki mu samu key dinshi"

Tace"yanzu kuwa ina zuwa"

NEESA tace"




Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
NIDA YAYA
SUDAIS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers, we are the best among the rest.

DEDICATED to TEAM NEESA sharhin Ku na birgeni

πŸ…Ώ4⃣7⃣&4⃣8⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Umma tace"miye haka?"

Wajen ummi yaje yace"ummi ki taimaka min maciji ya sare ni"

Abbu yace"a ina?"

Yace"a dakina"

Ummi tace"dai-dai ina"

Yace"a baya"

Daddy yace"bana tunanin maciji ne amma cire rigan in shine za a gan hakoran shi"

Yana cire rigan shi sai ga kunama ya fado ashe makalewa yayi

Abbu yayi tsaki yace"saboda kunnama kike wanan ihun kamar mace"

Yace"wallahi in baku taimaka min ba zan iya mutuwa"

Ummi tace"baza mutu ba son inshaallah bari in nimo bakin dutse"

Beela dai gefe ta samu ta zauna tana mamakin rakin SUDAIS

NEESA ko dama idonta biyu kome ke faruwa tana ji sai dai kawai tayi dariya

Can kuma ta dafe zuciyarta tace"ya nike ji kamar wani dake kusa dani na cikin tashin hankali iam feeling restless

Duk wani taimako an yiwa SUDAIS amma yaki yin shiru

Umma tace"ni dai na gaji ma hadu da safe"

Abbu yace"Allah ya kara lafiya"

Daddy ma shigewa yayi da mummy dake tayiwa ummi kallon bazan ko kulata bata yi ba

Ummi ne ta zauna tana me sannu itama beela komawa daki tayi tana me dariya

Tana zuwa ta fara bama NEESA labari suna dariya sai dai fa NEESA kasan zuciyarta tana jin ba dadi

Beela kwanciya tayi ta fara barci hankali kwance

NEESA ko tana zaune karshe zazzabi mai zafi ya rufeta

SUDAIS ko kwanciya yayi yana zubawa ummi shagwab'a tana biye me

Itama can anjima Abba ya zo ya d'auke matarshi suka barshi shi kadai kwance

Can anjima sai wani tunani ya fado me yace"kowa ya fito amma banda batul"

Wani zuciya yace"kila tayi barcine kuma ai tace ma zata kwanta dan ta tashi sallah dare"

Murmushi yayi yana jin tsonta har zuciyarshi

Yace"inshaallah gobe zanwa abbu maganar auren mu"

Abinda SUDAIS be sani ba tun misalin karfe 10 da suka rabu da batul ta bar gida dan zasu party

Mummy taje kofar d'akin ta taji ta a rufe sai ta d'auka barci tayi

Sai ta leka yaranta a wani d'aki duk sunyi barci

(Iyaye muna da sakaci sai ka gan uwa ta kwanta barci hankali kwance ba tare da tasan inda yaranta suke ba

Ya kamata mu gyara domin wanda yake da yara mata baya barci sai randa ya aurar dasu domin kana tarbiya ne shedainu kawaye na warwarewa a waje ya kamata mu kula muyi ta duba yaran mu ciki dare dan tabbatar da sun kwana a gida koda kuwa yara maza ne,domin shi uba in ya kwanta bashi da lokacin duba su,allah ya kare ya'yan mu da bin kawayen banza,kuma ki yi ta musu addu'a cikin dare)

Cikin NEESA da SUDAIS babu Wanda ya runtsa

Beela ko karfe 2:am ta tashi ta gan NEESA zaune

Tace"ya dai"

NEESA tace"zazzabi ke damuna"

Tasan NEESA bata son allura dan haka first aid box ta d'auko ta bata magani tasha tace"ki kwanta ki huta"

Ita kuma taje ta dauro alwala ta tada sallah

Sai 4:am ta mike bayan ta gama mika bukatunta wajen ubangiji

Hijabi tasa ta fito lokacin har barci ya d'auke SUDAIS a general falo besan lokaci da ta fita ba

Diba ruwa tayi tana kaiwa waje tana cikin zuba na karshe ta gan mota ya tsaya

A ranta tace"wanan waye ne yake zuwa cikin dare kullum yau sai na gan Wanda ke zuwa"

Zama tayi bakin masalaci inda batul ke Allah -Allah ta shige dan ta fito kafin a fara kiran sallah a fito

Jin sunki fitowa yasa beela ganewa jiranta suke ta shige dan haka sai ta mike ta shige ta boye bayan dakin mai gadi

Ai ko sai ga batul ta shigo tana cin cigum

Ba karamin mamaki beela ta ji ba tace"me hakan ke nufi kenan kuma ina take zuwa?"

A gaban idonta batul ta shige gida

A falo ta hango SUDAIS ai sai ta dafe kirji shiko jin kara bude kofa yasa shi bude ido

Yace"batul daga ina?"

Kafin ta bashi amsa beela ta shigo ko kula su bata yi ba ta shige daki

Hakan ya tabbatarwa batul beela ta ganta amma da shike yar duniya ce sai tace"daga waje ruwa na gama dibawa a masalaci,amma kai me kake yi a nan?"

Yace"kunnama ya halbe ni"

Tace"yaushe?"

Yace"da dare baki ji hayaniya na ba?"

Tace"wallahi ban ji ba kasan nayi barci da wuri sannu"

Yace"yauwa wancan kuma daga ina ta fito"

Batul tace"ai ni kullum in na fito diba ruwa sai na gan dawowar su an sauke su a mota ko ina suke zuwa oho yau dai ita kadai ce"

Yace"zargi na ya tabbata yaran nan yan iskane"

Tace"haba babu kyau zargi fa"

Yace"shiyasa nike son ki je ki kwanta gobe zamu gan juna"

Tana barin wurin ta sauke ajiyar zuciya tace "kafin Ku tona min asiti na gama b'ata Ku

Beela na shigan daki ta tarar da NEESA kwance amma ba barci take ba

Tace" besty kin San me na gani yau?"

NEESA tace"ah'ah"labari komai ta bata ta kare da cewa ashe yariyar nan yar iska ce iskanci take zuwa

NEESA tace "beela bana son zargi ki mata uziri kila wani abune ya fitar da ita"

Beela tace"wani abune zai fitar da ita cikin dare kuma kullum"

NEESA tace"beela ki daina yiwa mutum mumunan zato babu kyau in ma wani abune kika gan tana yi da bai dace ba kiyi mata addu'a shiriya haka yafi domin yana da kyau mutum ya zama mai sarkake zuciyar shi a kowani lokaci"

Beela tace"nagode besty kuma nagode"

Was he gari da sassafe beela ta shi taje gida rike da man gyda a hanun a dai-dai kofar dakin Hafiz ta zuba ta juyo a hanya ta hadu da abbanta

Yace"....




Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
NIDA YAYA
SUDAIS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

Dedicated to NEW HAUSA WRITERS

πŸ…Ώ4⃣9⃣&5⃣0⃣

Bismilahir Rahmanir Rahim

Abba yace"ke me kike yi a nan gidan?"

Cike da rashin kunya ba tare da ta kalleshi ba tace"wurin mami na na zo ko zaka raba uwa da yar'ta"

Yace"ke ni kikewa rashin kunya?"

Sai a sanan ta kalleshi ai Sai ta hango wani katon abu a wuyar

A razane tace"Abba meye haka a wuyar ka?"ta kai hannu zata taba

Tureta yayi yace"ina ruwanki"

Tace"you are wright babu ruwana"sanan tayi tafiyarta zuwa sashin Mani

Ba karamin dadi mami taji ba ta kawo mata wani abinci ko mai bai ishe shi ba

Kallon abincin tayi Sai kawai ta ji kwalla ya ciki mata ido a ranta tace"kama na a ce mami na na cin irin wanan abin cin dole ne in nimi mafita in taimakawa mami"

A haka ta fara ci tana jin wani yanayi domin ta dade da taci girki mamin ta

Ihu suka ji daga part din Hafiz da gudu mami ta fita beela ta bi bayanta

Hafiz da fitowar shi kenan zai fita ya zame hanun shi ya bugi dakalin dakalin kofar d'akin shi ga kwakwason shi zafi

Wani azaba yake ji kallon kasa yayi ya gan mai ai nan ya tabbatar aikin su NEESA ne

Beela tace"sannu yaya bari mu taimaka ma"

Taimaka me sukayi zuwa d'aki
Duk inda Hafiz ya so ya daure abin ya gagara

Mami ne ta kira mai dubawa ya duba hanun yace"ya samu karaya ne"domin dama ya taba samun targade a hanun

Ba tare da b'ata lokaci ba akayi me dauri sanda beela

Please Login or Register in order to submit comment