Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

๏ปฟ๏ปฟ๏ปฟ๏ปฟAn dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__
TAWA CE!!! ๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
1โƒฃ
Wata yar yarinya nagani karkashin mota ga dukkan alamun gyaran motan takeyi,, sai wani dattijo wanda akalla zaiyi shekera 59 yana tsaye yana mika mata sufanu.

Dattijon ne yace yar baba โ€ kifa daure notin da kyauโ€, tana karkashin motan tace to baba na. Fitowa tayi daga karkashin motan saida na tsorata danaga kyau yarinyar dukda da bakin mai a fuskan nata tana sanye cikin biri da wando sai wata bakar riga a ciki da alamu kayan aikin tane saboda duk bakin mai ajiki.

Murmushi tayima baban nata tace babana, nadaure notin amma exhaus din sai an sake sabo,saboda yana fitar da hayaki dayawa. yay murmushi yace yar baba kenan, yanzu harkin kware, oya muje ki dauraye jikinki kisa kaya kitafi islamiyya, inkika dawo sai mukoma gida ko??to tace, baban nata yakama hanunta suka shiga cikin wani dan shago na langa langa haka.

Biri da wando wanda muyan ph ke kiranshi da โ€œdongareโ€ dake jikinta nayin kanikancin tacire, ta dauko yar kodaddiyar atampanta riga da zani tasa ta daura hijab abunta tace babana na shirya, Kallonta yayi yace to Allah kiyaye, baruwanki da kawaye, banda magana da kowa ahanya kinajina ko??tace eh yace to wuce kitafiโ€ฆ

Tsayawa tayi ta turo baki, baban nata yace wuce kitafi mana, kuka tafarayi baba baka bani kudin break bafa, yace yar baba bakijin magana, kinsanfa kudin waec dinki nake tarawa saikin cinye kudin, kuka takara saki wlh baba saika bani ni bazan yardaba,tadinga bubbuga kafa a kasa, girgiza kai yayi ya dauko wata kodaddiyar naira goma yabata oya wuce kitafi ayi karatu dakyau.

Nagode babana tafada tana share hawayen idonta tazira takalmin ta dan madina tatafi.
Mikewa baban nata yayi yace Allah dai yasa mai motar nan yazo yabada kudin gyaran motanan, koma samu nacin abincin dare yau, ya girgiza kai yakoma wurin motan yaciga da aiki.
Maman shakur ๐Ÿ˜˜
[02/11 7:30 PM] Aishat muhโ€™d: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ TAWA CE!!! ๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
2โƒฃ
Wuraren karfe shida ta taso daga islamiyyan, direct shagon kanikancinsu tataho, tasamu baban nata yana hahhada kaya, da gudu takarasa ta rungume baban oyoyo babana, dariya yayi yar baba andawo tace eh baba na, me aka koyo?? Tace yau mungama suratu tauba, munyi hadith, da fiqhu.

Baba yace masha Allah, yace to kicigaba da karatu ki dage in sha Allah wataran zaki zama wani Abu a duniyan nan ki taimaki musulmai kinji ko, ki kasance mai yawan taimako, inhar kikaga mutane na bukatan abu inzaki iya taimaka musu ki taimaka musu. mekika siya da naira goman, taciro yar ragowan aya jikakka a leda tace babana aya nasiya narago maka ma.

Dariya yayi yace kai yar baba da wauta ni tsoho dani yaushe zan iya tauna aya cinye kayanki na gode, yanzu tayani mu kwashe kayanan mu maida cikin shago mu kulle mutafi gidako? Tace to babana.

Wani injin mota taje zata daga baban da sauri yazo ya karba haba yar baba kidena daukan abu mai nauyi ke mace ne kinji ko?? Tace yakuri baba nadena.haka suka shigar da komi ya kulle shagon yakamo hanunta suka tafi gida.

Irin katon gidan hayan nan ne dakuna kusan 15 bayi daya kacal a gidan. Dakinsu shine daki na karshe, bude dakin yayi suka shiga yace yace yar baba kiyi alwala kiyi salla bari naje masallaci, karfa kifita kinsan yan gidanan dukanki suke ko?? Tace to babana bazan fitaba, ta make murya tace babana kadan siyomin alawa kaji, banza yay mata yawuce yafita.

Kaman yanda yace alwala tayi tai salla ta dauko littafan bokonta taduba, bai dawoba sai bayan isha yashigo musu da ruwan bunu da beredi, kadan yasha yabata sauran dukdan ba koshi yayiba, tasha tai nak, tace babana zanyi wanka, yace muje narakaki.

Cire kayan jikinta tayi baban ya riko hanunta shiyaja mata ruwa daga rijiya yazuba mata abotiki, har bayi yakaita sanan yafito waje yana jiranta tagama su dawo daki, inba haka yayiba yan gidan dukanta suke saisama yake tafiya da ita wurin aiki.

Tafito suka koma daki tasa kayan baccinta ta kwanta sai bacci, baban nata kuma yafara shafaโ€™i da wuturi, bayan yagama yazo ya kwanta a gefen katifa ya kashe kendir din sai bacci.
Cikin dare yar baba ta tashi kuka take sosai tana babana tana bubbuga shi, babana wlh katashi, wayyo babana zafi zai kasheni, afirgice yatashi yadau mafici yana fifitata ya daura kanta kan cinyanshi yana shafa kanta har bacci ya kwasheta, mikewa yayi yafita donyin alwala .. Yana idar da salla yay shiru yana tunanin rayuwarshi dayar tilon yarshi SHUKRA.
Maman shakur ๐Ÿ˜˜
[02/11 7:30 PM] Aishat muhโ€™d: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ TAWA CE!!! ๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
3โƒฃ
Niko maman shakur nakara gyara zama kusa da wanan dattijon dajin labarinshi.
Asalin labari,
Sunana Muhammad, iya abunda nasani shine nataso a garin zamfara agidan al majirai haka nacigaba da rayuwata har nasamu aiki gidan wani babban alhaji mai suna Alh shuibu a matsayin mai gadi, matarshi daya Amina da yarshi mace kwara daya mai suna hajara.

Alh shuibu mutum ne mai kirki, son talakawa, ga sanin yalamata, matarshi kam amina ko kadan batada kirki batason talakawa, cikin ikon Allah soyayya mai karfi tashiga tsakanina da yarsu hajara, mamanta Amina babu yanda batayiba dan tarabamu amma Allah baiyiba, alh ya auramin yarshi hajara yabamu gidan zama bakin ciki kaman ya kashe mamanta.

Muna zamanmu lpy, tareda girmama juna hajara na sona sosai haka nima ina sonta, duk iya kokarin hj amina dan taga tarabamu hakan baiyuba, alh shuibu yakaini wani kamfani dasuke kera mota tare da gyaran mota, na dinga koyan gyran mota a kamfanin dalilin dayasa na iya gyaran mota kenan.

Mun dade bamu samu haihuwaba amma daga baya Allah ya azurta hajara da samun ciki munyi murna bayan wata tara ta haifi yarinya mace kakkyawa mai kama da ita wanda tace suna SHUKRA.

Alh shuibu nason shukra sosai lokacin da shukra keda shekara 5 a duniya Allah yama alh shuibu rasuwa. Munyi rashi sosai bayan yan watanni da rasuwa hj Amina ta tada balaโ€™i tacemin dole nasaki yarta kota hadani da hukuma tace musu nina kashe alh shuibu.

Dama dan Alh tabari auren yay tsawo haka datuni tarabamu dole haj taraba aurenmu nasaki hajara saki daya, hj tace wlh inhar tabini Allah ya tsine mata, hj Amina tabani shukra tace gayata nabar musu gida, karna kara dawowa inda suke, hajara tai kuka kaman zata mutu haj tarabata da yarta da mijinta. haka na tattara da shukra wanda ke shekara 5 mukabar zamfara gabaki daya zaria nadawo nafara neman aiki.

Bazan taba mantawa dawani matashi lokacin ya ganni dake muna yawon neman aiki yatausaya mana sosai sunanshi THARIQ, dukda bayi da kudi matashine amma haka yasaima shukra abinci yatambayeni aikin dana iya nace mishi kani kanci, shiya kamamin hayan shagon danake aiki yanzu, yan kudin daya rage mishi ya saimin su sufanu dadai kayan aiki namai godiya sosai yasaima shukra sweets yatafi, kana raina THARIQ akullum inama adduโ€™a dan kataimakemu.
Haka nacigaba da rainon yata duk inda zani da ita nake zuwa saboda gidan damuke basu sonta kullum dukanya suke. ina aikin gyaran mota, nasata a makaranta har yanzu datake ss3, abu daya nasan nai kuskure gameda rainon shukra na sangartata da yawa, ina balaโ€™in sonta kome takeso sainai mata.. tundaga lokacin ban kara ganin THARIQ ba, wanan kenan.

Maman shakur ๐Ÿ˜˜
[02/11 7:30 PM] Aishat muhโ€™d: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ TAWA CE!!! ๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
4โƒฃ
Da asussuba yatasheta har bayi yarakata ya tsaya yajirata tai wanka sanan yakoma da ita daki ya kulle kofan shikuma yatafi masallaci donyin sallan asuba, bayan yadawo ya tarar shukra nakaratun Al qurโ€™an yajonata suka karanta tare bayan sun gama tace babana ina kwana yace kin tashi lpy yar baba?? Tai murmushi, yace kiyi adduโ€™a Allah sa yau musamu aiki sosai kinga saina biya kudin wutan mu yanda zafi zai dena damunki ko, kuma sai mu dafa indomie din dakikeso yauko?? Dariya tayi ta rungume baban Nagode babana, yace to tashi mutafi shago inmukaje maci abinci acan.

Mikewa yayi amma yaji wani jiri jiri da sauri yakoma yazauna, shukra ta zauna kusa da shi babana lpy meke damunka?? Yace yar baba zazzabi nakeyi kwana biyun nan, kuka shukra tafarayi sosai babana shine baka fadamin bako??

Yace dena kuka yar baba bawani ciwo bane nasan yunwa ce kawai, amma anjima maci abinci sosai ya Mike tsaye kaman ba abunda ke damunshi nanko karfin hali yake, yaja hanunta mutafi suka fito harsunkai waje yabata key yace daukomin radio ta yau zanji jakan magori.

Tafito daga dakinsu kenan wata yar budurwa mai suna Pherty a gidan take ta bangajeta, shukra tace Pherty mehaka?? Pherty tai fari da ido naga kin tare hanya ne, kuma ai gidan banaku bane duk haya muke, yarinya sai yin abu kaman namiji, although ba laifin ki bane ke rainon namiji ce ke saisa, tai tsaki tawuce hartakai bakin kofa tace andaiji kunya mace da aikin kanikanci, shukra tabita da gudu dan ta daketa turus tayi ta tsaya dataga baba a tsaye yace wuce mutafi kidena amsamata yar baba yaja hanunta suka tafi.

Suna zuwa baba yasayo musu kosai sukaci sanan suka fara aiki shukra tana karkashin wata mota tana kwance inji baba na tsaye yana mika mata abunda take bukata, wata hadaddiyar mota jeep baka ce tashigo garejin baba ya tsaya yana kallon motan,

Saida yagama parking sanan nacikin motan yafito wani hadadden saurayi ne yafito mai kama da balarabe ma aboci fadin kirji ga gashi kwance akanshi yana sanye cikin black suit yay kyau sosai.

Baba goge idonshi yayi yace THARIQ kaine ko mafarki????
Thariq yay murmushi yakaraso har kasa ya tsugunna yagaida baba, baba ya amsa, baba yace thariq ina kashiga??? Tun lokacin nan bamu kara haduwaba, sosa kai yayi yace wlh baba kasan ni badan zaria bane, karatu nakeyi a ABU ina karanta medicine dana gama nakoma garinmu kano, yanzu ma wani asibiti nazo dubawa a garinan wata daya zanyi. Shine nace bari nazo nadubaka da kyar nagane shagon.

Baba yay dariya tasu ta manya yace kadawo likita bokan turai yanzu, thariq yace baba ina shukra mai shan majina?? Baba yace gatachan karkashin mota kallon inda ake nuna mishi yayi kafafunta kadai yake iya gani.
Baba yace yar baba fito munyi baki, tace to babana.
Fitowa tayi amma kwata kwata hankalinta baya kan baba yana kan hadaddiyar motan data gani zuwa tayi ta wanke hanunta sanan takoma wurin motan tana shafawa tasa kanta jikin glass ta leka cikin motan mezata gani sweets tagani dayawa hade da chocolate dasu biscuits zagawa tayi tabude motan taciro su tasamu waje ta zauna tabude biscuit din zata faraci taji baba ya daka mata tsawa shukra!
Maman shakur ๐Ÿ˜˜
[02/11 8:37 PM] Aishat muhโ€™d: [02/11 7:30 PM] Aishat muhโ€™d: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟTAWA CE!!! ๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
5โƒฃ
Ta kalleshi a firgice, ya daure fuska bakida hankaline?? Anbaki ne dazaki bude mota ki dauko?? Wuce kimaidasu kafin ranki yabaci, kuka tafarayi sosai tana buga kafa babana inaso nefa wlh bazan yardaba ni biscuit dinane saika bani, thariq dai yana zaune yana kallon drama, ga mamakinshi sai yaga baba ya rage murya haba yar babanta kiyakuri anjima zan siyo miki wanda sukafi wanan yawa kinga wanan ba namu bane na bakone ko ya share mata hawayen yauwa yar baba oya tashi kimaida yacigaba da mata kirari tawuce tamaida motan, juyowan dazatayi ne taga wani hadadden namiji zaune ya daura fuska yana Kallonta jitayi kirjinta yabuga dummm. Ahankali tazo tace ina wuni fakan idanun baba yayi ya balla mata harara sanan yace lpy, jeki dauki biscuit din dama kena siyomawa.

Jiyayi ya tsani yarinyan, shidai yaga baba mutum ne mai addini amma maisa bai tarbiyantan da shukra ba?? Ya sangartata dayawa, randa baya duniya ya yakeson rayuwanta ta karasa?? Komawa cikin shagon tayi dan taga bakon baba yanata hararanta, sai wuraren magrib yatafi yayma baba kyautan kudi fir baba yaki karba yace kayan kwalaman dayasaima shukra ya wadatar, haka yatafi zuciyarshi fall haushin shukra yarinya ace kometa keso sai baba yamata haba wanan ba rayuwa bace.

Suna komawa gida baba yatafi masallaci, ya dawo kenan kowaye yazuba man gyada akasa oho baba ya zamiye yafadi yaji ciwo akafa dan saida yakasa tashi, ihu yake babu wanda yafito, shukra tana zaune taji kaman muryan babanta tafito da gudu taganshi kuka take sosai da kyar ta iya dagashi suka shiga daki ciwon dayaji a kafa ta share jini yaki tsayawa baba yace ta jika tsumma da kalanzir tasa haka ko tayi sai jinin ya tsaya.
Da safe ciwo yay tsanani danko masallaci baba yakasa zuwa shukra bata iya komi sai kuka, dan ciwon dayaji wurin yay wani iri kaman kuraje, dari biyu dayakedashi gaba da baya yabata yace tasiyo musu ruwan bunu wurin mai shayi.

Zuwa tayi amma takasa shiga wurin dan tunda take bata taba zuwa wurin da akwai mazaba, ko school dinsu tamata zalla ne yanzu zatayi?? Wani karamin yaro yazo wucewa ta aikeshi yasiyo mata tabashi naira biyar. Tabiya chemis tafada babanta yaji ciwo akafa aka hada mata magani naira dari tabiya. Tadawo da sauri taba baba yasha da kyar dan jikinshi yay zafi sosai tabashi maganin yasha bacci yadan daukeshi kuka tayi sosai daga baya tadaura kanta kan hanunshi itama bacci ya kwasheta..
Wuraren 1 baba yatashi da kayr yay alwala salla ma a zaune yayi, shukra sai hamman yunwa take tabashi tausayi yace nawa ne canjin daya rage tace naira 20 yace to jeki siyo biscuit kici anjima inna samu karfi zan fita na nemo mana abinci.

Maman shakur ๐Ÿ˜˜
[02/11 7:30 PM] Aishat muhโ€™d: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟTAWA CE!!! ๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
6โƒฃ
Ta zauna taci biscuit din tasha ruwa baba sai Kallonta yake kome yake tunani oho, dago kanta tayi taga baba na Kallonta tai murmushi ahankali yace yar baba zonan kusa dani da rarrafe tazo ta zauna ya rike hanunta gam, yace yar baba ina sonki sosai ke kadai nakedashi a duniyan nan, banda kowa babu mai sona saike da Alh shuibu, hajara, dakuma thariq.
Tace baban suwaye haka?? Murmushi yayi yace zaki sansu yata zanfada miki kosu waye tari yafara sosai takara rudewa tafita da gudu taje dakinsu Pherty tace ma maman su Pherty mama babana baida lpy dan Allah kuzo mukaishi asibiti, maman Pherty tace wuce kifitarmin daga daki yamutu ma mai ruwan mu, kowanan lallaba rayuwanshi yake , duk dakunan dake gidan saida ta shiga babu wanda ya taima kamata,
Ta dawo dakin baba lokacin ko magana baya iyayi, Kallonta yayi yay mata murmushi karfin hali itama tai mishi yace yar baba zoki zauna kusa dani, kidena kuka babu abunda zai sameni anjima zanji sauki naje nai aiki nasiyo miki indomie ko?? Ta girgiza kai, ya kwanto da kanta kirjinshi ta fashe da kuka shima hawayen ne ya gangaro daga idonshi.

Ko kadan bayason yaga yartashi cikin wahala, da kyar tai shiru bacci ya dauketa.

Thariq yau yazo shagon yafi sau biyar amma akulle, hankalinshi yatashi baisan mesaba yanaji a jikinshi wani abune yafaru dabasu zo ba, gashi baisan gidansuba, har washe gari yadawo da safe akulle hankalinshi yatashi, yashiga mota yakoma asibiti karfe daya yadawo still a kulle.

Shagunan wurin yafarabi yana tambayansu baba sukace tun jiya baizoba, suma basusan gidanshiba, da kyar yasamu wanda yasan gidan yace yakaishi aiko har kofan gidan sukaje, dai dai lokacin itakuma shukra tafito dan yunwa takeji kaman ta mutu babama yunwa rabonsu da abinci tun jiya.

Ita bama tagane thariq ba shine yaganeta zuwa yayi kusa da ita da sauri ta matsa baya yace ina baba?? kalloshi tayi sanan tace baida lpy, yunwa yakeji nima haka, yan gidanmu babu wanda yabamu abinci, kuma yafidi da daddare kuma yaji ciwo, kumaโ€ฆ. Dayaga bayanin nata bamai karewa bane yace yanzu ina baban?? tace yana ciki yace kaini naganshi, juyawa yayi yabama wanda yarakoshi dubu biyu shikuma yabi bayan shukra.

Yana shiga yaga baba bayama numfashi da kyau, shukra tace kaga bacci ma yake, shidai yana dubashi yafita da sauri yakoga mutumin nan daya rakoshi baiyi nisaba yakirashi tare suka ciccibi baba suka sashi a mota shukra tafasa ihu ina zaka kaimin baba na??.
Daka mata tsawa yayi yimin shiru shiga mota mutafi asibiti, zaunar da ita yay a office dinshi ya aika messenger dinshi yasiyo mata abinci a kawo mata shikuma yasa coat dinshi yawuce yatafi dakin da aka kwatar da baba shida wasu likitoshi suka dukufa kanshi baba bai farfadoba sai wuraren 4 na rana.

Maman shakur ๐Ÿ˜˜
[02/11 7:30 PM] Aishat muhโ€™d: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ TAWA CE!!! ๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
7โƒฃ
Yana farfadowa thariq yay hamdala yahada ma baba tea yasha baba yace ina yar baba?? Thariq yace tana office dina kuka takeyi saisa nace ta zauna a wurin. Ahankali baba yace thariq Nagode Allah maka albarka, hakika kataimakemu.

Yace thariq maike damuna?? Thariq sauke ajiyan zuciya yayi dan bayason fadama baba cancer gareshi kuma yaci jikinshi sosai. Baba yace thariq kafadamin gaskiya tun bayauba nasan banda cikakkiyar lafiya kafadamin dan Allah.

Thariq ahankali yace baba cancer ce, baba yace kuma taci jikina sosai ko?? Bazan dadeba zan mutu ko?? Thariq yay shiru. Baba hawaye ya gangaro daga idonshi yace thariq banaso na mutu saboda yar baba, ban gama bata tarbiyaba, batasan komi kan rayuwaba, yarinya ce karama wanda take bukatar uwa mace ta koyamata abubuwa da dama, amma hakan baisamuba saboda wasu yan dalilai, baba kuka yake sosai thariq ya rike hanunshi, yace baba babu abunda zai sameka in sha Allah zaka warke, zakabama yarka tarbiya mai kyau be strong baba.

Baba ya girgiza kai, yadau dayan hanunshi yasake daurawa kanna thariq yace thariq wlh naji ajikina kwanakina kadan suka rage, inason nabaka amanar Shukra koda banda rai dan Allah karikemin shukra amana, thariq dukda bansankaba bansan kowa nakaba amma zuciyata ta aminta dakai sama dakowa plz thariq tace care of yar baba. Kabata tarbiya,
Thariq duk karfin zuciyanshi jiyayi hawaye ya gangaro yace baba nama alkwari zan kula da ita kadena magana yanzu hutawa yakamata kayi.
Baba ya girgiza kai yace banni nai magana nasan ta karshe ce thariq YAR BABA! YAR BABA!! YAR BABA!!! nabaka amanarta, inhar kaji kana sonta ka aureta nabaka ita dan nafi yarda dakai, idan kuma baka sonta inlokacin aurenta yayi kazaba mata miji nagari ka aura mata, sauke ajiyan zuciya yayi,
Yace thariq inaso kasani yar baba TAKA CE!! Ka kulan min da ita dan Allah..
Yace baba ina maman shukra?? Ta mutu ne?? Maisa kai kade ke rainonta?? Mesa kukadai ke rayuwarku??

Maman shakur ๐Ÿ˜˜
[02/11 8:38 PM] Aishat muhโ€™d: [02/11 7:30 PM] Aishat muhโ€™d: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ TAWA CE!!! ๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
8โƒฃ
Nan baba yaba thariq labarin komi thariq yaji tausayin baba da shukra sosai, da kyar ya lallaba baba yay shiru. **Gani yake kaman zafin ciwo ne kesa baba yake cewa bazai rayuba yaushe zai shirya da sarkin kwadayin chan shukra inaa** baba yace kawomin shukra yace to baba yajuya yafita, yana zuwa yatarar da ita zaune kuka take tama kasa cin abinci gyaran murya yayi yasa ta dago dara daran idanunta ta kalleshi da sauri yajanye nashi daga nata yace muje baba nason magana dake, da sauri ta share hawayen ta kwalalo idonta waje tace da gaske?? wani irin kallon mai kama da rainin wayo yamata batare daya cemata komiba yay gaba tabishi abaya, suna shiga dakin taje da gudu ta rungume baban tama manta baida lafiya sai murna take baba shima yanata murmushi fira suka dungayi hakan yasa thariq fita zuwa duba wasu patient,. bayan ya fita baba yace shukra duk randa bani a duniya kidau thariq a matsayin wanki, yanada kirki kinji, zumburo baki tayi tace baba baruwana dashi baya dariya kaman kai. Baba yace haba yar baban ta kamota kamota nan tadinga dariya harya samu ta yarda.

Karfe goma yadawo asibitin, direct dakin su baba yawuce yana shiga yaga daga baba har shukra suna bacci dukda karantan gadon baba ya matsa mata tare suka kwanta ta rungume babanta dankwalin kanta ya zamiye gashin kanta gabaki daya yarufe mata fuska.

Baitaba ganin yar Nigeria da tsawon gashi kaman na yan India ba saiyau, shagala yayi yana karemata kallo komeya tuna oho yay maza yajuya yabar dakin.
Wuraren karfe biyun dare taji jikinta kaman ta kwanta kan kankara, tashi tayi taga baba yana bacci ta taba jikinshi taji sanyi sosai tsoro taji wanan sanyi kaman kankara. Mikewa tayi tayi hanyar office din thariq tana shiga ga mamakinta taga yana rubuce rubuce laptop a gabanshi, tsayawa yayi yana Kallonta kanta ko dan kwali babu.

Yace waike bakisan dare bane kin fito ba dan kwali ba hijabi, kin shigo babu sallama, magana yake mata fada fada, rudewa tayi jikinta

Please Login or Register in order to submit comment