Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidan ya gaida hajiyansu, kanwar abakin nashi amina tazo gaidashi yakirata gefe yace ga patient dina kidanje ki gyarata.

Ya ciro kayanta daga akwati yabama amina, amina taja hanun shukra suka shiga ciki shikuma ya zauna yacigaba da fira da hajiya.

Saida amina ta taimaketa tai wanka ta gyarata tsaf sanan suka fito, thariq yay musu godiya yariko shukra yasata amota yaja motan.

Maman shakur 😘
[06/11 7:59 PM] Aishat muh’d: [06/11 7:30 PM] Aishat muh’d: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
2⃣9⃣
Shukra sai kuka take cikin mota baice mata komi ba har bacci ya dauketa.
Bashi yakai zaria ba sai wuraren 4 na rana, direct doc quarters inda gidanshi yake yawuce da shukra, suna shiga gidan tafara Amai, dukda yanajin haushinta saboda abunda mum tacemai shukra tayi, amma ya matukar damu da yanda take rashin lafiyan nan, koba komi shukra TASHI CE kuma amanarshi ce.

Riketa yayi harta gama yakaita bayi yahada mata ruwa yace tayi, shikuma yafito falo ya goge wurin, tana fitowa tasa doguwan rigan daya ajiye mata, yahado mata tea tasha kadan sanan yabata magani da kyar tasha, yay mata allura bacci ya kwasheta.

Zamayayi yana Kallonta hawaye ne ya gangaro daga idonshi ahankali yace shukra why?? Why?why with my dad?? Hannu yasa ya rufe bakinshi yacema kanshi nooo, shukra bazatamin hakaba, inhar abunda mum tace gaskiya ne shikenan shukra ta haramta agareni.. Yace i know dy must be an explanation behind all wot mum said, rike hunun shukra yay gam yace in sha Allah abunda mum tafada bahaka bane, ke TAWA CE nikadai shukra, Plz idan kin tashi kona tambayeki kin kwanta akan ciyan dad tell me no. Share idonshi yayi yafito daga dakin fita yayi tafiya kadan takaishi gidan amininshi isma’il,
Kallo daya isma’il yay mishi yagane akwai matsala, vita milk ya dauko mai sanyi yabashi kadan yasha ya ajiye yay huci huhhhh, isma’il ya dafa kafadanshi be strong friend u are a man, would u mind sharing with me?

Maman shakur 😘
[06/11 7:46 PM] Aishat muh’d: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
3⃣0⃣
Ahankali ya fadinma isma’il komi abunda ke faruwa.
Isma’il yay shiru, chan ya nisa yace aganinka shukra zata iya abinda mum tace?? Thariq yace wlh bansaniba, all i know is d word iskanci ma shukra batasan maiyake nufiba, she is 16, but bcuz rainon namiji ce batasan komiba, saisa nima zuciyata taki gasgata maganan mum.
Isma’il yace u know hw u are, zaka iya zama gida daya da macen daba matarkaba?? Zaka iya zama da shukra kubiyo a gida friend?? Thariq yace friend, banda any option i have to, ya kakeson nayi?? Mum tace na kaita wajen maman ta, to bansan inda takeba, kuma bazan iya wurgar da itaba Amanat ce, TAWA CE, nariga nadau alkawarin, yana maganan fada fada, isma’il yace calm down friend, calm down.

Kamo hanun thariq yayi yace friend remember we always share moment of happiness and sorrows together, u are not alone in dis, u can count on me, u can always count on my support for anything, kuma naima alkawari together zamu nemo maman shukra, is a promise friend, rungumeshi thariq yayi hawaye na diga daga idonshi.

Yace friend my biggest problem now is dad, idan yakirani bansan mezance mishi ba, bansan mesa dad keson shukra data kasance TAWA CE nikadai ba,

Isma’il yace abunda mum tace haka zaka fadanma dad, yanzu tashi muje naraka ka karta tashi daga bacci bakanan.. Har kofar gida isma’il yarakoshi sanan ya juya.

Thariq na shiga gida ko zama baiyiba yaji wayanshi na ringing, ciro wayan yayi daga aljihu kallon screen din yayi yaga ansa “DAD” gabanshi ne yafadi dummmm.

Ana wata gawata munafukin maza hahhah fans kubiyo ummu shukra 💃💃
Maman shakur 😘

mamanshakur Is all about novels.
Skip to content
Home
About
TSAFI 1to 11
← TAWA CE!!! 26 to 30TAWA CE 37 to 39 →
TAWA CE 31 to 36
Posted on November 7, 2015 by mamanshakur
[07/11 9:36 PM] Aishat muh’d: [07/11 4:53 PM] Aishat muh’d: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
3⃣1⃣
Cinkin sanyin muryanshi ya daga wayan, dad baima amsa gaisuwanshiba yace ina kakimin shukra baby?? Thariq adan rude yace dad wace shukra?? Nafa bar shukra a gida bayan nagama bata magani tasamu bacci aka kirani a asibiti akwai wata mata da takasa haihuwa saisa natafi, salati yaji dad nayi thariq kaga halin uwarka ko?? I no she have something to do with shukra disappearance, wlh nasan da hannunta aciki, yanzu idan shukra baby na tafada mugun hannu fa?? Wayyo Allah na shiga uku, thariq yace dad tokasa body guard dinka anemota, ni yanzu bazan iya dawowa ba saboda aiki yamun yawa, dad yace thariq karma kadamu kanka nasan uwarka ta koreta kuma wlh saita nemomin shukra baby ta ya katse wayan.

Thariq rike kanshi yayi wanan wani irin uba gareshi, yanzu dad bil haqqi son shukra yake, tsaki yayi.. Ya kishingida da kujera. Motsin dayaji a bedroom yasa yamike yashiga dakin, shukra yagani ta tashi daga bacci tana kokarin mikewa tsaye takasa.

Da sauri yakarasa jikin gadon ya zaunar da ita shukra kin tashi ahankali tace eh, ya maran yadena miki ciwo? Tace eh, kinajin yunwa?? Tace eh, yace to farayin wanka ki wanke bakin ki saikici abinci. Shiga bayi yayi yahada mata ruwan zafi, yafito ya mikar da ita tsaye ahankali take tafiya dan jiri jiri take gani, saida yaga tashiga bayi sanan yabar dakin.
Ahankali take wanka dan gabaki daya bata da karfi ga wani jiri datake gani, ga yunwa nacin cikinta, tana gamawa towel dinshi wani brown data gani ta daura tana takawa ahankali, tana bude kofan bayin taga kanta na juyawa gabaki dayan dakin na juya mata jiri sosai takeji suna daya bakinta yasamo yaya thariq,

Yana zaune falo yaji kaman takirashi da sauri yamike yashiga dakin itakuma daidai lokacin jirin ya dibeta tafadi akasan dakin…

Maman shakur 😘
[07/11 6:15 PM] Aishat muh’d: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
3⃣2⃣
Da sauri yadagata ya rungume ta yana shafa gashin kanta, sorry shukra kina ganin jiri ne? tace eh, murya kasa kasa tace yaya thariq abinci ni zanci yunwa nakeji ni, ya dagata ya daurata kan gado yatafi kitchen ya daukomata fried rice wanda yaji naman kaza ya kawo mata.

Ci tafarayi shukuma yazauna gefenta yana Kallonta, azuciyarshi yace tsarki ya tabbata ga ubangijin daya hallici yarinyar nan komi yaji a jikinta kirjinta cike yake kaman takai 20 kawar da tunanin yayi tareda koran shaidan, tana gamaci yadau plate din yace kisa kaya ni zanje masallaci inna dawo mayi magana, mikewa tayi da sauri yaya zan bika, ya kalleta tareda wulla mata harara kinji sauki zaki fara damun mutane ko, ki zauna bazan dadewa yay maza yafita dan bayason Kallonta haka da dan towel a jikinta.

Shirya kanta tayi cikin atampa riga da sket batai make up din komiba taciro wayanta daga jakan tace Allah sarki Nazir dina nasan yanacan yana nemana wayan akashe, sa wayan tayi a chaji ta kunna bako ajima Nazir ya kirata.

Nazir yace Shukra maiya sami wayanki tun safe akashe?, kuma yau dasafe nadinga jiranki a hanya maisa bakuje hadda ba??? Tace wlh nazir banda lpy ne, arude yace meke damunki??wlh yau koma maizai faru yafaru sainazo dubaki, wani dadi taji aranta tanason yanda Nazir ke damuwa da ita, tai murmushi tace to aini yanzu bana kano ina gidan yaya na, Nazir yace ina?? Karan bude kofan dataji anayi ne yasa ta katse wayan ta ajiye.

Thariq ne ya shigo yace dawa kike magana… Bai karasa maganan ba yaji wayan na ringing again shukra fitsari ne kawai batayiba, dan tana tsoron thariq, ya kalleta ya kalli wayan yace wayan waye wanan??

Atsorace tace wlh wlh yaya bani nacema dad yasaimin ba, kuma ni wlh ban rokeshiba, Allah yaya believe me kasan kahanani roko ko, kuma dama dama randa kakoma zaria dad yadawo yaban wayan… Wayan akasake kira cikin takun kasaita thariq yakarasa ciki yadau wayan yaga anrubuta MY CUP CAKE ajiki, annurin fuskanshine ya bace yajuyo ya kalleta…

Maman shakur 😘
[07/11 6:34 PM] Aishat muh’d: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
3⃣3⃣
Ya kalleta waye my cup cake?? Tai shiru, kai hannunshi yayi zai dauka sai kiran ya katse, daka mata tsawa yayi waye my cup cake?? Murya na rawa tace yaya kawata ce a school, haka nake cemata my cup cake, jikinta ko ina bari yake, yace banason kina waya dakowa kinajina tace eh, karatu zakiyi. Yace saa hijab kizo falo tace to.

Tana fitowa taganshi zaune kan kujera kusa da kafanshi taje ta zauna tareda rikemai kafa, yace shukra wai mesa kike rikemin kafa?? Dago kanta tayi tamai murmushi wanda suka bayyana dimple dinta tace haka nakema babana, kuma kaga kai babana na biyu ne.

Shiru yabiyo baya muryanshi taji yace maiya hadaki da mum?? Kuka tafara mai, yace bance kimin kukaba ki amsani, tace ni bansan menayimata ba, jiya daddare ina bacci naji anbugani da bango nai ihu ina bude idona naga mum da dad a dakina, shine mum keta dukana, tana cemin yar iska dad yahanata sunata fada, kumama yaya yaudasafe mum tace zata kasheni danaje tayata muyi girki tacigaba da kuka sosai, tace yaya thariq dan Allah karka kara kaini wurin mum banason gidan dukana zatayi kumani tsoron duka nake.

Thariq yay shiru inda abunda yagane a maganan shukra shine ita bama tasan da zance tana kan cinyan dad ba, to mai hakan ke nufi dad yasoyima shukra fiyadene tana bacci?? Yace ya isa dena kuka kinji shukra, takalleshi yaya dan Allah ni nafison gidanka plz dakai zan zauna kaji yaya ni banason chan, yace ok shikenan zaki zauna anan wani ihu tayi tafada jikinshi tana murna…..

Maman shakur 😘
[07/11 9:36 PM] Aishat muh’d: [07/11 7:30 PM] Aishat muh’d: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
3⃣4⃣
Tsaya yayi ya kalleta da kyau yana tunanin yaushe shukra zata fara abun kaman budurwa?? Yanzu jibi yanda ta shige jikinshi, yace cikani to, tasakeshi tana dariya, kallo yasa mata yace bari naje mosque tana zaune a wurin tana ta kallo film din namata dadi bai shigoba sai wuraren 9. Tareda take away na abinci.

Saida suka gamaci tace yaya ina kitchen?? Yanuna mata takai tadawo ta zauna murna kawai take yanda yanzu tana tare da babanta nabiyu.

Sai Wuraren 10 yace taje ta kwanta haka tawuce taje daki, tanason waya da Nazir amma tana tsoro kar thariq yajita haka tahakura tai baccin ta.

Washegari Wuraren 8 tatashi daga bacci dayake bata salla saisa tasha bacci abunta shiga bayi tayi tai brush ta watsa ruwa sanan tana fitowa tasa doguwan riga tana zaune taji alamun kauri, hijab dinta tasa tayi hanyar kitchen, tana shiga taga thariq daga shi sai yar singlet da 3quarter iya guiwa sai zufa yakeyi ga hayaki ko ina, taje kusa dashi yaya mai kakeyi?? Yace wlh kinga egg nake soya miki, saboda inkin tashi kiyi break yanzu sau uku kenan duk innayi yay baki kuma sai hayaki yakeyi, yakara tsaki wlh frypan din baida kyau ya lalace, shukra ta dinga dariya harda rike ciki ya tsaya yasaki baki yana Kallonta..

Tace yaya yanzu baka iya soya egg ba abu mai sauki, tsaya kaga taja hanunshi takaishi gefe cikin 2min tasoya musu egg tadafa ruwan tea takai falo tanata dariya ciki ciki.

Abangaren su dad kuwa ya haukacema mum wai dole tafitomai da shukra baby, mum tadage batasan inda takeba, yanzu dad ko magana bayama mum. yakai police station sanarwan yana neman shukra amma an tambayeshi hotonta baidashi, ayanzu haka abun yasoma maida dad kaman zararre dan ko zama yayi shukra baby kawai yake kira, mum tai tsaki tace kayi kagama wlh kaida ganinta har abada.

Maman shakur 😘
[07/11 8:08 PM] Aishat muh’d: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
3⃣5⃣
Suna gamaci takai kwanuka kitchen tadawo ta zauna tace yaya wai inane nan?? Yace doc quarters cikin ABU shika, tace okk. Mikewa yayi yace bari nadanga abokina. Tace saika dawo.

Yana fita tadawo daki ta kunna waya takira Nazir, katse wayan yayi yakirata back, shukra wai meke faruwa ne kinason hawan jini yakamani ne?? Kinsanfa ina sonki, tace Nazir wlh tsoron yaya nake banason yakamani ina waya ne zai iya zaneni, yace to yanzu ya jikin ki?? Tace naji sauki, kina inane yanzu?? Wlh muna zaria yace gaskiya nifa zanzo nadubaki, ta zaro ido wlh yaya inya kamani zai zaneni, yace bakiso nane?? Tace inasonka mana, kuma inason na aurekama, Nazir yay murmushi nasara yace to kimin kwatance zanzo nan tabashi address din gidan, suka cigaba da firan soyayya abunsu daga bisani ya katse wayan.

Wanni tsalle Nazir yayi yay murmushi yace ai tunda yanzu baki tareda tsohonan kina gidan yayanki yanzu ne zan taka rawar gani, zan bataki da yawan kyauta na sangartaki da kudi, zan samiki soyayyata aranki yanda bazakiyi marmarin soyayya dawani namiji ba, yace shukra ke TAWA CE, nan yahada kayanshi ko sallama baima mum dinshiba yaja mota sai zaria.

Thariq dayaje gidansu isma’il maganan zuwa zamfara sukayi inda suka tsaya ran Friday zasu tafi, Isma’il yace zai kawo kanwarshi Amina tazo ta zauna da shukra a gida haka sukabar maganan yatashi yatafi.

Washegari dawuri thariq yatafi clinic shukra harda kuka da kyar ya lallasheta, Wuraren karfe 12 Nazir yakirata wai gashi a kofar gidan tai mamaki kuma tanajin tsoro kar yaya yakamata, hijab dinta tasa ko kwalliya bata tsaya tayiba da murnanta ta gaidashi sai fira sukeyi ita batasan mesaba tana son Nazir sosai, yana bata dariya, gashi idan tai magana ya kwaikwaya abun na burgeta, karfe daya tace mishi kaga katafi kar yaya yadawo yace mata to, wani katon leda ya dauko ya bata ta zare ido mai wanan?? Yace kedai ki karba taki, yayi takarba taki wai yaya zai daketa ajiye mata yayi yaja motan yay gaba haka ta dauki kayan ya kaishi daki taboyesu.

Maman shakur 😘
[07/11 8:26 PM] Aishat muh’d: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
3⃣6⃣
shukra ta zauna gefen gado tai shiru, tana tsoron in yaya thariq yaga kayanan maizata ce mishi?? Na shiga uku, karya fa ba kyau, yanzu to ya zanyi?? Take tambayan kanta.

Tundaga ranan kullum sai Nazir yazo Wuraren 12 yatafi 1, kudi yake bata kaman hauka amma bata karba saidai ya ajiyemata yatafi, tarasa yanda zatayi saidai takai daki taboye, abunku da yarunta tsoro yahanata duba abubuwan ma daya kawo mata saidai takai taboye,

Thariq baitaba luraba dan aiki yamishi yawa, bayama dawowa da wuri Wani zubin sai 9 na dare. Amma kullum soyayyar shukra karuwa take aranshi kuma yaki fadan mata, yayinda Nazir yake gena soyayyarshi a zuciyar shukra dan yanzu yakai munzilin da shukra bata iya awa biyu batare dataji muryan nazir ba.

Yau alhamis tun safe Amina kanwar isma’il tazo zaria, shukra sai murna take, dayake gidan isma’il yakawota dan ta zauna da shukra har suje zamfara su dawo.

Thariq ya tattara abubuwan dazaiyi amfani dashi yakai gidan isma’il yayinda yabarma shukra da amina gidan.
Wuraren 10 nasafe shida isma’il sun gama shiri har sunma fito dan suje suyima su shukra sallama.

Wayan thariq yay ringing yaga sunan mum ajiki da sauri ya dauka, cikin muryan kuka yaji tana cemishi thariq kadawo gida ga babanka nan rai ahanun Allah, muna asibiti baya motsi baya magana. likitoci sunce hawan jininshi ne yatashi, inya bude baki maganarshi itane SHUKRA BABY, kidawo, mum tafashe da kuka.

Maman shakur 😘

mamanshakur Is all about novels.
Skip to content
Home
About
TSAFI 1to 11
← TAWA CE 31 to 36TAWA CE!!! 40 to 44 →
TAWA CE 37 to 39
Posted on November 8, 2015 by mamanshakur
[08/11 6:41 AM] Aishat muh’d: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
3⃣7⃣
INNALILLAHI kawai thariq ke fada da kyar yasamu bakin magana yace mum wani asibiti kukaje?? Tace muna aminu kano dan Allah kazo yanzu hala akwai taimakon dazaka iyabashi ta katse wayan.

Isma’il yace meke faruwa?? nan thariq ya sanar dashi komi. isma’il yace friend can i say something?? Thariq yace go ahead, isma’il yace u know i know alot about physiology to ni gaskiya abunda nake gani game da dad dinka is not just luv, idan ka lura kaman akwai wani bond da yay connecting dad da shukra, bawai soyayya yake mataba kadai, yawanci zakaji words dinshi are bayason ya ganta cikin bakin ciki, wahala da bacin rai, koda yace zai aureta yace saboda aganinshi intana tare dashi he will give her happiness, yadafa kafadan thariq yace friend kaman akwai wani boyayyen al’amari akasa wanda kai dad da mum dukanku baku saniba.

Thariq yace wani irin boyayyen al’amari?? zanyi tunanin akan abunda kace. isma’il yace yanzu katafi zaria ni zan zauna dasu shukra idan kaje kacema dad shukra takira ka taga parents dinta, saika kirani nabama shukra waya tayi magana da dad, inhar dad yaji muryanta ya warke believe to akwai boyayen al’amari akasa, inhar kuma bai warkeba yay insisting tazo taganshi sai musan soyayyan pure luv yake mata.

Thariq yace nagode friend suka shiga ciki yay ma su shukra sallama yaja mota sai zaria.

Maman shakur 😘
[08/11 7:06 AM] Aishat muh’d: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
3⃣8⃣
Yana shiga kano asibitin yawuce direct. ya shiga dakin yaga mum sai rusar kuka take, da sauri yakarasa jikin gado yarike hanun dad yace “dad” maiya sameka?? Plz wakeup dad dont leave me, dad yabude ido kadan jin muryan danshi, yabude baki alamun zaiyi magana thariq yay maza yakai kunneshi bakin dad,

Jiyayi dad yace ina shukra baby??? Rike hanun dad yayi gam yace dad shukra na wurin mamanta, tana cikin koshi lpy ka kwantar da hankalinka. dad baya iya bude ido amma yabude su ras ya kalli thariq yace how? Thariq yace dad nima jiya takirani a waya wai tana tareda mama n ta, dad yay hamdala yace thariq plz kira number nai magana da ita.

Dama already isma’il yariga yafadanma shukra yanda zatayi thariq na kiran wayan isma’il akaba shukra tace hello dad, dad ya sauke ajiyar zuciya yace shukra baby da gaske kinga mum dinki?? Shukra tace eh dad, dad yace hankalinki a kwance babu mai damunki ko?? Kina cikin koshi lpy shukra baby?? Shukra tace eh dad lafiyata kalau, yace to alhamdulillah inane gidan naku?? Isma’il najin haka ya katse wayan.

Dad tuni ya mike ya zauna ya kalli mum da harara yace ta Allah batakiba, gadaishi taga iyayenta, duk bakin cikin tanda sai anci waina, thariq yay murmushi, dad yace ban abinci naci. thariq ya dinga kula da dad kwanan su uku aka sallame dad.
Washe garin ranan isma’il ya diro kano sukaima iyayensu sallama sukadau hanyar zamfara.
Maman shakur 😘
[08/11 7:26 AM] Aishat muh’d: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
3⃣9⃣
Suna shiga zamfara thariq ne ke tuki, yace friend kakosan akwai yayan dad dina a garinan but he is late yanzu, isma’il yace ayya Allah jikanshi, thariq yacigaba da magana but yabar matarshi da yarinyanshi mai suna hajara wai yanzu ma tana aure minister of petroleum alh tafawa, kasan wani abu kuwa?? Isma’il yace saika fada. wlh bantaba haduwa da hajaran ba, kuma suna yawan zuwa gidanmu da hj amina but yawanci dat tym ina school. And recently da hj aminan tai ciwo nida dad munje har zamfaran wani ikon Allah bamu hadu da hajaran ba, hj amina tace wai sunyi tafiya Korean ita da mijinta.

Isma’il yace yanzu a ina zamu sauka?? Thariq yace y not mu sauka a hotel, anjima da yamma sai muje gidansu yayan dad din nawa, kaga tundasu sun dade a zamfara watan kilan susun alh shuibu din ko ya kace, isma’il yace hakane.

Suka kama daki biyu a hotel shi daya isma’il daya, karfe biyar suka shirya suka tafi gidan, hj amina na ganinsu tafara murna wai wai wai likita bokan turai, kainake gani ko mafarki nakeyi?? Thariq yay dariya yace zoki mintsileni sukadayi wasa da dariya aka zauna anata fira, hj amina tace kaga bari nakira hajara tazo kuhadu batasankaba, kaima batasankaba tadau waya.

Bayan mangariba wata hadaddiyar mota ta faka a tsakar gidan. hj amina tace ai gatachan ta iso ma, hajara tafito ta kulle mota tabude back sit tafito dawasu kyawawan yara maza daga ganinsu twins ne tariko hanunsu suka shiga ciki.

Sallama tayi saida kirjin thariq yabuga wacece haka da muryan shukra?? Bude labule tayi ta shigo twins da gudu sukaje suka dane jikin hj, itakuma ta karaso cikin falo

Isma’il da thariq suka mike tsaye ganin wata irin mata wanda babancinta da shukra shine ita wanan daga gani ta girmama shukra nesa bakusaba, thariq ne yasamu bakin magana yace hj wacece wanan??… ……

Maman shakur 😘

mamanshakur Is all about novels.
Skip to content
Home
About
TSAFI 1to 11
← TAWA CE 37 to 39TAWA CE!!! 45 to 46 →
TAWA CE!!! 40 to 44
Posted on November 9, 2015 by mamanshakur
[09/11 8:02 AM] Aishat muh’d: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
4⃣0⃣
Hj Amina tace ai itane hajara yata mana. Zama yayi akasa hj tace lpy thariq?? Ya share gumin daya zubo mai, yace hj dalilin daya kawomu zamfara munzo neman maman wata yarinya ne mai suna shukra.

Hajara ta rude tace shukra ta?? A ina ?? Ina take?? Plz ka kaini wurinta tareda babanta??hj dama nafada miki shukra bata mutuba, Thariq yay shiru yana kallon yanda hajara ta rude. Yace anty tana gidana, nan yabasu labarin komi har da na dad, bayan ya karake ya kalli hj yace hj maisa zaki raba uwa da ya?? Maisa zaki raba miji da mata?? Why??

Hj da tuni hawaye ya wanke mata ido tace Thariq wlh son zuciya da tsanan talaka kuma nai nadama,*****bayan na kori baban shukra da shukra, ko kwana biyu ba’a yiba hajara tafara ciwo kaman zata mutu, hankalina yatashi kullum magananta shine indawo mata da mijinta da yarta. Nayi matukar shiga tashin hankali dan hajara tafara haukacewa har India nakaita amma a banza bataji saukiba, nazo nafara nadaman abunda nayi dan banason na rasa hajara ita kadai gareni, ana sallamanmu muka dawo Nigeria nai mata alkawari zansa a nemo baban shukra da yarta shukra.
Babu inda ba’a nemesuba a zamfara amma babusu, nikuma ganin ba’a gansuba hankalina yakara tashi nazo nacema hajara ance sun mutu. Ranan hajara tai kuka ta kallen tace mama wlh inaji ajikina shukra da babanta na raye. Da kyar nasamu hajara ta dawo dai dai shekara uku dayin aurenta wayan nan twins din hassan da Hussain sune yaranta *******

Hajara tadau waya takira mijinta hello honey kazo yanzu, nan da nan yazo yaga matarshi na kuka rungume yayi yana lallashi.

Hajara tace ina shukra ta ku kaini wajenta wlh bazan iya bacci ba yau, Alh tafawa (mijinta ) yace honey cool ur mind gobe in sha Allah direct zaria zamuje kiga shukra ki.

Maman shakur 😘
[09/11 8:28 AM] Aishat muh’d: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!! 💞


Please Login or Register in order to submit comment