Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

motan yaga duk abunda yabama shukra bata taba komiba yay mamaki, amma daga baya yay murmushi, yacema kanshi dole nagano wanene wanchan guy din ( thariq) arayuwan shukra, anya kuwa yayanta ne?? Dan naga sonta a idonshi, yay murmushi yace inkunsan wata bakusan wataba, shukra TAWA CE, wlh ko ban auretaba, saina sha zumanta, idan kuma hakan bai samuba to zanba shukra tabon da harta mutu yana jikinta. yay wani saurayin murmushi yajuya yashiga gida.

Masu karatu wani tabo yakeson sawa shukra??? Wanda harta mutu yana tare da ita?? Ina jiran comment naku.
Maman shakur ๐Ÿ˜˜



mamanshakur Is all about novels.
Skip to content
Home
About
TSAFI 1to 11
โ† TAWA CE!!! 47 to 53TAWA CE!!! 60 to 63 โ†’
TAWA CE!!! 54 to 59
Posted on November 11, 2015 by mamanshakur
[11/11 7:51 PM] Aishat muhโ€™d: [11/11 8:26 AM] Aishat muhโ€™d: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ TAWA CE!!! ๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
5โƒฃ4โƒฃ
Da yamma shukra ta fito bataga thariq a falo ba tashiga kitchen ta dafa musu abinci. Coconut rice da stew, amma kwata kwata takasa ci, ta zauna akasa tai shiru tai tagumi, gashi cikinta har ciwo yake saboda yunwa.

Wuraren 10 yashigo gidan, yaganta zaune a falo idonta arufe tarike cikinta, da sauri yakarasa yarikota yana shukra lpy?? Ahankali ta bude idonta ta kalleshi tace yunwa nakeji, tashi yayi yashiga kitchen yadebo abincin yabata tace bazan iyaba kabani abaki, yafara bata yaki bari suhada ido, saida sukaki last spoon yazo zaisa abakinta ta daura hanunta kan nashi ta kalleshi hawaye ya zubo idonta tace yaya dan Allah kayakuri plz, bazan karaba kaji, ajiye spoon din yayi yamike yatafi dakinshi, binshi tayi ta tsaya bakin kofa tana kuka sosai amma thariq bai budeba har bacci ya dauketa a wurin yafito ya kaita dakinta.

Adaren thariq baiyi bacci ba, karshe ya yanke shawara zaikai shukra wajen mamanta, kota kara wayau tasan rayuwar ya mace.
Washegari da safe yakira hajara sukai maganan, tace Thariq gwara muhadu a kano kaga yakamata su baffa ( dad Thariq) da mum dinka susan wacece shukra, kaga hakan zaisa mum dinka da baffa su daidaita kansu ko?? Yace hakane anty, tace duk muhadu a kano yau, bari fadama honey mu shirya, sukai sallama suka katse wayan.

Dakin shukra ya shiga yaga tai zuru zuru ta balaโ€™in bashi tausayi amma dole ya share, yace kihada kayanki zamuyi tafiya, murya kasa kasa tace yaya ina zamu?? Yace zankaiki wurin mum dinki, tace yaya nafison wajenka wlh, ya ballamata harara kiwuce kihada kayanki nace.

Maman shakur ๐Ÿ˜˜
[11/11 9:17 AM] Aishat muhโ€™d: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ TAWA CE!!! ๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
5โƒฃ5โƒฃ
Thariq basu shiga hanyar kano ba sai Wuraren 4 saboda yadanje asibiti, hajara sai kiranshi take dayake su harsun dade da isowa.
Wuraren 6 suka isa kano, shukra tana ganin sun shiga gidansu thariq tafara kuka yaya dan Allah mukoma wlh mum zata dakeni, yanda yaga hankalinta yatashi yasa yace mata babu abunda zata miki i promise u. Side dinshi yafara kaita saida suka salla sanan suka fito hanunshi ta rike gam suka shiga falon da sallamnsu.

Kowa na falo, dad,mum, Hj amina, hajara,Alh tafawa, twins dakuma imran. Dad shiya fara mikewa tsaye yace shukra baby kece kuwa?? Dama nace ke TAWA CE nasan zaki dawo gareni, ya kalli mum wanda haryau fada suke basu shiryaba yace kinga tadawo gareni saidai ki mutu da bakin ciki.
Mum ta mike tana nuna shukra da yatsa wanda tarike thariq gam jikinta na rawa mekika dawo yi?? Bar gidanan kafinโ€ฆ
Hj Amina ne tamike tsaye itama da murmushi a fuskanta ta kalli dad tace yaya (dayake haka take kiranshi tunda kanin mijintane late Alh Muhโ€™d,). tace yaya, hj ku zauna yanzu ba lokacin fada bane, tajuyo ta kalli thariq tace likita samu wuri ku zauna yazauna shukra ta zauna kasa ta rike kafanshi gam.
Hj Amina itace tafadi masu ko wacece shukra garesu, shukra kam kuka take sosai yanzu dad na matsayin kakanta ne?? Yaya thariq dan uwanta?? Ashe maganan yafito fili, hj Amina tace kwarai kuwa, marigayi Alh muhd mijina yayan dad din thariq neโ€ฆ.

Maman shakur ๐Ÿ˜˜
[11/11 9:59 AM] Aishat muhโ€™d: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ TAWA CE!!! ๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
5โƒฃ6โƒฃ
Dad da jikinshi yay sanyi, yace ashe duk abunda nakeji game da shukra baโ€™a banza bane, ashe ke jikata ne saisa Allah ya dauramin sonki. yace yaya na marigayi Alh muhโ€™d yarigani aure danni banyi aurebama saida nakai shekara 45, saisa har Alh yay aure suka haifi hajara ni banyi aureba, kafin hajara tai aurene nazo nai aure ba dadewa alh ya albarkacemu da thariq.
Bayan haihuwan thariq dakusan shekara 15, akai bikin hajara inda itakuma bata samu ciki da wuriba, lokacin data haihu Alh yafadamin amma lokacin muna makka, Alh yacemin yasamu jika mai suna shukra nataya yayana murna sosai, muka dawo mukazo mukaga shukra sanan muka koma kano dayake ni achan nake aiki.
Bayan rasuwan yaya dayan watanni, hj takira waya wai baban shukra da shukra duk sun mutu.
Kowa jikinshi yay sanyi shukra yau taji inama babanta na wurinan, ashe ba laifin maman tabane, mum din thariq tazo wurin shukra tace kiyafemin dan Allah, shukra ta share hawaye tace mum na yafe miki bakimin komiba, hj Amina ma tazo shukra tace kaka nayafe miki wlh. shukra ta dagakai ta kalli ummanta hajara dake kuka sosai ahankali ta mike taje ta tsugunna agabanta tace umma na plz kiyafemin abunda namiki ranan, hajara tace bakimin komiba suka rungume juna yan biyu ma suka taso suka hadu suka rungume umman su.
Shukra tamike taje gaban alh tafawa da shima yay dan guntun hawayen tausayi, tace babana na uku ina wuni, kowa yay dariya adakin, yay murna yaji dadi yanda shukra takirashi babanta, shukra ta mike taje ta rungume dad din thariq ya kankameta yana jikalle ta ya isa haka kukan kinsan banison ganinki a damuwa ko, ta mike tajuyo ta kalli thariq, gudu tayi ta isa gareshi wani irin runguma ta mishi tana kuka sosai tace kaine Babana ne nabiyu, kai yaya nane, kaikuma dan uwanane, kaine gatana, u are my everything yaya thariqโ€ฆ

Maman shakur ๐Ÿ˜˜
[11/11 7:51 PM] Aishat muhโ€™d: [11/11 10:23 AM] Aishat muhโ€™d: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ TAWA CE!!! ๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
5โƒฃ7โƒฃ
Yanda yaji tana kuka ajikinshi saita karyamai zuciya, ya dagota yace shii, kukan ya isa haka karkiyi ciwo kinji shukra, ya share mata hawaye takoma kasa ta zauna ta rikemai kafa gam.
Ranan dai ankusa raba dare a wurin sai fira ake, dad da mum sun yafi juna sun shirya, hajara ma tayafema mahaufiyarta hj amina, kowadai murna yake. shukra, twins,da imran awurin suka bingile da bacci, yayinda dad Alh tafawa, thariq, mum,hj amina,da hajara sai fira suke suna dariya, hajiya na kara basu labarin yanda dad yadinga cewa zai aure shukra suna dariya. Mum ne ta kalleshi tace alh abu daya ne ya tsayamin arai har yanzu maiya kaika dakin shukra da daddarenan harna ganta akan cinyan ka?? Kowa yay shiru yana sonjin abunda dad zaice.

Dad ya sauke ajiyan zuciya yace bayan nagama abunda nake naji kukan shukra tana zafi zai kasheta ina shiga na kunna mata A.c. shine na zauna bakin gado ina shukra dena kuka na kunna miki A.c., kallona tayi tace babana sai ta daura kanta ajikina tacigaba da bacci, tausayi tabani sosai shine yasa ban cireta daga jikinaba ina shafa mata kai dan nasan yada da yakeji inbaida iyaye, dan nima narasa iyayena tun muna yara.

Kowa ya sauke ajiyan zuciya. Sai Wuraren 1 nadare suka gama fira, dad da mum suka tafi dakinsu, alh tafawa yadau hassan, hajara tadau hussain, ta kalli thariq tace dan kawo mana shukra side dinmu thariq yace to anty.

Ahankali ya janye hanunta daga kafanshi, ya daga kanta dake kan cinyanshi, ya dauketa chak kaman jaririya yabi bayansu Anty, dakin hajara ya kwantar da ita kan gado sanan yay musu sallama yatafi part dinshi.

Maman shakur ๐Ÿ˜˜
[11/11 10:48 AM] Aishat muhโ€™d: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ TAWA CE!!! ๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
5โƒฃ8โƒฃ
Yau kwanansu 4 a kano, kowa na gidanan murna kawai yake, Shukra takan rasa wayafi kula da ita da sonta tsakinin Mum, kaka (hj Amina ), d ummanta, duk kula da ita suke.
Idanko dad na gidan babu wanda ya isa yasa shukra aiki cewa yake babu wanda zai damu jikarshi, sai dai yabata jirida tazo kusa dashi tana karantamai yanaji. Thariq nedai har yanzu baya sakin mata fuska sosai, sotake ta rokeshi yabata wayan ta kotadanji muryan nazir dinta, amma bataga fuskan tambayaba.

Yau asabar gobe suke shirin wucewa zamfara, yayinda gobe shima thariq zaikoma zaria asibiti.
Shukra taci gayu taje dakin ummanta, tace umma inaso nasai uhm, umma tace menene uhmm?? Shukra ta rufe ido tace pad, umma tai murmushi ta dauko kudi tabata, tai godiya tawuce tatafi, da kafa take tafiya wani dan karamin super market na kasan anguwan ta shiga tasiya tafito, tana fitowa Nazir tagani tsaye yana mata murmushi da sauri takarasa wajenshi tana mauda mishi martani, ya akayi ka ganni?? Yace dazaki shiga,
Yace yaushe kuka dawo kano?? Tace yau kusan sati daya, yace wayankifa tace yaya ya kwace, nan suka dinga fira cikin hikima ya tambayeta wai yayan nan naki mamanku daya babanku daya?? Tace no, nandai tafadamai komi.

mota suka shiga anan yake fada mata zaije paris, babanshi yaturashi wani business wata daya zaiyi dazaran yadawo zai turo ayi maganan aurensu aiko sai murna take,

Ya kalleta yace inasonki sosai shukra, tace wlh nima haka, yace kimin alkawari babu wanda zai rabamu a duniyanan?? Ba mutum ba balle aljan?? Plz shukra dont ever leave me, yana maganan yana wani kashe mata idanu.

Maman shakur ๐Ÿ˜˜
[11/11 11:08 AM] Aishat muhโ€™d: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ TAWA CE!!! ๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
5โƒฃ9โƒฃ
Dago dara daran idanunta tayi tace wlh nazir ina sonka sosai amma kuma ni ina tsoron yaya na wlh, inni matarka ne nasan zamuyi aure, abar wani maganan alkawari.
Shiru yayi bai kara cewa komiba amma a zuciyanshi yace bari nadawo daga Paris wlh sainai miki abunda zaisa wanan shegen yayan naki ya tsaneki.
A kofar gida ya sauketa tafito tana daga mishi hannu Allah kaika lpy yadawomin dakai lpy murmushi yamata yace Amin yaja motarshi yatafi, saida taga motan yabace mata sanan taju dan tashiga gida wazata gani??

Thariq tsaye jikin gate fuskarshi kaman bai taba dariya ba a duniyanan, jikinta ya fara rawa yaya wlh is not wot u thinkโ€ฆ Mari ya koda mata, ya bugata da gate, dukanta yahauyi baji bagani, da kyar ta kwaci kanta tai cikin gida da gudu shima yabita.
Falo ta fada lokacin duka family suna zaune ana fira, dad ne yamike ya riketa shukra waya dakeki haka maiya sameki?? Daidai lokacin thariq ya shigo yana huci, jikinta na rawa tana kuka tace dad yaya thariq ne, waidan ya ganni da saurayina Nazir takara fashewa dakuka.
Umma tace yabaki izinin fira da saurayine?? Aiyamin daidai daya zaneki, nawa kike dazaki fara kula samari, babanki yabashi amanan ki dole ya ladaptar dake inkiyi badaidaiba,โ€ฆ Dad ya daga mata hannu rai abace ya kalli thariq me shukra baby tama dazaka daketa??
Wlh zanyi mummunan sabama thariq akan shukra, mai hujjanka na dukan yarinya dan kaganta da wanda takeso?? Mai hujjanka nace??dan katakura mata kome??
Kalmar data fito daga bakin thariq shine SONTA nake dad, i luv her, bazan juri ganinta dawani ba, i luv her, ku auramin ita, i cant leave without her, TAWA CE nikadai, neither Nazir nor anybody can have shukra apart 4rm me, shukra TAWA CE dad,i luv her, yanakaiwa nan yajuya yabar dakin rai abaceโ€ฆ

Maman shakur ๐Ÿ˜˜


mamanshakur Is all about novels.
Skip to content
Home
About
TSAFI 1to 11
โ† TAWA CE!!! 54 to 59TAWA CE!!! 64,65 โ†’
TAWA CE!!! 60 to 63
Posted on November 12, 2015 by mamanshakur
[12/11 12:24 PM] Aishat muhโ€™d: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ TAWA CE!!! ๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
6โƒฃ0โƒฃ
kowa afalon jikinshi yay sanyi harda dad, zaifi kowa murna in thariq ya auri shukra, amma a zuciyanshi yanaji cewa inhar shukra Nazir takeso shizai bata ba thariq ba.
Shukra ko jitayi kaman a mafarki wai yayanta na sonta anya kuwa yaya ne yafadi haka?? Kodai aljanu sun shiga jikinshine??daga baya kuma tafashe da kuka sosai ta durkushe a wurin.
Dad yace shukra Nazir kikeso ko?? Ta girgiza kai, yace karki damu shizaki aura, zanje nai bincike kan Nazir inhar yaro nagari ne shizan baki, mum ta taso tace shukra karkisa maganan thariq a ranki farinciki zamu baki kinji, inhar Nazir kikeso shizaki aura oya jeki kwanta.
Tana juyowa taga umma na hararanta, da sauri tai hanyar daki ta kwanta amma takasa baccin daโ€™akace tayi, kawai tunanin maganan yaya thariq take.

Washe gari har Suka tafi zamfara bataga thariq ba, duksai taji ba dadi, suna kaiwa zamfara gidan ummanta suka tafi yayinda hj amina tatafi nata gidan.
Alh tafawa yasa aka gyaramata daki komi pink dakin yay kyau sosai, yasaima shukra sabon waya sai murna take tai godiya.
Thariq bangarenshi ko dad yazo yasameshi adaki, yace son kai kuskuren kin fadama shukra son dakake mata, gashi har tafara soyayya dawani, nasan kai danane,amma in shukra ta nuna bata sonka bazan iya batakai ba, thariq yace dad inda ace Nazir mutum nagarine zan hakura nabata farin ciki, amma Nazir baida addini, yanashan taba, yana neman mata fa, baida girmama mace, he is nothing but a womanizer, baidau mace abakin komiba.
dad yace ban address din gidansu zan binciko dakaina thariq yabashi, yatashi ya shirya yatafi zaria.

Tunda yakoma zaria tunanin shukra yasashi agaba,.

Dad yaje har gidansu Nazir, akaimishi iso a falon baki, yana shiga yaga tangamemen hoton Nazir sarai dad yatuna dashi wanan wanda yamai rashin kunya, chief din gidan yakawoma dad drink, dad yanuna mai hoto wanene wanan?? Cheif din yace dan mai gidana ne sunanshi Nazir ai dad baima tsaya jiran baban Nazir ba yamike yabar gidan.

Maman shakur ๐Ÿ˜˜
[12/11 7:21 PM] Aishat muhโ€™d: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ TAWA CE!!! ๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
6โƒฃ2โƒฃ
Washegari Wuraren 10 nasafe dad da mum suka iso zamfara amma a gidan Hj amina suka sauka.
Umma, shukra da twins suka shirya dan zuwa gidan kaka, suna shiga gidan da gudu shukra taje ta rungume dad tana murna tasakeshi ta rungume mum, sanan ta rungume kaka, saida akaci akasha akai wasa sanan dad yay gyaran murya.
Yace shukra dama kece dalilin zuwan mu zamfaraโ€ฆ Shukra ta tari numfashin shi tace dad dama inason kazo nafadama na hakura da Nazir yaya thariq nakeso yanzu shizan aura.
Kowa adakin yaji yay mamaki, sunji dadi harda dad dan dama abunda zai fadamata shine bazai iya aura mata Nazir ba, dan baida tarbiyya.
Kaka tace yaya me muke jira tunda ta amince asa rana yanzu mana ko. atake akasa rana wata daya. Shukra dai murmushin yake kawai takeyi dan batajin son Nazir zai iya barin rantaba, nazir yadawo jinin zuciyarta bazai taba karewaba. umma ce kadai talura da yanayinta saisa tajata sukabar dakin sukaje garden anan tafashe da kuka tafada jikin mamanta.
Umma ta shafa bayanta tace yar baba wot u did was d right thing, thariq shiyafi chanchantan malakan ki, bawani chan wanda baisan wahalan kiba, ta share mata hawaye karki damu bazaki taba nadaman auran thariq ba, ta rungume maman tana kuka sosai, ta cigaba da shafa kanta tace nasan Nazir kikeso amma lokacin shizai nuna miki ko da gaske Nazir kikeso.

Atake awajen dad yakira thariq, hello son kanajina gobe kazo zaria inada magana dakai yace to dad.
Saida yamma su dad sukabar zamfara, shukra tai kokarin boye damuwar datake ciki dan umma tace karta bari su dad sukagane ( wayaga su shukra anfara wayau.).

Washegari karfe 12 a kano taima thariq side dinshi yafara zuwa yay wanka sanan yasa 3quarter da singlet fara fat sai kamshi yake direct dikin dad yawuce, yasamu mum a dakin.
Dad yay murmushi yace Hj bashi good news din, mum tai dariya tace Thariq jiya shukra tace ta amince zata aureka atake wajen muka sa rana 1 month, thariq zuwa yayi yarike cinyar mum yace mum are u sure??da gaske?? Ita da bakinta?? Mum tace jibimin yaron zamani natabama wasa ne, wani dadi yaji da sanyi ya ratsashi yay sujjada sanan yadago ya rungume mum sosai yadogo kanshi yay mata kiss i luv u mum. dad yace kai denama matana kiss, sosa kai yayi yabar dakin yana dariya. Dad yay mamaki dama haka thariq keson shukra, lallai son yay DAKON SO littafin Kawalli kausar.

Washegari da sassafe yadau hanyar zamfara gidan hj amina ya sauka sai bayan sallan laโ€™asar yaci gayu cikin wasu fararen yadi dikin half jumper sai uban kamshi yake driver hj tasa yajashi sai gidansu maman shukra.

Maman shakur ๐Ÿ˜˜
[12/11 8:03 PM] Aishat muhโ€™d: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ TAWA CE!!! ๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
6โƒฃ1โƒฃ
Yau kimanin satinsu biyu a zamfara umma batacema shukra komiba saboda tanason tasake da ita sosai.

Yau fariday Wuraren goma nasafe umma ta aika yar aiki ta kira shukra. Da sallamanta tashiga dakin tace umma gani, umma tace shukra inason ki natsu magana zamuyi gabanta yafadi tace to.

Maisa bakison thariq?? Maisa bazaki yarda ki aureshiba?? Shukra thariq dan uwanki y shukra?? Shukra ta share hawayen daya zubo mata tace umma wlh nibance banison yaya thariq ba, kawaidai inason Nazir ne. Umma azuciyarta tace shukra Allah nunamin randa zaki chanza kifara magana kaman adult.
Umma tace shukra karki manta thariq shine cinki, shanki, yabaki sutura, yasaki amakaranta, ya baki magani dabaki da lafiya, ya kasance uba agareki lokacin dakika rasa naki, nakasance uwa agareki, ya kasance jagorar rayuwarki shukra is dat hw u will pay him 4 all wot he did to u?? Haba shukra karki zama butulu, inda badan thariq ba daharyau bamu haduba, daharyau bakisanniba, thariq yafita yanemo miki mahaifiyarki. shukra duk abubuwan nan dayamiki baitaba tambayanki abu ba,
Amma rana daya yanemi abu a wurinki saikiki mai?? Tai maganan tana kallon shukra dake kuka sosai.
Tace umma wlh natuba, nayarda zan aureshi plz umma bazan sakeba, banason Nazir.

Umma tace abinda nakeso dake gobe su dad zasuzo kice mishi kin yarda zaki auri thariq kinji ko?? Tace to ummana. Saikuma ta kwanta jikin umma tana kuka.
Umma ta shafa kanta tace shukra nasan Nazir kikeso amma ki auri thariq lokaci shizai fadamana ko kinason Nazir. yar baba am sure duk inda babanki yake inhar yaji kin amince zaki auri thariq he will be proud of u. Shukra takara rungume umma tace i luv u soo much my umma, inason babana yay alfahari dani, inhar auren thariq zaisa haka wlh mama na yarda banason Nazir kuma.

Maman shakur ๐Ÿ˜˜
[12/11 8:09 PM] Aishat muhโ€™d: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ TAWA CE!!! ๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
6โƒฃ3โƒฃ
Shukra tana tsakar gida suna buga ball itada twins, tana sanye cikin wani 3quarter jeans baki, da blue top kanta ba dankwali jiya umma tai mata kalaba harda bid pink taca umma tasa mata, umma tace shukra waike yarinyace, ta shagwabe wlh umma inaso nidai kisamin haka ko aksamata kuma sun mata kyau sosai. sai ball sukeyi su twins sun fita iyawa sun cika gidan dahaya niya.

Suna shiga gidan driver yakoma. shikuma thariq ya karaso cikin gidan, inda yaji ana hayaniya yabi yana zuwa wazai gani shukra ce ke buga ball da twins tunda yake da shukra baitaba ganinta da irin shiganba tsayawa yayi yana Kallonta.
Shukra tasamu tabuga ball din yashiga cikin raga ihu tafarayi tana tsalle tsalle yess i won yeee harda yima twins gwalo, juyowan dazatayine idanunta suka sarke dana yaya thariq jikinta ne yafara rawa ko inaโ€ฆ.

Yana karasowa kusa da ita ta juya aguje tashiga cikin gida kan gadonta tafada tana kuka sosai, Nazir wlh inasonka, maiya sami wayarka? i want to talk to you, banason kace na yaudareka, inaso nafadama aure zanyi.tacigaba da kuka tana dukan gado.
Twins ne sukazo wurinshi da gudu suna oyoyo uncle thariq sukaja hanunshi har falo, da gudu suka kira umma tafito, thariq yace anty ina wuni yana wani dukar dakai, tai dariya tace doc barka da zuwa saida suka gaisa sosai sanan sanan takaishi dakin baki.

Dakin shukra ta shiga tace oya tashi kishirya, ta dago jajayen idonta tace ummu wlh banasonโ€ฆ Umma tace shiii, mike muje umma ce tashiryata da kanta pink doguwan riga na material mai taushi,tai kyau sosai. Sanan tahada mata abinci a tray takai mishi.

Da sallamanta tashiga dakin kallo daya tai mishi ta dukar da kanta saboda wani irin kwarjini daya mata, a table din gabanshi ta ajiye tray murya alamun ta kuka tace gashi, sanan ta juya dan tatafi karaf taji yarike mata hannuโ€ฆโ€ฆ

Maman shakur ๐Ÿ˜˜

mamanshakur Is all about novels.
Skip to content
Home
About
TSAFI 1to 11
โ† TAWA CE!!! 60 to 63TAWA CE!!! 66 to 70 โ†’
TAWA CE!!! 64,65
Posted on November 13, 2015 by mamanshakur
[13/11 5:56 AM] Aishat muhโ€™d: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ TAWA CE!!! ๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
6โƒฃ4โƒฃ
Yajuyo da ita taki hada ido dashi amma hawaye kawai ke fita daga idonta, murya kasa kasa yace shukra mesa kike kuka?? Bakisona ko?? Tai shiru, mum ne tace kicema dad kin yarda da aurena?? Nan mai ta shiru, sai dai kuka ya dago kanta yace look at me shukra kifadanmin gaskiya kinsan banison karya.

Yace Nazir kikeso?? Tadaga mai kai alamun eh, cikin muryan kuka tace yaya dan Allah karka cema umma nace Nazir nakeso, yace umma ne tace kifadama dad kinasona?? Tace aโ€™a, tadaice inhar na yarda na aureka babana zaiyi alfahari dani, ni inaso babana yay alfahari dani. Ta matukar bashi tausayi harga Allah yanajin cewa inda ace Nazir mutum nagari ne zai hakura yabarshi ya aureta.

Zaunar da ita yayi kusa dashi yace to kukan ya isa haka share hawayen, ta share yace duk randa kikaga dad kice mishi baki sona saboda afasa auren kinji, kaita girgiza mai. Yay shiru kanshi ma ya kwance zuciyarshi na zafi, kanshi na wani irin mugun ciwo haka suka zauna a wurin bai kara cemata kala ba.
Lokacin magrib ne yabar dakin yaje yama umma sallama yatafi.

Ranan kwata kwata thariq yakasa bacci, maisa shukra bazata soshi ba?? Nazir ya cuceshi, yacusama shukra sonshi, yaji kanshi na ciwo yasha maganin dakyar bacci yay awaon gaba dashi.
Washegari da sassafe yabar zamfara direct zaria yawuce.
A ranan umma da kanta tadau shukra takaita chan gidan wata kawarta buzuwa, dan afara gyaran jikin shukra sai ana jibi biki zata dawo. Akano za ayibiki, shukra nata kuka wai bataso da kyar ta hakura ta zauna, masu gyaran jiki aka fara tsuma shukra.

Thariq koda ya isa zaria gidan amininshi ismaโ€™il ya sauka yafadanma ismaโ€™il komi, ismaโ€™il yace friend to me, kaine zaka koyawa shukra sonka, kaizaka koyamata yanda zata manta da Nazir aranta. Just think about it, kafa waye amma ace shukra nabaka headache, thariq yace kasan ni bantaba soyayya ba, wlh basan tayaya zan bullo ma alโ€™amarinba. Ismaโ€™il yace cool ir mind yanzu kabari in ankawota gidanka saikafara janta ajiki kana nunamata soyayyar ka.

Maman shakur ๐Ÿ˜˜
[13/11 6:16 AM] Aishat muhโ€™d: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ TAWA CE!!! ๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
6โƒฃ5โƒฃ
Kwanaki sun jaa, shukra tayi wani irin kyau takara haske,

Please Login or Register in order to submit comment