Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bansan takamamman gidansuba, inda naga sun shiga naan naje kuma tsoho yacemin wai aurenta zaiyi, tace ka kwantar da hankalinka kacigaba da zuwa anguwar duk randa kaga yarinyar kafadamin, namaka alkawari ko wacece ita TAKA CE bomboy ya rungume mum din yana murna.

Thariq yajisu shiru yasa yabisu yana zuwa dakinta yaga bata wurin yana zuwa dakin imran yagansu kan gado tana koyama imran home, murmushi yayi har cikin zuciyanshi yaji dadi yanda tadan sake.

Washe gari Wuraren 10 yafito yasameta tareda mum suna gyara abinci a dining, abincin dake hanunta ta ajiye tana murna taje wurinshi dagudu kaman zata rungume yaja baya da sauri ke me haka?? Murya kaman tamai shirin kuka tace ina kwana, kafin ya amsa sukaji muryan dad yana thariq ka kiyayenifa, kaga yanzu ka bata mata raiko? Kai bakaji dadiba yarinya tasoma sakewa damu yau tareda mamanka sukai girki kawai dan tazo gaisheka zakaimata tsawa yay kwafa ya kalli shukra yace shukra baby jeki cigaba da aikin ki make kai tayi tace sunana yar baba.
Tawuce tatafi wajen mum tana tafiya tana waigen thariq daya saki baki yana kallon dad, harga Allah yasomajin wani iri game da dad amma ya basar yaje ya zauna a dining.

Abinci suka zauna ci, shukra ta zauna kusa da mum tana tsoron taje wurin thariq yamata tsawa abincin ma takasaci kadan taci, dad yace shukra baby cimana dan Allah kidanci kadan kinji, ta make kafada thariq yace jeki shirya nakaiki school registration ta tashi ta tafi daki.

Doguwan riga tasa ta daura hijab tafito, mum tace muje na shiryaki bahaka ake shiryawaba tabi bayan mum, mum ta dauko wani atampa riga da sket black da dot din yellow a jikinsu tasa takawo wasu takalmi masu dan tudu yellow tasa mata, tai mata make up tasa mata pink janbaki abun yahade da pink lips dinta ta daura dankwalin nan daurin nan da ake kira August meeting😜, tafesa mata turare ta dauko gyalee siriri yellow tabata. ita kanta mum tsayawa tayi tana kallon shukra kayan sun mata kyau gashi rigan yadan matseta kirjinnan acike, tai kyau kaman yar larabawa.

Shukra ko bata saba sa irin kayanba duk sun mata wani iri a jiki, mum tace mutafi thariq na jiranki, thariq yakira mun awaya tafito sauri nake, mum ta kalli shukra tace kitafi yana jiranki a mota ahankali take tafiya da takalmin dan jitake kaman zata fadi. tana fitowa daga dakin tai tuntube da ball din imran ihu tasaki ta tafi luuuu zata fadi thariq dayake tsaye yana danna waya yay maza yakai hannu ya tarota tafada kan hannunshi

Lumshe ido tayi sanan tabudesu ahankali ta daurasu kanna thariq, tsayawa yayi yana Kallonta har yanzu tana hanunshi bai mikar da itaba, zubawa juna ido sukayi…..

Maman shakur 😘
[04/11 9:12 PM] Aishat muh’d: TAWA CE!!!

2⃣0⃣
Kokarin kwace kanta daga hanunshi tafarayi dan tamike, firgigit yadawo daga duniyar daya lula ya kalleta are u all right?? Baki bugebako?? Tace eh, yasaketa yay gaba tana binshi a baya makaranta sukaje anmata interview duk thariq na wurin mamaki yake dama haka shukra keda kokarin ss3 suka bata ran Monday zata fara zuwa yabiya mata kudin komi suka baro school din.

Yana tuki yana satan Kallonta, murya mai zaki yaji tace Nagode Allah kara bude,murmushi yay mata kawai batareda ya amsaba,
Agaban wani super market mai suna EVERYDAY SUPERMARKET yay parking yace mata fito muje tafito siyayya yay mata sosai suna kaiwa wurin chocolate tasa hannu ta dauka zata bude taji thariq ya daka mata tsawa wanda saida yajawo hankalin mutanen wajen, Nazir dake tsaye yana biyan kudin abunda yasiya yajuyo wazai gani shukra shi, jiyayi thariq na mata masifa wot are u doing shukra?? Baki da hankaline?? Naki ne dazaki dauka?? Cikin muryan kuka tace inaso nefa, Nazir da ranshi yagama baci, wanchan guy din yanama shukra tsawa gaban jama’a.

Yakara daka mata tsawa ajiyeshi jiki narawa ta ajiye, ya gungura keken tana biyedashi yaje yabiya kudin abun suka fita, shikuma Nazir chocolate din yasiya dayawa yabiya yabiyo bayansu, da sauri yakarasa lokacin zasu shiga mota shukra sai kuka takemai,

Zuwa yayi kusa da shukra ya share mata hawaye a tsorace ta matsa baya, da gudu ta zaga inda thariq yake ta labe abayanshi, Nazir yakara biyota wurin baby na ga chocolate dinki kishaa, takara rirrike thariq, thariq yajuyo ya kalleshi malam bata bukatan chocolate dinka kawuce kabamu wuri.
Nazir ya kwantar da murya shukra inkina ma Allah ki karba kinji, ciro kanta daga jikin thariq tayi tajuyo har tamika hannu zata karba thariq yace wlh inkika karba zan bata miki rai wuce ki shiga mota da sauri ta shiga hartana tuntube.

Shikuma yajuyo ya kalli Nazir stay away 4rm my sister, ba kalar ka bace, kanwata matar natasastsen namiji ce, kamili, karabu da ita ka kuma dena binmun last warning.
Yawuce yashiga motan yaja, suna kaiwa gida yaba mai gadi kayanta yakai mata daki, shikuma yawuce ya shirya dan yanason yakoma yau saboda ana kiranshi a asibiti, yana gama shiri ya shigo yaganta zaune falo bai cemata komiba yawuce dakin mum yay mata sallama taimai addu’a, yafito ya ganta jugum.

Yace shukra zan koma zaria ana nemana a clinic,kimin addu’a kinji, yajuya yafita dagudu tabishi har zai shiga mota saiya tsaya daya ganta, rike mishi hannu tayi tana kuka sosai dan Allah karka tafi, wlh inhar dan abunda nayi dazune bazan karaba plz, kaga kaine babana na biyu, plz dont go, i dont want u leave me, kuka take sosai tana rike da hanunshi,

Dago jajayen idonshi yayi dan tabala’in bashi tausayi ahankali yace shukra bazan dadeba zan dawo kinji, ki zauna dasu mum kinji, ta make kafada tana kuka, sa hanunshi biyu yayi ya dago fuskarta shukra kallen i promise u next week Saturday zanzo nadubaki, kinsan ke AMANATA ce, i soo much care about u shukra, ki koma cikin gida tafiya take tana waigen shi yadaga mata hannu yana murmushi.
Saida tashiga gida sanan yashiga cikin mota dauran kanshi kan starry idonshi yay jajir dago kanshi yayi yashafa fuskarshi ya fuzar da iska yace shukra ke TAWA CE!!

Masu karatu kunfaji ga uba, ga da, gakuma Nazir,
Towai shin shukra TAWA CECE????.

Maman shakur 😘

mamanshakur Is all about novels.
Skip to content
Home
About
TSAFI 1to 11
← TAWA CE!!!16 to 20TAWA CE!!! 26 to 30 →
TAWA CE!!! 21 to 25
Posted on November 5, 2015 by mamanshakur
[05/11 7:59 PM] Aishat muh’d: [05/11 7:56 PM] Aishat muh’d: TAWA CE!!!

2⃣1⃣
Tada motanshi yayi yabar gidan, shukra na komawa cikin gida dakinta taje ta kwanta, ta fashe da kuka jitayi mutuwar baba yadawo mata sabuwa fill, mum ce tashigo tadinga lallabata haba shukra baganiba, bayace zai dawo next week yadubaki ba, nasan thariq akwai cika alkawari zai dawo kinji ta girgiza kai.

Mum ta rungumeta tana lallashinta hartai bacci, mum tabar dakin, lokacin da imran yadawo yazo dakin tadan sake harta koyamai home work daganan tafito taga mum a kitchen.

Mum tace shukra hala imran ne yatashe ki?? Ahankali tace no bashivane, takarasa cikin kitchen din tareda mum sukai girkin mum takoya mata abubuwa dayawa.

Bayan magrib duk suna zaune a falo imran na jikin ta yana wasa itakuma tai shiru tunanin baba take dayanzu fa suna hanyan dawowa daga gareji, sallaman dad sukaji mum ta tashi ta rungume shi, amma gabaki daya hankalinshi yanakan shukra, ture mum yayi daga jikinshi yakarasa cikin falon da sauri ganin shukra dayayi cikin damuwa ya tsugunna gaban shukra,

Murya kasa kasa yace shukra baby?? Menene?? Meke damunki?? Hj taimiki wani abune?? Kifadamin dan wlh bazan bari wani yatakura miki a gidanan ba yana maganan yana kallon fuskan mum da alamun da ita yake.

Shukra ta girgiza mai kai, yace to Menene yayanki thariq kikeson yadawo?? Ta dagamai kai, yakara kwantar da murya yace karki damu ran sati zaizo kinsan banason ganin ki cikin damuwa, imran dayaga dad yadane jikinshi dad ya dakamai tsawa kai bakaga ina magana bane?? Imran yatashi yana kuka yaje ya rungume mum,

Dad ya fito dawani kwali acikin ledan daya shigo dashi ya mika mata adan tsorace ta karba yace kinga wanan wayan takice, nasamiki layi da komi aciki, kinga ai zai debe miki kewa, banason ina ganinki cikin kunshi kisaki jiki kiyi walwala kinji.

Tace to Nagode, yace yauwa shukra baby, oya tashi muje kici abinci yarike mata hannu da sauri ta fizge hanunta, taje wurin mum tace mum kinga wayan da dad yasiyomin, ita shukra bata lura da yanayin mum ya chanza ba, mum tai yake tace Allah sanya alheri taja hanun imran suka bar falon.

Maman shakur 😘
[05/11 7:57 PM] Aishat muh’d: TAWA CE!!!

2⃣2⃣
Tana shiga daki ta lallaba imran yay bacci, babu abunda take furtawa sai INNALILLAHI, wai mai alh ke nufi ne?? Maisa zai nuna bai damu da ita da imran ba saboda shukra?? Kodai alh son shukra yake?? Danna lura da yanda yake Kallonta da yanda yake shiga cikin damuwa dazaran yaga shukra bata cikin walwala.

To maima alh zaiyi da yarinyan 16 years?? Girgiza kai tayi tace hj karki kai zuciyanki zuwa wurin, alh bason shukra yakeba, kawai tausayinta yake saboda ita marainiyace, takara cema kanta, komin tausayin dayakema shukra baikamata ya ture imran yana mishi oyoyo ba ai, kawar da tunanin tayi tacema kanta alh bason shukra yakeba, karki kuskura kifarajin haushinta kindai riga kindau alkawari zaki kula da ita, tashi tayi dan takoma falon batason shukra tai zargin wani abu.

Tana zuwa falo ta tarar alh shikadai yana danne danen computer tace alh ina shukra?? yace tatafi ta kwanta suka danyi fira daga bisani suka dunguma dansuje su kwanta.

Yau takama monday, babbar rana ga ma’aikata, babbar rana gayan makaranta, haka kuma takasance babbar rana ga shukra, ta shirya cikin uniform dinta blue wando, pink din hijab karami sai riga pink amma mai gida gida pink da blue. Mum kanta tsayawa tayi tana kallon shukra dan tai bala’in kyau kaman wata yar India dad kuwan kasa rufe bakinshi yayi, imran yace wlh aunty kinyi yau kaman kajool.

Suka shirya dad yarakosu har wurin da driver yake tsaye dad yacema driver karka sake kabatama shukra rai, duk abunda tace tanaso kayimata, inhar kabata mata rai to wlh abakin aikin ka. Driver jiki na rawa yace to alh, suka shiga cikin mota sukabar gidan, Nazir na cikin motanshi a anguwar kaman ance yadago kai yaga shukra shi agaban mota sun fito, wani ihu dadi yayi yace ke TAWA CE ya kunna mota yabisu.

Maman shakur 😘
[05/11 7:57 PM] Aishat muh’d: TAWA CE!!!

2⃣3⃣
Shukra suna cikin tafiya tahango wata makauniya tana tafiya ga kwata agabanta, kuma takusa karaso wa, a rude tacema driver tsaya yako parka motar gefen titi. tafito da sauri, Nazir na cikin binsu yaga motar ta tsaya shima ya tsaya yana kallon inda shukra tayi.

Shukra na kaiwa ta daga murya tace babba tsaya inzo karki fada kwata, tai maza taje ta tsallakar da makauniyar aiko tadingama shukra godiya, duk abunan a idon Nazir abu daya daya lura shukra nadashi shine tausayi ga yawan taimako, murmushi yayi yace yawan taimkonki ta hanyar kadai zanjaki jikina kashe motan yayi yafito ya tsugunna yana leka kasar motanahi kaman wani abu yabaci,
Shukra tajuyo kawai tahangoshi tana ganinshi taganeshi, hartaso takoma mota saikuma tafasa takarasa wajen cikin sanyin muryanta tace motan ya lalace ne?? tunda yake baitaba jin murya mai dadi irin tataba, cikin muryan damuwa yace bansaniba ina cikin tafiya kawai tamutu, shukra tadan dudduba motan taga babu wata matsala tace shiga ka kunna motan naga.

Ya shiga yatada motan tako fara aiki, yace kinga motan tana ganin kakkyawan fuskanki tafarayi, shukra tamai murmushi, hango irin wayan ta tayi a cikin motarshi tace laaaa kaima kanada irin wayata iPhone 6, murmushi yayi yace haba ina taki?? Tace yana mota yace kawo nagani da gudu ko taje takawo mai ya karba yasa number shi yay flashing nashi, ya kalleta kinada kirki kin yarda zaki zama kawata?? Ta rufe ido babana yahanani yin kawaye, yakama baki oooo to naji, zan dinga kiranki awaya mu gaisa ko? tace to dama babu wanda ke kirana, Yace amma maisa zakije da waya school?? Tace wlh mantawa nayi nafito da ita yace okk yi sauri kitafi karkiyi latti tamai murmushi harda dagamai hannu ta shiga mota driver yaja.

Nazir ya shiga mota yay wani ihu inda akwai abunda ya lura game da shukra shine yarinya ce, gata batada wuyan sha’ani yasan bazaisha wahala kantaba wani dariya yayi ya rungume kanshi yace ke TAWA CE shukra.

Maman shakur 😘
[05/11 8:00 PM] Aishat muh’d: [05/11 7:58 PM] Aishat muh’d: TAWA CE!!!

2⃣4⃣
Cikin yan kwanaki Nazir yakoyama shukra sabodashi, duda dai bai taba zuwa gidanba, amma kullum suna waya, tana gane karatunta sosai dazaran sun dawo sutafi islamiyya.
Bangaren dad kuwa ayanzu yafarakai mum jikin bango dan dazaran yaga shukra ko kallon kirki bayama mum da imran, ita shukra yarinta yasa bata lura da yanayin zaman da dad yake da mum ba, dazaran dad yafara damunta da firanshi zata mike tace zatai bacci. kullum saitai tunanin thariq gashi yau kusan 2 weeks da tafiyanshi bai dawoba yace aiki yamishi yawane a clinic saisa.

Yau takama Friday bayan sun dawo daga makaranta taje tataya mum aiki, da daddare taje dakinta danyin assignment tana cikin yi Nazir yakira sukasha firansu daga bisani sukai sallama, tacigaba da assignment din jitayi A.c. yamata sanyi dayawa ta tashi takashe tacigaba da assignment har bacci yay awon gaba da ita a wurin.

Wuraren 11 mum tace alh haryanzu baka gama recording files din a laptop din bane muje mu kwanta, yace wlh haj kije ki kwanta sainagama zan shigo tamike taimishi saida safe ta tafi yacigaba da aikin.

Dad baigamaba sai wuraren 2 nadare, daidai lokacin shukra zafi ya isheta dama haka take batason zafi, kuka tafara tana buga gadon da hannu babana wlh katashi zafi zai kasheni, babana wlh katashi nace, kuka take sosai amma idonta a rufe, dad harzai shiga daki yaji kukan shukra babyn shi ai a dari yay dakin.

Yana shiga yaga tana kuka tana laluben gado da hnunta tana babana katashi zafi zai kasheni ka fifitani dad da sauri yakarasa ya kunna a.c. ya zauna kusa da ita kan gadon yana shukra daina kuka na kunna miki a.c., dago kanta tayi ta daura kan cinyan dad tace babana zafi nakeji, daga haka tacigaba da baccinta, shikuma dad yasa hannu ya dinga shafa gashin ta daya zubo har tsakiyan bayanta.

Mum kaman an mintsileta ta tashi ta kunna wuta taga dad bai shigoba sakkowa tayi tafito falo still bashi ta rude to ina alh yashiga??, harta wuce bakin kofan shukra saitaga alamun wuta a kunne, tsaki tayi shukra da wauta tai bacci bata kashe wutaba tabude dakin dan takashe wutan maizata gani???

Maman shakur 😘
[05/11 7:58 PM] Aishat muh’d: TAWA CE!!!

2⃣5⃣
Gani tayi dad na shafa kan shukra, ga shukra daga ita sai dan wani figigin rigan bacci pink kuma transparent, alh shi harya soma gyangyadi baimasan da shigowan mun ba, mum wani kuka kura tayi ta finciko shukra daga kan cinyar dad ta hada kanta da bango, dad a zabure yamike, itako shukra tabude ido taji zafi tafashe da kuka mum menayi?? Dan Allah kiyakuri, mum ta kifa mata mari dukanta take tako ina, alh ne ya fizge shukra daga hanunta ya hankada mum tafadi kasa, shukra takara kankame dad,
Hj tace nika ture saboda yar iskan yarinyan nan?? Takara yo kanta dad yace wlh inhar kika kara dukanta abakin aurenki, hj tabude ido tana kallonshi, wato alh saboda kasamu swt 16 nikakema wulaknci, tunda yarinyar nan tazo gidanan kadena kulani, kana wani basar dani, dama a jikinta kake samun abun ko??yanzu dakuka gama shine harda daurata kan cinyanka kana…. Wani mari yakaima mum maikika maidani mazinaci kome?? Banyi zina tun inada kuruciyataba sai yanzu?? itadai shukra kuka take sosai dan bata gane maganan dasuke bama, kuma batasan meya kawo mum da dad dakintaba, kuma tarasa maiyasa mum maisonta take dukanta yau, mum zata kara magana alh yace bar dakinan tai kwafa tawuce tafita.
Tana zuwa daki takira thariq ranan yana nyt duty yana dauka yaji muryan mum a hargitse thariq kome kakeyi kabarshi kataho kano gobe, is an order thariq kazo gobe gobenan kuma dasafe ahankali yace to mum.

Alh yace shukra baby dena m
kuka kwanta kiyi baccin ki, ya kwantar da ita ya lulubeta da bargo yabar dakin, bacci yaki zuwan mata, maitaima mum tadaketa?? Kanta ne taji yana ciwo ta dinga kuka sosai tana kiran babana kadawo har bacci yay gaba da ita, da safe takama Saturday da kyar ta iya salla saboda ciwon kai gawani irin ciwon mara datakeji kaman ta mutu, fitowa tayi taga mum a kitchen taje dan tatayata mum ta mata tsawa, yar iska ashawo bar kitchen dinan kafin na kasheki da wukan nan, alh da sauri yafito haryana tuntube yacema shukra tafi daki shukra baby sumi sumi tatafi.

Mum tana gama abinci tadau key din mota tabar gidan dan taje tafadama kawarta me ake ciki, itakuma shukra imran yazo yajata sukaje garden tana zaune zazzabi takeji sosai jikinta zafi kaman wuta ga ciwon mara tamaji alamun jini yasoma zuba but bataga fuska tambayan mum always ba.
Dad ne yafito kallon daya yamata yagane tana zazzabi riko hanunta yayi shukra tashi mushiga ciki kishi magani tana mikewa tayi baya zata fadi saboda jiri datake ganin dad ya dauketa chak imran zai bisu yace kai zauna karka dameta. yakaita dakinshi ya shimfideta kan gadonshi yacire mata hijab….

Mum tayi kwanar fita daga anguwarsu taga motan thariq tare suka dawo suna shigowa sukaga imran. da gudu imran ya rungume thariq, thariq yace ina shukra,imran yay dariya yace wlh dad yazo yadauketa kaman wata baby jaririya, yakaita ciki kuma yace karna bisu bayason nadameta, Mum da gudu tayi cikin gida thariq yabi bayanta tare suka shiga dakin dad suna budewa sukaga dad yanama shukra……
Ku biyoni dan jin mai dad yakema shukra babyn shi😜

Maman shakur 😘

mamanshakur Is all about novels.
Skip to content
Home
About
TSAFI 1to 11
← TAWA CE!!! 21 to 25TAWA CE 31 to 36 →
TAWA CE!!! 26 to 30
Posted on November 6, 2015 by mamanshakur
[06/11 7:59 PM] Aishat muh’d: [06/11 7:08 PM] Aishat muh’d: 🌿🌿🌿TAWA CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
2⃣6⃣
Dad suka gani ya rungumo shukra wanda ga dukkan alamu tama suma jikinshi yana kokarin zage zip din riganta, gefenshi kuma wata yar karama bowl ce tana dauke da ruwa dakuma towel a ciki.

Hj zama tayi a wurin tana kuka sosai tace thariq kaga halin ubanka ko, wanan yar iskan yarinyan da aka baka amana ta kwacemin mijina, daga fitana har sun dawo daki, Alh Kallonta yayi yay tsaki yana kokarin zage zip din thariq alokacin yasamu bakin magana dad wot are u doing??

Dad yace dan uwarka karka cemin kala, kasan duk harda damuwarka taima yarinyan nan yawa yasa take rashin lpy, yarinya kamata alkawari sati daya zakayi kaje kaine harsati biyu thariq ka kiyayenifa, yau tan safe yarinyar nan ke zazzabi, uwarka na Kallonta taki bata magana takama hanya tafita yanzu bakaji jikinta ba kaman gidan biredi, to wlh nagaji yanda na tsani mutuwata haka na tsani naga shukra cikin damuwa to gwara na aureta kawai hankalina zaifi kwanciya,
Mum ta mike tsaye alh yanzu son shukra kake?? Aurenta??yarinyar dakayi jika da ita, cikin tsawa yace eh sonta nake, shukra TAWA CE aurenta zanyi,

INNALILLAHI shine abunda thariq ke ambata azuciyanshi,ya dafe kujera ya sulale kasa, mum tace wlh indan kaga ka aure shukra to saidai inbanda rai, wlh zan halaka yarinyar nan, thariq lura yayi kaman shukra bata numfashi yasa yakarasa ciki da sauri yataba jikinta kaman garwashi, daukanta yayi chak yafita da ita daga dakin dayaga fadan mum dana dad ba karewa zaiyiba, dad yabiyoshi da gudu thariq ina zaka kaimin shukra baby?? A hasale yace zan kaita side dina akwai kayan aiki achan inason nabata allurai da magani ne, dad yace to, plz ka kulamin da ita sosai nai baki a office bari naje nadawo bazan dadeba baima amsama dad ba yawuce.
Dad shikuma yakama hanya yabar gidan sukabar mum na sumbatu a wurin.

Maman shakur 😘
[06/11 7:15 PM] Aishat muh’d: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
2⃣7⃣
Thariq yakaita dakinshi ya shimfideta kan gado yana dago hanunshi yaga duk ya baci da jini zuwa yayi bayi ya wanke hanunshi, yashiga bata taimakon gaggawa harta farfado, yace shukra maike miki ciwo?? maranta ta nuna mishi da hannu,
yabata magani tasha yay mata allura tare da kara mata ruwa, mum ce ta banko dakin ta shigo tana ina ashawon take?? zoki barmin gida?? wlh wlh yau yarinyan nan bazata kwana a gidannan ba, thariq najin muryan mum yafito da sauri yatareta a falo,

Yace mum waime yake faruwane?? Mai shukra tai miki?? Ta balla mishi harara au bakama saniba banda wanda yanzu kagani da idonka, ubanka a dakin yarinyan nan yake kwana, zaro ido yayi yace wot?? Mum tace kadaiji, jiya da idona wlh na kamasu, tafashe da wani kuka maicin rai, yarinyar dana kula da ita, najata jiki kaman tawa amma take kwanciya da mijina, ganinta ma nayi akan cinyan alh wlh jiya Wuraren 2 nadare.
Idon thariq yay jajir neman wuri yayi ya zauna akasa yadafe kanshi da hannu biyu, maganan mum ce ta katse shi thariq inhar nina haifeka, inhar na isa dakai to wlh kadau yarinyar nan kubar gidanan yau, ka kaita wajen uwarta inkuma baka gantaba ka wurgar da ita, ni bukatana kawai ta nisanci mijina, ta nisanci gidanan.

Inba hakaba zan iya kasheta, ahankali thariq yace mum plz kiyakuri, kinga tariga tafara zuwa school, mum Amanata ce, kome tayi nariga nadau alkawarin, kuma bansan inda iyayenta sukeba babanta yacemin zamfara suke, amma baimin kwatance gidan ba, dan girman Allah mum kiyakuri .

Mum tace wlh wlh thariq zan tsine maka kuwa, kafison babanka yadawo tsohon banza?? Jibi yanda yahaukace kanta, nabaka minti biyar ku tattara kabar gidanan da yarinyar nan kafin babanka yadawo, just 5 min, or else i will do something dat both of us might regret it later, tai tsaki tabar dakin.

Maman shakur 😘
[06/11 7:21 PM] Aishat muh’d: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
2⃣8⃣
Mikewa yayi yana tafiya ahankali kaman kwai yafashe mishi a ciki yabi bayan mum, yana zuwa yaga tana fitomai da akwatunan shukra, murya kasa kasa yace mum kiyakuri dan Allah karki tsinemin, naji zankaita na nemo mata mamanta. amma Mum plz kidan bama shukra always wlh jikinta dukya baci bazamu iya tafiya ahakaba.

Wani mugun harara mum tamishi tace bazan badaba, kai ni ko sunan shukra na tsani ji kabarmin daki, wlh inka wuce 5 min zanzo na kashe yarinyar nan. juyawa yayi haryakai bakin kofa mum tace kuma in dad ya kiraka yace kana tare da ita kace a’a, kacemai kabarta a gida asibiti sun kiraka kanajinako?? Yace to mum.

Yana zuwa dakin yaga shukra na bacci kanshi yama kwance, haushi da tausayin shukra yake duka. yarasa yanda zaiyi gashi shukra dukta baci ga mum tabashi 5 min ko wanka zai mata bazai ishesuba, zuwa yayi yatashi shukra da kyar ta iya bude ido tashima takasa daukanta yayi yakaita bayan mota ya kwantar da ita, ya dauko kayanta yasa a boot, yakoma yace ma mum muntafi tace agais.

Yakoma mota yaja sukabar gidan, awani dan super market ya paka yasai mata pant da always yadawo yaja motan, gidan wani abokinshi yaje shima doc ne, but abokin nashi mai suna isma’il shima yana zaria. Yana zuwa gidan ya riko hanun shukra wanda da kyar take tafiya yana shiga

Please Login or Register in order to submit comment