Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

By


Sakeena ismail Cameroon
(Mom muwadda )




Page 37&38




Bismillahi rahmani rahim


_______tuki oncle Ibrahim yake yana tunanin inda zai fara nemo mai motar nn ,sai kawai yaji wayarsa na ringing yana dubawa yaga abokinsa ne yake kiransa,kamar bazai daga ba sai wata zuciyar" kuma yace mai ka daga mn kaji mai zaice maka dagawa yayi ya kara a kunansa sai yayi shiru,can bangaren kuwa naji ana cewa.. Hello a bokina kana jira..
Eh ina jinka Ibrahim ya amsa wai ya naga kwana biyu in na kiraka sai wani shan kamshi kake,abokin ya kuma fada.. kaga malam in bakada abin cewa ni zan kace,tsaya Ibrahim wai mesa kake min hakane wai ,mungama komai akan harkan nn kuma sai kazo ka kwapsa gaba daya ni da nasan haka zakamun da tun farko ban fara ba wllhy,ya bude baki zaici gaba da magana sai Ibrahim ya dakatar dashi,kaga malam ka rabu dani don allah ka barni nayi rayuwata "harka dai dama tun farko kaine ka zugani yanzu kuma nace ma nafasa ,ko ana dolene?kuma bari kaji daga yau sai yau kadaka kara kirana yana gama magana kit ya kashe wayan,


Bangaran abokinsa kuwa wani miskilin murmushi yayi ya shiga office dinsa
A zuciyarsa kuwa cewa yake sai na koya maka hankali Ibrahim danni ba'a fara aiki dani a bari indai an fara toh sai an karasashi,


Tada mota Ibrahim yayi ya bar wajan yana cikin tuki aka tsedasu a wajan danjaa, tsayawa yayi yana jiran a bada hannu
Yana tsaye ya lula cikin tunani har aka bada hannu bai saniba mutane sai faman yinmasa hone suke.
Ana cikin hakane ya dawo cikin hayyacinsa " yaga ashema an jima da bada hayya yana tsaye.tada motar sa yayi
Zai tafi sai ga wata mota ya tawo gadan_gadan shi baima kula da motar bama ashe tun dazu yake mai hone bai sani ba ,ga wani babban mota daya tawo
Kan titin bai kula dashi ba mai motar yayi mai hone har ya gaji Ibrahim bai kulaba "tahowar da motar zaiyi kenn sai ga Ibrahim shima ya tada motarsa zai tafi,sai kawai suka bige motar juna,amma na Ibrahim yafi nasa buguwa,saboda nasa glass din gaban motarne ya fashe...ai nan da nan mutane da yan sanda suka cika a wajan,daukarsu akayi aka wuce dasu a sibiti
Ana zuwa a sibiti aka shiga basu taimakon gaggawa,shi dayan ba wani rauni yaji sosai ba,shikuwa Ibrahim wann fashiwar glass din motarsa da yayi, a sanadiyar hakan ne gwalba ya shigan mai ido sai ammai aiki,


Matar barista ne zaune tare da minal walida kam tun lokacin da suka bar gidan su gaba daya rawuyarta ta janza,saboda yanzu ko hirama batayi, bata fita palo sai in saurayita ne kawai ya kirata zakaga murmushi akan fiskarta itta yanzu babban tashin hankalinta ma bai wuce rashin sanin halin da ma haifisu take ciki ba,ta kira wayarshi amma har yau bata shiga,tasan yanzukam anriga da ankashe musu ma haifi" yanzu shikenn suma sun zama marasu?


Tana cikin tunani wayarta ta shiga ringing sunn saurayinta tagani akan screen din wayan ai da sauri ta daga ta kara a kunne,gaidashi tayi ya amsa mata shikin so da kauna,sun dade suna hira sai daga baya sukayi sallama ya kashe wayan.
Mikewa tayi dan zuwa samowa kanta a bunda zataci dan tun safe tada karya batakuma cin komai ba har yanzu,gashi dare yayi,fitowa tayi zata wuce kitchen kienn ta hango momynsu zaune tare da minal suna hira su kam ko a jikinsu,itta abunma har mamaki yake bata yanzu kam zata iya cewa ma tsoro suke bata,ba mamaki ba.
Kai ta girgiza ta wuce kitchen,tana zuwa tea kawai ta hadawa kanta dan batajin zata iya cin wani abu ayanzu..fitowa tayi ta kuma wucesu,ta koma daki su kuna suka bita da kallo,


*India*




Bayan wata biyar
Jannat ce tsaye a kusada mirror tana shafa powda,ga waya makale a kunneta da dukkan alamu waya take..ta kara girma da kyau sosai fatarta ta kara haske sosai kamar ka tabata jini ya fito, blue wando da farar tishet ne jikinta tayi da farin mayafi tayi rolling din mayafin a kanta "tayi kyau sosai,


Magana naji tanayi,
Okay dear ganinn zuwa dan allah ki jirani nagama pls..tana gama magana bata jira taji mai wancan zatace ba ta katse kiran, back dinta ta dauka ta rataya tayi hayya fita babu kowa a palon da dukkan alamu dai ya nuna cewa su.aryan sun tafi school.
Su paa kuma sun tafi wajan aiki,rufe gidan nayi _nayi ayya waje a bakin kofa na hadu da arilin,arilin ta kansance kawatace mun hadu awajan zana jarabawa shiga University kuma alhamdulillah dukan mu
Mu biyun mun samu,a yanzu haka yaune ranarmu ta farkon shiga University "a yanzu hakama miyo min tayi mutafi tare dan su paa sun tafi nikuma bana son tafiya nikadai ,kasan cewa da motarta tazo,fitowa tayi muka rungumi zuna muna murna yau zamu shuga University,sai da kuma gama yin shanshancin mu tukun,sann muka shiga mota tajamu muka wuce school..


*kano* *Nigeria*


Anyiwa Ibrahim aiki kuma alhamdulillah anyi mai cikin nasara, amma har yanzu yana sa makin glass a idonsa "


Ya labarin matar matar barista?


A yanzu kam walida ta barwa allah komai dan yanzu kam tagama fidda rai akan mahaifinsu "yanzu ma tana zaune tana waya da wannn tsaurayin nn nata,mai suna Mahmud, Mahmud yana da kirki sosai,kuma gada gidan mutunci ta fito,su ba masu kudi mane amma suna da rufin a siri dai dai gwargwado,


Mahmud ya kasance Yaron barista ne,yana da yankali ga nitsuwa,yayi karatu addini dana boko alhamdulillah.


Kaga hubby na amince ka turo ayi maganar auran mu,yess naji dadi sosai masoyiyata "dariya walida tayi saboda tanajin sa tasan yana cikin farinciki,dan Mahmud ba karamin so yake mata ba,shiyasa itta ma take sonsa sosae..
Masoyiyata amma akwai mas'ala kinsan momynki bata son alakarmu,yanzu ya zamuyi,yayi magana alamar ya karaya,karka damu hubby ai momy ba itta zata dauramin aure ba, kaidai ka bar komai a hannuna nasan ta inda zan shawo kanta "kai dai kaje wajan kawu ka nemi aurena ,dan allah masoyiyata ? kai ta taga mai kamar yana ganinta,
Alhamdulillah ya furta sai da suka tattauna sosai,sai daga visani sukayi sallama ya kashe wayan,ajiye wayarta tayi gefen gadon ta kwanta tayi shiru,ta san tsarai auranne kawai mafita,inyaso taci gaba da karatunta a can,tana cikin tunani baccin barawo yayi awan gaba da itta,


*India*


Muna fitowa daga lecture muka nufi wajan cafeteria ,ban san meyasa tun da muka muni wajan irjina yake bugawa,dan dakadar da tafiyan da nakeyi nayi arilin ta juya tana kallo na,jannt"ya naga kin tsaya kuma,mukarasa mana,ba cewa kikayi yinwa kikeji ba?kallon arilin nayi kinga arilin kije kawai na fasa zuwa,wllhy baki issa ba sai da muka zo wajan sannn zaki cemin kin fasa, Dalla malama kixo muje,in ke bakiya ci ai ni ina ci ,jan hannuna tayi muka shiga ciki ,kamar yanda nake taku hakama irjina "yake kara harbawa,har muka karasa ciki muka zauna,muna jiran a kawo mana lis din abincin da suke dashi, ba'a wani jima sosai ba,sai ga daya daga cikin ma aikatan taxo,mika mana takardan tayi wai muduba abincin da mukeso a kawo mn,ni Dayake hankalina "baya cikina ko takan lis din ma banbi ba,


Zaune yake shi daya yana shan coffee,za wayarsa a hannu yana dannawa,dagawan da zaiyi Kenn ya hangota,tana zaune ta zuba uban tagumi,dayayi kamar zai dauke idonsa sai ya kasa,dan tayi mai mugun kyau yau,a jiye wayarsa yayi akan table din dake gaban sa,ya maida hankali sosai wajan kallon ta ,itta ko jannat "sai da arilin ta zabar musu a bincin,da aka kawo ba kadan taci ba deyewa ba,


Kinga arilin tashi mu tafi.
Ahaka dai itta ma arilin ta hakura da abincin da takeci ta mike,


Duk a bunda suke yana kallon su bai san sanda murmushi ya kubce masa ma,yana ganin zasu bar wajan, titshu ya zaro ya goge bakinsa ya tattara wayoyinsa da mukullin motarsa dake kan teburin,yabi bayansu....




Hahaha su jannat an hadu da masoyi 😂za'asha love ❤️🥰💃💃💃🏃‍♀️


Sakeena ismail Cameroon✍️


Comment and sharee pls
[8/29/2023, 1:49 PM] Mom Muwadda: 🧝‍♀️MIJIN ATTAJIRA 🧝‍♀️




By


Sakeena ismail Cameroon
(Mom muwadda)




Page 33&34




Bismillah rahmani rahim


*india*


______washe gari,tunda natashi ban koma ba kitchen na shiga nahada mana breakbeat,ina cikin gyerasu kan dinning sai ga maa ta fito ,gaidata ta nayi ta amsa cikin tsakin fuska,sai ta fara magana.. Jannat ke dai bakiya gajiya ko kadan,yanzu duk gajiyar nn da kika kwaso jiya amma sai da kika tashi da wuri kika hada mn breakfast..
Haba jannat "ki dinga wutawa mn kinji? murmuchi na danyi nace..ai maa gajiyan ya tafi shiyasa nace bari nahada mana breakbeat kafin na wuce school,zata kuma yin magana nayi tsaurin jaa mata kujera,zama tayi tana dariya,muna cikin hakane paa,mr ali haka yayanta suke ce mata shiyasa nima nake kiran shi da paa din,gaidashi nayi ya amsa ya jaa kujera ya zauna, abinci na zuba musu,na juya...
Jannat 'ina kuma zaki?
Paa ya tambaya,amsa na baza..zanje na tashe su aryan ne nayi musu wanka sai muwuce school...kafin paa ya kumayin magana..maa ta amshi zancen wllhy dear tun safe ta tashi bata koma ba tana ta aikin breakfast da gyaran gida..nayi magana tace itta bata gaji ba,yanzuma nasan bata bakinka kawai kake amma bazataci abinci yanzu ba,paa ya daga zai Kuma min magana sai yaga wayam babuni a wajan...dariya maa tayi tace kagani ko?ai dama nafada maka,saboda nasan bazata iya maka musune shiyasa ta paki idonka da taga baka ganinta "sai ta gudu,dariya yayi shima,sai suka soma cin a binci.


Ina shiga dakinmu dani dasu aryan tashisu nayi _nayi musu wanka na shiryasu cikin infom dinsu,ina gama shiryasu.
Na kalli aryan tunda shine babba,nace musu su tafi Palo suje suyi breakfast kafin na shirya nima toh ya amsa min,ya kamo hannun nihila suka wuce palo,


Wanka nashiga ban dau lokaci sosai ba na fito daure da tawul,mai na shafa da turare,shiryawa nayi cikin infom dina nayi kyau sosai har na gaji, powda na shafa da lipstick,sai Gashina danayi barking dinshi a sakiyar kaina, na dau bandana mai kalar infom din nawa na saka shima,kasan cewa ba'a saka hijabi,nayi kyau sosai in kaganni zaka dauka nima yer indiyan ce Cambodge dina na saka, school back dina na rataya nayi ayyar fita..
Ina zuwa palo kujera na jaa na zauna nima,na karya,muna gama karyawa muka wuce gaba dayanmu"saida muka ajiye maa a wajan aiki sann aka wuce damu muma,su aryan aka ajiye saboda school dinmu yafi nasu aryan nisa,nice a karshe,paa na ajiyeni shima ya wuce nasa aiki.


Jarabawa mukayi na shiga jamiya kuma komai ya tafi dai dai,sedai muce allah ya bamu sa'a...da wuri muka gama komai dan haka ban jira paa yazo daukana ba,motar haya na hau na koma gida dan hada mana abinci kafin su paa su dawo,duk da maa na hanani,aiki in na dawo daka school,


School back dina kawi na ajiye sai na shiga kitchen na hau girgi...




*Kano Nigeria*


Barista na jiye jannat" a airport wajan saida SIM card yaje ya siyo,daga nan gida ya koma..yana zuwa wanka yayi _ya kwanta kasan cewa ya rigada yayi Sallah isha'a ,




Wajan karfe biyun dare mutannn suka koma gidan barista"suna zuwa suka tadda komai a rufe.
Haurowa sukayi suka shiga.suna shiga sukaga babu barista babu alamarshi"wani murmuchi sukayi da sai su kadai sukasan ma'anarshi,fita sukayi suka bar gidan,suna fita wata number suka kira ana dagawa naji yana cewa kaga ka duba wayarka akwai wata number dana tura ma kayi mun tracking number din ...yanzu ina jira,yana gama fadar haka ya kace wayan,
Shiga motarsu sukayi suka bar gidan,


Gidan barista.
Cikin bacci yayi ma farkin wayenn mutann sunzo gidan sa, ai yana farkawa ya tashi matarsa "ya sata taje ta tashesu yayanta,yana gama hadasu,ya fara magana kamar haka..kinga lubabatu kuyi hakuri,naso mu rayu tare amma hakan bazai yuba nasan mutann bazasu barni ba,a yanzuma hakan mafarkinsu"nayi sunzo gidann,ki tattara yayanki ku gudu,wani jaka maga ya dauka ya mika bata,karbi ga wann kuyi anfani dasu kisiya muku gida kisasu a amakaranta "in sunyi karatu sosai sun gama nasan suma zasu taimakeki"kuyi tsauri karsu zo,bama sai kun dau komai naku ba,dan in kunce zaku dauka,zasu iya zuwa su sameku..ku tafi ?


Kai fah mai gida ?
Karki damu dani.in nace zam biku mu tafi toh bazasu taba barinmu ba,kudai kuje kawai.
Inyaso in inada tsauran rai zan nemeku insha allah.kuje.


Mikewa momy tayi jiki babu kwari su walida kam babu a bunda suke sai kuka...gonin ban tausayi.
Sai da hajiya lubabatu ta leka wajan taga babu kowa,sann suka shiga mota ta jaasu suka bar gidan har suka hau titi basu daina kuka ba.itta kanta hajiya lubabatun kuka takeyi..


Tuki take amma batasan inda jasu ba.


Bayan yen mintuna kadan saiga wanda ya kira dazu ka kirshi.dauka yayi ya kara a kunne, bansan me mutumin yace mai ba sai kawai ji nyi wana dariya,magana ya farayi..yauwa nagode guza aikinka na kyau,sai kajini..toh oga ya amsa sann ya kashe waya,


Gidan barista
tun tafiyarsu iyalansa bai samu ya koma bacci ba,Kawai jira yake yaga ta inda mutann zasu shigo,bai gama tunani ba yaji ana bugamai gida,
Kasa tashi yayi yana zaune a inda yake,ga wani sufa sai ketomai yake kamar babu AC a dakin..






Sakeena ismail Cameroon ✍️






Comment and Sharee pls
[8/29/2023, 1:49 PM] Mom Muwadda: 🧝‍♀️MIJIN ATTAJIRA 🧝‍♀️




By


Sakeena ismail Cameroon
(Mom muwadda )


Page 39&40




Bismillahi rahmani rahim


_______"Suna fita daga cikin cafeteria din cikin makaranta suka koma saboda suna da lecture karfe 1 yana ganin haka ya koma wajan motarsa ya shiga ya kunna AC ya dau daya daga cikin wayoyinsa "ya fara dannawa


*Jannat*


Bayan sun fito daga lecture suka nufi wajan
Aje motoci,kasancewa motarsu yana gaba da tashi shiyasa sai da suka wuce ta inda yake sann suka karasa inda sukayi parking,bude mota sukayi zasu shiga su tafi sai sukaji ana cewa..hy basu juyaba saboda basuyi zato dasu yake ba sai da ya kuma cewa.Hy beauty "sann suka juya a tare dan ganin waye,wani tsaurayine suka gani fari dogo kekkyawa "sanye da kananun kaya,ya nufesu juyowa sukayi suna kallon_ kallo, jannat na kallon arilin _arilin na kallon jannat "kowa da abindake cikin zuciyarsa"har ya karaso.jannat bata sani ba,itta dai arilin ta ganshi,a zuciyarta kuwa sai cewa take allah yasa wajanta yazo,bata karasa zancan zuci ba taganshi yana wa jannat mgn beauty baki ganeni ba?
Kallonsa nayi ,ina tunani inda na taba ganinsa amma na rase ina,dan dagowa nayi muka hada ido nayi tsaurin sunkuyar da kai saboda ya min kwarjini deyawa, I'm sorry
Bangane ka ba,nadai taba ganin fuskar ka amma na manta a ina ?
Sai Kuma nayi shiru ina tunani inda na taba ganinsa amma wllhy na manta ,na kasa tunawa...
Yanzu jannat "ko kamshin turarena baki gane ba, tinda har hankicif dina na baki kika share hawayanki in bammanta bama sanda kika bani harda majina nagani ajiki murmushi yadan saki ya kuma daure furka yaci gaba da magana kamar bashi yayi murmushin ba, amma yanzu kiri _kiri kikace baki ganeni ba ,ai shikenn, nikam duk kunya yayi sheni tin sanda yayi zancan majina,daker na iya bude baki.. I'm sorry kayi hakuri sai yanzu nagane ka,dama kaine?aa bani bane yayi magaa yana sakin murmushi,nima murmushi nayi dan maganarshi" ya bani,kaine mn dama ba a nn garin kake ba nayi mgn?kai ya geda min alamar eh..
Toh amma ya naji ka iya hausa, uhummmm ba ann aka haifeni ba,kai kawai na geda mai dan bnaso sakin jiki deyawa da wanda bansani ba ..


Kefah ya tambaya,ni ba'nan nake ba karatu ne kawai ya kawoni kuma ina gamawa zan koma kasata na bashi amsa, amma in dai kin samu miji ann zaki zauna ko yakuma jefa min tambaya
Shiru nayi kamar bazam bashi amsa ba sai kuma na bude maki nace aa bazanyi aure ann ba a can kasata zanje nayi aure na nayi magana,ai najeeb bai san sanda irjinsa ya buga ba danjin amsar data bashi amma ya dage zai bude baki ya kumayin magana.. sai arilin ta kasesu tace..humm jannat kenn tinda baki shirya tafiya yanzu ba ni bari na tafi gida.. jannat zatayi magana arilin ta bude murfin motarta ta shiga ta jaa motarta_ tayi tafiyar ta,ta bar jannat da najeeb baki a hangame saboda mamaki,toh me abun fushi nn itta bataga abin fushi ba,itta ko arilin badan komai tayi hakan ba ,saboda ta dauka wajanta najeeb yaxo,sai kuma taga akasin haka..dan tinda ya karaso wajansu ko kallo bata isheshi ba,suka tsaya sai hira suka,shiyasa taji haushi ta tafi.


Tafiya jannat ta farayi ko sallama bata saya yiwa najeeb ba ,Dan gani take kamar shine ya jaa mata har arilin ta tafi ta barta,da gudu ya sha gabanta me haka beauty taya zaki hau motar haya bayan ga motata,kixo muje na ajiyeki,ka barshi na gode.zanci gaba da tafiya yayi sauri rike min hannu wani yarrr naji dan tunda nake babu wani da na mijin daya taba rike min hannu sai yau ,kallon hannun nawa daya rike nayi na kuma maida dubana gareshi.kaga pls ka sakarmin hannu,ai kamar ma badashi nake ba,dan babu ko alamar zai sakeni,danaga dai sai batamin lokaci yake na ce mai muje kawai..tafiya ya farayi rike da hannu na ,muka nufi wajan motarsa' muna zuwa gaban mota ya budemin
Amma yaki sakin hannuna sai da nayi mgn sann ya sakeni..shiga nayi ya rufemin murfin motar ya zaga ta ma zaunin driver ya shiga ya kunna motar yajaa muka tafi,da taimakon kwatance danake mai har muka karaso gidanmu,ko kallon inda yake banyi ba na rike murfin mutar zan bude nafita sai yayi magana..haba beauty yanzu ko sallama babu zaki wuce ballantama in samu godiya,dan juyowa nayi na kalleshi.na gode sosai sai anjima,ban jira mai zaice ba na balle murfin motar na fita na rufo mai,shima fitowa yayi,ya zaga ta inda nake sayi ya mikamin wayarsa"karba nayi ina jiran karin bayani,samin number dinki ban san meyasa na kasa musa mai ba,saka masa number dina nayi nabasa wayarsa ..har na shiga gida yana saye,


Shi kuma najeeb sai da yaga shigowarta gida sann ya juya ya shiga motarsa shima yajaa ya wuce gidansa,


Da daddare nayi shirin bacci ina kwance,nayi shiru,yau in bam banta ba nafi wata biyar banyi waya da barista ba,da kuwa in andan kwana biyu in ya kira yana cewa paa ya bani,amma yamzu shiru nasan kuma sarai bariata bai taba kai wann lokaci bai ce paa ya ban waya ba.daya kira paa na tabbata zai bani muyi magana,yanzu ana nufin dawowata bai kira ba kenn?ina gaskiya aa,ina cikin tinani naji wayata na ringing dubawa nayi naga bakon number ne.kamar bazan daga ba sai wata zuciya kuma yace ki daga mn jannat kiji ko waye kilama barista ne,ai da tsauri na daga na kara a kunnena..






Sakeena ismail Cameroon ✍️




Comment and sharee pls
[8/29/2023, 1:49 PM] Mom Muwadda: 🧝‍♀️MIJIN ATTAJIRA 🧝‍♀️


By


Sakeena ismail Cameroon
(Mom muwadda )




Page 41&42




Bismillahi rahmani rahim


______yana kwance saman bed dinsa yaji tayi sallama da wann muryarnn tata mai dadin ,amsa mata yayi.. walaikum salam beauty ko kin fara baccine na tasheki ?kai na_ na girgiza kamar yana ganina.abun mamaki sai naji yace nifah banason girgiza kai da kikeyi ni baki nake son kibude kiyi magana,ba kai ba.. sorry ya kaje gida? alhamdulillah ya amsa , jannat " ya kuma kiran sunn,naam nasan baki sanni ba baki san ko waye niba sai lokacin da muka hadu a jirgi kika fara ganina,nima na fara ganinki, yanzu insha allah zaki san kowaye ni..nikam nayi shiru ina tsauraransa"da farko dai sunana najeeb Ahmad ni haifaffan garin kano ne amma ba a kano nayi girma ba saboda tun sanda Allah yayiwa ma haifina rasuwa muka bar Nigeria,kasan cewa ma haifinane kadai dan kasar Nigeria,ma haifiyata "yer Saudia ce,acan iyayenta suke,sanda mahaifina yaje kasar Saudia ne suka hadu da ma haifiyata, har soyayya mai karfi ta kullu a sakanin su ,saboda son da takeyiwa ma haifinane yasa ta yadda ta aure sa suka dawo Nigeria,duk da kuwa iyayenta bason barinta ba, kawai saboda itta kadai suka mallaka shiyasa suka dauki son duniya suka daura mata,shiyasa suka yadda ta auri Dady na,
Bayan wata bakwai allah ya azurtata da samun juna biyu,ai in na gaya miki murnn da sukayi ma bata lokaci ne,bayan wata tara ta haifo danta na mijin kekkyawa kamarsa daya da ma haifiyarsa fara sol kamar ba larabe ko kuma ince balarabe nema tunda uwarsa ba larabiya ce,
Ranar suna yaron yaci suna najeeb ! najeeb nada shekara goma kacal a duniya allah ya dauki ran Alhaji Ahmad (Dady) na kenn,sakamakon hatsarin da sukayi dashi da abokann sa,munyi kukan rashinsa sosai saboda ina da wayau sosai a lokacin saboda nasan in mutun ya mutu ba dawowa yake ba, shiyasa da naji ana zancan mutuwa nima nayi kuka.bayan ma haifiyata ta fita takaba ne ma haifinta yace lallai zamanta a can bazai yuba,tun lokacin da muka koma Saudia,aka samomin makaranta naci gaba da karatuna ..
Gaba daya naji banason kasar saboda na saba da Nigeria a bokanaina duk suna can,sai da aka kwana biyu sann na sake..


Idan minyi wutu ummina na daukana ta kaini wajan kakannina na wajan uba,har naxo nakai girman da zan iya zuwa da kaina wajansu "wnnn haduwar da mukayi a cikin jirgi ma daga wajansu nake,


Tun lokacin daya fara magana nayi shiru ina jinsa sai yanzu dan sauke ajiyar zuciya nayi,har yana iya jiyowa, jannat"wann karan kam ban amsa mai ba.bai damu ba yaci gaba da cewa,jannat kinsan da lilin dayasa nake baki labarina daga haduwar mu,aa sai ka fada..saboda tun lokacin da naganki a cikin jirgi naji kin kwanta min arai.naji duk duniya babu wanda nakeso na aura sama dake,na yaba da nitsuwarki da hankalinki sosai jannat "saboda a kullun bani da burin daya wuce na samu bace ni tsassiya mai hankali da nitsuwa duk da karancin shekaru na amma in har kin amince dani jannat "ko a yau zaa iya daura mana aure,saboda in nace zan jira shekarun da nakeso nayi aure a baya zaa iya kwace min ke,zan iya rasaki jannat,pls jannat karkice bazaki aureni ba,ki taimaka min ni kuma nayi miki alkawai zan barki kici gaba da karatunki har sai kingama,zan kaiki a miki alluran hana haihuwa saboda karki haihu da wuki har sai kin kammala karatunki,humm malamin soyayya ka bari sai nayi tunani kaga dai yaune haduwar mu ta biyu,kaga kuwa muna da bukatar sanin juna sosai..toh naji amma dan allah ina so kice eh kin amince da soyayya ta,kai dai ka bari in lokaci yayi zan fada amma ba yanzu ba ka dan bani lokaci.. okay naji zam baki lokaci Amma inso ki bani labarinki da kuma abunda yasaki kuka cikin jirgi rann dan murmushi nayi nace..waca irin labarina kakeson ji ?koma wace iri nidai ki bani kawai.. okay na fada, labarina na kwashe komai na bashi.
Najeeb yaji tausayina sosai..sai yaji son jannat ya kara ninkuwa akan na kwanakin baya, sanda suka hadu, sorry my beauty gaskiya na tausaya miki sosai..nidai ban ce mai komai ba sai kuka nake,ji nake kamar yaune iyayena suka rasu saboda komai naji ya dawomin sabo.daker ya samu ya rarrasheni wanna din ma cewa yayi in har banyi shiru ba zai iya zuwa gidammu shiyasa nayi shiru na dena kuka.saidaya tabbatar na dena kukan.sann ya kwantar min da hankali, sallama ya min ya kashe wayan,


*Bayan sati daya*


Soyayya mai karfi ya kullu sakanina da najeeb "najeeb mutunne mai barkwamci da kuma tsaukin kai.
Yana nunamin tsantsar soyayya ga kuma kulawa namu samman,sati daya kawai mukayi dashi amma ba karamin shakuwa mukayi ba...


Zaune mike a kan dinning muna breakfast Amma hankalina gaba daya baya wajan bama a bincin nakeci ba.paa na lura da itta dan tunda ta zauna ta saka hannu cikin a binci amma bayan loma daya datayi bata kuma kara koda loma daya ba sai jujjuya spoon dake a cikin abincin"dan gyaran murya paa yayi..
Jannat !ya kira sunana ban amsa ba sai daya kuma kira sann nace.naam paa!meyake daminki?kai na girgiza alabar babu.dan murmusawa yayi.ya kuma kallona,ban yedda ba jannat da akwai a bindake daminki,ina son ki fadamin in har na isa.yayi magana ,wllhy dama akan barista Dady ne .zam bude bakina naci gaba da magana ya daga min hannu,na fahimceki jannat "ni kaina abine ya kwan biyu yana damuna amma insha allah zamuje Nigeria cikin satinn mu duba ko lfy,dan barista

Please Login or Register in order to submit comment