Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ke abuja,ga takardun kanfanin nazo dashi "yana mota,in na tashi tafiya sai kabiyoni mota sai ka karba"sauran ta kardunma insha allah zan kawo maka yau zuwa gobe insha allah.




Mikewa barista yayi,ni zan tafi sai na dawo goben,rakashi oncle Ibrahim "yayi har bakin mota"barista ya dau ta kardun ya mikawa Ibrahim"godiya Ibrahim yayi,sai da barista ya bar kofar gidan sannun Ibrahim ya koma ciki...


Uffam bai cewa jannat"ba,
Bayan tafiyar barista" mamace ta shigo,zaiyana mata komai, Ibrahim yayi mama taji dadin dukiyar da aka mallaka musu" sosai, zama sukayi suka dan tattauna ,




Sai daga baya Ibrahim"ya tafi kanfaninsa,tunda yanzu ya dawo mallakinshi"yau kam har wani jiji dakai yake "in angai dashi ma daker yake amsawa,




Bayan magarib jannat"ce zaune a kitchen tagama girki dare Kenn,tana zaune kome ta tuna naga ta mike falo taje,inda take ajiye kayanta"ta bude ta dauko wana abu aleda,tana kalle _kalle karsu mama su ganta "fitowa tayi daga falon ta koma kitchen din,zama tayi akan sallayan data shimfida,




Bude ledan dake hanunta"tayi sai ga karamin waya ya baiyana, dan dennawa tayi taga harda layi a ciki,


Tunani take ko maiyasa barista ya bata wannan wayan ?"babu mai bata amsa,






Dazune kafin ta shiga gida, jannat"har zata bude murfin mota ta fita" sai barista ya dakatar da itta "dan zuyowa jannat"tayi,tana kallon barista",






Karamar wayace barista ya mikawa jannat"ta karba tana kallonsa"kinga jannat"ki ajiye wannan wayan koda wani abu zai taso saiki sanar dani,karki bari kowa ya san da wayanan kinjiko?"gedawa barista kai jannat"tayi,tafita "amma ittakam ta rasa anfanin me zatayi da waya,dahar barista zai iya cewa kar ta bari kowa ya san dashi"...
Kuma in ajiyeta akusa dani,mai hakan yake nufi?"ta tambayi kanta,
Itta yanzu ya zatayi insu mama sunga wayanan ,yanzuma suna cewa yawo take zuwa,ballantana in sunga waya,




Gidan barista kamal


Zaune yake tareda iyalensa a falo,dama al'adanshi ne in yagama cin abinci ya zauna tareda iyalensa"kallon matarsa barista yayi,ya fara maga ,kinga madam bari naje gidansu Ibrahim"yanzu zan dawo,saboda gobe ina da aiki dayewa, allah kiyaye,suka masa " fita yayi "ya hau motarsa ya 'nufi gidansu Ibrahim ",


Yana zuwa kasan cewa dare ya danyi shiyasa bai samu yaron dazai aika ba,mai gadi kawai ya tambaya yace mai Ibrahim din yananan,
Shiyasa barista ya shiga darek tunda ya fada masa dazu da safe zai dawo ko yau ko gobe,
Dan zai iya yuwama ya tarar da Ibrahim" din na jiransa",dan ya sanshi sarai indai akan dukiyane,






Shiga cikin gidan barista yayi "yazo dab da shiga falo kenan sai yaji wata magana daya girgiza mai tunani"ji yayi wani mutun yana cewa,wllhy batada anfani gwara tabi iyayenta "kawai ittama,kaga in tabisu dukiya yazama naka kenan,hakane kam abokina amma kasan bai kamata muyi kisan kaiba,kadai 'nemo mana wani ma fitar daban ba wanan ba,


Shikenan abokina yanzu tunda kaki yarda da wancan shawaran, ina da wani shawara guda daya,waca shawara kake nufi ?.Ibrahim ya tambayi,a bokinsa,




Ka dauketa kaje can nisa da garinan ka jefar da itta kowama ya wuta,
Kaga sai kace bata tayi "
Dariya Ibrahim" yayi,shegen a bokina dama ka iya bada shawara haka"dariya wadda Ibrahim ya kira da aboki yayi,




Ai barista najin kamar zasu fito yayi sauri barin kofar falon,magana yayi da mai gadi akan cewa karya sanarwa da Ibrahim yazo,sanan ya dan bashi wani abu yabar gidan,


Yana barin gidan,kiran jannat "yayi har ta fara bacci,a zabure ta mike zaune, ta dauki wayan,ta kara a kunne,
Daga can bangaren kuma barista ne ya fara magana "jannat"ki fito wajan mai gadi yanzu kiyi sauki,ina jiranki "..
Karki bari kowa ya ganki kinji,toh jannat ta amsa,mikewa tayi ta saka hijabi "fitowa tayi"ta zira takalmanta " waje tayi hanzari, saboda karsu mama su ganta ,
Bala mai gadi "na ganinta yamike suka fita tare saidaya leka ya tabbatar"babu kowa a wajan "sannun suka wuce inda barista ya kwatanta masa sai da suka danyi tafiya sannan suka hango motar barista shiga cikin motar jannat tayi ",barista yayiwa bala godiya yajà motar suka bar ......








Sakeena ismail Cameroon ✍️








Comment and Sharee pls
[8/29/2023, 1:49 PM] Mom Muwadda: 🧝‍♀️MIJIN ATTAJIRA 🧝‍♀️






By




Sakeena ismail Cameroon
(Mom muwadda)




Page 19&20






Bismillah rahmani rahim




_____"godiya barista yayiwa bala yajà motar suka bar layin ,sai da suka hau titi jannat "ta kalli barista",barista ina zamuje da daddarann,wllhy in su mama suka gane bananan, dukana zatayi in nadawo "ta fada kwalla na cikowa a idanunta"ki kwantar da hankalinki, jannat "ba wani waje zan kaiki ba,
Gidana zamu,kuma a can zakici gaba da zama har allah ya fito miki da miji kiyi aure,


Babu wadda zai kuma musguna miki,kafin allah yayiwa mahaifinki rasuwa ya danga a manarki a hannuna,shiyasa bayan rasuwarsa "da naji kinmanta komai bazaki iya tunawa da rayuarki na baya ba,na kyaleki a wajan oncle dinki,amma ba dare ba rana,kullun sai nazo layinku,a duk sanda zaki tafi makaranta ina ganinki,ban taba sallake ko da -da rana daya batare dana zo naduba halin da kike ciki ba,har i zuwa wannn ranar,


Na san tsarai bakiya jin dadin zaman gidan oncle dinki,


Naso tun a wancan lokacin na daukeki "amma ban samu dama ba sai yau,"yaudinma ina da dalilin dayasa na daukeki,amma ko nagaya miki dalilin ba lallaine ki fahimceni ba,saboda ke yarinyace har yanzu,




Jannat "dai tun lokacin da barista ya fara magana tayi shiru,tama rasa me zatace,


Har suka karasa gidan barista "batayi magana ba,fita sukayi suka nufi cikin gidan barista"suna zuwa ya tarar da iyalensa suna jiranshi,dama kuma dabiyarsu ce in har baya gida bazasu kwanta ba,har saiyadawo tukun.


Walida na ganin jannat "ta mike taje ta rungumota"jannat kinzo amma dai yanzukam bazaki tafiba,walida tayi magana,tana kallon Dadinta "insha allah daga yau tare zaku rayu da jannat"har sai sanda allah ya baku mijin aure.


Salle walida tayi kamar wata karamar yarinya , girgiza kai barista yayi,yana dariya,dauketa kuje ku kwanta dan daga yau tare zaku dinga kwana a dakinku,kuma insha allah zanje na nemo mata makaranta "da zata karasa karatunta"tunda wannan shekaran ne zata zana jarabawarta na ,WAIS da NICO .


Gaida momy jannat tayi "walida ta riko hannunta suka haura sama,


Suna zuwa walida tacewa Minal ta bawa jannat gadonta"ta kwanta,inyaso itta ta shimfida katifa,da farko dai kamar Minal tace aa,sai ta tuna labarin jannat "da momynsu ta basu na cewa, jannat yer gatace sosai kafin iyayenta su rasu,kuma a yanzuma tana da dukiya sosai wadda iyayenta suka rasu suka bar mata"
Shiyasa Minal na tunawa da zancen tayi saurin cewa shikenan taxo ta kwata "walida tayi mamakin na tsaurin amincewar Minal, amma bata nuna komai ba,dan tasan ruwa bata tsamin banza a kwai wata a kasa,




Ga gado kije ki kwanta jannat "dare yayi sosai,
Girgiza kai jannat" tayi tace aa aunty walida,nikam kubani katifan zankwanta"a kai,
Walida tace ina ai bazaiyu mu mukwanta a kan gado, ke ki kwanta a kan katifa ba, koda mun yedda mun kwanta a kan gadon ma Dady yana zuwa sai yayi fada,gwarama ki hau ki kwanta"




Babu yanda jannat"ta iya a haka ta hau ta kwata "
Itta Kuma Minal ta kwanta a kan katifa,


*Washe gari*
Kamar yanda na saba tashi a gidan oncle Ibrahim"ina idar da sallah na mike kenn walida da yanzu tagama ittar da sallah itta ma ta kalleni,
Wai ina zakije ne jannat"naga kin mike?
Wllhy aunty walida na saba yin aiki innatashi"da safe shiyasa,nakeso na sauka kasa nadanyi koda sharane na amsa mata" na bude kofa na fita,kallon walida Minal tayi, aunty walida"wllhy in Dadi ya dawo ya tarar jannat na aiki mu muna bacci,bazai mana da dadi ba ,kwara ma muje muhanata ko kuma mutayata muyi aikin tare,in bahaka ba wllhy jikinmu ya gaya mana,
Hakane Minal amma baga laure mai aiki tanayin komai ba,in banda rigimar jannat "
Walida tayi magana tare da mikewa,tabi bayan jannat" din tana saukowa taga jannat sai faman shara take dan ko Laure ma bata tashi ba,




Kinga jannat" ki bar Sharan kixo muje mu kwanta "in Dadi ya dawo bazaiji dadi ba,kinga munada mai aiki zata fito in tayi sallah, zataxo tayi komai,zomuje kinji,karban tsinsiyar
Walida tayi ta ajiye ta kamo hannu jannat "suka koma sama,




Kwanciya sukayi,nn da nn bacci ya dauke su walida"amma ni har lokacin banyi bacci ba,na rufe ido koda baccin zaixo amma shiru,saboda rashin sabo,
Dan ni rabona danayi baccin safe in bammanta ba tun bayan rasuwar iyayena,amma yau nice nake kwance a kan gado kuma mai aiki zata mana komai,kawai in mun tashi muje muyi wanka mu sakko muci a binci,wllhy ji nake kamar bani ba,ina cikin wannan tunanin ne bacci yayi awan gaba dani,
Bamu muka farka ba,sai wajan karfe tara nasafe wanka mukayi Minal ta bani daya daga cikin kayanta nasa amma yamun kadan,kasan cewa itta din ciririya ce sosai,sabanin ni kuma ina da dan jiki kadan.dan in kunganni zaku iya cewa walidace sa'ata ba Minal "ba ,saboda duk wadda ya ganni zaiyi tunani zanyi shekara sha takwas ko sha makwai haka,amma a zahiri kuma banfi sha biyar ba,




Sai da walida ta bani nata kayan na saka,muka sauko kasa,muna zuwa kuma tarar su momy,a kan dinning suna breakfast gaidasu mukayi muma muka nemi waje muka zauna,walidace ta zuba mana ,muka faraci,nikam daker na iyacin a bincin,saboda rabon dana zauna a kan dinning tun randa su momyna,suka bar duniya,
Shiyasa najini wani iri nikam ,da sun barni ma da a kan carpet zan koma na zauna naci a bincina na koshi,


Amma saboda karsu rainani ahaka na zauna mukaci a bincin muka gama muka koma falo,


Jannat "barista ya kira sunanta"na amsa na am.
Da nace zan samo miki makaranta anan amma hakan bazai yuba,mun tattauna da momynku"jiya,zamanki a nan garin babbar masalace a wajanki,dan nasan mutanenn ba kyaleki zasuyi ba,dan haka na yanke shawara tunda kina da passport gwara naje na gyara miki shi,kije kiyi karatunki a kasar waje babu wadda zai takura miki har ki gama karatunki,




Amma Daddy su wayene sukeson suga bayana ?"
Na tambayi barista,wayenda suka kashe miki iyaye Jannat"su sukeso suga bayanki,amma banaso ki tambayeni kosu waye,ke marainiyace jannat "ki rike maraicinki,in kinje kisawa ranki karatu ya kaiyi karatu kuma zakiyi kidawo,




Kiyi karatu jannat"kicikawa iyayenki burinsu" dama ke kanki,




Ki zama lawya mai gaskiya da amana,kamar momynki,


Ina so kizama lawya kizo, ki kwacewa iyayenki hakkinsu,


Mutane da basujiba basu ganiba akaxo aka kashesu a kan dukiya,da in an mutuma a nan gidan duniya za'a bari baza aje layira dashi ba,




Idona ne ya kada yayi jajawur jin kalamai barista "wai ankashe mun iyaye,dama kashesu akayi,?"




Dagowa nayi na zubawa barista wayenn jajayen idanun nawa, barista shi kanshi ma sai daya tsorata da idon ,


Nayi maka alkawari barista"ni jannat"zanyi karatu na kuma zama lawya,nazo na kwacewa iyayena hakinsu a wayenn azzalumai ,na fada ina mai mikewa zan hau sama,
Ina haurowa naji barista na kirana,zuyowa nayi,naji yace ki shirya anjima zakuje tareda momynku kasuwa,kije ki zabi a bubuwan da kike da bukata dama kayan sawa,kuma in kin tashi tafiya walida ta baki nikam kisaka,geda mai kai kawai nayi,ina mai karasa hau......






Sakeena ismail Cameroon ✍️




Comment and Sharee pls










.
[8/29/2023, 1:49 PM] Mom Muwadda: 🧝‍♀️MIJIN ATTAJIRA 🧝‍♀️






By




Sakeena ismail Cameroon
(Mom muwadda )




Page 21&22




Bismillahi rahmani rahim




______"sama na hau,ina shiga dakinsu walida ,na fada kan gado na kifa kaina,sai kawai na saki kuka mai suma zuciya"tunanin iyayena kawai nake, da kuma tausayin kaina,
Yanzu shikenn na resasu har abadan bazan sake ganinsu ba,




Maganarmu dani da momyna ta karshene ta fadomun, jannat "ina so kimun alkawari bazaki kara zubar da hawayenki ba,in har kinaso ,na kasance cikin farinciki,


Mikewa nayi zaune a kan gadon, ina goge hawayena,


Jin momynsu "walida na kirana_ na mike da tsauri,
Toilet na shiga na wanko fuskata"na fito,duba idona nayi a mudubin dakin naga idona har ya dan kumbura, powdan su walida "da nagani a kan mudubi na dauka na dan shafa,


Babu laifi na danyi kyau duk da ba wani kwalliya nayi ba,


Fitowa nayi,na sakko kasa, momyce ta kuramun ido, jannat ya naga idonki ya kumbura?"


Kuka kikaje kikayi ko?"
Girgiza mata kai nayi,aa momy ba kuka nayi ba,
Murmuchi irin nasu na mayya momy tayi,walida kije ,ki bawa jannat hijabi da nikab ,kixo mu wuce kasuwa kar rana tayi,
Walida ta amsa da toh momy ta wuce sama jannat "ta bita a baya,suna hawa sama,walida ta daukowa jannat"hijabi da nikab din kamar yanda momynsu ta umarceta,sakkowa suka kumayi, o ready dama kuma itta ta riga da ta shirya,fita sukayi suka shiga mota momy tayi hone mai gadi ta bude musu get ta cilla hancin motar ta waje,


Bangaren barista kuwa yana fita waya_ yayiwa Ibrahim ya tambayeshi in yana gida,ce mai yayi _yananan,yace toh gashinn zuwa, Ibrahim "yace mai sai yaxo,




Yana zuwa gidan Ibrahim"ya kuma kiranshi a waya,hello Ibrahim gani nazo ina kofar gidan,yana gama fadar haka ya kashe wayan,ya jingina jikinsa da bayan mota,


Ba'a dau lokaci ba,sai ga Ibrahim ya fito,karasowa yayi _yamikawa barista hannu suka gaisa,


Bismilla mana barista mushiga ciki,


Ciki suka shiga,a falonshi yayiwa barista ma sauki,suka zauna barista "ne yayi magana,ya naganka haka Ibrahim?"
Wllhy barista ba dole ka ganni haka ba,barista,
Jannat ce mun wayi gari mun nemeta sama ko kasa,amma bamu ganta ba,




Ware ido barista yayi kamarya?baku ganta ba, Ibrahim "yarinya dana dawo da itta jiya jiyann kace mun baka ganta ba,
Toh in baka ganta ba,ina taje?"..




Wllhy barista bamu ganta ba, Ibrahim yayi magana yana zare ido kamar wadda mai gamo,




Kai Ibrahim ka kalleni da kyau,taya yerka Ameera"bata ba taba,sai jannat "wato saboda itta ,ba yerka bace ba ko?"




Ka fiffita yerka,a kan marainiyar allah...




Toh bari nagaya maka allah sai ka nemota a duk inda take,ko kuma na makaka a kotu....




Barista na gama fadar haka ya mike saye,gata kartunka,ya jefa mai...ta kartun gidan a kasa ya fita ya bar oncle Ibrahim "a durkushe a wajan,


Bin bayan basirta, Ibrahim"yayi yana rokonsa,daya janye maganar kotun nn,




Barista najin a bunda Ibrahim "ya fada,ya dan juya _yana kallon Ibrahim,kanaso na janye maganar kotu ?.da tsauri Ibrahim ya geda kai,toh indai kana so na janye ,
Na baka yau zuwa gobe,ka nemo yarinyar in, in har baka nemota ba,toh yazama dole kaje kotu..




Barista na gama fadar haka,ya shiga motarsa,ya bar Ibrahim a wajan,hankali tashe...jiki babu kwari ya mike ya koma cikin gidan,zama yayi a kan carpet ya rafka uban tagumi,kai saika rantse, ka dauka wani nasane ya rasu,


Barista kuwa na barin kofar gidan Ibrahim"mai zaiyi in banda dariya,in ya tuno Ibrahim a lokacin daya gaya masa cewa zai kaisa kotu in mai nemo jannat"ba,




Su momy kuwa sai wajan karfe 2suka gama siyayya,dan ba karamin siyayya akama jannat"ba,




Sun gama siyayya amma sun resa wa zai daukar musu kayan kasancewa kasuwane,




Da mai shagon ya fahimci a bunda suke nema,shine ya hadasu da wani mai dako,ya daukar musu kayansu"ya kaimusu har bakin mota,


Godiya momy tayi masa sosai,ta dau 10k ta basa,yaji dadin kudin sosai sai godiya yake wasu momy,nagode hajiya,allah ya sakada alkhairi ya kara budi,
Murmushi momy tayi dan taji dadin addu'an daya mata sosai,(ameen)ta amsa,
Tana kallonsa,haba bawan allah dubu goma ai ba wani kudine masu yawa ba,




Murmushin sa mai kyau yayi yana kallon momy,
Haba hajiya 10k fah....
Toh wllhy tunda nake ban taba rike 10k ba hajiya sai yau,dan wuni nake,ann amma ban wuce na samu dubu biyar ba,saboda in nayi dakon kaya basu wuce su ban dubu biyu ko dubu daya ba,




Sosai momy,taji tausayinsa ",ya sunanka?"sunana adamu amma anfi kirana,da ado mai dako,shikenn ado karka damu daga yau in nazo kasuwa zan ginda nemoka kana daukarmun kaya,toh hajiya nagode allah kara girma,(ameen) momy ta kuma amsawa,


Mota suka shiga suka nufi gida...




*Wanene ado*


Dan asalin garin Niger ne,irin buzayen Niger dinn,ado kekkyawane ajin karshe, farine sosai,dogo ,mai dogon fuska,da kuma dogon hanci,yanada cikar zati da kuma maiyan idanu,




tun lokacin da allah yayiwa iyayensa rasuwa,
Bai samu aiki ba,dukda karatun da yayi ,mai zurfi amma allah bai bashi aiki ba, shiyasa ya _yanke sawara,dayaxo kano,yana zuwa kano,ann ma dai aikin bai yuba,a karshe dai kawai ya hadu da wani a bokinsa mai suna sufuyanu yana dako a kasuwar sabon gari, tare suke wuni,tun ado baya iya aikin har yasaba,kasancewa jikinshi ba mai son wahala ba,




Shiyasa har yanzu in yayi aiki sosai sai kaga jikin sa yayi jajur,




Su momy kuwa a gajiye suka dawo gida ga yinwa dake damunsu,suna zuwa sallah sukayi suka wasa ruwa sukaci a binci,




Sann suka zauna duba kayan da suka siya,su walida sai yaba kayan suke,abayoyine masu kyau da sheki,sai takalma jaka da sarkoki hade da dan kunnaye,sai mayafai dasu less, a tampopi, gasunn dai,kai in kagani sai ka rance ka dauka lefene sukaje suka hado.
Saboda yawan kayan, sai a kwati guda uku..




Da daddare sungama cin abinci kenn sun zaune a falo,barista yakalli jannat "




Alhamdulillah jannat"nagama miki komai insha allah gobe da safe zamu tashi,


Kundai shirya komai ko,
Eh mun shirya komai barista ,amma wayenn a tampopin sedai a kaimata daga baya,na kira tela zaixo gobe ya tafi da kayan..momy ta fada,tana kallon mijin nata,tam shikenn babu mas'ala,


Ke walida ki shirya dake zamu tafi kiyi mata rakiya in na tashi dawowa saimu dawo tare .




Ni kuma fah Dady,minal" tayi magana,tana kallon Dadynsu kamar zata fasa kuka,dariya barista,yayi haba minal kema zakije amma ba yanzu ba,in kun samu wutu seki kaimata,ziyara ko?toh Dady,minal ta amsa amma ba haka tasoba,


Barista kuwa badan komai yacewa walida ta shirya suyi tafiyan da itta ba,sai dan,ganin cewa jannat "ba muharraminsa"bace,bai kamata ya dauketa su tafi daga itta sai shiba,
Sadoba kaucewa shaidan..




Kutashi ku tafi kuje ku karasa shirinku,


Kusamu ku_ kwanta da wuri ,toh Dady suka amsa"suka mike suka wuce sama...


Suna zuwa shirya _shirye sukayi sosai ,suka taya jannat "hada komai nata,




Sai 1suka kwanta.




Bangaren Ibrahim kuwa.
Babu inda bai jeba,amma
Baiga jannat"ba,sai kawai ya dawo gida,sai sinewa jannat"suke,dagashi har matarsa,




Waya ya dauka ya kira abokinsa,yana dagawa suka gaisa,zaiyane masa komai yayi_,yakara da cewa, barista yace in har bai nemo jannat ba,zai kaisu kotu,




Daga can bangaren banji mai abokin nasa yace ba,ji nayi kawai oncle Ibrahim na dariya,




A haka dai suka gama kulle _kullensu sukayi sallama ya kashe wayan a kan cewa gobe zasu hadu su karasa tattaunawa...


Gidan barista Kamal.


*Washe gari*


Muna idar da sallah wanka mukayi dani da walida,na shirya cikin daya daga cikin a bayan da Dadynsu walida ya siyamun,nayi kyau har nagaji,su walida ma sai yaba kyau danayi..


Kwashe kayanmu mukayi muka sauko dasu kasa..
Muna gamawa,muka zauna,muka karya,


Sai dreva dasu momy suka rakamu airport,
Muna zuwa bamufi mintuna 15ba jirginmu ya daga zuwa kasar india....






Sakeena ismail Cameroon✍️




Comment and sharee pls
[8/29/2023, 1:49 PM] Mom Muwadda: 🧝‍♀️MIJIN ATTAJIRA 🧝‍♀️




By




Sakeena ismail Cameroon
(Mom muwadda)




Page 23&23




Bismillahi rahmani rahim




_______"jirginsu ya daga zuwa kasar India,sai a lokacin su momy suka wuce gida,minal kam sai cin magani take,wai dan meyesa ba'aje da itta ba,




Gidan oncle Ibrahim.
Da safe kamar yadda suka tsara zasu hadu da a bokinsa"su tattauna a kan maganar jannat"hakance ta kasance,sun hadu a wajan cin abinci,sun tattauna sosai,amma nikaina bansan me suka tattauna ba...a bunda nagani kawai bayan sungama tattaunawa naga sun rabu cikin farinciki" Daganan kowa ya wuce wajan aikinsa,


*Kasar India*




Su jannat "kuwa, sai wajan 7 na dare suka sauka, a babban bernin India,wato Mumbaï,suna sauka sai ga wani a bokin barista "da sukayi karatu tare,kasancewa shima barista a garin India yayi karatu, ya hada digirinsa "sun shaku sosai da Mr ali Khan ,




Mr ali Khan yanada,mata daya,da yaya biyu mace dana miji,macen, na da shekaru biyar,na mijin kuma nada shekara tara,kasancewa su basa aure da wuri,Mr ali Khan dan asalin kasar Pakistan ne,aikine ya kawoshi cikin Mumbai,


Yanzu hakama tare da yayan nasa sukazo airport daukansu barista,


Sun rigada sunyi magana da barista"kuma ,a wajansa jannat zata zauna har ta gama karatunta"...


Rungume juna sukayi..
Suna dariya,dan ba karamin dadi sukaji ba,na ganin juna, da sukayi,gaidashi su walida sukayi,suka dunguma zuwa gidan Mr ali...


Tarba namu samman suka samu wajan matar Mr ali,suna zuwa aka kaisu ma saukinsu, jannat "da walida_ daki daya, barista kuma daki daban aka ware masa shima...,




Wanka sukayi da sallah,
Suka fito falon abinci aka gabatar musu dashi. kala_ kala irin nasu na yen india ...sunci amma ba sosai ba,gwarama barista daya tsaba zuwa kasar..bugu da karima ya zaun a kasar,


Shiyasa ya tsaba da'a bincinsu babu kalan a bincinsu da bai sani ba...su Jannat "kam pizza kawai sukaci...suka mike suka wuce ma saukinsu",


Bin bayansu nihila da aryan sukayi...suna zuwa dakin, Jannat"ta jasu a jiki sai bata labarin makarantar su sukeyi,da turanci,kasan cewa daga turanci sai indianci suka iya,itta kuma jannat "bata iya indianci ba,sai turanci...yira sosai sukasha da yaran,ko bacci ma basaji,su jannat "kuwa duk sun gaji suna son suyi bacci amma yaran sun hanasu"?


Jin shirune yaran basuzo sun kwanta ba,sai Aneesha tabi bayansu "dan tasan halin yaranta tsarai,ai kuwa,tana zuwa ta tarar dasu suna nn sai zuba tsurutu suke,babu ko alamun bacci a idonsu",kuya hakuri jannat,sun hanaku bacci ko, girgiza kaina nayi nace aa ma'a..dariya aneesha tayi tana kallon yaranta,toh maza ku tashi muje ku kwanta dare yayi sosai...daga kafadunsu sukayi a lamun bazasuje ba,


Masu karatu, dama kuma kunsan fararen fatann da daurinkai,dagasu har yayansu,😂hummm baridai nayi shiru karsu jini 🤬




Kallon mamarsu nayi nace ma'a ki barsu su kwana anan din kawai..


Na takaita muku a karshe dai tafiya mamarsu tayi ta barsu" muka kwana tare,


*Washe gari*


Muna tashi sallah mukayi,da askar,muna gamawa bacci muka dan koma dan har yanzu gajiyan tafiya bai sakemu" ba ,sai wajan 8kuma tashi wanka mukayi,nida aunty walida.... maroon din abaya na saka,kasancewa..bani da wasu kaya sai abayan, dan ba'a dinkamun sauran kayana ba,sai daga baya za'a kawomun in andinka inji momynsu walida, powda da lipstick na saka ammma ba karamin kyau nayi ba,saboda abayan yayi mugun karban fatar jikina ",itta ma dai walidan abayan tasaka amma nata bakine,


Fitowa mukayi muka tarar mamansu nihila tana gyera kayan breakfast a kan danning ,
Tana ganinmu ta sakar mana murmuchi"..gaisheta mukayi tayi mana bismillah damu zauna,bamuyi musu ba,dan mukammu yinwan mukeji,saboda jiya ba wani a bincin kirki mukaci ba,


Yanzu ma dai kayan lambune kawai mukasha ..
Suna gamawa, barista ya kalli jannat "yata kitashi muje ko ina so na gama miki komai kafin jibi zan wuce,toh na amsa muka mike da walida,


"Ni da barista sai aunty walida,da kuma,Mr ali Khan,muka fita,kasan cewa yafi barista sanin gari tunda shi kasarsace"


Makaranta suka samomin mai kyau da sada,ga kuma tsari,ba kamar irin makarantunmu "na nan ba,...bamu muka dawo gida ba sai wajan la'asar,
Insha allah ranar Monday zan fara zuwa school,
Kasan cewa yau Wednesday ne....


Da ma'a dinsu aryan taga ba cin abinci mukeyi ba,shine tayi mana shinkafa da miyan vegetable...duk da ba wani dadi yayi sosai irin namu ba ,amma munci babu laifi dan mugun yinwa mukeji...




Washe gari Daddynsu walida ya karasamun wasu abubuwan da baimin ba,


Yau ya kasance Friday kuma a yau su Dady zasu koma Nigeria,


Airport muka rakasu "sosai Dady yamun nasiha..akan na tsare mutuncina,nakuma rike addini na sosai,nasan cewa kataru ya kawoni,karatu kuma zanyi na dawo...a haka suka shiga jirgi ,mukuma" muka dawo gida jikina a sanyaye,sai share kwalla nake...






Sakeena ismail Cameroon ✍️


Comment and Sharee pls
[8/29/2023, 1:49 PM] Mom Muwadda: 🧝‍♀️MIJIN ATTAJIRA 🧝‍♀️




By


Sakeena ismail Cameroon
(Mom muwadda)




Page 25&26




Bismillah rahmani rahim




*Nigeria* *Kano*




______ sai wajan 4 na yamma suka "sauka ...mommyce da kanta taxo tarban mai gidanta "itta da Minal...
Minal na ganin walida taje ta rungumeta,dan tayi missing din yer uwarta sosai,duk da kwana biyu kacal sukayi,amma ba karamin kewa sukayiwa zuna ba,


Sannu Minal watoni bakiyi kiwata ba sai yer uwarki kawai,dariya tayi tace afwan Dady ba haka bane,kaima nayi kewarka sosai my Dady, dariya barista yayi,naki wayon,kedai ki fadi gaskiya,mommy ce ta amshi zancen,kai ko alhaji ba dole tayi kewar yer uwarta ba,kasan daya baya daba tafiya tabar daya ba,kaga kuwa dole suyi kewar juna,geda kai barista yayi,muje gida ko?"mota suka shiga mommy tajasu suka wuce gida...


*Gidan*oncle Ibrahim*


Bayan tafiyar su barista" India da kwana daya.... oncle Ibrahim yaji shiru, barista "bai kirashi"akan maganar kotu ba,shi a tunanin sa ko baristan ya janye maganar kotun ne..
Bai ma san cewa barista" kam ma baya kasar gabaki daya....


Gidan barista
Bayan sun dawo gida yayi wanka yaci abinci,yayi sallah,yana zaune da matarsa "a dakinsa suna hira irin nasu na ma aurata,su walida kuma suna dakinsu,


Suna hira sai oncle Ibrahim ya fado masa.
Wayarsa dake gefensa ya dauka,ya dannawa Ibrahim "kira...zaune yake shima da matarsa a falo sai yaji wayarsa na ringing tunani yake wa zai kirashi a wannn lokacin,yana tubawa_wa zai gani inba number bariata ba...irjin sane

Please Login or Register in order to submit comment