Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta zauna a gefen bed din tana kallona,


Magana Minal ta fara, humm na dade da sanin cewa kina son Adam shiru kawai nayi kuma naga alamar soyayyarki a idon Adam din tun farkon haduwarmu dashi naga irin kallon dayake miki,


Kemma jannat ki rasa wanda zakiso sai mai dako haba jannat jibeki fah ?


Kinga dakata Minal"kinfi kowa sanin cewa Babu ruwanso da wayanan abubunwan da kika lissafa,


Ni ina sonshi a haka,humm toh in har da gaske kike son Adam "toh gwara ki fada masa kina sonshi"dan in har jira kike ya fada miki toh bana sammanin a kwai ranar da zai fada miki tun sanda Minal ta fara magana nake kallon ta har tagama dan ban fahinci inda maganar ta _ta dotsa ba,


Kamar Minal tasan tunanin da nake,tace kinga jannat ina nufin Adam yana sonki Amma bazai iya gaya miki ba saboda gani yake kinfi karfinsa"in ya gaya miki bazaki amince dashi ba,


Ai ina jin hakan na mike Minal na kallona na nufi wajan wardrobe dina hijabi na dauka na saka ina gama sawa gaban dressing din mirror naje na dau mukullin motana dake wajan na fice daga dakin Minal na tambayata inda zani ko kallon inda take banyi ba,


Nayi sa'a kuwa babu kowa a palon nayi waje abuna na nufi wajan aje motocin gidan ina zuwa na shiga motana mai gadi ya budemin get na cilla hancin motana waje,


Tuki nake Amma ina tunanin yanda zan fiskanci Ado da zancan,


Ina zuwa bakin kasuwa na sauka na nufi wajan da suke zama,


Ado ne zaune da abokinsa "idi sai fama yake da abokinsa a kan lallai sai ya gaya mai a bundake damunsa amma yayi banza dashi "
Haba abokina bai kamata ka boyemin a bundake damunka ba idan baka gaya min damuwarka ba wa zakaje ka gayawa dan allah ka fadamin me yake damunka"dan bakaga yanda duk ka rame kayi baki ba ,


Dan numfasa Ado yayi cikin sanyin murya ya bude baki yace wlly idi ina son hajiya karama sosai yana nufin jannat amma na resa yanda zanyi na tinkareta da maganar dan tafi karfina Ado yayi magana hade da share hawayen dake zubo mai shiru idi yayi yana kallon abokinsa saboda zai iya cewa ma tunda yake bai taba ganin abokinsa ya zubar da hawaye ba,amma gashi yau akan mace yake zubar da hawayensa "dafa kafadarsa idi yayi _ya fara magana kamar haka ka kwantar da hankalinka abokina insha allahu hajiya karama zata yedda dan girgiza kai Ado yayi tare da fadin aa idi bazata taba yedda ba dan in har nace ina sonta gani zatayi kamar kudinta nakeso amma ni wllhy ba kudinta nakeso ba itta din nakeso saboda tana da hankanli ga nitsuwa na dade ina rokon allah daya bani mace ta gari mai nitsuwa
A gaskiya abokina bazan boye maka ba ina son jannat sosai tayi kalar matan da nake burin samu arayuwa ta,toh amma meyasa baka fadamin ba sukaji anyi magana a bayansu juyowa sukayi a tare dan ganin waye,


Jannat ce tsaye ta zuba musu ido hawaye sai zubo mata yake a kumatu tana sharewa wasu suna sake fitowa kara sowa tayi garesu taci gaba da cewa haba _haba Ado meyasa baka taba fadamin ba meyasa ka boyemin Ado naji duk a bunda kuke tattaunawa naji komai Ado,


Kara sowa kusa da itta Ado yayi yana murmuchi dan yaji dadin ganinta sosai kusan tsati biyu basu hadu ba,


Hajiya lfy kuwa kwana biyu bakiya zuwa ?


Ba wannan na tambayeka ba Ado nace meyasa kana sona amma ka doyemin ?


Kasani cewa badan komai yasa kake ganina ba sai dan son da nake maka ka dauka wannn zuwan da nake haka kawai nake zuwane ?toh ka sani cewa ba haka kawai yasa nake zuwa nan ba sai dan son da nake maka amma kaki cewa komai,
Bayan kuma kaima kana sona,


Kiyi hakuri hajiya ki dena kuka dan wllhy kukanki dagamin hankali yake,


Wllhy ba dan komai yasa ban fada miki ba sai dan....bai kara saba jannat taci gaba da cewa kaga Ado naji duk a bunda kuka fada dazu da idi"kiyi hakuri hajiya da gaske ina sonki amma kinfi kowa sanin cewa banda wani aiki daya wuce wanda kika sanni dashi wato wannan dakon da mukeyi shi kadai aikin da nake dashi
Nasani Ado amma ba ka taba gayamin kana da digiri ba kai Ado ya geda naci gaba da tambayasa"ta kardunka sunanan ne ?eh sunanan in suna kusa ka daukomin ina jiranka a mota kai Ado ya geda ya nufi wani wajan da suke kwana yana zuwa bai wani dau lokaci sosai ba ya dawo rike data kardunsa a hannusa ya nufi wajan motar jannat yana zuwa ya bude ya shiga mikawa jannat takardun yayi karba nayi ina kallonsa "yauwa Adam zan nemeka insha allah sallama mukayi ya koma wajan zamansu ni kuma na wuce gida,


Da daddare na samu Dadynsu walida akan maganar karban takardun yayi _ya duba yaga komai yayi kyau,


Gaskiya takardu yayi kyau amma meyasa ke bazaki daukeshi a daya daga cikin kanfanoninki ba shiru nayi ban bashi amsa ba,


Dan murmushi irin nasu na manya barista yayi dan ya fahimci tsarai son Ado jannat takeyi,a zuciyarsa kuwa cewa yake in Allah ya yarda sai yayi bincike akan yaron kafin ya aura mai Jannat,


Dady sai da safe barista yaji jannat na cewa dawo daga tunanin da yake yayi yace allah ya kaimu jannat amma kicewa Adam din ya sameni a office dina toh na fada tare da sakeyi mai sallama na fita,


*Washe gari*


Ina tashi da safe kamar yanda barista ya umarceni akan na fadawa Ado ya sameshi a office dinsa haka kuwa akayi ina gama shiryawa na dau motata sai wajansu Ado ina zuwa na samu Ado da maganar yace bari yaje ya canza kaya yazo mutafi toh na fada nayi shiru ina jiranshi bai wani dau lokaci sosai ya dawo kuma dama ya riga da yayi wanka, takowa yake a hankali har ya karaso inda nake yayi kyau sosai dukda kayan nashi ya dan kode amma a wanke take sab yasha guga, Ado kuwa yana lura da itta "muna hada ido yayi murmuchi dauke kaina nayi nace mu tafiko kai kawai ya gedamin muka shiga mota muka nufi wajan aikinsu Dady,




Sakeena Ismail Cameroon ✍️




Comment and Sharee pls
[9/20/2023, 2:11 PM] Mom Muwadda: 🧝‍♀️MIJIN ATTAJIRA 🧝‍♀️




By


Sakeena Ismail Cameroon
(Mom muwadda)






Page 70&71




Bismillah rahmani rahim




_______kasan cewa yansu barista kamal yaji sauki sosai har yana iya fita wajan aikinsa" shiyasa sukayi da jannat akan cewa tazo tare da Ado su sameshi a wajan aiki,




"muna zuwa wajan aikin su Dady nayi marking muka fito daga cikin mota kallon Ado nayi na bude baki nace bismillah ko Ado mushiga kai kawai Ado ya gedamin yana bin wajan da kallo"shiga ciki mukayi muka nufi office din barista muna zuwa na kwan kwasa sai daya bamu izinin shigowa sannn muka shiga gai sheshi mukayi ya amsa yana bin Ado da kallo"alamun ya nuna mana da hannunsa" damu zauna zama mukayi na kalleshi tare da fadin Dady gashi nan wannan shine Ado murmushi barista yayi tare da geda kai masha allah sannu Adamu naga ta kardunka sunyi kyau sosai amma ina mamakin kana da wannan ilimin har haka kake dako a kasuwa wllhy yellabai babu inda banje nemon aiki ba amma ban samu ba kama daga Niger har nan Nigeria dana gaji kawai na yanke shawara na zauna tare da abokina nayi dako shine abokina ya daukeni ya kaini wajan ogansu toh tun daga ranar na fara dako Ado ya karashe magana cikin sanyin murya girgiza kai barista yayi amma mutane basu da tausayi da ilimin mutun ma baza'a daukeshi aikin ba allah shi kyau ta barista yace Ameen Ado da Jannat suka amsa mikewa barista yayi yana kallosu yace ku tashi mutafi wajan abokina nayi magana dashi tun jiya nayi mai bayanin komai dan ni bazan iya daukar Adamu aiki ba saboda bashi ya karanta ba kai suka geda tare da mikewa fita mukayi muka shiga mota muka nufi wajan aikin abokin barista".,






Muna zuwa muka nufi office din sa kwankwasa wa barista yayi muka shiga wani magidanci ne zaune a kan kujerar dake cikin office din ga medical glass akan idonsa ga kuma wasu ta kardu ajiye akan tedurin gabiro a hannusa yana wasu rubuce _rubuce a cikin sakama kon jin su barista sun shigone yasa shi dagowa hadeda yin murmuchi sannu ku ga wajan zama ya furta sai dasu jannat suka gama gaishesa ne ta zauna da itta da Ado.




Kara gaisawa barista da bokinsa "sukayi kallon barista alhaji jibril yayi sai ya fara magana Alhamdulillah na duba ta kardu komai yayi kyau daga yau kaine manajar wannan kanfanin insha allah zamu baka gida da zaka zauna da kuma mota"farincikin a wajan jannat kam ba'a magana dan ko Adon ma tafishi farinciki ,




"Kallon alhaji jibril Ado yayi yace da gaske baba ka daukeni aiki kai alhaji jibril ya gedawa Ado.


Hamdala Ado yayi tare da daga hannu sama yana godewa ubangiji daya nuna masa wannan ranar sai kuma kawai ya tino da iyayensa"sai ga hawaye suna zubo mai a kumatu dama yanzu suna rayé barista dake kusa dashi ne ya dafa shi Ado yayi saurin goge hawayen dake zubo mai,




Ya dai Adamu?"basirta ya tambaya babu komai baba kawai dai tunawa nayi da iyayena na tuna baba gashi ina cikin farinciki amma babu wanda zai tayani karkace haka Ado ba gamu nan ba jannat ta fada tama manta dasu barista awajan sai da tagama fada kuma sai kunya ya rufeta,tayi saurin sunkuyar da kanta ",


Dan dagowa ta danyi taga su barista bama itta suke kalla ba,




Tana ganin haka sai ta sauke ajiyar zuciya.




Kallon Ado shima barista yayi yace kwarai kuwa kana damu Adamu ka kwantar da hankalinka insha allah daga yau nine ubanka,kuma daga yau a gidana zaka zauna inyaso in kasamu matar da zaka aura sai kayi aure acan gidan naka kaji ?. kai ado ya geda hadedayi musu godiyar,


Kallon Ado alhaji jibril yayi yace yauwa kaje ka shirya gobe da safe sai ka fara aiki ko,kai Ado ya geda tare da karayi mai godiya,sukayi sallama da barista suka fita,


Barista yaso Ado ya bishi gidansa tun a lokacin amma Ado yace sai yaje yayi sallama da abokanai shi tukun inyaso gobe sai yataho,kai barista ya geda tare da shiga motarsa ya koma wajan aikinsa "jannat kuwa sai data fara ajiye Ado a wajan zamansu tukun sannan ta wuce gida,




*Washe gari*


Kamar yadda aka tsara jiya hakan ta kasance,yau Ado ya fara zuwa aiki,komai yana tafiya yadda ya kamata dan Ado akwai iya aiki da kuma ma'amula da mutane, Alhamdulillah komai yana yafiya yadda akeso"bayan an tashi daga aiki jannat tabi ta wajan aikinsu Ado ta daukeshi suka wuce gidan barista ,dama kuma barista ya Riga daya gaya mata time din da su Ado suke tashi daga wajan aiki,


"a gidan barista kuwa tun jiya barista ya gayawa matarsa zuwan Adon gidan shiyasa suka shiryawa Ado dakin da zai zauna.




Muna zuwa gida nayi parking kallon Ado nayi nace muje ko Ado kai Ado ya gena muka fito daga cikin mota dakin da aka warewa Ado shi muka nufa dan yanzu Dady barista bai dawo daga wajan aiki ba.
Kallon kidan Ado ya dingayi har muka isa dakisa"ina zuwa na tiro mu kullin da Dady ya ban jiya da daddare bayan angama shirya komai,




Tiro makullin nayi a cikin jakata na bude bakin bismillah Nayi wa Ado muka shiga kallon dakin yayi ya maida dubansa wajan jannat din yace hajiya karama kina nufin wannan dakin nawane dariya na danyi nace nakane mana Ado ko dakin bai maka bane ?"ina wllhy daki yayi kyau sosai hajiya kawai dai mamaki nakene,mamaki name Ado ?,




Mamaki na cewa wannan dakina ne,kaga Ado mushiga daga ciki ai wannan palo ne mu shiga bedroom,kai ya geda muka shiga bedroom,


Masha allah komai yayi gadone ma daidaici da wardrobe, toilet na nufa mudewa nayi shima dai toilet din yayi kyau sosai.Ado kam baki yaki sufuwa wai yau shine zai kwana a wannan daki ga bakeken gado ga kuma AC ikon allah kenan,


Ina gama nuna masa dakin muka fido kallon sa nayi nace yauwa Ado ka shiga kayi wanka kafin na kawo maka abinci.toh hajiya nagode sosai allah ya saka miki da alkairi kaga Ado ni ka dena kirana da hajiya ba sunana hajiya ka kirani jannat kamar yadda kowa suke kirana dashi toh na dena inshallah murmuchi nayi mukayi sallama na fita na rufo mai kofah,


Bangaren mu na nufa babu kowa a palon sai na nufi dakinmu ,na tarar da Minal kwance tana bacci kaina na girgiza na ajiye jakata da mayafina na wuce toilet wanka nayi tare da alwala kasan cewa ban samu nayi sallar la'asar ba,




Bayan na shirya nayi Sallah.


Fitowa nayi naje na hadawa Ado abinci na nufi dakinsa "ina zuwa na kwankwasa"sai da yace in shigo sannn na tura kofar a hankali na shigo yana zaune a palo yana karasa aikin da aka bashi a kanfani ,kallona yayi ya sakarmin murmuchi nima murmuchin nayi mai na karaso na ajiye abincin dake hannuna zubamai na somayi ya dagatar dani,haba ha...bude baki yayi har zaice hajiya sai ya tuna tace bataso,kinga jannat kibarshi zan zuba, murmuchi nayi dan yadda ya fadi sunan ba karamin dadi yamin ba.
Ya iya furta kalman sosai,


Ka bari na zuba maka ai ko ba komai kai babbane


Ko baka haifeni ba amma ai ka dirmeni.


Kai ya geda a bincin na karasa zuba masa na mika mai karba yayi ya faraci a hankali cikin nitsuwa yakeci ba karamin burgewa yamin ba ,waje na samo na zauna na zuba mai ido,in naga yayi kamar zai dago idanuwansa sai nayi saukin sunkuyar da kaina inyi kamar bashi nake kallo ba,shi dai Ado daya fahimci haka bai kuma dagawowa ba har sai daya gama cin abincinsa".ya dau ruwa ya shà, hamdala yayi,


Sai a lokacin ya dago,yace
Nagama ya faga a takaice,


Kai na geda tare da mikewa kwashe kayan nayi mukayi sallama na wuce cikin gidan,






Sakeena Ismail Cameroon ✍️




Comment Sharee pls 😍
[9/24/2023, 4:47 PM] Mom Muwadda: 🧝‍♀️MIJIN ATTAJIRA 🧝‍♀️






By


Sakeena Ismail Cameroon
(mom muwadda)




Page 72&73




Bismillah rahmani rahim




_______"washe gari ina gama shiryawa na fito palo yin breakbeat sai na tarar dasu barista da matarsa sai Minal" gaishesu" nayi na jà kujera zan zauna kenan sai barista yayi magana kinga jannat ya zaki zauna ba tare da kinje kin_ kira yayan ku ba har zance wana yayanmu sai kuma na tuna Ado yake nufi tashi nayi na nufi bangaren Adam din ina zuwa nayi sallama na shiga baya palo sai kawai na nufi cikin bedroom din a tunani na ko bai tashi daga bacci ba ai ina zuwa sai na tarar sabanin haka,jin kamar karar saukar ruwa da kuma kamshin sabulu a toilet ne ya sani fitowa na dawo palo waje na samu na zauna nayi shiru ina jiran ya fito,




Baifi 10 minute ba naji karar mude kofar toilet din da dukkan alamu ya gama wankan,sai da aka kara kusan 15 minute sannun na mike na nufi cikin bedroom din dan na tabbatar yanzu yagana shiryawa,sallama nayi kafin ya amsa na denno kaina cikin dakin ina shigowa kuwa na tarar dashi daga shi sai gajeran wando ga kuma dogon wandonshi a hannu daga gani sawa zaiyi jin motsin shigowa dakinne ya dakatar dashi daga sawan da zaiyi,




Ai Ina ganin haka nayi saurin juyar da kaina na bashi baya tare da fadin am sorry am so sorry na dauka kagama shiryawa ne shiyasa na shigo dama Dady ne "yace na kiraka kaxo kayi breakfast ina gama magana nayi hayyar fita har nakai palo naji ya kirani,


Jannat jannaaat ya kuma kira da wannan muryar tashi mai dadi,


Ai ina jin haka bansan sanda na tsaya cak ba
Har ya fito ya karasa inda nake ban motsa ba.


Har ya karaso gabana kije ki kawomin a bincin anan saboda kunyar su Dady nakeji bazan iya cin abinci dasu ba,sai alokacin na dago nayi magana humm wallahy ya Adam Dady bazai amince ba kona je na gaya masa "gwarama ka biyoni mutafi nayi maganar,


Kai Ado ya dafa ya zanyi bashi da zabin data wuce ya biyota su tafi,kai ya geda muka fita yajaa kofar ya rufe muka nufi cikin gidan,




Muna zuwa muka tarar dasu barista har sungama yin breakfast sun koma palo




Durkusawa Ado yayi ya gaida barista da mami wato matar barista kenan,


Kallo na barista yayi yace sai kuje ku karya mukam mungama namu mun jiraku har mun gaji ,




Wallhy Daddy na tarar dashi yana wankane sai dana bari ya fito sannun na fada masa" kai barista ya geda,tare da kallon matarsa mu tafi ko kai ta geda tare da mikewa har tafita suka somayi har sunxo bakin kofa sai barista ya juya ya kalleni tare da fadin yawwa jannat in kun tashi daga wajan aiki ku wuce shopping din kiyi duk a bunda na fada miki jiya zan turo miki da kudin a account dinki toh Dady"




Amma basai ka turo ba a kwai kudi a hannuna zasu isa insha allah,gidanku gidanku nace nafiki sanin kina da kudi a hannunki ai nidai na gaya miki zan turo miki da kudi Kuma kar na kumaji kince komai toh Dady na fada ina murmuchi,




Mai mami zatayi in banda dariya kai alhaji har yanzu yarinyace fah.




Naji ke kuma wuce mutafi, allah ya kiyaye Dady na fada Ameen suka amsa suka fita,


Karasa wajan cin a binci mukayi kujera na jawa Ado ya zauna sai da nayi serving dinsa sannun nayi nawa zama nayi muka somaci,


Bayan mungama cin abinci daki na wuce jakata da kuma takalmi na _na dauka na fito kallon Ado nayi nace mu tafi okay ya fadi tare da mikewa sai daya koma dakinsa ya dauko wasu ta kardu dayayi aiki jiya dasu,ya fito ya rufo kofa yayi wajan mota,


Yana zuwa ya tatar ina jiransa"shiga yayi muka muce sai dana fara ajiye shi tukun sannun nima na wuce nawa wajan aiki,




Bayan mun tashine na biyo ta wajan aikinsu Ado na daukeshi sai dana fara sayawa a Wani restored mukaci a binci sannn muka wuce shopping din,




Muna zuwa muka shiga kallon Ado nayi nace mai ya zabi duk kayan da yayi masa"kai Ado ya girgiza aa jannat ni da nasan saboda ni kikazo wanan wajan ma da ban yadda na biyoki ba,kaga dakata yah Ado badai kai bazaka zaba ba ka barni ni zan zabar maka duk a bunda nasan ya dace da Kai,ba yanda Ado ya iya a haka ya dinga bin jannat a baya har sai da tagama a bunda zata daukar masa sannun taje ta biya aka kai musu kaya niki niki a mota suka wuce gida,




Bayan mun koma gidane aka kawowa Ado motarsa"aka kumayi masa alkawai gobe za'a kaishi yaga gidan da aka bashi,




Mota tayi kyau Masha allah,


*Washe gari*


Kamar yanda akayi wa Ado alkawarin cewa za'a kaishi yaga gidan haka kuwa akayi ankaishi yaga gida yayi kyau sosai,mudai sedai muce allah ya sanya alkhairi.


*Bayan wata biyar*


Adam ne ya fito daga cikin kanfanin ya kara haske da kyau kamar ba a Ado da aka sani a baya ba dan kana ganinsa yanzu kasan kudi yana shigarsa sosai hannunsa rike da makullin mota da kuma laptop dinsa ya dufi wajan motarsa "ya nufa shiga yayi ya wuce gida,






Sakeena Ismail Cameroon ✍️


Comment and Sharee pls 🥰
[10/1/2023, 4:07 PM] Mom Muwadda: 🧝‍♀️MIJIN ATTAJIRA 🧝‍♀️






By




Sakeena Ismail Cameroon
(Mom muwadda)




Page 74&75




Bismillah rahmani rahim




_______"soyayya mai karfi ya kullu a sakanin Adam da jannat suna son junansu sosai dan yanzu kam Adam ya ajiye kunya da kuma wannan tunanin da yakeyi a dah na ganin cewa shi ba dan kowa bane bai kamata yayi soyayya da yer gidan basu kudi ba,amma yanzu kam ya fahimci cewa ba haka bane dama shi bashi da burin data wuce ya dogaro da Kansa kuma Alhamdulillah yanzu yana iya yiwa kansa komai duk da Dady yana hanashi "saboda shi yafison ya dinga mai kafin yayi aure amma da ya fahimci Adam yana son yinwa kansa"komai har ma da mutanan gidan ya gyaleshi kawai .




Zaman da Adam yayi da barista!barista!! ya kara gane halayan Adam sosai shi mutun ne marason hayaniya gashi mai hankali duk da barista bashi ya haifeshi ba amma duk wanda yagansu zai tunani shine ma haifinsa"saboda yadda suke alaka tamkar uba da dansa"gwanin ban sha'awa,






Yana dawowa bangarensa"ya wuce wanka yayi da kuma alwala ya fito shiryawa yayi cikin milk din jallabia turare ya dauka ya fesa yana gamawa ya dau laptop dinsa dake ajiye akan gado ya koma palo ya shiga yin aiki aciki.


Lokaci zuwa lokaci yakan duba agogon dake daure a hannusa'.


Bayan wasu yan mintuna ne naga ya rufe laptop din tare da mikewa ya dau mukulli yayi hayyar bakin kofa fita yayi ya rufo kofa,da alama masallaci zashi.




Bayan an idar da sallah ne suka jera da barista suka nufi cikin gidan kasan cewa masallacin ba nisa da gida daka fita kofar gidan kana ganin masallacin,




Cikin gidan suka nufa suna tafiya suna tattaunawa,




Kallon Adam barista yayi ya fara magana.




Yauwwa Adam nace yanzu kam tun da kun fahimci juna sosai dakai da jannat ya kamata mu zauna mu sa'a ranar bikin naku ko Adam kam duk kunya yayi shesa da yaji barista yayi maganar auransu amma a zuciya kam murna yake,


Sai da barista ya kuma kiranshi sannun yayi magana Dady kune iyayenmu dan haka ba sai kunyi shawara damu ba .




Kawai duk a bunda kuka yanke dai dai ne,




Dama ina da kudi dana ajiye a account dina insha allah in kungama yanke shawara komai sai kayi min magana na bawa mami kudin ta hadomin lefe murmuchi barista yayi tare da geda mai kai,




Shikenan son amma zancen hada lefe karka damu ni da kaina zam bawa mamin naku kudi taje ta hado lefe harda ma kayan dakin in yaso kai ka kawo Sadaki kawai.




Ado zaiyi magana barista ya daga mai hannu,




Kaga dakata Adam kasan dai bana son haka ko.


Kai Adam ya geda tare da fadin nasani Daddy Allah ya wuci zuciyarka.




Godiya nake sosai Dady allah ya kara girma Ameen barista ya amsa.




Karasa cikin gidan sunayi suka nufi palo ba kowa a palon sai sanyin AC ne kawai dake aiki a palon zama sukayi suna kara tattaunawa.


A dakinsu"jannat kuwa tana idar da sallah ta mike kallon Minal dake kwance a kan gado tana dedda wayan tayi kinga Minal ki tashi muje muci a binci dakatar da dedda wayan Minal tayi tare da mikwa ta kalli Jannat din tace muje,kai jannat ta geda suka fita a gyere,




Suna zuwa palon suka tarar mami ma har ta fito,




Shiyasa suma suka nufi wajan cin abinci darek.


A hankali jannat take takowa har ta karasa inda suke,


Tun fitowarsu jannat Adam yake kallon ta har suka karasa wajan bai dena kallon ta ba.




Sai da barista yayi gyaran murya sannun Adam ya dauke ido yana sosa kai dan ya fahimci tsarai dawa barista yake.


Dan murmuchi yayi _yaci gaba dacin a bincinsa"




Zama su Jannat ma sukayi suka zuba nasu suka soma ci.


Bayan sungama ci ne kowa ya koma dakinsa Adam da barista kuma suka nufi masallaci yin sallar isha,






Fitowata daga wanka kenan shiryawa nayi bayan nagama ne na hau bed dina addu'a nayi tare da shafawa.


Kwanciya ta ne yake da wiya sai naji wayata na ringing lumshe idona nayi tare da gyara kwanciya ta,


Dagawa nayi dan nasan tsarai wa zai kirani a wanan lokacin shiyasa ban ko duba ba,


Sallama nayi cikin nitsuwa Adam dake kwance shima jin sallamar tane ya lumshe ido tare da budesu"in kaji yadda yayi shiru dinan zaka zaci bazai amsa sallamar ba ko kuma ince zaka dauka ko sallamar ne bai jiba,


Jannat kuwa data saba da halin kayanta shiyasa bata damu ba dan tasan serai zai amsa,




Wslm habibtina barkanki da wanan lokacin barka dai habibi,




Ina wuni lfy lau alhamdulillah ya gajiyan aiki Alhamdulillah nima na

Please Login or Register in order to submit comment