Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Alhamdulillah ka kwantar da hankalinka,,,karka damu da maganar kaka rantane ya baci da jannat din tace bata ganeta ba"insha allah nn bada zumawa ba,komai zai dai- daita da yerdan Ubangi "geda kai oncle Ibrahim yayi"ya nemi kujera ya zauna, lokaci ya duba,a agogon dake dauré a hannunsa "karfe
Biyar da kwata,ya kalli doctor",,,pls doctor ko zan iya samu nurse din da zata kularmin da itta inje gida in dawo?" Ibrahim ya tambaya,


Sosai ma kuwa mai zai hana bari na yiwa fati magana sai taxo ta kula da itta,godiya oncle Ibrahim "yayiwa doctor"...
Allura bacci doctor yayiwa jannat "dan tana da bukatar wutu sosai,,,
Ai ana mata nan da nan bacci ya dauketa"...




Fita doctor yayi Oncle Ibrahim ya bibayansa har saida suka samu nurse din tukun sann ya bata wani abu ya wuce,sai da ya tsaya yayi sallar a subaha sann ya wuce gida ,,,






"Bayan sati daya da rasuwarsu Daddy"kuma yau akayi sadaka ba kwai, mutann gidan kana ganinsu kasan sunji mutuwar sosai,amma duk da haka basu kai Ibrahim" da kaka"....




Dá kaka sai gobe zata tafi amma tun lokacin da taji za'a sallami jannat "yau sai tace bazata kara kwana ko daya ba,,,


Wai yau -yau dinnn zata tafi " babu yanda Ibrahim maiyi da itta ba"akan ta bari sai gobe amma tace"itta kam gaskiya,bazata zauna ba,
Tafiya zatayi,,,a haka suka gyaleta ta tafi?"




Dama kuma maryam" matar Ibrahim" bataso ta sake kwana dan ta gaji da itta,allah -allah take ta tafi,






Kuma dama itta maryam maceece "da allah yayita ba mai son mutane ba,ko kadan,shiyasa ko momy ma bata fiya zuwa ba,dan tana zuwa' zata nuna bakin ciki, da,hassada,






Dan itta tana so ace mijinta ne"yeke da wannn dukiyar,ba mijin hajiya Asma'u (momy) yake dashi ba,




Babu yanda ta iyane kawai"




Bayan la'asar aka sallami jannat"daga a sibiti, oncle Ibrahim yaje ya dauko ta,suka dawo gida,




Daga dawo a sibiiti, jannat "ta fara ganin a bubuwa iri- iri,har take kwakwanto aiya,a bayama haka rayuwarta take kuwa,,, da tambayi kanta,,,amma babu mai amsa mata wann tambayar tata,






Dan suna dawowa, oncle Ibrahim" yace ta dinga kwana da ameera"a dakinta amma ina,hajiya maryam najin haka tace jannat"bazata kwana da ameera"ba ,




Sedai ta dinga kwana a palo,tajà a kwatunn kayan jannat "ta kwashe duka kayan jannat"din ta bawa ameera "wai su zata dinga sawa, ta kwashe na ameera"ta bawa jannat din,tunda kayan jannat yafi na ameera "tsada, ameera kam ba haka taso ba dan tana son jannat"babu yanda ameera ta iya a haka ta karbi kayan jannat"




Jannat "kuma aka bata na ameera mara tsada sosai,




Oncle Ibrahim ,kuwa dama soron matarsa yake,dan sai abunda tace,akeyi a gidan....






Bayan kwana uku jannat" duk ta rame' tayi baki ,kamar ba jannat "yer gatan momy da Dadi da aka sani a baya ba...




Dan duk aikacen gidan itta ake hadawa dashi"kama daga wanke_ wanke,sharan dakunn har da dakin ameera" itta ake hadawa dashi ta gyara...
Kuma bawai ta iya aikin ba, babu a bunda ta iya,


Atoh mema yer shekara hudu zata iya ?"


Amma a haka hajiya maryam take sata in batayi sosai ba ta zaneta"a yanzu haka bayanta duk shatin bulalane...




A yanzu haka sai data saka mijinta akan lallai sai ya canzawa jannat" makaranta wai wanda take zuwa' yayi sada sosai...




Shiyasa yanzu ba wancan makarantar,jannat "take zuwa ba,wata daban aka samo mata a cikin unguwa,saboda"a ganinta ba sai sun sha wahala wajan kaita makaranta ba,,,






Shiyasa aka samo mata kusada layinsu da kafa take zuwa "kuma bako wana lokaci take samu zuwa ba"saboda aikin da ake sata,




Har a kai ameera itta tananan bata tafi ba "




"A hankali hajiya maryam ta soma cusawa yerta sanar......










Sakeena ismail Cameroon ✍️








Commenta and Sharee pls
[8/29/2023, 1:49 PM] Mom Muwadda: 🧝‍♀️MIJIN ATTAJIRA 🧝‍♀️






By






Sakeena ismail Cameroon
(Mom muwadda)




Page 9&10






Bismillah rahmani rahim




________"a hankali hajiya maryam ta soma cusawa yerta sanar jannat"




Shiyasa yanzu kam ba kamar daba,in ana yiwa jannat "wani abu,ameera na nuna reshin jindadin ,
Sabanin yanzu kuma da in ansaka jannat "aiki ko a jikinta"shiga dakinta take, mamarta ta kunna mata katun ta zauna tana kallon"in jannat ta zo ta zauna zatayi kallo,ameera ta gayawa mamarta "taxo ta kori jannat"din daga dakin,




Zaune suke suna kallo da daddare jannat "gamawarta wanke_ wanke kenn ta shigo falon ta zauna tana kallon mama"




Mama nagama wanke_ wanken ina a bincina yinwa nakeji ?"


Jannat "ta tambaya mama"harara mama ta watsa mata"bakisan hanyar kitchen ba,,,da zaki tambayeni,a binci ko yawo nake da abinci ne
Mama tayi magana tana ci gaba da kallonta....




mikewa jannat "tayi ta wuce kitchen a binci tagani a wani dan karamin roba ko murfi babu wanda tafi awa daya a wajan, daukan a bincin tayi,kwalla na siyayo mata daga kan kuma tunta " ta fita daga kitchen din,,,ta tafi can bayan kitchen din ta zauna ta soma cin abincinta tanaci tana tunani aiya su mamane suka haifeta kuwa ?"






Itta fah gaskiya ji take kamar ba sune suka haifeta ba,,,tanann tana tunani har tagama cusa shinkafa da dan miyar da aka harfah mata akai,,,,




Mikewa tayi taje ta wanko roban dataci a bincin a ciki "tasan in bata wanke bama ittace" zata wanke gobe gwarama ta wanke tun yanzu ta wuta",tana gama wanke roban taje_ ta kifashi a kitchen,,,ta dawo ta zauna "tana jiran su mama da oncle Ibrahim"su tashi daga falon taje ta kwanta tunda a can take kwanciya "...




Tana wajan har wajan karfe sha daya,sann oncle Ibrahim"yazo ya tasheta "tamike daker tashiga ciki,sauro har sungama cinye mata kafah,,,kuma dama mama tana tsane ,bata tashi da wuri daga falon saboda,sauro su samu rabonsu su ma,,,




Kwanciya tayi a kasan carpet din dakin saboda mama ta hanata kwanciya a kan kujera wai kar tayi mata fisari a kan kujera,ta lalata mata" kujeru"shiyasa take kwana akan carpet,,,,




A haka rayuwa taci gaba da tafiya,, jannat" kuwa yanzu rayuwa ta juya mata"gaba daya,,






*Bayan shekaru goma*




"Da rasuwar iyayen jannat"


Kuma a yanzu kam ta fahimci cewa su mama" da oncle Ibrahim "basu suka hayfeta ba,saboda wani lokaci mama takan yi mata maganar iyaye,,,
Wani lokaci takanji oncle Ibrahim da mama sunayin maganar iyayenta "amma har yau ta kasa gane su waye iyayen nata,tunda har yanzu bata tuna rayuwarta" ta baya ba,,,




Jannat !jannat !!


Wata yarinyace sugunne a bakin pampo tana wanke- wanke jin kiran da ake matane,tayi saukin mikewa jikinta har rawa yake saboda tasan halin mama tsarai indai bataje ta amsa mata kiran da tayi mata ba "toh sai tasha duka a wajanta,,,karkade hijabinta tayi,duk_da kodewar da hijabin da tayi amma a wanke take samb babu dadti....




Falo ta wuce tayi sallama ta shiga bata jira an amsa mata ba ta saka kai ta shiga,dan tasan halin mama sarai ba amsa mata zatayi ba,in kuma batayi sallamar ba shima lefine,,,,sugunnawa tayi kanta "a kasa, ta bude maki tace mama gani,




Mtsssss mama taja saki,
Batun dazu na kira kiba?"sai yanzu kikaga damar zuwa kennn,mai bakin hali,kawai...




Wuce kije dakin ameera "dama ittace take kiranki"
Toh tace ta mike ta wuce daki ameera "mama ta bita da harara...




Tana zuwa dakin ameera "tayi sallama ta shiga,,,wata matashiyar budurwa ce take zaune a kan gado tana waya kana gani ta kasan da saurayi take waya yanda take lonkoshe muryar,,




Dan sayawa jannat tayi tana jiran ameera"ta gama waya ta gaya mata abunda yasa ta kirata "tannn saye kusan minti goma amma ameera"bata gama waya ba,mangaren ameera kuwa ta kullu iya kuluwa,,


Sai can ta cire wayan daga kullenta ta fara macifah,,wai ke jannat sayuwan me kikemun a dakine,,,kin wani tsaya kin kuramun ido sai kace mayu ni aiya a dangin momynki babu mayu ma kuwa" ameera tayi magana,tana kallon jannat "




Dama mamace tace naxo kina kirana,da akace kixo ina kiranki sai akace kixo ki sayamun akai,,,kiji mai muke fada da saurayina ?"




Girgiza kai jannat" tayi tace aa dama jiranki nake, ki gama wayanne ki gayamun a bunda zanyi miki "




Karya kike munafika"kawai de kinxo kiji gulma,,,toh allah ba taki ba,dan wllhy babyna yafi karfinki wallhy,,,
dallah malama wuce kije ki wankemun toilet dina wanka nakeson yi,tun dazu, kina bata mun lokaci,sum- sum jannat ta wuce toilé,,




Itta ko ameera "saki tayi"taci gaba da wayarta....




Sakeena ismail Cameroon ✍️




Comment and Sharee pls
[8/29/2023, 1:49 PM] Mom Muwadda: 🧝‍♀️MIJIN ATTAJIRA 🧝‍♀️




By




Sakeena ismail Cameroon
(Mom muwadda)




Page 11&12




Bismillah rahmani rahim






Jannat "na gama wanke toilet ta dau hijabinta" data rataya a kofar toilet din,ta fito ta samu ameera "har yanzu bata gama wayar da take da saurayinta ba,dan durkusawa tayi "tana kallon ameera"data zuba maba ido, duk da wayan da takeyi amma jannat"take kallo,dan wanni kyau ne allah yayiwa jannat din,shiyasa ameera"take bakinciki da kyau da allah yayiwa, jannat" dama ittace take da kyau din jannat da ba karamin rikita samari zatayi ba,




Duk da dai itta ma ba wai munine gareta ba,kawai dai rashin godiyar allah ne ,




Jannat "ce ta kasewa ameera tunani,aunty ameera nagama wanke toilet din,koda akwai a bunda zammiki bayan wanan?"jannat "ta tambayi ameera"...


Mikewa ameera tayi ta nuna mata kan gadonta ,da yenyasan hannunta", jannat ta fahimci mai take nufi shiyasa bata damu da rashin baganar ameera" ba,ta hau gyara gadon,ameera kuma ta koma kan kujera dake dakin,taci gaba da wayan da takeyi, jannat"na gamawa ta fita ta rufo mata kofa,ta koma kitchen ta karasa wanke! wanken !! ,tana gabawa,




Girki ta dora,sai wajan karfe biyu tagama girki,ta share kitchen din tas,ta dauki kulolin abincin data zubawa su mama ta kai musu falo,tadau na mai gadi ma ta kai masa,


Cikin gidan ta koma ,daukar a bincinta"tayi taci ta koshi ?"
tamike _ta kai kwanon kitchen ta ajiye ta fito,wajan pampo taje,ruwa ta tara a bucket, dauka tayi ta nufi toilet "
din sakar gidan ,kasancewa ann take wanka kullun,


Wankanta tayi ,tayi daurin irji ta maida hijabinta"fitowa tayi ta wuce falon lokacin mama bata ciki, mai dinta mara sada ta dauko ta shafa,ta saka infom dinta na slamiya,turare ameera data kusa karewa ta... bammata "shi ta dan fesa, jakarta ta dauka ta rataya,fitowa tayi ta nufi dakin mama,sallama tayi sai da aka bata izinin shigowa,sannn tasa kai ta shigo,


Dan durkusawa tayi,ta bude baki tace mama nagama aikin zan tafi islamiya?"dakowa mama tayi,ta fara magana,yanzu jannat "kin gama abinci tun dazu sai da kikaje kika cika naki cikin"mu kika barmu anan,bazaki iya zuwa kice kingama abinci ba?"shine sai yanzu zakixo kisameni kice kingama?"kiyi hakuri
Mama"jannat ta fada ?"saki mama tayi tace da allah malama ki tashi ki fitarmin daga daki ,mikewa jannat"tayi sum- sum ta bar dakin jiki babu kwari,


"Itta kam ta rasa wacha iriyar tsanace mama da yerta suke nuna mata ?"


Amma tayi alwashi saita gano koma menene ya haddasa shi,




Fitowa tayi, taiwa mai gadi sallama ta wuce islamiya,,,basu suka tashi daga islamiya ba sai wajan biyar da rabi,tana" tsauri ta koma gida ta dora abincin dare,




A hanyarta"'ta dawowa daga islamiya ne ,a wani kofar gidan da take wucewa kullun kafin taje islamiya,taga mutane cike a kofar gidan"kamar dai biki ko suna akeyi a gidan saboda yanda mutane ya jika sosai a kofar gidan,bata"gama tantancewa komai akeyi ba,taga anfito da gawa rike a hannun mutane "
Ai se kawai tunanin baya ya soma dawo mata"har take gani gawan da aka dauko a gabanta "gani take tamkar su momy da Dadinta ne aciki "dukda karancin shekarunta a wancan lokacin amma tana iya tuna komai,har da rayuwarsu da tayi tare da iyayenta"..


Ta yayama zata manta" da wannn rayuwar cike daso da kauna,


Itta din allah yayi mata baiwar rike abu sosai...




Shiyasa bazata taba bantawa da iyayenta ba.


Tana cikin wannn tunani_ tunanin ne,idonta ya soma rufewa tun tana iya hango mutanen dake gabanta har ta dena ganinsu gaba daya"...




Wani mutunne ya tawo da hanzarinsa"dagata" yayi bai saya ko ina ba sai a sibiti,yana zuwa a sibiti"aka karbi jannat aka shiga bata taimakon gaggawa,,,




"A can gida kuwa mama ta cika tayi fam ta inda take shiga batanan take fita ba "jannat"tasha sinuwa bila adadi,,,ta tafi wajan samari taje ta zauna ta barsu da yinwa,
Zata dawo ta sameta "wllhy sai taci ubanta"
Mayya kawai,tayi tayi har ta gaji tayi shiru...


Kai ce karanse ka dauka jannat din na wajan,,,yanda take wann balayin,,,,




Ga yerta ameera" ta fita har yanzu bata dawo ba, amma ko a jikinta "bata ma damuba ko kadan...
Dama kuma ta saba tafiya taje ta wuni da samarinta amma mama ko fada bata mata"


Sai sanda taga dama take dawowa,,




A sibiti "ba a wani dau lokaci sosai ba jannat"ta.....




Sakeena ismail Cameroon ✍️




Comment and Sharee pls
[8/29/2023, 1:49 PM] Mom Muwadda: 🧝‍♀️MIJIN ATTAJIRA 🧝‍♀️






By




Sakeena ismail Cameroon
(Mom muwadda)




Page 13&14






Bismillah rahmani rahim




_______ba'a wani dau lokaci sosai ba jannat "ta farfado,kuka sosai ta dingayi tana kiran sunnn momy da Dadinta,ai barista Kamal naganin haka ta mike da hanzari taje ta sanarwa da doctor jannat "ta farfado,
Bi bayan barista doctor.. yayi suka dawo dakin tare,har yanzu jannat" bata dena kuka ba,ta na cikin kukanta "kome ta tina oho ,sukam gani kawai sukayi tayi shiru tana goge hawaye.




Murmuchin mai ciwo tayi tana kallon doctor"


Sai ta fara magana, doctor ka sallameni naji sauki gida nake son komawa"nasan mama nacan na nemana,kallon doctor barista yayi,ya fara magana, doctor,ya naga ta ambaci sunan wayenan mugayen mutane?"murmuchi doctor"yayi ya dafa kafadun abokinsa"ka kwantar da hankalinka"yanzukam ta tuna da komai" kwakwalwarta ta dawo normal kamar yarda muke fata.




Murmuchin jin dadi barinta yayi shima,yace Alhamdulillah" masha allah, yace baby ya jinkin naki?"jannat "taji dadi da sunan da barista ya kirata dashi amma bata "nuna ba,tana mamaki ina yasan sunan baby in bata manta ba, zata iya cewa iyayenta ne kawai suke kiranta da sunan baby".
Barista ina kasan wanan sunn nawa?"jannat"ta jefawa barista Kamal tambaya ?"


Jannat"ba lallaine ki sanni ba,ni abokin ma hayfinkine ,kafin allah yayi masa rasuwa nayi mai alkawari da dama,
A ciki kuwa adda aurar dake ga mutun na gari ".
Bayan wannan a kwai wani kanfaninsa guda biyu daya mallaka miki shi tun kina shekaru hudu kacal a duniya..
Babu wadda yasan da maganar daga ni sai momynki mukadai muka sani ,ni dinma saboda yerda da Dadin naki yayi da nine yasa nasani,sai kuma yanzu da na gaya miki sai kuma doctor ".barinsta na kallon doctor yace doctor ina so kayi mun alkawari bazaka taba gayawa kowa"wanan maganar ba?"barista yayi magana,haba _haba a bokina sai kace baka san halina ba, nayi maka alkawari babu wadda zai sani insha allah"murmuchin jin dadi barinta yayi yace Alhamdulillah" nagode "sosai abokina,yanzu ya jikin jannat"din,shin zan iya tafiya da itta"barista ya tambaya?"sosai ma kuwa bari na rubuta muku ta kardan sallamar dan naji jikin nata normal,godiya barista ya kumayiwa doctor ".


Ta kadan sallama doctor"ya bawa barista,suka wuce gida.




Lokacin dare yayi sosai,shiyasa barista Kamal ya yanke shawara "ya kaita gidansa kawai gobe in allah ya kaimu sai ya maita itta" gidan oncle Ibrahim" din.


Jannat" na ganin sun nufi wata unguwa daban ba nasu ba,ta juya ta kalli barista,barista ba gidanmu zaka kaini ba ?"


Jannat" bakiga dare yayi sosai ba,muje gidana inyaso gobe sai na kaiki gidan naku ko?"girgiza kai jannat "tayi tace wllhy mama zata dekeni in na kwana a wani waje daban.


Karki damu jannat "in na kaiki gidan naku gobe zanyiwa maman magana,zan gaya mata cewa bakiji dadin bane shiyasa,baki dawo ba,




Geda kai tayi amma ba haka taso ba,itta kam tafiso ta kwana a gida,
Amma a haka suka wuce gidan barista"suna zuwa,ya yiwa matarsa bayanin komai,ta dauki jannat "ruwa mai zafi ta hada mata tayi wanka kaya ta kawowa jannat "cikin kayan yayanta,ta saka,ta bata a binci taci ta dauki magungunan da barista yace ta bata -ta
Bata shima tasha.




Umarni ta bawa jannat din data kwanta "kwanciya jannat tayi nan da nan bacci yayi awan gabada itta"sai data tabbar tayi bacci,sanan ta barta ta koma dakin mijinta"...




Washe gari


Jannat "tun a subaha data tashi bata koma ba,
Kan dagon data kwanta a kai ta fara gyarawa tana gama gya kan gadon, toilet din dakin ta wanke tas, kasa ta sauka ta share falon tana cikin yin moping matar" barista" ta sauko,durkusawa jannat tayi har kasa ta gaidata "matar barista ta amsa fuska a sake..




Haba jannat"ya zaki tashi tun yanzu kina aiki keda ba lfy ce dake ba,
Murmuchi jannat "tayi tare da fadin ai mama na saba,agida da wuri mamarmu take tashina inyi aiki,shiyasa na tsaba"ko banida lfy ba barina take ta kwanta"ba kinga kuwa dole na tsaba,geda kai matar barista tayi hawaye na ciyayo mata akan kumatu,wannn wana irin zaluncine haka,yen uwanka amma zasu nuna maka kiyayya karara..


Dan dafa kafadun jannat "matar barinsta tayi tana kallon jannat", jannat"innace kidawo nan da zama zaki yadda?"geda kai jannat"tayi tace eh zan yedda cedai kuma bazan iya dawowa nan ba,saboda "mama da oncle Ibrahim"zasu hanani,yanzuma in nakoma gida bansan wana hukunci zasu mun ba,na kwana a waje...




Ki kwantar da hankalinki jannat"babu a bunda zasu miki,kuma insha allah"barista zai masa magana,kinji yata ?"
Geda kai jannat"tayi,matar barista ta umarceta data je tayi wanka,in barista zai fita zasu tafi tare,a kaita gida,toh tace ta wuce sama"itta koma matar barista"dakin yayanta "ta wuce,tana zuwa'dakin,yemmatane kuda biyu daya batafi sa'ar jannat"ba daya kuma ta dan girmi jannat "da kadan,kallon karamar matar barista tayi,ke Minal ki ban kaya zan kaiwa jannat"zata saka in tayi wanka,
Dan yasine fuska wanda aka kira da sunn Minal tayi,ta fara magana,haba momy jiya ma fah na maki kayan baccina kin kai mata,yanzu kayan baccinne da kika bayer shine zaki tsaya kina magana akai,walida tayi magana?"


Tana kallon momynsu"
Momy bari ni na dauko mata a nawa sai na kaimata "geda kai momy tayi dace allah miki albarka walida"ke kuma Minal allah ya shiryeki "mé abun duniya dan allah,kullun sai nayi miki fada akan abun duniya amma bakiyaji ko?"toh shikenan "ni nasan ta waca hayya zanyi maganinki",ta fita tabar musu dakin, kallon Minal walida tayi,kedai allah ya shiryeki da bakin halinan naki Minal" ameen minal" ta amsa ba kunya ta kara gaba.




Toilet ta shiga ta bar walida a wajan, girgiza kai walida tayi"ta bude wardrobe dinta ta daukowa jannat"kaya,ta wuce dakin momynsu,kai mata kayan,dan tasan a can momyn nasu ta sauketa,




Tana zuwa tadan kwankwasa taji shiru sai kawai ta shiga, tana shiga ta nemi gefen gado ta zauna,tana jiran jannat"ta fito daga wanka,dan tana da yakini wanka jannat"take.......






Sakeena ismail Cameroon✍️




Comment and Sharee pls
[8/29/2023, 1:49 PM] Mom Muwadda: 🧝‍♀️MIJIN ATTAJIRA 🧝‍♀️




By




Sakeena ismail Cameroon
(Mom muwadda)






Page 15&16




Bismillah rahmani rahim


______ba'a dau lokaci ba jannat' ta fito daga toilet daure da tawol din da momynsu walida ta bata, "kanta akasa batama kula da walida dake dakin ba,har saida ta karaso dab da gadon taga kafar mutun ai batasan santa ta dago kanta ba,tana ganin walidace ta juya a guje zata koma toilet walida"ta riko hannunta tana mata dariya,sunkuyar dakai kasa, jannat "tayi saboda kunya,itta kam tunda take babu wanda ta taba ganinta a haka sai yau,duk da macece itta walidan amma sam jannat"bataji dadi ganinta da walidan tayi a haka ba.




Kai sis me haka,kunya ta kikeji ne,dama kayane momy tace nakawo miki,walida ta fada, tare da mikawa jannat "doguwar riga abaya dake hannunta",karba jannat "tayi ta mata godiya,bata jira walida ta amsa ba,tayi toilet taje ta saka rigar ta dawo dakin,


Sai a lokacin ta dago ta kalli walida sosai, murmuchi walida tayiwa jannat,tana tambayar ta ya sunanta,?" jannat ".
Jannat'din ta fata,waw suna mai dadi gashi kuma kina da kyau sosai.
Walida ta fada,dan kyau jannat"din ya tafi da imaninta sosai,




Zaki zama kawata ?"walida ta tambaya, murmuchi jannat"tayi dan itta kanta walida ta burgeta sosai...


Mutane deyewa sukeso ta zama kawarsu amma bata basu fuska ,


Shiyasa a school itta kadai take zama in anfita break kamar mayya...




Amma yau sai taji walida ta kwanta mata arai .
Bude baki jannat "tayi daker kamar batason yin magana,ta kalli walida tace..nikam ba kawance nakeso muyi ba, ina so ki zama yer uwata .. jannat "ta fada tana kallon walida".




Na yedda daga yau munzama sisters walida ta fada,dariya jin dadi sukayi su duka.


Nikam zan iya cewa ma ban taba ganin dariyar jannat "ba,sai yau.dan kullun cikin kunci take.
Amma yau hadda fararen hakoranta a waje..




Momy ce ta shigo dakin tace toh uwar tsurutu kinzo sai zuba tsurutu kike,ga abbanku can yana kira..


Mikewa walida tayi tana dariya ta fita,kallon jannat "momy tayi,tashi muje kiyi breakfast sai ku wuce ko?"mikewa jannat" tayi tabi mayan momy suka fita,suna zuwa falo,gaida barista tayi "yana tambayarta ya jiki tace da dauki,wajan zama aka nuna mata"ta zauna walida da mike ta zuba mata a binci..




Suna gama cin a binci ..
Barista ya kalli jannat ".
Jannat"tashi muje ko,mikewa jannat tayi jiki babu kwari ta wuce sama,su momy suka bita da kallon tausayi,kayan slamiyanta ta dauko da maganinta,tadawo falon rakiya suka mata "har bakin mota, tashiga suna daga mata hannu har suka bar gidan,hawaye jannat"ta goge barista ya juya ya dan kalleta yaci gaba da tuki.ba wadda yayi magana a cikinsu har suka karasa"kofar gidan...
Kishiga kiyi mun sallama da abban naku kice ana sallama dashi"kinji jannat ?"barista yayi magana,geda kai jannat tayi"ta fito daga motar kamar wata munafuka"
Ta shiga gidan,aiko tana shiga kamar dama itta suke jira, mama da ameera na ganinta suka hau masifah,


Kinganta ko mama ai dama nasan wajan sama rinta taje ta kwana bakiga har da wani kayan ma ta dawo dashi ba...
Bayan kuma da infome din islamiya ta fita dashi.


Ameera ta fada tana hararan jannat "kai seka rance itta bata zuwa ko ina,mamace ta karbi zancen,da cewa ai nagani dama na dade da sanin cewa jannat"na yawon banza, kawai dai ina jiran wannan ranar..
Alhamdulillah yau kam kuma kunkani da idonku.
Jannat "tace wllhy mama ba a bunda kuke tunani bane?"a hayyata ta dawowa daga islamiya naga wani gawa daya tunamin da iyayena"shine na yanke jiki na fadi,badan wanan baristan ba , da bansan a wana hali nake ciki yanzu ba , tunda jannat"ta fara magana suka tsareta da idanu,


Ameera tace karya take mama kinga wanan fuskan yayi kama da mara lfy ne ?"mama ta amshi zancen da cewa,ina fah kina ganinta kinsan babu wata rashi lfy da dayi, na tabbata baristan da take magana a kaima saurayinta ne suka hada baki su raina mana hankali,in da gaske meyasa bata xo tare da shi ba,ameera ta fada..
Yazo yana waje yace nayi mai sallama da abba,jannat "tayi magana,




Mamace ta fito kofar gida taje ta leka, babu ko mayafi a kanta,wata bakar mota mai kyau ta hango pake a gefen gidan nasu.
Cikin gidan ta koma,taje ta fadawa mijinta,fitowa yayi kofar gidan,yana hango motar barista ya karasa awajan,


Barista kuwa yana ganin Ibrahim ya fito daga mota,hannu barista ya mikawa Ibrahim sukayi musabaha,dama kuma sun san juna kawai dai babu a bunda ya taba hadasu ,ko zaisuwa ma bai taba hadasu ba sai yau,dan Ibrahim mugun tsana yake yiwa barista "wai barista ne yake zuga yayanshi,a kan komai har dama harkan kasuwancin sa,




Baristane ya kacewa Ibrahim tunanin da maganarsa "kwana biyu Ibrahim tun rasuwar yayanka, baka neman mutane, murmuchi mai kamar dole Ibrahim yayi,haba dai barista,kuma ai ba'a ganinku tun lokacin,da aminiyar ka ya rasu...




Yanzu dai ba wannanne ya kawoni ba,dama a kwai wani rasuwa da akayi a unguwar nan,shine naxo, zamu je zana'iza,sai ga jannat "ta fadi sakamakon ganin wannn gawar, da gudu na karasa wajan,da farko dai banganeta ba,sai dana karasa wajan,na ganeta,shine na dauketa na kaita a sibiti, alhamdulillah muna zuwa a sibiti,bamu dade sosai ba, ta farfado,a nan ne doctor yake shedamun cewa ai tunaninta ma ya dawo,ban tabbatar da zancen doctor ba,saida naji jannat"na kiran sunan iyayenta,sai alokacin na gamsu da maganar doctor..




Sanda aka sallamemu dare yayi sosai shiyasa ban dawo da itta ba,shine mukaje gidana "ta kwana,sai yanzu allah ya nufa dawowarta"...




Muma dama inaso mu tattauna wata muhimmiyar magana,daya shafeta kuma ya shafeka kaima,amma ina son musamu waje mu zauna tukun sai muyi magana..
Bismillah Ibrahim yayiwa barista "suka nufi cikin gidan,a falo suka zauna,
Ibrahim yace ina jinka barista,




Dan gyara zama barista yayi"sai ya fara magana,
Kafin dan uwanka ya rasu.....






Sakeena ismail Cameroon✍️




Comment and Sharee pls
[8/29/2023, 1:49 PM] Mom Muwadda: 🧝‍♀️MIJIN ATTAJIRA 🧝‍♀️






By






Sakeena ismail Cameroon
(Mom muwadda)






Page 17&18






Bismillahi rahmani rahim




_______"kafin allah ya dauki ran dan uwanka, ya bani wasu ta gardun kanfaninsa da kake aiki,yace ya mallaka maka itta,da kuma gidajensa guda biyu wadda suka zauna aciki kafin allah ya musu rasuwa,da kuma wanda

Please Login or Register in order to submit comment