Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mu tattauna” ai rige rige akeyi suka kutsa suka nemi guri suka zauna hajiya tasallah cewa take
“Likita ka gayamun halinda Farid yake ciki?”.

Likita ya numfasa yace “A gaskiya Farid yana cikin matsanancin hali halinda bazan iya misalta muku ba yana cikin tsantsar damuwa yana bukatan farinciki a tattare dashi koh kunada masaniyan cewa zuciyarsa gab take da bugawa? You are his parent dole kunsan damuwarsa?”
Hajiya tayi fiki fiki da ido lokacin da Ambassador ya kafeta da ido yace
“Likita ka ganta duk itace silar rugujewar rayuwar Wannan yaron ta rabashi da matar daya gani da idonsa yace yana SO sukayi aure ta rabashi da ita lokacin da take tsananin buk'atan taimako lokacin da yaron cikinta yake gabda fitowa duniya, tayi kokarin rabashi da matarsa da zafin hakan yasa yarinyar tayi masa bakin cewa saiya nemi DA' ido rufe yarasa ilai hakan tafaru gashi yana son haihuwa Allah bai bashiba likita ya kake tunanin uwar datayiwa wata uwa haka Allah zai duba lamarinsu?”
Likita ta numfasa ya jinjina girman maganar yace
“Ita matar tasa ina take? Kuma ina abunda ke cikin cikinta? Bakuda masaniyan inda take koh mahaifarta?”.

Suka kada kai hajiya tafara magana “Yarinyar ta kasance yar bariki ce don haka bamuda masaniyan inane garin nata ada nasan tana Garin Soba don achan aka daura aure kuma Bayan wasu lokuta farid yasha zuwa amma babu ita babu labarinta har makociyarta an tambaya amma tace batasan inda ta nufaba”likita ya jinjina kai yace koh zaku iya Sanin sunanta kila asa cigiya koh Allah zaisa a ganta?”Hajiya tace “Eh kwarai nasan sunanta farin sani”
“ko zaki iya sanar dani sunanta?”
Hajiya tace
“Sunanta RAINA” Dam Likita yaji gabansa yayi mugun fadi da mamaki masu karatu zasuce waye Wannan likitan toh ba kowa bane face abokin Yarima danish Wato Doctor moddibo, kallonsu yakeyi ido cikin ido yace
“Kunaso kucemun Gimbiya RAINA yar sarkin kajuru MAMUDA?”da mamaki hajiya ta kalli Likita tace
“Bafa Gimbiya bace sunanta RAINA wata yar bariki ce wacce taba bariki gaba ba bayaba tananan da wata tsohuwar kilakin uwarta wai ita Goggo” Likita yace yana zuwa wayarsa ya dauko ya budo hoton RAINA da yarima Danish yace
“Hajiya ki kalli Wannan hoton itace RAINA da kike magana? Don nasan itama Wannan ta taba fadawa irin Wannan halin ta sanadiyyan saceta da wata mata tayi a daidai lokacin da uwarta ta haifeta” da sauri suka amsa wayar Suna dubawa da mamaki hajiya tasallah tace
“Biri yayi kama da mutum ai Likita lokacin tsaida ruwan miya yayi itace Wannan Wallahi itace babu tantama” Likita ya amshi wayarsa ya maidata chargi, yaci gaba da cewa
“Amma inhar Wannan ce yar sarki ce kuma batada wani da banda cikin dake jikinta haihuwa yau koh gobe abokina take aure kuma shine yarima mai jiran gado, kuma ban tabajin labarin tanada wasu yaya ba kuma ni dinnan babu inda bana shiga babu wasu yara acikin gidan Wanda yake bako a wajena”.
[5/3, 7:29 PM] Melody🎤🎤: *191-195* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻


©
_*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_



This page goes to my Entire family which is MANGUTA @BIDA GBAKO LOCAL government may Allah continue toh shower his blessings unto my family Much love with my beloved sisters' MARYAM SHEHU MUHAMMAD, FATIMA SHEHU ABDULLAHI, SAHURA SHEHU AMEENU, SADIYYA SHEHU ADAMU love you all❤😘😍. PROUDLY NUPE💃🏻💃🏻💃🏻








BABI NA TALATIN DA TARA




Shuru hajiya tayi ta kasa koda motsi cikin ranta tace kaji rabo na minallahi daman yar sarki ce bansaniba kaico na duniya shiyasa wulak'anta Dan Adam bashida dadi tabbas nayi dana Sanin yiwa RAINA Wannan cin mutuncin Tabbas nasan bazata taba yafemun ba, Ambassador Buba yace “Likita duk yadda akayi itace Wannan koh zaka iya yimana kwatancen inda zamu samu RAINA?” Likita yace tabbas da kunje kajuru kukayi tambaya gidan sarki MAMUDA toh babu tantama gidansu raina za'a kaiku” sunyi godiya daga bisani wata nurse tafito tace musu Mara lafya ya tashi ai tuni suka fara rige rigen shiga kwance suka taradda Farid baya koh iya magana bare kuma yakaiga daga hannu kallon muneerah yake cikeda tsana tunda sukayi aure babu abunda ya tsinta illah tulin kaxanta daga ta jiki harta kaya zuwa abinchi ga tsantsar rashin kunya datakeyi mai babu girmamawa tsakaninsu daya fita itama zata fita Kullun tonon Asiri takeyimai wajen yan',uwa da k'awaye duk yadda sukayi dashi a gado saita fallasa abunda akace sirri ne tsakaninka da mijinka, hawayene suka zubo a girbin idanunsa lokaci daya ya kalli hajiya ya kauda kai tuni hajiya tafara kuka Likita yace “Baya bukatan kukanku face adu'a itace magani Ambassador Buba mahaifin Farid ya matsa kusadashi yace “Be a man and always be a strong hearted man men don't cry but women does DAT is the different btwn a man and a woman kasha kuruminka lokaci yayi dazamu he wajen RAINA mu roketa gafara Sannan ta sanar damu yadda tayi da Dan cikinta” ai Farid baisan lokacin daya tashi daga kan badon Asibiti ba yace “Dad are you serious dagaske kake kasan inda Raina take? Allah yasa RAINA ta aminche dani a karo na biyu tazamo matata koh zuciyata zata samu sa'ida”.

Tausayin Farid ne Yakama hajiya tace “Farid dole kadauki komai a matsayin kaddara data riga fata RAINA matar aurece babu kai babu aurenta yanzu haka tana daukeda juna biyu na mijin datake aure don haka hakuri yaxama wajibi a garemu baki daya” farid ji yayi ransa ya baci dajin kalaman hajiya acikin ransa yace “hajiya kece silar komai daya faru dani Allah ubangiji kasa RAINA ba zubarda Dan cikinta tayiba duniya dana muzanta Fatana Allah yasa Raina ta yafe mana nida mahaifiyata”ai tuni Farid ya warke suma dayake masu tsohuwar dukiyane haka akayi convoy na motoci sai garin kajuru abakin kofar gidansu RAINA Daga saman bene RAINA ta hangi motoci a kofar gida an bude musu kofa mamaki bai gama cikata ba saida tayi tozali da Hajiya tasallah Sannan ga farid da farida ga yayan farid sai kuma mahaifinsa mutum gudace raina bata ganeba Wato muneerah wacce babu tantama kila matar Farid ce
RAINA ta gyra zama tana shan madara wacce itace abun Shanta tunda cikinta ya tsufa.
Cikin fada Sarki MAMUDA yace su shiga suka zazzauna sai kirari akeyiwa sarki nan hajiya tasallah ta natsu saboda Sarauta ta wuce gaban wasa gashi fadar ta tsaru iya tsaruwa nan suka gaisa da Ambassador buba daga bisani Ya labarta mishi dalilin zuwansu da abunda ya kawosu sarki MAMUDA yayi matukar mamaki a inda yake Sanar dasu cewa RAINA bata taba aureba bare haihuwa yarima shine Wanda ta fara aura, Tuni Farid ta durkusa gaban sarki MAMUDA yace “Ranka yadade Allah yaja zamani RAINA matata ce wacce nafara aure tun farkon kuruciyana” nan shima Farid yasanar da mai martaba komai, lokaci guda yasa aka kira mishi sarauniya Maimuna cikin gaggawa jakadiyya tadawo tace “Allah yakarama imani Gatanan tafe” haka yasa aka kira mishi yarima shima akace gashinan tafe Gimbiya yar sarki kuma sarauniya Maimuna ce tafe cikin kayan kasaita fifita kawai ake mata tana tafiya kamar mahauniya dukda girma yazo bai hana kyawunta fitowa ba.
[5/4, 7:07 PM] Melody🎤🎤: *196-200* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻


©
_*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_



_*Wannan shafin nakine Mai Nicky din mummy na Wato (HAJJA CE) Allah yabar zumunchi yabar kauna Sannan kema kina RAINA🤔 ROOKIE KAX Wish you Allah's blessings😘*_





BABI NA ARBA'IN


Tana isa ta nemi guri ta zauna a kan kujerar zaman mutum guda sai kirari ake mata yar sarki jikan sarki matar sarki uwar Gimbiya RAINA Allah ya kara miki lafya da Nisan kwana, Hannu kawai tayi musu sukayi shuru ai hajiya tasallah sai aka kara sakin baki Allah magani sarki MAMUDA ne yayiwa Sarauniya Maimuna bayani abun yayi matukar bata mamaki tace
“Ai Wannan maganar cikin mu bamuda Wanda zai bamu amsar maganar nan da cikakken bayani sai RAINA don haka inajin Wannan ba lokacin magana bane saboda a halin da ake ciki Raina tana matakin da batason wani hayaniya saboda juna biyun datake dauke dashi kunsan mai ciki babu abunda takeso sai kula da tarairaya don haka ku kuje sai ta sauka hankalinta yadawo jikinta sai ayi magana Ranka yadade ina fatan banyi maka shisshigi ba koda yake ai mijinta shima yanada abun cewa”
Shima Danish haka akayi mai bayanin komai cikin razana da rashin fahimta yace “Ranka ya Dade Wannan ai zancen banza sukeyi zancen wofi inda RAINA tazo da DA' koh ta taba haihuwa koda bada aureba yaci ace mun sani amma yadda Ammi tace haka za'ayi kuje har saita haifamun Dan dake cikin cikinta saboda banaso wani koh wata suyi mana sanadiyyan salwantar abunda ke jikinta” hajiya tasallah tace
“Allah magani yau nan nake ganin iko da mallaka dank'ari uwarta da mijinta sunyi mana haka inaga uwar gayyan ai inajin saita tsireni hmm nan ake son DA' Niko danayi ruwa nayi tsaki ai gashi hau ta hauni Allah na tuba kayafemun ” haka yarima danish ya tashi aka bishi da kirari itama Sarauniya Maimuna ta mike koh sallama batayi musu ba saboda sun bata mata rai” mai martaba ne ya basu hakuri yace suje sa dawo wani loton, Farid sai sake sake yakeyi acikin ransa yana cewa “Hmmm lallai ne yarima kake kowa inajin duniya baka taba son RAINA irin yadda nasota ba amma Bai laifina bane rabuwa da ita haka baka kaini son Dan cikin RAINA ba dukda ba cikina bane amma Allah ka dubi zuciyana ka haskaka mun da haskenka kabani haihuwa ya Allah banida laifi.

Haka akayi musu rakiya haka da Ambassador buba da sarki MAMUDA sukayi Exchange na lamba don Susan lokacin da Raina tasamu lafya, farida haushin hajiya kawai takeji suna shiga mota tace
“Yanzu dai *Ruwa cikin chokali ya ishi mai hankali wanka* Wannan saiya zama darasi Allah ba azzalumin kowa bane kuma duk abunda ka shuka komin girmansa zaka girba Sannan kuma *Alhaki kwikwiyone* kuma baishi yakeci batareda yayi tambaya ba” Hajiya ta bige mata baki tace *“Ke Ubanwa kikewa jirwaye mai kamar wanka kisani ban taba son raina ba kuma bazan sota ba koh zuri'a banason hadawa da ita bare wani nata Wannan ma inayine saboda Wancan sakaran da yakeji kaman zai kashe kansa ga matar Arziki chan muneera*” muneerah dake gefe tace
“Hajiya bakida abun cewa a halin yanzu dole ki durkusa kiba RAINA take kowa hakuri ta yafe muku koh inada rabon ganin k'waina tareda annurin zuciyana Wato Farid a duniya hajiya yaci ace kin saduda kisani inhar nakara shekara ban samu cikiba Wallahi aurena da Farid yakare jiba juya ba amma a tauyeni lallai”hajiya bakaramin haushin zancen muneerah tajiba amma saita basar tana yake mugun kuka tace
“Aunty munee ai ba'ayi hakaba insha Allah kaman kin haihu me kikeci na baka na zuba?”farida tana jinsu saida aka kai wajen unguwansu tace
“Toh nidai zan sauka daman Idan mutum yaki sharan masallaci zaiyi ta choci”
Haka ta sauka sukuma suka wuce.
*GARIN SOBA*
Jamila ce Wato Ummu Abrar zaune yara sun zagayeta abun mamaki dana irga naga yara iri daya kala uku Bayan abrar da fai'z da fai'za dana sani zaune take ta tasasu tanayimusu ta tatsuniya daka gansu zaka gane suna cikin walwala ga wani kara kyau da Jamila tayi suna cikin wasanne Abban abrar yadawo da gudu yaran sukaje suka rungumeshi haka itama Ummu abrar ta rungume shi abun gwanin ban sha'awa ta amsa kayan hannunsa tana yimai barka da zuwa tanayimai sannu abunda yasa a koda yaushe yakejin tsantsar son Jamila kenan tun baysn samuwar farinciki a tsakaninsu, haka yaran suka wuce falonsu don yadda ta koyar dasu dazaran mahaifinsu yadawo sukayi mishi sannu da zuwa toh sauran lokacin natane, saboda bataso su samu tangardan tarbiya dukda yaysnta mata basuda yawa, dakin mata daban na maxa daban dukda suna kanana don babu Wanda take shayarwa, sai kuma katafaren falonsu Wanda aka kawatashi da kayan wasa iri daban daban basu kallon wani film inba carton ba har sun saba, saboda Jamila tace barin yara suna kallace kallacen film din India, america, Philippines, Nigeria film harma dana Hausa yana taimakawa wajen gurbata tarbiyan yaro Allah yasa iyaye muyi koyi da Ummu abrar Amin.
[5/6, 6:07 PM] Melody🎤🎤: *201-205* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻


©
_*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_



_*Kuyu hak'uri k'wana biyu makaranta ne ya boyeni amma nakusa karasawa in huta kuma ku huta😜 LYSM😘*_














*BABI NA ARBA'IN DA DAYA*



Falo yashiga ta taimakamai wajen gyra kansa donyin wanka da su cin abinchi saida ya natsu yafara sanar da ita labarin daya samu daga RAINA akan su fa'iz da faiza bakaramin razana tayiba tace
“Haba ai wasane yana ganin zamu bashi yayane a banza dole hukuma ta shigo Wannan maganar kohda munyi don Allah toh saimun kwato ma RAINA darajarta da kima yasancewa da ba abun wulakantawa bane da gashi har uwarsa data shirya muguntar” Abban abrar yace
“meye naki na tada jijiyoyin wuya? Iyeh ai saisunyi dasun Sanin amsansu koh ince zasu samu ysyansu da tsada”nan sukayita shawarwari nan suka zauna da shirin zuwan amsan yara.
***********
Raina ce kwance tana salati ciwo ya isheta sai sumbatu yakeyi tana kiran sunayen Allah saida Raina ta lissafasu daga farko har kashe gaba daya gida ya rude ga jini sai malala yakeyi tuni RAINA ta suke yarima Danish kuwa da Unaiza hankalinsu ya tashi adu'a kawai sukeyi cik aka dauketa aka sata acikin mota babu inda aka yi da ita sai Giwa hospital inda nanne folder din ilahirin zuriarsu take nan aka shigar da ita Emergency batasan Wanda yake kanta ba Danish karatu kawai yakeyi mata yassara duk abunda ya sauwak'a Unaiza kuka take rusawa acikin ranta tace
“Ashe haka haihuwa take tabbas mata abun tausayawa ne ya Allah ka dubi zuciyana inaso koda irin Wannan azabarce ta nakuda inaso inyini inayi inxan haihu” ni humairah nace yar sheba kawai Ashe dai kinason haihuwa.

Doctor nuraini ne yafito daukeda wani fayal yace
“Ina mijin patient dinnan?” da sauri danish yace “Gani”
“Inaso kasa hannu a Wannan fayal din Saboda matarka aiki zamuyi mata don da alamu batada karfin daxata iya haihuwa”cikin sauri danish yasa hannu fadawa da kuyangu suma adu'a sukeyi Unaiza kuwa babu um ba um Ummu sai ido dake zubarda hawaye cikin ranta tace
“Matsayine danka koh ya sukiraka da Mama saboda irin azabar da iyaye kesha wajen haihuwa tabbas duk macen datasan zafin haihuwa dole takara imani dason uwarta”.
Saida akayi awa biyu ana aiki duk aikin da akeyi ni humairah banga abunda RAINA ta Haifa ba Sannan naga alamun tana numfashi a cikin talabijin din dake manne a bango, likitane yafito fuskarsa babu wani walwala koh murmushi yace
“Munada buk'atan jini kaman Leda uku so samu kuma yanzu da gaggawa?”Danish yace “Likita muje inbada nawa wai Likita har yanzu bata haihu ba?” Unaiza tayi sauri tace “Likita koh nima za'a gwadani Idan jinin yazo daya sai a diva?” Danish yayi mata wani mugun kallo yace “Ke asuwa *KALAN DANGI* dallah ja chan nine dan'uwanta kuma jinina za'a diba asa mata mtwww barren kawai” Abunda yayi masifar batama Unaiza rai shine yadda Danish bayajin kunya koh nauyin cemata juya nida mai karatu mukace tsuntsun dayaja ruwa shi ruwa kan duka gefe takoma taci gaba da Adu'a Allah yasauke RAINA lafya ko badon tabata da' ba, suna shiga wani Daki akayi gwaje gwaje amma sai Likita ya kada kai yace
“Ranka ya Dade jinin matarka baya bukatsn wani jini sai irin nata kuma irin nata yana wahala” Danish yace “then Likita mai kake nufi? Kana nufin cewa jijina bazaiyi wa RAINA ba Nifa jininta ne kuma Dan uwa sosai”
“It doesn't mata my man blood group dinku ba daya bane koda uwa daya uba daya kuke” “yakamata Asama Wanda zaa samu jini irin nata koh aje bank asiyo Wanda zai mata” Danish yayi tsalle yace shifa Allan baran bai yarda ba waya yaciro yasanar ma gida Sarki MAMUDA da Sarauniya Maimuna suka hallara raina dai ana cikin tiyata room anacin kwakwa.
[5/6, 8:08 PM] Melody🎤🎤: *206-210* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻


©
_*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_



_*WANNAN PAGE DIN NAKUNE k'awayena abokan Arzuk'a, Abeeda Tautah, Mardia mossa Allah ya raba lafya, Zee Maman Suhailah, Hababi Aliyu T\W, Hauwa Salisu, Samrah, Hussnat, Maryam RUKOJI, Farida, RABI GOMBE, KHADIJA LAWAL ALIYU, Sannan tukwici ne ga MELODY NOVELS GROUP Allah yabar kauna LYSM❤😘*_











*BABI NA ARBA'IN DA BIYU*



Suna isowa aka shiga dasu ciki abun Allah babu Wanda jininsu yazo daya Likita yace toh mezai hana baza'a kira waccan matar dake wajeba koh jininsu yana iya zuwa daya ai Danish yace sam baza'a sa mishi jinin Unaiza a jikin mataba saida Maimuna ta daka mishi tsawa tace “Kai meye Kakeyi lafiyar RAINA itace muke nema yanzu koh me za'ayi ayi acetomun rayuwar yata Likita akirata”ana fita aka kira Unaiza aka dibi jininta aka gwada saigashi jinin yazo Daidai dana RAINA ai baayi wata wata ba aka k'wantar da ita aka diba, tuni aka shiga inda sauran likitocin suke kanta ana Abu daya tuni aka fara fid'a Abun mamaki aka Ciro yara uku akayi gefe dasu sannan aka fara dinketa saida aka gama tsaf sannan aka fito da ita zuwa Dakin Hutu Doctor Nuraini ne yafito fuskarsa cikeda murmushi kowa ya mike ana tambayan lafya aituni yayi musu albishir da cewa ta haifa yara uku amma har zuwa yanzu nurses basu fadi me aka samuba wani kara Danish yayi yace “Doctor pls koh zamu iya shiga ciki muganta?” Likita yace
“No ba yanzu ba bata bukatar komai sai Hutu Karin ruwa ake mata dana jini bata bukatan abinchi mai nauyi harna tsawon kwana bakwai sannan dazaran anji tayi tusa toh aiki yayi kyau”.

Sannan ya wuce hajiya Maimuna koh ince sarauniya tuni tafara kira tana yadawa, tuni takoma gida aka shiryo masu hidima, RAINA dai ta haifi mata biyu namiji daya murna wajen Unaiza ba'a magana duk Wanda yaganta yasan damuwarta ta kau kallon Danish tayi tace
“Nasawa mace da namiji suna” wani kallo yayi mata yace “ke kuma asuwa fi'ili fadi inji zugwai”
Cikin jin tsoro Unaiza tace“nasawa namijin Abdul-Jabbar macen kuma Amatul-jabbar” dariya yayi yace
“Gaskiya dole inyi miki kyauta sunan mahaifina waw wonderful nasawa dayar suna MARYAM” tuni suka kutsa inda Jariran suke akayi musu huduba Raina taga gata wai donma ance babu cin abinchi mai nauyi ga dogarai tsaye da an kwashe wayannan wasu ake kawowa kuyangu kuwa hmm ba'a magana Haka aka gyrawa RAINA gida komai Sabo ba aikin kowa bane saina uwarta da danginsu, kohda aka sanarda RAINA sunan yara tayi charaf tace “Uban kuturu yayi kadan ai ba'a isaba dole asa sunan uwata” tuni tasa aka kira Danish yana zuwa tace
“Inaso asake huduba sunayen basuyimun ba a ka'ida Idan za'a sawa da suna sai an sabarda uwa inda sunan datakeso sai awani zabi suna batareda sanina ba?”
Ai batareda bara lokaci ba aka sake wata hudubar Allah yaso baa yadaba Danish yace “Gimbiya ranki yadade wani suna kikeso a chanxa?” RAINA ta damre fuska tace
“Aciremun Maryam asamun Maimunatu(QUEEN)” ran Danish yayi masifan baci amma sai yayi shiru raina ta kara da cewa
“Indai nizan tsugunna in haifi ya toh baza'a taba samum Maryam acikin zuriata ba kasani daga rana irinta yau” Danish yace “tabbas ramuwar gayya yafita gayyar zafi yanzu cin mutuncin da raina ta tsnada zatamun kenan Ashe har gobe batason Rabin Raina Wato Ummi na?”ni HUMAIRAH nace fadi ka kara da Wannan kadai dole jama'a mu koyi darasi Dan maye yaci ya mance uwar diya bazata manceba.
Kwanan raina Tara a Asibiti aka sallameta dayake babu ruwan nono Bata fara basu nono ba suna zuwa gida bayan kwana biyu Raina ta sanarda Ummin ta akan zata bawa Unaiza da daya ta Aminche tace
“Kinyi tunani Raina tabbas dole Allah yaduba lamuranki Fatana Allah yayi miki kyakkyawar masauki”Raina taji dadi tasanarda mahaifinta shima ya aminche amma da sharadi sai mijinta ya aminche don shikeda iko dasu gaba daya........
[5/10, 9:26 PM] Melody🎤🎤: *211-215* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻


©
_*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_




*BABI NA ARBA'IN DA UKU*





Saida dare ya tsala Yarima Danish yadawo gida Dayake tunda Raina ta haihu a Dakin Unaiza yake kwana har sai tayi ARBA'IN kafin ta amshi girki haka Idan tanaso ta amsa babu Wanda zai hanata, Zaune take kuyangi suna daukeda yara suna jijjigasu tashi sukayi suka basu waje Danish ya kalli Unaiza a wulakance yace
“ke malama ubanme kikeyi anan juya kawai get out” Raina tace “Kaga irin abunda banaso wai ba Allah yake badawa ba kuma inhar kana ganin ita tayiwa kanta illah meyasa nibanyiwa kaina illah ba nida nayi zaman bariki pls kabari banaso”
Danish yace
“Inhar bakibar nan wajen ba sai ranki yayi mummunan baci”Allah sarki mai karatu zaice meyasa Danish yakewa Unaiza haka? Toh kusani Danish yanason Unaiza dalilin Yin haka shine yanaso taji kuncin abunda tayiwa rayuwarta ne tayi data sani inajin a hasashen HUMAIRAH ba son Unaiza ne bayayi ba ah ah halinta ne bayaso amma yana kunshe dason matarsa kutuna Itace First LOVE dinsa a rayuwarsa kuma shiya gani yakeso.










Haka Unaiza tafita Kamar munafuka shiko yanemi guri ya zauna Saida suka gaisa Unaiza tace
“Sweet inaso muyi magana kuma akan wayannan yaranne inaso zanbawa Unaiza QUEEN saboda in rage mata radadin rashin haihuwa datake fama dashi Ummi ta aminche haka Abby”
Wani tsalle Danish yayi yace
“Toh ni ban aminche ba kuma ban lumunta ba kisani kibarta da radadin daman banaso tasamu sauki tunda haka taso da rayuwarta” Raina tace
“Saidai kayi hak'uri don koh nono ban fara basuba za'a saboda wannan dalilin don haka kafin ranar da aka tsara nayin suna za'a sama mata magani ita zata shayar da Queen kasani don Allah zanyi badon wani kato koh katuwa ba ehe dole abunda zakamun itama sai kayi mata a matsayinta namai jego kasani kota dalilin haka Allah ya dubi duminiyata pls..........”
Mamaki ne ya kashe Danish yace ikon Allah.









Anyi shagalin suna Unaiza ta karbi QUEEN hannu bibbiyu Sai kula da take samu Kamar kwai koh kuda ba'a bari ya tabata haka Raina taci gaba danata rainon abun gwanin ban shaaawa.
*********
*Bayan Wata uku*
Sarki MAMUDA yakira Raina donsu tattauna gameda zuwan dasu farid sukayi “Raina Karki boyemun kisanar dani komai inhar kin boye mana bazaki bayewa Allah ba meye Wannan batun ya kunsa me kika sani kifada gani da Mahaifiyarki ga mijinki ga waziri ga maga takadda ka kilishi zaune”
Ai kawai hawaye sukaga yana zuba a gurbin idanun Raina ta cije baki tace cikin muryan kuka“Allah yak'ara maka lafya Duk abunda suka fada gaskiya ne Amma koda duniya da abunda suke cikinta zasu hadu baxan taba bawa Farid da Uwarsa yayana ba saboda basu chanchanta basu cika iyaye ba hajiya tasallah itace silar rugujewar rayuwana ta rabani da mijina lokacin da nake tsantsar bukatansa akusa dani ai nida ita har abada bana yafiya ga Wanda ya cutar dani”kukane yaci karfinta Jakadiyya ce keta faman rarrashi tana bata baki, Sarauniya Maimuna tace acikin ranta “Tabbas Yata Raina ita kadai tasan ciwon da takeji komaye Wannan abunda yasa tace hajiya tasallah da danta basu chanchaci zama iyayeba?”.











Saida Raina ta natsa kannan Sarki MAMUDA yace ta sanar dasu mafarin maganar datayi nacewa bazata bada yaraba sannan ina yara suke?
“Tun kafin muyi aure hajiya tasallah ta nuna bata sona Amma haka danta yaji yagani yana sona, babu irin sunayen dabata kirana Tacemun Karuwa tacemun kilaki dukna jure har saida wataran tazagi Goggo, Ansa ranar aurenmu anyi aure, bayan aure aka kwace komai da mijina yake dashi ta dalilin mahaifin shi Dan gidan damuka mallaka muka dawo babu” Raina tana magana tana kuka kowa a wajen saida ya tausaya mata ciki harda mijinta dayaji Kamar ya kashe farid da uwarsa
“Daki DAYA muka samu a tundun nufawa nan muke zaune mijina sai yayi dako mukeci mukesha hakanan muke zaune babu tashin hankali sai so da mutunta juna damukeyi har makota suna kwatance damu duk talaucin farid bai daina farantamun ba sai yakici yaga naci harda abun cikina
BAYAN WATA BAKWAI.
[5/10, 9:29 PM] Melody🎤🎤: *216-220* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻


©
_*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_




*BABI NA ARBA'IN DA HUDU*


_*SECOND TO THE LAST PAGE DEDICATED TO ALL MY FANS OVER THE WORLD🙋🏻🙋🏻🙋🏻*_ LYSM😘😍







Wacce wata Ranan lahadi tazama ranar bakin ciki ranarda bazan taba mancewa da itaba Aranan naga tsantsar kiyayyar uwar miji inda ta tasa danta gaba da cewa saiya rabu dani babu irin zagin da batayimun ba ina kuka ina rokonta amma ina mutane sun taru ana ta dubi abunda ke jikina amma tace Cikin shegene haka farid yasakeni saki daya toh kutayani figa yarannan sun halatta suzama yayansu? Nikuma nacema Farid karya sake ya nemeni sannan karya sake yakirasu da yayansa kuma inhar banida hakkinsa sai Allah yasaka mun

Please Login or Register in order to submit comment