Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

[3/11, 3:41 AM] Mummy: *1-5* *RAINA*
*(The beautiful princess)*


©
*HUMAIRAH (melody)*


*Alhamdulillah rabbil alamin nagode Allah mai kowa mai komai daya bani ikon dawowa dawani taska wacce nake fatan Allah yabani ikon idar da wannan sako banyi don cin zarafi ga kowa ba koh batanci ga kowa ba Allah yasa mu amfana da juna Amin.*

_INA KAUNARKU_
*UMMU SABREENA*
*FIRDAUSI SODANGI*
*ANEESA A RIMI*
*LUBBIE MTFSR*
*AUNTY SIS*💞
*SERDEYERH*😘

_KUNA RAINA_
*ABEEDA*
*MARDIA NIJAR*
*SARAH*
*ZAINAB DUBAI*
*MISS XOXO*
*FATTY AZLAND*
*HAULERT SKT*
*MARYAM M SADI*
*FATTY NASHUKA*
*MIENERH HAMIDAN*

_JINJINA GA FAMILY AND FRIENDS_

*YARA MANYAN GOBE SADIQ & FARUK(Twins)*
*MUHAMMAD*
*AMINA MAID*
*SAIF KT*
*AHMAD MS*
*SUHAILA*
*BEAUTY BOMO*

_SANYIN IDANUNA MUSTAPHA (Abba)_

*IYAYENA DR MB SHEHU DA HJY MALAMA DIJE WADA MANZO LOVING YOU IS MY PORTION MAY ALLAH BE WITH YOU FOR EVER AN EVER AMIN.*





_Bismillahir rahmanir rahim......_



*BABI NA DAYA*

Dan sarki ne magajin sarki duk Dan bakin ciki saidai ya mutu babu wata mata cikin gidannan dazata fini rawan gaban hantsi kuda haihuwa sai dai kuji a makota badai cikin gidannan ba ehe duk me magana tafito ina dai-dai da kowacce bora,

Wata matace yar k'arama sanye da alkyabba rikeda jariri a hannu dabai wuci wata biyar zuwa shida ba matar daganinta batada kunya babu sauran mutunci a fuskarka koh imani, Gimbiya Maimuna ce tafito tafiya take cikeda SARAUTA babu Wanda zai ganta bai kara kallonta ba saboda tsabar kyau kaman zai zube.

“Maryam ke baki isa ki kirani bora ba wallahi kinyi tsururu, me akeda agola kowa acikin masarautar nan yasan cewa badan sarki bane saidai idan kin zama shawo maida Dan wani naka yau koh mutuwa sarki yafadi yayi bashi da gado kinga koh sai kisawa kanki salama da kwanciyan hankali” Duk cikin matan dake cikin gidan babu wacce ta iya tofa wani abu sai Maimuna wacce tasha SARAUTA ta koshi gabanta da bayanta.

Haka suka gama cece kucensu kowacce tashige sashenta.

Maryam ce tsaye cikin falo ga kuyanginta sun zagayeta kowacce tana tarairayanta ta koh ina

*Danish* kuwa sai tsala ihu yakeyi hankalinta yayi matukar tashi tarasa abunda yakeda buk'ata binta ce ta russuna cikin ladabi tace
“ranki yadade mai zai hana kibani rainon yarima ko kya samu ki huta”

Dariya maryam tayi.

“Gashi binta nabaki amanarsa cinsa shansa duk nabaki ragamar komai sannan na baki wancan b`angaren kizauna aciki daga ke sai yarima don naga kina jidashi takowani fanni, daga ranan danish ya koma hannun Binta saboda tsabar kaunarsa Data keyi.

Sarki *MAMUDA* ne yashiga inda danish yake yana yimishi wasa cikin dabara shiko sai dariya yakeyi, yana bangale baki Hajiya Maimuna ce tsaye tana kallonsa, tuni taji takasa controlling kanta hawaye kawai yake ambaliya a idanunta.

“Tabbas mai martaba kana bukatan ganin k'wanka aduniya saboda nasan duk wani ikoh da MULKI na maryam zai ragu saboda dole mai martaba ya raba son da yakema danish gida BIYU.


Maryam ce tazo wucewa taga Maimuna a tsaye a taga tana kaiwa da komowa dafata tayi tare da cewa.


“Allah sarki juya aci ai kashi ki kwantar da hankalinki danish yariga zuwa duniya kuma babu yadda zaki iya da ikon Allah saboda shine yarima mai jiran gado koda SARAUTA saida MULKI” wucewa tayi tunkafin Maimuna ta lalubo amsar dazata bata amma ina kafin duk wani kalami ya shiryu Maryam tayi gaba.

******

*BAYAN SHEKARA GOMA*


Ana cikin takun sak'a da maryam da Maimuna.


K'watsam ciki ya baiyana ajikin Maimuna tuni jakadiyar sarki tayi fadan sarki aguje danta sanar dashi Abun farin ciki abunda ya dad`e yana nema ruwa ajallo ido rufe,

Tana shiga fada ta zube a k'asa ta kwashi gaisuwa tace

“Ranka ya dad`e gimbiya kuma sarauniya Maimuna tana dauke da juna biyu a gwaje gwajen da akayi likita yace cikine da ita”Farincikinsa yakasa boyuwa tuni yace,

“Kibi sasa sasa ki shelanta ma kowa cewa yar sarki jikar sarki matar sarki mamuda tana daukeda juna biyu sannan duk wata bukata ta duniya jakadiya na biya miki likita nabashi kyautar mota da kujeran makka” jakadiya tace
“Godiya nake Allah yakara Nisan Kwana Allah yakara ma sarki lafya da karama takawarka lafya rijiya ba wajen wasan yara bane kafara dai”

Haka jakadiya tagama kirarinta tayi waje guda kawai takeyi,



Tayi yakaina tsawon minti goma bayi da kuyangu duk aka fito matan sarki koh an kasa kunne Duk sun baza kunnuwa jakadiya tayi kirari tayi kirari, kowa ya zak'u dajin abunda zata fada, Maryam kuwa tanajin gud'a tuni ta kasa zaune tak'asa tsaye takai gauro takai mari gabanta sai faduwa yakeyi dukda murnan saukan Al'quranin danta Danish, tuni fuskarta ta sauya zuwa akasin haka.




*_MELODY_*😍
[3/11, 3:41 AM] Mummy: *6-10 RAINA*
*(The beautiful princess)*

*_BY_*

© *HUMAIRAH (Melody)*



*BABI NA BIYU*


Jakadiya tace

“Mun samu k'aruwa acikin gidan nan gimbiya kuma sarauniya maimunatu tana daukeda juna biyu ance in shelanta Sarki yace a tayashi farinciki Ashe yanada rabon ganin k'wansa a duniya,


Ras gaban Maryam ya yanke yafad`i takasa zaune ta kasa tsaye kowa Na murna amma banda ita har bak`in ciki take nunawa a fili bata b`oyewa saboda rashin tunani,

Haka ake rainon cikin cikeda kulawa lokaci guda Maimuna tazama wata katuwa Abu abinda ba'a girka mata daga zogale, rama, lansir Dan gauda duk abunda tace haka jiki ke rawa za'ayi mata.
Safiyar lahadi ne mai martaba yashirya zuwa kilisa kamar yadda yasaba a bayan gari,

Haka kowacce tafito take yimasa adawo lafya ciki harda Maimuna Wanda ciki yafito yayi titsitsi.

Dubansa yakai gareta yana mai yalwata murmushin sa yace “Ki kulada kanki da abunda ke cikinki ki kwanta ki huta don yanzu ke yar hutu ce Indai *SARAUTA* ce kin gada,”

Charaf Maryam tace.

" *MULKI* kuma shi muka gada saidai akaimu bola”

Dariya yayi don yasan halin Maryam saboda mugun kishin datake da maimunatu saboda ita ke bimata,
Jakadiyace tace,


“Uwar gida yakamata kidinga motsa jiki kin Dan zagayawa koh zaki dinga samun kuzari”
dariya tayi tace

“toh”

Tafiya take itada kuyanginta suna zagaye suna bata labari mai sanyaya zuciya sai dariya takeyi,



Maryam dake d`aki tasa Danish ya ruga da gudu ya tokari cikin ya zube haka ya rugo tuni kuyanginta suka tareshi sukace,

“Ranka ya dad`e yarima lafya waya biyoka da gudu ”?

saboda gaskiyarsa yace,

“Mum ce tace inzo da gudu in bige miki ciki kuma Na gayamata ni inason ki haifamun kani yadda zamu dinga kilisa tare”

Tab`e baki yayi kamar zaiyi kuka.


Maimuna ta kalleshi saboda yarima Danish yashiga ranta tun ranan dayazo duniya taji sonsa ya mamaye mata ilahirin zuciya ko d`an bata haifa bane Allah kadai yasani,


“Karka damu danish kazama yaro mai gaskiya da rikon amana sannan kazama mai tausayi saboda Allah yanason mutane masu tausayi da imani,

Ji tayi kamar daga sama ance,

“Wane hud`ubar akewa d`ana?

Fisgan danish tayi tana huci karki sake koda wasa ki sake tabamun da saboda ba tsaran abunda zaki Haifa bane wayasani koh cikin bayi kika samu wani yayi miki ciki kikace Na mai martaba ne?
Maimunatu tayi dariya Wanda yake bak'anta ran Maryam

“Allah kadai yasan uwar kwaddo”

Tana gama magana tayiwa kuyanginta magana suka ci gaba da tafiya suna shewa suna dariya,

Maryam ta mace a tsaye dole tace

“In samu mafita akan wannan cikin saboda banaso tazo duniya da rai koda tazo da rai saina San yadda nayi aka fitarmun da ita daga cikin gidannan”

tana juyowa taga binta tsaye ta rike haba tace,

“Uwar dakina meyasa kike damun kanki? Maiyasa kike tada hankalinki akan waccan abun hmmm tunda ki keda Binta saina share miki hawaye duk wani makirci daya kwana ya hantse nasan shi wani darene jemage bai ganiba?”maryam tace Daren haihuwarsa.

Anata shirye shiryen saukar danish gida yayi tankam da mutane haka akayi saukar aka gama washe gari aka wuceda Danish k'asar madina inda acan zaiyi karatunsa daga sakandiri har jami'a, nan akabar Maryam da kewa hakan yakara bata daman shirya magun abunta dabazai kaita ga komai ba sai halaka



Haka suka dinga k'ullawa suna k'wancewa itada kuyangarta binta suna cikin zancenne jakadiya taji komai ta kulle a hab'ar zaninta, ranan da watan haihuwar Maimuna ya tsaya sune gaba gaba wajen zuwa clinic din cikin gidan, inda aka kira likitan bayan ta haihu ne aka samo matacciyar ya mace akasa mata tuni binta ta Goya yar ta gudu da ita koh wanketa ba'ayi ba.



Haka aka sanar da maimartaba wannan mummunan labarin amma tuni jakadiya ta karbe tace karya akeyi tuni ta kwashe komai tafadi,

Inda mai martaba yashiga cikin rud`ani don zan iya cewa harda kuka saida yayi kowa Na gidan yayi kuka tuni aka kama Maryam da dakta akayi wani akurki dasu inda a k'aidar al'ada duk Wanda aka damk'a da laifi nan ake kaishi koda mai girman muk`ami ne a masa rautan,

Rayuwa tayi musu kunci amma suka fawwalawa Allah komai.




*_MELODY_*😍
[3/13, 12:53 PM] Melody🎤🎤: *11-15 RAINA*
*(The beautiful princess)*


*_BY_*


© *HUMAIRAH (Melody)*



*BABI NA UKU*



Tun tafiyar Binta basu sake sata a idoba bare labarinta, haka Kullun iyayenta suke kukan rashinta mahaifiyar Danish kuwa tashiga tsaka mai wuya axabar yau daban nagobe daban, tundaga haihuwar Raina baa sake wata haihuwa ba, daman tun kafin tazo duniya yasa mata suna RAINA wato beautiful princess _( Kyakkyawar Gimbiya)_
kuma hakan take......

******
*Tushen labarin*
Wai sai yaushe zakiyi hankaline ne ke Kullun saina miki magana kan ki daina shigowa gida kina ihu kin mata cewa ke macece namiji aka Sani da karaji ba mace ba maza kiyi yadda nace farayi ingani, Abu gwanin ban dariya duk Wanda yaga yarinyar da ake koyawa bariki saiya rik'e baki saboda tabar mamaki yarinyace yar kimanin shekara goma da ko irgan dangi bata faraba illah iyaka Dan jiki datakeda shi,


“Raina kalleni haka zakiyi da ido duk Wanda yakiraki sai kinyi yauki kannan zaki bashi cikin yanga” haka inna yalwa tadinga koyawa RAINA abubuwa daban daban dabarun bariki iri iri daga bisani ta daura mata mashe Wato wainar gero zuwa tashan garin Wato zangon Mati, inda ake cinchirindo wajen kawo abun soyarwa, haka fuskar Raina taji mai sai sheki take ga wani digi digo datayi kamar wata aljana, tana tafe tana yanga harta isa runfarsu da zuwanta yara suka dinga kwashe kayansu, suna ya mutsa fuska suna cewa ke mutashi kinsan halin wannan shegiyar dabatada uba, wata tace wayasani ba koh yar tsintuwa ce? Oho sukayi tafi sukayi shewa.

RAINA batako tankasu ba ta kallesu ta watsar tace

“Banda abunku *MULKI* baya Koran *SARAUTA* yara saidai saurauta ta kori *MULKI* saboda ita mulki wa'adi gareta *SARAUTA* kuwa saidai tayita zagaye mtwwww” taja tsaki taci gaba da saida mashenta kan kace me RAINA ta siyar duka bokitin ta dauka ta juya ta kallesu tace

“Shegiya ta siyar tabar masu uba da dangi” tafe take tana taunar cingam Wanda ya Dade tana ci salon ya fafe mata ciki, bakin shagon Kb ta faka ta siya gero Na wainar gobe sannan ta wuce gida tana shiga ta ajiye bokitin ta mikawa inna yalwa kudin tace “Inna waini meyasa yara suke cemun shegiya Mara uba? Nidai inna waye ubana?” tafadi tareda buga kafa, taba zunbura baki uwa durin jaka, Inna tace

“Tabbas ke kaskan tacciyace Mara usuli shiyasa suke cemiki haka ina ruwanki dasu kifita harkarsu kiyi rayuwarki ke kadai koh tare dasu kukazo duniya?”.


RAINA tace
“Ah ah”


Haka suka ci gaba da rayuwa cikin talauci da kaskanci inna yalwa tazama kamar karya itace fada da wannan fada da waccan kima Duk akan RAINA akeyi, saboda iyayen yara sunce basuso RAINA tana shiga cikinsu karta bata musu tarbiyan yara,

Indo ce kawai take kula RAINA saboda jinisu yayi masifan haduwa da juna.


Raina dai bata zuwa makarantar boko bare islamiyya zagon Mati babu makarantar arabi bare ta boko tsantsar jahilci ke dawainiya dasu yaron mai garine kawai yaje birni karatu wayo FU'AD.


Tunda sanyin safiya inna yashiga ta watsawa raina ruwan tsanyi a gigice ta mike

“Ubanwa ya baki Hutu maxa ki mik`e kikai nik'a”

Jitayi gabanta yayi mugun faduwa tace
“Inna wallahi banason kai nik'a matan gidan kyarata sukeyi,"

"Sucemun Mara usuli abunda yake batamun rai kenan haka zakiga yara sunata kallona suna yamutsa fuska wai inna meyasa bazasu gane cewa ba laifina bane?
Kaddara ce tafada mam”kuka ta barke dashi inna yalwa koh kallo bata isheta ba tace “Yida jiki kije ki dawo kar gari ya gama wayewa”


Haka takai nik'an ta dawo ranta babu dadi, inna yalwa Kullun batada wani buri sai Na RAINA ta kawo mata kudi tako wani hanya shiyasa take koya mata duk wata baraka, tuni Raina ta baci dason kudi idan taga kudi jikinta har b'ari yakeyi.


Yauma kamar Kullun ta dauki talla da barkakken zani silipas din Duk ya sud'e, RAINA babu zancen sallah bare salati saboda bata iyaba tafe take cikin layi tazo wucewa ta k`ofar gidan mai gari tun daga nesa Musalle yake tab`a abokinsa


“Kalli RAINA yar gidan inna yalwa mai waina inason yin harka da ita saboda nasan zatayi maik'o” lashe baki yayi itakoh sai wani rangwada takeyi kamar wata tsohuwar kilaki, tana isowa wajensu tace “Zaku siya?” da sauri musalle yace eh zan siya haka ta sauke tana wani juya idanu wanda gaba dayansu saida sukaji wani tsar.


Sun dauki waina ta murtala suka siya sukace tajeta dawo tabiya ta shago, tana siyarwa ta wuce sai shagon musalle ta tsaya ta rik'e k'ugu “Ah ah raina yan mata har an dawo shigo ki amsa kudin”



Haka ta shoge tace itadai ya miko mata haka yadinga janta harta shiga ta zauna irgan kudi yakeyi sulalla tuni ta zauna don tana ganin yau zatayi chamama haka yace ta tayashi irga kudin tanayi tana sokewa a haban zani, duk yana kallonta tana gamawa yace “nawane?”

Raina tayi far da ido tace “Na murtala biyarne” batasan yarigada ya irga murtala shida da goma bane ta zari talatin,


Musalle bai damuba saboda yanaso yaga yayi nasara cewa yayi
“Raina yan mata dauki kudin duka nabaki” ba musu babu Jan aji ta karbe yadauko murtala kudin waina yabata shima ta karbe

“Musalle kenan haka kakeda kudi?”



“Hmm Raina kenan inda zakizo shagona da dare kinga wayannan kudin wallahi duka zambaki” tuni ta zare ido tafita sai gida sallaman datayi ne yajawo inna ta waigo
“har an siyar haka nakeso maza shiga ciki biskin ki nanan kidauka, RAINA tace toh tana fadawa ta zuba kud`in cikin baki






*_MELODY_* 😍
[3/13, 12:53 PM] Melody🎤🎤: *16-20 RAINA*
*(The beautiful princess)*


*_BY_*


© *HUMAIRAH (Melody)*



*BABI NA HUDU*



Tadawo tanemi guri taci biskin ta,

“Goggo wallahi Laure zatayi aure kuma kinga zanyi anko Dan Allah kiyimun kinsan cewa duk cikin karkaran nan bayarda takesona sai Laure idan banyiba bazataji dadi ba kwata kwata”

“Ke dalla rufemun baki ba anko ba ankoko kina ganin zan iya baki biyar cikin kudinnan? Toh koh sile inzaki tashi ki nema ki nema kinada abun bayarwa sisi bazan miki koh chokali ba idan kika tashi aure”

Baki sake RAINA ke kallon Goggo yadda take magana kamar ba ita ta kawota duniya ba, misalin karfe bakwai saurane Raina ta tuga batareda Goggo ta saniba tuni ta mik'a layi sai wajen musalle, tana zuwa tundaga nesa taganshi tareda wansa Wato Fu'ad suna Alwala haka ta k'arasa jiki ba gwari,
“Musalle wajenka”

Kamar daga sama yaji maganarta cikin rudewa da rashin gaskiya tashi yayi yaje kusa da ita ya tsaya tace,

“Musalle nazo ne akan maganan dazu inacikin matsala zan iyayi maka komai donka bani kudin dakace idan nazo, Kaine kaidai zaka iyayimun maganin lalurata”.

Musalle duk ya muzanta agaban wansa Fu'ad duk yaji ya tsani kansa,

“Amma ke wace irin macece Mara aji mak'aryaciya Kawai ni an gayamiki irin sauran mazane yan iska masu laguda yayan mutane banda kin rainani yaushe nace kizo”

Mtswwww yaja tsaki cikeda borin kunya,

“Haba musalle yaza kayimun haka bacin kaida kanka kace inzo Dan Allah shine zaka cimun mutunci?”

“Ina kikaga mutunci inda kinada mutunci kamarni Dan Dan mai gari zakizo kinamun wannan maganar salon bata suna”

Ji yayi an dafashi tuni yasan ko waye Fu'ad kuwa ya tsare Raina da ido a rayuwarsa yana masifar sonta sona hakika amma gaba daya kwarjini takemai,


“Musalle sai yaushe zaka daina fasikanci da yayan mutane koh kamanta Zina bashi ce wataran saika biya, musalle zaiyi magana ya katseshi dacewa Mazinace baya arziki koyayi saiya talauce kuma mazinaci mak'aryacine duk amintarsa da mutane saiya haincesu, Sannan Allah yana fushi damaiyinta, duk abunda Raina tafadi na cewa tazo kafadi dabaka fadiba babu yadda za'ayi karamar yarinya kamar ta tazo wajenka” musalle tuni yanade tabarmar kunya da bori ya K'ara gaba.


“Ke kuma akanme kika zabi saida mutuncinki darjarki da kimanki akan kudi kudinda bazasu yimiki wani amfani ba, Zina musibace Raina kuma duk Wanda ke Zina baya tareda Allah kuma tabbas yacika Mara imani” Raina taji duk ta tsani kanta duk Goggo ne taja mata sai cije cije takeyi tana kwarkwasa takasa cewa uffan.


“Raina duk abunda kikeso zanyi miki koya yawansa yake namiki Alkawari fatana shine ki kama kanki abunda kika dashi kenan dazai sai miki mutunci a gidan mijinki kenan,

Yanzu meye matsalarki? Kin gayamun in miki maganinta yanzu Duk a zangon Mati banga yar da nakeso ba saike wallahi inada burin ki kasance masoyita abokiyar rayuwata ke bake jira raina”

Far tayi da ido saboda tsananin dad`i ance ana sonta

“Daman ankon Laure nakeso nayi kuma bansan yadda zanyiba abincima ya kyar mukeci bare anko kuma kawatace sosai idan banyiba zataji haushi na tace bata kwawancen dani”
“Raina yan mata muje toh in rakaki har gida koh suna tafe tana wasada kara ta tsinta wannan ta tsinta wannan tanata tsalle tsalle abunka da yarinta, har kofar soron gidansu sukazo ya dauki jaka biyar yabata yace tayi amfani dashi kuma duk in tanada bukatan Abu tayi mishi magana zaiyi mata haka ta shige gida tana dagamai hannu shigarta keda wuya taga Goggo labe a zaure tace,

“Zonan dan ubanki nawa yabaki kawosu nan”

Haka ta fizgi d`ari biyu raina tace

“Aiko kin dauki rabonki kuma mekikeyi a labe anan wallahi Goggo kezaki siyamun mutunci a garinnan amma Kullun kekike watsani shiyasa mutane sukemun cin kashi keda kika haifeni baki tarairayeni ba kin soni sai mutan gari ni inada shakkun cewa bakece uwata ba saboda duk wata uwa tanason danta harta jashi ajiki”

Kwab kakeji Goggo ta bige mata baki harsaida yayi jini


“Kajimun yar iskan yarinya Dan ubanki saboda sanadiyyan haihuwanki kika koranmun kostamomi kika hanani rawan gaban hantsi, kuma har jigila nake dake kar inji kar ingani wallahi.


Kuka raina takeyi maicin rai tarasa abunda yake mata dadi amma babu yadda ta iya saidai ta rungumi kaddara.


Haka Gwaggo yalwa taci gaba da yiwa Raina hud'ubar shaid`an tanata sata hanyar halaka nan Goggo taje wajen Malam ALU ta ansoma Raina maganin farin jini Dana Wanda samari zasu bata kudi, haka ya had`a mata yace jaka zata bada tace,

“wooooo jaka fa kace toh zan aiko raina”

A cikin ranta cewa take ai saidai tabada kudin don sisi bazan kashe mata ba.





*_MELODY_* 😍
[3/17, 7:41 AM] Melody🎤🎤: *16-20 RAINA*
*(The beautiful princess)*

*_BY_*

© *HUMAIRAH (Melody)*



*BABI NA BIYAR*


Haka ta tafi gida tana isa bata tadda Raina a gidaba, tadinga kwala mata kira amma shuru tana dasa mazaunenta RAINA tashigo aguje tana haki,

Goggo Ta dubeta tace,

“Ke lafiya kika fadoma mutane gida babu koh sallama kuma a guje, na hanaki wannan abun amma kinki kiji sai kiyitayi Sai kace wata namiji ina gayamiki mace rangwada takeyi ba guduba” bata gama rufe bakiba taji ana doka sallama ai tuni RAINA ta haure takan Goggo tayi dakinsu mai shegen duhu ta boye cikin tsumma cikeda kudin cizo,

Goggo tace

“Lafiya kike gudu haka ubanwaye ta biyoki? Mutumin dake waje yace

“Leko ki gani dakeda wannan shegiyar yar taki sai nayi karanku matukar bata fita harkan yayana ba”


“Daman Kaine ka biyomun ya toh bari kaji yadda kake tutiya da cewa yayankane haka itama yace, don haka kakai kara kotun koli muzuba nidakai shege kafasa, wallahi bakasan tsiyaba zan nuna maka idan baka bar kofar gidannan ba sainayima sharrin da Allah kadai zai iyama amma ba mutum ba” Sanin halinta yasa shi barin kofar gidan don yalwa makirar macece wacce nasan shedan dakansa yana tsoronta,

Ciki tashiga ta kama RAINA tayi mata d`an banzan duka

“Narabaki da shiga tsabgarsu amma kinki kiji ke kika sani banza Mara Yanci Mara gata Mara galihu shegiya bakar banza, maxa kidauko jaka daya cikin kudinnan kikaiwa Malam ALU” Hararan ta tayi tace


“Hmmm Goggo kenan kudinnan babusu nasai anko nabada dinki saidai kisan yadda zakiyi wallahi don ni ban aikeki wajen ALU ba keda kikaje aike zaki biya kudi”


“Iyeeh haka kikace kinji shegiyar yarinya Dan ubanki bazan biyaba”
“Goggo

Please Login or Register in order to submit comment