Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Maimuna, wani wawan Mari tayiwa kuyangar tace
“Ke wacece dahar zakice bazanga uwata ba? Ke kin isa toh kisani wannance rana ta farko kuma na k'arshe inada daman shiga koh ina bangajeta tayi tashiga ta taradda ita zaune ana mata fifita durkusawa tayi tagaidata cikin ladabi sannan tayi shuru nadan lokaci, Sarauniya Maimuna tace


_*KUYI HKR WAJEN NUMBER JIYA NAYI MISTAKE PLEASE 121-125 zansa nasa 121-126 bear with me*_.
[4/20, 6:46 AM] Melody🎤🎤: *131-135* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻


©
_*STORY & WRITTEN BYHUMAIRAH (Melody)*_




BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI











“Kiyi Hakuri Raina nasan kina cikin rudani nasan kina cikin matsanancin damuwa na Rashin Adalci dana nuna miki tun zuwanki cikin gidannan nayi hakanne saboda wani kunci dake dawainiya Dani, amma naji matukar dadi dakika zo inda nake hakan yanuna cewa kemai kaunar uwar data kawoki duniya, dakwai wata magana mai matukar muhimmanci Wanda nakeso inyi dake Ansa ranan aurenki nanda sati biyu keda dan'uwanki DANISH amma kisani yanada mata mai Suna Unaiza tana zaune acikin garin Kaduna ne” Ras RAINA taji gabanta yayi mummunan faduwa taji duniya ta tsani Danish Wanda shima take ganin alaman ya tsaneta budar bakinta tace
“Ummi A gaskiya banida raayin yin wani aure saboda nayi banji da dadi ba sannan Danish bayasona saboda babu wata magana data taba hadani dashi koda cikin Garden na shiga saiya watsamun kallon tsana yabar wajen Dan'uwanka mai sonka kuwa Janka zaiyi a jiki ganin yafaranta maka rai amma duk abunda kuka yanke a shrye nake da inyi muku biyayya a matsayin iyayena” Maimuna taji dadi tabbas da ace RAINA a gabana ta tashi nasan data zama abun kwatance saboda daga dukkan alamu tanada ladabi da biyayya.

Nan sukayita hira amma koda wasa RAINA bata taba fadin tanada yara har biyu ba rayuwa ta sauya RAINA taxama yar gari takan fita domin shakatawa tana samun kulawa daga mahaifinta sosai haka mahaifiyarta, kwatsam hanya tabiyo da ita ta wani labi dake cikin gidan kawai batayi auneba taci karo da mutum dagowan daxatayi taji an dauketa da mari, Agigice ta dago ganin Danish ne itama ta daukeshi da gigitaccen Mari Wanda saida taga taurari sannan RAINA tace
“Kul agolan gida kabi a sannu don karkaga kanka na rawa kayi tsammanin kafi yar masu gida iko da mallaka kul Dan mulki wannan yar saurautace a gabanka, Uwata yar sarki jikan sarkice kuma matar sarki uwar Gimbiya RAINA Idan ka mance in tuna maka yau shine rana na karshe dazaka sa wayannan doyan hannun naka ka mareni Ina umurtanka daka bani hanya kafin inbaka kunya” tsayawa yayi ya rike kunci yana mamaki RAINA yar karamar yarinyar dayaba shekara goma bangajeshi tayi ta wuce tana wasa dayan yatsunta, bangarenta ta wuce tafada kan royal bed dinta ta fada kogin tunani
“Dole inyi biyayyar aure Idan harna Auri Danish tabbas gwarzon namiji ne maijida kansa kyakkyawa ne ajin karshe ohhhh toh niwai meyasa Abbi ya zabamun Danish a matsayin miji da gudarin tunani ne bacci yayi awon gaba da ita, misalin karfe hudu ta farka Sallah kawai tayi akayi sallama cewa malaminta yazo mai koya mata duk wasu hukunce2 musulunci lokaci guda ta rikesu Kullun cikin istigfari take tana Neman gafaran ubangiji haka take sanarda Malam kan maganar aurenta.

Haka yayi mata Karin bayani akan Zaman *Istibra'i* da mace takeyi tsawon wata uku matukar tayi yawon bariki koh tayi zaman kanta sannan tana holewa da wasu maxan don haka yabata babban Sha'awaran a k'ara watannin aurenta zuwa wata uku da komai zai kammala, haka akayi bata zuwa koh ina daga gida sai gida babu wani namiji dayake zuwa inda take sai Azumi takeyi sallar dare kuwa kamar akanta aka saukar da Aya Abun gwanin ban shaawa kowa yayi mamakin Gimbiya RAINA yadda lokaci guda ta canza saidai batason raini koh nuna isa, Dayawa cikin family dinsu tsoronta akeji, Tuni aka fara nemawa RAINA gurbin karatu Wanda ake cewa yaki da jahilci Raina gata babu irin wacce bata samuba a halinda take yanzu.
*************
BAYAN WATA UKU
Komai ya daidaita Anfara shirin biki Gidajen radiyo babu inda ba'a shelanta ba, Zainab kuwa jin mijin ta zai kara aure kaman zatayi hauka saboda tsabar Rainin wayo irinna Danish bai sanar da itaba yace taji a gidan rediyo, Shida abokinsa ne mai suna Shureim ne suka zauna cikin wani folo dake kirada Tarazo suka aika ayi musu iso da RAINA batayi mamakiba haka ta tambaya waye akace da ita yarima Danish ne, saida tayi wanka tashirya cikin wata bakar doguwar Riga tayi mafla da gyale Green, tasa takalmi Shika Green tafito tareda rakiyar kuyanginta tana isa falon tace sukoma ciki ta kutsa kai Shureim ne kadai ya iya amsa sallamar RAINA harya kalleta shiko Danish wani garwashin tsanane ya turnukeshi babu abunda yake tunawa sai Marin data taba yimai........
[4/21, 6:38 AM] Melody🎤🎤: *136-140* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻


©
_*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_




BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS



_*Zakuyimun hakuri don baxaku jini ba kwana biyu saboda makaranta Allah yasa ku fahimceni LYSM my FANS*_😘







*DIX Page goes to my co-writer BADI'AT IBRAHIM kina kamshi inabinki da Humrah Allah yasa kifi haka yak'ara daukaka da laifin baseerah LOVE YOU SWEETHEART❤*











Sannan ganinta yake a matsayin karuwa har yanzu acikin zuciyansa guri ta nema ta zauna fuskarta babu yabo babu fallasa illah wani murmushi datake Wanda nikaina nakasa dangantashi dana farinciki koh akasin haka gaishesu tayi Shureim ne ya amsa da
“Amarya bakya lefi ta yarima bada kanki asare Idan bashiba sai rijiya rijiyarma mai kwalabe”
Tuni Danish ya zugureshi alamun bayaso Shureim yaci gaba da magana
“Amarya Mai sunan yan gayu daman munzo ne gameda hidiman biki kidakwai abunda kikeda buk'ata koh kuma wani shagali da kikeso ayi a ranan bikin” RAINA ta kare mishi kallo tace “Amatsayinka na aboki kuma Wanda yasan yakamata nabaka dama kaje ku yanke duk shaawarar data dace don as you guys can see am in a heast don haka left to you”Kafin ta tashi Danish ya tashi yaja uban tsaki ya fice saura kiris yataka mata Dan yatsa, Tashi tayi zata fita Shureim yabita yana bata hakuri dacewa saitayi hakuri da abokinsa budar bakin raina tace
“Shureim kenan yadda danish yake ikirarin bayason aurena dashi haka nima banaso biyayya kadai zanyiwa iyayena sako nabaka zuwa gareshi don kansa yadaina daukan huci koh ince zafi koh kuma rawa” haka ta fice tabar Shureim Wanda yake ganin tabbas RAINA macece mai klas k'warai gata da wani boyayyan kyau dake kwarara tayaya zanyi nasaran ganarda Danish cewa wannan itace zata share mishi hawayen dake zuba tsawon shekara biyar da aurensa, da wannan yafice anata shirin biki amma RAINA batako daukin bikin illah tunanin rayuwar aurenta da FARID Wanda yakasa gushe mata daga kwakwalwa..

RAINA ce zaune gaban mahaifinta Wanda yake tambayarta nawa take so kudin sadakinta? Haka tasanar dashi naira dubu Ashirin kacal ya isa Albarkan akeso sannan ita tasan a yadda rayuwarta take bata wuce hakan ba, Sarki MAMUDA ne yabada umurnin ashiga cikin garin Kaduna adawoda Unaiza cikin gidan saurauta matukar tanason aurenta ya daure da Danish wannan labarin daya isketa tayi masifar razana bin jakadiya kawai take da kallo tace
“Kina nufin DANISH aure zai k'ara kuma maimartaba ya Umurci da in koma masarautar kajuru?” jakadiya tace
“Kwarai ranki yadade umurni ne daga mai girma sarki MAMUDA Allah yakara mishi Nisan kwana kuma yar Sarki MAMUDA zai aura RAINA kyakkyawar Gimbiya”tsawa Unaiza ta dakawa jakadiya tace
“Nisan kwanan sarki kuya dama mijina kawai nake tunani RAINA koda itace sarauniyan kyau wannan ba matsalata bane don nasan saidai kyau na SARAUTA amma bana MULKI ba kubaiwa Maimartaba hakuri nanda kwana uku ashirye nake da'in koma kajuru
Kufita banda bukatar ganin ku sai nanda kwana UKU” Ai jiki na rawa suka fice koh waige haka suka koma sarki ya Aminche Unaiza Kullun cikin kiran danish take abunda bata tabayiba tsawon lokacin dasuka diba na zaman aure, shiko koh kallo wayar bata isheshiba sometimes har kashe wayar yakeyi.
★★★★
*WACECE UNAIZA?*
Unaiza dai yar Ambassador MB shehu ce Wanda yayi suna a fagen kulada yan Nigeria dake a kasar Amurka Susu uku iyayensu suka haifa kuma itace ta karshe Wato Auta duk wani iya shege akanta yak'are kuma duk abunda tayi a wajen iyayenta daidai ne, yadda uwarsu ta maida ubansu mijin tace haka suma suka maida mazajensu, Danish dai a wajen biki suka hadu inda yaji duniya Unaiza yakeso har ta kaisu ga aure Unaiza batada lokacin danish bare harta yimishi abinchi kafin a kaiga wajen k'wanciyansu nanma saiya sha daga sometimes har kudi yake ajiyemata kannan ta aminche mishi babu kwayar biyayya takan fita lokacin data so tadawo lokacin dataso haka ta Tara K'awayenta suyi bishasha yadda sukeso bashida ikon magana tace tafishi baki, harta wanki shara da wanke wanke shiyakeyi, har abokanansa suka daina zuwa gidansa saboda haushinsa kawai sukaji yadda mace ta rainashi kuma duk a sunan shike aurenta koh kusa dashi Unaiza bata zuwa data samu ciki saitasha pills ta zubar dashi kwata kwata babu biyayyan aure Wannan kenan.
[4/22, 7:21 PM] Melody🎤🎤: *141-145* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻


©
_*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_





_*Wannan page din nakine MARIYA AHMAD ILIYASU Son da nake miki is different ngd da karamcinki gareni @Anatare 😍😍 lets keep chillingGulx💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻*_





BABI NA ASHIRIN DA TARA





Akwana a tashi wajen mai rai RAINA babu abunda take zullumi sai gamuwarta da DANISH Wanda k'wata k'wata bayasonta haka ranar daurin aure ya rage saura kwana uku, UNAIZA ta dawo cikin gidan sarautan wajenta dabanne nesa da inda RAINA zata zauna, Unaiza ce tsaye a bakin taga inda take hangen masu kaiwa da komowa hankalinta yayi kololuwar tashi
“Yanzu nice zaayiwa kishiya? Tab lallai daman hakan nuwaira taji lokacin da AB zai kara aure?” Jitake kaman zata hadiyi rai ta mutu saboda tsabar son danish datakeyi sai yanzu tasan cewa miji mijine wacce ta raba miji da wata tayi gagarumin sake.

Wata sain ba sake bane kaddara ne kuma rubutaccen Al'amarine ana gobe daurin aure Unaiza ta fita mike k'afa ga gida ya cika dankam da mutane bata zarce koh inaba sai hanyar dazai sadata da bangaren RAINA tafe suke itada Kuyanginta da'aka bata don yimata hidima suna isa k'ofar RAINA tayiwa kuyanginta umurni dasu jirata koh sallama babu ta banka kofa, Raina tana sama itada zeenert k'awarta tafitowa tayi da sauri lokacin duk kuyanginta basa kusa, daga saman bene tace
“Wace yar akuyarce Mara tarbiya bare dabi'a take shigomun falo ba sallama? Koh bataje islamiyya bane?”
Unaiza data kulu tace
“Kul yar tasha ragowar bariki Karki kuskura ki zageni har kinada bakin zagin wani mara tarbiyya gaki BABBAR Mara tarbiya wacce rayuwarta ta kare a bariki inaso kisani igiyar rak'umi tayi nesa dana kaza kiyi gaggawan rabuwa da mijina kafin a haifi da Mara ido”.

Raina ce tafe zata sakko zeenert kuwa tana sama tana kallon abun al'ajabi,
saida RAINA ta zagayeta sannan tayi guda tace
“koh ba'a mijiba danish dan'uwana ne kuma inada right din aurensa tunda ba nono daya mukasha ba sannan Kuma ba uwa daya uba daya mukeba bare kice ba aure, kisani saikinyi kishi da Raina kafin in irga uku kiyi gaggawan fita inba hakaba kiji kunya ” Unaiza shuru tayi don abun yasha karfinta kishi da Baban miji Fita tayi a fusace cikin sauri kuyanginta ke biyeda ita tana shiga daki ta fada kan gado zufa kawai takeyi abun duniya ya isheta Kuyangarta ta aika aje a nemo mata Danish ace tanason ganinsa amma Ina abun yaci tura yana cikin garin Kaduna gidan Ab abokinsa, Unaiza tak'asa rintswa takai gwaro takai mari har misalin shadaya nadare lokacin dataji gunjin motar Danish bata tsaya bata lokaciba tafita da gudu tayi inda yake fadawa jikinsa tayi lokaci daya ya hankadata batareda yasan itabace yace
“RAINA ina kyautata zaton kinyi kuskure wajen zuwa ki rungumeni dis is the First and the last kisani banza kawai kina tunanin zan iya hada jiki dake toh kisani *Auren jeka nayika zamuyi* ba auren Darai yake muradi ba”.

Yana gama magana Unaiza tace “Baby ba RAINA bace nice matarka Unaiza kayimun rai kazo gareni ka ceceni don duniya ina cikin duniyar ladama nayi dana Sanin yimaka wasu abubuwa a baya pls forgive me i dont mean to hurt your feelings any more Darling” wani gigitaccen tsawa yayimata Wanda saida taji kaman zata gudu Yace
“Unaixa kinyi kuskuren zuwa inuwata bari Kiga yadda ake ganar da mutum irinki kuskurensa, kin manta cewa kinyi rantsuwa bazaki sake zuwa inda nakaba?” ai rufe baki tayi tana gunjin kuka
Ai batayi auneba saijin belt tayi tako ina sai hambareta yakeyi babu imani koh tausayi saboda Unaiza ta cutardashi ta inda mai karatu baya zato, Danish yana masifan son Unaiza lokacin da yakamata tayi amfani da damarta lokacin ta watsar saboda sonshi yafi nata tasiri, Akan Unaiza bata biya masa hakkinsa yafada ga aikata zina duk lokacin daya buk'aci mace saidai yaje waje tur da halin Unaiza wacce sanadinta mijinta yashiga halaka mata muyi imani mu kare hakkokin mazajenku.
[4/24, 6:40 AM] Melody🎤🎤: *146-150* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻


©
_*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_





BABI NA TALATIN


_*Wannan page nakune yan group dina Wato Melody novel group Allah ysbar zumunchi yabar kauna LYSM😘😍*_



Ai da gudu ta wuce cikin gida tana kuka washe gari Aka daura auren DANISH DA RAINA a babban masallacin dake kofar gidan Sarki MAMUDA inda manyan Mutane suka halatta daurin auren ciki harda sarki KAMAL Wanda shima sarkine Wanda ake jidasu a fadin Nigeria, Gida sai hidima akeyi Sarauniya Maimuna kuwa bakinta har baka gida yacika da jinin sarauta takoh ina harma jinin mulki ni humairah saida nagani abun masha Allah Amarya da Ango sunyi kyau Unaiza saboda bak'in ciki kamar zatayi kashi ajiki babu kowa a bangarenta saboda kowa ganin laifinta yakeyi dabata hana danish aure ba tafita zakka cikin yayan gidan Ambassador MB shehu, Misalin karfe uku ne aka wuceda Amarya nata sashen a al'adarsu mace bata Sallar La'asar a gidan iyayenta sai a gidan miji Nidai saboda tsabar son ganin Dakin amarya mai karatu saida naci tuntube, A gaskiya RAINA tazama ya mai gata mai yanci duniyace tayi mata kamun kaxan kuku lokacin datake matukar buk'atan iyayenta a kusa da ita babune babu acikin bangarenta yaji kaysn kwaliya na zamani wani bangaren na yar saurauta kirari kawai ake mata
*Yar Sarki jikar sarki yar sarauniya Maimuna takawarki lafya Allah yakara ma Yarima Danish lafiya Allah ya tsole idon makiya mahassadanki fadawanki kyakkyawar Gimbiya tun kan zuwanki duniya akasa miki suna kikazo duniya sunan yabiki Duniya Mai yadda yaso da bawa ke macece mai kamar maxa masu irin imaninki sai an tona Allah yasa muji albishir mai dadi Uwar yan biyu in Allah ya yarda*
Tunda Jakadiya tace yan biyu raina taji wani mugun faduwan gaba yaranta kawai ta tuna amma tasan yanzu sun zama na wasu bata burin karbarsu Amma tanajin irin sonda take musu har kokon zuciyarta kuka kawai tasaki Wanda babu Wanda yasan dalili.

Bayan an shiga da itane aka gama yan Al'adarsu ta masarautan kajuru, daga bisani akabarta daga ita sai jakadiyarta sai kuyangu tunda dole tasamu jakadiya saboda tazama matar aure al'adarsu, Zaune take bisa katon gado Wanda yasha ado Royal bed ne Wanda kansa ya kusa rabi da k'watan bango sai fifita ake mata misalin karfe Goman dare lokacin da Danish yadawo abun mamaki tana zaton inda take zaizo amma saitaga Akasin haka Jakadiyace tashigo hannunta rikeda wasu kayan bacci masu kyau da tsada
“Gimbiya kitashi kisa wayannan kayan muje in rakaki wajen Mai girma yarima” cikeda mamaki baki bude raina tace
“Jakadiyya kinada hankali kuwa? Mutum yana sonka yaka k'are dashi bare kuma bayasonka kakai kanka? Nifa bazansaba inace miji kebin mace har dakinta?” ta zunburo baki ta mike ta nade hannu tana kai gwaro takai mari, jakadiya ce a durkushe tafara magana cikin siga mai kashe jiki Nanta labartawa RAINA irin rayuwar Auren
“Gimbiyata mai zai hana mu gwada tamu baseerar saboda gani yake matan duk saya suke kije Gimbiya ta kidaure har hakarmu ta cimma ruwa” haka raina ta shirya cikin kayan ta sanya Alkyabba suka kama hanya jakadiya daga kofa ta koma RAINA kuwa gabanta sai dukan goma goma yake, tayi minti biyu a tsaye kannan ta zauna a gefen gado da alaman mutum a cikin Dakin cire Alkyabba tayi ta kwanta ta juyawa toilet din Dakin baya tasan duk yadda akayi wanka yakeyi.

Tanajin motsi tayi saurin rufe ido DANISH daya fito saura kadan ya arta a guje saboda bai taba ganin mace mai kira irinta RAINA ba, lokaci guda ya gusar da tunanin hakan a ransa yana Neman tsari da shaidan din sake Neman yin tasiri acikin Ransa Juyowa RAINA tayi tace “Barka da fitowa ranka ya Dade yayana yarima mai jiran gado Allah yabaka sarki ka nadani Sarauniyar masarautanka” tafadi tana murmushi ta sakko mai yake shafawa tayi saurin amsa cikeda kissa zata shafa masa tunda wani darene jemage bai ganiba dakatar da ita yayi yace
“Malam bansakiba banason Shishigi maxa ki tashi daga gabana kafin inyi ball dake ” RAINA tayi saurin dagowa takasa cewa komai ba laifin Wanda take gani sai nata dana jakadiyya bakin gado takoma sai satar kallonta yakeyi
Barcine tayi awon gaba da ita shiko sai daukanta hoto yakeyi yadda tayi masifan kyau cikin silk milk din kayan baccin amma fah yarasa meyasashi daukan hotonta *Koh me karatu yasani?*misalin karfe biyu da rabi raina ta tashi DANISH dai motsi yaji Alwala tayi ta shimfida sallaya ta dubi gabas tafara kiyamun lai Shiko Yarima Danish kallonta kawai yakeyi wai daman RAINA tana sallah? Tsmbayar kansa yakeyi nida mai karstu mukace Ah ah Batayi tunda Kaine kadai musulmi a duniya.
[4/25, 6:30 AM] Melody🎤🎤: *151-155* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻


©
_*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_






BABI NA TALATIN DA DAYA




Yana zaune yana kallon ikon Allah RAINA bata bar kan sallaya ba har saida tayi sallar Asuba ta daga hannu sama tayi adu'a ta shafa bata zarce koh inaba sai dakinta inda doguwar hanyace ta rabata da inda turakan Danish take wanka tayi tasa kaya marasa nauyi ta kwanta sai bacci.
Bayan yadawo daga Masallaci yanemi RAINA yarasa wani haushin kansa yaji Wata kujera yafada yana yamutsa gashin kansa tako ina ya buga hannunsa akan tebur anan shima bacci yayi awon gaba dashi misalin karfe shabiyu ya tashi lokacin am hada mishi duk abun kari kallon jakadiyyarsa yayi kaman zai tambayeta saikuma yafasa yaci gaba dacin abinchi badon yanaso ba ya tabbata da Raina tana nan zaune dayaci Dayawa don yanzu sonta yake amma kuma yaci damarsn sai taji kaman tace bata auren, itakoh zaune take tana kallo Bayan tayi Karin kumallo inda taketa ganin bak'i suna shiga suna fita itadai iyaka tayi musu sannu kuyangu ke kula daduk wani harkar sasan nata Wayarta ta dauko kiran Infinix 0 ta latsa lambar Mahaifiyarta tana dauka tace
“Ummi Barka da rana” cikin sigar shagwaba.

Sarauniya Maimuna tayi dariya tace
“Amarya kenan dafatan kin tashi Lafya kinjini shuru koh ai nasan kina tattare da gajiya shiyasa bankiraki ba Allah yayi miki Albarka yasa kusamu zuriar dayyaba”
“Amin” RAINA tace chan kasan makoshinta
Sarauniya Maimuna takara da cewa “Abu na biyu danakeso dake shine ki rike ibada sannan kibi mijinki da abokiyar zamanki sau da kafa” RAINA ta tabe baki tace
“Umm Ummi naji Abby yana kirana” karaf ta kashe tayi huci
“Hmmm duk Wanda yaso azauna Lafya shiyaso don Bazan dau ko wane irin cin kashi ba yadda ta nunamun haka zan nuna mata”
Kiran mahaifinta tayi yana dauka tace “Allah yakara maka Lafya Abby Kaine dawisu abun kallo zaki sa gabanka inda kakeso ranka yafi nawa dadewa Abby Mahassadan ka fadawanka kataka a sannu adon kowa” dariya sarki MAMUDA yayi abun yayi mishi dadi “Ina kwana beautiful princess dafatsn kin tashi Lafya ya Bakunta Allah ya kauda idon makiya yayi miki albarka keda zuriarki baki daya ngd da gaisuwa kirari yayi dafatan bakida wata matsala?”
RAINA ta gyada kai kamar yana kallonta tace
“Babu gaskiya Saidai inaso inji a ina maganar Karatuna ya tsaya?”dariya yayi yace “Karki damu insha Allah xaki cigaba” haka sukayi sallama.

Yauma kamar Kullun jakadiyya ce tashigo hannuta daukeda wasu kayan baccin masu kyau da sheki son kowa kin Wanda yarasa rigar dai wasu igiyoyine sukasa aka kirata da riga haka ma short din shima kulleshi akeyi RAINA tana ganinta ta tamke fuska cikin ranta cewa take Niko naga takaina ji irin wulakancin da bawan Allah nan yamun amma wai kuma yau in kara komawa tabdi jam.
Jakadiyya ce ta katseta da cewa
“Lokacin bacci yayi koh kina iya sanya wannan in rakaki?” babu musu Raina tasa suka kama hanya Tana shiga taji babu kowa amma kuma sai taji saukan ruwa kofar toilet din ta bude ganin Danish cikin kumfa yana wanka a baf matsawa tayi yace
“Barka da dare ranka ya Dade dafatan ka wuni Lafya Idan bazaka dumuba bari in tayaka goge kafa” fadi tayi tana fari daman na abun nema bane wajen RAINA tun tana karama ta iya fari, Sa hannunta keda wuya yaji wani iri sha'awarsa ta tashi wani banxan kallo yayi mata yace
“Waike meyasa kin fiye shishigine nifa Karki manta badan bariki bane irinki don haka kiyi gaggawan cire hannunki kafin inyi maganinki sakarya kawai Mara zuciya yarinya saikace karya?” Raina kanta a kasa yake don cin mutuncin danish bayau yafara ba amma nayau yafi kowanne muni dayace mata yar bariki, Tsame hannunta tayi tayi waje ta rufe fuska sai kuka saida tayi mai isanta ta nemi guri ta kwanta kamar Kullun ta mike donyin. Ibadanta sai taga Danish zaune yana kallonta batayi saurin bude idoba saida tayi motsi ya kauda idonsa RAINA tace acikin ranta
“Hmmmm lokacin ka ne Danish amma nawa yananan tafe” Alwala tayi tazo tayi sallah har saida tayi Asuba Bayan tafiyansa masallaci ne kafin ya dawo babu RAINA babu labarinta
“Wai me take nufi daga sallah saita wuce sasanta?”saida RAINA tayi kwana bakwai Danish yana mata wulakanci amma dukta jure mai martabane ya aiko a kira danish saboda yaune ranan dazai Tara matansa ya raba musu kwana Danish ya gamsu amma kuma dakamar wuya wai gurguwa da auren nesa shi bazai taba kiran Unaiza ba saidai ysba jakadiyya sako ya raba kwana biyu haka akayi Unaiza taji dadi don yau kwana takwas ba Danish babu alaman sa dadinta daya bayason RAINA, Nanta fara shirye shirye amma ni humairah nace Allah yarabaki da Tsiran makaho.
[4/26, 7:53 AM] Melody🎤🎤: *156-160* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻


©
_*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_




*BABI NA TALATIN DA BIYU*




Unaiza ta tanaji komai don mijinta amma da dare yayi sai taga akasin haka babu shi babu diriyarsa nan hankalinta ya tashi bata tsaya bata lokaci ba sasan danish ta wuce taganshi zaune dagashi sai boxer wani dadi taji aranta wucewa ciki zatayi danish ya janyota har saida kanta yakusa haduwa da gini a tsorace take kallonsa
“Amma Unaiza saiyau nasan cewa kina yaudaran kanki sannan Kisani ban yarda da shigo shigo ba zurfi ba kina tunanin zakizo mun cikin daki hakanan baysn iskancin dakikayita yi a baya Kisani kafin in kiraki matata sai kinje Asibiti anyi miki tests din STD( Sexual transmitted diseases) Sannan ki koyi ladabi oh Allah mai yasa mata masuda kunyane daga kunga anyi muku kishiya koh kunya saiku fara abunda da bakuyi toh Kisani Unai bazaki taba yaudarana ba kuma ki bacemun naji yau girkinki ne Amma kuma ngd bana bukatan zuwanki” Duk abunda suke Duk a kunnen Raina sukeyi Unai tabata Rai bata iya cewa komai ba tasan cewa Allah ne yake sakawa Danish abubuwan datayi mai a baya wasu hawayene suka kwararo daga idanunta durkusawa tayi har k'asa
“Mijina ka tausayamun kayi hkr kabani dama in nuna maka cewa yanzu bada bane daman duk rudin shedan ne”
“Tir da wannan shedan din Unaiza kuma karkiyi amfani da shedan wajen kare kanki don kina daya daga cikin shedaniyar kanki ki tashi kafin ranki ya baci banza kawai wawuya sakarya dubabki kaman wata tsumma a randa mtwwwew”.

Tashi yayi ya dauki jaridarsa ta Daily trust ya shige falonsa Ya b'ame kofa bam yabarta zaune a kasa tana kuka, haka akayi kwana biyu Unaiza bata samu wani rabo daga jikin Danish ba kwanan Raina ne yau amma bata wani dauki taci Alwashi saita gwara kansa tunda ya wulakantata a matsayin mace mai Aji da Sanin yakamata yau yaci ace tazo inda yake amma danish shuru yakeji har misalin karfe biyu na rana, Sai safa yakeda marwa saida yaji wani jiri yarasa meyasa yakejin Raina har kokon zuciyansa itakoh Azumi takeyi dayake yau litinin har ta wajen sasanta yaje kozai ganta amma

Please Login or Register in order to submit comment