Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Raina taja Goggo data kasa cewa komai abun duniya ya isheta, shiko magari tsaye yayi yace
“kumu tafi daman barewa batayi gudu danta yayi rarrafe ba shine da Fu'ad yake shirin jajibomun irin tsiya irin jaraba da haka zata dinga tsigeni nida marwa” haka suka koma Tuni akayiwa gida kudi Fu'ad ne yasiya har naira dubu Dari biyar badan komai ya siyaba saboda RAINA dayasan cewa duk abunda yafaru da ita daga Allah ne amma yajin baxai iya hada zuria da RAINA ba, haka aka kaimusu kudi washe gari tunda duku duku suka tashi basu sauka koh inaba sai Wani gari *Dinya* Gaba da SOBA inda akwai matattaran karuwai da masu zaman Kansu, haka suka samu hayan daki daya k'ato suka sai katifa Dadai sauran kayan aiki, nan RAINA tafara baje gwanjon tsiya itada yan gidan saboda samari suna kawo mata bara cewa suna sonta ita kuma kowa yitake dashi, indai zaka sak'ar mata kudi yan dubu dubu farare, Goggo itace magajiyarsu itake ba RAINA duk wani salon yaudara da samun kudi Haka basu zauna ba wajen bin bokaye don Neman sa'a, Raina koh tajik'u sosai da mugunguna don tace bariki tun ina k'arama na iya toh yanzu nasa kafa wancan sharan fage nayi, kowacce mercy kallon docas nake mata, Goggo batada wani buri saina ganin Rayuwar raina ta Daidai ce saboda kin jininta da Tayi tun zuwanta duniya kawo yanzu.

Raina dai tazama abar kwatance a gari tazama maiji da kanta a shekara Ashirin RAINA ta mallaki gida da mota Wanda babu kamar sa acikin garin soba da kewayenta haka bangare daban tayiwa Goggo sannan aka girke rikakken malami koh ince boka, Shike mata aiki don duk namijin daya kawo kansa gidan Sunanan sa sorry don bata amsan kudi a hannu sai Check dukda ba arabi ba boko wani yaga Raina zaice tayi digiri harda digir gir Abu yayiwa raina yawa ga sata ga maita, ga zina ga madigo babu Wanda batayi Alhaji bello shine Wanda ya tsarewa RAINA komai na rayuwa sannan ya hanata mu'amala da kowa wata rana k'watsam Matarsa takira shi don taji rade radin ya ajiye karuwa, kin dauka yayi saboda tsoro, RAINA tana kwance daga ita sai yar shimi sai pant nashiga Swimming pool ta dauki wayar ta kara a kunne
“Hello Ranki ya Dade uwar gida saurautar mata mai suna biyu lafya mijin naki bacci yakeyi pls kiyi hakuri zuwa gobe koh jibi don banison takura bare damu”
Kafin matar tace wani Abu an kashe wayar gaba daya haka Raina tafada kan jikinshi tana shafa mishi katon cikinsa tana mishi hirar love shiko Tuni ya sakankance yabada kai bori ya hau yana gamawa yashiga wanka yace zai wuce RAINA tace
“Miliyan daya nakeda bukata inaso zanyi yan wasu hidimomi ne kafin ka dawo daga England koma Mu wuce tarene?”

Alhaji yayi dariya
“Hmmm RAINA kenan sonki kawai nake kaunarki tana dibana mezai hana mutafi tare Visa akayi mata rana guda saboda dakwai kudin haka suka wuce kasar England saida suka Shari wata daya suka dawo,
Ni humairah nace
Raina tauraronki yana haskawa yanzu toh wata rana saiya dusashe yakoma hasken gulob daganan hasken rechargeable gaba gaba harken fitilar kwai sai kuma na aci balbal mai hayaki sai kuma dundim, komai yanada lokaci Allah yasa mugane ngd Allah daya bani iyaye masu kula ba irin Goggo ba daman batasan zafin haihuwa ba sannan batasan zafin lalacewar rayuwar da ba, zeenert ce kishingide akan kujera tana waya tana gamawa ne RAINA tace
“Zeenert kenan dole in tsula tsiya yadda nakeso saboda inada wacce ta tsayamun sanadiyyan Uncle Aymel rayuwata ta lalace sannan kinsan wacece silar? Goggo, babu wani makircin daban iyaba babu salon daban iyaba zeenert Abu daya nakeso shine a duniya yanzu in Sani waye ubana sannan yar wace Garice ni haryau Goggo taki gayamun amma nasan wata rana dole ta sanar dani komai”
Zeenert tace
“Tabbas kuma ai ranar wanka ba'a boyon cibi”
“Maganarki dutse yar uwa ”
[4/12, 6:55 PM] Melody🎤🎤: *76-80* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻


©
_*STORY & WRITTEN BYHUMAIRAH (Melody)*_




BABI NA SHA BAKWAI
_*I DEDICATED THIS HUMBLE PAGE TO ALL ONLINE HAUSA WRITERS MOST Especially my noble once Aneesa AR, Aunty SIS💞, Umma yahya Goyon kaka, Fatty Azland, Samrah, Hajja ce, Firdausi sodangi, Fatima Nashuka, Jannart, Asykhaleel, Xarahbukar, Ummi Aysha, Miss XOXO, Mjay, Husnat, Abeeda, basira, Mrs umar, tytrlorh, Aisha sayedi, Lots of more Tsintsiya madaurinki daya🤝LYSM😘😍 you ladies are wonderful😄*_








Cewar Raina haka taci gaba da kazan tacciyar Rayuwa wacce kowa yake gudunta ita zina bashi ce kowa yacita saiya biya koh ba jima koba Dade, faden Allah ne yace
“Ku kare iyalinku da zuri'arku daga halaka ” sannan yace “Mukare farjojin Mu daga zina” amma ina wasu basu ganewa sukanyi Zina kamar baza'a mutuba, yanzu Zina taxama ado baga matan aureba baga yan mataba hatta samari musibar dake dawainiya Damu kenan, meye ribarki yar'uwa idan kinyi zina? Kudin za za'a baki dabai zaisiya miki daraja a idon mutane ba, bare sabulun dazaki wanke kaxantar data zuba ajikinki, mezaisa kiyi abunda kike boyewa mutane Dakin gansu ki boye saboda kar ace anganki muji tsoron Allah tun kafin lokaci ya k'ure.

Dambe Raina take kwasa itada wani saurayinta, datakai mai ziyara yaci bai biyaba, tadinga gwanjon siya Akan titi kowa yana kallonsu gashi ta chukume mishi kwalar tiga ta rikemai wando
“Wallahi saika bani kudina aiba a banza zaka hayeni kaki bani asiba nidai zamuga mai naci”
Wani magidancine yazo wucewa yaga mutane sun taru sai dariya suke musu
“Baiwar Allah meye ribar dambe da mijinki a titi?”
Mutane suka fara ihu ba mijinta bane dadironta ne.
“Wa'iyazu billah Allah ya shirya haka sukaci dambe tundaga ranan Kasuwar Raina tadawo kasa babu wasu samarin arziki sai yan kuci kubamu, Goggo koh babu alaman ladama illah kara tunzura RAINA zuwa aikin assha, daga karshe gidan aka siyar suka koma daki daya suci banxa suci wofi, daga karshe wani Dan masu kudi yazo da niyyan zai auri Raina lokacin tanada shekara 22 a duniya, Amma kema dagas tak'i amma *Farid* yanace saboda auren dole za'ayi mai shikuma yace gwara ya auro karuwa mai zaman kanta ya shiryar da ita suci gaba da rayuwarsu ta so da kauna.

Goggo taga kudi Tuni ta zuge Raina da shawarwari haka aminche, tafara zaman istibra'i harna tsawon wata Uku bata zuwa koh ina amma fah acikin duhu takeyi saboda babu wani Neman tuba datakeyi, saidai taci tasha tayi bacci babu sallah babu salati, *Farid dai Dan gidan Ambassador GARBA BUBA ne Hamshakin mai arzikine kyakkyawan mutum ne son kowa kin Wanda yarasa, Sun hadu da Raina ne a filin jirgi dake mumbai lokacin datake shirin zuwa K'asar India don Neman Fu'ad Dan gidan mai gari amma haka tagama holewa ta dawo, danginsu Farid babu talauci gasu da kyau kamar su sukayi Kansu ga isa da iya MULKI, shiyasa aka hada Farid da farida aure saboda shakuwar da sukayi kowa ya dauka soyayya sukeyi dukkansu basuda buk'atar juna shiyasa suka bijirewa iyayensu akan cewa babu wata ALAK'A a tsak'aninsu illah so na yan'uwan taka, Mazauna garin Kaduna ne a malali sukeda zama, haka Farid yasanar da farida cewa shifa yasamu mata Farida tayi murna tace “me sunanta?”Farid yace “Nawa zaki biya don sunanta mai tsadane”tuni ta marairaice tanaso tayi kuka nanya sanar da ita cewa Sunanta RAINA*
Tsalle Farida tayi tace
“Wat a Nyc name bro kasan ma'anar sunanta kuwa?”
Farid yace
“No saikin fada”
“Beautiful princess” wani dadi yaji yace
“Amma fah xan gayamiki gaskiya Raina zaman kanta takeyi da itada Goggonta inta kaita miki wannan zance basan waye ubanta ba kinga koh akwai bikin zuwa babu zani, acan wani gari take kibari zuwa jibi zamu kiganta”
Farida tayi murmushi sannan ta figi Motarta sai gida.

Farid ne tsaye cikin falon mahaifinsa yanata kaiwa da komowa Chan yaji motsi har kusada stir case din benen yaje tarbo mahaifinshi,
“Barka da fitowa Daddy Allah yataimakeka, zama yayi akan cushion shiko Farid ya durkusa yace
“Daddy daman inaso in sanar dakai cewa nasamu wacce nakeso zan aura Ku gafarce ni daddy nasan cewa nidane nagari amma kudubamun Kuga halinda zan shiga Farida tanada Wanda takeso kuma babban abokina ne baxan iya aurenta inci amanar Abokina ba pls daddy kaikadai ne zaka sharemun hawayena daddy save the poor little boy pls”
Wata muryace ta katseshi da cewa
“Farid inhar Nina haifeka saika auri Farida itace matarda naxaba maka do or die saika aureta”
“Dakata Hajiya tasallah abunda Farid yakeso shiza'a yimai koda karuwa yace yanaso zan auramai matukar zai sanyata hanyar da Allah ya tanadar ma kowani mumini”
“Alhaji baxan yarda ba”shikuma
Yace
“Bazan dauka ba danane inada right akansa narigada na gama magana saboda yakawomun duk wasu dalilai nasa kuma na yarda dasu na aminche aure kuma rana ansa sati biyu kifara shiri”
[4/14, 7:37 PM] Melody🎤🎤: *81-85* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻


©
_*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_




BABI NA SHA TAKWAS


Juyawa tayi afusace yashige daki tana keta uban zufa
“yanzu ni Farid zai watsawa kasa a ido lallai saina hanashi kwanciyan hankali acikin gidansa muddin ina raye”
Wayarya ce ke kara tana duba tankamemen Screen din iPhone 7 dinta taga ansa unman Farida gabanta yafadi tace Allah yasa ba sun fasa bane don inkan bakana, karaf ta dauka tace
“Hello hajiyar Allah ykk ya sirikata?”
“Hajiya babu lafya fah Farida tace itafa batason Farid tace itafa tanada Wanda takeso tace do or die aure tsakaninsu da Farid babu gata tanata masifa tana farfasa kayan gida”
Jikake tas tas tas
Ni humairah dake labe don kar a jehomun flower vase ai tuni na fita aguje, katse wayar sukayi kowa yana jimami, Tuni suka shirya sai garin Dinya inda RAINA suke zaune dayake sunbar gidan karuwai, Raina itace karuwa mai ladabin kunama, RAINA yayi musu girki kala kala iri daban daban amma babu dadin sisi bare kwabo, Haka akayimusu tarban girma, tunda Farida taga Raina taji gaba daya ta kamu da sonta tana jinta tamkar yar'uwarta tajini haka sukayi hira mai kwantar da zuciya, Farid kuwa saboda tsabar kwaliyan RAINA har kasa magana yakeyi bare yayi mata kallon minti biyu ji yake kamar ya dau hannu ya tabata,
Raina dai jar fata ce son kowa kin Wanda ya rasa siririyar fuska gareta ga saje ta kowane gefen fuskanta, Bakinta bawani karami bane kamardai nawa, hancinta shima Dan daidai Wanda za'a iya misaltashi da dogo amma ba kwarai ba, idanuwanta kanana kamar maijin bacci, sannan sun danuwanta kamar na maciji yayi shape sosai, Raina dai baxamu kirata gajera ba haka baxamu ce mata tanada tsawo ba tana tsaka tsakiya, gashin kanta baida wani yawa bacin acuci datakeyi ai sai a gudu saboda kamar hammatan San iska yake,
Wannan kenan.

Misalin karfe uku Farid yace
“Princess zamu wuce duk abunda muke ciki zakiji sannan karkiji komai sannan ina umurtanki dakiji ki kiji saboda akwai wasu matsaloli, haka sukayi Exchange din number da farida suka wuce sai Kaduna,
Fitarsu keda wuya Raina takoma ciki tace
“Goggo yanzu yaxamuyi kina tunanin kezaki amsa kudin aurena kamar yadda kika amsa na Fu'ad? ”Goggo tace
“K'warai nizan amsa Susan cewa ke mara galihu ce Mara usuli bare tushe, koh kinada Wanda zai amsane bayanni?”
Goggo ce ke magana cikeda iko da isa da MULKI Raina tace
“Goggo kinsan cewa mulki baxai kori SARAUTA ba? Kinsan da haka toh inaso kisani baki isa ki amshi kudin aurena mutukar bazaki nemomun ubana ba saboda ba kimata bace bare daraja ace kece zaki amshi kudin aurena baxai taba yuwuwa ba, idan kuma kince ah ha maxa ki nemomin mahaifina, nasan cewa bazai ki jininsa ba”Tuni Goggo tafara ba RAINA hak'uri tana lallashinta haka Goggo tasamo mutane uku Wanda sune suka amshi kudin saboda kimarsu da darajarsu saida Ambassador Garba Buba yayi musu kyauta,
Sadaki dubu dari aka bada da akwatina guda goma cikeda kaya.

Bayan tafiyarsu ne Goggo ta fito daga inda ta boye ta amshe kaya tayi musu godiya abunda yabata musu rai kenan, har saida kyauta ya tsaidata yace “Me kike nufi tsohuwar kilaki koh kin manta yarda mukayi ne miko”
Hannu ya mikawa Goggo haka ta debo kudi tabasu adai rabu lafya, Ranan sati biyu akasa sannan a masallaci za'a daura auren,
Bayan k'wana Uku da kawo kaya hajiya tasallah tamatsa sai ankaita taga Raina sannan hankalinta zai k'wanta, Farid bashida yadda zaiyi haka yakira Raina yasanar da ita komai haka ta shirya cikin tsadadden lace tayi makeup komai yaji,
Sauraren zuwansu Farid kawai takeyi,
Dazasu wuce saida farid yabiyata gidansu farida yace tafito su wuce tare, sai garin Dinya.
“Farid wai ina kuke shirin kaini ne kar dai kacemun yarinyar anan take?”saboda yana tuki yarasa wace irin amsa zai bata shuru yayi baice komai ba
“Farid magana nakeyi kayi shuru”?
“Hajiya me kikeso ince miki kinsan dai Asalin kowa kyauye don wannan garin birnine akan wasu kyauyukan” tundaga haka bai kara cewa uffan ba farida kuwa Adu'a kawai takeyi kar umman farid ta wulakanta RAINA don raina bazata raga mataba saboda yar bariki ce.
[4/14, 8:06 PM] Melody🎤🎤: *86-90* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻


©
_*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_




BABI NA SHA TARA







Da isarsu Hajiya tasallah ba abunda takeyi sai yatsina fuska ta window raina ta hangi matar acikin ranta tace kindade baki yatsina fuskaba Daganin matar nan yar bala ce amma sainayi maganin iskancin mata ciki suka shiga sukayita k'wada Sallama ta fito tayi musu sannu da zuwa suka shiga, kan Chinese carpet suka zauna hajiya sai toshe hanci takeyi Farid sai kyafta mata ido yakeyi amma ina koh kallon bai isheta Raina tace
“Ina wuni hajiya kinzo lafya”? Hajiya tasallah tace
“Daban zo lafya ba zaki ganni wannan wane irin dakine farid saikace Masai sai doyi takeyi, wannan ai saiya janyo maka cuta akasa gane maganinta a Asibiti.
Ai tuni Farid ya dafe kai saboda tsabar kunya farida kuwa arsnta tace ai nasan a rina, Raina tacika da mamaki k'warai bin Hajiya takeda wani shu'umin kallo tace “Hajiya ga ruwa ga abinchi” ai tuni Hajiya ta watsawa Raina ruwan da abinchin Raina tayi dariya lokacinda Farid ya tashi don zuwa kusa da ita tace
“Basaika zoba Farid dadin abun mulki koh arziki baya tasa SARAUTA gaba saidai SARAUTA tasa mulki da Arziki gaba, Farid kai nakeso ba mahaifiyarka ba Kaine jin dadina ba wannan matarba, karkace naji haushi ah ah kodaya don na fuskanci Rayuwa wacce tafi wannan zafi dacin rai, Sannan kisani Duniya tafi bagaruwa iya jima, Ban nufin kowa da sharri sannan bana saka sharri da sharri sai in tura takai bango”.
“Farid daman irin wannan yarinyar zaka auro harta zama surikata toh bazata sabuba bindiga a ruwa, wane ni da daura zani uwar miji na yawo tsirara.

Fuuu ta fice batareda ta koh waiga ba kafin su gama rarrashin Raina ai hajiya tayi Nisa suna fita da mamaki babu ita babu labarinta, haka sukaci yawo wajen nemanta amma babu ita babu labari Raina aranta tace
“Yar iskan mata haka kawai ki addabi mutane wallahi danice baxan nemeta ba saidai ta bace mtwwwwww”
Nikoh HUMAIRAH nace Raina ba laifinki bane bakisan dadin uwaba bakisan soyayyar uwaba shiyasa kike tunanin kowa ya wulak'anta uwarsa..
“Farida Princess gaskiya daganan I can go beyond nan wajen am tired so tired yakamata Farida mukama hanya saboda bamusan abunda zai faru da hajiya ba”
Kallon Raina yayi cikeda so da k'auna yace “bari Mu tafi kinji saura dakwai kudi Dana ajiye miki banda bukatan komai na kayan daki ke nake bukata ranan daurin aure da'an daura kisa aranki zamu wuce kaduna, Goggo kuma nasama mata gida ita kadai Sannan na bude mata shago Wanda zata dinga siye da siyarwa, RAINA believe me you are my destiny you are my life I love you toh the moon and back”
Pec yayi mata yashiga mota Raina sai daga musu hannu takeyi, haka ta gyra kanta iya gyra amma sabo daban yakeda second new (Wato tsoho) amma Farid ya yarda ya aminche daduk yadda zai sameta,
Da isarsu gida farid ya kutsa hancin Motarsa cikin gida abunda ya tada mishi da hankali shine ganin fuskar kowa na gidan babu fara'a babu walwala, lokaci daya taji gabanta ya fadi tafiya sukeyi kaman kwai ya fashe musu aciki wucewa sukaje yi Ayman daya kasance Yayan Farid yace
“Dakata Mara mutunci Mara tarbiya zaka bige a yarinya fitsararra, wacce batada wani usuli yar cikin shege” .

Lokaci daya cikin k'araji Farid yace
“Karka sake Yaya karka kuskura ka sheganta mun mata ita nakeso kuma ita zan aura, Ku kukace inbidi mata kuma nasamo sai kuma yaxama abun gori Duk abunda Raina tayiwa hajiya ita taso kuma ta siya da tsabar kudinta don haka let me be on my own after ol inada madogara idan kukace inbar gidannan zan Bari koda kuwa yin hakan sabo ne yaya na gwammace in dauwama cikinsa”
Tas tas kakeji Ambassador Garba ne ya kwashe Farid da mari yace
“gobe za'a daura maka aure kuma a gobe zakabar gidannan don naga abun naka harda cin mutunci”
Farid yarike kunci yana zubda hawaye yace “Nagode kwarai daddy nagode da duk wata dawainiya dakayi dani daga haihuwa zuwa yanzu Allah yasaka muku da Alkhairi nagode” wucewa yayi yasamu wayar mahaifinsa yayi transfer din kudi naira Miliyar Goma ya ajiye kamar baiyiba, Sannan yashiga daki ya hada komai nasa Farida sai kuka takeyi Rumgumeta yayi yace
“Takwarata kar kiji komai Allah yana taredani a duk inda nake kuma jihadi zanyi na auren Karuwa mai zaman kanta, kuma ta dalilina indai me shiriya zata shiryu kukanki yana dagamun hankali”
Shuru Farida tayi nadan lokaci a inda take sauraren wayarda Farid yakeyi tasan bada kowa yake wayaba saida RAINA,
[4/16, 8:05 AM] Melody🎤🎤: *91-100* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻


©
_*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_




BABI NA ASHIRIN


_*ASSALAMA DAFATAN ALKHAIRI GA MASOYA JINNINA GA MARUBUTA, Dayawa mutane sunamun tambayan cewa meye dalinlin dayasa bana cikin kowacce kungiyar ta MARUBUTA? Dalili shine banida ra'ayi sannan ban fiyeson gutsuri tsoma ba koh kuma munafunci shiyasa na kiyayi kaina Saboda I don't want to be Dis-honoured🙅🏻 But tunda dayawa suna zancen yakamata inshiga zan shiga Wanda ya dace Idan kuma mutanen ciki zasu amincemun zanji dadi, sannan kohda ban shiga wata kungiya ba inada Manyan marubuta masu bani sha'awara daga cikinsu Akwai ANEESA AR sannan da dadewa akwai RASHKARDAM, Haka MIEMIEBEE she was one of the best, Sannan ga Uwar Arziki AUNTY SIS💞 Akwai ILILEE the chief baker😜 ALLAH YASA DAYAWA SU FAHIMCENI👏🏻.*_ #ANAMUGUNTARE😍😘





Washe gari haka aka daura auren Farid da Raina bikin bawani armashi abokansa dai duk sunyi mai kara sunzo kowanne cikinsu saida ya yaba da kyau irinna Raina, sannan sunga tsantsar SARAUTA acikin idanunta, motoci ne nagani nafade bayan kowa ya watse ne Ayman yace
“Mijin karuwa inada buk'atar mukullin motarnan saboda kasan da cewa yanzu you are not part of us”
Damamaki Farid yace “Bakada hurumin amsan mota a wajena my man yafadi tareda dafashi, don bakai ka siyamun ba kabari Wanda ya siyamun ya amsa my people if you guys are ready muje kafin sugama shiryawa”
Kad'a kansa yayi shida abokansa sukabar Ayman tsaye, misalin karfe hudu zukazo daukan amarya, haka Goggo tadinga yiwa Raina hudubar k'anzon kurege da matacce da rayayye itakoh raina wani kasurgumin tunani takeyi wai itace tayi aure shin meye aure me aure ya kunsa? Duk wayannan tambayoyin ni HUMAIRAH nace bansaniba Raina saikin shiga zaki tantance komai.

K'awarta zeenert itace ta rakata har garin Kaduna, a bypass gidanta yake babu ne babu acikin gidan komai yaji daidai ruwa daidai kurji, haka zeenert ta wuce nata waje acikin garin kaduna, abokai duka suka k'ara gaba, daga Raina sai Farid hankalin farid ya k'wanta
“Amarya bakya lefi yau gaki a sabon waje dole muyi hakuri da juna dole kiji kiki ji, yanzu inaso inyi miki wasu tsmbayoyi gameda Addini xaki bani amsa yadda yakamata daga bisani saimuyi Sallah Mu godewa Allah daya nuna mana wannan rana”
Ras Gaban Raina yafadi don tasan cewa kashinta ya bushe don babu abunda tasani, Farid ne yaci gaba da cewa
“Amarya raina inaso kimun Karin bayani gameda wankan tsarki Sannan sunnoni da mustahabban Sallah, Sannan da farillai saikum hukunce hukuncen musulunci”?

RAINA tayi kwalkwal da ido tarasa abunda zatace yau k'ayarta ta k'are,
Shuru tayi nadan lokaci daga bisani ta sauke girman kai
“Farid bazanyi karya donka soni ba a gaskiya banida wani Sani dangane da tambaoyinka , k'yauyen Dana tashi bamuda makarantar islamiyya bare na boko yadda ka ganni haka nake, fanko na sai tarin jahilci don haka inaso ka koyardani komai gameda Addina musulunci”
Farid yayi mamaki k'warai _*ni humairah nace Tabbas da'ace maza da dama idan sunyi aure suna tambayan matayensu irin wannan tambayoyin da suka shafi addini toh da yanmata dayawa sun rage girman kai sun koma mak'arantar islamiyya don samun ilimin addini don dayawa yanmata basu damuda zuwa islamiyya ba, sai kallo da karsnce karance toh kusani komai yanada lokaci mutuk'ar munaso Mu tsira da mutunci mu, gidan aure ba gidan shargalle bane zamane na har abada Sannan ibada ne, aure is not all about eating food, having sex all day all night, Sleeping and also gidan aure is not a club wajen gulma da tsegumi, dayawa mata basusan wannan ba, Allah yasa mudace da mazaje nagari Amin.*_

“Hmmm RAINA kenan naji dadi k'warai dakika sanar dani zan koyar dake komai gameda musulunci haka suka kashe wannan dare wajen fadakarda Raina abubuwan dasuka shafi wankan janaba haila dadai sauransu, Sannan suka gabatar da sallah Sannan Yakama gashin kanta yayi mata Adu'a yakori duk wani sharri daxai fada musu, Sannan Raina ta canza kaya duk kunyarsa takeji, ni humairah nace Ashe yan bariki Nada kunya?
Kwanciya tayi shima ya k'wanta ya rugumeta ajikinsa haka yadinga sarrafata daga bisani raina tafara baje nata baseerah,
A wannan dare sun farantawa juna rai gashi yadda farid yake tunani ba haka bane, tunda Asuba Farid ya tashi ya samusu ruwan zafi sukayi wanka raina ta sauya kaya.
Haka raina taci gaba da bautar aure kudinda Farid yake takama dasu komai ya kare basuda komai gashi kowa ya juya mishi baya, Raina Kullun faranta mishi rai takeyi haka zaije yayi dako yaciyar da ita amma duk bata damuba, har aka koresu daga gidan dasuke saida nayi musu kuka, amma hakan baisa farincikin su ya gusheba, daki daya suka samu a unguwan nufawa nan suke zaune dayake ba tsada duk wata Dari biyar ake biya amma wani lokacin sai farid yakaiga cin bashi gashi abokansa duk sun gujeshi bashida kowa sai Allah saikuma raina da farida.
[4/16, 7:56 PM] Melody🎤🎤: *101-105* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻


©
_*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_




BABI NA ASHIRIN DA DAYA


_*Dedicated to Fatima(Maman Beauty) From Kd Tnx for the love and care, And also masoya na over the world i shout out my greetings😘😘😘*_





Yasaida komai nashi bashida abun tunk'aho gashi babu wani abu da iyayensa sukeyi akai, haka zaman su yaciga babu tsana bare tsangwama, Raina ce zaune itada matar wani mai kudi a kusa dasu wacce suka kulla k'awance don har abun Alkhairi takewa raina,
“Jamila babu abunda yakai aure daraja, nayi bariki tun ina yar k'ank'anu wata amma wannan Rayuwan da nake ciki tafimun komai dadi mijina yana sona yana mun komai Wanda bai gazawa karfinsa ba, dalilina iyayensa suka gujemu suka daina yimishi komai saboda ya aura karuwa” kuka raina takeyi Wanda ni Humairah nace da ace Raina kinsan koke wacece wallahi dabaki damu kanki ba, amma muje zuwa mahaukaci ya hau kura.
Jamila ta tsareta da ido tace
“Raina dakinsan irin wahalar danake sha cikin gidannan sai kinyi mamaki Raina nasan zakiyi tunanin cewa mai Jamila tarasa dazata damu kanta kanta babu abunda Abban Abrar bayamun daga sutura, abinchi, kayan more rayuwa duk akwai amma narasa farincikin mijina, babu kwanciyan hankali bakin cikin yau daban na gobe daban ga kudi ga arzik'i amma idan babu farinciki Raina duniya takan zamemun Wuta nikadai nasan abunda nake fuskanta, idan Abban abrar ya mula sai inyi wata uku bansa shi a idoba, wallahi Raina na gwammace irin rayuwarki da tawa”.

Raina tace “gaskiga Ummin Abrar ganin miji kusada kai wani niima ne na daban Wanda bakowa yasani ba, amma dayawa mata sunfi ga kudi koda miji bayanan, nima ina daya daga ciki amma yanzu nasan meye duniya take ciki, dole idan mace taci takoshi ga kudi ka abubuwan more rayuwa amma Dole ta nemi namiji a kusada ita matukar tanada lafya Ummin Abrar Kiyi hakuri komai yayi farko zaiyi karshe kiyita yimishi Adu'a Allah ya dawo miki da natsuwan mijinki gareki toh Tabbas zakiga abun mamaki Allah maji rokon bawane.” Ummin Abrar tayi mata godiya sannan ta wuce gida fitarta keda wuya Farid yashigo kayan jikinsa kacha kacha kamar Wanda yayi dambe da

Please Login or Register in order to submit comment