Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kura gaban Raina ya yanke yafadi da gudu ta nufi inda yake tana kare masa kallo shiko Farid yakasa kallonta
“Mijina daga ina kake suwaye sukayi maka wannan ta'asar? Me kayi musu? Kayimun magana don ina iya fito nafito daduk Wanda yayi maka wannan raunin”?
Kallonta yakeyi ido cikin ido tausayin Raina kawai yakeji
“Raina muje daki zan gaya miki komai” ledar hannun sa ta amsa suka shiga Daki zaunar dashi tayi ta zauna a gabansa ta zabga uban tagumi yace
“Akan hanyata nadawo wa gida ne nahadu da gungun matasa suka k'wace Dan kudin dana samo sannan suka yankamun gefen wuya amma saida mukayi damben mutuwa daga bisani sukaci nasara kunsan ance sarkin yawa yafi sarkin karfi”
Raina ba k'aramin tausayi yabata ba haka tasa ruwan dumi tagasa mai jiki haka sukaci kanzon tuwo data jik'a suka k'wanta.

Washe gari Farid yatashi da k'arfinsa dukda yankannan baisa yaki fitaba Dukda Raina bataso ba haka itama zazzabi ya rufeta bayan tafiyarsa, sai uban amai take kwarawa kamar da bakin k'warya haka mutanen gidan babu Wanda yace bari yafito, Ummin Abrar ce tashigo kwatsam da gudu ta isa wajenta tace
“RAINA da lafiyarki kuwa irin wannan amai haka” Goya Abrar tayi tafara wanke mata baki takaita daki sannan ta share koh ina,
“Raina lafya kike meke damunki”?
“Wallahi bansani ba jinayi zuciyana na tashi ga zazzabi mai zafi cikina ciwo yakemun” Ummin Abrar tace bari taje gida ta dawo PT test tayiwa Raina saboda ta karanta Auxiliary nurse shiyasa Ta iya Dan gwaje gwaje harda amsan haihuwa, bayan minti biyu yanuna Raina tana daukeda juna biyu Farinciki wajen Ummu Abrar ba'a magana Raina itama ta nuna farincikinta gidan Raina Ummin Abrar ta wuni sai dare da Farid yadawo tayimishi albishir, a gsban Ummin Abrar farid ya rungume Raina saboda farinciki magani Ummin Abrar ta rubuta Dari uku gareshi haka yaje yasiyo.
[4/17, 11:21 AM] Melody🎤🎤: *106-110* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻


©
_*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_



_*This page goes toh AUNTY SIS💞 Thanks for all the love and care you hv for me am very greatful you are a QUEEN MOTHER👑 U'R different among odas Glory be to Allah may Allah continue to Guide and protect you from all Hypocrite and all Evil May you be the Shining STAR in our daddy's EYES Amin👏🏻*_LYSM😍







BABI NA ASHIRIN DA BIYU


Jiki na rawa yakawo, akwana a tashi wajen Allah ba wuya, ciki sai girma yakeyi yana dad’a fitowa yayi titsitsi zama da kyar tashi da kyar amma hakan baisa sun daina rayuwar aure ba don ba haramum bane a musulunci idan kinada ciki daga randa yashiga har ranan da zaki haihu an yarda miji yayi jima'i da matarsa saidai idan shine bashida buk’ata koh ita matar wallahu ta'ala wa'alam.
Farid sai fafutukan Neman aiki yakeyi da kwalin degree dinsa don har masters yayi k'watsam yasamu aiki Raina tayi murna da farinciki k'warai, Albashin farko farid a matarsa yak'are da dansa me shirin zuwa duniya Sannan ya saya musu kayan abinchi da sutura lokaci daya duka murmure Farida ce zaune cikin Dakin Raina tazo tayasu murna dukda Farida na gida batayi aureba, saboda duk Wanda ta kawo sai suce baimusu ba harta hak'ura, amma Kullun cikin Adu'a takeyi Allah yazaba bata da Alkhairi, haka ta yini kannan ta wuce gida.

Kwatsam wata safiyar Asabar Raina tana k'wance kan kafar mijinta yana mata tausa mugun kofa sukaji na rashin hankali Farid yace
“Raina waye wannan yake buga mana k'ofa kamar ya zautu? Raina ta tsbe baki tace
“Mijina kaje ka duba”.
Yana budewa hajiya tasallah yagani Wato mahaifiyar Farid sanye take da Atampha Super Aura mai ruwan bula ga jaka handbag tayi kyau kwarai amma fuskarta babu sauran annuri illah huci datakeyi Raina dake tsaye Farid ma tsaye yake Amma yakasa motsi bare yayi magana,
“kun kafeni da ido koh bazaku bani hanya bane in wuce?”ai tuni suka matsa tashiga ta tsaya tana karewa dakin kallo cikeda tsana
Gaisheta Farid yayi koh kallonsa batayiba Raina ta durk'usa a gabanta tace
“Sannu da zuwa hajiya kinzo lafya?”.

A fusace hajiya tasallah ta juyo ta daka mata tsawa
“Ke dallah rufemun doyin bakinki har kinada bakin gaisheni bayan kin rabani da dana Allah wadaranki matsiya ciya kawai yar tasha” hamb'are Raina tayi batareda taga cikin ba Farid da sauri ya daga Raina
“Haba hajiya bakiga halinda take ciki bane tsohon ciki gareta kika tureta Dan Allah hajiya karkiyi sanadiyyan kashe mana da Wanda zaiyi mana Adu'a bayan ranmu”
Hajiya tasallah ta kurewa Raina kallo tabbas cikine ajikin wannan makirar,
“Raina har wani ciki gareki ? Waya miki cikin? Kina nufin jikanane? Kina nufin kinada rabo ajikin dana? Kodai cikin shegene har kinsamu k'wanciyan hankali harda daukan ciki? Toh kisani wannan cikin ba jikana bane tun wuri ki nemamai uba”
Raina ta gama rudewa dafe cikin tayi tana kallon farid da idanunsa sukayi jawur yace
“Hajiya ina rok'onki da karki sake sheganta mun da ciki nawane nida Raina Hajiya irin kwanciyan hankalin da muke ciki shugaban kasa baya ciki yadda kuka kujeni saboda Raina babu gudu kuma babuja dabaya ina tareda Matana da dana, kusani da Allah kuke jayayya shiyace Mu auri karuwai musasu a hanyar k'warai wannan yanuna cewa mutum yayi jihadi kuma ladansa dabanne”.

Hajiya ta mutu a tsaye tace
“Kasani yau zama tsakaninka da wannan jarababban yakare, keda uwarki kun taru kun lashemun da dangin maita wayasani koh mayune Ku toh kisani wannan cikin saidai kiyimai uba amma ba jinina bane, koda kasuwa zaki Haifa kin Dade baki haifaba kaska kawai kisani yau kafana kafar dana” hannu Farid ta rike ta jashi waje tace
“Mutafi”
Zare ido yayi yace
“Hajiya intafi kike nufi inbar Raina da ciki? Saidai Kiyi hak'uri matata bata fikiba amma kuma bazan iya tafiya inbarta ba” komawa Farid yayi yarike hannun raina wacce take kuka kamar Ranta zai fita tace
“Farid Dan Allah karka tafi kabarni kadubi Girman Allah ka taimakeni da rayuwar abunda ke cikina” tunu mutane aka taru kamar anacin dank'o Ummin Abrar itama hayaniya tajiyo tafito ganin Raina na kukane tasan cewa ba Lafya ikoh hajiya sai masifa takeyi
“Karuwa kawai kin mannewa dana kin rabani dashi kisani saidai hawayenki su k'afe ko kuma suzama kogi don yawa amma Farid saiya barki dakeda shegen cikinki, woooo dakeda uwarki wayasani koh mayune”
Kara zuwa tayi taja hannun farid takaishi bakin mota tace yashiga amma Farid yak'i RAINA tace
“Farid karka tafito kabarni ka tausayawa abunda ke cikina ” dawowa yayi hajiya ta dak'atar dashi tace
“Muddin ka koma wajenta saidai kazaba koh ni koh ita ko kuma in tsine maka kabi duniya” ai Farid cik yatsaya Raina kuwa toshe baki tayi saboda kada kukan yafit.
[4/17, 10:16 PM] Melody🎤🎤: *111-115* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻


©
_*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_



BABI NA ASHIRIN DA UKU







Tsaye yake tace
“Ga takadda inaso ka saketa saki uku babu kome” Raina tak'ara sakin wani kukan Farid kam shima kuka yakeyi kamar Ransa zai fita Hajiya tak'ara cewa
“gashi rubuta”
“Hajiya saidai Kiyi hak'uri gaskiya bazan iya sakinta Matata ba saboda addini baice hakaba, Malamai da dama sunce inhar matarka tana cutarda Mahafiyarka kuma tace ka saketa toh ya halasta ka saketa saki daya idan babu cuta kabata hakuri cewa bazaka saki matarka ba, in tsinema tace zatayi toh tabbas tsinuwanta bazai taba tasiri akanka ba muddin kana kyautata mata don haka Kiyi hakuri Hajiya kibarni da Raina, bazan iya sakinta ba itace jigon rayuwata kidubi girman abunda ke cikinta Hajiya” ya marairaice
“Farid muddin baka saki waccan k'arfar ba toh saidai kazaba koni koh ita kana iya sauya mata amma uwa bazaka sauyaba”
Jin haka yasa Raina tace
“Farid kabi umurnin mahaifiyarka kabita amma kasani wannan cikin inhar yazo duniya karka kirashi da danka don bazaka sake ganina ba bare har kaga danka ke kuma uwar banza kinyi abunda kike buri kinji dadi inhar wannan cikin shegene Allah yana gani inkuma Farid danki shine ubansa toh insha Allah bazaki taba ganin jika daga wajen Farid ba”ta fadi hakanne badon batason mijinta ba ah ah saidon Mahaifiyarsa taga ishara Allah baya Goyon zalunci.

Juyawa Raina tayi har takusa shiga gida ta juyo tace
“Bani takadda ta” hannu ta mik'a Farid yabata saki daya yana kuka “Allah yagani inason matata da dana Amma hajiya kin tauyemun hakkina yanzu idan Allah ya amshi Aduar Raina kina ganin duniya ban muzanta ba?”Raina ta juyo wajen Hajiya tace “Ayyiiiiriiiiiii Jama'a gobe kuje Kaduna isa kaita road koh kafur ana auren Farid da uwarsa hajiya tasallah hajiya saiki zuba ruwa akasa kisha inaso ki aurawa Farid mace mai gindin gwal wacce tafini gata da iko harma da mulki, Uwar banza kisani kin Haifa kuma duk abunda kaiwa Dan wani toh wallahi rubutacce ne sai anyima” tsaki taja Wanda saida ni humairah na tsorata don yakai kusan second talatin haka hajiya ta turashi cikin motan sannan tace
“Ai farid koh mai gindin azurfa yace zai samu me akeda Kaska mai bak'ar kafa irinki andaiji kunya dakeda uwarki yan iska” hajiya yasa kai suka wuce suka bar *RAINA* cikin damuwa amma yata iya da Ikon Allah, cikin wata guda Raina ta haihu yara biyu mace da namiji Wato yan'biyu acikin gidan Ummin Abrar data rik'eta bisa yarda da amana itace cinta Shanta har mijinta yasan da zamanta don haka tana haihuwa tacewa Ummin Abrar
“Nagode k'warai da kulawarku keda mijinki saidai wani hanxari ba gudu ba nabaki yarannan bisa amana karki taba cewa nice uwarsu saboda zamana yak'are a cikin Kaduna zan koma Dinya wajen Goggo Kiyi hak'uri nabaki aiki amma ke kadai kika chanchanci wannan kyautar”
Abban Abrar yayi murna saboda yana k'aunar yan'biyu haka suka bata kud'ad'e suka kaita tasha ta tafi badan batason yaranta ba ah ah tabarsu wajen dazasu samu gatane Sanadiyyan yan'biyu Komai ya daidaita gidan Ummin Abrar, sunan yan biyun FA'IZ DA FA'IZA son kowa kin Wanda yarasa kyawawa ajin karshe duk inda suka kutsa sai an tanka haka aka dage dayimusu adu'a.

*DINYA*
Goggo na zaune tana karta itada tsaffi a zaure k'watsam Raina tagani tsaye tace
“Goggo barka da hutawa” Sannan ta wuce jiki ba k'wari ai tuni karta ta watse Goggo tafada gida tana mamakin yadda Raina takoma kamar wacce ta haihu zama tayi dirshan tace
“Ke lafya na ganki kamar daga sama lafya dai koh” Raina ta fashe da kuka tasa kanta a kafan Goggo tana kuka ta labarta mata komai duk abunda yafaru har cikin data haifa, Goggo tace
“lallai nema tace wani Abu karki damu yanzu bari afara wankan jego ki murmure kiyi fes acigaba daga inda aka tsaya” Goggo wai yaushe zata natsu tasan me duniya take cikine tambayan danake yiwa kaina kenan batada wani buri saina lalata rayuwar RAINA wacce batasan me ake cikiba tun zuwanta duniya,
Akwana a tashi wajen Allah ba wuya Raina ba karamin kyau tayiba a shekarunta Wanda basu wuce Ashirin da shida ba, amma wani ya rantse yace tsakiyan sha shida take tuni ta juya kambunta ta koma ruwa tsudum kamar yadda tasaba fita tadawo haka ta iske anyi chinchi rindo a kofar gida da isowarta mutane sukace gata ga mamaki naga ansa mata handcuffs a hannu motoci sai jiniya sukeyi abunda ya daure mata kai ganin Goggo dabatayiba, haka suka isa police station saida akasata a bayan kanta kannan ake sanar da ita abunda yafaru, ASP yana zuwa yaga Raina sai yaji tabashi tausayi k'warai tuni yace a fito da ita suka shiga office yayi mata nasiha har yace yana sonta amma bafa so irinna holewa ba don a rayuwarsa karuwa bata bashi shaawa asali ya tsani karuwa Amma a zaton Raina sone na hakik'a haka Kullun saita kirashi bayan ya sallameta wata rana ne taje office dinshi ta matsa kusa dashi tayi hugging dinsa lokaci guda yaji ransa yayi mugun bace ai jikake Tas tas mari takota ina Raina tuni tashiga rudu matsananci yace
“Kina tunanin inada lokacin yar iska irinki wacce batada kima bare daraja a idon mutane kina tunanin sonda nake miki na so ne? Me zanyi da karuwa irinki kisani koh mata sun kare bazaki taba zama uwar yayana ba tunda anasha a nono, this is the First and the last koh ahanya karki kalleni bare kice kinsanni get out of my office” karuwa kenan Mara kamun kai rayuwarta daman ta gaji rashin mutunci daga kowa babu Wanda yake ragamata saurayi yadaka kuma gobe yazo yace saurayi nake tabudemai kafa, tazama bola kowa ya zuba kazantarsa aciki Allah kasa mudace Amin.
[4/17, 10:58 PM] Melody🎤🎤: *116-120* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻


©
_*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_



BABI NA ASHIRIN DA HUDU




Haka rayuwarsu Raina da Goggo yaci gaba saboda tsabar iskancin Raina gari gari take zuwa bata Abuja bata Port Harcourt bata Tafa wata ranan asabar ne aka tashi da fada acikin gidan da Goggo take inda aka samu wata mai suna BELA ta zage Raina tas tayi mata wankin katon bargo sannan tayi mata gorin dangi hardana yan'uwa
RAINA bayau aka asaba yi mata gori ba hakan yazame mata tamkar Riga yar shara haka tashiga daki ta tasa Goggo dole ta sanar da ita inda danginta suke kodan tanunawa duniya ta wuce gori kuka take babu kakkautawa, Goggo ce zaune shurum takasa cewa k'ala bare tayi motsi mai karfi jiki ba k'wari tace
“Raina kinaso kisan asalinki?”
Raina tace
“kwarai Goggo maizai hana Ido rufema kuwa” Goggo ta yunk'ura tace
“Jeki bayan layi siyo mana k'osai idan mukaci muka gama sai in sanar dake inda yan uwanki suke batareda bata lokaci ba” haka *RAINA* ta mike badon ranta nasoba ta fice ai koh second sittin batayiba Goggo ta mik'e ta k'ulle kayanta ta k'washi yan kudi a lalitan RAINA kafa mainaci ban bakiba Goggo nafita ta tare Dan achaba tace yakaita cikin gari Dawowar Raina keda wuya ta kutsa daki da mamaki ba Goggo babu labarinta saida ta zauna tsawon minti Goma a tunaninta kewaye tashiga amma shuru kakeji Malam yaci shirwa.

RAINA ce tafito a hargitse tacema wata K'aruwar Gidan
“Dan Allah koh kinga Inda Goggo tayi?”
Budar bakinta tace
“Tafita da kullin kaya akai batayiwa kowa magana ba illah wuce mu datayi” RAINA tayi ihu ta tuma a kasa tace
“Waiyo nashiga uku ni Raina Goggo Dan Allah karki tafi kibarni ina zan dosa kiyimun rai Goggo kece gatana kece abun alfaharina yanzu idan kika tafi Zargin Mutane ya tabbata akaina duniya banida wani gata kashe kaina zanyi in huta Waiyo kaico duniya Ni Raina naga takaina” kuka mai tada hankali Wanda saida wasu suka tausaya mata
Tana cikin burari ne wayarta tafara k'ara cikin hanzari ta dauka ganin lambar Goggo tace
“Hello Goggo Dan Allah kidawo” harda dariyarta amma saitaji namiji ne yake magana Murna saita koma ciki.
“Baiwar Allah idan da namiji kuzo bakin kasuwar soba anyi hatsari kuma matar RAINA kawai take kira” karaf aka kashe RAINA ta hauk'ace kuka takeyi mara sauti da gudu ta fice gudu kawai takeyi tana zuwa taga Goggo k'wance acikin jini wani ihu tafasa ta mance da salati bare yadda akeyi.

“Goggo Dan Allah karki mutu idan kika mutu inazansa rayuwana Goggo kar kice yadda nazo duniya haka zan koma Goggo ke kadai nasani a duniya idan kika rasu inazan dosa Karyata tak'are Goggo ki tashi Dan Allah” jijjiga Goggo takeyi amma batasan halinda take cikiba zuwan Roads safety ne yasa akasa Goggo a mota sannan ga police da mamaki Raina tana daga ido tayi arba da ASP Ahmad Yari tuni taji sonsa ya karu cikin zuciyanta har suka isa Asibiti RAINA takasa daina Kallonsa saboda shak'uwar dake tsakanin zuciyarta da Asp, haka aka shiga da ita Emergency room inda likitoci sukayi cha akanta anata iyakar kok'ari haka Raina ke leken Yadda Goggo ke burari waiyo kawai takecewa babu alaman Rahma a tattare da jikinta bare sauki Babu Adu'a bare salati saboda mugun abunta daman karshen azzalumi kenan mutuwar Fuji'a mutuwar gaggawa Asiri Goggo, Zina Goggo, makirci Goggo, zalunci Goggo abun yayi mata yawa wai shege da hauka, Itadai RAINA fatanta Goggo tasamu sauki donta sanar da ita tushenta koh kuma Asalinta........

Bayan wasu awowine Goggo ta Umurci dason ganin RAINA haka ASP yakirata tafe take hawaye na k'waranya acikin gurbin idanunta tana zuwa ta rungume Goggo tace
“Allah yabaki lafya Goggo kece abar Kallo inji dadii karki mutu kinji”
Dariya Goggo tayi Wanda bata taba irin taba tace cikin Murya k'asa k'asa
“Raina mutuwa tazama dole Kuma nan bada jimawaba zan bakunci inda kowa saiyaje kiyafemun Saboda nayi miki laifi wanda girmansa yana iya wuce dutsen Mambilan”
Tuni Asp *Ahmad yari* yadauko Biro da takadda saboda ya dauki Statement din Goggo
Taci gaba dacewa
“RAINA ke yar Gata ce gaba da baya Duk wani kaskanci Nina jawo miki dana rabaki da iyayenki alokacin dasuke matuk'ar bukatanki Sunanan na Asali Binta kuma ni kuyanga ce acikin masarautar mahaifinki Wato *Sarki MAMUDA* Saboda tsabar makircina Yasa na saceki adaidai lokacin da Mahaifiyarki Maimuna ta haifeki Mahaifinki yafi kowa bakinciki Haka naji labari har ciwon hawan jini gareshi itako mahaifiyarki saboda kuka idanunta basu buduwa sun shiga matsanancin rayuwa wanda nake fata ki rokanmun su Alfarma su yafemun”
Raina da ASP dama likitoci sunyi masifar razana kallon Raina kawai sukeyi saboda ga kamanan wacce bata boyuwa Goggo taci gaba da labari...................
[4/18, 9:16 PM] Melody🎤🎤: *121-126* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻


©
_*STORY & WRITTEN BY*
*HUMAIRAH (Melody)_*



BABI NA ASHIRIN DA BIYAR



“Maryam itace tasa na saceki saboda nata Manufar, tabbas idan tabarki a cikin gidan Danta *DANISH* bazai samu wata kulawa ba saboda sarki MAMUDA bashida wani buri Wanda ya wuce ganin k'wansa a duniya Shiyasa muka kulla wannan makircin muka musanyaki da matacciya na gudu dake akan kudi kalilan Wanda basu amfaneni da komai ba, shiyasa nakasa baki tarbiya mai kyau saboda banaso kizama abun alfahari a duniya, tarine ya sarke Goggo Wanda saida tayi wani amai harda jini, ASP yace
“Ko zaki iya sanar damu inda zamu samu gidan Sarki MAMUDA?”
Goggo da kyar take magana tace “Yana cikin garin Kaduna dazama a k'aramar hukumar Kajuru..........

Tana gama magana tayi shak'uwa har sau uku daganan tasaki wani razanannen kara ai sai kuma akaji shuru, RAINA wani irin kara tayi ta rungume Goggo tana kuka tana “Goggo maiyasa zaki mutu kibarni? Dan Allah ki tashi” ikon Allah kenan kudubi girman laifinda Goggo tayiwa RAINA amma soyayyar Goggo yana cikin ranta harda zuciya nasan duk Kukan da Raina takeyi na tsantsar shakuwane, haka aka lullube Goggo cikin Zanen Asibiti, tuni yan sanda suka nufi Kaduna tun safe sai dare suka dawo saboda tsabar nisa jiniya kawai nakeji abun mamaki ina lekawa cikin harabar Asibiti motoci nagani convoy bak'ak'e wani mutumi nagani black beauty yana tafe cikeda kasaita cikin Alkyabba.

Ana takamai baya suna shiga Dakin da Goggo keciki sukayi tozali da RAINA jiyayi gabansa yayi mugun fadi kallon kallo kawai sukeyi kujera aka sa masa ya zauna RAINA koh takasa kuka takasa dariya saboda tsabar farinciki, Danish ne tsaye yana kallon raina jiyake ya tsaneta saboda tundaga kallon fuskarta yaga dukta kone saboda tsabar bilicin, Kirari kawai ake yiwa Sarki MAMUDA haka likita ya budema sarki fuskan Goggo yana gani yace
“Ai wannan binta ce” tuni ya Umurci RAINA data matso kusa dashi haka yadafa kanta yacema likitoci ayi gaggawan yimata sutura don su daganan Kaduna sukayi komin dare, haka aka yiwa Goggo sutura Harda ASP a wucewa kajuru kafin isarsu gida yacika yayi makil sai sarewa akeyi da kalangu abinchi kuwa kala kala saboda tarban Gimbiya RAINA, basu isa garin kajuru ba sai misalin Asuba amma gidan yadda kukasan rana, Haka raina tafito harabar tank'a sheshen gidansu acikin ranta cewa tayi yanzu Ashe nimai gatace amma aka shiga dani duniya na wulakanta? Kaico duniya Allah Kaine gatana, kuyangune sukazo suka wuce da Gimbiya RAINA zuwa bangarenta da tunkafin zuwanta duniya aka killa ceshi.

Ciki Raina ta kutsa kai tashiga Tunda take bata taba katari da kayataccen daki irin wannan ba kalle kalle kawai takeyi wata daga cikin kuyangin tace
“Ranki yadade wannan shine dakinki mune masuyi miki hidima duk abunda kikeda buk'ata muzamuyi miki , suna cikin magana akayi sallama jakadiya ce tsaye daukeda wasu kaya masu kyalli da shek'i
“Gimbiya ranki yadade Allah yaja kwana Wayannan kayane saga sarauniya Maimunatu mahaifiyarki tace ki sanya idan kin kammala wanka”
kuyangin ne suka amsa suka ajiye tuni aka hada mata ruwa mai tsafta turaruka kuwa sunkai kala goma da'aka acikin bath din ciki tashiga tayi minti Talatin tana wanka ita kanta tasan tayi wankan dabata taba bata lokacinta wajen yiba, fitowa tayi tuni kuyangin suka dau towel suna tsane mata jiki zama tayi tana shafa mai masu kamshi sannan ta shirya cikin kayanda aka kawo mata har bayan Sallah Asuba hidima akeyi gari na wayewa fada tacika makil da Al'umma haka aka kawo RAINA tafe take jitake kanta yakara girma, Jitayi tabbas SARAUTA tafi mulki kuma SARAUTA ajini take baa kudi koh dukiya ba, haka akayi Adu'a akayiwa Gimbiya barka sa dawowa daular mai martaba sarkin Kajuru.
[4/19, 8:31 AM] Melody🎤🎤: *126-130* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻


©
_*STORY & WRITTEN BYHUMAIRAH (Melody)*_




BABI NA ASHIRIN DA SHIDA

*DEDICATED TO YOU MY VERY OWN LOVE YOU ALOT😍😍 MISS XOXO THANK FOR FOLLOWING MY NOVEL BIT BY BIT😍❤👏🏻 LYSM😘*






Bayan kowa ya watse ne aka gabatar da RAINA ga dan'uwanta Wato DANISH Wanda gaba daya yaji ya tsaneta tunda yaji ance Karuwa ce, bayan RAINA ta koma shahenta ne aka aiko jakadiya cewa ASP zai wuce in tanada abuncewa, cikin Zumudi tace kwarai tanada bukatan magana dashi tunda Maimartaba yace Idan tsnada Wanda wakeso tafito dashi itakuma duniya ASP Ahmad yari take muradi dukda cin mutuncin da yayi mata Haka aka rakata kofar dazai sadata da Lambun da Asp yake da isarta tayi wani kasaitaccen murmushi tace
“Ranka yadade banida abun cewa sai godiya kayimun karamci Wanda babu wani mahaluki a zamaninnan dazaiyimun irinsa inada magana mai muhimmanci danakeso muyi kasan ance zuciya kabata abunda takeso duk girman abun Asp bantaba ganin namijin daya kwantamun arai irin kaba inasonka ina kwanarka ka ceci rayuwana banida burin daya wuce in aureka kazama uban yayana”.

Tsawa ya dakama raina yace
“Dakata malama dakata hakanan Karki yaudari kanki don bantaba jin sonki acikin raina ba kamar yadda na sanar dake a baya babu abunda zanyi da karuwa irinki mara mutunci karkiyi tunanin mahaifinki Sarki ne toh kisani uwa tagari nakeso insama ma yarana wacce babu wani aibu acikin rayuwanta koh nakasu wacce duniya yake kallonta a matsayin mutuniyar Arziki, bani ba auren karuwa irinki kaskantacciya maxa nawa sukayi amfani dake suka zubda Wato gani Mara wayau koh toh kinyi a banza sonki nakeyi a matsayin kanwata amma baa masoyiyaba”
Hawaye ne kawai ke zuba daga gurbin idanunta, ranta yayi bala'in baci da munanan kalamansa tace
“Asp wannan shine karo na karshe daxaka gayamun munanan maganganu meka maida karuwa? Waya gaya maka karuwa bata auruwa? Meye aibun karuwa Idan tace ta tuba? Amma inaso kasani ba laifina bane amma kuma babu komai kaje duniyace ta ishi kowa karka chire rai dasamun Irina acikin zuri'arka sai inga wanda zai auri taka y'ar mtwwwww Guards” sai gasu cikin hanzari tace
“sonake ku fitarmun da wannan Mara mutuncin kuma aka nakeso ku daukeshi” haka kartin suka daukeshi sai waje gurshekin kuka kawai raina keyi “tabbas Goggo kinyimun Illah kin wulakantamun rayuwa tsakanina dake Allah saiya isarmun kin shegantani da iyayena kaico duniya inazanga Farid shine silar farincikina a duniya bayaga iyayena a yanzu”.

Ciki ta wuce rikeda doguwar rigarta mai bayan dawisu dakinta tashiga tayiwa kuyanginta izini dasu fita tanaso ta kadaice cikin yini daya ta fige koh abinchi takasaci, tun zuwanta gidan sau daya ta sa mahaifiyarta a ido abunda ke damunta kenan,
★★★★
BAYAN WATA DAYA
Maimartaba Yakira Danish yasanar dashi buk'atan sa na auren RAINA hankalin danish yayi kololuwar tashi saboda babu macen daya tsana irin RAINA kuma,
“Mai martaba inaso abani lokaci inyi tunani ”
“Babu wani tunani umurni nabaka ba shawaranka nake nemaba koh tunani ba kashirya nanda sati biyu”yana gama magana yamik'e danish saida yayi kuka Wanda nikadai nagani sai kunkuni yakeyi
“maxanyi da karuwa wacce gaba daya rayuwanta ta hulakance”.

Yini yayi yana tunani yadda zai bijirewa umurnin Mai martaba amma yakasa ni HUMAIRAH nace dole ka aureta saboda uwarka itace silar lalacewar rayuwan RAINA, kwanci tashi cikin kankanin lokaci RAINA ta kilance tayi kyau amma ta kudiri aniyar Yau saita nemi hanyar zuwa wajen mahaifiyarta tanemi afuwanta don taga kaman fishi takeda ita saboda takasance karuwa Mara galihu ada,
Zuhra itace ta rakata har kofar Dakin mahaifiyarta kutsa kai tayi tashiga cikeda fargaba kuyangin sasan sai gaisheta sukeyi amma bataba kowa amsaba cikin Dakin mahaifiyarta zata shiga aka hanata wai sai an tambayi sarauniya

Please Login or Register in order to submit comment