Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zan iya jurewa ba a wannan karon"


Mummy ta ce "Malam, ka san yarinyar, wadda ka taɓa yi mini aiki a kanta ce shekarun baya, kawai ka yi wani abu a kai"


"To ya aka yi ƙasa ba ta nuna mini ita ce ba? Ban ga taurarinta sun fito a cikin nasa ba, amma duk da haka babu damuwa, ta jiramu a waje, zan bata abun da za ta yi"


Samha ta jinjina masa kai, ta yi godiya, sannan ta tashi ta fita ta bar su Mummy.


Hajiya Lubabatu ta ce "Malam, ya ake ciki ne? Haryanzu galadima yana nan a raye, ga lokaci yana ƙurewa, bana son wani dalili da zai gifta, da Jabir zai gaza mallakar zunzurutun dukiyar nan da sarauta".


"Allah ne mai kashewa da rayawa ba ni ba, dole ki cigaba da jira, ke kuma ya aka yi?" Yayi maganar yana kallon Mummy.


"Malam, kamar aikin da yake tsakanin yaran nan ya fara sanyi, kamar mahamud ya sassauta ƙiyayyar da yake yiwa ɗan uwan, sannan malam yadda yake yinƙurin yin auren nan, a sake damalmala lamarinsa, bana ƙaunar ganin wani cigaba a tare da yaran nan".


Malamin ya ce "Ina iya ɓata aiki ne, ba sauya ƙaddarar bawa ba, zan yi abun da ya dace a kai, ku tafi ta kudu, ku ajiye abun sadaka a mararraba ta uku, sannan shekara ta kusa, za a shayar da ƴar baƙa ta arewa da jini, sai dai ta daina samun jinin da take sha, dan haka za ayi mata sadaukarwa da wani abun, na sallameku".


Da haka suka fita, Samha take ce musu bai faɗa mata mai za ta bashi na aiki ba, suka ce kar ta damu, suka yi abun da ya ce sannan suka tafi gida.


***
Abubakar ya dawo, sun kuma tattauna sosai a tsakaninsu, a kan auren rumaisa, suka yanke shawarar a sake jarraba sayar da gonarsu, domin a samu abun yi mata kayan ɗaki.
Ɓangaren rumaisa kuwa, sai koke-koke take a kan ita fa ba ta so, gashi har fargabar kwanciya bacci take yi, saboda munanan mafarkan da take yi, ta je ta samu malaminsu a islamiyya ta ce ya bata Addu'a, tana yawan yin mugun mafarki ya bata shawara da cewa "A duk lokacin da ki ka yi mummunan mafarki, ki nemi tsari sannan kar ki gayawa kowa, ki din ga kwanciya da alwala, sannan ki kwanta da ɓangaren dama, ya zamana kina Adduoi na safe da na maraice, sannan ki karanta na kwanciya barci, idan razana ki ake yi a mafarkin, ki daina tsorata, ba abun da yake samun bawa sai da iznin Ubangiji, kin riga kin yi azkar kin nemi tsari, babu abun da kuma zai cutar da ke".
Rumaisata riƙe maganar malaminsu, ta dage da addu'a da alwala, shine ta ɗan samu rangwame.


Rana bata ƙarya, sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, tun da su ammi suka tafi, sai ana gobe kai kuɗi suka yi waya da mama, ranar juma'a bayan an saukko daga Masallacin juma'a, mai girma turaki da wasu manya a masarautar kano, suka kai kuɗin auren rumaisa gidan ƙanin mahaifinsu, naira dubu ɗari biyar, suka saka wata ɗaya rak.


Ƙanin mahaifin rumaisa ya nemi su ƙara musu lokaci, saboda shirin aure, ba abu ne mai sauƙi ba, amma suka ce basa buƙatar komai, rumaisa kawai suke son a kai musu, dan haka wata ɗaya suka saka.


Ayshercool Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment