Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗan yi shiru sannan ya ce b"Babu laifi, zan shigo in sha Allah, amma a bita a hankali dan Allah, ko a bari na zo tukuna"


Mama ta ce "ai shi ya sa na ce sai ka zo ɗin"


Bayan sallar asuba, Adam ya karɓi wayarsa a hannun Aliyu, ya kira ammi, suka yi magana, ta ji daɗi sosai da jin muryarsa, tayi masa addu'a da fatan alkhairi.
Ya kira Bashir ma suka gaisa, tare da sanar da shi, ya je ya taho da Ammi.


Kiran jabir ne yake ta shigowa tun bayan da ya kunna wayar, kamar ya share sai kuma ya ɗaga.


"Wai ina ka shiga haka baka ɗaga wayata? Ya ake ciki ne akwai wani labari ne? Ko ka koma wurin yarinyar?"


"A'a ban koma ba, zan koma bacci yanzu zan zo gida in sameka anjima" bai ko tsaya saurarar mai jabir zai ce ba, ya kashe wayar ya ajiye, haryanzu ya kasa gazgata maganganun rumaisa, wai Aisha ta mutu, ganin abun yake kamar almara, sai yanzu ya gane ka rasa mutum ka ga gawarsa wata ni'ima ce, ba irin tunanin da bai zo masa a kan gawar Aisha ba.


Abun mamaki yau ruma taƙi komawa bacci, mama har tambayar ta ta yi ba zata koma bacci ba, ta ce ba ta ji.


Ta dubi in da mama ta haɗa kayansu ta ce "Mama wai tafiya zamu yi ne an sallame ni?".


"Eh, in anjima za a sallame mu"


"Yeeee dama na gaji da zaman asibitin nan wallahi, yau sai gida, ga kayana ga na babyna nima na samu mai sunan babana, sai dai Allah ya sa kar yayi halin mai sunan kakanmu" tayi maganar da sigar tsokanar mama, amma mama ba ta tanka mata ba.


Har gari ya waye ruma idonta biyu, ta damu mama a kan ta bata sabir, amma mama ta hanata.


Wajen ƙarfe tara, Usman da mai sunan baba suka zo, ruma tana ta murna zata tafi gida, dan zumuɗi ta ce abincin ma sai ta je gida zata ci.


Usman ya din ga kwasar kayansu yana fitarwa, sai murna take yi yau ba kwanan asibiti, dan takardar sallama kawai suke jira daga likita.


Bashir ne ya shigo ɗakin rumaisa, ya kalleta yayi murmushi ya ce "Yau sai gida uwar rikici"


Ta yi murmushi ta ce "Ɗan uwanmu, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi, jin godiyar nake ma ta yi kaɗan a baki, amma zan din ga yi maka Addu'a idan na yi salla"..


Yayi murmushi ya ce "Kai masha Allah, amma na gode ƙwarai da gaske, sister na asiya ma tana gaishe ki, ita ma ba ta da lafiya ne. Amma kin je kin duba baban sabir kuwa?"


Ta ɗan yi turus tana kallon mama, mama ta ce 'Yanzu zan sakata a gaba mu je ta duba shi, sai mu tafi".


Bashir ya ce "Yauwwa mama, dama ga ammi can ma ta zo sai ku yi sallama, ai bai kamata ku tafi babu sallama ba".


"To ai yaya Aliyu ya ce bai mutu ba, har ya tashi"


"Haba rumaisa, idan da kara yakamata ki je ki duba shi, ko dan albarkacin sabir ɗinki".


Usman ya ce "Sai ka lallaɓata ma, wuce mu je, kuma saura mu je ki yi rashin kan gadon naki, ya saka dogarai su saita miki zama".


Suka ɗunguma zuwa ɗakin da takawa yake, suka tarar ammi na zaune a kusa da shi, ta riƙe hannunsa, tana share masa hawaye.


Ammi na ganinsu tayi murmushi ta ce "Kun fito? Yau ban ƙaraso mun gaisa ba rumaisa, hankalina ne a tashe"


Ruma ta durƙusa ta gaisheta, ta amsa mata cikin girmamawa.


Usman ya ce "Ki yi masa sannu mana"ta dubi Adam za ta yi masa magana, amma gabanta ya faɗi, ganin gaba ɗaya idonsa ya koma baƙi, yana fitar da hayaƙi.


Mannewa ta yi bayan usman, tana leƙo shi, taga ita yake kallo, amma idonsa yana ta hayaƙi, kallonsu take yi, tana jiran ta ji wani yayi magana a kan idon takawa, amma ta ji babu wanda yayi magana da alama su ba sa gani.


"Ba zaki yi masa sannun ba?"


Ta sunkuyar da kanta ƙasa ta ɗan zuro kai ta ce "Sannu, Allah ya bada lada" tayi maganar a rikice dan a razane take, bata taɓa ganin idon mutum a haka ba.


Bashir ya ce "Ladan me kuma rumaisa, shi da ba shi da lafiya?".


"Au ba lada ba, Allah ya warkar da shi"


Usman ya ce "Yau kuma meke damunki ne?"


Mama ce ta kwance Sabir daga bayanta, mai sunan baba ya karɓe shi, ya ƙarasa gaban gadon Adam ya ce "Allah ya ƙara lafiya, ya jiƙan mamansa, kamar yadda ka buƙata ga yaronka, Allah ya raya shi, Allah ya biyaka ɗawainiyar da ka yi da ƙanwarmu". Adam ya karɓi Sabir, yana ƙoƙarin mayar da hawayen idonsa.


A rikice ruma ta ce "Ban gane ga ɗan sa nan ba, da shi zan tafi ai, ni anty aisha ta bar wa shi" tayi maganar tana nufar Adam, amma mai sunan baba ya tare ta ya ce "Juya mu tafi" karo na farko da ta tsaya ta saka idonta a nasa ta ce "To ka karɓo mini ɗana".


"Ni nake magana ki ke mayar mini?".


"Haba mai sunan baba, ya za ayi a ƙwace mini yarona, dama abun da aka shirya kenan? Mama ki saka baki" ta dubi Ammi ta ce "Dan Allah ku bani yarona, na sha wahala kan mu tsira tare, idan aka ƙwace mini shi, mutuwa zan yi, wallahi ina son sa sosai, ɗan uwanmu yaya bashir, dan Allah ka karɓo mini ɗana"
Gaba ɗaya sai tausayin rumaisa ya kama su. Ammi ta ce "Kina ji ruma, ki kwantar da hankalinki, babu mai rabaki da yaronki, zamu je a kai shi cikin dangi ne, kuma in sha Allah za a din ga kawo miki shi ki ganshi".


Rumaisa ta fashe da kuka ta ce "Da na san haka ne, gara na zauna mu mutu a dajin, da da wannan mutumin ya ce in tafi ba zan tafi ba, gara a harbeni, kwanana biyu ba ma bacci ni da sabir, saboda sanyi yana kuka, kwanana uku ina bulayin hanyar da zamu dawo, kuma a ƙwace mini shi bayan mun sha da ƙyar, ba anty aisha ba sabir ɗina. Dan an ga ni yarinya ce za a ƙwace mini ɗa" Mai saunan baba ya danƙi hannunta zai yi waje da ita, tana kuka tana miƙa hannu tana "Dan Allah ku bani sabir ɗina" tun da ruma ta fara kukan nan tana zuba, ko ɗaga kai Adam bai yi ba ya sunkuyar da kansa ƙasa.


Kuka sosai rumaisa take yi, tamkar an ce mata mama ta mutu, bashir ya rakosu yana ƙoƙarin rarrashinta, amma mai sunan baba ya ce ya rabu da ita, ya buɗe mota ya sakata, amma sai miƙa hannu take taka kuka.


"Ki rufewa mutane baki, idan an baki ɗan ya zaki yi da shi, ke wace irin yarinya ce da ba a isa a gaya miki, ko ki rufe mini baki, ko na casaki a wurin nan" mai sunan baba yayi mata wata irin tsawa mai razanarwa.


A gigice ta ƙanƙame mama tana ƙoƙarin haɗiye kukanta, amma ta kusa ƙwarewa saboda kuka, ga hawaye ga majina har da yawu, saboda kuka.


Ammi na tsaye tana hango rumaisa yadda ake fama da ita, wani irin tausayinta ya kamata. Allah kenan ya karɓi uwar yaron, kuma ya sanya soyayyarsa mai tsanani a wata zuciyar.


A hankali ta juya ta koma ɗakin da adam yake, yana rungume da jaririnsa.


Ammi ya dube shi ta ce "To me ka yanke? A ganina mu bari nan da ko kwanaki biyu ne ka gama warwarewa".


Adam ya girgiza kai ya ce "Ammi, ba zan taɓa warkewa ba, barin lamarin ina sake jinkirta loka8, abubuwa caɓewa za su cigaba da yi, daga nan gidan turaki zan wuce, zan je na sanar masa da laifina gaba ɗaya duk hukuncin da ya yanke a kaina shikenan".


Cikin damuwa Ammi ta ce "Kana ganin hakan shine mafita?".


"Ammi dole ita kaɗai ce mafita, na yi zaton aisha tana raye ne dama, shi ya sanya nake ta jinkirtawa, amma na yadda ta rasu yanzu, yanzu zan fara fuskantar mai girma turaki, daga baya kuma sai na fuskance ƙalubale na gaba".


Ammi ta ɗan yi shiru yana kallon ƙasa, daga bisani ta yi ajiyar zuciya ta ce "Shin, Ubangiji Allah ya yi mana jagora baki ɗaya "


Ya amsa da amin.
Bashir suka shigo tare da likita, likitan ya dubi adam da yake rungume da jariri ya ce "Allah sarki rumaisa, gaskiya ta shaƙu da yaron nan, ba ka kyauya ba da ka ƙwace mata ɗa" Adam ya sunkuyar da kai ba tare da ya iya yin magana ba.


"To Yanzu me yake damunka, zan rubuta maka teses na yi reviewing file ɗin ka, na ga vitals ɗin ka duk normal".


"Sallama nake so" ya faɗa a taƙaice.


"Meyasa zamu sallameka? Dole mu riƙe ka zuwa gobe in Allah ya kaimu mu ga abun da hali zai yi".


"Ba zaku hana Allah zartar da hukuncin sa ba, ku yi haƙuri tafiya zan yi " duk yadda likitan nan ya so lallaɓa adam ya ɗa zauna, amma yaƙi ammi ta ce ya basu sallama kawai, suna da issue a gida.


Haka kan likitan ya rubutawa adam sallama, da yayi tunanin ya kira jabir su tafi tare, sai ya ga babu wani amfani ma da jabir ɗin zai yi masa a halin yanzu, dan haka kawai ya share suka tafi.


Suna tafe a mota, yana kalon sabir da yake ta ƙamshin turare, yana wasa da hannunsa, har da farar hoda da kwalli mama ta shafa masa, ba ayi masa aski ba, dan haka suma ta cika masa kai, ga ta a cike baƙa siɗik, har ta ƙasan hularsa ta fito, ga gashin girarsa a hankali yana tofowa.
Ƙasan zuciyar Adam yana ta fargaba da tunanin, yadda zai fuskanci turaki.


Har gidan turaki bashir ya kai su, sai dai shi ya tsaya a mota, su kuma suka shiga.


Da fari ta ƙofar turakar turaki ta harabar gidan, Adam ya shawarci Ammi su shiga, amma sai suka tarar da ita a rufe, dan haka dole suka bi ta cikin gida.


Falon ba kowa sai hadimai, suna ganin Ammi tare da Adam, cikin rawar jiki suka gaishe su, aka tafi nema musu iso wurin matar gidan.


Ba su jima a zaune ba sai ga mama ta fito cikin taƙama, ta dubi Ammi ta yi murmushi ta ce "Giwa, yau ke ce a gidan namu?"


Ammi ta ce "Ni ce, kin san ɗaurowa take a ɗaure alƙali, ya gida ya iyali?"


"Alhamdilillah, takawa magajin takawa, dan kujerar galadima ta yi maka ƙanƙanta babbar kujera muke fata" tayi maganar tana kallon jaririn hannun Adam.


Ta sake cewa "Ina ku ka samo ɗa?"


Adam ya ce "Dan Allah idan babu damuwa, muna neman iso wurin mai girma turaki idan yana nan"


Ta ɗan jinjina kai ta ce "Yana nan, bari ayi masa magana".


Ƙanwar Samha ce ta fito sumayya, ta gaida Ammi tare da takawa, ammi tambayeta ina samha, ta ce mata ta je abuja.


Mama ta fito ta ce "Bisimillah, ku shigo"


Ammi ta tashi, tana gaba adam na bin ta a baya, suka shiga falon turaki.


Yana zaune a falonsa, gefensa ga Alqur'ani a ajiye, da alama karatu ya idar.


Ya kallesu yayi murmushi ya ce "Maraba da manyan baƙi".


Ammi ta risuna ta ce "Barkanmu da wannan lokaci"


"Barka dai, ya iyali ya kuma rayuwa"


Ammi ta amsa da Alhamdilillah, maimakon mama ta fita ta bar ɗakin, sai ta nemi wuri ta zauna.


Turaki ya kalli Adam ya ce "Takawarka lafiya, ana lafiya?"
Adam ya jinjina kai kawai, amma bai yi magana ba.


Ammi ta gyara zaman ta ta ce "Allah ya baka nasara, wata muhimmiyar magana ce ke tafe da mu, amma kan in ce komai, zan fara da neman afuwa sannan a sassauta mana hukunci"


"Babu laifi, ku muke sauraro".


Adam ya tashi a hankali, ya tafi gaban turaki ya durƙusa, ya ɗora masa Mahmud a kan cinyarsa".


Turaki ya rungumi sabir ya ce "Masha Allah, ina na samu ɗa, ɗan kyakykyawa Masha Allah?".


"Ɗan wurin aisha ne" takawa ya faɗa jiki a sanyaye.


Turaki ya faɗaɗa fara'arsa ya ce "Ikon Allah, uwata yaushe ta haihu?, yaushe rabona da ita?"


"Allah ya baka yawan rai, haƙiƙa ni mai laifi ne, kuma a shirye nake da karɓar hukuncin da duk ka zartar a kaina. Wannan jaririn ɗan wurin aisha ne matata, kamar yadda aka kai ruwa rana da surutu a kan karatu da nace zata tafi. Duk ba wannan ba ma, maganar da nake maka, yanzu haka fulani ba ta duniya, ya rasu" Adam yayi maganar kansa a ƙasa hawaye na gangaro masa.




Ayshercool.


paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, masu buƙatar vip ko special kuma, suna iya garzayawa arewabooks ku searching sunan littafin*








Haka suka cigaba da ƙulla mugunta kala-kala suna dariya.


Wunin yau Samha ba ta bi ta kan wayoyinta ba, sai yanzu ta nutsu, ta ɗau wayoyinta ta kunna, ta ajiye su a kan gado, ta shiga wanka. Daga shigarta wanka zuwa fitowar ta missed calls sun fi goma sha.


Mamaki ne ya kamata, tana shirin duba missed calls ɗin, kiran Fauziyya ya shigo wayarta. Ɗan ɓata fuska ta yi ta ce "Wai lafiya ake yi mini wannan kiran kamar mara gaskiya?".


Fauziyya ta ce "Ke dalla can, idan ma wani rabon ne har ya wuce ki baki ɗaga waya ba, kawai kin wani kashe wayoyi".


"Ke karki ɗaga mini hankali, hutu na zo yi dan me za a dameni? Ina jin ki"


Fauziyya ta ce "To, ai ni zancen ne ma ban san ta ina zan yi miki shi ba, abun farinciki zan ce miki, ko kuma tashin hankali da jimami, ko kuma abun ɗaure kai?"


Samha ta ɗan juya idonta ta ce "Fauzi, zan kashe wayata fa".


"Katangar da ta daɗe da tsaye miki, ta hanaki cikar burinki ta rushe".


"Kamar yaya kenan?".


"Ƙanwarki ce ta mutu"


Miƙewa Samha ta yi, ji ta yi kamar ba ta ji dai-dai ba, wai ƙanwarta ta mutu.


"Ƙanwata wacce? Wace ƙanwar tawa?"


"Ahh, wacece ta sha gabanki ta hana cikar burinki na auren yayanmu, aisha ɗazu aka ce wai ta rasu a wurin haihuwa, a garin da ta je karatu, amma an dawo da jaririnta, amma dai kamar akwai wani abu da ake ɓoyewa ba a son a sani".


Wata iska samha ta fesar ta ce "I hope ba ƙarya ki ke yi mini ba?".


Samha ta ce "Ana ƙarya da mutuwa ne? Ki tambayi wanda ba sa yi miki ƙarya sai ki tabattar".


"Am sorry, ba haka nake nufi ba, zan kiraki" ta kashe wayar ta cillata kan gadonta, ta hau sintiri a ɗakin.


To murna za ta yi ko kuwa jimami, wata zuciyar ta ce "Ke ina ki ka gata jimami, damar da ki ka daɗe ki na jira, Allah ya kawota a sama ki tsaya wani jimami? Yanzu hanya ta miƙe miki fetal, aiki kaɗan ya rage miki".


Wayarta ta rarumo, sai dai ta rasa wa za ta kira ma, jefar da wayar ta yi, ta janyo akwatinta ta hau shirya kayanta, ko ba ta samu jirgi ba a mota zata koma gida gobe.


A daren ranar babu wanda ya runtsa a iyalin ammi, mussaman ita, da a kunnenta kishiyarta da facalolinta ke jifanta da miyagun maganganu.


Sabir kuwa tuni mama ta aike da shi gidan wata 'yar garinsu da take aure a kano, matar kamar ƙanwa ce a wurin ammi, dan haka aka kai sabir can, duk surutun da aka din ga yi ba ta faɗi in da sabir yake ba.


Washegari ma haka aka ɗora zaman makokin aisha, samha kuwa tun da sassafe ta taho kano, sai dai ta rasa wani mood yakamata ta shiga, na farinciki ko akasin haka? Duk yadda ta so ta ji lamarin ya ratsata ta kasa, babban fatanta Allah yasa da gaske Aisha ba ta raye.


Sai da ta isa gida ta tarar da tarin mutane, sannan ta tabattar da gaske aisha ta mutu, tun daga waje ta fashe da kukan ƙarya, dan kar a fuskanci wani abu, kai tsaye ta nufi cikin gidan tana kuka kamar gaske.
Nan yan makoki suka din ga rarrahinta suna yi mata nasiha a kan aisha addu'a take buƙata ba wannan kukan da take yi ba.
Abu kamar gaske, Samha ta din ga kuka tana tumami, ana rarrashinta da ƙyar ta yi shiru, ta tafi ɗakin mamanta ta kwanta ta samu bacci.


Sai bayan la'asar sannan Hajiya Asama'u ta shiga ɗakin ta tashi Samha.


Ta dubi Samha ta ce "Ke yanzu Samha dan aishar ta mutu ki ka zauna kina wannan uban kukan kamar ni na muty? Yarinyar da ta hanaku rawar gaban hantsi a wurin mahaifinku, har wani kukan mutuwarta zaki yi?".


Samha ta ɗan duba bayan mama, ta ji babu almar wani zai shigo, sannan ta dubi mama ta ce "Mama na dole ne, ko ba kowa ba wasu san da cewa ina son Adam, idan har na nuna ban damu ba, wasu ma ai sai su ce ina murna da rasuwarta ne, nima na dole ne kukan, amma mama ya aka yi ta mutu wai? Sannan ina ɗan da ta haifa ɗin?"


Mama ta kwaɓe baki ta ce "Mhmm, su suka san me suka yi mata dai, wai can in da ta tafi karatun a can ta zo haihuwa ta rasu, jiya nan suka zo da jaririn, ammma sun ƙi fito da shi yanzu, tun jiya ake fama amma Giwa taƙi faɗar in da yaron yake sai ɓoye shi take sai ka ce ciwo".


Samha ta jinjina kai ta ce "Taɓ a nan aka yi mata sutura kenan?".


"To waye ya ga gawarta, wai a can london ɗin ta mutu aka binneta, haka suka ce fa, ni ko yaushe ta yi cikinma oho, na ga dai tana can tana karatu, to can ya bita yayi mata cikin? Ko kuwa da cikin ta tafi Allah masani, saboda wata lalacewa ma, ita ya turata karatu ƙasar waje, ya zo yana nema ya haikewa iman".


Samha ta girgiza kai ta ce "Mama ba haka aka yi ba, batun iman wannan wani abu ne da Mummy ta shirya shi, amma yadda abubuwan ne suke wakana, akwai wani abu a ƙasa, amma dai bari na yi wanka na sauya kaya".


Ta tashi ta ɗau wayarta ta shiga banɗaki, lambar Khalifa ta nemo, ta kira shi, sai da ta kusa katsewa sannan ya ɗauka.


Ba sallama ba komai ya ce "Ya akwai labari ne?"


"Eh kusan haka, Allah ya yi wa matar adam rasuwa ne".


"Na ji labari" ya katseta.


"A ina ka ji?".


"Kin manta fitacce ne shi? Labarin duk ya karaɗe dandanlin sada zumunta".


Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Haka ne, sai dai an ce a can london wai aka binneta, ba a kawo gawarta ba, sai jaririnta kawai".


Da sauri khalifa ya ce "What? Jariri kuma? How a wace maƙabartar aka binneta a London ɗin? Suwaye suka halarci jana'izar ta a can?"


"I don't know, nima abun da na zo na tarar kenan" ta bashi amsa.


Khalifa ya yi dariya ya ce "Shikenan, kin zo mini da labari mai daɗi, wannan ma wani abu ne na yaƙar adam".


"Amma dai ina fatan ba cutar da shi zaku yi ba, sannan ina son cire hannuna a contract ɗin nan, tun da ma dai wadda ta hanani rawar gaban hantsin ta mutu, ina ga na samu chance"


Khalifa ya ce "Haka ki ke gani?"


"Eh mana, babu abun da yayi saura ai"


"Ba zai yiwu ki saɓa yarjejeniyar mu haka kanki tsaye ba, dole ki kammala mini aikina".


A fusace samha ta ce "Kai saurara, ba fa 'yar ka ba ce ni, ka daina yi mini magana da isa kana bani umarni, ka kiyayeni" da haka ta kashe wayarta tana tsaki.


Kwanaki uku aka yi aka watse daga makokin aisha, sai dai adam sam baya hayyacinsa, kana kallonsa ka san a tashin hankali yake, ko abinci baya iya ci, haka yake tafiya gidansa, ya zauna ya saka kayan aisha a gaba yana kallonsu.
Ranar da suka rabu ya tuna, da zai yi tafiya, lokacin kwananta biyu da dawowa tana yi masa magiyar ya barta ta yi tafiya, ya din ga jan kumatunta yana yi mata dariya ya ce "Cikin nan naki ya sanya kumatunki ƙara cika, kuma sun fi daɗin wasa a haka" kwaɓe fuska ta yi za tayi masa kuka ta ce "Dan Allah ka mayar da maganata serious please ka bari na je".


"Ki bari idan na dawo da kaina zan kai ki, kin ji fulanina".


Kamar ƙaramar yarinya ta shiga turza ƙafarta za ta yi kuka ta ce "Dan Allah kar ta mutu ban je na dubata ba".


Ya ɗan tsuke fuska ya ce "Bana son rigima fa, ke ba ki ga yadda cikinki ya tsufa ba, kin san hatsarine ki fita a san kin dawo, a sirri fa na bari ki ka dawo, tun da kin kasa riƙe kanki, sai kin dawo wurin mijinki"


Buɗe baki ta yi ta ce "Ni haka nace maka?"


Dariya yayi mata ya ce "Idan ma baki ce ba, yanayinki ya nuna ai, tun da ki ka dawo ko waje ban leƙa ba, soyayya kala-kala kawai nake sha, ki yi haƙuri jibi zan dawo in sha Allah sai na kai ki"


Idonta ne ya cika da hawaye, amam ya mayar da abun jokes, ya cigaba da ja mata kumatu yana kashe mata ido.


Da ya zo nan a tunaninsa ya durƙushe a kan gwiwoyinsa, yana kallon kujerar dressing mirror da ta zauna, suka yi wannan abu, da washegari ya ga message ɗin ta na ban haƙuri, a kan ba zata iya jiran dawowoarsa ba jikin kakarta ya tsananta da yawa.


Ya dinga zubar da hawaye yana surutai a hankali, wata irin kewarta tana ratsa shi.
Wani abu ne mai kama da bacci ya ɗauke shi, kawai sai ganin rumaisa ya yi a kan kujerar, tana zaune tana ta yi masa dariya, 'Sarki mai koriyar alkyabba, ka ɗananiba dokinka" tayi masa maganar tana murmushi, daga bisani ta taso ta nufo shi, tare da miƙa masa hannu, ya miƙa hannunsa zai riƙo nata, kawai yayi firgigit ya farka yana kalle-kalle. Ɗan tsuke fuska ya yi, ya tuna yadda ya din ga fama rumaisa tana yi masa gizo a baya, da ƙyar ya daina ganinta, kwatsam yanzu ma ta cigaba da yi masa gizon, ba dan ya ganta tare da 'yan gidansu ba, to da babu shakka zai gazgata cewar aljana ce ita.


Kusan kwanaki ukun nan, rumaisa ta ƙi sakin jikinta, kusan kullum cikin kuka take a kan a dawo mata da jaririnta, tun mama tana ta tata har ta gaji ta ƙyaleta, abinci ma sai an yi kamar za a zaneta sannan take ci. 'yan islamiyyarsu tawaga guda suka yo, har da malamansu suka sake zuwa dubata, amma mirsisi taƙi kulasu, taƙi magana.


Kwanaki huɗu da sallamar su, mama ta ce wa usman yakamata su je gida su yi wa ammi gaisuwar rasuwar aisha.
Mai sunan baba na jin jaka ya ce bai yadda ba, kar su zata wani abun suke nema a wurnsu, tun da sun yi musu gaisuwar a asibiti ya isa.


Mama ta ce "Kai ka san ba zamu je wurinsu domin neman wani abu ba, amma dai-dai gwargwado sun yi ɗawainiya da ƙanwarku, kuma babu laifi dan an bisu gida an kuma yi musu gaisuwa, shi ne abun da yakamata ai, tun da rashi suka yi. Shi dai mai sunan baba ba haka ya so ba, amma babu yadda ya iya haka ya haƙura ya ƙyalesu.


Mama ya shirya ya saka rumaisa ta shirya, ta ce usman da Aliyu suka raka su, ruma sai murna take ko ba komai, zata ga Sabir, sai jin daɗi take yi, ta shirya cikin riga da hijjabi, sannan ta kawo face mask ta saka.
Usman ya ce "Meye kuma na rufe fuska?".


"Bana son a din ga kallona duk in da na je"


Ya ce "Ko kuma baki da gaskiya ba, ko kin yi wa wani laifi"


"Haba yaya usy, yaushe na dawo da zan nemi maganar ma".


Yayi murmushi ya ce "Ashe kina sane ki ke neman maganar"


Gyara zaman hijjabinta ta yi, ba tare da ta sake magana ba suka tafi.


Gidan galadima kuwa, ammi ta karɓo sabir, su iman sun kewayeshi suna kallonsa, yaron haƙurinsa har yayi yawa, ba ya kuka sai ya ga dama, sai dai yayi ta bacci.
Babu in da ya bar adam, kamarsa ɗaya sak da adam, an yi masa wanka an shirya shi, nusaiba tana bashi madara a feeder.


Iman ta ce "Allah sarki rayuwa, Allah ya yi wa anty aisha rahama, mun ci buri sosai a kan haihuwar nan, duk da yadda ake ɓoyewa ba a son a san da cikin, amma tayi buri a kan cikin, kusan

Please Login or Register in order to submit comment