Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawo shi, a lokacin da hadiman ke kaiwa suna komowa.
Dama tuni ammi ta hana Adam fita, ta ce lallai koma menene ya zauna ayi a gabansa, dan haka shima yana nan.


Ammi ta sallami hadimanta, Sannan ta nutsu ta fuskanci turaki.


Hakan ba ƙaramin ɓatawa baba uwani rai yayi ba, dan babu damar samun rahoton da take son samu.


Ammi ta dubi turaki ta ce "Ranka ya daɗe an dawo lafiya ya hanya? Ban samu shigowa ba, saboda ba na son zuwan nawa ya zama takura ko matsi a gareka, shiyasa ban yi maka sannu da dawowa ba"


Turaki ya ce "Kar ko damu, da ke da abun ya shafi zuriyar marigayi, dolenmu ne, kuma babu yadda za ayi ku zama takura a garemu.
Toh! Na zo da saƙonki, a can saudiyya ma na je gidan ɗan uwanki mahadi, mun tattauna da shi sosai, kuma ya bayar da amanna sosai. Sai dai da muka dawo gida da kwanaki uku, mun sami wambai, in da ya nuna rashin amincewarsa da nuna za a sake zubar da darajar masarauta, ta hanyar auro wadda ba jinin sarauta ko tushen arziki ba, sai dai na yi iya yina na nuna masa ƴar gidan daraja ce da kuma gudunmawar da ta bayar.
Har ila yau ya gaya mana zancen da bamu ji daɗinsa ba, ya kawo ƙorafi sosai a kan ka takawa, ciki har da yinƙurin taka ɗan uwanka da mota, wannan lamari bai yi mana daɗi ba, ya ce ya bayar da saƙo ka je, nan ma ka yi burus. Abun bai yi mana daɗi ba, har yayi iƙirarin babu shi babu kai, sai dai mun yi ƙoƙarin kwantar masa da hankali, in da har mai ɗakinsa ta sanya baki, ta hanyar nuna masa tsaurinsa a gareka yayi yawa, shiyasa ba kwa shiri, amma dai duk da haka yakamata a din ga lura ana kiyaye wasu abubuwan, yanzu idon duniya a kan ka yake".


Ammi ta ce "Wallahi ranka ya daɗe, abun da nake yawan gaya masa kenan, amma dai a cigaba da jaddada masa"


Turaki ya ce "Haka ne, akwai buƙatar a din ga kai zuciya nesa, akwai abun da yarinyar nan ta faɗa mini a kan ka, wanda kuma tabbas haka ne ba ta yi ƙarya ba, yana daga dalilan da ya sanya na yi amanna da auren nan sosai, nake yi muku fatan alkhairi".


Ammi ta ce "Allah sarki, Adam kuma ya sunkuyar da kai, yana murza zoben hannunsa.


"To, mun dai yi ƙoƙarin shawo kan wambai da ƙyar, duk da yana nuna ba da yawunsa ba, amma ba wani abun damuwa bane ba zai sakko, illa iyaka kai takawa ka je ka same shi ka bashi haƙuri.
Magana ta gaba kuma, a sanar da iyayen Yarinyar nan, ranar juma'a zamu kai kuɗin aure, kuma wata biyu zamu sanya rak, Allah ya tabbatar mana da alkhairi dan ba ma fatan a jinkirta wani abun ya zo ya gilma".


Ammi ta faɗaɗa murmushin ta tana faɗin "Alhamdilillah, Allah ya sanya alkhairi ya nuna mana da rai da lafiya"


Yayin da adam wata irin mummunar faɗuwar gaba ta same shi, kansa ya sara da ƙarfin gaske, ya ji tamkar ɗakin yana juya masa!




Ayshercool
08081012143


*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*


*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*


*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*


👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*


*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*


*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*


*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*


*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*


*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*


*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*


*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*


*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*


*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*


*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*


*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*


*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*


*15. Supplement for Acne, dark spots remover*


*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*


*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*








*PAID BOOK NE, ₦500 ME VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK, SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143*










Gaba ɗaya Adam bai san yadda aka ƙare zaman ba, da ƙyar ya tashi ya nufi ɗakinsa, yana neman yayi karo da bango, dan ko gabansa ba ya gani sosai, saboda matsanancin ciwo da kansa yake yi, ga juya masa da duniyar take yi, ga wata irin kururuwa da yake ji a kunnensa.


Innalillahi wa Innalillahi raji'un, yake ta maimaitawa.


Gadonsa ya laluba ya kwanta, yana ta sauke numfashi, yana addu'a, sai dai kamar a hayaniyar yake jin muryar rumaisa, duk da baya gane me take faɗa, daga haka bai kuma sanin in da kansa yake ba.


Bai san iya adadin lokacin da ya shafe a haka ba, ya ji ƙamshin turaren ammi, tana taɓa shi ta ce "Adam wai lafiya kuwa?" Ya buɗe idonsa a hankali yana kallon ammi.


"Wa meyafaru da kai ne? Tun da turaki ya zo aka yi maganar nan, daga yi masa rakiya, na dawo na tarar baka nan, tun ɗazu kake bacci sallar magariba fa ake yi yanzu"


Haryanzu kansa bai daina ciwo ba, ya dubi ammi ya ce "Bacci ne yayi mini nauyi, bari na tashi"


"Ka hanzarta ka rama sallolinka, kar ka sake bari lokaci ya ƙure maka ba ka yi salla ba, sonake mu je gidansu rumaisa, mu sanar musu, yau asabar ka ga nan da kwanaki shida kenan za a kai kuɗin"


Magana yake son yi, amma ammi ta ce "Bana son musu, ka hanzarta bana son ɓata lokaci"


Kawai ya jinjina mata kai, dan shikaɗai ya san abun da yake ji, cikin dakiya ya tashi ya shiga yayi alwala, ammi kuma ta koma falo.


Iman kuwa tausayin rumaisa take ji sosai da sosai, ji take kamar ta sanar musu da abun da yake faruwa, da irin furucin da Samha ta yi.


Sai dai tana tsoron abun da ka iya biyo baya, mussaman yadda Samhan ta ƙware a iya fuska biyu da masifa, dan ita ba ta tausayawa kanta, yadda Samha ta yi zaton ita adam zai aura, kamar yadda take tausayawa rumaisa.


Adam saboda yanayin jikinsa, ya ce wa yaronsa sidi ya kaisu gidansu rumaisa, yayi iya ƙoƙarinsa da jarumta ya danne yanayin da yake ciki, sai dai jirin ya kasa barinsa.


Rumaisa kuwa, tana gida jikin mama tana ƙunƙuni, ta yi wa Huzaifa da Yasir rashin kunya, sun ce wannan satin ba za su wanke mata kaya su goge ba sai dai ta yi abun ta. Mama ta goya musu baya, ta ce "Kar ku wanke mata, tun da ba ta da ta ido, ai yakamata ta fara wanke kayanta da kanta yanzu, ke zaki wanke abunki yau"


Cikin shagwaɓa ta ce "Dan Allah mama ki ce su wanke mini, idan na yi wanki rashin lafiya zan yi"


Mama ta kalleta baki buɗe ta ce "Sangarta mai sanya kifi kukan wanka, samun wuri ne ya sanya ki ke wannan maganganun ma, ke ba dan Allah ya sa da su ɗin ba, ai shekara tara kin fara wankin ki, ko yaushe su suke yi miki, ba kuma dan baki iya ba, dole ki karɓi abunki"


Rumaisa ta sake langaɓe kai ta ce "Dan Allah mama ki ce su wanke mini, ni fa yarinya ce"


"Eh nono ma ki ke sha" ta kwanta a jikin mama tana cewa "Mama dan Allah" mama na shirin ture rumaisa, ruman ta tashi zaune da sauri, ta ɗan tsuke fuska.


Mama ta ce "Lafiya kuwa?"


"Kamar baban Sabir zai zo gidan nan, yana hanya"


"Baban Sabir kuma?" Ruma ta jinjina kai ta ce "Haka nake ji a jikina"


Huzaifa ya ce "Iyeee soyayya da ƙauna, bari zamu gani ai"


Rumaisa ba ta iya yi wa Huzaifa martani ba, saboda ji ta yi ƙirjinta ya yi nauyi, jikinta kuma yayi sanyi ƙalau.


A hankali ta zame ta kwanta a jikin mama, ta lumshe idonta.


"Ki tashi bana son barcin la'asar, ki yi shi ki tashi da fushi ki hanamu sukuni da koke-koke da ɓacin rai"
Maimakon ta tashi, sai ta sake langaɓewa, ta riƙe hannun mama.


Mama ta kalli rumaisa ta ce "Ke! Lafiya kuwa?"


Ruma ta jinjinawa mama kai alamar eh.


Mintuna ashirin, sai ga sallamar ammi, mamaki ne ya kama mama, dan ba su yi waya ammi za ta zo ba.


Ta ɓoye mamakinta, ta amsa mata cikin mutuntawa.


Suka gaisa da mama, ammi ta ce "Maman sabir bacci take yi ne?"


Mama ta ce "Rigima dai take ji, wai sai an yi mata wanki, na ce ma ta tashi kar ta yi mini barcin la'asar, ta tashi ta ishi mutane da kukan banza"
Ammi ta yi murmushi ta ce "Haba maman rumaisa, kamar rumaisa idan ba ayi mata wanki ba, ai ba zata iya ba, kar a ramar mini da ita kan ta zo fa"


Suka yi dariya, ruma daga kwancen ta ce "Ammi ina wuni"


"Lafiya ƙalau rumaisa, kina lafiya?"


"Lafiya ƙalau"


Ammi ta ce "To masha Allah, tare muke da takawa fa"


Mama ta ce "Ahh kuma ki ka bar shi a waje, Yasir ka ce ya shigo mana"


Ɓoye mamakinsu suka yi, dan rumaisa ta ce ta ji a jikinta yana hanya.


Tun da yayi sallama jikinta ya kuma sanyi, ta rasa menene yake yi mata daɗi.


Ya shigo ɗakin mama, suka gaisa, mama ta ce wa rumaisa "Ba zaki tashi ki gaishe shi ba?" A hankali ta tashi zaune, ta kalli Adam sau ɗaya, ta kawar da kai ta sake kallonsa na biyu amma ta kasa magana.


Mama ta ce "Ba magana nake yi miki ba rumaisa?"


Ammi ta ce "Wannan ƴar tsamar ta su, idan da sabo sun saba".


Mama ta ce "wannan rashin ɗa'a ne, ya girmeta, kuma mutumin da zaka aura ka din ga yi masa haka, iskanci ne kawai, ai ba haka take yi wa sauran mutane ba"


Rirriƙe mama ta yi cikin kuka ta ɓoye fuskarta ta ce "Mama baki san me nake gani ba ne"


A rikice ammi ta ce "Me ki ke gani rumaisa, yi mini bayani?"


"Hararata yake yi, idan ya harareni ni tsoro yake bani" haka kawai mama ta ji rumaisa ƙarya take yi, dan ta sha faɗa ita fa ban da fuskar mai sunan baba, babu wata fuska da take bata tsoro.


A zahiri kuwa, a karo na biyu yau ta ga abun da ta gani a tare da adam, kamar yadda ta taɓa gani, lokacin suna asibiti.


Idonsa gaba ɗaya ya koma baƙi ƙirin, babu wannan farin, sai hayaƙi da yake fita, kamar ana kunna itace, a wannan karon har da kamar harshen wuta daga idanun nasa.


Shi kansa adam, cikin jikinsa wata irin rawa yake yi, amma a zahiri yana zaune normal, jikinsa ji yake tamkar ana sassra shi, ba bu wani abu da yake muradi, banda ya shaƙe ruma ko ya riƙe ta, ya samu sassauci.


Ya sunkuyar da kai, mama kuma ƙuluwa ta fara yi, da lamarin rumaisa, dan a ganinta rashin mutunci ne kawai.


Ammi ta ce "Haba rumaisa, shi ne har da kuka, ba hararki yake yi ba, haka yake dai bai fiye fara'a ba, ku da kun kusa zama abu guda ma. Maman rumaisa dama zuwa na yi na gaya muku, a sanar da dangin mahaifinta, ranar Juma'a za a kawo kuɗin aure"


Mama jikinta yayi sanyi ta ce "Da wuri haka?"


"Kar ki ce haka maman rumaisa, jinkirin ba shi da wani amfani, kin san mu masaurata ba sa son jira, ayi musu addu'a dan Allah, in sha Allah za a kawo kuɗin aure"


Har mama da ammi da suka gama tattaunawar su, babu wani ƙwarin gwiwar cewa wani abu, a tsakanin adam da rumaisa, kowannensu shi ya san halin da suke ciki.


Bayan sun gama magana, suna fita rumaisa ta tubure da kuka ta ce ita fa ba ta so, ba zata aure shi ba, da fari mama ta fara rarrashin ta, ta zaci abun na ta na hankali ne, amma ta ga ba ta da niyyar nutsuwa, ita dai ba ta gaya wa mama, me take gani ba, amma ta ce ba zata aure shi ba.


Shihowar mai sunan baba ce, ta sanya ta ɗan nutsu, Aikuwa tambayar da ya fara yi, shi ne meya sameta take kuka.
Mama ta sanar masa da duk abun da ya faru, rumaisa ta zaci yanzu ma zai turje, sai ji ta yi ya ce "Allah ya tabattar mana da alkhairi, nan kano zasu kai, ko can katsina?"


Mama ta ce "Wai da su kai wa kawunku na mandawari, ba sai an wahalr da su ba"


Mai sunan baba ya ce "Babu laifi, Allah ya kaimu"


Cikin kuka rumaisa ta ce "Mai sunan baba ni fa na fasa bana son shi".


Wani mugun kallo ya yi mata ya ce "Suwa zaki mayar ƴan iska, ko yau suka ce a ɗaura, sai an ɗaura, ki bari na fita na dawo na tarar kina wannan kukan, ki ga yadda zan yi ƙasa-ƙasa da ke".


Haka nan rumaisa ta tsinci kanta da kasa gaya musu abun da take gani a tare da adam, da alamu suka nuna mata su basa gani, ita kaɗai kawai take gani.


Usman kuwa cewa yake "Wallahi ba zaki yi mana baƙin ciki ba dan ubanki, haka kurum ke fa ki ke son auren mai kuɗi, kuma Allah ya kawo, ki ce ke ba kya so, kin yi kaɗan yarinya, dole ayi auren nan, ko ba komai ma hau doki, kina kallo albarkacinsa aka fito da Aliyu, yanzu malam shamsu har gaisheni yake, saboda yadda ya kankaro mana mutunci, sai kin je".


Cikin kuka ta ce "To ni bana son shi"


"Uban da ya sanya, ki ka amince tun da fari, shi zai sa ki haƙura ma a yanzu" gaba ɗaya aka ƙi goya mata baya, ta din ga surutai da koke-koke suka ƙi kulata.


Ammi da suka tafi gida, jikinta sanyi yayi, da ganin yadda rumaisa duk ta rikice lokaci ɗaya, kuma ta ga bai kamata ta ɓoye musu wasu abubuwan a kan Adam ba, amma tana ji a jikinta rashin lafiyar ta sa abu ne da ya shafe shi, da shi da ita rumaisan, ta din ga fatan Allah ya sanya hakan ba zai zama cutarwa ga rumaisa ba.
Nusaiba ta din ga tambayar ammi yadda suka yi.


Ammi ta ce "Sun amince, rumaisa ce dai take nema ta ce ta fasa, amma ina ganin rigima ce kawai irin ta ta, kuma kai takawa, kamar yadda na gaya maka a baya, dole ka sassauta ka mayar da kanka dai-dai da ƙuriciyarta, bana son ayi auren nan ya zaman tana jin tsoronka, ko tana ganin kamar ba ka da imani"


Adam bai iya fahimtar abun da ammi take faɗa sosai, ya kwanta a kan 3seater, ya lumshe tabbas.


Iman kuwa tausayinsa da na ita kanta rumaisan ya kamata, mussaman da ta ji cewar nan kurkusa sosai za ayi auren.


Har dare yayi, ko abincin kirki rumaisa ta ƙi ci, sai koke-koke, suka shareta suka cigaba da harkokinsa, usman sai tsara yadda abubuwa za su kasance yake yi.


Mama ta kira yaya Abubakar a waya, ta sanar masa da batun, ya ce zai shigo kano, Yakamata tun wuri su san me suke ciki, su san mai yakamata a fara tanada na auren rumaisa.
Jin abun da yaya Abubakar ya faɗa, ya sanya rumaisa jin kome za ayi mata ba zata iya barin gidan nan ba, sai dai idan an yi auren ya dawo gidan ya zauna, ko ya barta a gida ya bata sabir kamar yadda aka yi mata alƙawari.


Tashi ta yi ta nemi wuri ta yi kwanciyarta, saboda hirarrakin ɓata mata rai suke yi.


Daga nesa take hango shi cikin hayaƙi, a hankali hayaƙin yake bajewa, yana ƙara kusantota, ganinsa ta yi cikin sarƙa hannu da ƙafa, ga idonsa na ci da wuta a wannan karon ba hayaƙi kawai yake yi ba, fiƙarsa duk ta fito daga bakinsa, ga faratansa sun yi zaƙo-zaƙo. Tunkarota yake yi, yayin da ita kuma take ja da baya, cikin tsoro da razani.


Duk iya ƙoƙarin ta na addu'a, ta kasa dan ji ta yi tamkar an danne mata masarrafar tunaninta, zuwa maƙoshinta, ta kasa Addu'a.


Tun tana ja da baya, har ta kai bango, fizgota yayi da ƙarfi, ya danna mata faratansa a maƙoshinta.


"Wayyo Allahana mama na shiga uku, Innalillahi wa Innalillahi raji'un"


Ko sallame sallar da take mama ba ta yi ba, ta yo kan rumaisa jin tana ihu, kamar wadda za a kashe.


Mama ta fizge net ɗin rumaisa, ta riƙota tana tambayarta "Lafiyarki kuwa? Menene?"


Rirriƙe mama ta yi tana mayar da numfashi, hannu ɗaya kuma ta riƙe wuyanta, da take jin kamar yana yi mata zafi.


Tuni Aliyu da mai sunan Baba suka taso da gudu suka yo ɗakin mama, saboda yadda kururwar rumaisa ta cika gidan.


Mama ta jijjigata ta ce "Rumaisa menene ki yi magana mana"


"Mama baban Sabir ne, shine"


"Me yayi miki?" Numfashi take saukwa, amma ta kasa gayawa mama abun da ta gani.


A fusace mai sunan baba ya ce "Wulaƙancin naki da iskancin har ya kai ki din ga yi mana ihu cikin daren nan? Kar ki kuskura ki kaini bango, na kuma jin bakinki sai na zaneki, ki yi addu'a ki kwanta, idan ma kina yi ne saboda ba kya son auren, to kin yi kaɗan"


Mama gaba ɗaya jikinta yayi sanyi ta kuma cewa "Me ki gani ya razanaki haka?" Rumaisa ta yi shiru.


Mai sunan baba ya ce "Ba wani abu da ya razanata, shirmenta da take yi ne yake zuwar mata har a mafarki"


Aliyu ya yi tsaki ya ce "Rigimarki ba ta ƙarewa, har tausaya bawan Allah nan nake faman da zai sha" ya fice daga ɗakin, mai sunan baba ma ya fice.


Duk iya rarrashin mama, da lallaɓa yaro a matsayin ta na uwa, ta yi, amma rumaisa ta ƙi gayawa mama ainihin abun da ya faru, haka mama ta ƙyaleta ta sake tayar da salla.


Tsoro ya hana rumaisa ko rufe idonta, dan haka ta tashi ta je ta yi alwala, ta zo ta tayar da salla ita ma, sai dai tana yin raka'a biyu, wani nannauyan bacci ya ɗauke ta.
Mama tana jin yadda rumaisa ke ta surutai a baccin, kamar tana hannun ƴan bindiga.


Sai da mama ta sanyata a gaba tana ta tofa mata adduoi, har mama ta fara tunanin, ko rumaisa na da aljanu ne, maganar aure ta taso za su fara motsawa.
Dan haka ta ƙudurce a ranta, dole ta nema mata maganin sheɗanu.


Ta cigaba da sallolinta, tare da tsananta addu'a a kan lamarin auren nan da yake tunkarosu.


***


Mamaki Samha take ba ɗan kaɗan ba, ganin irin surƙuƙin ƙauyen da suke kurɗawa, ita da Mummy da kuma Hajiya Lubabatu.
Kasa ɓoye mamakin ta yi ta ce "Wai yanzu Mummy har nan ku ke zuwa? Ni fa ma fara jin tsoro"


Mummy ta yi murmushi ta ce "Yaro yaro ne, ke ranar biyan buƙata, rai ba a bakin komai yake, tafiya duk nisanta da surƙuƙinta, in dai da biyan buƙata ai shikenan, tafiya ɗazu ce".


Hajiya Lubabatu ta ce "Ke idan babu wannan ƴan biye-biyen mutum ya zauna lafiya, mussaman a irin gidajen sarautar nan, ai ni tun da Allah ya taimakeni, na kaɗa duk wata mata da ta raɓi gidana, na ga tsuguno ba ta ƙare mini ba, sai na dangana da mallakawa Jabir kujerar galadima,"


Samha ta ce "Takawan fa? Ba gidansu sarautar za ta koma ba".


Mummy ta zunguri Hajiya Lubabatu, sannan ta ɗora da cewa "Yauwwa, mun kusa ƙarasawa, daɗinta kowa yake gani, idan muka je sai ya katse ya sauraremu".


Samha ta ce "Ni fa idan za a kasheni, ban san hanyar komawa ainihin titi ba, gaba ɗaya kaina ya juye".


Hajiya Lubabatu ta ce "Zaki zama ƴar gari ne da zarar kin waye".


A cikin surƙuƙin ƙauye sosai mutumin yake, dan an fita daga gari sosai wurin kamar daji, a nan aka yi masa wani shinge, suka tarar da tarin mata da maza a wurin, da masu zubin hannu da shuni, da masu saffa-saffa, ga marasa lafiya kuma, wasu abun nasu ma dai ba kyawun gani.


Ba tare da ɓata wani dogon lokaci ba, bayan an sallami na ciki, suka shiga, wurin duk an kafe ƙahuhuna da ƙwarangwal ɗin dabbobi, ga wani irin wari da tsamin turaruka da magunguna da ɗakin yake yi. Mutumin yana zaune cikin wasu tsummokaran kaya, ga wasu irin kayan tsubbu a gabansa shi kansa duƙun-duƙun da shi, kamar ba ɗan Adam ba, ga idonsa ɗaya hakiya ta rufe, ɗayan kuma a juye ga idon jawur.
Sai da kan Samha ya sara, ta nemi faɗuwa, Hajiya Lubabatu ta riƙeta suka zauna.


Mummy ta ce "Barka da warhaka malam, ya aiki ya ƙoƙari"


"Lafiya ƙalau, kin yi nusau, ko buƙata ta biya ne, ko kuma dai kin fasa aikin da ki ka buƙata, tun da ki ka ce mana akawai maganin da ake masa amfani da shi, muke jiran ki kawo mana maganin mu yi aiki a kai, amma mun ji ki shiru".


"Ai malam maganin ne yaƙi samuwa, duk wata hanya da zan bi a samu, ba a dace ba, amma ba haƙura na yi ba, ina nan zan dawo. Gamu tare da baƙuwa, ƴar facalarmu ce, da ita da shi yaron Adam, duk iyayensu ƴan uwa ne, ta daɗe tana son shi, amma ya auri ƙanwarta, yanzu ƙanwar ta mutu, amma uwarsa na son aura masa wannan ƴar tsintuwar da na taɓa baka labari, kuma wannan ɗin ta kuma rasawa, shine muke son ayi wani abu a kai".


Yayi shiru, sannan ya ɗebi wata ƙasa ya zuba a wani fai-fai, ya dinga juya hannunsa, sannan ya kalli fai-fan ya ce "Tirƙashi, tabbas ga maganar aure nan, sai dai ita yarinyar tana tafe da wata irin guguwa mai ƙarfin gaske, sai kun tashi tsaye sosai"


Cikin sauri Samha ta ce "Malam so nake kar auren ya yiw....."


"Aure sai an yi shi, ma'aunin ƙaddarar yarinyar da zai aura ya rinjayi tasa, sai dai idan ɗayansu ne ya mutu"


Kamar Samha za ta yi kuka ta ce "Dan Allah malam a kasheta, ba

Please Login or Register in order to submit comment