Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fuskar sidi ba, wanda suka taɓa kamota suka kaiwa takawa.
Bai saurare ta ba, ya buɗe bayan motar takawa ya jefata, ya rufe motar, Adam ya sauke glass ɗin motarsa ya jinjinawa Sidi kai, sannan ya rufe glass ɗin motar ya fara ja.


"Malam ka tsaya in sauka daga motar nan, bana son ka kaini gidan ka sauke ni bana so" banza yayi mata ya cigaba da tuƙinsa.


"Na ce maka ka sauke ni, wai kai meyasa ka ke mini haka ne? Ka sauke ni"


Ganin bashi da niyyar kulata, ya sanya ta fara kiciniyar buɗe motar, amma ta ji ƙofar motar a rufe gam.


Adam a zuciyarsa yake jinjinawa masifa da taurin kan rumaisa, da a buɗe motar take haka za ta buɗe ta ce za ta fita.
Ganin ba za ta iya buɗewa ba, ta zauna ta cigaba da kuka tana ƙanan maganganu.


Bai tsaya a ko ina ba sai ƙofar gidan su, mamaki take yi a ina ya san gidansu?.


Ko da yayi parking bai fita daga motar ba, sannan kuma bai buɗe motar ba, rumaisa ta hau kiciniyar buɗe ƙofar motar, amma ta ji a rufe.


"Ka buɗe mini in fita" ta kai masa duka dan takaici.


Danna wayarsa ya hau yi, na wani ɗan lokaci sannan ya buɗe motar ya fita.
Sai dai ya kulle rumaisa a ciki, bai buɗeta ba, bubbugawa tayi ta yi, amma ya fita ya tsaya ya ƙi saurarar ta.


Aliyu ne ya fito daga cikin gida, yana ganin Adam ya faɗaɗa Murmushin sa, ya ƙaraso suka gaisa, rumaisa ba ta iya jin mai suke cewa, amma sun ɗan jima suna tattaunawa sannan ya buɗeta ta fito tana wani basarwa.


Wani mugun kallo Aliyu ya yi mata, sannan ya ce "Sai ki wuce ki shiga" ko a jikinta, ta yi gaba dan ita yau ko za'ayi mandaƙo da ita tun da buƙatar ta ta biya shikenan.


Wani wawan burki ta yi, da ta ga mai sunan Baba a ƙofar ɗakin mama, yana gyara botirin hannun rigarsa.


Wani irin mugun yawu ta haɗiye, ta fara takawa a hankali kamar hawainiya.
Fuskarta ƙarara ta bayyanar da tsantsar tsoro da razanin da take ciki.


Aliyu ne ya yi sallama da shi da Adam, mai sunan Baba ya amsa ba tare da ya ɗago ya kallesu ba, sai ma ja da yayi da baya ya basu hanyar shiga falon mama.
Bai kula Adam ba, shi ma bai kula shi ba, suka shiga ɗakin mama da sallama, da gudu rumaisa ta bi su tana waiwayen mai sunan baba.


Mama ta faɗaɗa murmushinta tana yi wa Adam barka da zuwa.


Ya ce "Tuba nake mama, tun da aka bar asibiti ban samu na zo na gaisheki ba, abubuwa ne sun yi mini yawa ƙwarai da gaske"


Mama ta ce "Babu komai, ya gida ya hajiyar take? Ya kuma mai gidana".


"Duk suna nan lafiya, ta ce a gaishe ki"


Rumaisa ta kalleshi a ranta ta ce "Kalleshi, kamar ba yanzu ya gama wulaƙanta ni ba, har da shigo mana gida ya zauna, yana washe baki dan ace masa mutumin kirki".


Mama ta ce "Rumaisa duba kitchen, ki kawo masa ruwa" sai da ruma ta ji kamar ta yi fitsari, saboda kar ta fita mai sunan baba ya kamata.


Sai da ta leƙa ta ga baya nan, sannan ta shiga kitchen da gudu, ta ɗauko pure water ɗaya, ta dawo ta tsaya a kan Adam ta miƙa masa.


Kallon da mama ta yi mata ne ya sanya ta rasa in da za ta sanya kanta, dan gaskiya a tsorace take sosai.


Da ƙyar ta sake komawa, ta zubo ruwan a wani ƙaton baho, kusan guda goma sha biyu, ta ɗauko ta zo ta dire masa.


Aliyu ya ce "Wai ke wace irin taɓaɓɓiya ce ne? Ya zai yi da wannan ruwan babu plate a kitchen ki ɗoro masa ko huɗu ne, sai ki yi wannan shirmen?"


Adam ya ce "Rabu da ita, yanzu zan tafi nima, daga gida nake Alhamdilillah a ƙoshe nake, dama ammi ce ta sanya na dawo da ita gida,kamar yadda na kira Aliyu a waya na yi masa bayani, maimakon ta je makaranta ta taho cikin gari ganin sabir, kuma ta tafi a ƙafa wanda akwai hatsari a hakan, mussaman da yanzu yakamata ace tana ƙarƙashin tsaro sosai, na kawota ne a ɗan ƙara sanya ido a kanta sosai, a kula da ita kar a sake bari ta zo, idan tana buƙatar ganinsa ayi waya za a kawo mata shi.
Sannan makarantar su ma yakamata ce, sun bibiyi abun da ya sanya ba ta je ba yau, kamata ya yi ace sun kira gida"


Aliyu ya ce "Makaranta suna iya ƙoƙarin su, ita ce dai kamar ƙanwar aljanu, saboda rashin ji da kafiya, duk abun da idan ta san za ta yi ayi magana shi take yi. Kuma makarantar ta gwamanti ce, suna da ɗalibai sosai babu lallai ma su san ba ta zo ba"


Mama ta ce "Ai idan ba ta je ɗin ba suma hutunsu ne, mun gode sosai da sosai, in sha Allah za a sake kulawa, hakan ba zata sake faruwa ba".


Ran rumaisa ya ɓaci, yadda su mama ke ta ce mata fitinanniya a gabansa, salon ya sake rainata.


Babu wanda ya san da shigowarsa, sai gani suka yi yayi sama da rumaisa yayi waje da ita, tana ihu. Adam ya bi mai sunan baba da kallo, ganin yadda ya ɗaga rumaisan kamar ya ɗaga kara.


Aliyu ya ce "Madalla, dama tun da ki ka dawo baku haɗu ba, ai gara ya tuna miki yana nan".


Adam ya ce "Amma wannan ɗaukar da yayi mata, kar ƙashinta ya samu matsala, tun da ba ta gama warwarewa ba"


"Da zai samu matsala, da ba ta kawo yanzu ba da hannun a jikinta, zata yi facing displine master". Da fari ruma tana ta kiran sunan mama, tana bashi haƙuri, amma da yayi mata wata irin tsawa tuni ta nutsu ta rufe bakinta.


Ruwa ya saka ta janyo, ta cika wani ƙaramin bokiti, ya ɗora mata a ka, ya tsayar da ita a rana, ya sanya takalmansa ya fice.


Hirarsu suka cigaba, babu wanda ya sake bi ta kan rumaisa, duk da mama a cikin ranta, ta ɗan ji tausayin ruman.


Sai da suka ɗan taɓa hira, a kan abubuwan da suka din ga yawo a kansa a social media, haka nan yake yabawa da nutsuwar mama, tare da jinjina mata raino da tarbiyyar wannan zaratan mazan su bakwai itakaɗai, kuma wasunsu na karatu wasu suna sana'a a yanzu haka. Hakan ya sanya yake jin tana da wani experience na rayuwa, a ɗan haɗuwar da suka yi a asibiti, da yadda take magana yanzu, ya sanya ya fuskanci surutun rumaisa yana da nasaba da rayuwa cikin mazan nan, wanda kowa da kalar tunaninsa da kuma irin halinsa.
Ga uwa uba yadda mama ke bayanin wasu abubuwan da ya shafi ƙasa, sai ka ce wata babbar mai kwalin karatu ce, amma wai kawai jin radio da bibiyar labarai ya sanya take sanin abubuwa sosai a kan lamarin ƙasa.


Adam ya yinƙura ya ce zai tafi, mama ta ce "Gashi ka zo bamu ko sauke abincin rana ba, kuma ka ce wurin aiki zaka koma, Gadanga ko ka kusa sauke shinkafar?"


Aliyu ya ce "A'a da saura, kuma ga miya ma, ko wani abun za a sayo maka?"


Adam ya ce "Kai ka ke yin girki? Ka iya girki?" Yayi maganar cikin mamaki, dan shi ko gas tsoron kunnashi yake balle girki.


Aliyu ya yi dariya ya ce "Ko in zo ammi ta ɗaukeni kuku ne? Ba abun da ban iya dafawa ba"


Dariya suka yi, Adam ya tashi ya ce "Kar ku damu, a ƙoshe nake sai anjimanku".


Mama ta ce "A'a tsaya"


Ta shiga ɗakinta ta fito da tasar turare, da kuma dabino lubiya a leda ta ce "Ga turare ka shafa, dabino kuma a bawa hajiya"


Adam yayi murmushi ya ce "To na gode sosai mama, Allah ya saka da alkhairi"


Aliyu ya rako shi tsakar gida, hannun ruma sai rawa yake da bokitin ruwa a ka, ta haɗa uban gumi ga hawaye ya wanke mata fuska.


Kallo ɗaya Adam yayi mata ya kawar da kansa, suka fita.


Sai da suka fita sannan Adam ya kalli Aliyu ya ce "Ku sauke mata ruwan nan, za ta galabaita da yawa, ta yi tafiyar ƙafa nisa sosai"


Aliyu ya ce "Ai wannan ruwan babu wanda ya isa ya sauke mata shi sai wanda ya ɗora mata, ka ƙyaleta ba jin magana take ba". Bai kuma cewa komai ba suka yi sallama ya tafi.


Yana tafe a hanya yana tunani a ransa, abun da rumaisa ta faɗa ɗazu ne ya dawo masa, idan har za a ce a kashe sabir, ta tsaya ta kuɓuto da shi, mai zai sa a haɗa baki da ita a cutar da shi? Waye ya ce a kashe shi, kuma saboda me?" Ya tambayi kansa.
Basar da tunanin yayi ya cigaba da tuƙinsa.


Mama kuwa tun da takawa ya tafi, ta saka rumaisa a gaba da faɗa, ta in da ta shiga ba ta nan take fita ba. Ta kai a ƙalla awa ɗaya da rabi, sannan mai sunan baba ya kira Aliyu a waya ya ce rumaisa ta sauke ruwan nan.


Ba punishment ɗin da mai sunan baba ya sakata ne ya sanyata kuka ba, idan ta tuna wulaƙanci da maganganun da takawa yayi mata a kan ɗan sa, sai ta ji ranta ya ɓaci sosai, wasu hawayen takaici su cika mata ido.


A haka su Huzaifa suka dawo daga makaranta suka tarar da rumaisa, idon nan jawur dan ko abincin rana ta ƙi ci, ta koma gefe kawai tana kuka.


"Ke wai me aka yi miki, meya sameki?" Huzaifa ya yi maganar yana zungurinta da ƙafarsa. Banza ta yi masa taƙi kula shi.


Yasir ya ce 'Mama me aka yi mata ne? Ko ba ta da lafiya ne?"


"Lafiyarta ƙalau, tsagwaron iskanci ne da rashin mutunci kawai ke ɗawainiya da ita, tun da ita har abada a rayuwarta sai ta yi abun da za a zageta ace ba ta kyauta ba take jin daɗi. Yau ba ta je makaranta ba ta wanke ƙafa ta tafi cikin gari, wai ta je ta ga Sabir, saboda rashin kan gado a ƙafa"


Yasir ya ce "Kaii, yaushe na rakaki gidan ki ka ganshi yau ki ka koma musu gida, anya kan ki ɗaya kuwa?" Ganin duk sun tarar mata ya sanya ta ƙara sautin kukanta.


"Zaki rufe mini baki, ko sai na jibgeki tukuna" mama ta yi maganar a matuƙar fusace.


***
Ko da su iman suka dawo daga makaranta yau, gaba ɗaya sun lura da yadda ammi ba ta walwala, kamar akwai wani abu na damunta, nusaiba ma ta lura da hakan, sai dai iman ta kasa jurewa sai da ta magantu "Ammi, wata matsalar ce ta kuma tasowa ne?"


Ammi ta ce "Me ki ka gani?"


Gani na yi kamar wani abu na damunki, kamar jikinki duk a sanyaye yake.


"To, damuwa dai ba a rasata Iman, tausayin yarinyar nan nake ji"


Nusaiba ta ce "Wace yarinyar?"


"Rumaisa, yarinyar da ta dawo da sabir?"


Iman ta ce 'Ni dai ban taɓa ganinta ba, amma wani abun ne ya sameta?"


"A'a, sai dai ina tsoron kar wani abun ya sametan a dalilinmu, son da take yi wa yaron nan har tsoro yake bani, yau tun daga gidansu har nan ta zo a ƙafa wai dan ta ga yaron nan, ina tsoron kar mu ɗau hakkinta"


Nusaiba ta ce "Too ikon Allah, tana da ƙarfin hali gaskiya".


Ammi ta nisa ta ce "Ashe Mahmud kuma ya dawo"


Gaban iman ya faɗi, Nusaiba ta ce "Yaushe? Ganinsa ki ka yi?"


"Ban ganshi ba, amma sun haɗu da rumaisa"


Nusaiba ta ce "Mai ya ce mata?"


"A'a ban sani ba, sun haɗu dai ta zata takawa ne, shikenan dai ina son in ɗan fita an jima, zan je gidan turaki"


Iman ta ce "Ammi me zaki je ki ce masa? Ko akwai wata matsalar? Kin san mama tana ganinki za ta fara tunanin wani abu"


"A'a ina buƙatar ganinsa ne kawai, kuma ai ni ba wurinta zan je ba".


"To shikenan, a dawo lafiya".


Kafafen sada zumunta suka cigaba da ɗaukar hazo, a kan lamarin mutuwar aisha, adam yayi iyakar ƙoƙarin sa, wurin kawar da kansa a kan abun da yake faruwa.
Yana zaune a cikin motarsa, ya nutsu yana duba social media da yadda ake ta surutai a kan lamarin, kwatsam! Ya ci karo da posting ɗin Senator Usman wakili yayi posting a shafinsa yana yi wa adam ta'aziyyar mutuwar matar sa.


*A madadina da iyalaina, ina miƙa saƙon ta'aziyyata ga ɗaya daga cikin jami'an tsaronmu, Adam Sharif Galadima bisa ga rashin matarsa, ina fatan Allah ya yi mata rahama ya sanya ta huta, sai dai abun mamaki ne ace matar jami'in tsaro kamar wannan, da ya tsayawa ƙasa ace matarsa ta mutu a hannun'yan bindiga, wannan babban abun kunya ne ga ƙasa baki ɗaya*


Nan da nan mutane suka shiga tofa albarkacin bakinsu, in da suka dinga jinjinawa senator wakili na yi wa adam ta'aziyya duk da yadda ya sako shi a gaba, da ƙoƙarin binciko laifukansa.


Wata irin nannauyar ajiyar zuciya adam ya sauke, ya sake shafa fuskar wayarsa yayi sama, ya sake cin karo da gidan jaridar da suka fara wallafa cewar ya kashe matarsa, sun sake wallafa labari kamar haka.


*Lauje cikin naɗi, Abun da Kamar wuya gurguwa da auren nesa, ace babban jami'in tsaro guda, ayi garkuwa da matarsa ba tare da sanin hukuma ba, a ƙaddara an ɓoyewa duniya, domin gudun abun kunya ace jami'in tsaro ya gaza bayar da kariya a gidansa balle ƙasa, me zai sa ace an ɓoyewa hukuma, idan har rayuwar matar jami'in tsaro ba ta da amfani an gaza ceto ta su kuma sauran al'ummar ƙasa su ce me?.


Ayshercool.


*KANWAR MAZA*


*35*




*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*


*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*


*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*


👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*


*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*


*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*


*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*


*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*


*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*


*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*


*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*


*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*


*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*


*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*


*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*


*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*


*15. Supplement for Acne, dark spots remover*


*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*


*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*










*Paid book ne, ₦500 via 0009450228
Aishs adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143






A hankali ya rufe datarsa, ya yi shiruu yana tunanin mai ya yi wa mutane haka, da har wasu suka sanya rayuwarsa a gaba suka mayar da ita hanyar su ta neman abinci.


A hankali ya ajiye wayar ya kunna motarsa ya tafi.




Baba uwani ce durƙushe a gaban Mummy, jikinta sai rawa yake yi, Mummy ta dubi baba uwani ta ce "Uwani me ki ke nufi ne? Ƴan kwanakin nan duk wasu ayyuka da na sakaki ba kya iya yi mini, sannan babu wani rahoto da ki ke kawo mini"


"Tuba nake ranki ya daɗe, ayi mini afuwa, ayi mini aikin gafara".


Ta ɗan ja numfashi ta ce "Yarinyar da aka ce ta zo da ɗan wurin Adam an ce ta na zuwa gidan nan haka ne?"


Baba uwani ta ɗan yi jimm sannan ta ce "Wallahi ba na ce ba uwar ɗakina, kin san yaron ko fito da shi daga sashin giwa ba ayi, babu wata hadima da aka amincewa zuwa in da yaron yake, ciki har da ni, dan haka ba na ce ba, amma akwai wata yarinya da take yawan zuwa, ban san alaƙarsu ba, amma zan iya cewa ita ce dan kuwa kwanaki na ji an ce za a kaita wurin mai girma turaki, amma abun da ya sa ban gazgata ita ce ba, yarinya ce fa sosai bana tunanin ita ce".


"Ba tunaninki nake son ji ba, abu ɗaya zan saka ki, daga yau idan ki ka sake ganin ta zo, ki yi gaggawar zuwa ki sanar da ni, bana son ta zo ta bar gidan nan ba tare da na sani ba".


"An gama ranki ya daɗe, in sha Allah zan sanar da ke"


"Saura wannan karon ma ki tsaya shashanci, tashi ki bani wuri " jiki na rawa baba uwani ta tashi ta bar ɗakin.


***
Jamil ne zaune a turakar turaki, bayan sun gaisa, ya ɗan gyara zama ya ce "Allah ya taimake ka, wata magana nake son mu tattauna idan babu damuwa"
Turaki ya jinjina masa kai ya ce "Ina sauraronka".


"Dama na ce game da riƙon ɗan wurin aisha, a hannun giwa yaron zai zauna kenan su cigaba da riƙonsa?".


Turaki ya ce "Eh, wannan hukunci in da zai zauna mahaifinsa ne yakamata ya yanke, ya rasa matarsa bai kamata ɗan kuma a saka masa ido a kan sa ba"


"Amma, ba kwa tunanin yana da kyau a sanya ido, idan maganar aure ta taso ya auri wadda za ta riƙe yaron da amana ta kula da shi?"


"Adam ba ƙaramin yaro bane ba, na san zai samo mace mai mutunci da kirki, ba zai auri wadda za ta cutar da yaron ba".


Jamil ya sake gyara zamansa ya ce "Amma ina ganin ku yakamata ku zaɓo wadda za ta maye gurbin aisha, kuma a ganina Samha ita yakamata ta maye gurbin aisha, a wannan karon yakamata a ba ta wannan damar"


Turaki ya ɗan yi shiru yana nazarin maganarsa, ya ɗago ya ce "Ka zo da magana kai ma, amma ka bari zan yi tunani a kai, kuma zan yi magana da shi in sha Allah, Allah Ya sanya hakan ya zama alkhairi"


"Amin ya rabb, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana"


Turaki ya jinjina masa kai tare da ɗan yin murmushi.


Duk wani ƙoƙari da dagewa, rumaisa tana yi wurin ganin ta kawar da tunanin sabir daga zuciyarta, amma abu ya ci tura, kullum sake jin ƙaunarsa take da tunanin sa a cikin zuciyarta.
Idan ta tuno da maganganun adam sai ta ji ina ma za ta iya zuciya, ace ko kallon sabir ba zata sake yi ba, balle ta ɗauke shi, amma ina sai ta ji ba zata iya ba, yanzu ma kawai daurewa take yi.
Gashi yanzu an ƙara mata tsaro, wataran mai sunan baba da kansa yake makaranta, islamiyya kuma tare da su huzaifa suke tafiya dan haka ba damar satar hanya. Haka za ta ɓoye ta yi kuka wasu lokutan dan tana kewar sabir sosai da sosai.


Yau asabar tana ta shirin tahafiz, mama ta ƙwala mata kira tana daga ɗaki.
Rumaisa ta shiga ɗakin, mama ta miƙa mata waya ta ce "Gashi Gwaggo ce za ta yi magana da ke".


Rumaisa ta karɓi wayar ta kara a kunnenta ta yi shiru.


"Hello rumaisa"


"Na'am".


"Ja'ira ki na ji na ba zaki yi magana ba"


Rumaisa ta ce "Ina kwana"


"Lafiya ƙalau, ya ki ke ya ƙarfin jiki?"


"Na ji sauƙi ai, har na koma makaranta ma"


"Ahh to Alhamdilillah, ya firgitar da ki ke yi fa cikin dare kin daina?"


"A'a ina yi wataran"


Gwaggo ta ce "Subhanallah, ki din ga addu'a sosai da sosai, dama zama a cikin wannan dajin ai dole ki yi gamo, wataƙila ma kin kwaso makarai. Zan saka a haɗo miki magunguna, a haɗo miki da kayanki a kawo miki".


Da sauri rumaisa ta tari numfashin Gwaggo ta ce "A'a gwaggo, kar a kawo mini kayan nan yanzu, ki ɗaure mini su, ki ɓoye su sosai, kar ki bari wani abu ya same su, zan gaya miki lokacin da za'a kawo mini"


"To shikenan babu damuwa in sha Allah, zuwa sati mai zuwa zan aiko miki da magunguna"


"Ni fa lafiyata ƙalau, ba wasu aljanu da na kwaso"


"Idan ma kin kwaso ai ke ba zaki sani ba, kuma idan aka kawo magani ki ka ƙi yi, da kaina zan zo har kanon na zane miki jikinki"


Rumaisa ta yi shiru, gwaggo ta gama maganganunta, ta miƙawa mama wayarta ta ɗau jakarta ta fice zuwa makaranta.


***
Ringing ɗin da wayarsa take yi ne ya sanya shi farkawa daga baccin da yake yi, a hankali ya yi miƙa ya buɗe idonsa, ɗan guntun tsaki ya ja, dan ya ji haushin katse masa barcin da aka yi.
Ya miƙa hannu ya ɗau wayar, ya ɗaga ya saka a kunnensa.
"Assalamu alaikum warahmatullah, barka da safiya"


"Yauwa barka" ya amsa murya can ƙasa.


"Ya gida ya ƙoƙari"


Cikin ƙosawa ya amsa da "Alhamdilillah, waye?".


"Khalifa Usman wakili ne, na kiraka ne domin yi maka ta'aziyya tare da jajanta maka abun da ya faru da kai".


"To ka saɓa lamba, ba wanda yakamata ka kira ɗin ka kira ba"


Khalifa ya ce "Na sani, ba Mahmud Sharif Galadima ba ne?"


"Eh, Adam sharif galadima yakamata ka kira"


"Ba laifi bane idan kai ma an yi maka ta'aziyya ai, abun da ya shafi adam ya shafeka"


"Kai ka ga, abun da ya shafe shi shi ya shafa, ku je can ku yi abun ku, don't ever involves me, ba na son fuska biyu, wataƙila da har zuciyarka da gaske ka ke ka kirani ka yi mini ta'aziyya sai in amsa maka, amma kowa ya san abun da yake tsakaninsa da mahaifinkaa da kai kanka, jiya mahaifinka yayi masa ta'aziyya a kafafen watsa labarai, kai kuma yau ka kirani wai kana yi mini ta'aziyya bana son munafuncinku na ƴan siyasa, kar ka sake kirana" ya yi tsaki ya kashe wayar ya ajiye.
Ya tashi zaune yana mamakin tsabar rashin kunya na wasu ƴan siyasar, ya san da biyu ya kira shi, ba dan Allah ba.


Ya miƙe ya shiga banɗaki domin ya yi wanka.


Ya gama abun da yake yi, ya fito ya shirya, ya fita falo domin karya, a falon ya tarar da Samha da Fauziyya ga ruky da Mummy sai hira suke yi,

Please Login or Register in order to submit comment