Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne na siyasa, domin juya tunanin talaka baibai, ka san shi talakan Nigeria idan har zai ci ya ƙoshi, duk abun da zaka ɗora shi a kai zai bi a haka, babbar damuwar ɗan Nigeria ya ci ya ƙoshi ne, daga haka ba shi da wata damuwa da yadda abubuwa suke wakana, suma Dss ɗin muna nan zamu yi abun da ya dace a kan su"


Mutumin ya jinjina kai ya ce "Yanzu ranka ya daɗe wannan kwamitin da aka naɗa na binciken shi ma plan ne?"


Kamar mara imani haka wakili ya sake ƙyaƙyacewa da dariya ya ce "Ka je ka cigaba da yi mini aiki, nima zan yi amfani ƙarfin kujerata da faɗi a ji na ƙasar nan, na cika maka naka burin".


Risunawa mutumin ya yi yana jinjinawa wakili yana faɗin "Allah ya ida nufi, wakili na kowa"


Yayi maganar yana kamabama wakili, yayin da shi kuma yake ta ɓaɓɓaka dariya.


***
Kamar yadda Adam ya faɗa, da azahar bashir ya zo, zai kai rumaisa wurin X-ray, amma mai sunan baba ya ce bai yarda ba, su zasu kaita kar son banzan na su yayi yawa.


Bashir cikin mutuntawa ya ce "Haba Yallaɓai, rumaisa fa ta zama ƙanwarmu mu ma, ko ma in ce maka 'yar mu, duk abun da muka yi mata bamu faɗi ba, ka duba girman aikin alkhairin da ta yi mana, ai tafi ƙarfin abun da muke yi mata a wurin mu, dan Allah kar ka damu, wallahi ba son banza bane, idan dai har kuɗi ne, akwaisu adam ba shi da matsalar su, ku kwantar da hankalinku, dan Allah ka bari a kaita".


Mai sunan baba ya ce "Wanda ku ke yi mana, da wanda ku ka riga ku ka yi mana ma mun gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, amma muma a matsayin mu na ahalinta yakamata mu tagaza".


Bashir ya ɗan langaɓe kai ya ce "Zaku ja mini magana a wurin uban gidana, ga kuma uwa uba Ammi, ba za ta taɓa jin daɗi ba, sun ɗora ni a kan kula da komai, dan Allah ku yi haƙuri wallahi baku da wata damuwa a kan hakan, ɗaukar ɗawainiyarta ba yana nufin gazawarku bane ba, yana nufin nuna godiyarmu da jin daɗinmu ne a gareku, da yaba karamcinku, duk da mun san ba biyanku zamu yi ba".


Abubakar ne ya ce "Shikenan ɗan uwa babu damuwa, Allah ya saka da alkhairi".


Bashir ya ce "Yauwa ɗan uwa Amin, ku gama kintsawa sai a fito da ita ga mota can a waje" yana gama maganar ya fita.


Mai suanan baba ya ce "Malam wannan wane irin abu ne, shikenan sai mu zuba musu ido suna ɗawainiya da mu, bana son nan gaba su yi amfani da wannan damar, su ce zasu juyamu ka san ba zai yiwu ba".


Abubakar ya ce "Haba dai, in sha Allah babu abun da zasu yi".


Sai da rumaisa ta tabattar da mama ta goya Mahmud, wanda take wa laƙabi da Sabir, ta ce saboda haƙurin yaron take kiransa da sabir, tun da suka baro daji bai fiye kuka ba, ba kamar ɗan wata malamarsu ba jarababbe mai kukan masifa.
Suka ɗunguma suka tafi kai rumaisa x-ray, mama na ta fatan Ubangiji Allah ya sa lafiya babu wata matsala.


***
Adam ya idar da salla yana zaune a kan sallaya, yayi shiru ya rasa abun da yake yi masa daɗi, babu tsammani ya ji an turo ƙofar bedroom ɗin sa.
Jabir ya gani, ya shigo bakinsa ɗauke da sallama.
Ya amsa masa a ciki, yau ya manta bai yi wa masu gadi warning na kar su bar kowa ya shigo ba, koma yayi musu ya san basu isa su hana Jabir shigowa wurinsa ba.


"Adam, wai ina ka shiga ne a kwanakin nan, na zo gidan nan ba adadi, bana samunka idan na je can gida ma baka nan, ina ka shiga haka?".


"Ina nan" ya faɗa a taƙaice.


"A'a, ɗan tsaya meyake faruwa ne, ka wani rame, ga fuskarka duk ta kumbura har idonka, menene?"


Tashi Adam yayi ya ninke sallayar, ba tare da ya kula Jabir ba.


"Adam magana fa nake yi maka, ka wani shareni, ni ne fa nake yi maka magana, meya sameka haka?"


"Idan ka tashi tafiya, ka sanarwa masu gadi, kar wanda ya sake zuwa wurina" yayi maganar yana ƙoƙarin hawa gadonsa ya kwanta.


Ture shi jabir yayi ya tsaya a gabansa ya kalleshi ya ce "Kalleni, da Jabir kake magana, har akwai wani abu da kake ɓoye mini a rayuwa? Muna ɓoyewa juna wani abu ne?".


Adam ya dafe kansa ya zauna, yana ajiyar zuciya, ya dubi Jabir ya ce "J, gaya maka matsalata ba shi ne maganinta ba, ka yi mini addu'a kawai".


"Mu kan tattauna abubuwan da suke damunmu a tsakanin mu, ko da bamu da mafita, sai dai hakan yana ƙara mana yarda da juna da jin matsalar ɗayanmu ta dukkaninmu ne, dan haka babu buƙatar ɓoye mini komai".


Adam ya kama hannun Jabir, suka zauna a tare, ya kalli Jabir ya ce "Haƙiƙa ka tuna mini abun da na kusa mantawa, tabbas damuwar ɗayanmu, ta dukkaninmu ce, duk da ina ta ɓoye abun, ban bari kowa ya sani ba, amma a kowane lokaci na san dole komai zai fito, amma a yanzu ku ɗaga mini ƙafa please ".


Jabir ya jinjina kai ya ce "Shikenan" ya fice ya bar Adam, da ganin s yadda ya fita Adam ya san bai ji daɗin abun da yayi masa ba, sai dai shima dole ce babu yadda ya iya.


Sai daf da magariba sannan Bashir suka dawo da rumaisa daga wurin X-ray, yanzu tana iya taka ƙafafuwan ta sannu a hankali.


Sai bayan sallar magariba, sannan Bashir ya yi musu sallama, mama ta yi ta masa godiya da sanya albarka.


Daga nan asibitin bai wuce ko ina ba, sai gidan Adam, ya tarar da shi ya dawo daga masallaci sannan, lokacin an yi sallar isha'i.
Bayan sun gaisa Bashi ya ce "Yauwwa, mun je an yi mata hoton, likita zai ganta gobe in Allah ya kaimu, sannan ya duba idan da yiwuwar a sallameta"


Adam ya ɗago ya kalleshi ya ce "Babu in da za a sallameta sai ta faɗi in da matata take, ko na sanya a tsareta"


Bashir ya girgiza kai ya ce "No, Adams, a hankali zamu bi ta, duk da muna cigaba da ɓata lokaci, kuma can katsinan ma, babu wani cikakken bayani, dan haka na yanke shawarar zamu je da police, kai tun da ban san meye a tsakaninku ba, kamar wasu maƙiyan juna kai da ita, za mu je da masu uniform, wataƙila su ta yi musu bayani, yadda ake ciki sai mu san abun yi".


"Zuwa yaushe kenan?"


'Zan yi magana da Hassan, sai muje ko zuwa gobe in Allah ya kaimu da safe ne".


"Wannan shi ne chance na ƙarshe, idan har ba ta yi magana ba, zan saka ta yi ta ƙarfin tsiya!".


Ayshercool.






*Littafin kuɗi ne, ₦500 via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143*


*Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, masu buƙatar special kuma, suna iya zuwa arewabooks su yi searching.*






Bashir ya ce "A'a, ba sai an kai ga amfani da ƙarfin tsiya ba, zata yi magana a hankali, ƙuriciya ke damunta, amma duk da haka kamar akwai wata 'yar tsama tsakaninka da ita, yanayin abubuwan da take yi maka, kamar da gayyya take yi maka".


Adam ya ɗan yi guntun tsaki ya ce "Manta da ita kawai, sai gobe in Allah ya kaimu, X-ray ɗin na ta babu wata matsala?"


Bashir ya ce "Ai na gaya maka sai gobe in Allah ya kaimu likitan zai duba".


"Allah ya kaimu"


Bashir ya amsa da "Amin".


**
Nusaiba tun da ta ji abun da yake faruwa, ta rasa nutsuwarta, ko abincin kirki ba ta iya ci. Yanzu haka tana tsaka da tunanin da ta saba ta ji Iman ta dafata "Anty Nusaiba" Nusaiba ta ɗan zabura sannan ta sauke numfashi ba tare da ta ce komai ba.


"Anty Nusaiba tunanin me ki ke yi haka ne?"


"Bari kawai Iman, tun da Ammi ta gaya mana zancen nan, na kasa nutsuwa ina tausaya mana idan zancen nan ya fita, kin san yadda aka samu a gaba da ma a masarautar nan, ƙiris ake jira wani abu ya faru, to ga wannan babbar magana gaba ɗaya na kasa nutsuwa, idan har ba Anty Aisha aka gano ba, wallahi muna cikin tashin hankali".


"Haka ne, amma babu abun da ya gagari addu'a anty nusaiba, kuma babu ta yadda muka isa mu kaucewa ƙaddara, in sha Allah babu abun da zai faru".


"Iman, na san kina dakewa ne kina ƙoƙarin kwantar mini da hankali, amma kar ki manta abun da aka gaya wa mutane a kan barinta ƙasar nan, kin san yadda aka sako yaya Adam a gaba, yanzu idan maganar nan ta fasu, babu irin sharrin da ba za ayi masa ba ba shi ba har Ammi da mu baki ɗaya. Shiyasa ni tun farko ban so hukuncin da ammi ta yanke ba, tun da komai muƙaddari ne" ta ƙarasa maganar tana kuka.


Iman ta rungumeta ita ma tana zubar da hawaye ta ce "Na sani Anty Nusaiba, amma Ammi uwa ce, duk abun da zata yi, tana yi ne dan bamu kariya da wanzuwar farincikinmu, kuma in sha Allah ƙoƙarin ta ba zai tafi a banza ba, komai zai zo ƙarshe da yardar Allah, ki daina damuwa, komai zsi zo da sauƙi, ai babu abun da ya gagari Allah" suka cigaba da kuka iman na rarrashin Nusaiba.


Baba uwani ce ta shigo tana sallama, tare da zuro kai. Da sauri suka gyara iman ta amsa mata.


Ta dubi iman ta ce "Uwar ɗakina lafiya kuwa?".


Iman ta ƙaƙalo murmushi ta ce "Lafiya lau baba uwani, akwai wani abu ne?"


"Ni fa na kasa gane muku gaba ɗaya, giwa ta daina walwala, mai gida ma haka, kuma gashi na tarar kuna kuka, dan Allah me kuke ɓoyewa ne meyake faruwa haka? Gaba daya gidan babu daɗi, babu wata walwala saboda yanayin nan da ku ke ciki" Ta yi maganar tana neman fashewa da kuka.


Nusaiba ta ce "Baba Uwani babu wani abu kar ki damu".


Cikin damuwa iman ta ce 'Dan Allah kar ki yi kuka baba uwani, komai zai daidaita ba wani abun bane ba, Ammi jikinta ne ya ɗan tashi shiyasa bata walwala, kuma kin san walwalarta ce ta mu, kar ki yi kuka Please" baba Uwani ta matse ƙwalla ta ce "To shikenan, Allah ya bata lafiya, ya sanya komai lafiya, ya jishe mu alkhairi" tana gama maganar ta juya ta fice.


Iman ta ce "Allah sarki baba uwani, tana sonmu da yawa, bana son in ga masu shiga damuwar nan suna ƙara yawa, Allah ya bamu mafita, ina shirin gaya miki wani abu, wannan maganar ta kunno kai".


Nusaiba ta dubeta ta ce "Wane abun?"


"Ki bari wannan matter ta yi settling, zan gaya miki".


"No, kin san ba zan jure ba, ba zan iya jira ba, ki gaya mini yanzu kawai".


Iman ta ja numfashi ta ce "Kin san me uncle J ya ce mini?"


Nusaiba ta girgiza kai ta ce "Sai kin faɗa".


"Wai so na yake yi, kuma ko ban amince ba zai bi ta in da ya san za a bashi ni"


Nusaiba ta yi murmushi ta ce "Ni na san a rina ai, take-takensa duk ya gama nunawa, amma ke mai ya sa na ga kamar ba kya son shi ne? Mai uncle J ɗin ya yi?"


Iman ta ɗan murza zoben hannunta ta yi shiru.


"Do you still loves him?" Nusaiba ta yi maganar tana kallon fuskar Iman.


Iman ta ɗan waro ido ta ce "Who?".


"Your recent ex, ɗan......"


"Shhhhh" iman ta katseta.


"Kar mu kai ga nan Please, mu bar maganar ma kawai"


Baba uwani kuwa da ke laɓe a ƙofar ɗakin, jin sun sauya hira ya sanya ta tafi tana tsaki "Aikin banza jarababbu, sun ƙi yin maganar gaba ɗaya, zancen da suka yi kuma, idan na kai mata ba so take yi ba, aikin kawai".


***
Adam yana kwance ya ƙura wa roofing ido, sai ya tuna Jabir, abun da yayi masa ɗazu ya tuna, sai ya ji bai kyauta ba, jabir a komai yana tsaye a kan lamuransa, bai kamata ya yi masa haka ba, kuma jabir mutum ne mai kaifin tunani da hangen nesa, sanin ko ya so ko bai so ba zancen zai fit6, ya yanke shawarar ya yi wa jabir zancen, mussaman da suna tare Ruma ta yi masa abun da ta yi masa da farko, tare da saka ran Jabir zai iya samo masa mafita.
Da sauri ya tashi ya fita, ya ɗau mota ya tafi gidan Galadima mai ci.


Sai dai tun a hanya yake kiran wayar Jabir ya ƙi ɗagawa, ya je gida ya tarar Jabir baya nan, sarai ya san in da zai same shi, dan haka bai tsaya ko ina ba sai can.


Ko da Jabir ya ga Adam, ƙoƙarin share Adam ɗin ya yi amma ya kasa.


"Wurinka na zo" Adam yayi maganar yana duban idon Jabir.


"Ina jin ka" jabir yayi maganar yana basarwa.


Adam ya sanya hannu ya ɗago Jabir da kwalar rigarsa, ya ja shi suka fita waje.


"Wai meye haka ka ke yi?".


Adam ya tsuke fuska ya ce "Yaya na zo wurinka in ce wurinka na zo, ka shareni ba ka fini mulki da jin kai ba, na san ka sani".


Jabir ya kalli Adam ya ce "Har ka manta few hours ago abun da ka yi mini?".


"Forget about it, just feel like to share it you"


"Ka riƙe sirrinka, tun da bai kamata na sani ba".


Adam ya dafa kafaɗar Jabir ya ce "Kar ka yi mini yawa mana, yakamata ka saurareni".


"Ina jin ka"


Adam ya ɗan yi shiru, sannan ya gaya wa Jabir abun da yake faruwa.
Sak jabir yayi, gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi, wani irin gumi ya shiga tsatsfo masa ya ce "Takawa, wannan fa ba ƙaramar magana ba ce, case ne mai girman gaske, ni gaba ɗaya sarƙaƙiyar nan ta yi yawa, na kasa ganewa gaba ɗaya, an ce Aisha zata tafi ƙaro karatu, kuma tana Saudiyya rainon ciki, ta dawo ba wanda ya sani an yi garkuwa da ita, ta haihu jariri ya kuɓuta ita ba a san in da take ba, wannan zancen kamar film ko almara ni ban gane ba".


Cikin matsananciyar damuwa Adam ya ce "Bar shi a baka gane ɗin ba, ka san wacece ta zo da yaron?"


Jabir ya girgiza kai, Adam ya ce "Wannan yarinyar da ta zageni a social media, da na yi niyyar hukuntawa ka hanani".


Jabir ya waro ido kamar su faɗo ya ce "Again? Ita a ina ta samu jaririn naka?"


"Wai kai Jabir anya ka ci waec kuwa? Duk bayanin da nake baka ganewa, amma ni babban mamakina bai wuce yadda yarinyar nan take manne da ƙaddarata ba, ita ma an yi garkuwa da ita watannin baya, Bashir ne ya tsinceta a Katsina, a hanyar kai kuɗin fansar aisha, ta zo da ɗankwalin aisha wanda ya ƙara tabattar mini ba ƙarya take yi ba, sai dai duk yadda muka kaɗa muka raya taƙi faɗar komai a kak aisha, kamar tana amfani da hakan ta rama abun da na yi mata ne".


Zamewa jabir yayi ya tsuguna yana maimaita Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Adam kuma yana tsaye yana murza yatsunsa ya na jin yadda hawaye ke cika masa ido.


Sai da Jabir ya gama salallaminsa, sannan ya tashi tsaye, ya dubi Adam ya ce "Yanzu ba lokacin tattauna wata magana ba ce, babu isasshen lokaci, dole a nemo in da aisha take kan kowa ya ji wannan zancen, gashi ka ce sun daina kiranka a kan kuɗin fansarta".


Adam ya jinjina masa kai alamar eh.


"Ka ga, maza mu je mota, muje Asibitin".


Haka Adam ya ɗauki Jabir suka tafi wurin rumaisa.


A can unguwa kuwa, mama na nan suna ta fama da jinyar rumaisa, amma maganar jaririn nan ta cika gari, kasancewar mama babu wanda suka yi wa bayanin in da rumaisa ta samo jariri, ko a 'yan uwa ba kowane ya sani ba.
Wasu suka din ga cewa ciki rumaisa ta yi, shi ne aka kaita wani wurin ta haihu, dama wannan shegiyar fitinarta ta da rawar kai ta yi yawa, tsaf zata aikata, ba su yi la'akari da irin raunukan da suke jikinta ba, wasu ma cewa suke yi, ba wani saceta da aka yi, rainon ciki ta yi. Ya yin da wani sashen suke cewa gaba ɗaya rumaisa ba ta yi kama da wadda ta ɗau ciki ta haihu ba, dan a yadda take ɗin nan, idan ma cikin ne, abu ne mai wahalar gaske ace ta iya haihuwa da kanta, haka unguwa ta ɗauka, wasu suna sukarta, wasu suna bata kariya, sai dai su mama sam basu sani ba, dan ko a gari babu wanda ya iya tarar zaratan samarin nan ya yi musu zancen.


Yanzu ma mama na ta shirin su kwanta, ruma ta sha magungunan ta, tana ta shafa dogon gashin jaririnta, tana kallon dogon hancinsa.


"Meyasa ka yi kama da babanka, dama babarka ka yi kama, da ka fi haka kyau boy na" ta yi maganar tana kissing ɗin sa a goshinsa, tana murmushi da jin soyayyar Sabir na shiga zuciyarta.


Yaya Abubakar ya dubeta ya ce "Mama boy, zan tafi gida, gobe in Allah ya kaimu zan biyo mu yi sallama, zan koma school zamu fara exams".


Ruma ta ɓata fuska ta ce "Dan Allah kar ka tafi, bana son ka tafi".


"Ki hi haƙuri, exams ɗin nan ce zata saka na koma, ba dan haka ba a kusa da ke zan kasance in ta kallonki gudan jinina"
Ta yi murmushi ta ce "Allah ya bayar da sa'a"


Mama ta ce "Ka zo ka tafi kar ka yi dare"


"To mama, ban gaji da ganinku bane" kan mama ta yi magana Adam suka shigo.


Ruma ta kawar da kai tana faɗin "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" domin ta gaji da ganin takawa, da kullum sai ya zo sau biyu, kuma duk zuwa sai ya ɗaga mata hankali a kan ta gaya masa in da Aisha take.
Ba ta ƙara haɗe rai ba sai da ta ga Jabir, sarai ta gane shi, da shi aka haɗa baki Adam ya ɗaukota yayi mata wulaƙanci.


Cikin girmamawa suka gaisa da ammi, yayin da jabir ya ƙurawa rumaisa ido, da ta haɗe rai.


Suka gaisa da Abubakar ma, da yake tsaye yana shirin tafiya.


Mama ta ce "Ana ta ɗawainiya da rumaisa fa, mun gode sosai Allah ya yi albarka, ya shiga lamarin ka ya kareka da ga sharrin maƙiya".


Adam ya ce "Bakomai mama, yi wa kai ne, ki daina godiya ma, addu'a muka fi buƙata"


Rumaisa a ranta ta ce "Ji shi, wai mama sai ka ce babarsu, dan tsabar kuturun iyayi, wallahi mamanmu ce kawai" ta yi maganar a zuciyarta.


Abubakar ya ce "Ruma baki iya gaisuwa bane?"


Ta ɗago ta ce 'Au wai baƙi mama ta yi, sannunku"


"Ya jiki kuwa?" Jabir yayi maganar yana kallon ruma.


"Da sauƙi".


"Ai da yake ban san meyafaru ba, sai yau, shiyasa bamu zo da shi na dubaki ba, mu ga jaririn"


Maimakon ta miƙo shi, sai saka hannu ta dafe shi, tana harare-harare.


Abubakar ya matsa ya ɗauko masa jaririn, ya bashi sannan ya fara yi wa ruma mita "Wai ke wace irin yarinya ce ne? Ke shikenan ba wanda zai taɓa yaron nan sai ke, ke da kece uwassa ban san yadda za'ayi ba".


"To ai nice mamansa, ai dai bar mini shi ta yi".


Ya ce "Ke tafi can, ke ma ɗin ai Haryanzu rainonki ake yi, mama bari na wuce na je gida na haɗa kayana"


"Yaya Sadik, sai da safe ka gaishe da su"


"Ba yanzu duk suka tafi ba, duk kuna tare sai da safe, ban da yi wa mama rigima dan Allah, a bari sai mun zo mu ayi mana" murmushi ta yi Abubakar ya kama hanya ya fita.


Jabir ya zubawa yaron ido, Adam da ke zaune a gefensa ma, ya zuba masa ido yana saƙa abubuwa daban daban a ransa.


Mama ta juya tana amsa waya, ruma ta lallaɓa a hankali ta sauko daga kan gadonta, ta saka hannu ta ɗauke jaririn daga hannun jabir, a gabansa ta ce "A'uzubi kalaimatillahi tammat" ta ƙarasa gadonta ta kwantar da jaririnta, ta hau gadon tana ta haɗe fuska.


Adam ya ɗan kalli jabir, kallon irin ka gani ko?.


Jabir ya girgiza kai ya ce "Rumaisa, na ji duk abun da ya faru, ina fatan Allah ya tsare gaba, amma yakamata ki bayar da haɗin kai wurin kuɓutar da maman yaron nan in dai kina ƙaunar ɗan ta da gaske, da haka zaki tabattar mana son gaskiya ki ke wa ɗan ta".


A wulaƙance rumaisa ta kalli Jabir ta ce "An gaya maka ina abu dan na burge mutane ne? To kar Allah ya sa ku yadda ɗin mana ina ruwana, wataƙila shi sai in gaya masa kai ban gaya maka ba, mugwaye kawai, kuma ni ba dan ta bar mini jaririn nan ba, ba abun da zan yi da ɗan ku, dan ni bana ko ɗaukar yara, idan aka bani riƙon ɗa ma, mintsini yake sha da cizo, wannan kuwa ɗana ne, ba wanda ya isa ya ƙwace mini shi ehe" ta yi maganar tana fari da murguɗa baki".


Jabir ya ce "Kan uba, haka ki ke?"


"Ai na fi haka ma, idan kun gama zaman kwa tafi, ko ku cigaba da zaman jirana in gaya muku in da take, tun da ni na saceta" tana gama maganar ta juya ta kwanta.


Jabir ya riƙe haɓa yana jinjina kai, Adam kuwa tuni ya fusata ya tashi fuuuu ya bar ɗakin, a waje ya tarar da mama yayi mata sallama suka wuce.


A mota Jabir yake cewa Adam "Ban taɓa zaton azabar taurin kan yarinyar nan ya kai haka ba, ji yarinya ƙarama da iya shege".


"Shawarar da bashir ya bayar, ita ce last option ɗina, idan taƙi ba da haɗin kai, zan yi abun da ba ta zato" a haka suka tafi gida suna tattaunawa.


Washegari da safe Ammi ta shirya, zata asibiti Nusaiba da Iman sun so bin ta, amma ta ce a'a su yi haƙuri ba yanzu ba, ta saka aka sheƙa girki, ta saka a mota, tana shirin shiga motar su tafi, ta ji yo muryar Mummy "Giwa, waye Babu lafiya ne na ganki da kulolin abinci da safiyar nan? Ko wani ne a cikin yaran amma ki ke ɓoye mini?"


Ammi mamaki ne ma yakamata, ya aka yi ta fito da sassafe haka, har ta ganta.


'Ba ɗaya yara duk suna lafiya, wani abu ne mai muhimmanci" daga haka Ammi ta shige motar, ba tare da sake tanka Mummy ba.
Mummy ta riƙe ƙugu ta jinjina kai ta ce "Lallai ta tabbata akwai abun da ki ke ɓoyewa giwa, kuma da alama yana da muhimmanci a wurinki, bari mu ga idan na bankaɗo ko menene in da zaki saka kanki, zan saka a bi bayanki, domin ganin in da ki ke zuwa"


Rumaisa tana jin zuwan Ammi, suna ta hira ita da mama, amma ta yi bakam kamar bacci take yi, alhalin idonta biyu maganar ce kawai ba ta son yi.
Sai da likita ya shigo, sannan ta tashi suka gaisa da Ammi, likita ya duba X-ray ɗin ta ya ce babu wata matsala, haƙararin nata ma buguwa ce kawai, zai rubuta mata magani.


Mai sunan baba ma tuni sun zo, tare da Abubakar ya biyo yayi musu sallama zai koma makaranta.
Ammi take tambayar mama ko 'yan biyu ne saboda kamanin da suke yi, ba ta gane su, kawai dai ta lura da ɗaya yana da fara'a ɗaya baya yi.
Mama ta ce "Eh 'yan biyu ne, Abubakar da mai sunan babana, shi ne sa, ba ka dariya sai hamma".


Ammi ta yi murmushi ta ce "Tubarkallah Allah ya ray miki, familynki sun burgeni sosai da sosai, rumaisa a yayyen nan naki ki bani biyu mana, na je na ƙara da nawa yaran mana, ni nawa duk rasuwa suke yi, saura uku a raye"


Mama ta ce "Allah sarki, Allah ya raya wanda suka rage, ya jiƙan wanda suka rasu".


Ammi ta amsa da Amin.


Aka zubawa ruma abinci, Abubakar yana bata a baki, tana ta shagwaɓa.


Bashir yayi sallama, da shi da 'yan sanda huɗu cikin uniform.


Ruma ta tsaya cak tana bin su da ido, nan suka gaggaisa da kowa, Ammi ta bi bashir da kallon ko lafiya.


"Maman Boy, ya jiki? Yau zaki ganni da police, su ne case ɗin binciken aisha yake hannunsu, dan haka za su yi miki tambayoyi ne" a take rumaisa ta haɗe rai, ta kawar da kanta gefe.


Ɗaya daga cikin 'yan sandan ya ce "Baby

Please Login or Register in order to submit comment