Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa, "ba zaki taso mu tafi ba kin tsaya kina kalle-kalle?"


Cikin tsiwa ta ce "Eh ba za'a taso ba ɗin ni na gayyace ka?" Tayi maganar a fili, tana buɗe ido, tsaki tayi tana ƙoƙarin gyara kwanciyarta ta ce "Aikin banza, ko me yake kawo shi mafarki na oho, idan na kuma ganinka a baccina, sai na yi maka rashin mutunci, dan wallahi sai na rama abin da ka yi mini"


"Ke da waye ne baby rumaisa"ta ji muryar anty aisha.


Ruma ta sake buɗe ido ta ce "Ba kowa".


"Haba dai ba kowa, tun ɗazu ki ke surutu fa kina masifa a cikin bacci, har wancan yake cewa zai taka ƙafarki ki tashi,"


Duk da duhu ne, Ruma ta zare ido ta ce "Haba dai, me nake cewa?"


Aisha ta ce "Ina ta fama da kaina ban riƙe ba, amma dai faɗa ki ke da wani a bacci"


Ruma tayi ajiyar zuciya ta ce "Wani mara kirki ne yake zuwar mini, taimako ɗaya Allah zai yi masa, shine na mutu a wurin nan, amma muddin na fita ko ni ko shi, sai ya gane bashi da wayo"


Anty Aisha ta ce "Subhanallah, me yayi zafi haka?".


"Baki san rashin mutuncin da yayi mini ba, nonona ya taɓa mini, kuma mama ta ce duk wanda ya taɓa nan wurin na zama 'yar iska cikin shege ne zai fito mini"


"Ya salam, ke ya aka yi ya kai hannunsa nan wurin?"


"Sa wa yayi aka ɗaukoni, wai zai yi mini warning, ya shaƙo hijjabina ya taɓa wurin, ni kuwa na din ga bin diddigi sai da na gano gidansu, na je na rubuta masa wasiƙar rashin mutunci na ce a bashi"


"Kai ruma lallai jan wuya ke ce, irin wannan ƙarfin hali haka?"


"Rabu da shi, ai wallahi ya bari na fita daga wurin nan zai gane kurensa, Anty Aisha wai ke a wani gari kike?"


"Zan gaya miki ruma, na san zuwa yanzu labari ya samu mijina da dangina abin da ya faru da ni, sai dai ban ga alamar kuɗin fansa suke so ba,. Tun da sun ƙi yin waya su faɗi abin da za s bayar idan.... Ba ta ƙarasa maganar ba ta riƙe ƙugunta ta ce "Washhh"


A ɗan rikice ruma ta ce "Sannu Anty Aisha, kwanta a kan cinyata ki miƙe ƙafar to".


"A'a kar na hanaki bacci baby ruma, yi kwanciyarki".


Ruma ta ce "A'a ai ba zan iya komawa ba kwanta".


A hankali Aisha ta ja jikinta ta kwanta a kan ƙafafuwan rumaisa, Ruma ta ce "Bari na yi miki tsifa, kin san ni nake yi wa mama tsifa har kitso na iya" Aisha ba ta hana ruma ba, ta dinga jagwalgwala mata gashi, sai dai duk da mawuyacin halin da take ciki, ruma dariya take bata, dan sam ruma ba ta da rufi.


"Anty Aisha ina son in ga kina dariya, daɗi nake ji, tun da ki ka zo wurin nan na rage damuwa duk da ina missing ɗin gidanmu, in sha Allah idan Allah ya ƙaddara muka bar nan, ko a wane gari ki ke zan zo gidanki".


Tayi murmushi ta ce "Nima haka ruma, tun da na zo wurin nan, kawai nake jin ki a raina, nake kuma sarawa jarumtarki, sai dai babu lallai na bar wurin nan a raye haka jikina yake bani"


"Ɗaga mini cinyata tun da ba zaki daina wannan maganar ba" ruma ta faɗa rai a ɓace.


"Haba ruma, ni ɗin ki tsaya ki ji mai zan gaya miki, idan ma na mutu lokacina ne yayi kuma zan yi shahada". Ruma ta ture kan Aisha daga kan cinyarta ta tashi ta ce "Sai ki je ki yi ta shahadar ai, ba zan sake kulaki ba"


Kowa yayi bacci, sai masu gadi da su ruma ne idonsu biyu, da wani ne yake wannan surutun cikin daren nan, da yanzu ya sha tijara ƙila a haɗa masa da duka ma, amma kasancewar rumaisa ce take magana ba wanda ya kulata, dan yanzu da an taɓata zata hau kwarmato, idan kuma ba a isa ayu mata wani abun ba kamar tayi musu asiri.


Ɗayan ya kalli ruma da ta tashi zata canza wuri daga kusa da Aisha, ya ce "yau kun yi faɗa da uwar taki ne?"


"To meya dameka ne, ka cigaba da gadinka mana, sa ido sana'ar banza".


"Ni ki ke cewa sa ido sana'ar banza, dan kin ga ana ƙyaleki?"


"Ai wallahi ko me zan yi, baku isa ku yi mini wani abu ba, addu'a nake banka muku ta ko ina, in gaya maka, ka san wani abu kuwa?"


"Bana son ji, wuce ki nemi wurin kwanciya".


Ruma ta ƙarasa wurin da suke zaune sun kunna wuta, wasu suna shaye-shaye, ta zaune a gefansu ta ce ta yi ƙasa da muryarta ta ce"Ka san meya haɗani da anty aisha muka yi faɗa kuwa? Cewa take yi wai zata mutu ta tafi ta barni, shine ta bani haushi"


"To ina ruwana? Sauran da suka mutu meyasa baki damu ba?"


Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Tana sona ne wallahi, nima kuma ina sonta, dan Allah ku saketa, ko ku kai ta asibiti ba ta da lafiya"


Ya ce "Wallahi na yadda addu'a ki ke yi mana, ko kuma daga can gidanku ake yi, ban da haka ba a taɓa kawo ɗan iskan mutum mara tsoro irin ki ba".


"A'a nifa ba 'yar iska bace, so nake ku kasheni, amma kun ƙi ya zan yi, kalli yadda na koma kamar 'yar jari bola, wataran a gidamu mama sai ta yi mini wanka sau biyu a rana, amma yau ban san adadin kwanakin da na shafe ban yi wanka ba, tun ina warin har na daina".


"To ai ko ni ma sai na yi miki wankan, akwai kogi a gaba"


Aisha tana daga can nesa, amma ko ƙifta ido ba ta yi a kan ruma, dan kar wani abu ya faru, ruma tayi zaman dirshen sai zuba take, duk da ba ta san mai ruman take cewa ba, amma hirarta kawai take yi da su hankali kwance.


Ba ta sake bi ta kan Anty Aisha ba, har aka yi sallar asuba, ruma ta yi salla tayi kwanciyarta bacci.


***


"Mummy, wallahi na san in da maganin nan yake, a ɗakin iman yake, kuma na sake tabattar da takawa yana nan da wannan ciwon mai kama da na aljanu, mai kuma kama da na hauka"


Mummy ta kalli Fauziyya a tsanake ta ce "Fauziyya, bana son shirme da ƙarya fa".


"Haba mummy, kamar wata ƙaramar yarinya, kin ga yadda ya shaƙe iman a ɗakinta kuwa, ya ɗage mata riga baki ga ba"


Mummy ta yi murmushi ta ce "Kin tabattar kin ga in da maganin yake? Idan kin tabattar ina son gaya wa uwani ta kawo mini shi, dan da maganin wannan malamin yace zai mini aikin da zai kawo ƙarshen hankali a jikin adam, kin ga ba shi ba sarauta kenan"


"Wallahi mummy na gani, sai dai akwai mukulli a drower mudubinta ne"


"Fine, kafin nan, ina son ayi raising issue na cewar yayi yinƙurin yi wa iman fyaɗe, wani sashin kuma ace an kama shi shi da ita, hakan zai ƙara ɓata sunansa, da yi wa zuriyar binta baƙin jini a cikin masarautar nan"


Fauziyya ta ɗan yi jimm sannan ta ce "Anya Mummy, decision ɗin nan naki bai yi tsauri ba kuwa?"


"Ban gane tsauri ba, duk wannan fafutukar ba dan ku nake yi ba, ki shiga hankalinki fa"


"Am sorry, ba zan sake ba duk hukuncin da ki ka yanke dai-dai ne"


Mummy ta yi ƙwafa ta tashi ta fice.


***
Habiba ƙawar ruma kullum sai ta je layinsu ruma, ta tambaya ko an ga rumaisa, dan tsoron zuwa gidan su ruma take saboda yayyen ruma, tsoro suke bata, ita a da can ma idan ba dole ba ba zuwa take yi ba, balle yanzu da suke cikin damuwa da tashin hankali.
A ƙofar gidan su ruma take tsaye tana leƙe.


"Me ki ke dubawa ne?" Ta ji muryar usman.


Da sauri ta waiwaya tana kallonsa.


"Me ki ke yi a nan?" Ya maimaita.


Habiba ta ce"So nake na ji ko zan ji yo muryar ruma ta dawo"


Cikin sanyin jiki usman ya ce "Ruma ba ta dawo ba Habiba, na san kina yi mata addu'a, to ki cigaba kar ki daina dan Allah".


Hawaye ya cika idon habiba za ta yi kuka, usman ya ce "Kar ki yi kuka kin ji, maza tafi gida kar a neme ki kin ji"


Haka nan ta juya ta tafi gida.


***
Ruma kuwa sai da rana ta take, sannan ta tashi daga baccin da take yi,ta tashi zaune ta ɗaga kai suka yi ido huɗu da Aisha, amma rumaisa ta kawar da kanta gefe taƙi kula Aisha.
Sai dai a kallo ɗayan da ruma tayi mata, ta hango damuwa a fuskar aishan.


Gaishe da mutanen wurin tayi, ta koma gefe ta tattara duwatsu ta hau 'yar carafke.


"Sannu rumaisa, ke rayuwarki baki da wata damuwa, yau ba kya jin yunwar ne?" Cewar wanda suke kira da sha tara.


"To kun bani abincin ne?"


"Ga abinci nan barde ya kawo miki kina bacci"


"Nifa na gaji da buredin nan ba yau ba gobe... Au ashe waina ce yau" tayi maganar tana murmushi, yayin da mutane suke kallon tsabar samun wuri da ruma ta yi.


Ta koma gefe da nufin ta fara ci, suka yi ido huɗu da Aisha ta zubo mata ido,haka nan ruma ta ji jikinta yayi sanyi, dan haka ta tashi ta je gaban Aisha ta zauna ta ce "zo mu ci"


Aisha taƙi magana, kawai ta zubawa ruma ido.


"Mu ci mana" ruma ta sake maganar tana kallon idon aisha, amma ga mamakinta taga hawaye a kwance a cikin idonta.


"To Meyasa kuma zaki yi kuka?" Ruma tayi maganar kamar ita ma ta yi kukan.


"Meyasa ki ke fushi da ni ruma? Na ji daɗin kwanciyar da na yi a kan ƙafafuwanki, har na ji ina son yin bacci, amma ki ka tashi ki ka barni" tayi maganar cikin damuwa.


Ita ma ruma cikin damuwar ta ce "Ba ke ce ki ke cewa zaki mutu ba, na gaya miki kuma bana so".


"To na daina, amma ki matso kusa da ni in kwanta a kan ƙafarki, ko zan ɗan ji daɗin kwanciyar, kwana na yi ina ciwon baya da ciwon mara, ƙafafuwana kamar ana sara mini su"


"To mu ci wainar, sai ki kwanta"


Ta girgiza wa ruma kai, ta karkata da ƙyar ta kwanta a kan cinyar ruma, sannan ta kalli ruma ta ce "Har na ji daɗi, mu daina faɗa dan Allah ƙawata, gurin nan yana bani tsoro, da sakani cikin damuwa ke kaɗaice ƙwarin gwiwata, idan na ganki nake jin daɗi, kuma ko ina cikin damuwar barkwancinki na sakani nishaɗi".


Murmushi ruma ta yi ta ce "Ni wallahi idan ki ka ce baby ruman nan, sai na ji kamar na fara rarrafe da shan hannu, kamar wata jaririyar zanin goyo, wai da mama baby take ce mini da har a yanzu sai na din ga fitsari a wando, zan zuba taɓar wallahi".


Cikin dariya Aisha ta ce "Ki gauraya da mai sunan baba ba" tare suka cigaba da dariya, kamar babu abin da yake damunsu duk su biyun. Can aisha ta ce "Wai ina ɗan kunnenki, na ga kunnenki babu yari".


Ruma ta haɗiye lomar wainar da ke bakinta ta ce "Ai ni ina ga sai salla salla nake saka ɗan kunne, nifa kamar su Huzaifa haka nake yawona, dan da za a barni, zan iya yawo da gajeren wando a cikin unguwa, in je ayi mini askina"


Aisha ta girgiza kai ta ce "Ruma idan na biye miki, sai ki saka na fara naƙuda yanzu" ta saka hannu ta ciro ɗan kunnayen kunnenta, ta sakawa ruma.


Ruma ta yamutsa fuska ta ce "Ni fa bana son ɗan kunne, idan suka dameni tsaf zan ciresu na watsar"


"Ruma kin san kuɗin abin da na saka miki a kunnenki kuwa? Gold ne tafiyayye daga dubai, dan Allah kar ki yar".


"To ni me zan da shi?" Ruma ta tambaye ta tana shafa kunnenta.


"Bar miki na yi, ga wannan ma, ta miƙawa ruma ɗan kwalin kayanta, ta ƙulle wani abu a ciki ta ce "Sarƙar ɗan kunnen ce, da zobuna da kuma sarƙar ƙafa".


"To su kuma me za ayi da su?" Aisha ta ɗan yi shiru, daga bisani kuma ta ce "Ajiya ce na baki, zan karɓa, idan kuma ban karɓa ba na bar miki"


"To ni yanzu wannan ajiyar taki, a kaina zan ɗaurata ko kuma ƙuguna zan ɗaurawa, dan tsaf zan manta ya kama gabansa na kama nawa"


"Amana ce fa, ki kula da su sosai" ruma ta takurawa aisha sai da ta ɗan ci wainar nan, amma kallo ɗaya zaka yi wa aisha ka san bata da lafiya, amma sai ƙarfin hali take tana biyewa rumaisa.


A 'yan kwanakin nan kusan kullum, akwai kalar mutanen da suke zuwa wurin nan, wasu idan sun zo su ɗauki manyan jakunkuna.
Yau ma wasu ne suka zo a babura kusan huɗu, amma su waɗan nan sanye da baƙaƙen coat, suma fuskokinsu a rufe, ruma ba ta damu da su ba, ta mayar da hankalinta kan aisha, tana fatan kar ƙarar baburan nan nasu ya tasheta.


Bayan mutanen sun tattauna da waɗanda suka sace ruma, kai tsaye aka nuno musu in da su ruma ke zaune, suka tunkari su rumaisa.


Tsayawa ruma ta yi taga ikon Allah,wurin wa aka zo, wurinta ko kuma wurin Aisha....


Ayshercool




*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*


*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*


*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*


👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*


*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*


*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*


*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*


*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*


*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*


*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*


*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*


*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*


*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*


*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*


*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*


*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*


*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*


*15. Supplement for Acne, dark spots remover*


*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*


*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*


Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*












Cigaba da tunkaro su ruma suka yi, ruma kuma ta tattara hankalinta ta ga me za ayi.
Suna zuwa suka kewaye su rumaisa, ɗaya daga cikin su ya sanya hannu zai ɗaga Aisha, amma ruma ta saka hannu ta kare, ta ce 'Wai me zaka yi mata? Matar aure ce fa yaya zaka taɓa ta?".


"Ke, ni ki ke yi wa wannan maganar?" Ya kuma kai hannu zai janyo Aisha, amma ruma ta riƙe hannunsa. Jin hayaniya ya sanya Aisha motsawa a hankali ta buɗe idonta, ta kalli mutanen da ke tsaye a kanta, ta yinƙura da ƙyar ta tashi zaune ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un Lafiya?"


A karo na uku, mutumin ya kai hannu ya danƙi Aisha, ya fara janta, ruma kuma ta miƙe zata bi bayansa, ɗaya daga cikinsu ya danƙo ruma, yayi jifa da ita a gefe ya saita ta da bindiga.


Da sauri sha tara ya ce "A'a kar ka kuskura ka yi mata wani abu, akwai yarjejeniya tsakaninmu da ƙungiyar su barde, mun yi yarjejeniya a kanta, muddin wani abu ya sameta zamu yaƙi juna, babu ruwanku da ita, zan riƙe muku ita, dan ba zata yarda ta bari ku yi aikinku ba".


Yayi maganar tare da ƙarasawa ya danƙo ruma, aikuwa ta hau bori, tana kiran Anty Aisha, Aisha kuwa ta kasa magana, sai miƙawa ruma hannu take yi, mutumin nan kuwa babu imani sai janta yake yi.


Cikin gigita ruma ta ce "Dalla ka cikani, suwaye su me zasu yi mata?"


Sha tara ya ce "Ke a shegen shishshigin ki, zaki jawa kanki abun da ba shikenan ba" kan ruma ta kuma yin wata maganar, sha tara ya watsa wa ruma wani abu a fuska, ta silalale a wurin nan, tana gani sama-sama.


***
"Uwani ki buɗe kunnenki da kyau ki ji ni, bana son a wannan karon a samu wata matsala, ki yi mini aikin nan yadda yakamata"


Baba uwani ta risuna ta ce "In Allah ya yarda ba zan bari a samu wani kuskure ba uwar ɗakina".


"Yauwwa, aikin da na saka ki ki ka kasa, Fauziyya ta yi mini rabin aikin, dan haka ƙarashe ne zaki yi yanzu, Fauziyya ta tabattar mini da ta gano in da maganin nan yake, yana ɗakin iman, a cikin drowern mudubinta, dan haka duk yadda zaki yi, ki samo mukulli ki buɗe wardrobe ɗin nan, ki ɗauko mini, akwai wani aiki da za ayi mini, wanda lallai sai da shi".


Baba uwani ta ɗan yi shiru tana nazarin yadda za ta ɗau wannan kasadar.


"Ya ki ka yi shiru ko ba zaki yi ba?"


"Wace ni? Ki ƙaddara an gama wannan aikin uwar ɗakina, zan yi da iznin Allah".


"Ai na zata ba zaki yi bane, sai kuma abu na biyu, wata jita-jita nake son ki yaɗa mini a gidan nan, na san daga nan har masarauta kowa zai ji, dan duk wani mufurci ku hadimai kun iya shi. Ina son ki je ki yayata cewar, Adam ya yi shaye-shaye ya bugu ya tashi yinƙurin yi wa iman fyaɗe!"


Ras! Gaban baba uwani ya faɗi, ta gyara zamanta ta ce "Uwar ɗakina, fyaɗe kuma?"


"Eh, ko baki ji ba?"


"Allah ya baki yawan rai, na ji zan kuma aiwatar"


A wulaƙance "Mummy ta ce "Tashi ki je"


Jiki a sanyaye baba uwani ta tashi ta bar ɗakin.


A hanyar komawa sashinsu ta haɗu da baba sabuwa, sabuwa ta ƙure uwani da ido, uwani ta ce "Lafiya ki ke yi mini wannan kallon haka?"


"Lafiya lau, kawai ina tunanin ranar da dubunki ta cika ya zaki yi? Baiwar Allah can ta yarda da ke ta baki amanar kanta da ta 'ya'yanta kina ci, duk wahalar da take yi miki"


A fusace baba uwani ta ce "To ina ruwanki, bana son saka ido fa, wallahi idan ba ki yi wasa ba, sai na gaya mata ta ɗau mataki a kan ta".


"Wallahi ki ka gaya mata, kan ta ɗau mataki a kaina zan ɗauka a kanku, dan sai na ja abun da za'a ɗauremu duka, dan nima na san sirrinta tana sakani aiki, ni idan nayi mata babu laifi, dama hadimarta ce ni, ke kuwa fa? Ki dai ji tsoron Allah wallahi" ba ta jira me baba uwani za ta ce ba, ta tafi ta bar wurin.


Hajiya Jamila ɗawisu sarkin ado, sukari ba ka yi farin banza ba, gugar ƙarfe sha kwaramniya. Haka hadimanta suka shiga jera mata kirari, sai dai babu wanda ta kula ta cigaba da takunta ɗai-ɗai ta nufi sashin Ammi.


Ammi kuwa na zaune ita da Adam a ɗakinta, yana zaune a gabanta ya sunkuyar da kansa, sai dai duk ya rame, cikin nutsuwa da tawakalli Ammi ke yi masa nasiha.
"Har kullum Adam ba zan gaji jadadda maka batun yin addu'a ba, addu'a na da muhimmanci a rayuwarka, tun da na haifeka a cikin jarrabawa ka ke, ko in ce muke, ka ƙara haƙuri wannan ma zamu cinyeta da yardar Allah, ka yi haƙuri ka jure, na sani akwai ciwo amma ka sani, jarrabawa alamar soyayya Allah ce ga bawansa, kullum cikin Addu'a nake maka, har abada maƙiyanka fadawanka ne, waɗanda ka sani da wanda ba ka sani ba, Allah zai ije maka su in dai har kana Addu'a, ni dai fatana ka rage zafin zuciya adam, babu in da zuciya zata kai ka, ka din ga haƙuri da yanayin da duk zaka tsinci kan ka" wata hadimar Ammi ce ta nemi izini ta shiga, ta sanarwa da Ammi zuwan Mummy.


Sai da gaban Ammi ya faɗi, ba ta ƙaunar abin da zai haɗata da Mummy, dan ba ƙaramin fargaba take shiga ba, ƙarfin Addu'a ne yake sanya ta iya riƙe kanta.
Jiki a sanyaye ta tashi ta fita falo, ta tarar da Mummy a zaune a falon tana yi wa iman magana, sai dai ba ta kai ga jin abin da take cewa iman ɗin ba ta yi shiru.


Ita kanta iman ba ƙaramin tsoron Mummy take ji ba, saboda haɗuwarsu babu daɗi sam, ta tsaneta sosai da sosai.


Fuskar iman Ammi ta kalla, ta san akwai wani abu da Mummy ta gaya mata, da ya sanya Iman shiga ruɗi, dan fuskar iman kullum idan ba murmushi ba, to tabbas shagwaɓa, amma sai ta ga iman a razane.


Mummy kuwa na ganin Ammi ta faɗaɗa murmushin ta, ta risuna ta ce "Allah ya taimaki giwa, barka da fitowa".


Ammi ta nemi wuri ta zauna, ta ce "Barkan ki dai, kuna lafiya?"


"Eh to, mun gode Allah sai dai ba na ce lau ba, yara babu wanda yake zuwa, duk sun ɗauke ƙafarsu".


"Kin san yanayin makaranta, ba sa samun zama shi ne kawai".


Mummy ta yi murmushi ta ce "Haka ne, dama yara ne suka zo mini da batun rashin lafiyar takawa, na ce bari na zo na yi masa sannu, Allah ya bashi lafiya, amma gaskiya yakamata ki tashi ki nema masa magani, shi da ake sanya ran ya gaji mahaifinsa, amma ya din ga abu kamar mahaukaci, gaba ɗaya zance ya cika masarauta har kunnen manya".


Kalmar mahaukacin da ta kira Adam da shi, ba ƙaramin dukan Ammi ya yi ba.


Amma ta maze ta ce "Ai shi lamari irin wannan, duk maganin da zaka nema, lafiya ta Allah ce, idan ka miƙa masa lamarinka kuma, sai ya kawo maka mafita, tun da shi ya halicci kowa".


Mummy ta ɗan kaɗa ƙafa ta ce "Haka ne, akwai wasu ɗabi'unki da suke burgeni, wanda har nake koyi da su, ƙarfin hali da yarda da kai, bari mu gani idan yana da rabon warkewa, Allah ya bashi lafiya, na barki lafiya uwar masu jiran gado" ta miƙe tana wani irin

Please Login or Register in order to submit comment