Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba biya suke yi ba, an riga an ɗau nauyin lafiyar rumaisa a aljihun takawa, dan tun da bashir ya ji yaron nan na Adam ne, ya sanya aka canza musu asibiti zuwa babban asibitin kuɗi, domin samun kulawa ta musamman tun da ya san adam yana da kuɗin biya, ko magani likita ya rubutawa ruma, sai dai kawai a ɗauko a kawo musu, sai dai wanda babu su je waje su saya.


***
Tana zaune a kan katafaren gadonta, sai shirya mata kayanta mai aiki take a cikin akwati, dan ta ƙallafa ranta a kan tafiyarta Abuja nan, sai ba wa mai aikin umarni take cikin isa da kuma gadara gami da wulaƙanci.
Samha kenan akwai gayu da ƙwalisa, sai dai babu hali mai kyau, ɗaya daga cikin wayoyinta ta duba ba ta gani ba, ta js ɗan gajeren tsaki, ta fita ta tafi ɗakin mama.
Mama ta tarar tana ta ƙananan surutai tana mita. "Mama na bar Samsung ɗina a ɗakin nan ne?".


"Ke ni rabu da ni da wata wayarki, turaki ya ɓata mini rai".


Samha ta ce "Too ikon Allah, mai Baban kuma yayi miki?"


"Manta kawai, jirgin ƙarfe nawa zaki bi?"


Samha ta ɗan yi ajiyar zuciya ta ce "Ƙarfe biyar na yamma, amma ki din ga haƙuri mama, kin san tsufa yana taka muhimmiyar rawa a kansa yanzu, idan ki ka matsa zaki yi ta damuwa ne ranki yana ɓaci".


Ɗan shiru mama tayi sannan ta ce "Abun nasa dai ba tsufa bane, ba wani tsufa kawai halinsa ne, ina yi masa maganar wani abun daban, amma yana nuna mini maganata ba ta da muhimmanci yana kawo mini nasa zancen da bai shafeni ba".


Samha ta yi murmushi ta ɗau wayarta ta ce "Na san tatsuniyar gizo ba ta wuce ƙoƙi, yakamata ace zuwa yanzu kin saba mama, ki yi haƙuri, bari na je na cigaba da shirina" daga haka ta fice ta koma ɗakinta.


***
Abubuwa suka cakuɗewa Adam gaba ɗaya, kallo ɗaya zaka yi masa ka san a cikin tashin hankali yake da matsananciyar damuwa, Ammi ta ce sam ba ta yarda ya je gidansa ya zauna shikaɗai ba, don tun da ya shiga damuwar nan take cikin fargaba, kar ciwonsa ya tashi abu ya ƙara haɗe musu.
Yau da safe Ammi da kanta ta je ta saka Adam a gaba a kan ya ci abinci amma ya kasa ci, sai da ya ga ta matsa sosai da sosai sannan ya ɗan cakali kaɗan ya bar shi.


Ammi ta dube shi a tsanake sannan ta ce "Takawa" ya ɗaga kai ya dubeta.


"Yanzu meye abun yi ne? Me ka yanke a kan lamarin nan, kuma ya ake ciki game da binciken?"


Ya ɗan yi jimm sannan ya ce "Dama Bashir ne incharge ɗin da case ɗin yake a hannunsa, sannan police ɗin da case ɗin yake hannunsu suna ta ƙoƙari, ina ga in anjima za su je asibitin da kansu, su yi mata tambayoyi".
Ammi ta ɗan sauke numfashi sannan ta ce "Bana son a cigaba da yawan matsawa yarinyar ne a kan maganar, na ga haryanzu tana cikin razani, dole a bita a hankali".


Adam a ransa ya ce "Babu wani razani, tsagwaron iskanci ne, kuma da ni take zancenta, ba zan lamunci iskancinta a kan rayuwar matata ba'


Amma a zahiri ya ce "Amma Ammi dole ta yi magana domin gaggauta ceto Aisha".


"Eh haka ne, amma ita ma 'ya ce, kuma yakamta a bita a sannu, saboda lafiyar ƙwaƙwalwarta, kana kallona gabanka jiya take ihu wai an harbe wani" Ammi ta dafe goshi ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Allah ya shiga tsakanin na gari da mugu, dole yarinyar nan ta shiga ruɗu, ayi kisan kai a gaban yarinya ƙarama kamar wannan"


Shiru Adam yayi, yana ta addu'a Allah ya sa Aisha tana lafiya.


Ya kalli ammi ya miƙe tsaye ya ce "Ammi, bari na je asibitin nan da kaina".


"A'a kar fa ka je ka nuna musu zafin zuciya da zafin kai, ka bi komai a hankali".


Ya girgiza kai ya ce "Ba wani abun zan yi ba, kin san yau za'a kai ta x-ray, so nake na je na ga yaron, in kuma jarrabawa ko zata yi magana".


"To shikenan, ka gaishe su, ni sai zuwa dare in Allah ya kaimu na je" ya jinjina wa ammi kai ya fice.


Likita ne a tsaye a kan rumaisa da take ta bacci, tun bayan da mama ta yi mata wanka, ta yi wa jaririn, ta kwantar da shi a kusa da rumaisa suke ta bacci, haka nan mama ma yaron ya shiga ranta, ga yaron da matuƙar haƙuri, idan yayi kuka ko dai ya gaji da kwanciya ko kuma yana jin yunwa, daga bacci sai cin hannu kawai yake yi, mama ba ta taɓa jin ta gaji da ɗawainiyar da take da ɗan da bata da alaƙa da shi ba, ji take yi hakkinta ne na uwa ta kula da shi, gefe guda kuma tana matsanancin jin tausayinsa tare da fatan Allah ya kuɓutar da mahaifiyar sa, ita kanta da ta ɗaukowa rumaisa zancen uwar yaron, sai ta hau zabure-zabure.


Likita yana duba file ɗin ruma yana kallonta, mama ta ce "Likita babu dai matsala ko?".


Ya ce "Eh babu, duk wasu gwaje-gwaje da yakamata ayi mata mun yi mata, babu wani mummunan ciwo a tare da ita, sai dai zan rubuta wata allaura a sayo ayi mata, saboda ciwon haƙarƙarin da take kuka da shi, kan ku yo hoton".


"Eh, in anjima za aje yin hoton in Allah ya yarda, dan sai daf da asuba ta samu bacci, da gari ya waye na tasheta, tana ta kuka da wurin".


Ya ce "In sha Allah idan aka yi allurar, za ta samu releif, kan muga sakamakon".


Mama ta ɗan nisa sannan ta ce "Amma likita ba su yi mata wani abu ba dai ko? Basu taɓa ta ba kun duba?".


Ya jinjinawa mama kai ya ce "Ki kwantar da hankalinki, akwai report da police suka bamu, tun daga asibitin farko da aka kaita, da na biyu zuwa nan, muma da namu binciken, komai lafiya ƙalau".


Mama so take ya bata amsa ƙarara, amma kamar bai fahimci me take nufi ba, ba ta son ya ga kamar ta matsa masa, dan haka ta ƙyale shi".


Ganin yadda rumaisa ke kuka da ciwon haƙarƙarin nan ya sanya ta ce bari ta yi sauri ta je ta sayo allurar, gashi da wuri Abdallah ya tafi, yau yana da jarrabawa a makaranta, gwaggo kuma daga ita har iya suna fama da jikin girma, suma mama cewa tayi su tafi gida su huta, dan haka ganin ruman na barci ya sanya ya fito nursing station ta ce musu dan Allah ga rumaisa nan, za ta je sayo allura.


Mama na fita takawa ya iso asibitin, dan direba ya saka ya kawo shi, shi ba zai iya tuƙin ba.


Yana daf da shiga ɗakin da rumaisa take, likita ya fito daga ɗakin kusa da nata, suka tsaya suna gaisawa.


Takawa ya tambayi likitan ya jikin jaririnsa?.


Likita ya ce "Baby yana nan lafiya Alhamdilillah, shi ya samu sauƙi sosai Alhamdilillah, mamansa ce dai iya rigima haryanzu muna fama ba ta warware ba, muna jiran sakamakon hoton da zamu turata mu san abun yi na gaba".


Adam ya ce "Haryanzu ta ƙi magana a kan in da mahaifiyar yaron nan take, da an yi maganar sai ta hau ihu, dan Allah hakan yana da nasaba da razani ko kuma iskanci ne kawai"


Sai da doctor yayi dariya ya ce "To kowanne ma zai iya kasancewa, amma razani kam tabbas tana cikinsa haryanzu, wasu lokutan tunanin ya kan ƙwace mata ta zaci tana hannunsu haryanzu, amma abi komai a hankali, sannan dan Allah idan ku ka tashi karɓar yaron nan, ku bita a hankali ta shaƙu da shi sosai, kar ku rabata da shi lokaci ɗaya".


Bayanin likitan na yanzu ya shiga ta kunnen Adam na dama, ya fita na hangu, dan bai ji zai iya saurarawa ko ɗaga ƙafa wurin karɓar ɗansa ba, yanzu ma don yana cikin tashin hankali ne, da damuwa da son sanin in da matarsa take, ba dan haka ba, da tuni ya ɗauk ɗan sa.


"Thank you very much" ya faɗa a taƙaice ya shiga ɗakin rumaisa.


Sai dai yayi mamakin ganin babu kowa, baccinta take hankali a kwance, gefenta ga jaririn shi ma yana barci, kai ka ce uwarsa ce.


Ya ƙarasa gaban gadon ya tsaya ya ƙare mata kallo, a haka tana bacci looking so innocent, amma a zahiri halinta idan ba ka kai ziciyarka nesa ba, sai ta sa zuciyar mutum ta buga.


Ya kalli ƙafarta da aka rage bandejin da ake saka mata, saboda raunukan da suke ƙafar, ga wani yanka a ƙwaurinta, kai da gani ka san faɗuwa ta yi, ga tabo a gefen goshinta, kai ba sai an gaya maka iya wannan ya isa ya tabbatar wa mutum da ruma ta azabtu kan ta kuɓuta.


Hannunsa biyu ya saka a kan gadon, ya ƙurawa yaronsa ido da yake daga lungu, ya tuna irin yadda suka shirya rayuwa da shi da Aisha idan Allah ya sauketa lafiya, da irin budurin da suka shirya yi, da yadda take nanata masa sai dai su bawa mutane mamaki, ba wanda ya san da cikin sai dai su ce wa mutane ga babynsu, yau ga baby amma ita ba ta nan.


"Aisha why, meyasa a karon farko ki ka tsallake umarnina abun da baki taɓa yi ba, gashi kin sanya mu a wani hali" ya furta lokacin da hawayensa ya gangaro ya zuba a hannun rumaisa.


Juyi tayi zata gyara kwanciyarta, ya ga tana nema ta danne masa ɗa, dan haka cikin azama ya miƙa hannu zai ɗauke yaron. Caraf rumaisa ta riƙe hannunsa ta buɗe ido ta kalleshi.


"Wayyo Allah zai sace mini ɗa, mama kina ina" ta ware murya iya ƙarfinta tana ihu.


Ayshercool.


*₦500 ne, via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143*




https://chat.whatsapp.com/G9XU8tDJMjq02zlZMHurZ5
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*


*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*


*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*


👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*


*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*


*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*


*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*


*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*


*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*


*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*


*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*


*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*


*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*


*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*


*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*


*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*


*15. Supplement for Acne, dark spots remover*


*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*


*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*


Tsayawa yayi cak ya ƙura mata ido, sai yayi mata kwarjini sosai da sosai, hakan ya tilasata yin gum da bakinta tana cigaba da bin sa da kallo.


Hannu ya saka ya ɗauko jaririn daga kusa da rumaisa, ai kuwa ta tashi zaune sosai ta tsatstsasreshi da ido, ko ƙiftawa ba ta yi, dan kar ya shammaceta ya gudar mata da jariri.


Ya nemi wuri ya zauna, ya ɗan tsurawa yaron ido, a hankali ya kai bakinsa kunnen yaron, yayi masa huɗuba da Mahmud kamar yadda ammi ta buƙata, ba kuma dan yayi niyyar sanya sunan ba.


Ya sauke yaron a hankali yana cigaba da kallonsa, ya ɗaga kai ya kalli rumaisa ya ce "A karo na babu adadi, ina sake tambayarki ina aisha take? Bana son ki kai ni bango, in yi miki abun da ba shikenan ba, ki bani amsar tambayoyin da nayi miki, matata na cikin hatsari dole na san in da take"


Kawar da kanta ta yi gefe, ta ƙi kallonsa.


"Am talking to you" yayi maganar cikin tsawa ganin yadda take nema ta mayar da shi mahaukaci.


Sake kawar da kanta gefe ta yi, ta dafe kanta da hannayenta, tana ƙunƙuni.


"Da ke nake, ki bani amsa" ya sake maganar kamar zai kai mata duka.


"Wai dan Allah me kake so na ce maka, ni na san a in da take? Nima fa saceni a kai, ko garinmu ne da zan san ina ne, ka je da kanka mana ka duba, ni na san sunan wurin ne? Kuma wallahi kar sake yi mini tsawa bana so"


Ya yinƙura zai sake magana mama ta yi sallama. Ya haɗiye maganar ya waiwaya ya kalli in da mama take.


Cikin girmamawa suka gaisa, mama ta ce "Ashe ka zo, na je sayo mata magani ne a waje"


Adam ya ce "Eh na zo, ban jima ba, amma ku din ga kai takardar pharmacy zasu baku ba wani abu".


Mama ta ce "A'a basu da shi ne, ai yakamata muma mu din ga taɓukawa, masu shagunan ne ma basu fito ba, saboda haƙarƙarin da take kuka da shi, ya sanya na fita dubawa".


Adam ya karɓi takardar hannun mama, ya ɗau hotonta, ya kalli mama ya ce "In anjima Bashir zai zo, zai taho da maganin sannan ya kai ku wurin X-ray ɗin".


Mama ta girgiza kai ta ce "A'a, mun gode ɗawainiyar ta yi yawa, hakan ma Allah ya saka da alkhairi yayi maka albarka, ka bari kawai wannan zamu yi ba zai gagara ba da yardar Allah"


"Nima ɗan ki ne, ba zan ji daɗi ba idan ki ka nuna ba kya son na yi muku abu"


Tsidik ruma ta sanya baki ta ce "A'a bama so, yaya Abubakar zai zo su kai ni, idan ma wayo kake yi mini na fika wayo in gaya maka" ta yi maganar tana harare-harare.


Da ido ɗaya yayi mata wani irin kallo, mama kuma ta yi mata daƙuwa ta ce "Ke bana ciki da rashin hankalinki, sa'anki ne ko wani ya saka baki da ke? Kin ma taɓa yi masa godiyar ɗawainiyar da yake da ke?"


Ruma ta yi shiru tana basarwa, kar mama ta cigaba da yi mata faɗa a gabansa ya rainata.


Huzaifa ne yayi sallama da kwandon kayan abinci, suka amsa masa bayansa kuma Gwaggo ce da lawisa.


Nan suka zauna suna gaggaisawa, Huzaifa ya ƙarasa ya karɓi Mahmud a hannun takawa ya riƙe hannun jaririn ya ce "Mai sunan babanmu, kana lafiya?" Yayi maganar kamar jaririn zai amsa masa.


Takawa kuwa bin su yake da ido, lawisa ma ta bi Huzaifa tana cewa ya bata ta ɗauke shi.


Adam ya tashi yayi musu sallama ya fice, tabbas ranar da zai karɓi jaririn nan akwai daru, mussaman a wurin uwar riƙonsa rumaisa, yarinyar da ta riga ta fara shi kai bango saboda halinta.


***
"Ammi kin yi shiru baki ce mana komai ba"


Ammi ta ce "To Nusaiba me zan ce muku?"


Iman ta ce "Ammi kina ɓoye mana abun da yake faruwa, amma gaba ɗaya yanayinki da na takawa a 'yan kwanakin nan ya tabattar da akwai wani abu a ɓoye, bama jin daɗin yanayin nan sam".


Nusaiba ta ce "Ni fa ina daf da sanarwa Anty laila, wataƙila ki gaya mata meke damunku ku ka ƙi gaya mana"


Ammi ta numfasa ta ce "Kar ki kuskura ki haɗa ni da laila, koma menene dole zaku ji, amma ba yanzu ba"


"Yanzu Ammi haka zamu cigaba da kallonku a haka, ba fa haka muka saba rayuwa a tsakaninku ba, taya zamu yi adopting hakan lokaci guda, ammi walwalarki ce fa tamu" Nusaiba tayi maganar kamar za ta yi kuka.


Iman kuwa tuni idonta ya tara hawaye ta ce 'Ammi ko dai nice, idan saboda ni ne, ki kai ni Gombe can family house ɗin ku, zan zauna, kuma duk wanda ki ka zaɓa mini zan aure shi, amma dan Allah ki cigaba da walwala muna ganin murmushin ki"


Tausayin Iman ya kama Ammi, ya kamo hannun iman ta ce "Haba iman ɗina, ki na tunanin akwai wani ƙalubale da zai ta so na rabu da ke ne? Kar ki kuma wannan maganar, wani abu ne yake faruwa daban, amma komai zai daidaita in sha Allah".


"Ammi wai muma 'ya'yanki baki yadda da mu ba, muma munafukai ne kenan yaya takawa ne kawai mai iya riƙe sirrinki?" Nusaiba ta yi maganar har cikin zuciyarta.


Duk da halin da Ammi ke ciki, sai da Nusaiba ta bata dariya, ta girgiza kai ta ce "Ba abun da ku ke tunani bane ba Nusaiba, wata yarinya aka tsinto a katsina da jariri" sai kuma ta yi shiru.


"Ammi to meye haɗin hakan da damuwar da kuke ciki?"


Ammi ta ce "Ɗan takawa ne"


Nusaiba cikin rashin fahimta ta ce "Wane takawan? Ta ina za a tsinto yaro a katsina kuma ya zama ɗan sa?"


"Ɗan sa ne" Ammi ta basu amsa.


Iman ta ce 'Amma Ammi, ta yaya?"


"Ɗan Aisha ne, ta kawo ɗan kwalinta da gwala-gwalanta"


Nusaiba ta ɗan dafe goshi a rikice ta ce "Ammi kin hargitsani ban gane ba, ta yaya Anty Aisha da take Saudiyya za'a tsinto ɗan ta da ɗan kwalinta a Nigeria kuma a katsina, anya ba ƙarya yarinyar take yi ba, ko wani abun ake shiryawa ba"


Hawaye ya cika idon ammi, ta ɗauki wayarta, ta buɗe ta nemo hoton jaririn ta miƙa musu.


Cikin tsananin mamaki suke kallon hoton, babu in da yaron ya bar Adam saboda kamanni.


Iman ta ce "Ammi, ni fa haryanzu ban gane ba, a ssudiyyan ta haihu ko kuma yaushe ta dawo Nigeria har aka tsinci jaririnta, ita tana ina?"


Nan Ammi ta warware musu komai, kamar yadda takawa yayi mata bayani.


Nusaiba ta dafe kai ta fashe da kuka ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Ammi yanzu mai za'a cewa mai girma turaki, tayaya za'a warware wannan lamari? Anty Aisha a hannun 'yan bindiga tsawon wannan lokaci babu wanda ya sani? Kuma Ammi ki ke ɓoyewa, idan zancen ya ɓullo ta wani wurin daban fa, kar ki manta ba'a san da cikin nan ba, kuma cewa aka yi zata ƙaro karatu, aka yi ta surutu a kai, tayaya za a dawo ace ba ƙaro karatu ta tafi ba, har ta je ta dawo an saceta ya haihu sai ɗa da ɗankwalinta da gwala-gwalanta, ana ma da tabbacin tana raye?"


Gaban Ammi ne ya sake faɗuwa, jin abubuwan da Nusaiba ta faɗa, take hawaye ya fara gangarowa daga cikin idon Ammi.


Iman ta ce "Anty Nusaiba, komai da muhallinsa, kan ƙalubalen ya zo, za a nema masa mafita, wannan maganganun naki zasu sake jefa ammi cikin damuwa"


Iman ta dubi Ammi a tsanake, ta fara goge mata hawayen fuskarta ta ce "Ammina, ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki, duk wani surutu da ƙazafi da zs ayi mana, ba zai kai wanda aka yi mana a baya ba, na san da tashin hankali, amma ammi ba zaki taɓa yanke hukuncin da zai cutar da wani ba balle mu. Ki na ji ammi ƙaddarar haihuwar yaron nan ce ya sanya anty aisha dawowa ƙasar nan, kuma suka ɓoye miki, duk da yadda suke biyayya ga umarninki, kar ki ɓata ranki ammi, kin san addu'a da ki ke yi mana ce ta zama katanga daga dukkanin sharri. In sha Allah mai girma turaki zai fuskance ki. An tambayi yarinyar ina Anty Aisha take?".


Ammi ta yi ajiyar zuciya ta ce "Haryanzu fama ake ba ta yi magana ba tukuna".


"To shikenan, in sha Allah za ta yi magana, Sai a bi komai a hankali Allah ya sa tana lafiya, shi kuma jaririn Allah ya raya shi" iman ta sake ɗaukar wayar Ammi, tana kallon hoton jaririn.
Nusaiba ta ce "Ba wai tayar muku da hankali zan yi ba, amma kar ku manta masarautar nan ba a iya samun bala'i ba, idan aka sako mutum a gaba da baki da surutu sai zaman garin nan ya nemi ya gagare shi".


Iman ta ce "Haka ne, amma in sha Allah babu abun da ya gagari Allah, Addu'a zamu duƙufa babu dare babu rana. Amma Ammi yaushe zamu je asibitin mu ga yaron muma?".


Ammi ta ce "Ba yanzu ba, ku ɗan bani lokaci, bana son mutanen gidan nan su fuskanci wani abu tukuna"


Haka suka cigaba da tattaunawa, sai dai Nusaiba ta kasa magana domin kuwa ta riga ta gama karaya.


****
Ƙaton katafaren office ne, mai ɗauke da duk wani kayan alatu na jin daɗi da more rayuwa, Senator Usman wakili na zauna a ɗaya daga jerin kujerun office ɗin, sai kuma baƙonsa da yake zaune a kan kujerar da take fuskantar sa.


"Kana ɗaya daga cikin makusantan wancan yaron, da ya dage kai da fata sai ya ga bayana, sai dai kuma kwana biyu na ji shi shiru, duk na gama duk wani shiri da zan yi maganinsa, ko kuma akwai wani abu da yake ƙullawa da ban kai ga sani ba, kar yayi mini bazata".


"Ranka ya daɗe shi ɗain banza ja da ikon masu ƙasa? Ku ne fa ƙasar nan yadda ku ka dama haka ake sha, shi da duk masu goya masa bayan gayyar rashin sanin ciwon kai ce, dan tabbas manyan ƙasar nan akwai masu goya masa baya, wanda nake kyautata zaton 'yan adawarka ne".


Wakili yayi murmushi ya ce "Ba abokan adawata bane ba, domin abokan adawata muna aiki tare ne, mabiya kawai muke rainawa hankali".


"Haka ne Yallaɓai, amma a yanzu haka dai, bana tunanin wani shiri yake yi, dan a 'yan kwanakin nan akwai abun da ya ɗauke masa hankali, ko office bai fiye zuwa ba, ya ce bashi da lafiya, amma babu tabbas a maganar ta sa"


Wakili yayi murmushi ya ce "Yaro bai san wuta ba sai ya taka, shikenan ka cigaba da sanya mini ido a kan sa, da kawo mini rahoton duk abun da yake ciki, sannan zamu cigaba da shirye-shiryen tsayar da khalifa takarar gwamna, shi ma ba zamu baro ya ɓata masa suna ba".


"Amma ranka ya daɗe, na ji wancan satin majalisa ta naɗa kwamiti, domin bincikar gaskiyar abun da hukumar dss suke zarginka da shi, ya za'ayi da wannan"


Wata iri dariya wakili yayi ya ce "Duk saɓatta juyatta

Please Login or Register in order to submit comment