Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tas a saman kawunansu. Kamshi dai nasa ne, dan daga su sai turarrukansu sukazo kasar. An sake gaisuwa irin ta manyan attajirai masu mulki da karfin iko, sannan a nutse sukai buda baki mai sauki (ba irin na su bily ba da sai anji ciki yay nak babugurin tura kosai 🥱), Karancin lokaci ya saka sarakunan biyu mikewa zuwa gabatar da sallar isha'i. Suma kuma su Iffah suka kora bedroom din uwarg/klan Sultah suka gabatar da tasu. Suna idarwa basu zauna ba, dan tafiya tsakanin nan da Madina akwai nisan gaske, dan ma lafiyayyun motocine. Sai lokacin Iffah ta san ashe tare da Sultan din da matar tasa ma zasu wuce. Tofa wayaga in da ranka kasha kallo, dan kuwa dal acikin zukekiyar motar da zasuyi tafiyarma dai an shirya musu abincine, ga an shiryar motar daga aiki kamar wani daki ha musamman. Iffah dai da al'amarin ya zame mata sabo ga kauyanci ga son nuna class t3, haka mutunivar tamu akaita basarwa kamar komai ba komai dai kun gane ai 😉(Kuka yarda naje gurin nan alkur'an sai na nuna hali, dan kowa sai yasan Bilyn Abdull daga 9ja nazo 🤣😆🚴).

A yanzun kam sarakunan biyu sun baje filin hirarsu a nutse ga matansu a gefensu. Har takai ita dai Iffah ta fara ma hamma. Cikin mamaki Tajwar Eshaan yake mata kalion nan nasa na kasan ido, dan ya fara sakama yawn barcin nan nata alamar tambaya. Abu kadan ta fara hamma, yanzu zata tashi anjima kadan ta sake kwanci. Kuma bazaka taba ji tace barcin yaisheta ba. Anya kuwa? (Sa a bincika mana mai rumawaja🚴).







* MADINA BABBAN BIRNI BURIN ZUWAN DUK WANI MUSULMIL*



Duk da dare yayi kai tsaye massalacin MANZON ALLAH (S.A.W) suka wuce, inda nan ma suka samu tarbar da ga shugaban garin na Madina da tawagarsa cikin girmamawa ga Sultan din nasu a Saudiya gaba daya da kuma babban bakonsa shugaban kasar ruman. sai da suka gabatar da salla raka'a biyu sannan sukai zaman jira karasawar lokacin asubahi Basu bar mascalacin ba sal bayan sallar asuba. Yanzun ma dai wani katafaran gida aka kaisu. Gida daya amsa sunansa gida bawai muna gida ba. Gajiyar da ke tattare da kowa yasa ruwa kawai suka watsa kowa ya kwanta musamman ma Iffah dake jin kamar zatayi adungure tun a massalaci…..✍️

DAUDAR GORA
Book 2
68

...……….Lokacin da azhar ta gabato Tajwar Eshaan ya tashi yay wanka ya kimtsa babu alamar Iffah zata motsa, kwance take sharkaf tana kwasar barci kamar wadda ta mutu. Zama yay a bakin gadon ya zuba mata ido, tare da kai yatsunsa saman goshinta da wuyantan amma babu alamar wani zafi da ke nuna tana a cikin ciwo. Da kyar ya tadata tana faman tura baki gaba, ya kafeta da kaifafan idanunsan nan, sake tunzura bakin tai ta kauda kai. Sai shima ya dan girgiza kan a fusge ya furta, "Ki daina turamin wannan bakin na dinga kai azumina lafiya batare da ya raunana ba. A haka za'ai ibadan Nigar?".

Kwalkwal tai da idanunta kamar zata saki kuka tace, "Nima zuwa fa barcin kawai yake, konace bazanyi ba sai na kasa". Shi dai kallonta kawai yake zuciyarsa na raya masa abubuwa masu yawa. Amma sai bai furtaba ya ce, "Okay tashi ki shirya muje massalaci ga su Sultan na jiranmu". Babu yanda ta ia dole ta tashi ya taimaka mata ta shirya din, dan a hakan ma sai faman lumshe masa idanun take da sakin hamma. Shi dai lallabata yay suka wuce dan ya fahimci abin bana lafiya bane. Kilama Aljanun nata ne ke sakata barcin dan kar tai ibadar....


(A gurguje Please munada sauran aiki, gashi nagaji walle. Gara muyi mu gama kowa ya huta 🏃‍♀️).



Rayuwa a Saudiyya wani rubutaccen al'amari ne da Iffah bazata taba mantawa da shi ba a rayuwarta, dan rubutaccen labarine tsakaninta da Maleek dinta mai zaman kasan ga ma'abocin bibiyar labarinta, amma ta tattara ta killacema zuciyarta kawai kuma sai ku kiyasta da hasashenku. Duk da dai ta samu nakasun raunana a dalilin barcin da bata san kansa ba balle karshensa. Amma duk da haka tana matukar yaki da shi da ganin tayi cikakkiyar ibada. Dan abu mafi birgeta shine yanda Tajwar Eshaan ke tsaye akan kafafunsa koda yaushe babu wasa tattare da shi ko nuna gajiyawa a dare da rana. Gaba daya ya maida hankalinsa a bautar Sarkin sarakunan nan mahaliccin duniya da kayan cikinta, mai rahama da mukullin aljanna. Sarkin da babu kamarsa kai koda kwatankwacinsa ma babu. Gaba daya ya mika lamuransa garesa cikin kaskantar da kai da zubda gwiwunsa bisa kasa. A duk sanda yake addu'a zaka samesa da hawaye share-share da inba gaban UBANGIJINSA ba bazaka taba gani ba. Kullum cikin gayama ALLAH yake kan samun warwarar al'amuran da suka shige masa duhu musamman akan mutuwar yaran da basujiba basu gani ba a daliln aurensa. Duk da wannan jajircewar tasa kuma yana bata kulawa a dan kankanin lokacin da suka daukarma kansu na hutawa. Dan ko bayan kammala Umrah din su bai lamunce su zama a karkashin inuwar lalaci ba.

A gefe kuwa wata Irin shakuwace ta shiga. tsakaninta da uwargidan Sultan. Mace hamshakiya ma'abociyar kyawawan halaye da nuna tsattattacen iko saman na kasa da ita. Nutsuwa sosai Iffah tai tana koyan abubuwa, yayinda itama bata tsaya boye-boye ba ta fito tana gyarama Iffah'r duk abinda zai bata martaba da kima a wajen mijinta da al'ummar da mijin nata ke shugabanta. Dan tayi dubi ne da karancin shekarun Iffah'r da ma labarin data bata na cewar ita iyayenta basu da alakan mulki. Ba halayyar Iffah da dabi'u ba hatta jikinta wani irin gyara yake samu na musamman ga uwargidan Sultan din.

Hadimanta kam tunda sukazo bata gamsu sun ganta sau cikakken biyar ba. Hakama duk dokinta da tsammanin zal hadata da su Babiy tunkan su taho babu alamar zai yi hakan. Har magana ta masa cikin hikima amma sai baice mata komai akan hakan ba. Dole ta hadiye komai ta nuts bisa shawarar uwargidan Sultan din.

Shanyewar tai kuwa, dan yanzu Iffah an koyi halin dattako da shanye abu a ral, sai dal fa à gaban Tajwar Eshaan bakin baya mutuwa, idan kin jita shiru barci take, a lokacine kawal zai huta da tsiwarta.





Alhamdulillah yau an kai azumi na ashirin da shida, a yau ne kuma su Iffah sukayi ziyarar bankwana cikin dakin ka'aba ita da Tajwar Eshaan da Sultan na saudiya, da uwargidansa, sai wasu manyan masarautar tasu. Iffah tasha kuka lokacin da taganta cikin tsakkiyar dakin ka'aba, Abune da bata taba zaion kasancewarga ba koda a cikin matarkinta. Kal ita ketare kasar ruman ma bata taba zaton tana da rabon yi ba a rayuwarta. Amma yau sai gata da kwanaki ashirin da biyar cikin kasar Saudiyya, tare da mijin aurenta shugaban kasarta. Hannunta kawai ya rife cikin nasa alamar lallashi har suka fito, suna shige mota kuwa ta fada jikinsa ta kankamesa. Murmushi yay mai sanyi da dagota yana mata yan harara tare da lakace mata hanci. "So kike ki karyamun azumi ne?"

Baki ta dan tura tana wan kikkitata Idanun dake cike da hawaye, a shagwabe tana war idanun da yanayin mamaki ta ce, "Dama maza azuminsu a karyewa ne?". Murmushi kawal yay ya dauke kansa, sai kuma ya sake juyowa a yanayin wanda ya tuna wani abu, kallonta yay da ga sama har kasa kafin ya jeho mata tambayar data daure kanta da bata yar kunya-kunya. "Mrs Eshaan kin sha wani magani ne dan kar kisha azumi?". Da kunya-kunya mamaki-mamaki ta dubesa, sai kuma ta girgiza kanta alamar a'a. Itama kuma sai kirjinta ya shiga harbawa da sauri-sauri. To al bama watan azumi kawal ba, idan bata manta ba rabonta da ganin proud din ta fa kamar tun wanda ta gama da kwanaki kadan ya ziyarceta bafa ta sake ba. Kai kodai ta sake ta manta, to idan ma ta sake din ai a watan nan ne na Ramadan ya kamata ta gani farkonsa, juya mata kanta ya fara yi saboda neman takurama kanta da tai na sai ta tunano. "Kinga relax karki takurama kanki"., Ya fada a hankali yana kwantar da ita a kujerar.Gaba daya jiyay yama kagara su koma cikin masarauta, suna isa kuwa masaukinsu aka zarce da su. Duk da an bude mata kamar yanda aka bude masa kofa shima sal ya fito da ita ta inda ya fita, basu fi zaman mintuna goma ba doctor din da ya bukaci gani ya iso tare da uwargidan Sultan da hankalinta ya tashi da tunanin ko kukan da Iffah tayi ne ya zame mata matsala,

ita Iffah sai ma abin nasu ya bata mamaki da dariya,ta kal dubanta ga Tajwar Eshaan da yay zaman kasaitar nan tasa. Cikin langabe kai ta masa magana da ido alamar wai mike faruwa? Dauke kansa yay gefe a ransa shi kadal yasan miyake ji na farin ciki, ya kagara doctor din tace wani abu. Amma a zahiri baka isa fassara abinda ke ko"a kan fuskarsa ba balle zuciyarsa. Doctor da tai yan gwaje-gwajenta a gabansu abinka da gidan manya ta dago tana murmushi, cikin girmamawa ta fuskarci uwargidan Sultan ta mika takardar da tai yan rubuce-rubuce.

"Ya ALLAH"

Uwargidan Sultan ta fada fuskarta da kayataccen
murmushi. Ta kai dubanta ga Tajwar Eshaan da ke jin kamar ya fisgo takardan hanuntan amma ya dake a zahiri. "Ina mai farin cikin kasancewa ta biyu bayan doctor akan sanar muku samun karuwa da mukai, ALLAH ya sauki Zawjata-almilk lafiya". Wani irin lumshe idanunsa yay da sauke sassanyar ajiyar zuciya kamar wanda aka zarema numfashi. Yayinda Iffah tai fakare tana kallonsu cikin rashin fahimta sam. Dan ita kanta ma sat ya toshe kawai a wanna gabar. Har suka gara bidironsu Uwargidan Sultan ta wuce bata iya tofa komai ba..



Wani irin dagata yay bayan ficewar kowa a falon ya shiga juyi da ita. Kawal ita sal abin ma ya bata dariya ta shiga kyalkyalawa. Bai hakura ya direta ba sai da yaga ta fara date kal alamar jujuyatan da yake akwai matsala. A tare suka dinga sauke numfashi, ya tsareta da idanun nan nasa masu kaifi ga kayataccen murmushi mai matukar tada da yakan dace baka gani a fuskarsa ba, Sal dal kuma a zahirance bakin ya gagara cewa komai. Sal da ya mula dan kansa a hankali ya furta "Mrs Eshaan kin mallakeni da komal na. Da gaske fa ni din bawanki ne". Da sauri tasa hannu ta rufe bakinsa tana zaro idanu da girgiza kanta. Cikin rawar murya kamar mai shirin sake masa kuka ta ce, "Please Sultan ka daina fadar haka karma yan kasar ruman suji sumin yankan rago. Kai fa shugabana ne, sannan ashekaru ka fini, gaka mijina,uban yayana", Hawayen suka silalo mata a hankali. Hannunsa ta kamo ta daura akan cikinta. "Nagodema ALLAH da ka kasance mahaifinsu badan ya baka daukakar mulki data dukiya ba. Domin su a duniya aka samar mana da su a cikinta kuma zamu tati mu bari wataran. Ina alfahari da kai ne matsayin uban yayana saboda nagartarka da adalcinka. Tsoron ALLAHn ka da kyakylyawar zuciyarka. Maleek kai na dabanne a cikin daban. Ba yan kasar ruman bane kawal suka dace a dalm shugaba ba. Daular musulunci ma kai abin alfaharinta ne. Sannan kuma nice kololuwar dacewa da ka kasance miji gareni, Nauyin mulki bai sa ka gaza bani farin ciki da sauke duk wasu hakkokina ba. Kana samar da nishadi a tsakaninmu ka manta da kai sarki ne mai jagorantar talakawan kasa bawai jaha ko wani dan yanki ba,
Kwanciyar hankalin da nake samu da ga gareka bana jin wasu matan da mazansu basu da nauyin kowa na sarun makamancin sa. Maleek kai ne gwarzo na, kai ne Barde na, kuma kaine gagara badau dina".

Idanunsa kawai ya lumshe a zahiri, maimakon ita da ke kuka a bayyane shi a zuciya yake yin nasan. Tabbas yaga ribar hakuri, kai shi baima san mizaice da UBANGIJI ba akan kyautar wanna yarinya da ya bashi. Ita din ta dabance. Tabbas itace komansa. Tsam-tsam ya rungumeta a jikinsa na tsawon lokaci, sal da ya ji tana sauke numfashi a hankali alamar barci ya dauketa sannan ya dagota. Kwantar da ita yay a hankali ya cigaba da kalionta hannunsa saman shafaffen cikinta da kamar babu komai a cikinsa abubuwa da yawa na masa kaikawo tun daga randa ya fara ganinta soyayyar farat daya ta shigesa har zuwa yau da ajiyar gudan jininsa ke à cikin jininta…..✍️

DAUDAR GORA
Book2
69


.....WASHE GARI ta kasance ranar da zasu koma kasar ruman. Da safe bayan Tajwar Eshaan ya gama ganawa da Sultan na saudiya sunyi sallama amintaccensa da Sayeed Tasadduq-Husain da sai daga baya yazo ya samesu a saudiyyan da wasu mutane biyu suka samesa. Cikin girmamawa suka mika gaisuwa, kafin Sayeed Tasadduq-Husain ya mika ma Amintaccensa file din hannunsa. Amsa yay da sauri yaje gaban Tajwar Eshaan din shima ya ajiye.

"Wannan shine result din binciken ALLAH ya kara ma adalin shugabanmu lafiya da nisan kwana. Sannan wadan nan sune sukai binciken. Sun kuma kasance kwararrun likitoci ta wanna fanin".

Da sauri daya a cikinsu ya karbe zancen Sayeed Tasadduq-Husain din cikin harshen turanci, "Idan mukai bincike so daya ba'a samun kuskure, amma domin cire tantama sai da mukai wanna sau uku. Abu daya yake tabbatar mana shi namijin mahaifinta ne, mace kuma ba ita ta haifeta ba. Bayan muni sau uku mun sake bayarwa was asibitocin ga results din nan dai duk abu guda suke bayarwa".

Baice komai ba, sai amintaccensa ne ya amsa da
yawunsa. Da ga haka sukai masa sallama Sayeed Tasadduq-Husain yay musu rakkiya. Duk abinda akeyi Iffah na daga kofar falo na biyu ne tsaye zata fito zuwa sashen Uwargidan Sultan da zasuyi sallama. Duk da bata san manufar zancen ba sai duk taji ta tsargu, amma kasancewar yanzu an koyi wasu halaye musamman akan hadiye abu koda ta fito wucewarta kawai tavi tunda yasan da fitar tata.. Koda taje can kuma abun nata mata kaikawo har tana jin kwadayin son sanin abinda ke a tattare da file din da son sanin akan wama ake maganar da har sai anzo wata kasa za'ai binciken bayan kowa yasan kasar su suna daya a cikin masu kwararrun likitoci a duniya. Sai kuma a ka kara yin sa'a lokacin da take dawowa sashen ta samu Sayeed Tasaddug-Husain da Tajwar Eshaan din suna maganar again. Cikin kasaitar nan tasa da magana a fisge yake sanar masa. "Ayi musu komai da ya dace, nan da kwanaki biyar bayan anyi salla sai ku biyo bayanmu, dan ina son ku iso ne randa zamu koma zaman shari'ar".

"Umarninka da cikawa shine abin jiranmu Insha ALLAHU"

Iya abinda Iffah kenan ta iya ji ta shige. Lokacin da ya shigo dakin zai shirya tata fatan ya shigo da file din amma sai ya shigo babu komai. Kuma bai mata maganar ba. Amma koda suka kammala shirinsu suka fito Sultan da kansa yau ma da yayansa maza biyu da uwargidansa sukai musu rakkiya har airport Iffah harda kwallarta hakama Uwargidan Sultan abinka da sabon mata bayan shigarsu jirgi sun zauna tana a jikinsa yana lallashinta sai ga file din nan ajiye a gefensa. Ta danyi mamaki amma sai ta basar, sai dai zuciyarta na sake tabbatar mata da koma akan wa file din ya kunsa yanada matukar muhimmanci ga mijin nata. Jirginsu na dagawa babu dadewa barci ya kwasheta…...



* KASAR RUMAN



Duk da saukar dare sukai tako ina a airport din zagaye yake da matakan tsaro. Kai da gani kasan mai kasar ruman dinne da kansa zai sauka. Ta bangaren masu tarbarsu kuwa manyan masarautar ne masu fada aji. Ga wasu lafiyayyun motoci ababen birgewa ga mai kallo. Sosa barcine a idon Iffah dan yanzu kam bata da aikin da yafi wannan. Hakan yasa ta kasance a kusan rabin jikinsa lokacin da suke fitowa, Dole duk wanda ke wajen yay kasa da kansa cikin jin nauyi. Shika gogan nasu ko'a kwallar rigarsa rungume yake da ita hankali kwance yana daga musu hannu daya alamar amsa gaisuwarsu har zuwa motar da aka ajiye domin su kawai. Sai da suka shiga har aka rufe sannan hadiman da sukal masu rakkiya ke fitowa a jirgi suma. A wannan tawaga musamman ta matan Diwa ce kawai zuciyarta ke a tsarkakake game da nado labari, amma sauran duk yan daukar rahoto ne. Sai dai kuma basu samo yanda suke so ba sam kasancewar su/Iffah'r sun musu wahalar ma gani ba kamar yanda su Uwa sukai tunani ba.

Tun daga airport har cikin masarauta jami'an tsaro ne, a cikin masarautar ma tarba suka samu da taima Iffah dadi, dan harda Malikat Haseenat da Daneen Ammarah da kanta. Sal wata da Iffahr bata sani ba amma suna kama da Daneen Ammarah sosai kuma tana kama da Jaddah. Haka kawai taji a ranta itace Daneen Waheeda da aketa fada. Lokacin da take dagowa da ga rungumar da taima Malikat Haseenat zata rungume Daneen Ammarah idanunta suka sauka kan wata kyakykyawar farar budurwa sol tana balla mata harara. Bata santa ba, dan haka ta dauke idanunta ta maida hankali ya Daneen Ammarah din cikin rashin damuwa. A hankali ta saketa ta nufi Daneen Waheeda da ke tsaye tana kallonsu kusa da Malikat Ashwaq fuskarta babu yabo babu fallasa. Gabanta ta rissina ta gaisheta tare da Malikat Ashwag din. Amsa mata tai da dan murmushin yake sakamakon kallon da Malikat Haseenat ta watso mata. Sai kuma ta nufi Malikat Bushirat ta rungume, itama dai gain kallon da ake musu ne yasata shafa kanta tana yake, Jasrah kam saita boye bayan Malikat Bushirat din dan da gaske kunyar Iffah take ji. Murmushi Iffah tai itama ta rungumeta, dan koba komai kafin faruwar hakan al ta nuna mata soyayya ta gaskiya..

Tuni shi Tajwar Eshaan ya shige ciki, dan haka itama Malikat Haseenat ta kama hanunta tana facin,"Kinga zomuje kema ki huta kunyi buda baki a jirgi babu nutsuwa". Da ga haka ta nufi ainahin sashenta da ita dan an sake masa gyara na musamman. Bayan wucewarsu abubuwa da yawa sun faru a cikin masarautar, ciki hard jajircewar Malikat Bushirat akan komawar Iffah sashenta. A zahirance dai babu wanda ya kawo komai a ransa game da hakan, sai Malikat Haseenat ce ma take gain Malikat Bushirat din na son hakanne da tunanin Iffah ta kanainaye mata Eshaan, ta kuma san sai dai Bushirat din tayi ta gama Iffah da Tajwar Eshaan sun riga sun gama zama abu daya. Ga tabbaci nan ma a yau ta sake gani, dan duk mai hankali da zai kalli Iffah'r a yau yasan tana tare da juna biyu. Komai nata ya canja, ga kyau data kara da budewa. Yanzun ma Malikat Bushirat na gain sun nufi can ta saki wani lafiyayyen murmushi tana fadin, (yes) a zuciyarta alamar akwai abinda suka kulla a sashen kenan.

Ko dar Iffah bataji da komawarta sashenta ba. Sai ma farin ciki data tsinta kanta a ciki. Ga hadimanta duk an dawo mata da abinta, a ganinta ma ita wannan wata dama ce da zatai yakinta da kyau a yanzun. Wanka ta farayi bakinta dauke da addu'a, kasancewar duk tayi sallolinta tun a jirgi shirin kwanciya kawai tai ta haye gado abinta sai ko barci.




Cikin barci take jin kamshinsa na sake shige mata hanci, a zatonta mafarki take, sai tai kokarin yin juyi abunta. Jinta jikin mutum a gaske ya sata bude idanunta da kyar. Akan kyakykyawar fuskarsa ta sauke idanun nata. Tashi tai a dan zabure ya rikota, maidata yay ya kwantar yana mai tura yatsunsa cikin gashin kanta, sai kuma ya matso da fuskarsa saitin tata ya daura goshinsa kan nata hancinsu na gogar juna.

"Yaushe kazo?"

Ta fada cikin muryar barci. Shiru kamar bazaice komai ba, sai da ya mula dan kansa sannan. "Dama zaki iya barci babu ni a tare da ke?". Kankamesa ta sakeyi tana sakin ajiyar zuciya, itama a hankalin ta furta, "Kawai dan banda yanda zanyi ne".

"Toni gani nayi yanda zanyi ai".

Ya bata amsa yana sake matseta cikin jikinsa kai kace amshe masa ita za'ai. Luf ta kwanta kuwa suna sauke ajiyar zuciya a tare. Sai kuma ya hade bakinsu a hankali. Da ga haka labarin ya sauya salo...

Karfe uku nayi ya gudu, sai farkawa tai taga babu shi a dakin. Murmushi kawai tayi ta tashi zuwa bayi tai brush da tsaftace jininta ta fito. Madara mai dumi kawal tasha matsayin sahur. Duk da barcin dake cin idanun nata sai bata kwanta ba tayo alwala ta danyi nafilfili da karatun Alkur'ani. Bata tashi a wajen ba sai da tai sallar asuba, Tana idarwa kwanciyar ta sake yi, bata tashl ba sal azhar. Tayi mamakin barcin da tayi, amma kuma sanin yanayin da take ciki da rashin isasshen barcin da bata samu a Saudiya ba yasa ta fahirci akwai ramuwa dole dama.

Tsaf tai shirinta cikin kyakykyawar abaya kamar ka sace ta ka gudu. Dama ga ko'ina ya sake fita da fitar kwarjini da kyawun haiba na ciki. Cike da girmamawa a gareta hadimanta ke zubewa Rasa gaisheta lokacin data fito. Nuni tai musu da su tashi, cikin sanyin da ciki ya haifar mata yanzu ta basu izinin mata rakkiya zuwa sashen Malikat Haseenat da ga nan su wuce na Malikat Bushirat. Da girmamawa suka arsa mata tai gaba suna take mata baya. Duk da akwal tazara a tsakaninsu bata shiga motar da aka ajiye domin ta ba tunda ta fito, A kafa ta taka hadimanta na take mata baya. Dolene ta birgeka, dan yanda ta fito da kafan ma sal ta kara kima a idanun hadiman. Ta ko'ina kuwa ta gitta hadiman ne ke zubewa mika gaisuwa, hannu kawal take daga musu fuskarta da dan murmushi dan sam bata daureta ba. Yayinda Amintacciyar hadimarta ke amsa musu da baki ita kuma.

Tun kan shigowarta aka sanar da Malikat Haseenat da ke zaune Daneen Ammarah da Daneen Waheeda tare da ita. Sai Iftihal diyar Daneen Waheeda dake zaune a can gefe tana latse-latse a laptop. A nutse ta shigo bakinta dauke da sallama. Dan haka suka dago a tare. Sai dai kuma a hankali Iftihal taja sirrin tsaki da maida kanta ta cigaba da abinda take yi. Babu wanda ya jita, sai dai Iffah kam taga kallon da tai mata sarai. Amma tai kamar ma ita bata ganta ba ta nufi Malikat Haseenat da ta bude mata hannu fuska duke da murmushi alamar tazo gareta. Ita din ta nufa cike da kunya, ta durkusa a gabanta tana murmushi da gaisheta. Cikin murmushi Malikat Haseenat ta ce, "A'a kinga Hafidah tashi ki zauna keda ke fama da kanki, ALLAH dai ya raba lafiya".

Sosai kirjin Daneen Waheeda ya buga, yayinda Daneen Ammarah ke murmushi kawai tana bin Iffah'r da kalion kasan ido, Bayan ta gaishe da su duk cikin girmamawa Daneen Ammarah ta nuna mata Daneen Waheeda. "Ga wata maman taki nan tazo kuna Saudiyya, nasan kin san dai sunanta da labarinta tun kafin yau". Fuskar Iffah cike da murmushi ta jinjina mata kai. Kafin ta kara gaishe da Daneen Waheeda din da zancen cikin nan va sata sumar zaune, cikin murmushin yake ta kai hanunta kan Iffah'r ta shafa. Daneen Ammarah ta sake waiwayawa ta nuna mata Iftihal da tai kamar ma bata san mi ake ba "Wannan yar uwarki ce ita kuma, sunanta Iftihal, itace first born a wajen mamanki. Tanada kanne maza har uku".

Murmushi kawai Iffah tai sai dai batace komai ba kamar anda itama Iftihal din ko dagowa batai ba. Yanda tai din kuma sai ya zafi Daneen Ammarah. Ita kanta malikat Haseenat dai tayi shiru ne amma fuskarta ta nuna jin zafin abinda Iftihal din tayi. Ita kam Iffah ko'a kwalar rigarta, hankalinta kwance suka cigaba da hirarsu da Daneen Ammarah da Jaddah...✍️

DAUDAR GORA
Book 2
70



....Sai da tai sallar la'asar a sashen Malikat Haseenat sannan ta baro, fuskarta dauke da murmushin abinda take kullama Iftihal. Dan ta dau alwashin sai tayi dana sanin zamanta

Please Login or Register in order to submit comment