Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nuna alhini, a can ƙasan ransa kam zafi yake ji a jikinsa shima kamar yanda ya fahimci tana ji. Wani kukan taɓara-taɓara ta sake fashe masa da shi tana nuna masa agarar ƙafarta da faɗin, “Shikenan ƙafana ya cire, ni dai ka kiramin Mamy da Jaddah wayyo ni Ummu, Iyyani ƙafana ya karye Hanash Akhi”.
(Stubborn girl) ya faɗa a zuciyarsa idanunsa na wani shanyewa a kanta. A zahiri kam yi yay kamar zai share sai kuma ya kai duƙe gabanta a hankali. Maimakon duba ƙafar da take faman riƙewa cak ya ɗagata a wajen. Babu shiri tai saurin saƙalo hanunnta a wuyansa jin kamar zata faɗi tana waro manyan idanunta. Fahimtar magana zatai ya kauda idanunsa, a can ƙasan maƙoshi kamar an masa dole ya furta,
“Ban son surutu..”
Takaici kamar zai shaƙe Iffah ta cuna bakin nan gaba ta kauda kanta gefe itama lips dinta na motsawa da alama magana take wadda ba'aji. Ganin inda ya nufa da ita ta ɗan sauke ajiyar zuciya a ɓoye, yana sauketa a gadon ta yunƙura zata tashi, maidata yay ya kwantar yana watsa mata shegen kallon nan nasa na ƙasan ido da Iffah ta kasa gano fassararsa har yanzu, ba zato taji ya ture hanunta da ke dafe da ƙugunta dan anan tamafi jin zafin faɗuwar ya maye gurbinsa da nashi........✍️



_🥱To kuma dai, Ni na gaji da wagga lalata ta Iffah. Anya bazan koma team Shanshani ba😒😬🚴._



*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*


_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲


✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨
(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)



𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻



𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (37)




.........Da sauri ta sake maida natan kan nasa ta danne ta hanashi motsawa. Fuskar data kumbura yabi da kallo yana sake tsuke tashi, babu alamar wasa tattare da shi ya ce “Miye kuma?”.
“Ni wlhy ba sai ka taɓa ba zan yi da kaina, kuma ai yama daina”.
(Yarinyar nan zata kasheni wlhy) ya faɗa acan ƙasan ransa yana mai ture hannun nata ya matsa wajen. Zabura ɗaya tai ta kanannaɗe jikinsa tana fasa ƙara dan taji zafi na gaske. Yanda ta faɗo jikin nasa a bazata, ga hannunsa da yake ƙoƙarin toshe kunne saboda ƙarar da tai har cikin kansa. Baya sukai su duka, shi ya faɗa kan bayansa ita kuma tana a kansa. Bashi da zaɓin da ya wuce riƙota kawai. Wani irin dab-dab da juna fuskokinsu suka kasance, har hancinansu na gogar juna. Hakama idanunsu sun sarƙe cikin juna. Wani irin al'amari da ya sake rikita mata lissafin data manta da zafin ciwon da take ji ta gano cikin tsakkiyar ƙwayar idanunsa, da sauri ta kauda ƙwayoyin idanun nata a cikin nashi da son zame jikinta gaba ɗaya tsigar jikin nata na wani irin tashi, numfashinta kam fita yake da sassarfa. Hannunsa dake saman ƙugunta yasa ya sake maidota jikin nasa. Zafin da taji wajen bigewar ya sata matse fuska, sai kuma ta tura baki tana buɗe idanun nata kan ƙyaƙyƙyawar fuskarsa da gaba ɗaya kwarjininsa ya sa takeji ta kamar a wani kogon dutse suke a matse.
Yanda taki yarda ta sake kallonsa ya sa yaji murmushi na zuwa masa. Amma tsabar iya miskilanci da jin kai sai ya haɗiye kayansa yana ɗan lumshe idanun da sake buɗewa kan ƙyaƙyƙyawar fuskarta da tai wani takwaf-takwaf kamar zata saki kuka. Cike da son ta magantu ya ɗaura hannunsa kan inda ta bugun da ƙyau, murya a shaƙe kamar mai raɗa ya ce, “A kira Doctor?”.
Yanda yay maganar yana busa mata numfashinsa kan fuskarta ba ƙaramin yamutsawa tsigar jikinta tai ba. Cikin sauri ta jujjuya masa kanta tana ƙara ƙwaɓe fuska. Ita kanta bata sanin sanda take masa shagwaɓar nan, kawai samun kanta take a hakan. “Ni dai ya daina, ka barni na tashi ba ƙyau”.
Kafeta yay da kaifafan idanun nasa da suka sake shanyewa can ƙasa, cikin wani irin salon ɗagesu ya furta, “Mike nan?”.
A hakali saman lips. Idanunta a rufe ta nuna yanda suke tana kauda kai. Wani makirin murmushi ya suɓuce masa a karo na farko, a hankali ya juyata suka koma kwance a gadon su duka kan hannayensu suna fuskantar juna. Baya tai yunƙurin ja ya tareta da hannunsa ya sake maida fuskarsu daf da juna.
“Nace na gama da ke ne?”.
Iffah fa gaba ɗaya ji take ma bada Shahan-shan take tare ba wani aljanin ne yazo mata a siffarsa. To inba haka ba taya za'ace ma Shahan-shan ne wannan. Mutum data sani ko kallo mutane basu ishesa ba, gaskiya wannan aljani ne, aljanin da ta jima tana gani kafin shigowarta masarautar nan....
Iskar da ya busa mata kan fuska ya sata jan numfashi mai nauyi alamar dawowa hayyacinta. Ya ɗan yamutse fuskan ta sa dake tsuketa, sake maida idanunta tai ta rissinar. Shima sai ya lumshe nasan ya ɗan sake buɗewa kanta yana motsa lips ɗinsa a hankali kamar wanda akaima dole. “Shi kuma wanda ya biya sadakinsa fa?”.
Idonta a rufen kanta tsaye, duk da muryarta a kasalance alamar ta fara laushi ta ce, “Kai dai ai baka biya ba, dan ta ƙarfi aka kawoni masarautar nan dan a lasheni kamar yanda aka lashemun yayu na”.
Da ƙyar ya iya gimtse murmushin da ke son kufce masa ya sake tsuke fuska a zahiri duk da ita bama kallonsa take ba. Daɗin biye mata yake ji, dan haka cikin ƙara ƙasa da murya ya ce, “In ma ban biya ba ai lokaci ne zai nuna. Mun taɓa lasar wani ne a gabanki zaki mana sharri?”.
“Babu wani sharri. So babu adadi ma”.
“Sai ki faɗa dawa-dawa muka lasa a gaban naki?”.
“Matarka da ta mutu mana. Kuma nima dan namana da ɗaci ne yasa kuka kasa, dan nifa nafi ƙarfin mayu, kaima nasan tsorona kakeji yanzu haka”. Ta faɗa da ƙarfin ikon son tabbatarwa tana wani ƙara tsuke fuska.
(Bazaki kasheni ba yarinyar nan) ya faɗa a zuciyarsa yana danne dariyar dake taso masa. A zahiri kam hannunsa ya maida a ƙugunta dai-dai inda ta bugu yana wani lumshe idanu da buɗewa, a hankali yake murza mata wajen batare data farga ba duk da tana ɗan jin zafi kaɗan-kaɗan. “Yaushe kika fara gano inajin tsoron naki? Dan nima dai naga kamar tsoron naki nakeji da gaske. Da alama baki barni haka ba kema mayyar ce ko?”.
Lips ɗinta tai wani irin turawa tana ƙwaɓe fuska, ita ala dole taji haushi yace mata mayya, “Ni ALLAH ya kiyaye na zama mayya. Tsorona kuwa tun randa ka fara ganina mana, kuma inba tsoro ba miya maidaka Ajmaal ka dinga naɗar min sirri...”
Yanda ta ƙare maganar da yin takwaf-takwaf da fuska kamar zatai kuka ya sashi jan wata irin wawuyar ajiyar zuciya jin numfashisa na fisga, kansa har ya fara masa ciwo saboda ya gaji da surutun, itako oganniyar ya fahimci ko'a jikinta ma. Cikin nuna alamar gajiyawar har cikin harshensa ya ce, “Ashe dai ni kike jin tsoron, saboda na kasance Ajmaal duk wani sirrinki na sani?”.
Idanunta da ke rufe ta buɗe fes a kansa, cikin son dakewa ta ce, “Hu'im lallai ma tsoro fa? To kaima ai naka sirrin na a tafin hannuna basai na faɗa ba”.
“Ni ɗin?”.
Ya faɗa a fisge yana waro duk girman idanunsa kanta. Jikinta tai ƙoƙarin janyewa da ga nasa dariya na taho mata ganin yanda ya waro idanun, a nata ganin ai ya tsorata ne. Sake riƙota yay suka koma daf-daf fiye ma da ɗazun, cikin wani salon da ke neman girmar kanta ya kai hancinsa kan wuyanta yana busa mata numfashinsa. Da wani irin karyayyar murya data sata zabura can ƙasan maƙoshi ya ce, “Faɗamin wane sirrina kika sani? Na yi alkawarin zan ƙara miki da wani ma yanzu duk ki haɗa”. Yanda yay maganar numfashinsa ma sauka saman wuyanta tare da murza hannunsa wajen ciwonta batare daya fargaba babu shiri ta zabura zatai magana, rufff ya rufe bakin da tausasan pink lips ɗinsa. Ɗifff komai na jikinta mai aiki da motsin ruhinta ya tsaya cak da aikin na wucin gadi kamar yanda nashi ya kasance. Idanunsa ya lumshe a hankali da sake buɗesu kan fuskarta, kafin ya kai hannunsa baya ta ƙeyarta ya tura yatsun kan tattausan gashinta, a hankali ya fara warwaro ribbon ɗin data ɗaure gashin a tsakkiya da juya lips ɗin nasa kan nata ya mirginata suka sake komawa kan hannayensu ta ɗaya ɓarin yanzu ma suna fuskantar juna. Wannan ne karo na farko da hakan ta faru a tsakaninsu, abune kuma da bai taɓa faruwar ba, hakan ya sata shiga cikin ɗimuwa da gigita, dan da wani irin salon dake neman ɗage numfashin nata da ga gangar jikinta yake juya lips ɗin nata cikin nashi tamkar ba Shahan-shan ɗin nan ba mai tsananin miskilanci da izza da ƙasaitar mulki, wanda hatta magana wahala take masa. Murmushinsa kam abune mafi tsada ga duk wanda ya sanshi. Gaba ɗaya duk sai ta daburce jikinta ya shiga rawa, ciwon ma da ƙafar ke mata da ƙugun ta nemesu ta rasa... (🤭Bily ki kiyayi kanki🏃)

Da alama Shahan-shan Eshaan ya tafi, tafiya irin mai toshe kunne daga jin ko wane irin motsin sauti da ke a doron duniya, dan dukkanin takaicinsa akan waɗan nan lips ɗin masu masa tsiwa yau da alama sai ya hucesu. Ita kanta ɗalibar tasa tun zaburar farko da tai na dawowa hayyaci bata sake motsin kirki ba. Sai da taji hannunsa na ƙoƙarin shiga cikin ƙaramar rigarta ta sake zabura da ƙoƙarin dafe hannun nasa da nata tana son janye lips dinta da ya riƙe da nashi cikin kar-kar-war jiki. Babu alamar zai bata damar da take buƙatar, dan da gani dai yayi zurfi shi kam. Da sauri tasa dukan ɗan sauran ƙarfinta wajen jan jikinta baya, kamar zai riƙota sai kuma ya barta yana mai rumtse idanunsa da sukai wani irin mahaukacin kaɗawa jazur da ɗan ƙarfi. Baya ta juya masa tana mai dunƙule jikinta dake tsuma har yanzu waje ɗaya. Tunda Ummu ta haifeta tai hankali tai wayo babu wani da ya taɓa kai hannunsa inda Tajwar Eshaan ɗin ya kai yau a jikinta, kai itafa ko riga bata yarda ta saka gaban su Arfa ma dake yayunta tsabar yanda take jin kunya. Amma yau sai ga abinda batai zato ba, da ga mutumin da batai tsammani ba, wayyo ita Fhareedah ta ga takanta. Wani irin yarrrr yarrrrr take ji kamar har yanzu hannun nasa na'a jikin nata ne tsabar yanda ta firgita. Ɗaya da ga cikin filos ɗin da aka ƙawata gadon ta fisgo ta ƙanƙamesa a ƙirjinta dan ta kasa nutsarwa waje guda, da gaske ta tsorata tsoro irin wanda batajin ta taɓa shigarsa a rayuwarta, sai kawai wasu hawaye masu ɗumi da bata san na minene ba suka shiga rige-rigen sakko mata a kan fuskarta.
Ajiyar zuciyar da take ja mai tafiya da kamar shashshekar kuka-kuka ta sakashi buɗe lumsassun idanunsa da sukai wani irin shanyewa sosai, akan bayanta data juya rigar ta ɗage sosai saboda tattareta da yayi ya sauke su. Ya ɗan rufe ya ƙara buɗewa yana mai ƙarema bayan nata fari sol kallo. Wani irin harbawa zuciyarsa ta sakeyi da ɗan ƙarfi lokacin da idanunsa ke sake sauka kan wannan dai tawadar ALLAHr babba da ke a ɗan sama-saman bayan nata ta gefen kafaɗar dama. Da sauri yake ɗan girgiza kansa alamar hakan bazai yuwuba kama ce kawai da ga ALLAH. Ta inama hakan zata faru? (Kai noo.. noo.. ba haka bane) ya faɗa a cikin ransa da kaushi sosai yana ɗauke idanun nasa da ga wajen. Sai ma ya miƙe a matuƙar kasalance, zama yay ya ɗan bata baya, cikin muryarsa dake a matuƙar sarƙe ya furta, “Ga wani sirrin nan nawa na baki ki haɗa ki adana min”.
Batare da ya sake yarda ya kalleta ba ya nufi bathroom kawai yana mai sake ƙaryata zuciyarsa da taƙi amsar dagiyar tasa kan abinda idanunsa suka sake gani yau ma a jikintan........✍️


_Oh ohh girma ya daɗi🥱🚴🚴🚴🚴_




*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*


_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲


✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨
(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)



𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻



𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (38)




........Da wani irin zazzaɓi mai masifar zafi da ƙullewar ciki ya fito da ga bayin, amma kasancewar sa jarumin jarumai ya shanye komai yana cigaba da ƙoƙarin shanye wanda ma ke taso masa sabo. Babu kowa a ɗakin da alama Iffah ta gudu, dan rigarta da ya cire ce kawai yashe a ƙasa, sai dai babu after dress ɗin da alama ita ta saka ta fice. Samun kansa yay da ɗan sakin wani miskilin murmushi yana cije lips ɗinsa da azabar ƙarfi. Duk yanda yake son dannewa hakan ya gagara, dan wannan shine karo na farko da ya iya nisan kiwo da mace kamar haka. Hakan na nufin ya tsokaloma kansa abinda ya fi ƙarfin jarumtarsa, dan yanda cikinsa ke cigaba da ƙullewa har numfashinsa ya ɗan fara fisga lokaci zuwa lokaci. Duk da sanyin da ya fara ji na ratsa shi bai iya ya canja bathrobe ɗin jikinsa ba ga sumarsa ma jiƙe take da ruwa ya kai kan gado da ƙyar ya zauna, zufa yake ga jikinsa na tsuma abun kamar wani tsafi. Addu'ar da duk tazo bakinsa ya fara ambato da damƙo fillon data runguma ɗazun ya matse cikin hannunsa da azabar ƙarfin da ke bayyana asalin gwarzantakarsa. Wannan ranar yake gudu, wannan ranar ya ɗauka tsahon shekaru yana kaucemawa. Amma duk da haka sai da ta zo masa a gaɓar da bai shirya amsarta ba. Gaɓar da bai shirya fuskantarta ba. Gaɓar da bai shirya komai na yanda zai fara gudanar da ita ba. “Ya arrahaman”. Ya furta a hankali komai na masa kaikawo cikin gizo. Ya tabbatar idan har aka cigaba a haka to tabbas yau aiki zai buɗe, dan babu shakka kwaɓarsace zatai ruwa. Da ƙyar ya iya miƙewa, maganin da ya jima da daina sha ya shiga nema a inda ya tabbatar ya killacesa, da ƙyar ya samosa dan yayi nisa kasancewar ya daɗe da kauda idanunsa a shansa saboda abinda ka iya zuwa ya dawo kamar yanda doctor ya sanar masa har yay sanadin ajiyewar. Kwalin ya buɗe ya ciro, sai dai a mamakinsa babu komai a ciki sai kwafsan ashe ya shanyesa ma a wancan lokacin, bashi da zaɓin daya wuce sakin kwalin a wajen ya kai kwance yana jan bargo jikinsa dan rawar sanyinsa ƙaruwa yake yi, ga wani irin sarawa da kansa kemasa. Da gaske abubuwa sun masa matuƙar yawa, har ma yakan rasa wane irin tunani zaiyi. Ammien sa da sharaɗinta? Ko Iffah da abubuwan ban tsoronta? Ko Uncle's na sa da son zuciyarsu? Ko matsalolin talakawarsa da dogaransu kan jiran adalcinsa a koda yaushe? Ko.... Ko.... Ko.... Ɗin sun masa yawa, yawan da matsalar dake tattare da shi a yanzu kamar tana son nuna fin ƙarfinsu. Dan ya jima da fahimtar kansa, amma ya zama mayaƙi na gaske akan kansa da kare mutuncinsa da ga taɓa ƴar kowa. Babban fatansa a koda yaushe ALLAH ya bashi ikon riƙe kansa har zuwa ga halalinsa da zai iya bama sirrinsa, sirrin da yake fata bayan matar aurensa kar wani mahaluki ya taɓa koda kwatanta sani insha ALLAH. yana ganin ko yaƙi ko yaso lokacin yayi, sai dai lokacin yazo da wasu abubuwa masu nauyin gaske. nauyin da ya rasa ma ina ya kamata ya fara kamawa......

★A ɓangaren Iffah data sulale ta gudu tun bayan shigarsa bayi duk yanda tayi domin ganin ƙamshinsa ya bar jikinta hakan ya gagara. Tayi wanka, ta shafa nau'in turarruka daban-daban sai dai ƙamshin jikinsan na nan daram a cikin hancinta da yaƙi bata damar jin kowane ƙamshi bayan shi. Kamar wadda aka zarema lakar jiki tai sakwat a jikin bango tana lumshe idanu. Ita kanta bata san ainahin mima take ji a kansa ba, abinda kawai ta sani komai kawai ya ƙwace mata, bata da wani ƙarfi a zuciya da jikinta a halin yanzun, abinda ya farun kuma yay mata tsaiwar sojan badakare a ƙahon zuciya babu alamar zai motsa. Hanunnta ta kai ta shafi lips ɗinta, sai kuma tai saurin janye yatsun biyu tana mai girgiza kanta kamar wadda akema magana a kunne. Buɗe idanun nata tai cikin sauri ta sake nufar inda turarrukan suke, ɗaya bayan ɗaya ta dinga binsu tana shafama jikinta, ita dai a dole sai ta daina jin wancan ƙamshi. Abin dariya abin tausai harta gama ƙamshin na nan dai bata daina jinsa a cikin hancin nata ba duk da yanda ɗakin yay wani masifar haukacewa da ƙamshin data baza har ana jinsa waje. Miya rage kawai ta saki kuka ta huta, sai ko tai takwaf-takwaf da fuska kamar zata fashe...
Haka taita kai kawonta a ɗakin har mai gyarawa yazo gyara da sanar mata an gama shirya break fast. Da gaske yunwar take ji, amma bazata fita su haɗu da shi ba, dan haka ta bada umarnin kawo mata nan tana mazurai a karo na farko. Cikin ƙanƙanin lokaci aka cika umarnin nata kuwa....

★★.... ★....

A can fada tun kusan awa ɗaya baya ake tsammanin fitowarsa, amma shiru kakeji. Hakan abune da ba faruwa yake ba. Tajwar Eshaan mutum ne da baya saɓa alƙawari. In har yace zaiyi abu to zai yisan komai girman ƙalubale da zai iya fuskanta a yayin yinsa kuwa. Hakama in har yace bazai yiba tofa ko kai waye bazaiyi ɗin ba. Kaifi ɗaya ne shi, mai faɗa da cikawa. Mai gaskiya da son tabbatar da ita a mulkinsa, waɗan nan halayensa ne dake matuƙar sake ƙawatashi da kwarzantashi ga al'ummar sa a bayyane.
“Anya kuwa lafiya yau?”.
Miran Arshaan daya matsu da ganin fitowar Tajwar Eshaan ɗin ya taso zuwa inda Sayeed Fayzul-haq ke tsaye ya faɗa cike da nuna damuwa. Kai Sayeed Fayzul-haq ɗin ya jinjina masa shima da ƴar damuwar a fuskarsa. “Banajin matsala ce insha ALLAH. Dan ban daɗe da ganawa da shi ba, sai dai kasan mutum mai iyali...” ya ƙare maganar da wani ɗan murmushin su na manya. Kamar Miran Arshaan ya sokama Sayeed Fayzul-haq wuƙa a ƙirji yaji, dan haka kawai maganar iyalin na Tajwar Eshaan ta soki ransa, murmushi Sayeed Fayzul-haq ya ɗanyi yana kauda kai kamar bashi ya takalosa ba, dama kuma ya fadane da biyu....

★★..... ★....

Shikam mai gayya da aikin har akai sallar azhar bai gama samun kansa yanda ya kamata ba, dan haka yay sallarsa a ɗaki cikin ƙarfin hali. Rashin fitowarsa salla ya sa su Sayeed Fayzul-haq suka tabbatar da akwai dalili mai ƙarfi daya hana shi fitowar kam tabbas. Ya cigaba da son ganin ya dawo normal, hakan bata samu ba sai kusan gab da la'asar da ya sake komawa Gym ya maida kansa busy, dan wani irin mahaukacin work out yayi, kafin ya fito sharɓan da zufa idanun nan babu alamar rahama yau kam an tsokalo maza. Tsaf yay shiri cikin ɗan sauran ƙarfin da ke jikinsa, dan gaba ɗaya jinsa yake sai a hankali. Haka dai ya daure ya fito domin zuwa massalaci.
Iffah dake sharce ruwan alwala da tayo a fuskarta da wani irin sauri ta buɗe idanunta jin an buɗe ƙofar. Ido huɗu sukai da shi, da wani shegen sauri ta maida nata idanun ta rumtse da juyama ƙofar baya, cikin salon nasa na basarwa da shegen miskilanci da ƙasaitar nan tasa shima sai ya ɗauke kai tamkar bai ganta ba. Ta bayanta ya raɓa ya wuce, wasu takardu da ya ajiye ya ɗauka a kan study table ɗin ɗakin ya sake zuwa zai gittata. Tsaye take har yanzu idanunta a rufen ita a dole bata son su haɗa ido. Ƙirjin Iffah bugawa ya dingayi da sauri-sauri jinsa a kusa da ita, idanun ta buɗe kaɗan dan son tabbatarwa. Shi ɗinne dai a gabanta ya zuba mata idanunsa da ke cikin eyeglasses masu ɗan duhu. (Wayyo ni ALLAH) ta ambata a zuciyarta tana maida idanun ta rumtse a daburce ta ce “Barka da rana”.
Idanunsa dake a wani irin yanayin da ya tilasta mishi saka gilashin ya ɗan lumshe yana sake buɗewa a kanta. Cikin dakewar muryarsa dake ɗan shaƙe fiye da koda yaushe data sani kamar wanda akaima tilas acan ƙasan maƙoshi ya furta, “After Isha ki sameni”. Idanunta ta buɗe a firgice, sai dai shi

Please Login or Register in order to submit comment