Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

๏ปฟ ๐Ÿฅ‚ GIDAN MAZA ๐Ÿฅ‚


๐Ÿ’™๐Ÿ’ฆ ( THE MAFIA'S HOUSE ) ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’™




____FUNNY , DRAMATIC , REVENGE , ROMANCE & DESTINY ____




๐Ÿ”ฅ๐Ÿ‘‘ MALLAKIN AMIRA ABDOULAYE A.K.A MEERAH ๐Ÿ‘‘๐Ÿ”ฅ







GARGADI ! GARGADI !


WANNAN LITTAFIN MALLAKIN AMIRA ABDOULAYE ( MEERAH ) NE , BAN YARDA BA WANI KO WATA , YA SAUYA MIN KO DA KALMA DAYA CIKIN ABUN DA NA RUBUTA , YADDA KU KA GAN SHI , TO KU BAR SHI A HAKA , WANNAN KIRKIRAREN LABARI , BAN YI SHI BA DAN CIN ZARAFIN WANI KO WATA BA , BA LAIFINA NE BA IN YA YI KAMA DA RAYUWAR KU , YADDA MU KA FARA LITTAFIN NAN CIKIN AMINCIN ALLAH , INA FATAN ZA MU KAMMALA SHI A HAKA , IDAN NA FADI ABUN DA BA DAI'DAI BA , INA NEMAN AFUWAR KU , DUK KUMA WANDA YA ZAGE NI KO YA YI MIN WATA MUMUNAR FAHIMTA YA JE SHI DA ALLAH ...........................




FOR INFORMATION +22798999753 WHATSAPP ONLY



TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP
https://chat.whatsapp.com/LWmuu0yv6C9DAhpdepDb4i


https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i



*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM. mun fara da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai, da shi muka dogara kuma a gare shi kawai muke neman taimako Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Manzon Rahma ษ—an gata a wajen Allah, kuma fiyayyen halitta wato Annabi MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA๐Ÿค*





STEP ....... 1 โœ๐Ÿ”ฅโค




BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM




THE BEGINING




โ–ชNIGERIA ( JOS STATE )



Wani kasurgumin daji ne , babu allamun rai ko da ta dabbobi ce , ga wajen da mugun duhu allamun dare ne , ko yatsar ka ba ka iya gani saboda itacen dajin su na da mugun tsawo ga shi sun rufe wajen , hasken wata ba iya kawowa har kassa , cen na hango wata doguwar hanya , ta raba dajin gida biyu , hanyar doguwa ce , babu kwana ko guda , ga shi duk duhu ne wajen bare ka san akwai kwana ko babu

a hankali na hango wani haske ya na tunkaro ni , wata bakar mota ce , ke tafiya a hankali saman titin nan , da ga ganin motar ka san ba ta kananan mutane ba ce , tafiya ta ke a hankali da allamun wanda ke tukin ya na cikin nitsuwa

a hankali na kurewa motar kallo har ta karaso in da na ke
nan na ga wani dan dattijon ne a cikin motar , a shekaru zai kai 50 zuwa 55 haka , ya na sanye da kayan shadda , fuskar shi babu yabo babu fallasa , ga waya a kunnen shi allamun waya ya ke

cikin nitsuwa na jiyo Muryarsa ya na fadin " ki kontar da hankalin ki haba , ba abun da zai same ni , nan da one hour ina shigowa cikin gari , meeting din ce wlh ta tsayar da ni "

a daya bangaran kuwa , na jiyo Muryar wata mace ta na fadin " Abban Kausaar , don Allah ka koma cikin gari , ka sani kwanan nan garin babu security bare kuma cikin daji , don Allah ka koma kar wani abu ya same ka "

cikin sigar rarrashi ya ce mata " please ki kontar da hankalin ki , in sha Allah ba abun da zai....... "

bai kai karshen maganarsa ba ya ja burki a hankali
" Abban Kausaar lafiya ka yi shiru ? " Fadin matar nan dan ta ga bai kai karshen maganar shi ba

a sanyaye ya ce mata " ina zuwa , zan kira ki " ya na gama fadar haka ya katse kira ya ajiye wayar ya na kallon gabansa

ba komai ba ne ya gani sai wani dan saurayi ya juya mishi baya , ya na sanye da wasu bakaken kaya , gashin kan shi ya zubo har bayan keya , ya na rike da wata jump rope ya na tsalen shi cikin konciyar hankali

kalmar shahada mutumin nan ya karanta , ya na tunanin ko dai aljani ne , ga shi shi kadai cikin wannan kasurgumin daji , hankali konce ya na jump

a hankali ya bude kofar motar shi ya fito , zuciyar shi na duka uku uku , a hankali ya fara takawa ya na fadin " dan saurayi me ka ke yi a nan kai kadai ? ko dai ka bace ne ? "

a hankali dan saurayin nan ya saki kuka , ba tare da ya tsaya da ga jump din da ya ke ya ce " Uhm , Uhm , Ka bar wajen nan "

a hankali ya fara taku biyu baya ya na karanto addu'ar tsari
cak ya ga saurayin nan ya tsaya , ya daga kai sama ya bushe da wata shegiyar dariya ya na fadin " ni mutum ne , ba aljani ba , ba abun da addu'a za ta yi maka "

dum mutumin nan ya ji zuciyar shi ta buga , a dubu dari ya juya zai bar wajen
ya na juyawa ko ya ga wani saurayi zaune saman motar shi , ya na sanye da bakaken kaya shi ma , da face mask baka , ko idanun shi ba ka iya gani saboda wajen duk duhu ne , kafarshi na reto bakin motar , hannun shi rike da gun

cikin sanyin murya ya ce " don Allah ku kyale ni na tafi , don Allah ku kyale ni , akwai kudi cikin motata , ku dauki har motar ma don Allah ku kyale ni " ya kai karshen kamar zai yi kuka

wanda ke bayan shi ne ya ce " uncle , ba za ki wassa da ni ba " ya fada cike da shagwaba kamar wani dan karamin yaro

wanda ke zaune saman mota ne ya karbi zancen da cewa " ka yi sa'a fa , ba kowa Cookie ke yarda su yi wassa tare ba , Cookie ka na son mu yi jump ? " ya fada ya na lekon saurayin da ke bayan mutumin nan da allamun sunan shi Cookie

da sauri ya juyo , nan na ga ashe shi ma Face mask ya ke sanye da sai wani dan bandana black color daure a goshin shi
da sauri ya nufo mutumin nan , ya riko hannunshi ya mika mishi bakin jump rope din hannun shi , dai'dai lokacin da wanda ke saman mota ya diro , ya riko dayan bakin ya yi baya kadan ya na fadin " Oya , mu fara " ya fada ya na fara kada Igiyar ban

๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ Allah wadanan diyan iska ne ma ba kidnappers ba

ba dan ya so ba mutumin nan ya fara kada igiyar shi ma idanun shi cike da ruwa , ya ma rasa ya zai yi

a hankali Cookie ya shiga ya fara tsallaka igiyar ya na jump , ya na wata yar karamar dariya ya na fadin " Yeah , yeah , yeah ku ci gaba ya yi min dadi sosai "

nan take dattijon nan ya saki kuka ya na fadin " don Allah don son annabi ku kyale ni na tafi , don Allah "

" Joker , ka ce babu inda zai je , sai na gama wassa na " Cookie ta fada cike da shagwaba

Wanda ya kira da Joker ne ya ce " ai dama babu inda zai je "

ya na gama rufe bakin shi , wasu samari guda biyu su ka fito da ga cikin dajin ta bayan shi , su ma bakaken kaya ne a jikin su tak tak irin na Joker , su ma su na sanye da face Mask , gudan black , gudan kuma Green , mai sanye da Green din ya na rike da wata chaine a hannayanshi , ya kuma saka hula a kai

wani dan karamin tsaki ya ja ya na fadin " don Allah ku yi abun nan da sauri mu tafi , ni barci na ke ji , Joker , ka rabu da shirmen Cookie mu tafi don Allah "

a hankali Joker ya daina kada igiyar ya na fadin " I'm sorry cookie , bari idan mun je gida za mu ci gaba "

gyada mishi kai Cookie ya yi kafin ya nufi motar mutumin nan ya Haye ya na kallon su

ya na hawa Joker ya yi charging gun din hannunshi , ya saita kan dattijon nan
da sauri ya juya zai tsere , kawai sai ya ji ya bugi kirjin mutun har sai da ya fadi kassa ya na kallon shi
wasu samari ne biyu tsaye , suma sanye da bakaken kaya da face Mask , dayan na sdaure da bandana red color a goshin shi , dayan kuma bai tara gashin kai sosai ba , dan duk gashin su kamar na Cookie ne ya zubo har bayan keya

razana iya razana dattijon nan ya razana , dan har kuka kassa kassa ya ke ya bin su da kallo su biyar tsaye gaban shi , sai cookie da ke zaune saman motar shi ya na kallon su

a hankali me Green face mask ya karaso wajen dattijon nan ya riko kafafun shi ya ce " ba kai ba mara mutunci , ka na kashe yaran mutane kuma ka rufe zancen ? yau kai ma zan kashe ka , kuma na rufe zancen " ya fada ya na kokarin daure shi da chaine din hannun shi

cikin kuka ya ke fadin " don Allah ku kyale ni , kar ku kashe ni don Allah don son annabi Muhammad ( S.A.W ) "

" kai don Allah yi wa mutane shiru ka cika ni da surutu " wanda ya fito tare da mai green face mask ya fada


wanda bai tara gashi ba ne ya ce " Delta , Loven , Lunas , Joker , Cookie , ku daina min wannan shirmen naku , ku daure shi mu bar wajen nan tun rana ba ta fito ba , kai kuma Joker ka kona motar shi "

da sauri Cookie ya diro ya na fadin " Alexander , please na rike motar ? ta shiga raina wlh " ya fada ya na marairaice fuska

wanda ke geffen wanda ya kira da Alexander ne ya ce " soory Cookie , idan mu ka bar ka da motar nan za mu samu matsala "

me sanye da green face mask ne ya ce " Cookie , duk motocin da gareka ba su ishe ka ba , me za ka yi da wannan ? ko ten millions ba ta kai ba , ka bari zan yi maka order din sabuwa da ga US "

" Loven , ku yi aikin gaban ku , Cookie mu tafi " Alexander ya fada ya na mikawa Cookie hannu

da sauri Cookie ya riko hannun shi , su ka juya su ka koma cikin dajin nan ,
su na barin wajen Loven ya mike bayan ya gama daure dattijon nan da chaine , ya dauke shi ya saba a kafada , su ya bi bayan su Alexander

a tare su ma Delta da Lunas su ka bi bayan shi , Joker kuma ya nufi motar dattijon nan , sai da caje motar , ya fiddo duk wani abu mai mahimanci kamar su takardu amma ya bar kudi da phones din dattijon nan a ciki bai taba su ba

da ga haka ya nufi hanyar shiga cikin dajin nan , sai da ya zo dab da shiga sannan ya tsaya ya juyo , ya saita wajen zuba oil din motar da gun din hannunshi , sannan ya yi harbi wajen uku , nan take motar ta tashi kamar bomb ta kama da wuta
ya na ganin haka ya juya ya shiga cikin dajin

Tafiya su ke yi cikin wannan dajin babu ko tsoro , ba tare da sun san abun da ke jiran su ba a cen fitar dajin , da ga gani sun saba shigowa dajin nan , dan duk da wajen duhu ne sun san inda su ke takawa



โ–ชWASHE GARI โ›…โ›…



wajen zagaye ya ke da motocin sojoji , ga motar dattijon nan duk ta kone kurumus , sai zagayen motar su ke yi

su na a haka wata babbar mota baka kirin kirar Range Rover , ta iso wajen , ta ja burki , dan nesa kadan
da sauri daya da ga cikin sojojin nan ya nufi motar , geffen driver ya bude kofar ya daga kafa ya na sarawa na cikin motar

a hankali ya sa kafa ya fito , Wani kyakyawan Saurayi ne fari kal , amma ba cen ba , da ga gani ba cikaken bahaushe ba ne dan ya yi kama kadan da korean , a shekaru ba zai wuce 32 years ba , ya na da kananan idanu farare kal kamar madara , kwayar cikin su kuma blue ce mai mugun kyau , ga wani dogon hancin shi kamar pencil , da dan karamin bakin shi , lips dinshi duk pink color , bai tara gashi ba dan yanayin aikin shi ba a bari su tara gashi , duk da hakan gashin kan shi ya na da laushi , ya konta mishi gwanin burgewa

ya na sanye da kakin soja , sun zauna mishi sosai a jiki ga shi kuma ya na da murdaden jiki da fafaden kirji , rigar ta shi kamar ma ta yi mishi kadan , abun dai Masha Allah

cike da nitsuwa ya bude baki da wata zazzakar Muryarshi ya ce " what happened ? "

cike da girmamawa sojan da ya bude mishi " Sir , The Six Butterfly ne , yanzu ma sun sake KIDNAPPING "

bai ce mishi komai ba su ka fara takawa ya nufi motar , da sauri duk sojojin nan su ka raba gefe su na sara mishi
a hankali ya fara zagaye motar , ya na bin ta da kallo , babu wani abu da za a iya samu a matsayin shaida cikin motar , dan komai ya kone kurumus

a hankali ya dawo gaban motar ya na kallon sojojin shi ya ce " me a ka sani game da wanda su ka sace ? "

cikin girmamawa daya da ga cikin su ya ce " Sir , yanzu dai mu ke shirin yin binciken a kai "

a hankali ya gyada kanshi kafin ya ce " Okay , ina jiran dukkan bayanai nan da one hour " ya fada ya na fara takawa

" Yes sir " su ka fada a tare su na daga kafa su ka sara mishi
kai tsaye wajen motarshi ya nufa
cak ya tsaya , kafin ya juyo a hankali ya kalli wata igiya yade a kassan motar shi
a hankali ya ci gaba da takawar shi ya nufi wajen mai zaman banza , ya sa hannu ya bude kofar , bai shiga ba , sai ya zura hannun shi ya bude wani box ya fido wasu bakaken gloves kamar na leda sabi kal , ya saka a hannun shi , sannan ya fido wata plastic , ya juya ya rufe motar , sannan ya dawo gaban motar , ya ajiye plastic din saman hancin motar , kafin ya zube saman guyiwowinshi , ya duka ya kai hannu ya janyo igiyar sannan ya mike tsaye

laulaye ta ya yi , sannan ya dauki plastic din da ya ajiye saman motar , ya saka igiyar a ciki , sannan ya nufi wajen driver ya bude kofar ya shiga , ya ajiye plastic din saman kujerar geffen shi , ya tada motar , ya bar wajen da mugun gudu , ya na barin wajen sojojin nan su ka ci gaba da aikin su kafin su bar wajen su ma




๐Ÿฅ‚ GIDAN MAZA ๐Ÿฅ‚



๐Ÿ‘ป( THE MAFIA'S HOUSE )๐Ÿ‘ป





____FUNNY , DRAMATIC , REVENGE , ROMANCE & DESTINY ____




๐Ÿ”ฅ๐Ÿ‘‘ MALLAKIN MEERAH ๐Ÿ‘‘๐Ÿ”ฅ









FOR INFORMATION +22798999753 WHATSAPP ONLY



TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP
https://chat.whatsapp.com/LWmuu0yv6C9DAhpdepDb4i


https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i





ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ูู…ู‘ูŽ ุตูŽู„ู‘ู ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏู ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุตูŽู„ู‘ูŽูŠู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ู‘ูŽูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒุŒ ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ูู…ู‘ูŽ ุจูŽุงุฑููƒู’ ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏู ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุจูŽุงุฑูŽูƒู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ู‘ูŽูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒโค๏ธ





STEP ....... 2 โœโค๐Ÿ”ฅ






Wani kyawatencen parlour ne , komai na cikin shi white color ne , ya kyawatu da wasu lamusasun Sofas white color ma su mugun laushi , da ga tsakiyar su kuma wani chinesse carpet red color mai mugun kyau , an daura wata table ta glass da ga sama

nan na hango Cookie konce saman sofa three seaters ya tada kai da cinyar Joker sai wassa ya ke da hannayanshi a sama kamar wani karamin yaro

a geffen sofar kuma Delta da Loven su na zaune saman sofa guda su na rike da wayoyinsu
Lunas kuma ya na konce saman sofar da ke fuskantar ta su Loven , ya daura hannu saman forehead ya lumshe idanunshi
har yanzu dai bakaken kayan nan ne a jikin su har da face mask ba su cire komai ba , amma yanzu na Samu damar ganin idanun su kuma duk iri daya ne kwayar cikin su baka ce kirin

su na a haka Alexander ya fara sauko stair da sauri sauri ya karaso cikin parlourn kai tsaye sofar su Cookie ya nufa ya na fadin " Cookie , where is your jump rope ? "

a hankali Cookie ya sauko da kafafun shi kassa ya mike zaune ya na fadin " what happened ? "

da sauri Alexander ya ce " Cookie , tambayar ka na ke ina ka baro igiyarka ? "

cikin rudu Joker ya ce mishi " ina ga mun baro ta saman hanya , wani abu ya faru ? "


Please Login or Register in order to submit comment