Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cream yau ba zan fita ba " ya kai karshen ya na kai cookie a baki

da to kawai su ka amsa mishi kafin su nufi kofar fita parlourn su fice
cikin nitsuwa Abeeram ya ci gaba da shan smoothie din shi ,
sai da ya share wajen ten minutes a haka kafin Ya jiyo takun Ashur ya na sauko stair

ya na sanye da wani Trouser brown color da wata Polo red color mai dogayen hannu da sneakers farare a kafafun shi ya na taku cikin nitsuwa

a haka har ya karaso cikin parlourn ya zauna geffen Abeeram ya kai hannu ya dauki cookie guda ya kai a baki kafin ya ce mishi " Abee , please cewa Chef ya kawo min breakfast "

turo dan bakin nan nashi Abeeram ya yi ya na fadin " ni gaskiya babu inda zan je , ka kira shi mana "
" ka ga abun da ke gama ni da kai , please je ka amso min "
wani dan karamin gunguni Abeeram ya yi kafin ya mike tsaye a hankali ya fara takawa ya nufi kitchen ya na turo dan bakin nan nashi

da kallo Ashur ya raka shi har sai da ya shiga sannan ya yi wata yar karamar dariya
Ko one minute bai yi ba da shiga ya fito ya na faman turo baki ya dawo saman sofar ya zauna

ya na zama ko Chef ya fito da ga cikin kitchen din rike da tray , dama ya riga da ya shirya komai kawai jira ha ke Ashur ya fito

kai tsaye saman center table ya ajiye kafin ya juyawar shi ya koma kitchen
ya na barin wajen Ashur ya fara yin breakfast din shi cikin konciyar hankali

a hankali Abeeram ya konta mishi a saman shoulder
wani dan karamin murmushi Ashur ya saki kafin ya ce " what happened ? "

a sanyaye Abeeram ya ce mishi " Ashu , akwai wata yarinya a university din mu , kullum in na je na yi mata magana sai ta kyale ni , ko gaishe ta na yi ba ta amsawa ni kuma gaskiya ba na jin dadin hakan saboda duk makarantar ita kadai na ke bude baki na gaishe ta amma ta share ni "

murmushi mai dan sauti Ashur ya yi kafin ya ce " na tambaye ka mana ? me ya sa ka ke gaishe ta , tun da ba ta amsawa ka kyale ta kawai "

cike da shagwaba Abeeram ya ce mishi " Ashu , ba zan iya ba , ko na ce ba zan yi mata magana ba sai na yi mata , ban san me ya sa duk lokacin da na gan ta sai na ji wani bakon yanayi cikin zuciyata , jiya har mafarkin ta na yi ta na min magana "

wani dan karamin murmushi Ashur ya saki ya na ga fa autan nasu ya fada tarkon soyayya , to wacece wanan yarinyar ?

ya yi nisa duniyar tunanin shi kawai ya jiyo Muryar Abeeram ya na yi mishi kukan shagwaba ya na fadin " Ashu , please tell me ya zan yi na daina kula ta , ni ba na ma son na sake ganin ta , please ka yi wa captain magana a sauya min university ni ba na son wannan , in kuma ba a sauya min ba ba zan sake zuwa makarantar ba "

wata yar karamar dariya Ashur ya yi kafin ya juyo ya kalli dan uwan nashi ya ce " ka na ji ko Benji ? gobe idan ka koma school ka je ka fada mata wannan abun da ka fada min , amma in ka tashi fada mata ka yi kamar ka na cikin bacin rai , ka yi maganar da dan karfi yadda za ta ji tsoro , ita da kanta za ta yi maka magana nan gaba "

wani kyawatencen murmushi Abeeram ya saki ya na fadin " Ashu da gaske ka ke za ta min magana ? "

a hankali Ashur ya gyada mishi kai ya na murmushi ya ce " Eh , in kuma bayan haka ba ta yi maka magana ba , ka dawo ka fada min zan yi maka maganin ta "

wata yar karamar dariya Abeeram ya yi kafin ya ce " shikenan , yanzu tashi ka je ko ? kar fa ka yi late "

da to kawai ya amsa mishi kafin ya kammala breakfast din sa , ya sha ruwa , sannan ya mike tsaye , ya dan sunkuyo ya mannawa Abeeram kiss saman forehead , da kumatu , sannan ya yi mishi kiss saman lips din sa kafin ya ce " sai na dawo "

wata yar karamar dariya ya yi kafin ya ce " ni ka daina yi min kiss saman lips , ba na so " ya fada cikin yar shagwaba

murmushi mai dan sauti Ashur ya yi ba tare da ya ce komai ba , ya fice gidan




๐Ÿฅ‚ GIDAN MAZA ๐Ÿฅ‚



๐Ÿ‘ป ( THE MAFIA'S HOUSE ) ๐Ÿ‘ป




____FUNNY , DRAMATIC , REVENGE , ROMANCE & DESTINY ____




๐Ÿ”ฅ๐Ÿ‘‘ MALLAKIN MEERAH ๐Ÿ‘‘๐Ÿ”ฅ






FOR INFORMATION +22798999753 WHATSAPP ONLY




https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i




TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP
https://chat.whatsapp.com/LWmuu0yv6C9DAhpdepDb4i











ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ูู…ู‘ูŽ ุตูŽู„ู‘ู ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏู ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุตูŽู„ู‘ูŽูŠู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ู‘ูŽูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒุŒ ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ูู…ู‘ูŽ ุจูŽุงุฑููƒู’ ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏู ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุจูŽุงุฑูŽูƒู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ู‘ูŽูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒโค๏ธ





๐Ÿ†‚๐Ÿ†ƒ๐Ÿ…ด๐Ÿ…ฟ ____ 4 โœ โค ๐Ÿ”ฅ







ko da ya fito parking space ya nufa , inda ya shiga daya da ga cikin dankararen motocin da ke cike a wajen , goma ma Albarka

da ga haka ya danna hancin motar saman titi ya baro gidan ,
ya na haka kawai ya ji wayarsa ta ringing , ba tare da ya tsayar da motar ba ya kai hannu cikin aljihunsa ya fiddo wayar , ya duba screen din

wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya dauki kiran ya kai wayar a kunne ya na fadin " Hi guys , ya a ke ciki ne ? "

a daya bangaran murya wani saurayin na jiyo ya na fadin " me fa a ke ciki , prof bai zo ba yau ma "

wani dan karamin tsaki Ashur ya ja , sannan ya ce " Allah prof din nan Ya raina mana hankali , ya san irin barcin da na ke ji amma na tashi a haka na shirya ? "

wata yar karamar dariya saurayin nan ya yi kafin ya ce " kai guy kontar da hankalinka , mu hadu a restaurant zan fada maka abun da ya faru "

" okay " Ashur ya fada a takaice kafin ya sauko wayar ya katse kiran
kai tsaye restaurant din da su ke haduwa da friends din sa ya nufa , dama restaurant din cikin unguwar ya ke , ko ten minutes bai yi ba ya isa

ko da ya je , ya yi parking din motar a parking space , ya sauko ya shiga restaurant din
a irin wannan lokacin babu mutane dayawa a cikin restaurant din , kowa ya tafi wajen aiki
clients din ba su wuce ten ba

cen na hango wasu samari uku cikin VIP Space , sai hira su ke su na dariya
kai tsaye su Ashur ya nufa , da sallama a bakinsa ya iso wajen ya janyo chair ya zauna

a tare su uku su ka amsa mishi sallamarsa ,
wanda ke fuskantar sa ne ya ce " guy lafiya ka ke yamutse fuska tun da safe ? ko ba ka yi breakfast ba ? " ya fada cikin yar zolaya

wani dan karamin tsaki Ashur ya yi kafin ya ce " Aryan ka kyale ni kawai , wlh prof din nan ya bata min rai , wai ka san yadda na kashe kaina jiya , kawai saboda exams din yau , amma dan banza bai zo ba "

wanda ke geffen damarsa ne ya dafa shoulder din sa ya na fadin " calm down bro , wai ba ka da labarin abun da ya faru ? "

" me kuma ya faru ? " Ashur ya fada ya na yamutse fuska

" kidnapping din sa a ka yi , jiya ya dawo da ga Jos , wajen taron da su ka yi , da ga nan a ka yi kidnapping din sa , ba abun da a ka samo nasa , ko motarsa sai da su ka saka mata bomb "

zaro idanu Ashur ya yi kamar za fu fado kassa , a rude ya ke fadin " kidnapping fa ? how ? su wa su ka yi kidnapping din shi ? "

" ya wuce gang din Six Butterfly , ni fa na gane tsarin kidnapping din su , ina jin labarin nan na san da su ne " Fadin Aryan

iska Ashur ya furza da ga bakinsa , kafin ya koma ya jingina bayansa da chair din ya na fadin " yanzu ya familyn nasa ? wane hali su ke ciki ? "

na geffen hagunsa ne ya amsa mishi da cewa " matarsa ta na likita , lokacin da ta ji labarin zuciyarta bugawa ta yi ta fadi , har yanzu ba ta farfado ba , yarinyarsa kuma ba wanda ya san inda ta yi , tun lokacin da ta sa kafa ta bar gidan ta na kuka ba ta dawo ba , wlh har sun ban tausayi wlh "

wani dan tsaki Ashur ya yi kafin ya ce " Aryan , Karim , Bill , ina ga gida kawai zan koma , i'm not feel well " ya fada cikin sanyin murya

dafa shoulder din sa ya ce " ba za ka tsaya ba ? Zee fa ta ce ta na nan zuwa "
a tare su uku su ka bushe da dariya kafin Aryan ya daura da cewa " guy yarinyar nan ta na bala'in son ka , kar ka so ka ga mazan da ke bin bayanta ko number ce ta ba su amma ta ki , ita kai kadai ta ke so , you're very lucky "

wani dan karamin murmushin gefen fuska Ashur ya yi kafin ya ce musu " you're crazy , na fi karfin na jira Mace , sai dai ita ta jira ni , in ta zo ku ce ta neme ni in ta na son magana da ni " ya na gama fadar haka ya mike tsaye ya juya zai bar wajen

bai yi taku biyu ba ya tsaya cak waje guda ya na kallon kyakyawar budurwar da ke shigowa wajen
ba laifi yarinyar ta hadu gaskiya , a shekaru za ta kai 18 or 19 years haka , skin din ta chocolate mai mugun kyau , da ga gani renon madara da ice cream ce , bul bul da ita ga shape Masha Allah ,
ta na sanye da wando palazzo Pink color da T-shirt purple mai dogayen hannu , ta yi Rowling wani veil white color a kanta , da wasu medical glass white a idanunta , sai school bag din ta pink color
ta na tafiya a sanyaye
tun da Ashur ya sauke idanu saman ta ya tsare ta da ido ya na sakin wani dan karamin murmushin gefen fuska

a haka har ta karaso gabansa ta tsaya ta saki wani dan karamin murmushi, murya cen kassan makoshi ta ce mishi " tafiya ka ke shirin yi ? "

slowly ya juya ya kalli su Aryan da su ka tsare shi da ido su na kus kus
wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya juyo ya ce mata " me ki ke yi a nan ? "
dan sunkuyar da kai ta yi kafin ta ce " prof din mu ba ta zo ba , shi ne da na ji ka taho nan na biyo ka na ji yaushe za ka fara min lectures din dan mun kusa fara exams ? "

wani dan karamin murmushin gefen fuska ya saki kafin ya matso dab da ita ya kai bakinsa wajen kunnenta ya yi mata rada ya na fadin " now ina son na tafi Police Station , zuwa yamma mun yi waya sai mu San yadda za mu yi " ya na gama fadar haka ya raba ta geffenta ya wuce
ya bar ta nan tsaye ta na sakin murmushi kai a sunkuye

sai da su ka bari Ashur ya fice restaurant din , sannan su ka taso su uku su ka tsaya a gabanta
Aryan ne ya fara ce mata " ki na wassa da wuta Rehan , kin san irin son da Zee ke yi wa Ashur , shi ne ki ke kokarin shiga hanyarta ? kin fa san wacece Zee kan abun da ta ke so "

ko sannu Rehan ba ta ce musu ba ta juya ta fice restaurant din dama saboda Ashur ne ta zo , to ta samu abun da ta ke so

sai da ta fita sannan Bill ya kalli Aryan ya ce " wai me ya sa duk kyawawan yan matan universityn mu Ashur su ke so ? , shi ko kula su ba ya yi "

dariya Karim ya yi kafin ya ce " wace Mace za ta ga Ashur ta kassa kamuwa da son sa ? dubi fa hadaden gaye ne ga kudi ga basira , ga izza ga karfin Hali , ai dole su fada , kai dai ba abun da za mu ce sai dai Allah ya zaba mishi mafi al'heri gare sa "

" kai ka fada , dan ma su ga Captain ne ba , ko Abiram na san sai sun haukace , specially Abiram da wani dan bakinsa kamar pen " Bill ya fada ya na dariya
a haka su ka sa kafa su ka fice restaurant din su na hira su na dariya


NIGERIAN POLICE FORCE COMMAND HEADQUATERS ( N.P.F.C.H )


Zaune ya ke cikin wani kyawatacen Office , da gani ka san ba office din karamin jami'i ba ne dan komai na cikin sa a gyare a goge har wani sheki su ke yi

cen na hango sa zaune saman office chair din sa , ya na rike da jump rope din da ya samo a wajen crime scene din , sun kai ta a yi test ko sun samu print amma ba abun da su ka samo kamar wajen fiddo ta da ga cikin ledarta ne ta fado , ya yi tunanin wannan rope din za ta kasance hujjarsa ta kamo the Six Butterfly , amma kash

ya na a haka Ashur ya turo kofar Office din ya shigo ya na sallama
wata boyayyar ajiyar zuciya Captain ya sauke kafin ya ajiye jump rope din hannunta saman table din ya juyo ya na amsa wa Ashur sallamarsa

cikin nitsuwa ya karaso cikin office din , ya janyo chair ya zauna ya na fadin " lafiya na ga ka yi sanyi ? "

" ka san abun da ya faru da prof din ku ? " Captain ya jefo mishi tambayar

" yeah na sani , yanzu a ke fada min , ina ga nan gaba sai mun shiga confinement dan Gang din nan ya na neman hana fita garin Jos "

" ni abun da ya tsaya min a rai shi ne ina ma su ke kai mutanan da su ka sace ? wajen mutum goma su ka sace amma babu su , babu alamun su , ko kudi su ke so ya kamata a ce yanzu sun kira sun fadi abun da su ke so , amma shiru , ni na fara tunanin anya ba gomnati ba ke anfani da su wajen kawar da makiyanta ba , abun nan ya daure min kai wlh "

shiru Ashur ya yi bai ce mishi komai ba ya na kallon shi cikin ido
sun yi wajen one minute a haka kafin Ashur ya bushe da dariya har da buga table din
wata yar karamar dariya Capitain ya yi kafin ya ce mishi " wannan dariyar taka sai a hankali , don Allah tashi fice min da ga nan ina son na yi aikina "

tsagaita dariyarsa Ashur ya yi kafin ya ce " Sorry , abun da ka ce ne ya ban dariya , yanzu a ce duk fadin jami'an tsaron Nigeria a ce kun kasa kamo 6 guys ? haba don Allah , ai duk wannan shirme ne "

murmushi mai dan sauti Captain ya yi kafin ya ce " in ka na ganin karamin aiki ne bismillah , zan ba ka matsayina na Captain tsawan one week , duk shawarar da ka yanke duk abun da za ka yi ba wanda zai yi kokarin tsayar da kai , na ga in ka iya kamo su tun da ka dauki abun wassa "

" shikenan na yarda , za ka gani , cikin one week zan kawo maka su " ya fada cike da gwarin guyiwa

wani dan murmushi mai sauti Captain ya yi kafin ya ce " okay , in na sauka zan kai maka paper din yarjejeniyar mu , da ga gobe kai za ka fara aiki cikin office din nan , a matsayin Captain , yanzu tashi ban waje "

ba musu Ashur ya mike ya na murmushi
kafin ma ya bar wajen chair din Captain ya ce mishi " amshi , kai wa Benji Rope din nan , ba za ta anfane ni ba "

ba musu ya karbi Rope din ya juya ya fice office din ya na murmushi
Captain kuma ya ci gaba da aikinsa


โ–ชUNITED KINGDOM ( LONDON )


โ–ชThe Mayor's Office for Policing And Crime (MOPAC)


a Zaune Jimy ya ke cikin kyawatacen office din sa , ya na faman latsa laptop din da ke gabansa ya na aikinsa cikin konciyar hankali
ya na zaune a ya jiyo wayarsa ta na ringing
hannu ya kai ya dauki wayar ya na kallon screen din ya ga lambar ba ta yi kama da ta U.K ba
cen sai ya saki wani dan karamin murmushi ya dauki kiran ya kai wayar a kunne ya na fadin " Hi , Sai yanzu ki ka samu ki ka kira ni ? "

a daya bangaran muryar wata mace na jiyo ta na fadin " I'm sorry , wlh sai yanzu na samu na gane lamarin garin ka san ba jima rabo na da Nigeria , wasu abubuwa duk sun sauya min , kuma kar ka manta Undercover na ke nan , sai na yi created personage di na "

" na dai ji ke kullum ki na da excuse din kare kan ki , yanzu ya a ke ciki ? aikin mu ya na tafiya ne ? "

" har yanzu ban shiga gidan ba , amma yanzu haka ina opposite din gidan , duk wani me shiga da fita ina sane da shi "

" sai kin yi fa a hankali , ba karamin hatsari ne da su ba , move guda za ki yi su gano ki , dan kaifin basira ne da su , ki yi tunanin mutanan da za su iya yin sata a China da U.K . Europe zuwa Dubaรฏ , kuma su bar kassar ba tare da an kama su ba , kin san ba karamar kwakwolwa ce da su ba "

a hankali na jiyo ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce " Haka ne , zan kiyaye in sha Allah , kawai ka yarda da ni "

" na yarda da ke , that's why ma ke na tura a wannan mission , duk wata information da ki ka samu , ko da suna ne ki yi saurin fada min , ke ma kin san in mu ka yi nassarar kama su ba karamar girmamawa za mu samu ba "

wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " kar ka damu zan kiyaye komai , you gonna be proud of me "

murmushi mai dan sauti ya yi kafin ya ce " i'm always proud of you my officer , take care of yourself , za mu yi waya da ga baya "

" okay sai ka ji ni " ta na gama fadar haka ya ji kawai ta tsinke kiran
sauko wayar ya yi ya na murmushi kafin ya ajiye ta gefe ya ci gaba da aikinsa

( ๐Ÿค”๐Ÿค” To fa , bari dai na yi shiru mu ci gaba )



โ˜† UNITED STATE OF AMERICA โ˜†

โ™ก WASHINGTON DC โ™ก



Wani kyakyawan Matashi ne zaune cikin wani kyawatacen office mai girman Bala-i kai ka ce parlourn wani gida dan har sofas na hango cikin office din , ga shi ko komai na cikin office din white color ne , ga haske da ke shigowa ta ko ina saboda duk wajen glass ne

Matashin kyakyawa ne ajin farko , fari sol da shi kamar ka taba jini na fito , ya na da sexy eyes farare kal kamar madara kwayar cikin su kuma Green ce mai kyau , bayan wadanan idanun green ba abun da ya banbanta shi da Captain da Abiram , su na kama tak tak da ga gani dan uwansu ne har wannan lalawsan gashin nasu sai dai shi wannan brown ne nashi , kuma ya na da karfafar surar jiki kamar dan danbe , a shekaru zai kai 34 haka zuwa 35
ya na sanye da wasu





๐Ÿฅ‚ ๐‘ฎ๐‘ฐ๐‘ซ๐‘จ๐‘ต ๐‘ด๐‘จ๐’๐‘จ๐Ÿฅ‚



๐Ÿ’™๐Ÿ’ฆ ( แด›สœแด‡ แดแด€า“ษชแด€' s สœแดแดœsแด‡ ) ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’™




___FUNNY , DRAMATIC , REVENGE , ROMANCE & DESTINY ___




๐Ÿ”ฅ๐Ÿ‘‘ ๐Œ๐€๐‹๐‹๐€๐Š๐ˆ๐ แดแด‡แด‡ส€แด€สœ ๐Ÿ‘‘๐Ÿ”ฅ


The writer of
๏ผด๏ฝ๏ฝ•๏ฝ’๏ฝ‰๏ฝŽ ๏ฝš๏ฝ•๏ฝƒ๏ฝ‰๏ฝ™๏ฝ
๏ผฅ๏ฝ˜๏ฝ‰๏ฝŒ๏ฝ…๏ฝ„ ๏ผฐ๏ฝ’๏ฝ‰๏ฝŽ๏ฝƒ๏ฝ… ( ๏ฝŒ๏ฝ๏ฝ–๏ฝ… ๏ฝ๏ฝ…๏ฝ…๏ฝ”๏ฝ“ ๏ฝ๏ฝ๏ฝ—๏ฝ…๏ฝ’ )
๏ผด๏ฝ—๏ฝ ๏ฝŒ๏ฝ‰๏ฝ‡๏ฝˆ๏ฝ”๏ฝ“ ( ๏ผน๏ฝ๏ฝ’ ๏ฝŠ๏ฝ๏ฝ’๏ฝ‰๏ฝ„๏ฝ )
๏ผด๏ฝ๏ฝ•๏ฝ’๏ฝ‰๏ฝŽ ๏ผบ๏ฝ•๏ฝƒ๏ฝ‰๏ฝ™๏ฝ ( ๏ผฒ๏ฝ…๏ฝ”๏ฝ•๏ฝ’๏ฝŽ )
๏ผฆ๏ฝ๏ฝ‰๏ฝ’๏ฝ๏ฝ”
๏ผณ๏ฝ๏ฝ™๏ฝ๏ฝ™๏ฝ™๏ฝ๏ฝ’ ๏ฝ‡๏ฝ๏ฝ“๏ฝ‹๏ฝ‰๏ฝ™๏ฝ ( ๏ผด๏ผฒ๏ผต๏ผฅ ๏ผฌ๏ผฏ๏ผถ๏ผฅ )
๏ฝ๏ฝŽ๏ฝ„ ๏ฝŽ๏ฝ๏ฝ— ๐†๐ˆ๐ƒ๐€๐ ๐Œ๐€๐™๐€ ( ๐“๐‡๐„ ๐Œ๐€๐…๐ˆ๐€'๐’๐‡๐Ž๐”๐’๐„ )


FOR INFORMATION +22798999753 WHATSAPP ONLY




ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ูู…ู‘ูŽ ุตูŽู„ู‘ู ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏู ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุตูŽู„ู‘ูŽูŠู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ู‘ูŽูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒุŒ ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ูู…ู‘ูŽ ุจูŽุงุฑููƒู’ ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏู ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุจูŽุงุฑูŽูƒู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ู‘ูŽูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒโค๏ธ




๐Ÿ…‚๐Ÿ…ƒ๐Ÿ„ด๐Ÿ„ฟ ____ 5 โœ โค ๐Ÿ”ฅ






ya na sanye da wasu Suit white color da ga gani tsadadu ne dan har wani shining su ke kamar yanzu a ka fiddo su da ga cikin leda
ya na rike da waya a kunnensa da alamun kira ne ya ke , amma lips din sa sam ba su motsi
cen na hango wata kyakyawar mage fara kal konce saman office din sa , ta na barci , da hannunsa guda ya na shafa bayanta

a haka na ga ya motsa lips din sa a hankali kamar an yi mishi dole , da wata zazzakar sexy voice din sa ya ce " no , Next week ne zan tafi , ku tabbatar an yi duk wasu shirye shiryen da su ka dace "
ya na gama fadar haka ya sauko wayar ya ajiye saman table din
na ga ya saki wani dan karamin murmushi gefen fuska

Please Login or Register in order to submit comment