Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


har Alexander ya bude baki zai yi magana Lunas da ke konce ya ce " akwai imprint din yatsunku a sama , Idan su ka samu igiyar wajen yin investigation to...... " ya na gama fadar haka ya yi shiru abun shi ba tare da ya bude idanunshi ba

a hankali Loven mai sanye da green face mask ya ce " Cookie , why ba ka tunani kafin ka yi abu , yanzu a ka samu fingerprint din ka , cikin sauki za su iya gano mu "

" ya kamata mu koma mu dauko igiyar nan " Fadin Delta

wata yar karamar dariya Cookie ya yi ya na fadin " ku dai kun cika tsoro wlh , i'm not stupid , tsaya ku gani " ya fada ya na kai hannu ya tada fatar hannunshi kamar scotch , nan na ga fatar hannu nashi ta gaskiya

" ka gani , fake ne , kun taba ganin leda da Fingerprint ? , ba abun da zai faru ku kontar da hankalin ku " Cookie ya fada ya na tilla scotch din gefe

a tare duk su ka sauke wata nanauyar ajiyar zuciya kafin Alexander ya ce " okay , ya kamata mu koma gida yanzu , kar ku manta ku na da school gobe " ya na gama fadar haka ya nufi stair ya Haye

ya na hawa Cookie ya kalli Joker ya ce " Joker , mutumin da mu ka dauko kuma fa ? ya zamu yi da shi ? "

a hankali Lunas ya sauko da kafafunshi kassa ya mike zaune ya na fadin " kar ka damu , tare da sauran za mu hada shi , har Big bro ya dawo "

da sauri Cookie ya ce " Big bro zai dawo ? " ya fada ya na dan zaro idanu

hannu Joker ya daura hannu saman kan Cookie ya na fadin " yeah , Next month ya ce zai dawo "

mikewa tsaye Cookie ya yi ya na tsalle kamar wani karamin yaro ya na fadin " yeah , yeah big bro zai dawo , Big bro zai dawo " ya kai karshen ya na nufar Stair da gudu ya haye

daya bayan daya su ma su ka fara mikewa su ka nufi stair su na hayewa



▪UNITED KINGDOM ( LONDON )


▪The Mayor's Office for Policing And Crime (MOPAC)



wata babbar meeting room ce , ga wata doguwar Table a tsakiya zagaye da office chairs guda 20 , goma a wannan geffen , goma a wancen geffen , sai wasu guda uku da ke da ga tsakiya su na fuskantar wata makekiyar Tv plasma makale a bango

cen na hango wasu sojoji guda ashirin zazzaune saman chairs din duk shekarun su ba za su wuce tsakanin 30 to 35 ba , kowane gaban shi akwai laptop da bottle din ruwa

sai wasu guda uku zaune saman chair din tsakiya , suma sanye da kaki , sai dai na tsakiyar suit ne bakake a jikin shi kuma da ga gani zai fi su shekaru dan gashin kan shi duk fari ne

cikin nitsuwa ya fara magana da dan karfi ya na fadin " UK , Europe , China , Dubaï , duk babu inda The six Butterfly ba su yi sata ba , ba kuma kananan kudi ba , ya a ka yi har yanzu ba ku kamo su ba ? zaman me ku ke yi ? "

cikin girmamawa daya da ga cikin sojojin ya mike ya na fadin " Sir , ba fa kananan barayi ba ne , manyan Mafias ne , yanzu haka tare da jami'an tsaron Europe mu ke kan wannan case , but sir wlh yaran nan mugun wayo gare su , yadda mu ke tunani duk sun wuce hakan "

cikin bacin rai wanda ke zaune geffen damar me suit ya ce " zamen me ku ke yi ? wajen one milliards of soldiers amma kun kassa kamo kananan yara shidda da ba za su wuce 20 years ba , ba fa kananan kudi su ke sata ba , a china One milliards su ka sace , 500 millions a Dubaï mu nan UK a bar ma zancen dan mu koma saniyar tatsar su , Jira ku ke sai sun gama kwashe kudin garin ? "

" i'm sorry sir " ya fada kafin ya koma ya zauna

a hankali guda cikin su ya mike tsaye ya na rike da laptop din shi ya ce " Sir , ina ga na samo track din su "

"okay mu na sauraron ka " wanda ke sanye da suit ya fada

shiru wanda ke tsaye ya yi , ya na ci gaba da latsa laptop din shi , ya dauki one minute a haka kafin , Tv din nan ta kunnu ita da kan ta , ta na kamawa ko sai saman map din Nigeria

a hankali ya ajiye laptop din kafin ya fara takawa ya karaso gaban Tv din ya ce " Sir , wannan garin a cikin Africa ya ke , last night na fado saman wani reportage à kan kidnapping din da ya addabi garin cikin watanin ban , kuma sunan Gang din The Six Butterfly , abun da ya sa ba mu taba kamo su saboda a Nigeria su ke tserewa , please cikin mu akwai wanda ya taba yin tunanin neman su a Africa ma kadai ? "

shiru duk su ka yi dan ba karya ya yi ba , babu wanda ya taba yin tunanin fita UK dan neman wadanan barayin , yanzu kuma a cen kidnappers ne

( 🤔🤔🤔 idan na gane Gang din nasu sunan shi The Six Butterfly ? , a Nigeria su yi kidnapping , wajen ta kuma su yi Satar kudi ? )

cikin nitsuwa ya dawo ya dauki laptop din shi ya ci gaba da latsawa , nan take pics din Alexander ya bayana a saman Tv din

ajiye laptop din ya yi ya na fadin " ALEXANDER , DELTA , LUNAS , LOVEN , JOKER & COOKIE , shi sunayansu , yanzu ya kai mutum goma su ka yi kidnapping , ba su kira ba bare su fadi kudin da su ke so , kuma har yanzu babu wanda ya san ina su ka kai mutanan goma , Idan mu na son mu kamo su , mu kawo karshen satar da su ke yi dole sai mun bi ta Nigeria "

" Fine , ya kamata mu kamo su tun kafin Mr president ya sa baki cikin wannan harkar "

" that's why we decided to send one of our elements there undercover to lead the investigation "

" okay , yanzu yaushe za ta tafi ? kuma wa ku ka aika ? "

" i'm sorry sir , tun jiya ta tafi , duk wani abu da a ke ciki za ta fada mana , we keep contact "

a hankali ya mike tsaye , da sauri duk sojojin nan su ka mike su ma
cikin nitsuwa ya ce musu " nan da one month ina son ganin yaran nan a prison,"

a tare su ka daga kafa su na sara mishi su na fadin " yes sir ! "
bai ce musu komai ba ya nufi kofar fita ya fice , su ma biyun da ke geffen shi su ka bi bayan shi su ka fita

sai da su ka fita sannan sojojin nan 20 su ka sauko da hannayan su , kowane ya shiga tattare kayan shi

wanda ya fara yin magana ne da farko ya nufi wanda ya yi maganar su Alexander ya ce " Jimy , wa ya tafi wannan mission din ? na ji ka ce ta tafi ? you mean mace ce ? "

a hankali Jimy ya gyada mishi kai ya na fadin " Yeah , Mace ce , kuma ita ta fi dacewa da wannan mission din , yanayin fatarta zai janye zargi a saman ta , that's why she is the best person for THIS mission "

" ka na ganin Mace za ta iya yin nassara a kan Maza shidda , ba kuma yara ba , manyan Mafias , ma su kaifin basira , na san ko one hour ba za ta yi ba za su gano ta , yanzu haka su na da labarin zuwanta Nigeria kai ba ka sani ba "

murmushi mai dan sauti Jimy ya yi kafin ya ce " kar ka damu , ta san aikinta , kuma ba za su gano ta , ko kai idan na ce ka fada min wa ya tafi wannan mission din ba za ka iya fada min ba "

" yanzu kuma maganar jami'an tsaron Europe , mu sanyo su cikin maganar ko kuwa ? "

" Ohhhh , Eliot , wai me a ba ka gane ba cikin undercover ? "

" i'm sorry , kawai na ga tare da su mu ke investigation din "

" okay , da ga ka yi wa jami'an tsaron Dubaï da china su ma su shigo zancen ko ba haka ka ke so ba ? "

wata yar karamar dariya Eliot ya yi ya na fadin " Sorry , kai dai ba a iya yin maka magana , na ji shikenan mu bar zancen kawai "

" da dai ya fi maka , yau Friday ba za ka je Church ba , karfe goma ta yi fa " Jimy ya fada ya na fara takawa ya nufi kofar fita wajen

" ba za ka je ba kai ? " Eliot ya fada ya na bin bayan Jimy

girgiza mishi kai ya yi ba tare da ya tsaya ba ya ce " no , gaskiya ba zan iya zuwa Church ba , na daina zuwa baki daya , see you later " ya kai karshen dai'dai lokacin da ya fita ya yi hannun dama
Eliot kuma ya nufi hannun Hagu su ka yi hannun riga

( duk maganar nan da su ka yi da turanci su ka yi , kar ku manta kassar UK da turanci su ke magana , yawwa )




🥂 GIDAN MAZA 🥂



👻 ( THE MAFIA'S HOUSE ) 👻




____FUNNY , DRAMATIC , REVENGE , ROMANCE & DESTINY ____




🔥👑 MALLAKIN MEERAH 👑🔥






FOR INFORMATION +22798999753 WHATSAPP ONLY




TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP
https://chat.whatsapp.com/LWmuu0yv6C9DAhpdepDb4i


https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i






اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️




STEP ____ 3 ✍ ❤ 🔥





▪NIGERIA ( JOS STATE )

▪TUDUN WADA



wani kyawatencen parlour ne ya kyawatu da kayan more rayuwa na ji da gani , da ga gani mutanan gidan ba ma su kananan hali ba , ba zan bata lokaci wajen yi muku description ba yawwa kowa ya yi tunani da nashi brain

cen na hango wata kyakyawar mace zaune cikin dining room , ta na Sanye da wata Abaya white color me mugun kyau , ta yi Rowling veil din ta a kai , macen cikakiyar bahausa ce gaba da baya , launin skin din ta chocolate ne , da ga ganin yanayin jikin ta ka san mace ce mai mugun son gyaren jiki , akkila za ta kai shekara 50 , amma sam jikinta bai nuna hakan ba

ta na zaune ta na breakfast cikin konciyar hankali
ta na a haka wani kyawawen saurayi fari kal , ya shigo dining room din ya na sallama cen kassan makoshi cike da shagwaba

saurayin Fari ne kal , sam ba ya kama da matar nan , ya so ya yi kama da korean , ya na da dara daren idanun farare kal kamar madara kwayar cikin su kuma blue ce , ga dogon hanci sai dan karamin bakin shi , lips din shi pink color ma su mugun laushi , ya na da darck black smooth hair , ya zubo mishi har bayan keya duk a tirje ya zubo mishi har gaban goshi kadan ya rufe mishi idanu , a shekaru ba zai wuce 19 to 20 years ba , amma yanayin jikin shi bai nuna hakan ba , dan jikin shi a murde ya ke da ga gani ya na yawan motsa jiki

da ga shi sai short da singlet , dukka farare , sai yamutse fuska ya ke da allamun yanzu ya tashi da ga barci

matar nan na ganin shi ta saki wani cool murmushi ta ce " Good morning my Abee "
a hankali ya karaso wajen matar nan , ya kai bakin shi saitin kumatun ta ya manna mata kiss , cikin wata yar siririyar Muryar shi cike da shagwaba ya ce " Good morning Ma "

ya fada ya na janyo chair a geffen ta ya zauna , kawai ya kontar da kan shi saman table din ya lumshe idanunshi
murmushi mai dan sauti matar nan da ya kira da Ma ta yi ta kai hannu ta fara janye mishi gashin gaban goshin shi ta na fadin " Abeeram , yau ma ka cika dare ka na kallon film ko ? "

a hankali ya ware idanunshi murya cen kassan makoshi ya ce " Ma , wani assigment ne da a ka ba mu na kammala , shi ya sa na cika dare , dadin abun ma yau ba mu da class sai monday "

" da gaske ka ke ? " ta fada ta na janye hannunta
a hankali Abeeram ya gyada mata kai allamun Eh
ta na shirin magana wani mutum ya fito da ga cikin Kitchen , ya na sanye da wasu suit bakake da allamun Chef din su ne , amma bai yi kama da mutanan Nigeria ba , da ga gani cikaken korean ne gaba da baya shi ma

da murmushi a face din shi ya karaso cikin dining room din ya na kallon Abiram ya ce " Abee , na hada maka smoothie din ka ? "

" No , bari har a jima , yanzu ka kawo min fruits , Thanks "

gyada mishi kai Chef ya yi kafin ya koma cikin kitchen
ya na komawa matar nan ta cewa Abiram " where is your brothers ? "

wani dogon nunfashi ya ja kafin ya lumshe idanunshi ya ce mata " Captain tun karfe 7 ya fita tare da Talal , Ashur kuma ya na Gym , Ramadan & Abdul-Aleem har yanzu su na barci "

a hankali Ma ta gyada kai kafin ta mike tsaye , ta matso kussan Abeeram , ta manna mishi kiss saman kumatu ta na fadin " Okay , na tafi , sai na dawo "

" see you later " ya fada cikin sanyin murya , da ga haka matar nan ta sa kafa ta fice dining room ta bar parlourn

ta na fita ko chef ya fito da ga kitchen rike da tray cike da fruits ya karaso wajen dining table din ya ajiye tray din gaban Abiram ya na fadin " Abee , ka na bukatar wani abu "

" ba ka da maganin barci , barci na ke ji sosai wlh " ya fada a sanyaye

wani dan karamin murmushi chef ya yi ya na fadin " Sorry Abee , tashi ka koma ka yi barcin ka , ka ce yau ba ka da class "

a hankali ya dago kan shi ya na wani dan lumshe idanu , har ya bude baki zai yi magana wani dan saurayi ya shigo dining room din ya na sallama
kamanin shi daya tak da Abeeram kamar Twins , sai dai shi kananan idanu ne da shi amma kwayar cikin su blue ce irin ta Abiram
ya na sanye da wandon Tracksuit white color sai singlet ita ma white color , wannan murdaden jikin nashi duk a waje , har wata yar zufa ya ke yi da allamun da ga Gym ya ke

a hankali ya karaso wajen Abeeram ya manna mishi kiss saman kumatu ya na fadin :" Benjamin , har ka tashi ? yau ai ba ku da class "

wani dan karamin murmushi Abiram ya saki kafin ya ce mishi " Ashur , ni ma ban san yadda a ka yi na tashi ba , ga shi yanzu barci na ke ji "

a hankali ya kai hannu saman kan shi , ya tirje mishi gashi ya na fadin " All right , Chef ka shirya min breakfast yanzu ina zuwa " ya na gama fadar haka ya janye hannun shi ya fice dining room din

a hankali shi ma Abeeram ya mike tsaye
da sauri Chef ya ce mishi " ba za ka sha fruits din ka ba ? "
" no , ka shirya min smoothie kawai , ina parlour " ya fada ya na fara takawa ya fice dining room din
kai tsaye parlour ya dawo ,
parlourn irin wannan Sofar doguwar guda daya ce a kawata shi da ita , sai wasu one seaters guda biyu kusan juna dukkan su Sky blue color , da ga tsakiya kuma wata kyakyawar table ce ta glass fara kal

kai tsaye doguwar sofar nan ya nufa ya haye ya konta , ya daga kafa ya daura ta saman forehead din sofar , ya kai hannu ya janyo wani pillow da ke ajiye wajen chock din sofar , ya tada kai da shi ya lumshe idanunshi

ko five minutes bai yi ba da konci Chef ya shigo parlourn ya na rike da wani dan karamin tray , dauke ta wani glass a sama chake da smoothie pink color da allamun na strawberry ne , an saka wata straw a ciki
kai tsaye saman table din tsakiya ya ajiye tray kafin ya kalli Abiram ya ce " Abee , ga smoothie din nan "

ba tare da ya bude idanun shi ba ya ce mishi " okay , na gode chef "
gyada mishi kai kawai chef ya yi kafin ya bar wajen ya koma kitchen

ya na shiga ko Abeeram ya bude idanun shi , ya sauko da kafafun shi sannan ya mike zaune , a hankali ya kai hannu ya dauki glass din saman tray , sai ya ga har da wani dan karamin plate na cookies , wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya kai hannu ya dauki cookie guda ya kai a baki sannan ya kai bakin straw din cikin glass a bakin ya dan ja , har wani dan lumshe idanu ya ke da ga gani ya na jin dadin Abun

ya na zaune a haka wasu samari biyu su ka fara sauko stair a tare , guda na sanye da Jeans Black color da t-shirt Red color , gudan kuma ya na sanye da Trouser purple sai shirt white color mai dogayen hannu ya soke ta a cikin trouser din shi kuma gashin kan shi brown sabanin dayan black curly ne , amma dukkan su gashin ya dan taru ya zubo musu har bayan keya

mai Black curly hair din ba zai wuce 25 years ba , dayan kuma 27

kamanin su daya tak tak kamar an tsaga kara , ga shi kuma su na kama sosai da Abeeram kallo guda za ka yi musu ka san brothers ne , har blue eyes din su duk iri daya ne , da yanayin jikin su , da allamun fa su na gym dan su na da murdaden jiki gaskiya

a haka har su ka sauko stair su ka nufi Abiram , a jere su ka manna mishi kiss saman kumatu sannan mai black curly hair ya ce " Benjamin , har ka tashi ? yau ba ku da class ai , ko dai Ashur ne ya je ya tashe ka ? "

a hankali Abiram ya girgiza mishi kai ya na fadin " no , kawai dai na tashi ne , za ka sha smoothie ? " ya kai karshen ya na mika mishi Glass din hannun shi

a tare su ka girgiza mishi kai sannan dayan ya ce " Ramadan mu tafi , Abee sai mun dawo , ka kula da kanka ka ji ko ? " kenan wannan shi ne Abdoul-Aleem to

" sai kun dawo , but ku biyo min da ice

Please Login or Register in order to submit comment