Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya matso kusa magen nan , ya kai bakinsa saitin kunnenta ya na fadin " Snow , wake up mu tafi gida "

wani dan karamin kuka ta yi kafin ta mike tsaye ta na mika sannan ta diro da ga saman table din
mikewa tsaye shi ma ya yi ya dauki wayoyinsa har wajen uku , kuma dukka tsadadu , ya nufi hanyar fita office din ya fice



▪NIGERIA ( JOS STATE )

▪TUDUN WADA



a zaune duk samarin gidan su ke a parlour kowane ya na sanye da kananan kaya sai Abeeram da ke sanye da Short da singlet kadai
Ramadan da Abdoul su na rike da wayoyinsu su na latsawa
Captain kuma da laptop saman laps din sa ya na latsawa
Abeeram da Ashur kuma su na game da Tv
cen na hango wani saurayin da ban gani ba dazu da safe ya na zaune gefen Captain da Laptop shi ma saman laps din sa ya na latsawa da alamun shi ne Talal dan ya na kama tak da sauran samarin gidan sai dai zai kai 30 years shi
su na zaune a haka Ma ta shigo parlourn ta sallama

a tare duk su ka amsa mata sallamarta su na fadin " Welcome Ma "

murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta ce " Thanks my Beautiful Babys , please ku ajiye wayoyinku ina da surprise "

ba musu ko wane ya ajiye abun da ya ke su ka juyo su na kallon ta
Abeeram kuwa har da mikewa tsaye ya na fadin " Wace irin Surprise Ma ? "

wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta juya ta kalli kofar ta na fadin " My Baby ? come in " ta fada ta na mika hannunta alamun wani ta ke jiran ya shigo

wani dan karamin yaro ne ya shigo parlourn , ya na sanye da wani Jeans Brown da T-shirt white color , a shekaru ba zai wuce 4 years ba , ya na da kananan idanu Green color , ya na kama tak tak da su Abeeram har gashin kansa shi ma ya zubo mishi zuwa bayan keya
kai tsaye hannun Ma ya riko ya na boye wa a bayanta

da sauri Ashur ya mike , a tare shi da Abeeram su ka nufi yaron nan su na murmushi
Ashur ya sa hannu ya dauke shi ya na fadin " my Baby , Sai yau ka tuno da mu ? na yi kewar ka sosai ka sani ko ? "

da harshen English yaron nan ya amsa mishi da cewa " I have missed you too my uncle "
wata yar karamar dariya Ashur ya yi kafin ya manna mishi kiss a kumatu

da sauri Abeeram ya sa hannu ya kwace shi da ga hannun Ashur ya na fadin " My Baby , mu tafi mu yi game , na ajiye maka chocolate da Sweet dayawa "
ya fada ya na komawa in da ya taso ya zauna , ya zaunar da yaron tsakanin cinyoyinsa , shi ma Ashur dawowa ya yi gefensa ya zauna su ka fara Game

wata yar karamar dariya Ma ta yi kafin ta karaso cikin parlourn ta zauna
sai da ta zauna sannan Captain ya ce mata " Ma , me ya ke yi a nan kuma ? "

" kamar ya me ya ke yi a nan ? Danish fa yaronku ne "

" na sani Ma , amma kin san halin Big bro , ba ya son yaron nan har cikin zuciyarsa " Fadin Captain

" To yanzu dole ya so shi saboda ya dawo wajen mahaifinsa baki daya , dama a yarjejeniyar da mu ka yi zai zauna wajen su ne har lokacin da ya wuce shan nono , tun last year na so na je na kamo shi but su ka koma Kanuda da zama , yau kuma na je na karbo shi kuma sun amince ya zauna wajen mahaifinsa , dan haka da ga yau Danish ya dawo nan da zama " ta kai karshen ta na mikewa tsaye

ta kalli su Abeeram ta ce " Danish , mu tafi ka yi wanka ko ? "

da sauri Danish ya juya ya rungume Abeeram tsam ya na girgiza kai alamun ba ya zuwa

a hankali Abeeram ya juya ya kalle ta ya ce " Ma , bar shi kawai , in mu ka kammala na yi mishi wanka "

" okay , kayansa na cikin motana idan kun tashi , zan shiga na konta , kuma please , please kar ku ji mishi ciwo na san halinku da mugayan wassa "

" don't worry Ma , za mu ku kula da shi " Fadin Ashur
da okay kawai ta amsa musu sannan ta nufi stair ta Haye

ta na barin wajen Talal ya dago kai ya kalli Captain ya ce " Fayd , na lura kai ma ba ka son yaron nan "
( 🤔🤔 okay , kenan Fayd shi ne sunan Captain )

wani dan karamin tsaki Captain ya ja kafin ya mike tsaye ya dauki laptop din sa ya nufi stair ya Haye
maimakon ya shiga bedroom din sa sai na ga ya wuce part din Ma
da sallama a bakinsa ya shigo parlourn ta , cikin sa'a ko ya tardo ta nan zaune ta na rike da wayarta a kunne da alamun kira ne ta ke

ta na ganin sa ta saki wani dan karamin tsaki ta sauko wayar ta na fadin " ni da Fahd ne , ya ce next week zai dawo , ku shirya mishi bedroom din sa , sannan ka fadawa Ramadan ya ce zai koma office din sa , ya sa a gyara shi kafin ya dawo "

zama ya yi saman sofa ya na kallon ta ya ce " Ma , ina ga ba shawara ce mai kyau ba dawo da Danish gidan nan , kin fi kowa sanin Yadda Big bro ba ya son yaron nan duk da shi ya haife shi , kuma kin ga gidan babu mace bare ta kula da shi , ya ki ke tunanin Big bro zai ji in ya ga Danish a gidan nan ? "

( 🤔🤔 in na gane Danish yaron Fahd ne ? kuma ba ya son shi ? to mi ya sa ya tsani yaron da ya haifa da cikinsa ? )

zama ta yi gefensa ta riko hannunsa ta ce " Fayd , Danish fa yaron Fahd ne , duk yadda zai nuna ba ya son shi karya ya ke , ya na son shi har cikin zuciyarsa saboda shi kadai ne abun da ya yi mishi saura na Beenish , dole ya so shi ko dan ya dinga rage kewar ta , duk duniyar nan Danish ba ya da wani gata da ya wuce mahaifinsa , na dawo da shi ne nan dan Fahd ya samu damar zama da yaronsa , har ya saba da shi "

" yanzu Ma in ya yanke shawarar kai shi gidan marayu fa ? "

" kai za ka yarda ya kai yaronsa tilo gidan marayu ? " ta fada ta na tsare shi da ido

wata yar karamar dariya ya yi kafin ya mike tsaye ya na fadin " sai na je na yi adopting din shi " ya kai karshen ya na nufar hanyar fita

tashi ita ma ta yi ta shiga bedroom din ta dan ta yi wanka

bangaran Captain kuma nashi part din shi shi ma ya shiga ya ci gaba da aikinsa
bari mu leko wani bangaran na labarin kuma


☆ GIDAN BARISTER AABID ☆


Barister Aabid , babban mutum ne cikin jahar Jos , ba karamin mai kudi ba ne ya tara dukiya ta a zo a gani , mutum ne mai saukin sha-ani kuma mai kirki
duk wannan uban kudin da ya tara duk ta hanyar halal ya tara su , duk case din a ka kawo mishi a na son ya yi defended a gaban kotu sai ya fara bincike a kan wanda su ka kawo mishi case din , in har mutanan kwarai ne sannan ya yarda , in kuma na banza ne ya watsar da case din duk irin kudin da za a ba shi , shi ya sa ma samun shi a matsayin lawyer sai wane da wane , amma dai yanzu ya yi retreat
ya na da matansa biyu , bai yi shekara biyar da farkon ba ya auro ta biyun , ta farko wanda ba su taba samun haihuwa da ita ba tun lokacin da ya fara aiki , ya na kiranta da Hajiyah dan ya kai sau goma ya na tura ta Makkah saboda hakurinta da sanyinta , duk dabi-unsa ta dauko su saboda zaman da su ka yi
asali ma ita ce silar aurensa na biyu , tun da ba ta iya haihuwa ta zabar mishi mata da kanta wadda zai aura ta haifa mishi zuri'ar da ita ta kassa ba shi
bai musanta mata ba ya amince , da ga haka ya mallaka mata duk rabin dukiyarsa nata ita kadai , duk bayan shekaru biyu sai ya biya mata Makkah ta je ta yi ibada , ita dai wannan matar hankalinta konce ya ke da mijinta ta na shan duniyarta dan ko shi Barister Aabid sai abun da Hajiyah ta ce mishi ya ke
sai kuma matarsa ta biyu , mai sunan Ramatou amma ya na kiran ta da Amarya , wadda su ke da yara hudu yanzu tare da ita , na farko mai sunan Nasser wanda zai kai 30 years haka kuma shi kadai ne namiji cikin yaransa , sai ta biyu Karima , da ke karatu a China , sai Rehan sai autarsu Afiya da ba za ta wuce 15 years ba , su na rayuwarsu cikin konciyar hankali da zaman lafiya

" Rehan ! please zo ki dauka min wayata " fadin wata Mata zaune cikin wani kyawatacen parlourn da ya sha fournitures na a zo a gani da ga gani ba kananan kudade a ka kashe a wajen nan ba , ga shi ko duk white color ne mai daukar ido , wajen na goge a share sai tashin qamshi ya ke da ga gani matar nan mai tsabta ce

ta na zaune a haka na ga Rehan ta fara sauko stair din gidan ta , ta na sanye da wani Jeans brown da wata Shirt mai dogayen hannu blue , sai wata yar karamar hula a kanta , ta na sanye da medical glass
ta na rike da wasu wayoyi guda biyu ta karaso cikin parlourn ta nufi matar nan ta mika mata guda ta na fadin " please momy , ki dinga tahowa da wayarki , na gaji kullum sai kin bari ina aiki za ki ce na dauko miki waya "

hannu ta kai ta karba ta na tsaki
Rehan kuma ya vi gaba da takawarta za ta fita
da sauri ta taro ta da cewa " ke Madam , ina kuma za ki je ? ba ki ga dare ya yi ba ? " ta fada cikin tsare gida

ba tare da ta tsaya ba ta ce " Na sani momy , zan je garden ne , akwai call din da na ke son yi " ta fada ta na ficewar ta

ko da ta fito harabar gidan kawai na ga ta nufi dayan part dan part biyu cikin gidan su na kallon Juna , da alamun dayan shi ne na Hajiyah

da sallama a bakinta ta shigo parlourn kanta na sunkuye ta na latsa wayarta
kamar dai part din da ta baro haka nan shi ma ya ke har fournitures din , shi ma a share a goge qamshi na tashi har da ac

cen na hango Hajiyah zaune saman doguwar sofa ta na kallon Tv , ta na sanye da wata gown pink colour irin ta barci haka , da wata yar karamar hula a kanta irin ta Rehan , yanayin jikinta sai ka rantse yar shekara 30 ce dan sam ba ta da jiki bare ma da ya ke ba ta taba haihuwa ba, ga skin din ta chocolate mai kyau da ga gani ta na kashe kudi wajen kula da kanta

slowly ta juya ta kalli saitin kofar shigowa ta na amsawa Rehan sallamarta
da murmushi a face din ta ta ce " Titi ? me ki ke yi a nan a wannan lokacin ? "

ba tare da ta dago kai ba Rehan ta karaso gefenta ta konta ta daura kai saman laps din ta , ta na latsa wayarta ta ce " Momy , ni nan zan kwana yau "

hannu Hajiyah ta kai saman kanta ta na fadin " nan kuma ? haba Titi , kar ki janyo wa kanki fada , kin san halin momynki ba ta son ku na kwana a wajena , yanzu ma in ta ji nan ki ka taho sai ranta ya baci "

" momy , na ga ai duk gida guda ne , wai me ya sa momy ba ta son mu na zuwa wajen ki ne ? "

murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta ce " sani sai Allah , sai kuma momynku , me zai hana in ki ka....."

da sauri Rehan ta katse ta da cewa " shiii , momy , yi shiru a na kira na "

ba musu Hajiyah ta ja bakinta ta yi shiru ta meda kallonta kan Tv
Rehan kuma ta kai wayar a kunne ta na sakin murmushi ta na sallama kassa kassa

a daya bangaran , Muryar Ashur na jiyo ya amsa mata sallamarta , sannan ya ce " Ashe ki na kusan wayar ma "

murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta ce " tun safe na ke jiran kiranka ba dole na tsaya kusa da wayar ba , ina fatan ka na lafiya ? "

" i'm fine , what about you ? fatan ki na lafiya ? "

" Alhamdoulilah " ta fada a takaice ta na sakin murmushi ita kadai
" okay , ya maganar lectures din da zan fara yi miki ? kin fidda lokacin da za mu yi ? "

" Yeah , me zai hana ka zo gidan mu ? bayan sallar isha , sai mu shiga garden na san Daddy zai amince "

" gidanku kuma ? No ! gaskiya ba zan iya zuwa gidanku ba , zan janyo miki matsala idan Daddynku ya gan ni , zan yi mana magana da secretaryn Headmaster in za ta yarda ta ba mu class mu dinga yi a ciki school zai fi a gani na "

marairaice fuska ta yi kamar ta na gabansa ta ce " please Ashu , Wlh Daddy ba zai yi fada ba tun da karatu ne za ka koya min , kuma na yi wa momy maganar ta ce in ya amince gobe sai ka zo na gabatar mishi da kai , please "

shiru ya yi bai ce mata komai ba duk ta bi ta kashe mishi jiki specially ma yanayin da ta kira shi da Ashu , nan take ya ji ta gama tafiya da zuciyarsa

ta na a haka kawai ta jiyo Muryarsa ya na magana kamar shi da wani , da alamun fada ne ma ya ke
kawai ta tsaya ta na sauraron su , ta na dariya da alamun da kanansa ne ya ke fadan

a haka ta jiyo Muryar Abeeram ya na fadin " Hello ! akwai wani a kusa ? "

murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta ce " Hello , da wa na ke magana ? "

cikin shagwaba Abeeram ya ce mata " I'm Benji , little brother din boyfriend din ki , in ki na son Ashu ya dinga yi miki lectures sai kin biya , in ba haka babu in da zai je "

" uhmmm , nawa zan biya to ? "

" Ten chocolate ko wane week , in kuma ba ki yarda ba yanzu na katse kiran , yawwa "

wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " shikenan , gobe in ya zo zan ba shi chocolate din ya kai maka , okay ? "

" Yeahhh my Aunty , i love you so much "
dariya kawai ta yi jin abun da ya ce , ta so a ce Ashur ne ya furta mata wannan kalmar da yau sai ta kwana ta na sallat ta na yi wa Allah godiya , amma ba komai tun da har ta saye zuciyar kanansa , haka shi ma ya saye zuciyarta dan ya shiga ranta gaskiya , da ga gani ba ruwansa

ta yi nisa duniyar tunaninta ta jiyo Muryar Ashur ya na fadin " Sorry , ki turo min Adress din gidanku ta Text , gobe ina zuwa , Good night "

ya na gama fadar haka bai jira amsarta ba ya katse kiran
a hankali ta sauko wayar ta na murmushi kamar an yi mata albishir da gidan Aljannah
ta na a haka ta jiyo Muryar Hajiyah ta na fadin " da wa ki ke waya ? na ga sai murmushi ki ke kamar an yi miki albishir da gidan Aljannah "

cikin ko in kula ta ce " da sirikinku na ke magana "

dan zaro idanu Hajiyah ta yi ta na kallonta ta ce " what ? Siriki fa ki ka ce ? ni na ce na ba shi auren ki ? "

" momyyyy , yanzu kenan za ki iya hana min abun da na ke so ? wlh ina son shi har cikin zuciyata "

" ya ya ke ? ya na da kyawawan halaye ? he is muslim ? "

" yeah , musulmi ne but ba na tunanin dan africa ne , dan ya na kama mutanan Korea sosai momy , ya na da kirki kuma ba ruwansa , ko a school ba kowa ya ke yi wa magana , kar ki so ki ga yadda mata ke biyan shi da sunan so , amma bai taba kula su ba , asali ma duk wadda ta zo mishi da zancen soyayya wulakanta ta ya ke yi gaban sauran dalibai kuma sam bai nuna ya damu "

" hmmmm , ki na ganin ke ma ba zai iya yi miki hakan ba watarana ? namiji fa abun yarda ba ne , cikin sauki zai bad'a kama ya sauya kamar ba ki taba sanin shi ba "

ta na gama rufe bakinta kawai ta jiyo Muryar wani dattijo tsaye bakin kofar parlourn ya na fadin " oho , kenan haka ki ke tunani dangane da ni ? "

a tare su ka zaro idanu ita da Rehan , da sauri ta mike zaune su ka juya su na kallon kofar
ya na tsaye sanye da wata farar jallabiya alamun da ga massalaci ya ke , ba kowa ba ne sai Barister Aabid
🥂 𝑮𝑰𝑫𝑨𝑵 𝑴𝑨𝒁𝑨🥂



💙💦 ( ᴛʜᴇ ᴍᴀғɪᴀ' s ʜᴏᴜsᴇ ) 💦💙




___FUNNY , DRAMATIC , REVENGE , ROMANCE & DESTINY ___



🔥👑 𝐌𝐀𝐋𝐋𝐀𝐊𝐈𝐍 ᴍᴇᴇʀᴀʜ 👑🔥


The writer of
Taurin zuciya
Exiled Prince ( love meets power )
Two lights ( Yar jarida )
Taurin Zuciya ( Return )
Fairat
Soyayyar gaskiya ( TRUE LOVE )
and now 𝐆𝐈𝐃𝐀𝐍 𝐌𝐀𝐙𝐀 ( 𝐓𝐇𝐄 𝐌𝐀𝐅𝐈𝐀'𝐒𝐇𝐎𝐔𝐒𝐄 )


FOR INFORMATION +22798999753 WHATSAPP ONLY




اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️




🅂🅃🄴🄿 ____ 6 ✍ ❤ 🔥




cikin nitsuwa ya karaso cikin parlourn ya zauna saman sofar da ke gefen ta su Rehan
cike da kula Hajiyah ta ce mishi " sannu da dawowa Dear "

wani kallon ya wurga mata ya na yamutse fuska ya ce " ba wani Dear , ai na ji abun da ki ka ce mata , wato haka ki tunani har a kaina ko ? "

da sauri ta girgiza mishi kai ta na marairaice mishi fuska ta ce " haba Dear ta ya ce za ke haka ? ni fa kawai na fada mata hakan ne dan ta kiyaye "

bushewa da dariya ya yi har da tapi ya na kallon ta ya ce " gaskiya kin cika matsoraciya , Rehan maganar me ku ke yi haka ne ? " ya fada ya na dawo da kallonsa kan Rehan

wasu yawu ta hadiye kafin ta kai hannu ta fara shafa kontacen sajenta ta na fadin " Ummm , dama Daddy , akwai wani dan Universityn mu da na roke shi ya yi min lectures kan abubuwan da ban gane ba a class , kuma ya amince , shi ne na ce mishi ya dinga zuwa nan gida ya na min in kun amince "

mikewa tsaye ya yi ya na fadin " shikenan , gobe in ya zo ki fara kawo shi na gan shi sannan "

" okay Daddy " ta fada ta na murmushi

kallon Hajiyah ya yi ya na fadin " ke kuma , zan kama ki gobe jira ki gani " ya kai karshen ya na fara takawa zai fita

da sauri Rehan ta ce mishi " Sai da safe Daddy , ku ce wa momy ni a nan zan kwana "

bai ce mata komai ba ya sa kafa ya ficewar shi
ya na fita Rehan ta mike tsaye ta na tsale kamar wata karamar yarinya ta na dariya
ita dai Hajiyah ta yi zaune ta zuba mata ido ta na murmushi , duk cikin yaran mijinta Rehan kadai ce ke iya bude baki ta kira ta da momy ko bayan idon Barister ne , sauran a bayan idonsa duk Aunty su ke ce mata , sai in sun gan shi su ke ce mata momy , kuma da wuya ta yi kwana guda ba ta zo wajen ta ba sun yi hira , ta dauke ta tamkar wata friend's din ta komai fada mata ta ke yi , ko lokacin da ta fara period maimakon ta je ta fadawa momynta , Hajiyah ta nufo ta fada mata , hakan ko ba karamin dadi ya ke yi mata ba ko ba komai ta samu d'iya ita ma

bangaran Barister bayan ya baro part din Hajiyah , kai tsaye part din Amarya ya nufa ya shigo parlourn ya na sallama
nan ya tardo ta zaune tare da Nasser , ya na Sanye da jallabiya shi ma , da alamun tare su ka fito mosque shi da Barister

a tare shi da Amarya su ka amsa mishi sallamar sannan ta yi mishi sannu da zuwa
sai da ya karaso gefenta ya zauna sannan ya amsa mata

ya na zama ta kalli Nasser ta ce mishi " please je ka kirawo Rehan ta na garden "

har ya mike Tsaye Barister ya taro shi da cewa " no ba ta garden , ta na part din Hajiyah , ta ce a cen za ta kwana , ka yi wa auta magana ta tarda ta su kwana a cen "

gyada mishi kai kawai Nasser ya yi kafin ya mike ya nufi stair ya haye
ita dai Amarya tun lokacin da ya ce ta na part din Hajiyah yanayin face din ta ya sauya alamun ba ta ji dadin hakan ba

" Lafiya na ga kin yi sanyi ? " fadin Barister ya na kallon ta dan sarai ya lura da sauyawar yanayin face din ta

" ba komai " ta fada a takaice ta na kallon Tv

" ni fa ba makaho ba ne , ki fada min me ya ke faruwa ? ko ba ki ji dadi dan na ce Rehan da auta su kwana wajen Hajiyah ? na ga dai ita ma yaranta ne , laifi ne in sun kwana a wajen ta ? na

Please Login or Register in order to submit comment