Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

damu da abun da za su yi tunani karya "

dago kai ta yi , ta ce mishi " in da gaske ka damu da abun da zan yi tunani me ya sa jiya ba ka zo ba ? na yi kokarin kiran ka , tun safe , har na hakura na daina , ka san irin damuwar da ka saka ni a ciki ? " ta fada idanunta na cikowa da ruwa , ta kauda kai gefe

wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya ce " I'm so sorry , jiya na tafi Headquater ban samu damar fitowa ba sai bayan karfe 10 na dare , na so na fada miki amma ban samu dama ba , Jiya mu na game ne da Autan mu da yaron yayan mu , shi ne su ka karbi wayata , cikin rashin sa'a yaron Big bro din mu ya shiga wani waje ya bata duk programe din wayar , har ta mutu , shi ya sa da ki ka kira ni ba ya yi , Ki yi hakuri please kar ki yi min kuka , ban iya rarrashi ba wlh "

wata yar karamar dariya ta yi ta kai hannu ta fara goge ruwan da ke cikin idanunta
sannan ta juyo ta na kallon shi , cikin yar shagwaba ta ce " na ji shikenan , amma da sai ka karbi ko da wayar daya da ga cikin su ne ka kira ka fada min , ba ka san yadda hankalina ya tashi ba "

" yanzu ba dai kin yi hakuri ba ? shikenan mu bar maganar kawai mu fara aikin da ya kawo mu "

noke mishi kafada ta yi ta na fadin " No , ni ban yi hakuri ba "

" Na tambaye ki ? kin kawo ni nan dan na koya miki ko dan mu yi hira ? " ya fada ya na daga mata gera guda

daga idanunta sama ta yi na dan lokaci kafin ta sauko su ta ce mishi " dukka biyu , wane ka zaba ? "

hannu ya kai ya janyo Bag d'inta ya na fadin " karatu za mu yi , ki fada matter din da ba ki ganewa , sai na yi miki bayani "

" ummm , ni dai na fi samu matsala a physical "

" Ni kuma kin ga abun da ke burge ni , Physical ta fi english sauki , just in kin san formula , law da condition , saboda kullum su ne a ke aiki da su , ba su sauyawa , just hanyar da za ki bi ne wajen samo su ke sauyawa , na fada miki ? Physical ta fi mathematics sauki , saboda ita physical duk irin problem din da za a ba ki , ko da kuwa formula din da ki ka daura ba dai'dai ba ce za ki samu solution , ko da kuwa wrong solution ne , amma kin ga ita mathematic , babu formula guda wadda za ki iya aiki da ita , da brain din ki za ki yi anfani , in har ba ki fara dai'dai ba to ba za ki taba samun solution ba , makalewa za ki yi ki kassa gaba ki kassa baya , shi ya ce a ke ce wa mathematics exact science ne "

wani dan karamin kuka ta yi ta na fadin " ka gani ko ? shi ya sa na ce ba na gane komai , dadin abun ma da ba mu yin mathematic "

wata yar karamar dariya ya yi kafin ya ce " wa ya fada miki ? kun fara a second semester "
marairaice mishi fuska ta yi kamar za ta yi kuka
dariya ya yi kafin ya ce " kin san wani abu ? "
girgiza mishi kai ta yi alamun a-a

sai da ya dan jinkirta sannan ya ce mata " akwai wani Prof din mu da ya taba ce mana , duk lokacin da ku ka samu kanku gaban wani problem , in har kun san solution din to kai tsaye ta ke taho muku a kai , amma da kun fara sa karfi , ku matsawa Brain d'inku dole sai kun samo solution din to ba za ku taba samo ta ba , ko kun samo ba dai'dai ba ne "

ajiyar zuciya ta sauke ta na sakin murmushi ta na kallon shi sai zuba ya ke kamar an kunna Radio
ita ba ta san ya na ta kwatanta mata yadda za ta gane abubuwa cikin sauki amma sam hankalinta ba ya tare da ita sai kallon shi ta ke ta na hadiyar yawu

sai da su ka share one hour da 30 minutes sannan ya ce mata zai koma gida
a tare su ka baro garden din , amma sai da ta kai shi wajen Hajiyah su ka gaisa ya yi mata sallama sannan su ka fito
ta raka shi har wajen motarsa sannan su ka yi sallama , ya shiga motarsa ya bar gidan

ta na tsaya waje guda har sai da gateman ya rufe kofar gidan sannan ta juya ta nufi part din Amarya ta shiga da sallama a bakinta

Barister ne kadai ta tardo da amaryarsa zaune a parlourn
har ta nufi stair Barister ya taro ta da cewa " Har kun kammala ? "
da murmushi a face din ta ta amsa mishi da cewa " Eh Daddy , har ya tafi "
" Ya tafi ? ya bai shigo mu ka yi sallama ba ? "

" ya ce wai Captain ba ya son su na tsayawa waje har karfe 10 ba su dawo ba , shi ya sa ya tafi dan kar hankalinsa ya tashi "

da okay kawai ya amsa mata , da ga haka ta Haye stair ta koma bedroom din ta

Bangaran Ashur kuma , sai da ya fara biya wa ya sayo Ice cream kamar yadda ya yi wa Abiram alkawari sannan ya koma gida , har karfe 10 ta kusa ba dan mintina

da Sallama a bakinsa ya shigo parlourn gidan ya na rike da ledar ice cream
kamar yadda ya bar su haka ya dawo ya tardo su , sai dai yanzu Danish ya koma saman cinyar Captain

da murmushi a face din sa ya karaso cikin parlourn ya na fadin " wa ke son ice cream ? "
da sauri Abeeram ya mike ya nufe shi ya kwace dayar ledar hannunsa ya dawo saman sofar da ya tashi ya zauna

cikin shagwaba Danish ya ce " Uncle , ina nawa ? "
karasowa Ashur ya yi ya ajiye dayar ledar saman table ya fiddo bowl shidda na ice cream ya ajiye ya na fadin " Duk wanda ba ya so ya bari , na san Benji zai ji dadin kammala su baki daya "

daya bayan daya kowane ya tasso ya dauki bowl guda har da Danish , guda ya yi saura ,
da kansa Ashur ya dauke shi ya bawa Sana
ba musu ta kai hannu ta karba ta na yi mishi godiya

komawa ya yi ya zauna gefen Abiram ya na fadin " Benji , ni ba za ka bani ba ? "
ba musu Abeeram ya fiddo dayan bowl ya mikawa Ashur , ya san Ma ba ta shan Ice cream shi ya sa ma Ashur bai saka da ita ba
godiya Ashur ya yi mishi , sannan ya fara shan ice cream din kamar sauran yan uwansa

kowa ya yi nisa duniyar tunaninsa su ka jiyo Muryar Sana ta na fadin " Strawberry , shi na ke so "

a tare duk su ka dago kai su ka kalle ta
cike da kula Ma ta ce mata " Strawberry kuma ? "
gyada mata kai Sana ta yi , ita kanta ba ta san ta fada , kawai ta ji a jikinta kamar ta na yawan shan ice cream mai taste din Strawberry
cikin sanyin murya ta ce " just na ji a jikina kamar ina yawan shan Ice cream mai taste d'in Strawberry "

wani dan karamin murmushi Ma ta saki alamun Sana ta na tuno wasu abubuwa na rayuwarta

kowa ya yi zugum ya na kallon Sana , su ka jiyo Muryar Abdoul ya na fadin " Ashur , ba ka fada mana ina ka tafi ba ? "

wani dan karamin tsaki Ashur ya ja kafin ya ce " Wai kai ina ruwanka da in da na tafi ? ba ga ni na dawo ba ? "

har zai yi magana su ka jiyo wayar Captain ta na ringing
hannu ya kai cikin aljihunsa ya fiddo wayar , wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya ce " Big bro ne , ku tsaya na mayar da shi Video call , Benji kunna Tv "

da sauri Abeeram ya tashi ya dauki remote ya kunna Tv sannan ya koma ya zauna
cikin nitsuwa Captain ya fara latsawa wayarsa
ya yi wajen one minute ya na latsa wayar kafin su ka Fahd ta cikin Tv din

ya na zaune saman dining table ya na shan juice ya na kallon wayarsa
Danish na ganin shi ya sauko da ga jikin Captain ya nufi Tv din da gudu ya na fadin " Daddy , Daddy "

wani dan karamin tsaki Fahd ya ja ya na dan kauda kai kafin ya juyo ya kalli Fayd da ya ke tsawon Danish bai ida kai Tv din ba , ya ce mishi " Me wannan yaron ya ke a nan ? "

Ma ce ta amsa mishi da cewa " Ni na kawo shi ko ka na da ja ? "
ko sannu bai ce mata ba ya kai glass din hannunsa a baki ya sha sannan ya ce " Captain akwai maganar da ke son yi da kai , amma bari idan na zo sai mu yi "

cikin shagwaba Abeeram ya ce mishi " Big bro , wai yaushe za ka zo ? ni fa ina kewar ka sosai "

" Ni ma ina kewar ka sosai Benji , just aiki ne ya yi min yawa , kun ki yarda ku zo taimaka min mu ci gaba da kula da companyn Daddy ba dole na tsaya ba , da a ce kun yarda kun shigo da na samu ina hutawa , ku duba don Allah har tsufa "

a tare su ka yi dariya sannan Ramadan ya ce " gaskiya Big bro ba wanda ya shirya wannan d'awainiyar , a dai ci gaba da hakuri "

" haba zan yi maganin ku , ku dai jira na dawo " fadin Fahd

da sauri Danish ya ce " Daddy , amma za ka taho min da tsarabar chocolate ko ? "

tsaki Fahd ya yi kafin ya ce " please ku janye min wannan abun da ga gabana "

a fusace Ma ta ce " Fahd ! yaron naka ne ka ke ce wa Abu ? Danish fa d'an cikinka ne , kai ka haife shi , ta ya za ka mayar da shi bare ? a tunanina mun riga da mun wuce wannan Step din , in ba ka nuna mishi kula ba wa zai nuna mishi ? Fayd ko Abdoul-Aleem ? ko kuwa Talal ?, duk irin soyayyar da za su nunawa Danish ba ta kai taka ba , ka tausaya mishi mana , yaro ne fa , wannan kiyayar da ka ke nuna mishi ba ka san irin tasirin da za ta yi ba a kansa idan ya girma "

shiru Fahd ya yi bai ce komai ba ya na sauraron abun da ta ke fada , shi kuwa Danish bawan Allah sai kuka ya ke , kamar zai hadiye zuciya

MY BOOK IS ONLY N300
VIA
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank

Dm +22798999753 for evidence


๐Ÿฅ‚ ๐‘ฎ๐‘ฐ๐‘ซ๐‘จ๐‘ต ๐‘ด๐‘จ๐’๐‘จ๐Ÿฅ‚



๐Ÿ’™๐Ÿ’ฆ ( แด›สœแด‡ แดแด€า“ษชแด€' s สœแดแดœsแด‡ ) ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’™




___FUNNY , DRAMATIC , REVENGE , ROMANCE & DESTINY ___



๐Ÿ”ฅ๐Ÿ‘‘ ๐Œ๐€๐‹๐‹๐€๐Š๐ˆ๐ แดแด‡แด‡ส€แด€สœ ๐Ÿ‘‘๐Ÿ”ฅ


The writer of
๏ผด๏ฝ๏ฝ•๏ฝ’๏ฝ‰๏ฝŽ ๏ฝš๏ฝ•๏ฝƒ๏ฝ‰๏ฝ™๏ฝ
๏ผฅ๏ฝ˜๏ฝ‰๏ฝŒ๏ฝ…๏ฝ„ ๏ผฐ๏ฝ’๏ฝ‰๏ฝŽ๏ฝƒ๏ฝ… ( ๏ฝŒ๏ฝ๏ฝ–๏ฝ… ๏ฝ๏ฝ…๏ฝ…๏ฝ”๏ฝ“ ๏ฝ๏ฝ๏ฝ—๏ฝ…๏ฝ’ )
๏ผด๏ฝ—๏ฝ ๏ฝŒ๏ฝ‰๏ฝ‡๏ฝˆ๏ฝ”๏ฝ“ ( ๏ผน๏ฝ๏ฝ’ ๏ฝŠ๏ฝ๏ฝ’๏ฝ‰๏ฝ„๏ฝ )
๏ผด๏ฝ๏ฝ•๏ฝ’๏ฝ‰๏ฝŽ ๏ผบ๏ฝ•๏ฝƒ๏ฝ‰๏ฝ™๏ฝ ( ๏ผฒ๏ฝ…๏ฝ”๏ฝ•๏ฝ’๏ฝŽ )
๏ผฆ๏ฝ๏ฝ‰๏ฝ’๏ฝ๏ฝ”
๏ผณ๏ฝ๏ฝ™๏ฝ๏ฝ™๏ฝ™๏ฝ๏ฝ’ ๏ฝ‡๏ฝ๏ฝ“๏ฝ‹๏ฝ‰๏ฝ™๏ฝ ( ๏ผด๏ผฒ๏ผต๏ผฅ ๏ผฌ๏ผฏ๏ผถ๏ผฅ )
๏ฝ๏ฝŽ๏ฝ„ ๏ฝŽ๏ฝ๏ฝ— ๐†๐ˆ๐ƒ๐€๐ ๐Œ๐€๐™๐€ ( ๐“๐‡๐„ ๐Œ๐€๐…๐ˆ๐€'๐’๐‡๐Ž๐”๐’๐„ )


FOR INFORMATION +22798999753 WHATSAPP ONLY




ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ูู…ู‘ูŽ ุตูŽู„ู‘ู ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏู ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุตูŽู„ู‘ูŽูŠู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ู‘ูŽูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒุŒ ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ูู…ู‘ูŽ ุจูŽุงุฑููƒู’ ุนูŽู„ูŽู‰ ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏู ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ู…ูุญูŽู…ู‘ูŽุฏูุŒ ูƒูŽู…ูŽุง ุจูŽุงุฑูŽูƒู’ุชูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽ ูˆูŽุนูŽู„ูŽู‰ ุขู„ู ุฅูุจู’ุฑูŽุงู‡ููŠู…ูŽุŒ ุฅูู†ู‘ูŽูƒูŽ ุญูŽู…ููŠุฏูŒ ู…ูŽุฌููŠุฏูŒโค๏ธ




๐Ÿ…‚๐Ÿ…ƒ๐Ÿ„ด๐Ÿ„ฟ ____ 11 โœ โค ๐Ÿ”ฅ




da sauri Sana ta mike ta nufi Danish ta zube saman guyiwowinta ta rungume shi , ta dan bubuga bayansa cikin sigar rarrashi

rungume ta Danish ya yi ya na fadin " momy , Daddy ba ya so na , he hate me "

Dam Fahd ya ji zuciyarsa ta buga jin Danish ya ce mata momy , shi tun lokacin da su ka fara call din bai lura da ita ba sai yanzu
nan take ya ji jikinsa ya yi wani mugun sanyi , ya tsare ta da ido , a hankali ya sauke ajiyar zuciya , kafin ya ce " I'm sorry Ma " da ga haka ya kashe kiran

Danish na jin kiran ya mutu ya kara sautin kukansa
da sauri Sana ta dago shi da ga jikinta ta na fadin " Baby , please yi hakuri ka daina kukan nan , Daddynka ya na son ka , sosai , fiye da rayuwarsa ma , ka ga ba hannunsa ka tasso ba , shi ya sa bai san ka ba , bai san abun da ka ke so ba , amma bari ka ga idan ya dawo zai dinga daukar ka ku tafi shan ice cream shi da kansa zai dinga kai ka school , ko ba ka so ? "

" ina so " ya fada ya na turo dan karamin bakinsa , hawaye na zubo mishi
hannu ta kai ta goge hawayensa ta na fadin " shikenan , yanzu ka daina kukan nan , mu tafi na yi maka wanka mu konta mu yi barci ko ? "

gyada mishi kai ta yi ta saki wani dan karamin murmushi
murmushi ita ma ta yi kafin ta mike tsaye ta sa hannayanta biyu ta dauke shi , sannan ta juya ta kalli Ma ta ce mata " Aunty , zan je na kontar da shi "

gyada mata kai Ma kawai ta yi , da ga nan Sana ta nufi bedroom din ta ta shiga da shi

sai da ta bar wajen Captain ya ce " Ma , wai ba ki lura da yarinyar nan Danish ya makale mata sosai ba ? like kamar ya san ta sosai , in ita ta na iya boyewa , shi yaro ne ba za iya controling abun da zai yi , kun ga tun da ta zo ya ke makale da ita , har ya na ce mata momy , kuma lokacin da ya gan ta dazu har ya fada jikinta , na ji ta kira sunansa Danish , bayan tun lokacin da ta ke zaune da mu ba wanda ya fadi sunan Danish , duk Baby mu ka ce mishi "

nan fa ya ja hankulansu dan abun da ya fada duk gaskiya ne , tabbas akwai wani abu tsakanin Sana da Danish

cikin nitsuwa Ma ta ce " gaskiya ba na tunanin haka , kamar yadda ka ce Danish yaro ne , bai san abun da ya ke ba , may be a cen gidan mahaifiyarsa akwai wadda ke kula da shi , ya yi tunanin ko ita ce "

da okay kawai Captain ya amsa mata kafin ya tashi ya nufi stair ya Haye , amma cikin ransa ya na da tabbacin abun da ya ke tunani haka ne , tabbas akwai wani abu a kassa dole ya samo ko minene
daya bayan daya su ka fara tashi su na yi wa Ma sai da safe , su ka koma bedroom din su dan su yi barci


โ˜† SANA ๐Ÿงธ โ˜†


Bayan ta shiga bedroom din ta da Danish , kai tsaye saman gadonta ta kontar da shi , ta Haye ita ma ta na kallon shi ta ce " My Baby , kukan ya isa haka , na yi maka irin wassan da mu ke yi a gida ? "

da sauri ya mike tsaye ya na fadin " Eh , Eh , ina so "
murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta zauna bakin gadon , ya karaso ya konta saman bayanta ya zagayo da hannayansa a wuyanta

mikewa tsaye ta yi da shi ta nufi tsakiyar bedroom din ta fara juyawa da shi
dariya sosai Danish ya yi , su na ta juyi , ita ma ta na dariya
sai da ta gaji sannan ta sa hannu ta zagayo da shi gabanta , ta tilla shi saman gadon sannan ta Haye saman gadon ta konta ta na dariya

sai da ya tsagaita dariyarsa sannan ya ce " momy , me ki ke yi cikin gidan nan ? ba Kaduna na baro ki ba ? "

" Uhm , biyo bayanka na yi , ta ya za a raba ni da babyna haka kawai ? na tafi school ina dawowa wai Gwoggo ta ce min ka tafi gidan Daddynka , ba zan iya jure rashin ka ba My baby , shi ya sa na taho ni ma na zauna tare da kai " ta fada ta na daura hannu saman face din sa

( ๐Ÿค”๐Ÿค” Kenan Captain ya tanka dai-dai , Sana ta na da hadi da Danish , sun san juna Sosai , hakan na nufin ba ta yi amnesia ba ? , to minene asalin sunanta ? wacece ita ? me ta zo yi cikin gidan ? ni fa har yanzu ban ga kan labarin ba ๐Ÿ˜ช๐Ÿ˜ช๐Ÿ˜ช )

cike da shagwaba Danish ya ce mata " that's why i love you so much Momy , dama na san ba za ki taba kyale ni ba "

hannu ta kai ta ja mishi hanci ta na fadin " ni ma ina son ka sosai my angel "

marairaice fuska ya yi ya na fadin " amma kin ga Daddy ba ya so na "

" kar ka damu , ba ina nan ba ? bari ya dawo , za mu shawo kansa , ya ji ya na son ka fiye da rayuwarsa , saboda kai ne rayuwarsa , Daddynka ne kuma dole ya so ka , in kuma ya ki na fasa mishi baki "

dariya sosai Danish ya yi har kananan hakwaren su ka bayyana
ita dai ta zuba mishi ido ta na murmushi , sai da ya gama dariyarsa sannan ta kai hannu ta janyo duvet ta rufe su har zuwa kugu sannan ta kashe lamps din dakin ta kunna bedside lamps ta ce mishi " now close your eyes mu yi barci "

" Good night momy " ya fada ya na lumshe idanunsa
a hankali ta kai lips din ta ta manna mishi kiss , sannan ta konta ta kai hannu saman kansa ta na shafawa a hankali har barci ya yi gaba da su


โ˜† UNITED STATES OF AMERICA โ˜†


*WASHINGTON DC*


- FAHD ๐Ÿงธ -


konce ya ke tsakiyar lafiyayen gadonsa , ya na sanye da kayan barcinsa white color
ya zubawa laptop din sa da ke ajiye saman bedside drawer ido
ba komai ba ne ya ke kallo sai dan uwansa , kowane cikin bedroom din sa , duk bedroom din gidan da camera a ciki har bedroom din Sana , kuma duk ya na ganin abun da ke faruwa saboda cameras din na kunne
hakan na nufin duk abun da Sana ta yi ko ta fada tare da Danish duk ya ji su , amma bai yi wani yunkurin ba , asali ma ko motsi bai yi ba da ga konciyarsa

sai su Ashur kuma
shi dai Ashur ya na konce rike da waya a kunne alamun kira ya ke , ga face din sa dauke da murmushi , har da rungume pillow
Abeeram kuma ya na sharar barci , da ga shi sai short , ko lamps din dakin bai kashe ba
Captain ya na zaune bakin gadonsa rike da wayarsa ya na latsawa da alamun aiki ya ke
Talal da Ramadan duk su na barci , su na sanye da kayan barcinsu
Abdoul-Aleem kuma ya na konce tsakiyar gadonsa ya na kallon film cikin laptop d'insa , da alamun irin comics ne dan sai dariya ya ke har da dafe ciki
bangaran Ma , ita ma ta yi barci sai dai ba ya iya ganin ta sosai dan ta kashe lamps din dakin baki daya

ya na a haka kawai na ga magensa ta hayo saman gadon ta na kuka a marairaice
wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya ce " ke sauka min da ga nan , ba na ce kar ki sake hayo min gado ba ? "

wani dan kuka ta yi mai karfi kafin ta sauko da ga saman gadon ta nufi kofar fita dama kofar na bude
a hankali ya dago kai ya na fadin " Snow , ba dai fushi ki ka yi ba ? " ya fada kamar za ta iya jin sa , asali ma ita ta ficewarta

sai da ta fita ya koma ya konta ya ci gaba da kallon yan uwansa
ya yi wajen two minutes a haka kafin ya kai hannu saman bedside drawer ya dauki wayarsa ya kira lambar Captain
ya na kallon shi ta cikin laptop har ya dauki ya dauki kiran ya kai wayar a kunne

cikin nitsuwa ya ce mishi " Ina so ka yi bincike a kan Yarinyar da Ma ta kawo cikin gidan "

dan jinkirtawa ya yi kafin ya ce " Ni kaina hankalina bai konta da ita ba gaskiya , ko ba ta da niyar cutar da mu akwai abun da ya kawo ta cikin gidan nan "
" shi ya sa na ce ka yi bincike a kanta "

" Okay , amma Big bro zan so na yi maka wata tambaya please "
" Uhm " ya fada

sai da ya dauki lokaci kafin ya ce " me ya sa ba ka son Danish ? na ga babynka ne , jininka ne , why ba ka son shi ? "

wani dan karamin tsaki Fahd ya ja ya lumshe idanunsa a hankali
a haka ya sake jiyo Muryar Captain ya na fadin " Please ka fada min , ko ma minene matsalar ka fada min , ba na jin dadin abun da ka ke , Fahd wlh in ka rasa soyayyar Danish a wannan shekarun nasa ka rasa ta har abada kenan , duk irin soyayyar da za ka nuna mishi da ga baya kullum zai dinga tuno wannan kiyayar da ka nuna mishi lokacin da ya ke karami "

ko sannu Fahd bai ce mishi ba ya sauko wayarsa ya katse kiran , ya rufe laptop din sa , ya daura wayar sama sannan ya kashe lamps din dakin baki daya , ya janyo duvet ya rufe jikinsa baki daya


โ–ชUNITED KINGDOM ( LONDON )

โ–ชThe Mayor's Office for Policing And Crime (MOPAC)


Zaune Jimy ya ke cikin office din sa , ya na kallon laptop din sa
ya na zaune a haka Eliot ya shigo rike da wata yar karamar laptop ya na fadin " ka ji abun da ya faru a China ? ni fa ina tunanin gang din nan akwai abun da su ka shirya aikatawa "

wata yar karamar ajiyar zuciya Jimy ya sauke kafin ya rufe laptop din sa ya ce " no ba tunanin gang din Six Butterfly ne , su na sata su na garguwa da mutane amma ban taba ji an ce sun tashi Bomb , kuma har da gawar mutum guda , bayan su har yanzu mutanan da su ka sace su na a raye a hannunsa , akwai wani abu da ya bace mana tabbas

Please Login or Register in order to submit comment